Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun iya kurmanci.
Raihana kuma tana tsakiyar gida tanata kiciniyar tafasa tea da yin miyar asuba,
miyar dege-dege take musu dan Ummi dubu d'aya ta bada Hayatuddeen ya sayo musu hanta da jan nama,
tofa shine aka gyarashi tayi miyar ganyen albasa da yaji kayan miya dana d'an-d'an dan aji dad'in yin sahur.
koda ta gama tafasa tea d'in da tasa citta da kanumfari,
sai ta d'ura a filas kana miyar kuma ta barshi a tukunyar sai ta dorashi saman kanta sannan taja kitchen d'in ta rufe sai da asuban Rahma zata k'arisa aikin.
tana rufe kitchen d'in taje sukaci gaba da hira,
nan Saifuddeen ya bawa Ummi shawarar a hana Aunty Nina girki dan tana laulayin wani cikin,
to shiyasa yake son a hanata girki su had'a tukunyar,
sosai Ummi taji dad'in haka dan itama taso hakan sabida tasan Bappa Ali mutum ne mai kawaici tana sane cutar mijintane ya medasu basu da wasu yawan kadarori.
koda Saifuddeen ya tashi daga nan k'ofan Bappa Alin ya nufa inda ya samu Aunty Nina tana kiciniyar hura wuta a murhun gawayi yayinda shi kuma bappa Ali,
yake ruggume da Qur'an alamun zai fita masallaci.
nan ya gaya mishi shawarar da suka yanke shida Umminshi.
bawan Allah Bappa Ali sai yake jin kunyar wai shi ya kamata yaci dasu ya gaza sai kuma shima su ciyar dashi,
da fari kamar bazai yardaba to dole dai ya yarda dan Saifuddeen ya kafa ya tsare haka ya hak'uri,
sannan suka kama zance tafsir d'in da zasu fara gobe ya jaddawa Saifuddeen ya shirya dashi za'ake zuwa bayan sun gama mgnane ya fita wurin abokanshi.


Salisu ya samu da Mudasir sai Warisu ganin Saminu baya nanne yasa suka raja'a gidan sarki gidansu Saminun kenan,
a d'akin saminu suka yada zongo sunata hira,
har dai dare ya fara nisa kafin suka fito,
Warisu ya shiga gidansu shima Mudassir yayi hanyar gidansu.
Saifuddeen kuma da Salisu tare suke tafiya dan kusan katangar gidansu d'aya ne.
suna isa bakin masallaci Saifuddeen ya zaro biro kana yayi rubutu a jikin takardar daya b'alla.
"Yauwa Salisu dama inaso in gaya maka an rage balance enka ka rink'a bada dubu biyu duk sati,
sai mu rink'a tasowa biyar dai-dai na yamma kafin a kira magrib kuma mun iso dukku kaga zamuyi bud'a baki a gida kuma zamu dena tafiyan dare,
in kuma gari ya waye in yaso ana fitowa masallaci mu tafi tunda ba batun jiran karyawa."
cikin tsananin jin dad'i Salisu ya ruggumeshi tare da cewa.
"Kai Alhamdulillahi wlh ka kawo shawara mai kyau, amman dubu biyu yayi kad'an gsky zan dai bada 4k tunda du-du du dai awa d'aya da rabine aka rage.
Ngd matuk'a Allah bar zumunci da k'auna my friend."
cikin sanin mutuncin juna ya kuma ce mishi.
"No kai dai kabar 2k d'in ai kaima kanada buk'atun kanka dana iyayenmu."
cikin sanin ya kamata Salisu yace.
"To naji na kuma gode, amman gsky 3k zanke badawa kada ka cemin komai."
jin haka yasa Saifuddeen rubuta.
"To Allah ya musu al'barka."
da haka sukayi sallama,

Koda ya shiga gida tuni su Ummi sunyi bacci acewarsu kada suyi dogon hira su zo su makara.

Shima hakance a wurinshi shiyasa yanayin wonka yayi al'wala yazo yayi konciyarshi.


2:00 Am Ummi ta farka kamar yadda Ummi takeyi ko wanne lokaci in dai cikin Ramadan ne,
kana ta bud'e k'ofa ta fito tsakar gida yayinda iska mai sanyi ke kad'awa, babbar taburma ta shimfid'a kana ta fito da wani d'an madaidaicin cainis carpet amman irin na da fa,
ta shimfid'a bisa taburmar kana ta ajiye hijabinta da carbinta da Qur'an sai lantanta mai wadaceccen haske.
al'wala tayi kana kana taje baki k'ofar d'akinsu Rahma kira d'aya ana biyu Rahma ta amsa.
Itako Ummi tana jin Rahma ta amsa ta koma bisa taburmar ta fara nafila,
Rahma kuwa tana tashi ta tada Raihana Raliyya.
sun jima kafin suka tashi,
suna fitowa duk sukayi al'wala kamar yadda aka sabar musu tun basu kai hakaba,
kana sukazo ko wacce tayi iya nafilar da zata iya daga bisani suka fara karatun Qur'an.
Yayinda tuni Saifuddeen ma ya tashi yazo ya tashi Hayatuddeen sun je bakin k'ofar d'akinshi bisa k'aramar taburma ya shimfid'a musu sallaya,
suka fara nafila bayan sun zauna sun fara tilawa ne ba jimawa Hayatuddeen ya fara gyangyad'i yana rab'awa jikin Hamma Saifuddeen d'in nashi tuni bacci ya sureshi shiko Saifuddeen gyara mishi jinginar yayi kana yaci gaba da tilawarshi.

3:20 Am Rahma tayi addu'a tare da shafawa kana ta mik'e ta cire hijabinta ta ninke ta ajiye gefe sannan ta shiga kitchen ruwan zafi ta d'ora bayan ya tafasa ne ta d'an zuba man gyad'a cikinshi kana ta d'ebo couscous dai-dai misali tazo ta zuba kana ta meda marfin ta rufe,
sanan ta harhad'a kofuna tare da pilet da cokula,
ta fitar taje ta jera bisa babbar taburmar,
kana ta dawo ta d'auki filas d'in duka biyu babban da k'aramin,
sannan ta koma kitchen d'in,
bud'e tukunyar tayi tare da duba couscous d'in yayi lugub yadda akeso kuma yayi wasar-wasar bai kwab'e ba amfanin zuba man gyad'an kenan,
sauk'e tukunyar tayi ta ajeshi gefe sannan ta mik'e ta sauk'o dana miyar ta d'orashi kan rushin.
sai ta kuma sauk'o da kuloli guda biyu d'an madaidaci shi ta fara zubawa saida ta cikashi yadda zai iya isar mutun ukuma,
kana ta kwashe sauran duka a babbar kulan,
sannan ta kwashi kulolin ta kaisu bisa taburmar,
tana dawowa ta bud'e tukunyar miyar da sai bol-bol yakeyi sai mai da tsokokin da suka yiwa miyar k'awanya,
tukunyar ta d'auka baki d'aya kana ta d'auki d'an k'aramin kulan miyar,
tana fitowa ta zauna gefen taburmar kana ta kalli Raihana tare da cewa.
"Na mance ban d'auko biredin nan ba,
tashi ki kawoshi yana d'akin Ummi."
to tace tare da mik'ewa ta nufi d'akin.
Ita kuwa Rahma miyar ta saka a k'aramar kulan tare da tsokoki kusan shida kana tasa k'ashi biyu,
sannan ta d'auki k'aramin filas d'in nan ta had'a da kulolin kana ta amshi biredi d'aya a hannun Raihana da ta iso da su a hannunta,
cikin nitsuwarta tace.
"Yauwa Raihana bari in kaiwa su Bappa Ali nasu ke kuma ki sa mana ki sawa d'an uwana." da yake haka take kiran Saifuddeen wasu lokutan
ba musu Raihana ta tsuguna tare da fara zuba musu,
shi kuwa Saifuddeen da sauri ya mik'e yaje ya amshi abincinsu bappa Alin kana yayi mata nunin da ta koma taci abinci bari shi ya kai musu.
To tace mishi kana ta bashi kulolin,
sannan ita kuma ta koma ta zauna kofi ta d'auka tea ta had'a mishi mai kauri ta san ba wani abinci mai yawa zai iya ciba,
bayan ta had'a mishi ne sai ta kuma d'iba mishi couscous d'in tare da sa mushi miyar hantar a d'an k'aramin side soup tuni Raihana kuma ta gama had'a musu nasu a tire,
ta ajewa kowa kofin tea a gabanshi.
bisimillah sukayi tare da addu'a sannan suka fara sahur d'in.
Shi kuwa Saifuddeen koda ya dawo tuni k'arfe hud'u ta kusa gefen Umminshi ya zauna tare da d'aukan kofin tea d'in da Rahma ta had'a mishi ya fara sha,
ido ya lumshe jin k'amshin citta da kananfari da masoro da ganyen na'a-na'a, yana sha yana lumshe ido ko dan dama shi yana son tea yana nan kamar buzu,
ita kuwa Ummi cikin kula tace.
"Babana kaci abincin mana kanata shan ruwan zafi."
ido ya zuba musu yadda suka had'u su duka sunaci a kwano d'aya sai ya tuna mishi da baya, wanda baushe ke cewa kowa ya tuna bara baiji dad'in banaba,
idon ya kuma bud'ewa yana mai tunanin dah
ita Ummi taci da yaranta mata shida Nuruddeen kuma tare sukeci da Abbansu da bappa Ali koda last year haka sukeyi,
sai gashi bana kuna ba Abba ba Nuruddeen bappa Alinma da yake raye baizoba sabida rashin d'an uwanshi,
oh mutuwa wato dama haka abin yake ta rabaka da macecce ta rabaka da rayeyye,
gashi Hayatuddeen yanata baccinsa.
itako Ummi kamar ta gane me yake tunawa sai ta d'an gyara zama sannan ta zare cokalin cikin abincinshi ta saka cikin tiren da sukeci tace.
"To muci tare, kada kayi zurfin nazari gamu Allah ya barmaka mu gashi nanda bad'i kuma zakuyi taci da autana."
ganin ta tsareshi da ido ne kuma in baiciba bazata ji dad'iba yasa ya d'anci kad'an kana ya kuma amsar kofin tea d'in da Rahma take rik'e dashi tana sha kurb'a biyu yayi kana mik'a mata sannan ya mik'e da sauri.
ruwan wonka ya d'iba sannan ya shiga d'akinshi ruwan randar sanyinshi ya d'ansha kana ya d'auko soson shi da makilin da burosh.
a nitse yayi wonkanshi yana fitowa ana kiran assalatu.

Dama tuni su Ummi sun gama sahur d'insu har Raliyya ta tattare wurin.
D'akinshi ya shiga kasan cewar yau jumma'a ace kuma azumine,
shiyasa ya zaro wani tattausan yadi mai sauk'in kud'i fari k'al rigar anyi mata d'inkin zamani anyi d'an aiki da yellow zare, bayan ya gama sa kayan sunyi d'as a jikinshi sai yasa hular zannabukar mai d'an surkin yellown zare sai takalma suma farare masu d'an ratsin yellow.
Sosai yayi wani irin baiyanennen kyau,
wanda gani d'aya zakayi mishi kasan Allah ya masa cikar halitta da haiba, gaba d'aya alamun zarra da tsurar cikekken d'a namiji sunata baiyana a jikinshi tuni muryarshi tayi kauri alamun cikar balaga da d'an dad'ewa,
gwarabanshi suna ta hab'aka yayinda duk wani sashi na jin d'an adam dake iya fidda gashi,
nashi sunata yabanya,
hatta gefen kunnenshi yana ta nuna alamun tsirowar saje,
hakan sharabanshi da singalalin hannunshi da k'irjinshi,
tuni gashin girarshi ta zama d'aya daga cikin abinda ke Jan hankalin mutane ih zuwa ga kallonshi dan gashin girarshi har had'ewa suka bisa karan hancinsa,
hakama gashin idanunshi zar-zar dasu lips enshi kuwa jazir dasu ko yaushe kamar an shafa musu man baki zakaga suna shek'i sirarane sai dai sunada d'an fad'i da taushi dan ko d'an dannesu yayi da harshenshi sai kaga wani wurin ya lotso ya kuma yi fari,
yana kuma janye harshenshi zakaga ya koma janshi,
yatsun hannunshi da sawunshi kuwa suma kansu abin ganine.

Tsayuwa yayi gaban wannan dogon madubin hannunshi rik'e da turare,
feffesawa yayi a jikinshi yadda bazaiji gafinshi a mak'oshinsa ba.
carbi ya d'auka kana ya fita nan ya samu Raihana ta tada Hayatuddeen da Faruq sunyi al'wala,
shiyasa ya tasasu a gaba suka nufi masallacin k'ofar gidan nasu.

Bayan an idar da salla su Hayatuddeen suka tafi gida shi kuma sai ya d'an zauna yayi azkar saida ya gama sannan ya mik'e ya fita a harabar tsank'ayarsu ya samu Salisu na jiranshi.
Dan haka sai yayi sauri-sauri ya shiga gida a tsakar gida ya samesu duk suna ninnike hijaban da sukayi salla dasu,
Ummi kuwa har yanzu carbine a hannunta gefenta ya d'an rusuna kana ya motsa lips enshi a hankali alamun. "Ina kwana?."
"lfy lau Babana har zuku tafi ko?."
tace dashi cikin kula kai ya gyad'a mata alamun eh,
sai ya kuma gaida Adda Rahma kana su Raihana suka gaidashi,
Raliyya kuwa tuni ta har-had'a kwanun wonke-wonke tana wonkewa.
da sauri Ummi tace.
"To Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lfy ya dawo daku lfy." sabida jin Salisu nata danna mishi hon
Amin Amin suka amsa baki d'aya kana ya mik'e ya fita.

Suna isa gombe kamar kullum Salisu ya ajiyeshi kana yaja ya tafi ya fara aikinshi.
Shi kuma cikin masallaci ya shiga,
baccin da baibane ya dan fara fizgarshi haka yasa ya konta,
cikin k'ank'anin lokaci yayi bacci.
8:00 Am ya farka da sauri ya mik'e,
ya fita harabar wurin ruwa ya saya yayi al'wala sannan yazo yayi walaha,
daga nan ya nufi cikin kasuwa.

Yana shiga kai tsaye dilansu ya wuce yana zuwa ko yayi sa'a ba layi sosai tofa nan take aka bashi na 60k ganin bashi da wurin zubasu ne sai yace musu bari yazo,
shagonsu Hisham yaje yace musu kwali yakeso nan take suka bashi yankekken kwalin Gas
yana amsa yaje ya cika kwalin da lododin.
Da shagon ba mishkila ya fara dan yafi kusa dashi kuma yasan me yawa zasu karb'a zasu rage mishi nauyi,
yana zuwa kuma ya samu shagon a cike mak'il da masu sayan abubuwa irin su Gero, kunu gyad'a kunun wake k'osai, waken awara.
Rid'i, sugar, madara, acca, al,kama, masara, maiwa, shinkafa, dawa, fulawa, da dai sauransu a k'alla yaran shagon sun kai goma amman still ga layin masu awu,
d'aya daga cikin yaran shagon ne ya yafitoshi tare mik'o mishi 5k d'in jiyan kana yace.
"Alhaji yace yau na 15k zaka bamu ko?."
kai ya gyad'a mishi kana ya sunkuyo ya rink'a mik'o mushi faket-faket na ledodin hawa-hawa kamar dai yadda yaga Baba Bello ya basu jiya.
Yana basu ya rubuta kana ya bawa yaron shima yasa hannu,
daga nan ya fara bin duk shagunan da Dottijon ya nuna mishi,
inda yasamu wasu basu firfitoba,
sai ya wuce gaba, wasu a dawowa sai ya samu suna bud'e shagun nasu sai ya basu,
yana basu suna bashi kud'in na jiya,
haka dai tuni kafin k'arfe sha d'aya ya gama rabawa,.
Cikin nitsuwa ya koma rumfar dilan nasu inda ya had'a lissafin kud'in ya samu dubu hamsin da shida ne ga 2k d'in da Baba Bella ya bashi jiya nan ya had'asu wuri d'aya 8k kenan.
wato fad'in farin cikin da Saifuddeen yayi a wannan lokacin bazai yuwuba.
Kawai sai yayi sujjada ya godewa Allah gashi yau da ribarshi kusan 8k.
ai cikin aminci da farin ciki ya basu kud'insu 50k dai-dai kana aka d'auko littafi akayi alamar ya biya na jiya sai kuma na gobe 60k cikin tsananin farin ciki yasa kud'inshi a al'jihu kana ya bar shagon da zummar sai gobe.

Tuni kasuwa ta cika tayi tambul sabida yawanci akanzo da sanyin safiya koda maraice sabida yanayin azumi ba'a zuwa da tsakiyar rana.

Bayan ya gama rabawanne
sai ya kuma d'auko botikin pure water inshi ya saro leda d'aya,
dan bin shawaran baba bello amman ina a gari na gombe garin musulmai zakayi yawa har ka gaji cikin kasuwar gombe da wuya kaga arne ba irin kasuwar Yolanmu ba,
ita kasuwar gombe du musulmaine sai yerobawa da terawa kuma duk masallatane bana ce ba kirsoticiba amman gsky basu da yawa.
ganin wahalar banza zaisha sai ya rabawa Al'majirai ruwan.

Shagonsu Jabeer yaje wai ko su d'an tab'a hira amman ina sai ya samu shagon mak'il da mata ba ko hanyar wucewa,
dole ya wuce shagonsu Hisham still nanma shagon cike yake da mata,
gun bayarben nan mai robobi yaje canma kazalika,
koda ya koma shagonsu Kabir mai ruwa kuma sai ya sumu sun rufe wai saida yamma zasu dawo su bud'e.
gefen shagon nasu ya zauna ya lumshe ido yana nazarin to sana'ar me zaiyi,
ya dad'e yana tunani a ranshi yake cewa.
"Alhamdulillahi Allah ban raina sana'ar daka baniba,
Allah kaine mai badawa ka kuma k'arawa mutun ya rabbil izzati ka nunamin wata sana'ar da zanyi mana kar in wuni zaman kare a karofi."
yana gama fad'in haka a ranshi sai ya bud'e idanunshi yana bud'esu ko sai kan wani mai saida omo irinsu Good mama kilin Zep viva sabulun kamaru da dai sauransu.
da sauri ya mik'e yaje ga saurayin mai amalanken kana ya yagi takarda ya rubuta mishi cewa,
shima yana son saida su omon ya nuna mishi inda zai sara,
cikin gatsali da zoleya saurayin yace.
"Hahaha kanada amalanken ne, ko akai zaka d'ora kana da kud'in jarin ne?."
rubuta mishi amsa yayi cewa a kwali zasu bashi zai d'aura a kai.
cikin zolaya ya nuna mishi shagon da suke sari,
aiko yana zuwa sai yaga suma shagon ya kawo musu leda koda ya rubuta wa mai shagon dalilinshi ba b'ata lokaci ya bashi su Omo kan ya saida ya d'auki ribarshi ya kawo mishi uwar kud'i.

Kamar wasa ya aza kwalin su omo yana yawo koro-koro sak'o da luggu,
amman ina ko asi bai saidaba.
har azahar har yayi niyar in yayi salla zai maida musu sai ya kuma fasa,
koda akayi salla sai yaci gaba da zagaye har ya shiga layin yan badaru,
nan aka fara kiranshi ana saya kad'an-kad'an sai gashi kafin la'asar ya saida stab yana had'a kudin yaga dubu hud'u ne kuma kayan 3,500 aka bashi kenan yaci ribar d'ari biyar a ciki dan harda irin manyan nan na 500.
koda ya kai kud'in sai ya kuma amsar wani cikin ikon Allah shima ya saida.
aifa ranar da Jabeer ya ganshi dasu Omo da sabulu ya mishi tsiya wai ko dai aure yake bid'ane.

K'arfe biyar saura ya maida kwalin oman da sauran nan ya samu ribar 200 lissafin ribarshi yau dubu takwas kenan,
hamdala yayi kana ya duba agogon hannunshi ganin biyar saura kwata,
sai ya nufi gaban wani mai dabino,
mudu d'aya ya saya, kana ya fito bakin kasuwar inda yaga mai kankana dasu lemu da ayaba kankana ya saya babba da k'ari kana ya sayi lemun d'ari uku,
duk dai dubu d'aya ya kashe tsakanin dabino da lemu da ayaba,
ganin saura 7 minutes buyer ta cika sai ya gangara gefen masu nama/naman 1k ya saya,
sannan ya sayi su tattasai, albasa, attaruhu, karas, kabeji. da dai sauransu a ta k'aice dai 3k ya kashe kana sannan ya adana 5kbda zummar in ya koma zaiyi musu asusunsu da ban ribar omo d'ari takwai d'innan kuma ya barsu a aljihu ko ya rink'a jin kud'i a jikinshi. biyar dai-da Salisu yazo suka tafi.

Alhamdulillahi sun isa Dukku rana tanayin mudun kuyangi alamun ta kusa fad'uwa.
inda ya samu tuni Rahma sarkin aiki ita da Raihana sun gama komai,
inda sukayi kunun gyad'a mai kyau, da tea daya sha kayan k'amshi sai soyayyan doya daya sha kwai dasu albasa da citta kanumfari onga,
sai kuma tea wanda akayi dan Saifuddeen da Bappa Ali,
kana sai jolof d'in taliya da yasha kifi,
sannan sai biredi da aka soya da kwai sai kuma su dabinon da kankana da ayaba da lemun daya kawosu yanzu.
da sauri Raihana ta amshi ledodin kana ta mik'awa Adda Rahma ledan naman dasu tattasan,
ita kuma ta d'ebo ruwa a roba tare da d'an tarfa gijishi kana tazo wonkesu ayaban da kankanan da lemun kafin ta yankasu kana dabinonma ta wonke,
shi kuwa tuni ya shiga wonka yana fitowa yasa Hayatuddeen yaje ya kira mishi Salisu,
kafin ya shafa mai ya fito har sun taho tare,
kana su Ummi sun gama shirya komai Raliyya ta kaiwa Aunty Nina nata sannan na bappa Ali da ban,
tuni ita kuma Rahma ta had'awa Saifuddeen nashi da abokinshi,
su kuwa duk sunyi al'wala kowa na zaune rik'e da carbi,
yayinda Raliyya ke rik'e da dabino a hannu alamun kiran salla kawai take jira Raihana kuma ruwa tafi bege,
ana kiran salla duk sukayi addu'a kana aka fara bud'a baki,
da sauri Ummi ta rik'e hannun Raihana kana tace.
"Ki fara da dabino kafin kisha ruwa."
da sauri ta amshi dabinon.

Su kuwa Saifuddeen da Salisu dabinon sukaci bayan sunyi addu'a sannan suka sha kankanar da Adda Rahma tayi mata mayafi da garin madara,
saida sukayi gyatsa kana suka mik'e jin ana shirin tada ik'ama a massalacin nasu yasa suka kuskure baki kana suka tafi dan dama duk sunyi al'wala suna fita harbar matsallacin ana...!







By
*GARKUWAR FULANI*


*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 6*


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


```Hukuncin Allah fans one ku na musamman ne a gareni fatana, Allah ya bar zumunci da Ζ™auna a tsakaninmu```

_Littafinga na kuΙ—ine nairanki Ι—ari uku kacal ya biya miki buΖ™ata ,turo katin mtn na 300 ta wannan number 09097853276 ko transfer ta 0005388578 jaiz bank Aisha Garkuwa Aliyu, sai ka/ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276_

free page

Suna isa harabar masallacin suka d'an k'ara sauri sabida tuni liman ya kabbarta.
Bayan anyi salla an idar duk sai kowa ya firfito dan a d'anci wani abu, wasu kuma zafine yasa suka fito sabida babu wuta kuma basu da gen kana in mutun ya wuni da azumi tofa lokacin da kasha ruwa zufa na iya keto maka.

To hakane ta kasance dasu d'in.
da yawa cikin gida suka shisshiga,
haka ma su Saifuddeen da Salisu tare da Mudassir da suka samu a masallacin,
suna shiga Ummi suka gaida kana suka wuce d'akin Saifuddeen inda suna shiga wuta ta dawo,
dan haka cikin farin ciki suka zauna Rahma da kanta ta kawo musu abincin suma tea sukace zasu sha dan haka ta kawo musu kana ta aika musu ruwan sanyi soyayyan doya da kwan sukaci suna korawa da ruwan tea da yaketa k'amshi,
daga nan kuma cikinsu ya cika,
suna cikin hira sukaji an kira sallan isha,
kusan a tare suka mik'e sukaje suka sabunta al'wala a tsakar gidan kana suka nufi woje suna fita suka shiga sahu, bayan anyi isha sai kuma aka fara yin sallan asham.
Suma su Ummi suka sabunta al'wala kana suka fara sallan.

Bayan an idar duk an fiffito ne sai Bappa Ali yacewa Saifuddeen zasufa tafi masallacin fada yanzu zasu fara tafsir d'in dan takwas ta kusa.
Mudassir ne ya kalllesu kana yace,
"Bari inje in cewa Ummi tafa ajiye mana jolof d'innan in mun taso tabsir zamuci dan ni in nazo konciya sai naci abinci."
dariya sukayi mishi kana Warisu dake bayansu yace.
"Anya ko kai bafullatanine Mudassir dan gaskiya fulani basu da yawanci."
Ahmad ne da shima yanzu ya iso yace.
"Yoh ai shi iyamburi ne bakaga yadda yayi k'atoba."
shiko Mudassir shafa cikinsa yayi tare da cewa.
"Me yafi raina."
dariya suka kumayi sai Saifuddeen da yaketa murmushi sai kuma Warisu ya kalli Saifuddeen kana ya kallesu tare da cewa.
"Ni ai ko dan kar inyi k'aton ciki zan yiwa kaina k'aidar ci abinci,
wlh da nasan yadda zanyi in koma kamar Saifuddeen da nayi na koma,
kalleshi komai na jikinshi dai-dai da shekarunsa,
shiyasa yake tafiya da kenshi da k'uruciyarshi,
wlh koda namiji d'an uwanshi in ya ganshi sai ya kuma kallonshi in ka ganshi kamar balarabe ko ba indiye."
cikin kauda kai Saifuddeen ya d'an shafa suman kanshi tare da mishi alamar.
"Kai Warisu in naga wani kyau."
daga nan suka shiga cikin gida bisa taburmar da Ummi ke zaune suka zauna bayan sun gaisane ta kallesu cikin kula tace.
"Ya kamata ace iwar haka kuna wurin tafsir, ku rage yawon dare kun san wannan wata ta musammance ga musulmai."
mik'ewa sukayi da sauri sai kuma Mudassir yace.
"Yauwa Ummi a ajiye mana taliyar nanfa in mun taso zamuci."
cikin jin dad'in had'in kan yaran tace.
"Ba matsala sai kun dawo."
daga nan suka juya har sunje bakin k'ofa tace.
"Ahmad kwana zamuyi ko."
cikin tsiya wasu Salisu yace.
"No Ummi ba kwana zanyiba ai inada yan rakiya."
yana fad'in haka sukayi ca a kanshi wai bazasu rakashi ba.
ita kam Ummi da murmushi ta rakasu.

Bayan sunje suka samu anata taruwa manya da yara da dottab'ai duk an cika can ta wojen gidan sarki kuma wani rumfane da mata ke taruwa a ciki.

Suna shiga duk sukayi gefen da aka ajiye mazaunin malam,
wuri d'aya suka zauna yayinda tuni,
Saifuddeen kuma ya zagaya bayan Bappa Ali da alarammanshi Abdurahman gyara tsayuwarshi yayi gefen d'an agajin dake bayansu Bappa Alin.
shi kuwa Bappa Ali da alarammanshi gyara abin sautin mgnar dake gabansu sukayi tare da d'an sunkuyawa kan Qur'anen dake bud'e a gansu inda bana zasuyi tabsir d'in ```suratul Maedah.```
shi kuwa Saifuddeen ta cikin glass d'in table d'in gabansu yake ganin fuskar Bappa Ali ras har yadda zai gane motsin bakinshi da abinda yake fad'in.
dan haka ya maida hankalinshi bisa bakin bappan nashi.

Bayan anyi addu'a an bud'e taro kana ya kuma jero addu'o'i. gyara zamanshi yayi kana cikin sakekken sauti yace.
"Alhamdulillahi Allah ya kawomu watan Ramadan tun kafin mu shiga cikin tafsirin namu zan d'anyi tsokaci ga yan kasuwanmu."
sai ya kuma d'ago kanshi ya d'an kalli taron

Please Login or Register in order to submit comment