Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shaida mishi cewa gobe iyayenshi zasu zo cikin mutuntaka alhaji Kabirun yace to sai sun zo d'in.

Daga nan Saifuddeen ya wuce gidansu Ishaq yana shiga yayi kicibis dashi da a tsakar gidan,
a tare suka shiga parlour Babansu nan ya samu Ya Rabi'u ya iso, bayan sun gaisane suka tattauna lamarin nan ya sanar musu gobe ma su Bappa Ali zasu zo sundai ajiye zance sai goben.


Washe gari kuwa koda su Bappa Ali da Baba Ashiru suka taho da babban yayansu Samisu yariman Dukku kenan kai tsaye gidansu ishaq suka wuce.
sosai suka samu tarba ta mutuntaka,
suka gaggaisa sannan sukayiwa juna k'arin bayani,
daga bisani suka sa ishaq yayiwa Saifuddeen text cewa sun isofa a ina zasu had'u dasu Alhaji Kabirun.
Yana ganin text d'in ya wuce shagon Alhaji Kabiru d'in ya gaya mishi cewar sun isofa,
cikin kula ya mik'e tare da cewa.
"To muje can gidansu abokin naka sai muyi musu jagora zuwa can gidan Alhaji Sanin."
cikin jin dad'in haka Saifuddeen ya gyad'a mishi kai sannan ya juya yabi bayan Alhaji Kabirun,
motarshi suka shiga kai tsaye suka isa gidansu ishaq sosai Alhaji Kabiru yayi mamaki ganin manyan mutane dan barrister Rabi'u sanannene hakama mahaifinshi baraden Gombe, ga kuma Yariman dukku ga kuma Malam Ashiru da Bappa Ali wanda da ka gansu kaga kamala irin ta malaman addinin musulumci.
bayan sun gaggaisa ne kuma suka mimmk'e suka nufi gidan Alhaji Sani wanda tuni Alhaji Kabiru ya mishi bayanin zuwansu a waya.

G.R.A suka nufa inda nanne anguwar gidan Alhaji Sanin yake,
suna isa mai gadi ya bud'e musu gate ganin tsaleliyar motar ya Rabi'u a gaba wanda Saifuddeen da Ishaq ke ciki a baya Yariman Dukku kuma yana gaba kusa da Barrister Rabi'un,
sai kuma motar Alhaji Kabiru wacce Malam Ashiru da Babba Ali ke ciki Babansu Ishaq kuma na gaba kusa da Alhaji Kabirun,
suna shiga harabar gidan sukayi parking,
suna firfitowa wanni d'an matashi wanda zai kai sa'an su Hayatuddeen ya iso gabansu cikin nitsuwa ya gaidasu,
kana ya kalli Alhaji Kabiru tare da cewa.
"Abba ku shigo ciki inji Daddy na."
shafa kanshi yayi tare da cewa.
"To Sulaiman." sai ya kuma juyawa ya kalli su Babba Ali tare da cewa.
"Bisimillanku mu shiga ciki."
to sukace kana suka biyo bayan yaron da aka kira da Sulaiman ,wanda yake rik'e da hannun Alhaji Kabiru yana cewa.
"Abba ina Isma'il baka zo min da shiba."
dai-dai lokacin kuma suka shiga cikin tamfatsetsen parlour yayinda Alhaji Kabiru yayi sallama tare da cewa Sulaiman.
"Isma'il baya nan ai sun tafi Yola shida Maminshi."
sai kuma yayi murmushi ganin Alhaji Sani ya nufi gaban Babansu Ishaq cikin mamaki yace.
"A a yau inada manyan bak'i kenan kaida kanka Baraden Gombe ai da kayi aike ka kiranima zan amsa kiran."
Sai ya kuma kalli su Bappa Ali dake cikin shiga ta kamala cikin sakin fuska yace.
"Marhabikun ku iso ku iso."
cikin kamala suka zazzauna shi kuwa Alhaji Sani cewa Sulaiman yayi.
"Sulaiman maza je ka kawo musu abin sha."
da sauri yaron ya juya ya fita ba jimawa ya dawo da wani babban tire cike da ababen sha mai sanyi,
sai ya kuma juya da sauri ya fita,
yayinda tuni su kuma suna gaggaisawa,
cikin nitsuwa Sulaiman ya kuma shigowa tare da tire cike da fruits ya ajiye bisa stol dake tsakiyansu,
sannan ya fara ajiye musu gorunan ruwan dana juice sai cup d'ad'd'aya a gabansu.
yayinda tuni su kuma suna tattauna abinda ya kawosu,
sosai Alhaji Sani ya d'auki abin da mahimmanci dan ganin manyan mutane suna cikin lamarin,
nan take yayi musu k'arin bayamin sannan suka bashi kud'in da dama sun taho dasu nan shaidu suka sa hannu,
Barrister Rabi'u da Barrister Salman yayan Saminu kenan Yariman dukku suka rattaba hannu ga manyan shaidu.
A nan take kuma sukayi mgnar hayan shagon da in kayan sun iso zai ajiyeshi.
ba tare da b'ata lokaci ba Alhaji Kabiru ya shaida musu akwai wani shago can k'arshan layinsu amman a luggune,
murmushi Babba Ali yayi tare da cemishi.
"Ba matsala nawane kud'in hayan."
Alhaji Sani ne ya d'an gyara zama tare da cewa.
"Shagunanshi ne ai, in kunaso ku biya kud'in wata shida in kuma kunga ba matsala ku biya kud'in shekara d'aya yadda dai kasuwa ta kama."
Barrister Rabi'u ne ya kalli Bappa da Saifuddeen tare da cewa.
"In dai da hali ku biya kud'in shekara d'aya."
da wannan shawarar bappa Ali ya biya kud'in shekara d'aya,
sannan Saifuddeen yasa hannu a cikin dukkan takardun da ya kamata na company maggi daga nan suka gama komai sannan suka sallami juna a mutunce suka tafi.

Koda suka koma gida kuma Bappa Ali ya fito da sauran kud'insu na hayan filinsu da za'a kafa services ya nunawa Ummi dasu Saifuddeen dan cikinsune ya biya hayan shago,
nan kuma suka tsaida shawarar bappa Alin ya sari kayan abinci tunda dama sana'arsa ce aune-aune.
nan bappa Ali ya fara sari a duk kasuwannin da yake zuwa kamarsu.
Ngalda, bajoga, Nafad'a, Hashidu, dogon ruwa, kiri, Malam Sidi, Kurugu, kumo, Dad'in kowa D'ukul togo. Da dai sauransu.
kasan cewar lokacin Kaka'ace amfanin gona ya nuna so kayan abinci yana araha inda tuni masu kud'i keta sara suna boyewa da nufin sai yayi tsada su fitar to wannan dalilin yasa Bappa Ali fara sara da kekyawar niya dan taimakawa masu k'aramin k'arfi yayi aniyar zai canza salon wannan kasuwancin da ya sara ya ajiye in yayi tsada shi kuma ya fitar ya fara saidawa a farashi mai sauk'i.
to nanfa ya k'ara k'aimin bin kasuwannin k'auyuka yana sarar buhuhhunan su.
Masara, Dawa, Gero, Maiwa, Shinkafa, Rid'i, kalwa, Wake, Gyad'a, da dai sauran kayayyakin abinci,
cikin wata biyu duk ya gama sarin inda ya cika tsoffin d'akunan iyayensu duka biyu da buhunan kayan abincinshi.


Tuni Magginsu Saifuddeen kuma ya isa har an shirgesu a babban shagon da Saifuddeen d'in ya kama haya inda aka cikashi mak'il da katon d'in MAGGI mak'il kana aka ja shagon aka rufe, yayinnda shima burinshi irin na Bappanshi ne.
Ya kuma ci gaba da sana'o'insa da ya saba, yana kula da ahlinshi da ahlin Baba Bello,
yana kuma zura ribar shi a wani sabon asusunshi d'aya saya dan wancan asusun tuni ya cika a cewarsa sai ya cika asusu uku kafin ya bud'esu duka.

Bayan wata bakwai da saran Maggin kenan
Rayuwa taci gaba da gudana yau dad'i gobe akasin haka abu da dama ya faru.

Ana cikin haka rana tsaka Maggin da aka sani a hud'u goma sai gashi yayi gauron zabbi ya koma biyar ashirin kusan ninkin ba ninkin kenan,
yayinda yan kasuwa masu harkan magging da sun samu sun sara suketa farin ciki anata hidimar kasuwa anata hidima.

kusan tsawon mako uku kenan da farashin maggin yayi sama,
wanda yayi dai-dai da cikin tsakiyar damuna ne sama ruwa k'asa ruwa, kayan abinci yayi tsada,
tuni talaka ya fara shiga hau'ula'in rayuwa,
bappa Ali da Saifuddeen kuwa tuni sun fara shirye-shiryen bud'a kasuwancin nasu Yau jumma, kuma tun bayan sallan la'asar aketa zuga ruwa kamar da bakin gwarya,
dole cikin ruwan Salisu da Saifuddeen suka kamo hanyar dukku,
daga gombe har cikin Dukku ruwane yake dukansu tamkar zai jasu ya tafi dasu,
k'arfe shida dai-dai suka isa cikin dukkun sauri-sauri gudu-gudu Saifuddeen ya shiga cikin gida lokacin da Salisu ya sauk'eshi dan har lokacin ana d'an yayyafi irin na alamun ruwan ya d'auke sai yaf-yaf ruwan keyi.
Yana shiga kai tsaye d'akin Umminshi ya nufa dan wannan al'adarshi ce muddin ya dawo ko ruwa ko iska ko dare ko rana sai ya fara shiga inda take ya ganta ta ganshi kafin ya wuce d'akinshi,
yayinda ita kuwa Ummi duk nisan dare bata tab'a iya yin bacci har sai taga dawowanshi, duk ruwa kuma bata rumtsawa sai taga ya dawo.
Yana isa bakin k'ofarta yasa hannu ya bud'e labule,
murmushi yayi ganinta zaune ta zubawa k'ofar idanu yayinda Hayatuddeen ke konce yayi pillow da cinyarta Rahma kuwa na gefenta tana gugan kayan data wonke,
Raihana kuwa nayiwa Ummi kitso,
ajiyan zuciya Ummi tayi tare yin murmushi ganin gudan jininta,
cikin tausayawa Raihana tace.
"Sannu da hanya Hamma Saifuddeen."
kai ya jinjina mata alamun yauwa.
Rahma kuwa ajiye anyone d'in tayi tare da cewa.
"Saifuddeen jeka canza kaya kalli yadda ka jik'e jilik sanyi zai kamaka illah fa."
cikin body language yace da ita.
"To."
sai ya kuma yi musu alamun ina Raliya dasu Faruq."
gane abinda yake nufine yasa Ummi ce mishi.
"Suna wurin Aunty Nina."
kai ya jinjina dan yasan dama su Faruq suna son zuwa wurin Aunty Ninan wacce tuni ta haifi d'anta wanda akayiwa Abba mai suna shiyasa su Rahma ke kiranshi da Abban tuni yaron ya girma har yana rarrafe.

Juyawa yayi ya nufi d'akinshi daga bakin k'ofa ya mik'a hannunshi ya jawo towel inshi dake shanye a kan k'ofanshi, botiki ya d'auka ya cikashi da ruwa kana ya d'auki kondon soson wonkenshi,
ban d'akinshi ya juya ya nufa dan jin ruwan ya d'auke kit.

Wonka yayi fes sannan ya d'aura towel d'in ya fito,
buta ya d'auka yayi al'wala sannan ya shiga d'akinshi mai ya dauka kana ya zauna bakin katifarshi murze jikinshi yayi ciki da woje sannan ya mik'e tsaye ya zaro tattausan boxer inshi fari k'al ya fesheshi da turare sannan ya saka,
yana gama gyara zaman boxer d'in a k'ugunshi ya konce towel d'in ya d'anyi taku biyu zuwa uku sannan ya isa bakin k'ofar wore towel d'in yayi ya shanshi kan k'ofar,
sannan ya juya ya isa bakin 'yar durowar tashi ya zaro farin vest fara kal ya fesa mata turare yasa sannan ya kuma zaro bak'ar jallabiya ya zurata a jikinshi,
sai ya kuma feffesa turaren,
sannan ya matso gaban madubin shin hannu yasa ya gyara suman kanshi da yake konce lib sai shek'i yakeyi wayarshi ya zura a al'jihu sannan yasa takalmanshi dake bakin k'ofa ya fita.

A tsakar gida ya samu su Ummi dasu Raihana da Hayatuddeen suna al'wala,
kitchen ya lek'a ganin Rahma na kwasar abinci,
ganinshi a bakin k'ofa yasa tayi murmushi tare da cewa.
"Yauwa je kayi salla ana idarwa ka dawo yau miyarka nayi tunda naga hadari nasan zaka dawo da yunwa."
murmushi yayi tare da mata alamun tayi sauri ta gama lokacin salla yayi,
sai ya kuma kalli fuskarta ganin alamun saida tayi al'wala kafin tazo ta fara kwasan tuwon shiyasa ya juya ,
ya kamo hannun Hayatuddeen da Faruq da yanzu ya shigo suka nufi masallaci.

Koda aka idar da salla, basu dawo gidaba nan ya zauna da Hayayuddeen da Faruq saida akayi sallan isha sannan suka fito.
a bakin masallacin Saifuddeen ya kamo hannun Warisu sai ya kuma yafito Salisu tare da musu alamun su zo suci abinci,
kasan cewar yanzu su ukune rak suka rage a dukkun dan Ahmad, Samuni, Mudassir, duk suna cikin gombe,

Cikin yamutsa fuska Warisu yace.
"Tab aini bani cin abinci da dare dan wlh kun sani bani son k'iba,
gwara kai Saifuddeen jikinka ba irin nau bane."
Salisu ne ya d'an harareshi tare da cewa.
"Kuma in sha Allah wata rana sai kayi k'iba."
sai ya kuma juyo ya kalli Saifuddeen tare da cewa.
"Ni kam a koshe nake muna dawowa na samu iya shatu tana kwasar tuwo tayi wannan hegiyar koriyar miyar nan tata kad'a kwarya yunwace ta sani cinta dole."
dariyar mugunta Warisu ya mishi tare da cewa.
"Hege ka dai biyewa wannan tsohuwar yaseen sai ta toshe maka kwanyarka da koriyar miyar nan ka zama huhulahu."
yana fad'in haka ya juya da sassarfa ya gudu ganin Salisu zai kai mishi duka,
shi kuwa Salisu hamma yayi tare da cewa.
"Kaga mai jajayen kunnuwa ni zanje inyi bacci saida safe."
daga nan sukayi saida safe, shi kuwa yasa Hayatuddeen da Faruq a gaba suka shiga cikin gida yayinda Bappa Ali ke binsu a baya.

Suna shiga tsakiyar gidan ana dawo da wutar nepa,
kai tsaye d'akin Ummi suka shiga suna shiga ya mik'awa Raihana woyarshi tare da mata alamun taje ta sa mishi caji a d'akinshi,
da sauri ta karb'i wayar kana taje ta jona wayar sannan ta dawo.
tana shiga kuma Rahma ta kalleta tare da cewa.
"Je kitchen ki kawo musu abincinsu."
to tace tare da juyawa ta nufi kitchen d'in,
Ummi kuwa gyara zamanta tayi tare gyara sallayan da take zaune a kai sannan tayiwa Saifuddeen d'in alamun yazo ya zauna,
kai ya gyad'a mata kana yaje ya zauna a gefen damanta Hayatuddeen kuma ya zauna gefen hagunta yayinda Faruq ya zauna gabanta,
Adda Rahma kuma kan gadon ta hau ta kwanta tare yin mik'a sannan ta bugi k'afad'an Raliya da tuni ta fara bacci yayinda Adam ke bisa ruwan cikinta,
a hankali ta bud'e ido,
sai ta kuma yunk'ura ta zauna jin Rahma na cemata.
"Ke tashi kije ki shiga kada kiyi bacci anan ki d'auki Adam ku tafi tare."
Kai ta gyad'a kana ta mik'e ruggume da Adam ta fita ta nufi d'akinsu, tana fita Raihana na shigo musu da abincin.



By



*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 10*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Free page


_Ga masu buΖ™atar sayan littafin turo katin mtn na 300 kacal ta wannan Number 09097853276. Ko ka/yi transfer ta bank ac na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa_



A gaban shi ta ajiye tiren, sannan ta d'an zauna gabanshi kular miyar ta bud'e sannan ta zuba mishi miyar a pilit mai d'an zurfi sai ta kuma bud'e na kulan ta sako mishi malmala biyu duk da tasan da wuya ya cinye d'aya ma,
kolban man shanun da Ummi ke mik'a mata ta karb'a bud'e marfin tayi ta tsulala man shanun mai d'an yawa, sannan ta jawo gongonin dakekken yajin borkonsu wanda yakeda ta k'amshi kanamfari da tafarnuwa d'an kad'an,
spoon tasa ta d'an motso miyar da yake wadace da kifi banda da busasheshen nama dariko kana ga wadacecciyar gyad'a da saida ya bulbulo mai,
robar da ta zubo ruwan wonke hannu ta mik'a mishi,
jawo robar yayi ya fara wonke hannunshi.
Ita kuwa Raihana wani pilet d'in ta kuma d'auka tasa malmala d'aya kana ta zuba miyar a kan tuwon sannan tasa man shanun tare da tarfa yajin borkonon a kai,
sai ta kuma kalli Hayatuddeen daketa yamutsa fuska shida Faruq cikin had'e fuska tace.
"Ku tashi kuci abinci."
Hayatuddeen ne ya zame ya konta tare da cewa.
"Ni wlh bazanci tuwoba na k'oshi."
shima Faruq had'e fuska yayi tare da cewa.
"Shima bazai ci tuwoba."
tura musu pilet d'in tayi tare da cewa.
"Kada Allah yasa kuci, cikina ko cikinku hegun yara sai iyayi da son k'arya talaka yace bazaici tuwoba."
Ummi dai sai ido ta zuba musu,
Rahma kuwa murmushi tayi sanin halin Raihana da gajin hak'uri bata jurar rainin wayo hak'urinta kuma ragaggene,
shi kuwa Saifuddeen gyara zamanshi yayi sannan ya jawo hannun Hayatuddeen da Faruq ya gyara musu zama sannan yasa hannu ya gutsuri d'an k'aramin loma tare da dandalo miyar sannan ya mik'awa Faruq wanda shi biyewa Hayatuddeen yake bawai baison tuwon har haka bane, bud'e baki yayi da sauri dan yana matuk'ar jin dad'in yaga Uncle inshi na bashi abinci a baki,
murmushi Saifuddeen yayi sannan ya kuma gutsuro loma ya dandali miya ya mik'awa Hayatuddeen dake zuzzumbura baki,
a hankali ya bud'e baki ya amsa dan dama muddin Hayatuddeen yaci tuwo tofa sai dai in Saifuddeen ne ya bashi da kanshi,
cikin lashe baki Hayatuddeen d'in yace.
"Adda Rahma miyar tayi dad'i yaseen kinfi Adda Raihana iya girki."
dariya sukayi baki d'aya yayinda tuni Raihana ta hatsala ta kai mishi bugu wanda ya kauce ya rab'a jikin Umminshi,
ita kuwa Raihana mik'ewa tayi ta fita ganin Saifuddeen ya sauya fuska,
shiko Saifuddeen loma ya kuma gutsura ya d'an dandali miyar da taketa nason man shanu da man kuli yasa a bakinshi,
idanu ya lumshe dan jin d'and'anon miyar nasa yawun bakinshi tsinkewa,
tabbas yasan yan uwanshi sun iya girki ko dan gada sukayi wurin Umminsu.
daga nan yaci gaba da basu abinci, yana basu yanaci, saida sukaci sukayi hanik'an sannan Adda Rahma ta tattare filin,
ganin Faruq ya fara hamma yasa Ummi ce musu.
"Maza ku hau gado ku kwanta saida safe."
da sauri suka hau suka konta tare da yin addu'a,
shi kuwa Saifuddeen alama yayiwa Adda Rahma da taje ta kira Bappa Ali,
kasan cewar tana ganewa yasa ta juya ta nufi side d'in Bappa Alin.

ita kuwa Ummi ta fito da asusun Saifuddeen duka uku dan ya mata alamun ta fitar dasu.

Ita kuwa Rahma da sallama ta shiga d'akin Aunty Nina wacce take yiwa Abba nabkin cikin kula ta zauna gefenta tare da karb'an yaron taci gaba da sa mishi kayan sanyin dake gefensu cikin sanyinta tace.
"Anty Nina Saifuddeen ke son mgna da Bappa Ali,."
mik'ewa tayi tare da cewa.
"To bari in gaya mishi."
to tace sannan ta fara kiciniyar sawa Abba hula shi kuwa sai zillewa yakeyi.
Ita kuwa Aunty Nina tana zuwa turakan Bappa Ali tace.
"Malam,
Saifuddeen ke son Magna da kai."
kai ya jinjina tare da cewa.
"To gani nan zuwa."
daga nan ta juya taje ta gayawa Rahma da tuni ta gama kimtsa Abba,
mik'ewa tayi tare da bata yaron sannan ta fita ta tafi.

Tana shiga ba jimawa shima bappa Ali ya shigo da sallamarshi,
kan kujera ya zauna yayinda suna fuskantar juna dasu Saifuddeen,
pepar da biro Saifuddeen ya matso dashi kana yayiwa Rahma nuni data zauna ta harhad'a kan kudad'en asusun da suka farfasa shida Ummi suka juyesu bisa k'aramin sallayar Hayatuddeen.

Gyara zama yayi sannan ya fara rubuta mishi abinda yasa ya kirashi.
"Bappa Ali kar dai har kayi bacci na tasheka?."
kai ya jujjuya tare da cewa.
"A a banyi bacciba Saifuddeen dama nima inason mu tattauna."
murmushi yayi tare da rubuta mishi.
"To dama tun last two weeks nace ma maggi yayi tsada ko yayi ma fiye da yadda aka zata,
to shine nake son in sanar maka muyi shawarar yadda zamu saida,
sai kuma batun ribar ledodin da nike saidawa ina sawa a asusu to shine wannan yanzu muka fasa asusun."
ita dai Ummi tana saurarinsu yayinda ita kuwa Rahma taketa had'a kud'ad'en in ta had'a dubu tara sai tayi musu d'amara da cikon na goma kana sai ta ajiyesu.

Shi kuwa bappa Ali cikin nitsuwa yace.
"Eh lallai farashin Maggi ya k'aru sosai, ga kuma na kayan abinci ma ya k'aru matuk'a buhunan wake da na saya kan dubu 12 yanzu ya zama 30k ake saidashi, masara dubu 8 na sassaresu gashi yanzu sun koma dubu 15 ,
Kalwa na sayeshi buhu dubu tara-tara to gashi yanzu buhu dubu ashirin da biyar,
gero na sayeshi buhu dubu bakwai yanzu ya koma buhu dubu sha hud'u.
Gaba d'aya kayan abinci sun tsefe sunyi tsananin tsada talaka na fama da yunwa manoma sun saidashi tun yana araha gashi yanzu zasu dawo suna sayanshi da tsada kuma a yanzun suke fama da noma damuna tayi zurfi sama ruwa k'asa ruwa,
to dama na ajiyeshi ne kan haka yanzu zamu san yadda zamuyi mu sakeshi da araha yadda talaka zai samu sauk'in saya."
cikin jin dad'i Ummi tace.
"Madallah da mai zuciyar imani inama ace duk masu dama da kud'i suna haka to tabbas da masu sayanshi dan muguntar sai yayi tsada su fiddashi da sun bari."
shima Saifuddeen murmushi yayi cikin jin dad'in yanaga zasu samu damar taimakawa marasa k'arfi ya rubuta musu.
"Yauwa Bappa Ali wannan abu yayi kyau,
Magging ma dole zamu sake fara shinsa dan talaka ya samu yadda zaiyi."
jinjina kai bappa Alin yayi tare da cewa.
"Yauwa to muga ya lissafin zaiyi,
kaga lokacin dana sai wake ana saida mudun akan d'ari da goma,
kaga yanzu kuma ana saida mudun akan d'ari biyu da saba'in,
to Alhamdulillahi dama ana kasuwa dan ribane,
dan haka mu zamu rink'a saida mudun wake akan d'ari da talatin, mudun gombe kenan mudun kano da sauran garuruwa masu amfani da kwanon sha kuwa in munyi kiyasti da kud'in mudunmu zamu saida musu mudun akan d'ari biyu da settin
sab'anin sauran mutane dake saida mudun akan d'ari biyu da saba'in a mudun gombe mai cin gongoni takwas zuwa tara
kaga ko wanne mudu minbi ribar naira ishirin kacal fatanmu Allah ya musu al'barka ya kuma sa kasuwar ta d'aure."
wasu zafafan hawayen farin cikine ya rufe Ummi dan tana ji a jikinta ahlinta masu cikar imanine da zarra.
Shima Saifuddeen murmushi yakeyi da godewa Allah da tsarkake mishi zuciyarshi data ahlinshi,
shi kuwa bappa Ali ciga yayi da cewa.
"Lokacin dana sarin kayan mudun masara naira 100 ne yanzu kuma mudun ya koma d'ari da tamanin,
to mu zamuke saidashi bisa d'ari da ashirin munyi ragin naira sattin akan farashin sauran mutane munbi ribar naira ishirin."
sai ya kuma gyara zamanshi tare yi mishi lissafinsu dalla-dalla gaba d'aya sun karya farashin kayan abincin nasu inda suka rink'a bin ribar naira ashirin-ashirin kacal,
sai a buhunan kalwa da rid'ine, sukaci ribar naira hamsin-hamsin a kan ko wanne mudu,
dan shi ba kayan abinci bane baya zama dole sai mutun ya saya musammam rid'i wanda shi kamfanunnuka ne ke sayanshi ana fiddashi k'asashen k'etare.
inda suka tsaida farashin sari kuma akan buhun shinkafa sharshera sun sayeta dubu tara to yanzu ana saidata dubu sha shida to su dubu goma sha d'aya suke saidata sukanbi ribar dubu biyu a cikin ko wanne buhun shinkafa.
Rahma da kanta ajiye irgen kud'in tayi ta zuba musu idanu domin tabbas tasan k'anin mahaifinta ya cika adalin malamin d'an kasuwa,
shi kuwa bappa Ali gyara zama yayi yaci gaba da cewa.
"Gero da dawa duk ribar dubu bibbiyu zamubi akan ko wanne buhu sab'anin sauran mutanen dake bin ribar dubu bakwai da d'ari biyar-biyar.
Sosai sukaci gaba da lissafin inda a cikin ko wanne buhun rid'i da kalwa suka bi ribar dubu biyar-biyar sab'anin wasu dake bin ribar dubu goma sha d'ad'd'aya.

Saida suka gama lissafin kab sannan ya gaya mishi yawan buhunan ko wanne abu inda buhunan masaransu kawai sun kai d'ari da biyar
sai buhun gyararriyar shinfaka mai cin mudu tamanin inda ake saidashi dubu talatin so su kuma sun barshi kan dubu sha bakai sunci ribar dubu uku cikin ko wanne buhu,
nan suka kiyasta komai,
sannan ya karb'i takardar da Saifuddeen ke mik'o mishi inda yake ce mishi.
"Duk cikin katon d'in maggi akwai ribar da ta kusa uwar kud'in,
sabida MAGGIN naira goma ya koma d'aya rak za'a k'ara ya koma ashirin,
to ribar tayi yawanda talaka shine da wuya,
dan haka sai nayi tunanin mai zai hana mu mu rink'a saidawa uku goma tunda dama hud'u gomane mu rink'a bin kwaya d'ad'ad'aya,
sannan ana saida ledan akan d'ari biyu da hamsin a da can wota bakwai baya yanzu kuma ledan ya koma d'ari hud'u dai-dai shine nace to nawa ya kamata muke sakin ledan?."
murmushi Bappa Alin yayi dan ganin umarninshi Saifuddeen ke jira cikin nitsuwa yace.
"Kabi riba kad'an mai al'barka kabar ko wanne leda akan d'ari biyu da saba'in kaga ai dama can hamsin d'in sama ribar tasuce a company a d'ari biyu ake basu.
Kaga kuma kai a kasuwane in ka sakeshi da yawa abokan kasuwancinka zasuji haushinka zasuga zaka kashe musu kasuwane hakan kuma zai iya jaza maka matsala shiyasa badon hakaba da d'ari biyu da hamsin d'in zaka saidashi ko ya kuka gani Hajia Ummi."
kai ta jujjuya mishi cikin jin dad'i tace.
"Allah dai yasa Alhaji Ali Allah ya sa munada ranon zuwa makka da madina birnin ma'aiki."
Amin Amin sukace baki d'aya sannan taci gaba da cewa.
"Wannan ai mgnar ta uba da d'anshi ne ni saidai in sanya al'barka ina kuma nema muku tsari a wurin rabbil izzati."
gyara zama Saifuddeen yayi tare da rubuta musu.
"Eh hakanma yayi Bappa Ali amman kada ka damu ni zanbi hamsin d'in a cikin ko wanne leda,
shagunan zanbi in musu talla in zasu sara zan basu a farashin da d'in amman suyi min al'kawarin saidawa

Please Login or Register in order to submit comment