Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shida ashirin sab'anin biyar ashirin d'in da suke saidawa,
kaga zai zama uku goma kenan,
ni zanbi k'aramar ribar,
a dai wannan sarin in yaso a sari na gaba in naga hakan bazai yuwuba sai inbi sahunsu tunda nima dole da tsadan zan sara."
sosai suka gamsu da wannan shawarar suka k'ark'are komai aka gobe in yaje zaiwa su Alhaji Kabirun tallan.

Shi kuwa bappa Ali cikin nitsuwa yace.
"Dole zaka ci gaba da rik'e shagon nan da aka ajiye maggin,
lokaci yayi da zaka samu sauk'in wahala,
zamuje a gyara kayayyakin in an samu wasu sun sara to sai a samu akori kura a cikata da kayayyakin abincin ta kai shagon sai a fara saidawa."
cikin gamsuwa Saifuddeen ya rubuta musu.
"Hakan yayi shike nan kuma nasan Warisu zai kular mana da komai,
zan kuma yiwa ba mishkila talla nasan zai sara kuma zai bari a farashin da zamu bari dan nasan shi adalin d'an kasuwane mai imani".
sosai sukaji dad'in wannan zaman nasu,
yayinda tuni Rahma taketa famam irga kud'in ganin ta kusa gamawa ne yasa duk suka zuba mata ido dan suna jiran suji nawane kud'in.

Minti hud'u tsakani ta d'ago kanta tare sauk'e numfashi cikin sakin fuska da sanyin muryarta tace.
"Kud'in dukansu dubu d'ari uku da tamanin da biyar ne kud'in baki d'ayansu."
sosai yawan kud'in ya basu mamaki sai dai kuma idan suka tuna kusan tsawon shekara d'aya kenan yake tara kud'in da iriyar azaba da hawala da yake sha ruwa da iska zafin rana da wahala sai suga wahalarsa tama zarta kud'in,
amsarsu Bappa Ali yayi tare da mik'awa Ummi yace tasa musu al'barka cikin murmushi tace.
"Allah ya sanya musu al'barka."
Amin Amin sukace baki d'aya kana Bappa Ali ya kalli Saifuddeen cikin kula yace.
"To ga dai kud'i su kuma me zakayi dasu?."
gyara zamanshi yayi tare da tonk'oshe k'afafunshi ido ya d'an lumshe sannan ya rubuta musu.
"Duk shawarar da kuka bada hakan za'ayi."
da sauri bappa Ali yace.
"A a ka gaya min me ka shawarta kaida zuciyarka?."
kanshi ya d'an sunkuyar sannan ya rubuta musu.
"Dama ni tunanin da nayi, machine d'in Salisun nan ta tsufa yanzu wahal dashi kawai takeyi shiyasa ko balance d'in da keret yake had'a 1,500 gashi yanzu ya fara karatu yana buk'atar kud'i to shiyasa nayi tunanin ko zan saida tsohuwar sai in in saya s mishi sabuwa,
zaifi jin dad'in aikinshi zai samu yadda zai kula da ah'linshi da karatunshi muma kuma balance d'in zai taimakawa cefenen gida na yau da kullum."
sai ya kuma yi shiru ya zuba musu idanu
ganin suma shi suka zubawa idanun alamun sun gamsu da bayaninshi suna kuma son jin k'arshen mgnar,
sai ya d'an had'e yatsunshi tare rubuta musu.
"Sauran kud'in kuma inason zanci gaba da karatuna,
zan yi idimar karatun kama da hidimar sharan fage da saurauran hidimomi na sabbin d'alibai da suke harin zuwa jami'a dole in samunda su Jamb waec da Neco to dole akwai kashe kud'i."
Rahma ce ta fara yin Magna cikin jin dad'i tace.
"Alhamdulillahi burin Ya Seyo zai cika,
yayi kyau naji dad'in haka."
Ummi kuwa cikin sanyi tace.
"To ya zakayi da kasuwancin naka kuma?."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Raba leda ba wuya cikin awa uku ana hud'u nake gamawa,
sannan akwai uzuri tsakanina da abokan kasuwancin na in banje bama ana rabamin kinga kwanaki da banda lfy ma Jabeer ne ya rarrabawa costumes d'ina,
kinga duk lakacin da bani da darasi inada damar kasuwanci na,
sai dai cinikin pure water dasu omo nane zaiyi k'asa."
cikin bada k'arfin guiwa bappa Ali yace.
"Hakan yayi Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a.
ni kuma in sha Allah daga gobe zan fara d'aukan Warisu zan fara nusar dashi da koya mishi harkan awu da sanar dashi farashin sari da sayan d'ad'd'aya,
dole in koya mishi awun kanshi gudun kar yaje yayi ta tauye mudu."
sosai dai suka zauna suka tattauna yadda komai zai tafi,
shi kuwa Saifuddeen dubu d'ari ukun ya ware kana ya d'auki na saman ya rabawa Ummi da Bappa Ali dubu goma-goma,
ya bawa su Rahma da Aunty Nina dasu Raihana dubu biyar-biyar,
Su Warisu, Saminu, Salisu, Ahmad Mudassir, kuwa duk suma dubu biyar-biyar ya ware musu shi kuma yasa saura a al,jihunshi.
da zummar zai bawa Jabeer da Hisham dubu biyar-biyar sai ishaq inshi dubu biyar shima.

Inda yasan machine bajat zataci kusan dubu d'ari da ashirin,
saura kuma zai ajiyesu dan hidimar karatunshi.

Da haka dai sukayita hira sai har kusan shabiyu na dare sukayi saida safe kana duk suka mik'e kowa yayi makoncinsa zuciyarshi cike da farin ciki.

Washe gari kamar yadda suka tsara hakan Saifuddeen yayi ya tallatawa su Alhaji Kabiru Maggi ba musu kuma suka amince dan ai sune da riba mai yawar,
yayinda Alhaji Sani kuma yaketa taraddadin shigo da yaron cikin harkarsu a cewarshi karfa ya lalata musu kasuwa so amman ya amince da tsarin,
nan take suka buk'aci daya basu account number inshi,
Allah sarki Saifuddeen sai yau ya tuna da wata abba tashi account number shi dan shi tun last year bayan s Ya Rabi'u ya aiko mishi woya da ishaq ya matsa mishi dole sukaje suka bud'e account number d'in da shi a lokacin yanaga account d'in baida wani amfani,
dan babu ko sisi a ciki in bada wanda ya bud'e dasu babu ko asi a ciki dan shi lokacin yafi ganewa asusunshi,
murmushi yayi jin dad'in ya haddace komai na account d'in a kanshi,
nan take ya basu account number,
inda sukayi sallama da cewa sai gobe zasu tura mishi,
inda sun saye kashi biyu cikin kashi uku na kayan.

Daga wurinsu kuwa wurin Bello ya nufa na shagon ba miskila nan yayi sa'a ya samu ogon nasu ya mishi bayanin komai,
cikin farin ya amince nan take suka tsadance suka kuma ajiye farashinsu dai-dai dana juna,
inda ya koka mishi da zai samu yana son ya ara mishi d'aya daga cikin yaran shagonshi dan yaje ya kyautata awun yaran shagonsu tunda su sabbin shigane,
cikin aminci da mutunci da kamala da cikar imani ba kyashi bare hasada ba miskila ya amince inda yace Bello zai koma ya kula da lamarin shagon su Saifuddeen nan ya gayawa Saifuddeen farashin yadda yake sallaman yaran shagonsu a kullum da kuma k'arshen wata,
shima Saifuddeen ya amince duk da yawan kud'in yasan wannan shine adalcin da ubangida zaiwa yaran gidanshi gudun kada su zama masu zagon k'asa.

Daga nan ya shirya yaje makarantarsu yayi cuku-cukun komai daya dace dan ci gaba da fafutukar neman damar shiga jami'ar G.S.U.

Shi kuwa Bappa Ali a ranar ya fara nunawa Warisu harkan kasuwancin inda yaji dad'in haka sosai, dan ko ba komai zai samu damar kula da kanshi da ah'linshi.

Washe gari kuwa saiga Saifuddeen yanata ganin ruwan miliyoyi a account number inshi,
wanda Alhaji Sani Da Alhaji Kabiru da ba miskila suka turo mishi,
a ranar su Alhaji Kabiru suka kwashi kayan maggin da suka sara a wurin Saifuddeen suka kai sito insu.

Bappa Ali kuwa ya nemi akori kura guda biyu yasa aka lodawa ba miskila kayan daya sara a d'aya motar,
d'ayar kuwa yasa aka loda wanda zasu ajiye a shagonsu,
nan aka tafi da Warisu da Bappa Alin bayan yan gama sassauk'e kayan ko wanne an ajiyeshi a muhallinshi,
sai Bello da da Warisu da Bappa Ali suka tare a shagon su Ssifuddeen d'in nan suka k'ara kimtsa komai sannan bappa Ali yayi musu nasiha da suji tsoron Allah su kyautata awun mudunsu, nan kuma sukayiwa shagunan layinsu ihsani da kayan abinci dama duk wanda yazo gilmawa ta gaban shagon nansu,
hakan yasa a take duk layin nasu suka san da shagon dan sanadin bada ala koron.

Wasa-wasa kasuwa dai nata d'an tafiya,
sai dai yawanci masu sarine ke saya,
dan masu sayan d'ad'd'aya basu fara sanin shagonba tukun,
tuni kuma masu dattin zuk'ata sun fara suka suna wani cewa.
"Yoh aiyi dai mu gani, nanda yaushe wai maye yayi amarya tuni zai lamushe abarsa,
sabida wasun gani suke Saifuddeen yazo da wani salo na kashe musu kasuwa da hanasu riba mai yawa,
to dama in ubangiji yayi niyar d'aukaka d'an adam a bakin masu hasada zai d'aukakashi tuni masu hasadan dake k'ananun Magna ne yasa kasuwar gombe ta cika da batunsa inda kamar da wasa suka rad'awa shagon dama layin suna wai ,
*ALHAJI BUTU* wai alhajin araha kenan,
abu kamar wasa sai ga sunan shagon dama layin ya zauna hakan.

Cikin mako uku kasuwanci yaci gaba da gudana,
yayinda Ssifudddeen kuwa har yau bai fasa tallan ledanshi dasu omoba,
ana kuma ta shirye-shirye fara WAEC.

Sun gama zana exam d'in WAEC, hakama NECO tuni kuma ya zana JAMB inshi bayan wasu makonni sakamon jarrabar na Jabm ya fito inda ya samu 220 kuma Alhamdulillahi waec da neco d'inma result yayi kyau matuk'a gaya.

Bayan wata hud'u, tuni Saifuddeen ya samu nasarar zama cikekken d'alibi a Gombe state university.

Warisu da Bello kuwa sosai kasuwa take tafiya dai-dai da yanayin cinikin sabbin shaguna masu araha,
a dai-dai lokacin ne kuma komai na kayan abinci ya dawo gida a hannun manoma,
tuni masu hannu da shuni sun fara rige-rigen saye kayayyakin abincin dan b'oyeshi sai yayi tsada su fiddoshi.

A kuma dai-dai lokacin ne company layin Mtn suka kuma biyansu kud'in hayan filinsu da suka kafa services nan suka had'a kud'in suka rub'anya jarin kayayyakin abinci da bappa Ali zai sararo musu.

Kamar bara haka banama bappa Ali da Saifuddeen sukayi,
bayan sun harhad'a cinikinsu suka ware asalin uwar kud'insu sannan suka ware tarin ribar da suka samu na gefen maggi da kuma sauran kayayyakin abincin da kud'in hayan fiinsu Alhamdulillahi kasuwa kuwa tayi Al'barka dama ance kad'an mai al'barka yafi mai yawan da akasa dan zalumcin,
ware kud'in sukayi na maggin jarin da ribar wanda ya basu million uku ,
sai suka rabasu suka kuma saran maggi million biyu,
sannan suka d'auki million d'aya suka sari 'yan kayayyakin masarufi kamarsu,
spaghetti, macaroni, indomi, sugar, fulawa, da buhunan madarar awu ajiniyo moto, suka had'a da sarin maggin nasu.
Sai kuma suka had'a jari da ribar kayan abincin dana hayan bappa Ali ya fara bin kasuwannin k'auyuka yana sari babu kama hannun yaro,
saida ya cika d'akunan iyayensu mak'il ,
sannan ya fara sara yana sawa Warisu na kaisu kasuwa cikin shagonsu tuni shago ya cika mak'il,
masu sari sukayo musu caa ko yaushe kazo bakin shagon zaka samu dafifin mutane mata da maza manya da yara,
ganin haka yasa Saifuddeen fasa asusunshi na wata hud'un ya fito da kudad'en suka sari buhunan al'kama da acca suka had'a a ciki.

Nan fa kasuwa ta d'auka sosai da batun shagon Butu da yawa suna son sanin asalin mai shagon kuma sun gaza ganewa,
dan wasu kance ai shima wannan shagon butun reshen shagunan Ba miskila ne da yawa kuma suna yarda da haka ganin babban yaron shagon ba miskilan a shagon butun Bello kenan,
wasu kuma na cewa shagon Bappa Ali ne, wasu ko na cewa na Warisu ne,
sam dai mutane basu gane sahihancin zancenba sunata kame-kame dai,
Saifuddeen kuwa time to time yake lek'a shagon.

Salisu kuwa sosai yake jin dad'in sabuwar machine d'in da Saifuddeen ya saya mishi inda yaketa karatun shi a F, C, E Gombe.

Su Ahmad da Mudassir kuwa Karatu yayi nisa hakama Salisu,
tuni Saminu kuwa sune masu gama wannan shekaran.

Yayinda Saifuddeen kuwa sune 'yan level 100.

Bayan shekara d'aya, kasuwa taci gaba da gudana komai yana tafiya dai-dai da tsari na taimakon talakawa da marasa k'arfi.
Kullum jarinsu habaka yakeyi da d'an riban da suke bi da kuma kud'in hayansu,
inda kayan masarufi yake mallakin jarin Saifuddeen ne halak d'inshi ba surkin kud'in gadonsu.

Yau kusan wata d'aya kenan Saifuddeen da Bappa Ali sunata kan harhad'a cinikinsu na tsawon shekarar suna ware ribar su da hauhawar jarinsu.
Koda suka gama had'e komai sai suka fara ware hak'insu Bello da Warisu sunka biyasu biya mai daraja a matsayinsu na masu kula da kasuwancin,
daga nan kuma suka ware adadin zakkar da zasu fidda na shekarar bayan sun gama ware zakkar tasu,
sun bawa wad'anda shariya ta misalta da a basu sai kuma suka fara shirye-shiryen sari tako wanne sashi inda Bappa Ali zai sarar musu kayayyakin abinci a kasuwannin k'auyuka kamar yadda suka saba,
shiko Saifuddeen zai yi musu sarin kayan masarufi wanda wasu direct daga company yake musu sarin shiyasa suke samun damar sakin farashinsu da rahusa,
dole zuwa yanxu sunfi k'arfin shago d'aya hakan yasa suka nemi k'arin hayan wani k'aton shagon dake kusa da nasu, ba b'ata lokaci aka basu da yake na Alhaji Kabiru ne,
cikin kwana uku aka had'a shagunan sannan aka barsu da k'ofofi biyu.

Ya Adnan kuwa tuni ya isar da batun soyayyarshi da Adda Rahma ga manya tuni mgna ta kankama dan iyayensu Adnan sun san nagartar Rahma tunda a gabansu ta girma shiyasa basuyi wata rigimaba,
tuni antsaida ranar aurensu bayan sallan layya da mak'o d'aya.

Saminu kuwa ya gama karatunshi har ya samu damar tafiya bautan k'asa mgnar sosayyarshi da Raihana kuma tanata kankama har iyaye sun shiga,
an bari a kan cewa sai ya gama bautan k'asanshi ya fara aiki sannan ayi musu auren.

Mudassir da Ahmad da Ishaq ma duk sun kusa gamawa.

Hayatuddeen kuwa shima yana shekararshi ta k'arshe a primary school,
Faruq kuwa yana primary 3 Adam na primary 2,
Raliyya kuma tana SS 1.

Abba yaron Bappa Ali shima ya girma har an yayeshi.

Rayuwa dai taci gaba da gudana cikin nasara da ci gaba.

Anyi bikin Ya Adnan da Rahma lfy an watse lfy,
ta tare a gidanshi dake cikin Gombe wanda yake cikin jerin gida jan ma'akatan lfy na Medical Center Gombe,
wannan had'i yayi matuk'ar yiwa Ahmad da Mudassir dad'i dan dama a gidan Ya Adnan d'in suke sukewa kansu girki a cewarsu yanzu sun huta sun samu mai musu girki.

Bayan bikin da mako ukune Ya Adnan yaje har dukku da batun yana son a basu Faruq da Adam a cewarsa zai rik'esu,
to Ummi dai tak'i amincewa ganin ya tasa gabata da magiya ne yasata ce mishi Saifuddeen ne ya hana ba itaba kuma shi yana can gomben,
jin haka yasa Ya Adnan tura mishi text cewar,
yana son ganinshi gobe, yana ganin text d'in ya maida mishi amsa da to Allah ya kaimu.
daga nan Adnan ya sallami Ummi ya tafi gidansu a nan ya wuni sai da yamma ya koma.

Washe gari da safe Salisu da Saifuddeen ko breakfast basu tsaya yiba suka wuce cikin gombe,
kasan cewar basu da lectures da wuri sai zuwa k'arfe biyu so kai tsaye gidan ya Adnan suka nufa,
a harabar gidan Salisu yayi parking,
sannan suka nufi bakin mashigar ainihin cikin gidan,
a bakin k'ofa suka tsaya door bell suka d'an danna,
jim kad'an aka bud'e k'ofar ganin Ahmad ya bud'e musu k'ofar ne yasa su yin murmushi shima murmushin yayi tare da bawa Salisu hannu tafawa sukayi cikin salon gaisuwa ta abokai da suka shak'u da juna,
sai ya kuma juyo ya d'aga hannu alamun zai tafa hannu da Saifuddeen da k'arfi irin yadda yayi da Salisu,
shi kuwa Saifuddeen ganin haka yayi saurin janye hannunshi tare da rab'awa gefenshi ya wuce yayi cikin parlour,
cikin dariyar shek'iyanci Ahmad ya kalli Salisu da shima dariyar yakeyi, sai ya kuma juyo ya kalli Saifuddeen da tuni ya isa tsakar parlour suna ruggume da juna shida Mudassir, dariya ya kumayi tare da cewa.
"Hege mai d'an karen son jiki da tsoron wahala."
cikin dariya Salisu yace.
"Yaseen gskyanshi nima d'in ai bani kuma yarda ka kima min wannan hannun naka, kalli yadda hannuna yayi jazir hege mai suffar samudawa."
duka ya kaiwa Salisu,
da sauri ya kauce tare da cewa.
"Wayyo Ya Adnan kaga Ahmad ko."
da sauri Rahma ta yunk'ura zata tashi ta fita jiyo muryar Salisu tasan sarai da Saifuddeen suka zo.
Shi kuwa Ya Adnan da sauri ya jawota jikinshi tare da cewa.
"Ina zakije?."
fuska ta d'an marairaice tare da cewa.
"Parlour zanje kaji su Saifuddeen sun zo."
ido ya d'an kashe mata tare da cewa.
"Barsu suyi ta sabgoginsu muma muyi namu in mun gama ma fita."
cikin sanyi tace.
"Allah ko nayi missing Saifuddeen tunda akayi bikin nanfa bai zoba."
mik'ewa yayi tare da kamota ya tsayar da ita sannan yace.
"To muje muyi wonka."
a dole ta bishi suka shiga bathroom.

Su Ahmad kuwa a falo hira sukayi tayi na yaushe gamo,
daga nan suka shiga kitchen suda kansu suka fara kiciniyar had'a breakfast nasu.
to Ahmad da Mudassir su sun iya sun saba,
Salisu da Saifuddeen kuwa basu iyaba,
shiyasa suka kame suka zauna gefe,
Ahmad na fire dankali shi kuwa Mudassir yana kiciniyar tafasa musu ruwan tea.

Bayan kamar 35 minutes Rahma da Adnan suka fito a tare a parlour ta tsaya tana kasa kunne dan jiyo ta inda hayaniyarsu take,
jinsu a kitchen ne yasa tayi sauri ta nufi kitchen d'in tana shiga duk suka juyo murmushi tayi musu ganin duk suna murmushi,
sai kuma Saifuddeen yayi saurin tasowa ya iso gabanta murmushi ya kuma yi tare da mata alamun,
"Iye-iye kinyi kyau fa."
kunnenshi ta d'an rik'e tare da d'an matsewa da d'an k'arfi, d'an tsalle yayi tare da yarfa hannu,
Ahmad kuwa sai tsalle yakeyi yana dariya tare da cewa.
"Yauwa Adda Rahma matse da kyau."
Mudassir kuwa fuska ya kwab'e tare da cewa.
"Please Adda Rahma sakar mishi kunne kinsan baya son wahala."
Salisu ne yayi dariya tare da cewa.
"Kaji banza to waye ke son wahala,
kuma a yar wannan matsarne wahalar."
shi kuwa Saifuddeen hannunshi d'aya yasa ya kamo d'aya kunnenshi cikin body language ya mata alamun ya tuba.
ganin haka yasa ta sakar mishi kunne tare da cewa.
"Zaka sake yin sati uku har kusan hud'u baka zoba kuma kana cikin lfy."
Kai ya jujjuya mata yana mai shafa kunenshin,
daga nan sukaci gaba da hira tana mai tayasu aikin nanda nan suka gama girkin suka jera komai a dinning table,
daga nan suka zauna suka karya,
Saifuddeen ne ya fara cire hannu sai kuma Rahma sannan Salisu nandai duk sukaci sukayi nak,
suna gamawa Ahmad ya tattare wurin sannan ya nufi d'akinsu dan yana son watsa ruwa,
Salisu ne yabi bayanshi sai kuma Mudassir.

Ya Adnan kuma gyara zama yayi tare da cewa.
"Ummi ta gaya maka dalilin kiran da nake maka ne?."
kai ya jujjuya mishi alamun a a,
cikin nitsuwa Adnan yaci gaba da cewa.
"To batun Faruq da Adam ne naje jiya dan zan d'aukosu su dawo nan da zama a gabanmu zamufi samun konciyar hankalin da damar basu kulawar da ta dace a matsayinmu na iyayensu, sai Ummi tace min wai ai ka hana,
shiyasa na nemeka inji dalilin da yasa zakace kada a bamu su."
kanshi ya d'an sunkuyar cikin dottaku da sanin ya kamata ya kuma d'ago kanshi tare da mishi mgna cikin body language yace.
"Ba komai kawai dai naga gidan naku a cike yake gasu Ahmad sannan kuma kace zaku k'ara dasu Faruq,
kuma nasan Baba Hamisu bazai amince ba."
murmushi Adnan yayi tare da cewa.
"To jiyan ai saida na fara zuwa wurin baba Hamisun na nemi al'farma kuma ya amince, hakama Bappa Ali sai dai in kai d'inne zaka k'i amincewa ban saniba ko ban dace da a bani su bane."
da sauri ya jujjuya mishi tare da zaro wayarshi ya rubuta mishi.
"Ba haka bane Ya Adnan wlh bana son rabuwa da yaran ne,
hakama Ummi itama suke d'ebe mata kewa,
sannan Hayatuddeen shima sune masu d'ebe mishi kewa tun kafin ayi auren yaketa cemin kar in bari Adda Rahma ta tafi da yaranshi fa."
ita kam Rahma ido ta lumshe lokacin da Adnan ke karanta rubutun,
tasan duk farin cikinta sukeso tasan irin son da Saifuddeen kewa su Faruq,
tasan shi kuma ya Adnan yana son yaran sosai kuma yasan zatafi samun farin ciki in suna kusa da ita ido ta zubawa mijin nata kuma abokin yayanta jin yana cewa.
"Dan Allah da sonka da manzosa ku bamu yaran nan mahaifiyarsu zatafi samun nitsuwa tashi d'aya a rabata da yaranta abin da ciwo a rai."
da sauri Saifuddeen ya zubawa Rahma idanu ganin tana zubda hawaye alamun tabbas tana tare da kewan yaran nata.
Hannunshi yasa ya sharte mata hawayenta sannan ya amshi wayarshi tare da rubuta musu.
"Kiyi hak'uri Adda Rahma kada ki zubda hawayenki kinsa Raihana da Raliya zasuyiwa su Faruq duk abinda uwa ke yiwa d'anta kinsan Ummi kuma zata basu ink'antacciyar tarbiya,
ni kuma zan zame musu uwa uba."
kai ta jujjuya tare da cewa.
"Na sani Saifuddeen na sani ai ni kaina ka zame min uwa uba bare yaran da nasan ka fini sonsu duk da ni na aifesu."
sai kuma hawaye yaci gaba da zubowa ganin hakane yasa Saifuddeen mik'e tare rubuta musu.
"To ba matsala zan kawo muku Adam amman kuyi hak'uri bazan iya baku Faruq ba."
murmushi yayi ganin itama tana murmushi shi kuwa Ya Adnan dariya yayi tare da cewa.
"To Hamma Saifuddeen mun gode a hakanma,
dan naga yanzu ka zama kaine babba a kanmu."
dariya sukayi baki d'aya sannan suka mik'e suka dawo parlour
cikin kula Rahma tace.
"Saifuddeen zo ka duba bedroom mana ka kashe min kud'i kuma baka zo ka duba kayan d'akinba kaga yadda parlour kam yayi kyau ko d'an uwana."
murmushi yayi tare da mata alamun.
"No shi bazai shigaba komai yayi kyau."
sai ya kuma mata alamun in akwai abinda take buk'ata ta gaya mishi, cikin jin dad'i tace.
"Ka gama min komai d'an uwana ba abinda baka yi minba komai sabo ko budurwa bazata nuna min sabbin kayaba."
sai ta kuma kalleshi tare da cewa.
"Yauwa dama ina son in ce maka kasa su Raihana su jerawa Ummi tsoffin kayan d'aki na d'in nata kuma ta bawa Goggo Dada su."
kai ya jinjina mata alamar to,
sannan ya nufi d'akinsu Ahmad nan sukayi ta hirarsu ta abokai,
sai k'arfe tara Saifuddeen ya mik'e ya shiga bathroom wonka yayi yana fitowa yasa kayan Ahmad daga nan suka fito da shirin tafiya dubu uku ya bawa Adda Rahma kana ya bawa Ahmad da Mudassir dubu bibbiyu sannan suka sallamesu suka tafi.

A daren ranar yaje ya gayawa Baba Hamish batun ya Adnan ya nemi da a basu Adam.
Cikin aminci baba Hamisu yace ba matsala a basu.

Washe gari ya rarrashi Ummi ya samu ya kai musu Adam.



*************

Lokaci yaja kwanaki sun tafi makonmi sun gibta sun juye ih zuwa shekaru.
Rayuwa taci gaba da tafi,

Al'barka yanata ratsa dukiyar marayun nan yayinda adalcin Saifuddeen yake tasa dukuyar habaka,
tausayinshi da gskyanshi da taimakonshi da yawan sadakanshi ya zamewa dukiyarshi Garkuwa.

Abubuwa da yawa sun faru a shekarun nan.

Tuni Saminu ya fara aiki a kaduna har an aura mishi Raihana.
Suna can kaduna garin gwamna mai mata had'i da mota.

Ahmad da mudassir da Ishaq ma sun gama karatunsu,
tuni har ishaq ya samu gurbin karantarwa a jimi'ar Gombe state University,
wanda wannan abu yake matuk'ar bawa mutane mamki ganin gashi makaho kuma yayi karatu kuma gashi har yana karantarwa.

Mudassir kuwa da Ahmad basu samu aikin yiba kasan cewar yanayin k'asar ne digiri ya zama ruwan dare ko wanne gida da akwai sai dai samun aiki sai d'an talaka yayi dace,
wannan dalilin yasa Saifuddeen ya jawo Ahmad da Mudassir cikin kasuwancishi cikin ikon Allah kuwa taurarinsu suna haskawa kasuwancinsu yaci gaba,
kasan cewar dama shi Ahmad business administration ya karanta shi ya bawa kasuwansu damar habaka gabas da yammaka kudu da arewa.

Alhamdulillahi shima kanshi Saifuddeen da Salisu sun gama karatunsu,
to amman basubi ta kan neman aikiba,
dan a ganinsu duk sunada sana'a kawai dai sun nemi ilimin ne dan shine gishirin rayuwa,
to ta inama zasu fara tunda sunaga Ahmad da Mudassir ma shekaru biyu kenan har zuwa uku da gamawarsu basu kuma samu aikinba bare su da kwanannan suka gama bautan k'asarsu.

Zuwa Yanzu ko bappa Ali bai san adadin dukiyar da Allah ya azurtasu da shiba shi,
Saifuddeen ne kad'ai yasan k'a'ida da adadin dukiyarsu, kasan cewar shi yana ajiye komai a rubucene yanayin hakane kuma dan ta hakane zasu san adadin zakkar da zasuke cirewa duk shekara.

Ganin harkar k'arfe ya karb'i Salisu to sai ya bare kud'i kimanin 3 million ya bawa Salisu ya fara zuwa sarin motoci a Cotono da mota biyu rak ya fara sari yan million d'aya da rabi-rabi cikin ikon Allah a ko wanne mota ya samu ribar dubu dari uku-uku, koda ya ware kud'in mai da kud'in sauran uzururruka da kud'in da ya biya wanda ya tashi d'auko motor ya samu sauran ribarsa dubu dari uku da hamsin,
nan yaje ya bawa Saifuddeen su,
shi kuwa Saifuddeen yace bazai karb'i ko asiba,
yace yaci gaba da

Please Login or Register in order to submit comment