Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk mai nuna mata barazana da kuɗi ko wani matsayi baya ranta
duk kud'in na miji baya gabanta.
Tace ita soyayyar gsky zatayi duk wanda zata aura take kuma son ya mata tafi son miji jarumi mai tausayi da taumakon na ƙasa dashi kana har ranta tana son kekyawan miji bata son mummunan miji a ranta
Wannan kenan sune ahlin Zaleeha...
***
Ita kam Zaleeha sam bata wani damu da k'a'idar da aka bataba don ganin tsawon lokacin da aka bata takeyi kamar bazai zoba,
so bata wani damuba asalima duk damuwarta da tunaninta a kan son gano ina wanda ya taimaketan yake.

Bayan ta gama shirin baccinta ne,
tazo ta zauna bisa gadonta, ta ajiye system enta da wayarta a gefe,
da niyar had'e muryoyin wadanda tayi hira dasu yau a kaltingo,
kuma sai tayi shiru ta zuba fuskar System en idanu ko k'ibtawa batayi,
ta kai tsawon 5 minutes a haka kana taja dogon numfashi tare da lumshe ido cikin sanyin murya tace.
"Waya sani ma ko sun kasheshi ne?." sai kuma tayi maza ta girgiza kanta tare da cewa.
"Ya Allah ka kare minshi ka sake gaddara haɗuwata dashi."
sai kuma tace.
"To in ma yana raye ta ina zan ganoshi bare in mishi godiyar taimaka min da yayi,
ba abinda na sani a kanshi suna ko anguwa ko aiki ko dangi ko abakanshi bare in mik'a godiyata a gareshi koda a gidan radionmu,
ko menene sunanshi? ta yaya zanyi cekiyarshi ta ya zan ganoshi a faɗin duniyar nan?."
bud'e idanun tayi a hankali kana ta sharte hawayenta dan tabbas ta tuno lokacin da zata fito daga cikin sitadiyon d'in taga sun caka mishi wuk'a a bayanshi, da sauri ta kuma rumtse ido hawaye na zuba kana tace.
"Allah ya isan mishi, Allah zai saka mishi, mugayen banza azzalumai Allah zai saka mana."
sai ta kuma ture system en kana ta zame ta konta,
tana mai zubda hawaye a haka bacci ya saceta.

Dalla kuwa wani babban d'an kalarene wanda ya addabi birnin gombe da kewaye muddin yaga mace ko wacece ita inda ta mishi zaisa yaranshi su kamo mishi ita ya biya buk'atarsa da ita,
Dalla ya addabi garin gombe yayinda duk naci da k'ok'arin hukuma basu tab'a kamashi ba,
yana kuma da d'aurin gindin wani manya da suka medashi d'an bangar siyayasa shiyasa yake cin karensa babu babbaka babu wanda ya isa ya taka mishi birki.
To a yanzu dai babu 'yarinyar da yake cike da cikinta in ya kamata zaiyi mata Dalla-dalla sai Zaleeha,
sai dai shima a sashinsa ana shirin fitar dashi woje dan yana jinyar raunin da Saifuddeen ya ji mishi a gabanshi wanda yake sashi firgita dan gaba d'aya alamu suna nunawa kamar joystick d'inshi zata mace,
shiko fatanshi koda zata mace tayi hak'uri har sai ya rarake Zaleeha a cewarshi...

***
A nan Abuja kuwa

Su Ummi kuwa suna shiga Hayatuddeen yayi saurin nufar gadon da Saifuddeen yake konce,
yayinda shiko Saifuddeen ya mik'owa mishi hannu alamun yazo,
da sauri ya ruggume k'anin nashi kana yasa hannu ya kamo hannun Umminshi dake tsaye tamkar ta d'agoshi,
tuni hankalinta ya k'ara konciya ganinshi konce cikin haiyacin shi,
Ahmad kuwa matsowa yayi gafenshi yana jan yatsun k'afanshi yayinda Ishaq kuwa yake mik'o mishi hannu ganin haka yasashi saurin sakin hannun Ummi ya kamo na Ishaq,
wani sassanyan murmushi sukawa juna,
ita kuwa Ummi kanshi ta fara shafawa tare da cewa.
"Alhamdulillahi Babana jiki da sauk'i ko?."
kai ya jinjina mata tare dasa hannu ya d'an ture Hayatuddeen wanda tuni yaketa zubda hawaye dan tuno bayanin da Dr Aliyu ya yi musu na nakasar da yayan nashi ya samu.
Ita kuma Ummi hawayenta take ta son medawa dan tasan in Saifuddeen yaga tana kuka hankilinshi zai tashi.
Shiko Saifuddeen hannu yasa yana sharewa Hayatuddeen hawaye fuskarshi kana yasa hannu ya zaro woyar shi dake aljihun Hayatuddeen in,
juyota yayi gareshi,
rubutu ya d'anyi kana ya mik'awa Ummi, da sauri ta amsa dan tasan ta wannan hanyarce suke mgna dashi.
Murmushi tayi gani abinda ya rubuta.
"Ummi ki cewa Hayatuddeen ya bar kuka ya zama jarumi, ki tuna mishi yanzufa ya girma ya rage sakalci, ki sanar mishi jikin Hamma Saifunshi da sauk'i, kice mishi in dai yana son in sai mishi mota to ya dena kuka."
cikin samin sauk'in fargabanta ta kalli Hayatuddeen tare da mishi bayanin Hamman nashi, da sauri yasa hannu ya goge hawayenshi tare da cewa.
"Hamma nayi shiru na bar kuka kaji ko zaka saya min motar ko?."
kai ya gyad'a mishi alamar yaji fuska d'auke da murmushin da yasa dimples nashi duka huɗu suke lotsewa, kana ya amshi wayar tashi ya shiga message ya kuma rubutu kana ya turawa ishaq ta inbox nashi,
text d'in na shiga wayar ishaq tayi wani sautin mgna da sauri-sauri hakan yasa ya gane Saifuddeen ne ya turo mishi text alamun yana mishi Magna,
Dr Batulu kam yar kallo ta zama sabida ganin yadda abota take tafiya tsakanin kurma da makaho kuma har suke Magna da juna kuma har kowa ya fahimci d'an uwanshi.
shiko Ishaq lallatsa woyarshi yayi, jim kad'an ya karata a kunne sai ga wannan Magna sauri-sauri ya karanta mishi abinda Saifuddeen ya rubuta mishi kamar haka.
"Ishaq ya su Umma ya Amira da jiki?."
gyara tsayuwa Ishaq yayi tare da fuskantarshi yace.
"Alhamdulillahi suna lfy, sunce in gaidaka da jiki, kana Amira jiki yayi sauk'i har an sallamesu, kai yanzu ya jikin naka?."
rubutu ya kumayi kana ya turawa ishaq.
"Alhamdulillahi jiki da sauk'i, ina amsawa. ya an kai sak'on gidan marayun nan?."
Masha Allah ishaq yace tare da cewa.
"Eh an kai."
daga nan sai kuma Ahmad yace.
"Suifuddeen ya jikin?." murmushi yayi tare da rubuta mishi.
"Alhamdulillahi jiki da sauk'i yaushe ka dawo daga Lagos?."
bayan ya karanta rubutun ne yace.
"Jiya na dawo."
sai ya kuma kalli Dr Batulu sai ya d'an dungula hannunshi ya mata irin gaisuwarsu sabida ya tabbatar ta haifi kaman shi.

Ummi kuwa cikin kula ta shafa kanshi tare da cewa.
"Kai Hayatuddeen bashi wuri ya tashi mana ya samu ya watsa ruwa."
shiru duk sukayi sabida ganin kamar Ummi bata san menene ainihin matsalarshi spinal cord injury ba, ita a zatonta zai iya tashi da kanshi a yanzu haka a taken,
shima Saifuddeen da yanada halin boy'e mata daya boye mata gskyar laturarshi sabida gudun tashin hankalinta.
Itako Ummi sai juyawa tayi ga Ahmad kana tace.
"Ahmad tallefeshi ka kaishi bathroom kasan Saifuddeen da yawan son shiga ruwa."
Dr Batulu ce tayi saurin cewa.
"Ummin Saifuddeen kin mata bazai iya tsayuwa bane, kin mance ya nakasane kike ta cewa a tasheshi yaje yayi wonka, ai an mishi wonka d'azu kafin azo a bashi mgna, a yanzu haka bama zai iya tashi zaune bama sai mu zuba ido mu jira har lokacin da aka mishi aiki ko Allah zaisa a dace, ya tashi ya.....!



Wasa farin girki Ana wata sai ga wata.



By
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BA KASAWA BACE*


*PAGE 19*


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


~Wannan shafi nakune Nakasa ba kasawa bace fans 3 kuyi yadda kuke so dashi~

_Turn Katim mtn na ɗari ukku rak ta wannan no 09097853276 ko kuma ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa_


~Hmm Free page dai suna gab da ƙarewa saura ƙaɗan in rufe, hanzarta biyan ɗari uku kacal dan ka/kici da karantashi har ƙarshe~


Yauwa fa ba editing zakusa typing errors


"Ranan tashinsa tsaye sai dai muna tsammanin samun lfyarshi a ko wanne lokacin."
tuni idanun Ummi ke kwaranyar da wasu zafafan hawaye masu tarin k'una zuciyarta tamkar zata faso k'irjinta ta fito woje dan tsananin firgita da tashin hankali uwa uba tsananin tausayi gudan jinin nata.
kukanta ya k'ara tsananta ne jin tafin hannunshi bisa hab'arta yana share mata hawayen tare da jujjuya mata kai kana yana wani irin sihirtaccen murmushi mai cike da zallan tawakkali da yarda da k'addara,
Hayateddeen kuwa kanshi ya kife bisa pillow da kan Hamma Saifunshi ke konce goshinshi ya manna da hab'ar d'an uwan nashi kuka yakeyi mai cin rai da cushe farin ciki murya na rawa yake cewa.
"Dukkan jarrabobinmu sukan riskemu da tsananin zafi da tarin k'una, ko yaushe ciwo ko mutuwa basa zabi duk inda Allah ya aikosu nan suke zuwa, mutuwa ta yashe mana jigonmu, yayinda kowa ya yanke k'auna sai ubangiji ya sauk'ar da k'udurarnsa bisa d'an uwana da duniya ke ganin bama zai amfanin kanshi bama bare ya amfane mu, Hamma Saifuna ya karya zaton mutane da suke ganin nakasa kasawa ce,
ya tashi ya tsaya kaida k'afa ya shiga rana dare zafi sanyi ya ratsa duhu da ruwa da iska na damuna dan tsaida hawayenmu ya zame mana Garkuwa kana bongo abin jingina jigonmu abin al'faharinmu."
sai ya kuma taso ya kalli Hamman nashi da yaketa juya musu kai murya na rawa yace.
"Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! da ana canza ciwo da na canzashi ya dawo kaina, da ciwo bazai kuma rab'ar d'an uwana ba da ina da dama da na tsare maka dukkan wata cutar da zata kai ga tab'aka bare ta nakasa mana kai."
Ummi kam ta kasa cewa komai sai sunkuyar da kanta tayi k'asa tana zubda hawaye tare da ambaton Allah.
Shiko Saifuddeen jawo Hayatuddeen yayi bisa k'irjinshi ya rink'a shafa kanshi cikin alamun lallashi kana ya d'auki woyarshi da d'aya hannun rubutu yayi mai yawa ya mik'a wayar ga Ummi.
ba tare da ta kalleshi ba ta amshi woyar,
sabida hawayen dake kwaranya a idanunta yasa take ganin rubutun bibbiyu d'ad'd'aya rumtse idonta tayi hawayen da suka cika mata idon suka zubo sannan ta fara ganin rubutun a dai-dai kana ta fara karanta abinda ya rubuta mata
"Ni kam Saifuddeeen bani da wani ciwo da zai firgitani koya tayarmin da hankalin a duniya, kamar yadda ganin hawayen Ummi na da k'annena zai sani d'imuwa, zuciyata na k'untatuwa in naga hawayenki,
Ya Nuruddeen ya bar komai a hannu na bisa ya k'inin zan hana idanunku zubda hawaye,
ya Nuruddeen ya shaida min nakasa ba kasawa bace, ya gina min zuciyata da rayuwata ta yadda zan iya zame muku Garkuwa duk da nakasata,
Ya Nuruddeen ya haram tawa hannuwana rik'e k'ok'on bara ya damk'a min Al'k'alami da da jarumta.
Ummi ya zanyi da raina? sai yaushe zanyi nasarar tsaida hawayenki?
Sai yaushe zan saku farin ciki,
Ummi bani da baki dana fad'i miki irin k'unar da zuciyata keyi in naga zubar hawayenki bana jin k'unci a kan larurata sai naga hawayenki na zuba. Ummi kalli yadda Hayatuddeen ke kuka tamkar zai shid'e wannan ya nuna min gazawata ce kenan, ni nasan Ya Nuruddeen bai tab'a barina na zubda kwallaba, to ya akayi ni na kasa hanaku zubda naku hawaye ko dai nakasa tace sila? yanzu Ummi kema kuka kikeyi su Rahma Raihana Raliyya kuwa ya zasuyi,
Kalli kunsa Ahmad ma kuka, kalli ishaq bawan Allah da baya ganima kukanku ya sashi kuka, kalli Dr da kanta kun sata zubda hawaye, shin Ummi kin mance imanin bawa baya cika har sai ya yarda da k'addararshi mai kyau ko akasin haka."
tuni wani azabebben kuka ya kwabcewa Ummi wanda yasa ta kife mishi woyar gefenshi tare dasa hannunta tsakiyar kanshi ta shafa sumanshi har zuwa kan goshinsa sai kuma ta juya ta fita da sauri, domin tasan in yaga tana kuka zai birkice,
Abban Farida kuwa, hannu yasa ya kamo Hayatuddeen suka fita.
Yayinda tuni Dr Batulu kuwa tabi bayan Ummi,
shi kuwa Saifuddeen hannu ya mik'o ya kamo na Ishaq kamar yadda suka saba, shi kuwa Ishaq murmushin k'arfin hali yayi still kuma hawaye na kwaranya a idanunshi murya a raunace yace.
"Ya Rabi'u yace in gaidaka da jiki. Kana sak'on gskysuwa daga k'ungiyarmu sunayi maka fatan samun sauk'i."
hannunsu ya k'ara hadewa tare da jijjigawa alamun ya gode.
daga nan sukayi d'an hirarsu sannan Ishaq ya fito.

Nan ya samu Dr Batulu da Abban Farida sunata lallashinsu.
ganin lokacin salla ya kusa yasa suka, sallami Dr Batulu suka tafi ba tare da Dr Adnan ya fitoba.

Shi kuwa Dr Adnan ya dad'e tare da Dr Aliyu yana mishi k'arin bayani,
inda yace mai tunima an fara mishi alluran,
sannan kada su damu zai rink'a taho mishi da abincin daya dace yaci,
a nan asibitin Dr Adnan yayi sallan isha kana daga bisani suka shiga wurin Saifudddeen shida Dr Aliyu d'in.
suna shiga suka samu, nurse biyu maza masu gyara mishi jiki kamar taimaka mishi yayi wonka da al'wala da da juyashi ya fuskanci Al'k'ibllah yayi niya yayi sallanshi a koncen.

Suna shiga su kuma suka fita dan sun gama mishi shirin baccinsa,
Yana ganin Dr Adnan yayi murmushi tare da lumshe ido kana ya bud'esu ya kalli Dr Aliyu dake zaune bisa welchair d'inshi,
a hankali ya mik'o mishi hannu sukayi musabaha,
cikin kula Dr Aliyu yace.
"Ya jikin?." lips enshi ya motsa alamun da sauk'i kana ya jinjina kai,
shi kuwa Dr Aliyu cikin tausayawa yace.
"In sha Allah in an fiddaka zuwa India nanda wani d'an lokacin zaka fara tashi zaune da kanka."
da sauri Dr Adnan yace.
"Allah yasa."
Amin Dr Aliyu yace kana ya duddubashi sannan suka d'an k'ara bashi k'arfin guiwa da sama mishi nutsuwa sannan suka fita,
a bakin harabar wurin Dr Aliyu da Dr Adnan suka had'u da Nurse d'innan Amina,
da sauri ta iso inda suke, cikin shigarsu ta nurses wanda sunyi mata cib a jikinta sai d'an k'aramin hijabi,
hannunta na cikin haljihun gefe da gefen rigardata da iya karta guiwa, rusunawa ta d'anyi tare da cewa.
"Sir barka da dare."
"Barka dai Amina Usman Jada."
murmushi tayi dan yadda ya kira cikekken sunanta, gaida Dr Adnan tayi kana tace.
"Sir bari inje in bashi maganinshi, zan wuce gida."
jim ya d'anyi kana yace.
"To ba matsala amman dan Allah kiyi sammakon zuwa, kinga na damk'a amanar wannan aikin a hannunki, dan naga bafulatanine d'an uwanki."
cikin girmamawa tace,
"In sha Allah ba matsala zan taho da wuri".
daga nan sukayi sallama ita tayi ciki su sukayi woje.

A hankali ta tura k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama,
kasan cewar idonshi biyu yana rubutawa Ummi text ne yasa yaga shigowarta, baibi ta kantaba yaci gaba da sarrafa woyar tashi,
ita kuwa gefenshi ta tsaya,
tana harhad'a alluran da zatayi mishi,
bayan ta gama ne ta d'an matsoshi, tare da d'an zuba mishi idanu,
kallonshi takeyi tamkar tauraro,
gashin girarshi ta zubawa idanu wanda suke tamkar an zanasu da gazal sunyi lub lub dasu kana hancinshi zuwat har baki lips inshi jazir sai shek'ek'i sukeyi,
ido ta lumshe tare da cewa.
"Matarka taji dad'i koda ranta a bace yake in taga kekyawan fuskarnan taka farin cike zai kauda bak'in cikin."
lip's enshi ya d'an tsotsa ta ciki dan yana kallon motsin bakinta ta cikin fuskar woyarshi. So ya gane duk abinda tace.
ita kuwa yatsunshi ta zurawa ido yadda yake sassarafa wayar tamkar shi ya halicceta,
lips enshi ta kuma kalla kana tace.
"Wannan labban da ganinsu zasuyi taushi, ji yadda suke shek'i."
still bai kulata ba, ganin ta shagala wurin kallonshi,
ido ya lumshe yana tuno Zaleeha a ranshi sai yake jin inama itace kusa dashi,
a hankali taja numfashi kana tasa hannu bisa fuskarshi ta karkad'a mishi yatsunta,
d'ago lumsasshun idanunshi yayi ya d'an kalleta.
ganin ta nuna mishi allurane yasashi,
rumtse ido kana ya d'an mirgina tare da gyara zaman damtsen hannunshi na dama ya bata damar mishi allurar,
a hankali ta zira mishi allurar kana ta fara tura ruwan,
ido ya kuma rumtsewa kana yana sunkuyar da yatsun hannunshi har suna bada sautin k'aras-k'aras.
a hankali ta kalleshi cikin tausayawa tace.
"Sannu."
bai nuna mata ya ganeba dan ya lura bata san yana gane mgnar mutaneba in yana ganin bakinsu,
maganin ta babballa kana ta mik'a mishi.
Hannun dama yasa ya amsa kana ya afasu a baki tare da amsar robar ruwan da ta mik'o mishi,
sannan ya had'iyesu, bayan ta gama mishi komaine ta k'ara mishi gudun AC ganin tunda ta mishi allurar yake d'an had'a zufa,
gaban gadon ta dawo ta gyara mushi mayafin sannan ta kalleshi tare da cewa.
"Zan tafi gida, dare yayi, dan kai gobe da sassafe zan dawo Allah ya baka lfy, da masu kula da kai zasu ku kwana tare."
A ranshi yace.
"Amin ngd." a zahiri kuma bai kuma kulataba,
itako fita tayi,
shi kuwa text yayiwa Rahma da Raliyya da Hayatuddeen kana yayi addu'a ya rufe ido dan allurar ta fara sashi gyangyad'i.


Rahma kam dama da Adnan zai taho cewa yayi ta koma Side d'in Mamanshi dan yana soron kartayi ta kuka,
kuma Alhamdulillahi dake uwar mijintan na sonta suna kuma tausaya mata suna kula da ita shiyasa ta d'an sake bare yanzu da taga text d'in k'anin nata yana ce mata.
"Adda, yanzu Ya Adnan yazo, mukasha hira, yace min wai kince sai dai ku taho tare,
ni kuwa gani garau na samu sauk'i itama Ummi da Hayatudden zasu dawo, an bar gida ba manya ga Ahmad ma yazo nan, duk sun tare a kaina sai kace basu da aikin yi."
murmushi tayi tare da cewa.
"Zan zo kam in su Ummi sun dawo, in banzo na gankaba to wa zai zo ya ganka?."
murmushi yayi kana yace mata.
"Budurwata mana zatazo."
dariya tayi cikin samun nitsuwa tace.
"Iye to me sunanta surkar tawa."
kai ya rausayar tare da cewa.
"Sai na dawo zan gaya miki." daga nanne ya rufe wayar tashi.
Shiko Dr Adnan tare suka tafi da Dr Aliyu a can ya kwana.


Ummi kuwa tunda suka koma ta kasa samun sukuni duk da ta fawwala Allah lamarinta,
Amman ta kasa cin abinci,
Hayatuddeen kuwa ya d'an sake sabida yadda Ya Rabi'u, da Ya ishaq da Ahmad suka rink'a yi mishi nasiha da bashi k'arfin guiwa da nuna mishi yarda da k'addara.

Aunty Mami kuwa tausayin Ummi ya hanata sukuni sabida da ka ganta kasan tana cikin damuwa da fargaba,
shiyasa data gama shirin baccinta ta kuma soya mata gwai da biredi kana ta had'a mata tea ta nufi d'akin da suka sauk'i Ummin inda suke sauk'e Mamansu Ishaq in tazo.
bisa sallaya ta sameta tana rik'e da carbi,
gefenta ta zauna tare da tank'oshe k'afafunta, ganin har yanzu Ummi hawaye take zubdawa cikin sanyi Aunty Mamin tace.
"Kiyi hak'uri Ummi ki dena kuka dan Allah kiyi ta mishi Addu'a, insha Allah zai samu lfy."
cikin sanyin murya tace,
"Mami ya zanyi in banyi kukaba, me zanyi da hawayen nawa, ce minfa sukayi Saifuddeen na bazai sake tsayawa da k'afafunshi ba."
cikin tausasawa tace.
"A a fa Ummi ana kyautata zaton wata rana zai iya mik'ewa."
kai ta jinjina kana tace,
"Kayya ba dai boye min sukeyi ba, hakama sukayi min lokacin Nuruddeen da Abbansu."
Sai kuma ta share hawayenta cikin tarin damuwa taci gaba da cewa.
"Ina rasa nitsuwata da konciyar hankali na in naga Saifuddeen yana cikin wani hali,
ina jin tausayinshi a raina ina rasa samun nitsuwata gaba d'aya a kanshi,
ina tausayawa Saifuddeen in na tuna lfy lau na haifeshi, sai kuma abubuwa suketa biyu bayan rayuwarshi."
cikin tausayawa Aunty Mami tace.
"Ummi. Wayene Nuruddeen d'in da Abbansu?."
a hankali Ummi ta nisa kana cikin sanyi ta fara bata lbrin asalinsu Saifuddeen dama yadda ya samu larurar rashin ji...
Cikin tsananin kuka da tausayawa Aunty Mami tayi saki wani nannauyan ajiyan zuciya.
Numfashi ta fudda a hankali sannan ta jingina da gadon tana mai sheshesk'an kuka har saida Ummi ta dawo tana bata hak'uri,
cikin rauni ta share hawayenta tare da cewa.
"In sha Allah daga yanzu duk sanda nayi salla zansa Saifuddeen cikin addu'o'i na ya bani tausayi tun yana yaro k'arami yayita fuskantar k'alubalen rayuwa."
sai ta kuma gyara zamanta tare da cewa.
"Dan Allah Ummi na rok'eki ki daina yawan kuka,
kiyi ta mishi addu'a in sha Allah Saifuddeen bazai tab'eba."
Sassanyan ajiyan zuciya Ummi ta sauk'e tare da cewa.
"In sha zan daina yawan kukan zanyi ta mishi addu'a."
cikin jin dad'i ta mik'a mata kofin tea d'in,
ba musu ta karb'a tare da cewa.
"Ngd Allah ya miki al'barka."
Amin Amin tace sannan ta mik'e ta fita dan bata wuri.

Washe gari kuwa tuni Doctor Aliyu ya harhad'a dukkan bayanan cutar Saifuddeen ya turawa Dr Acash prasat wanda yake aiki a wani babban asibiti dake New Delhi India,
Ahmad kuwa E passport d'in Saifuddeen da Hayatuddeen da nashi ya tattara ya nufi Airport tun da sanyin safiya ya fara musu cuku-cukun samun visa,
A nan ya samu Adnan ya taho dan tare zasu tafi dole yayi musu jagora a matsayinshi na likita da yaso ace da Dr Aliyu zasuje to shi aiyuka sun mishi yawa,
sai da suka gama duk abinda ya dace na zirganiyar samun tafiyar nasu cikin sauri cikin sa'a kuwa suka samu jirgin da zai tashi jibi nan zuwa India direct New Delhi Indira Gandhi Enternational Airport, saida suka gama komai na tafiyar sannan suka baro airport d'in.

Ummi kuwa da Ishaq da Saifuddeen Ya Rabi'u ne ya kaisu Asibitin.

Suna isa Dr Batulu tayi musu jagora har d'akin da Saifuddeen d'in yake,
sosai Ummi taji dad'in samunshi cikin nitsuwa yana rik'e da wayarshi fuskarshi d'auke da murmushi,
da sauri ta isa bakin gadon kujerar dake kusa dashi taja ta zauna,
ishaq kuwa yana isa bakin gadon ya rik'e k'arfen gadon ya tsaya,
Hayatudddeen kuwa gefen shi ya tsaya kusa da Umminsu,
da sauri ya ajiye wayarshin tare da juyawa inda suke jin Ummi na shafa kanshi,
murmushin ya kumayi tare d'ago hannunshi ya shafa kan Hayatuddeen yayinda Ummi kuwa ke shafa kanshi,
sai ya kuma mik'o hannunshi d'aya ya kamo hannun ishaq.
Ya Rabi'u ne ya d'anyi murmushi tare da cewa.
"Masha Allah. Alhamdulillahi jiki da sauk'i ko?."
kai ya jinjina alamum eh.
Dr Batulu kuwa sai binsu da idanu takeyi cikin shawar shak'uwar dake tsakaninsu.
Cikin kula Ummi tace.
"Sannu ko babana ya jikin?."
wayarshi ya d'auka da sauri ya rubuta mata.
"Alhamdulillahi jiki da sauk'i."
cikin jin dad'i duk sukace.
"Allah ya k'aro mana sauk'i."
Amin Amin ya amsa a saman lab'b'ansa.


Dai-dai lokacin kuma su Ahmad da Adnan suka shigo,
bayan duk sun gaisa sun tabayi ya mai jikine sannan Ahmad ya kalli Ummi cikin nitsuwa yace.
"In sha Allah jibi zamu tafi india,
kuma Alhamdulillahi kafinma muje bayanan zuwanmu ya shiga hannun doctors d'insu."
cikin sauk'e numfashi Ummi tace.
"To Allah ya kaimu lfy ya kuma bada sa'an aiki."
cikin son kontar mata da hankalin Dr Adnan yace.
"Yanzu Ummi keda Ishaq zaku koma gombe gobe."
da sauri Ummi tace.
"In koma Gombe kuma?." Cikin nitsuwa Ya Rabi'u ya gyad'a mata kai tare da cewa.
"Eh Ummi ba matsala ke da Ishaq ku koma gombe,
Ahmad da Hayatuddeen kuwa dasu za'a tafi,
tare da Dr Adnan kuma shima in yaje ba dad'ewa zaiba in yaga anyi aiki dai to zai dawo kiji labarin jikin Saifuddeen d'in kuma,
in ya dawo keda Ishaq da bappa Ali zakuje."
kai ta sunkuyar kana murya a sanyaye tace.
"Yanzu sai in zauna a tafi dashi har wata k'asa ta daban."
Ahmad ne ya d'an kalleta tare cewa.
"Ummi nida Hayatuddeen zamuyi duk abinda zakiyi mishi karki damu zamu kula dashi."
still dai kamar bata gamsuba ido ta zubawa Dr Batulu da ta dafa kafad'unta tare da cewa.
"Ummin Saifuddeen ki kwantar da hankalinki shi jinyan namiji saida namiji d'an uwanshi hakama mace saida macce yar uwarta,
kuma duk sanda kikeson zuwa zakije ki duboshi."
cikin gamsuwa

Please Login or Register in order to submit comment