Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasa aranta cewa komai wahala komai daɗi,  komai kusa komai nesa zata bada kai da ƙarfinta wajen zaman jiransa, sau dayawa zuciyarta na gaya mata cewa watarana zaizo gareta, ta kuma aminta da hakan, saboda haka tasa aranta cewa, har abada bazata taɓa daina so da ƙaunarsa ba.

Balkeesu ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ganin Zaleeha kwance na kuka, yasanyata taɓe baki, cikin ranta tace.
"Bakiyi komai bama Zaleeha, sai alokacin da idanunki suka buɗe ki ka gane cewa kinrasa nagartaccen namiji  kamarsa, daga wannan lokacin zakiyi kuka irin wanda ake ƙiransa da sunan kuka bawannan sharan fage ba, wanda ni kuwa dama hakan shine burina."
Afili kuwa ƙarasawa gaban gadon tayi tare da zama abaki bakin gadon, cikin son  zuga tasanya hannu ta dafa kafaɗan Zaleeahan, cikin ƙoƙarin ɓoye manufarta tace. 
  "Kuka baya maganin damuwa Zaleeha, sam kuka bai kamaceki ba ba kuka yakamata ace kinyi ba."
Afusace Zaleeha ta tashi zaune, fuska caɓa-caɓa da hawaye tace.
"Bakuka yakamata nayi ba? dariya kenan kikeso nayi mai gado? okay nagane saboda ke bakisan zafin ƙiyayya dana soyayya ba ko shiyasa zakice haka, da ace kinsan yanda nakejin zafi a zuciyata wallahi da ke ce zaki fara cewa naƙara sautin kukana tayanda gaba ɗaya Nigeria zasu jiyoni bama iyaka Gombe kaɗai ba, Natsaneshi Mai gado, Natsaneshi, banason koda ganin fuskarsa, aurensa dai-dai yake da tarwatsewan zuciya da rayuwata gaba ɗaya, da ace na buɗi idona naganni matsayin matarsa gwara ace na wayi gari bana numfashi.!"

Wani irin ƙatuwar ajiyar zuciya Balkeesu ta sauƙe, tabbas haƙanta gaf yake da cimma ruwa, saidai kuma har yanzu bata hango irin zazzafar tsanar da takeson Zaleeha tayiwa Saifuddeen ba, haƙiƙa komai na Zaleeha na bayyanar da tsanar Saifuddeen saidai ita har yanzu akwai abun da bata gamsu dashi ba.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
  "Bance kiyi dariya ba Zaleeha, ni ƙawarkice maison duk wani abun da kikeso, saboda haka burina shine ki samu wanda kikeso,  kishare hawayenki Zaleeha, saikin cire tsoro haɗi da kunya kin fuskanci kowa sannanne zaki samu cikar burinki, saikin dage kin kuma ɗaga hankalin kowa dake gidannan, sannan zasu fuskanci cewa babu soyayyar Saifuddeen aranki."

Ɗago jajayen idanunta wanda suke cike da ƙwalla tayi ta kalli Balkeesu, murmushi Balkeesu tayi tare da dafa shoulder ɗinta, cikin son tarwatsa nutsuwar Zaleehan tace.
   "Nasan kin fahimci abunda nake nufi, dole ne ki tashi tsaye wajen ganin kin samawa kanki ƴanci,  wani irin kallo kike tunanin mutane zasuyi miki aduk sanda sukaji cewa da kyawunki da komai  kin kashe ƙuruciyarki wajen auren nakasashshe? ki dubeki Zaleeha, kyau, ilimi, diri, hutu, wayewa, aji, sanin darajar kai, duk fa kin mallakesu, babu wani ɗa namiji da zaki gifta ta gaban idanunsa matuƙar ya amsa sunansa namiji ace baiji komai game da ke ba, sam bakiyi kama da matar nakasashshe ba, zama da nakasashshe kuwa agareki tamkar tarwatsa rayuwarki ne!."
Ɗan tsagaitawa da maganan tayi tare da miƙewa tsaye, duban Zaleeha tayi da kyau, tare da sakin wani ɗan guntun murmushi, ahankali tashiga takawa harta ƙarasa jikin ƙofar fita daga ɗakin, juyowa tayi still fake smile ne ɗauke akan fuskarta, cikin son tausasa zance tace. "Nabarki lafiya ƙawata, ina fata zakiyi tunani me kyau akan maganata, idan kuma kin amince nakasashshen kurma yazamanto ango agareki am fine, mudai always zamu tayaki murna." Tana kaiwa nan azancennata ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fice, tana sakin wani dariya mai ɗauke da tsananin mugunta.
Lumshe idanu Zaleeha tayi saiga wasu sabin hawaye shaaaa sun kwaranyo daga cikin idanunta, wani zafi-zafi ɗaci-ɗaci haka takeji acikin maƙoshinta, cikin ɗaya daga cikin trow pillows ɗin dake watse bisa kan gadon ta jawo ɗaya, tare dayin hugging ɗinsa a ƙirjinta, kanta ta jingina da saman gadon tare da sake sakin wani sabon kuka, sosai shawaran Balkeesu yasamu mazauni acikin zuciyarta, don ta ƙudurta aranta cewa daga yau babu wani wanda zai ƙara bacci cikin daɗin rai acikin gidan, saita ɗaga hankalin kowa, bazata nutsa ba kuwa harsai taga ta samu abunda takeso...

Ɓangaren su Saifuddeen kuwa daga gidan su Zaleeha kai tsaye wani babban Cafe dake cikin unguwar federal lowcost suka nufa, wanda ananne suka narka kuɗi don buga musu ƙawataccen katin auren nasu wanda yanzu kwana biyar ne kacal ya rage, koda sukaje tuni suka samu an gama kammala musu komai, nanfa suka amsa, daganan gidansu Ishaq suka wuce, domin kuwa musamman Ummu'n Ishaq taturowa Saifuddeen ɗin saƙon text message akan cewar tayi masa tuwon semovita miyar moringa (zogale) sanin cewa yana matuƙar son miyar, koda sukaje gidansu Ishaq ɗin nan sukaci abinci suka ƙoshi, domin kuwa harda wani irin daddaɗan coconut drinks da kuma zoɓo Ummun ta haɗa musu, anan gidansu Ishaq ɗin Ahmad da Salisu da Jabeer sukatarar dasu, suka karɓi kusan rabin katin, daga gidansu Ishaq ɗin kaitsaye Ahamd wajen ƴan uwa da abokan arziki ya nufa inda yadinga raba musu katin auren nan kowa yake cika da murna da kuma fatan al'khairi.
***

Ƙarfe 6 dai-dai jirgin Azman Air Land ya sauƙa ababban airport ɗin dake cikin garin Gombe, wato Gombe International Airport, mutanene da dama cike a airport ɗin, dagani kowa da wanda yazo tarba, can nesa kaɗan na hango wasu matasan samari wanda aƙalla zasu kai su 10 sunyi gungu guda, gabaki ɗayansu hankalinsu naga ƙofar fita daga cikin jirgin.
Sannu ahankali mutane keta sauƙowa daga cikin jirgin, shine wanda yayi kusan na ƙarshen fitowa.
Cikin isa, izzza, haɗi da zallan iskanci da kuma tsageranci, haka yake sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, kallo ɗaya zakayi masa kafuskanci cewa riƙaƙƙen ɗan iskane irin wanda babu wanda ya isa sashi babu kuma wanda ya isa hanashi, ko daga nesa ka hangosa saiya baka tsoro balle kuma ka kai gayin face to face dashi, *Dalla* kenan, riƙaƙƙen ɗan iskan da ya riƙa a iskanci, sannan kuma sunansa ya buwayi ko ina na cikin gombe, babban tashin hankalin ko wacce ƴa mace shine wani ya ambato mata sunan Dalla, musamman ga waƴanda suka sansa, sam baya ragawa mace wajen yi mata Dalla-Dalla da virginity ɗinta.
Cikin yanayinsa dake nuna nutsewarsa acikin daba yaƙarasa sauƙowa daga kan matakalan jirgin.
Da wani irin ihu haɗi da shewa yaransa sukayo kansa, cikin tsananin jin daɗin ganinsa da kuma murnar samun lafiyansa, suka shiga yi masa ƙirari da yi masa take irin nasu, take kan Dalla ya ƙara huruwa har takai ha yanajin kansa kamar wani sarki, nan yasoma ɗaga kai yana hura hanci, cikin nuna isa da halinsa wanda sama da shekara ɗaya yakasa sanjawa ya dubi yaran nasa, hannayensa ya zura acikin aljihun wandonsa, tare da ɗage kansa sama, cikin murya da yanayin magana irin tasu ta riƙaƙƙun ƴan daba yace.
"Allah yayi dawowana yau, bayan nashafe sama da shekara ɗaya ina jinya a k'asar Jermany, Wallahi Na rantse da sarkin dake busan numfashi, babu wani mahaluƙi aduniya daya isa ya hanani yiwa yarinyar da a sanadinta na haɗu da lalurar da takaini.shafe sama da shekara ina jinyan kaina Dalla dalla, ni Dalla al'ƙawari naɗaukarwa kaina cewa duk inda tashiga tafita saina nemota, zan banƙarata kamar kaza, sannan zanyi mata dalla-dalla irin wanda ban taɓayiwa wata mace ba, zan keta mata haddi irin ketawar cin zarafi, sannan zanyi watsi da duk wani mutumcinta, wallahi saina yaga rigar budurcinta na tarwatsa shi tayanda bazata ƙara numfashi ba bare takai ga yin motsi, idan kuwa har hakan bata kasance ba Ni Dalla ban haifu acikin uwata da ubana ta hanyar sunna ba, sannan kuma al'ƙawarine akanta zan fara gwada lafiyar dana shafe tsawon lokuta ina nema!!!."

Ihu haɗi da kirari yaran nasa suka yi masa, haka suka cigaba da masa kirari suna ƙara fasa masa kai, shikuwa Dalla tuni kansa ya ƙara girma, ayanzu burinsa ɗayane a duniya shine ya damƙi tsinaniyar yarinyar nan da sanadinta ya fita daga sahun mazaje tsawon wasu lokuta, haka suka cika mota shida yaransa ƴan daba, kaitsaye babban gidan na Dalla wanda acanne yake hutawa idan yazo suka nufa, inda nan cikin unguwar shango estate gidan yake.

***
Ummi ce zaune akan makeken gadonta, yayinda gaba ɗaya hankalinta sam baya jikinta, sosai tayi nisa cikin tunani, zuwa yanzu kwata-kwata takasa jure rauni, damuwa, fargaba, haɗi da tsoron dake kwance cikin ranta, sam kwana biyunnan bata tare da nutsuwarta, wani irin tsoro haɗi da fargaba suke cika zuciyarta, har yakai ga ko bacci take fargaban baya barinta, sosai al'amarin auren na Saifuddeen ke mugun ɗaga mata hankali, kwata kwata bata da nutsuwa akan maganan auren, musamman yanda labarin irin tsanar da Zaleeha keyiwa Saifuddeen dayazo kunnenta, ko acikin ƴaƴanta son da takeyiwa Saifuddeen daban yake, har acikin jininta takejin soyayyar ɗan nata, sam koda wasa bata ƙaunar abun da zai cutar mata da Saifuddeen ɗinta, haka ko kaɗan batajin son wanda bayason Saifuddeen ɗinta, sosai takejjn tsoron abun da zaije yazo idan Saifuddeen ɗin ya auri Zaleeha, daga gefe guda kuwa tsananin tausayin Saifuddeen ɗin ne kullum ke ƙara cika zuciyarta, musamman yanda ta lura da irin sonda Saifuddeen ɗin keyiwa Zaleehan kamar ransa, aduk sanda ta so tunkarar Saifuddeen da maganar son fasa auren nasa da Zaleeha, takansamu kanta cikin rashin ƙarfin guiwa domin kuwa da ta kallesa zata hango tsantsar soyayyar da yakewa Zaleehan kwance acikin idanunsa, wannan shine abun da yake karya garkuwanta ako da yaushe, ɗan numfasawa Ummin tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, a hankali tace.
"Lallai yanzun kam bazan iya jurewa ba, dan dole zan aiwatar da abun dake zuciyata, sam bazan taɓa yarda in zuba idanu inga Saifuddeen yakai kansa inda za'a halakar min dashi ba, shiɗin garkuwa ne agaremu, muna tsananin buƙatarsa, daga ini har ƴan uwa da abokansa bazamu taɓa son abun da zai cutar dashi ba, saboda haka na gama yanke shawara tabbas zan ƙira Baffa Ali da Malam Ashiru kamar yanda sukaje suka nemawa Saifuddeen ɗin auren Zaleeha, to ayanzu ma zasu koma suce Saifuddeen ɗin ya janye, saboda kwata kwata babu wani alfano wajen auren matar da bata sonsa, babu komai cikinsa sai, danasani, baƙin ciki, da kuma tashin hankali, sam kuma bana fatan Saifuddeen ɗinna yaji koda ɗaya daga cikin waƴannan ne, burinna shine yayi aure yaji daɗi, ya kuma samu kwanciyar hankali, da nutsuwa, sam bana fatan akasin ɗaya daga cikinsu ya samesa, saboda haka na aminta da shawaran da zuciyarta ta yanke min, dole ne za'a fasa auren Saifuddeen da Zaleeha." ta k'arishe maganar tare da kwanciya.

Hayatuddeen da abokansa kuwa, tuni suke ta murnar bikin, inda suka shirya partyn da zasuyi a bikin nasu na musamman, tuni Hayatuddeen ya watsa hotunan katin auren ashafinsa na Instagram da kuma WhatsApp status ɗinsa, tuni Ameena ta haukace masa da tayi tozali da invitation card ɗin, nan tafara kuka yayinda zuciyarta tacika da kishi haɗi da raɗaɗin auren na Saifuddeen da zaiyi, wasa-wasa fa Ameena harda kwanciya zazzaɓi.
Asma'u ma sosai tayi takaici domin bata da wani buri daya wuce kasancewarta da Saifuddeen, ita kanta batasan soyayyarsa tashigeta sosai ba saida taga katin na aurensa da Zaleeha kuma dai hakan baisa ta sauya k'udirinta ba.


Ɓangaren Zaleeha kuwa tun jiya da ta sa kanta aɗaki ta kulle bata ƙara ko leƙowa ba, gaba ɗaya haka ta wuni cikin ɗaki, zuciyarta cike da ƙunci, haɗi da takaici, tuni tagama shirya duk wani plant ɗinta na yanda zata fitowa da ƴan gidannasu sabon tsarin takunta, na yanda zata rufe idanunta ta shumfuɗa taɓaran ƙin auren Saifuddeen da ake ƙoƙarin laƙaba mata. Hakanan ta-tashi yau da son zuwa gidan yayarta Maryam, don haka tun safe ta kammala shirye shiryenta, wanka tayi inda ta shirya kanta cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga navy blue colour mai kyaun gaske, sosai rigan tabi shape ɗin jikinta ta ƙafe, yayinda adon stones ɗin rigarta keta shinning yana ɗauke ido, parking dogon gashinta tayi atsakiyar kanta, kana tayi rolling ɗan maidaidaicin vail ɗin rigan akanta, wanda ya sauƙo har zuwa kan ƙirjinta, wani ɗan maidaidaicin hand bag ɗinta shima me kalar navy ta riƙe ahannunta tare da ɗaukan wayoyinta, ƙiran iphone da kuma samsung, wani navy blue toms masu kyau da taushin gaske ta sanya aƙafafunta, wanka tayiwa jikinta da daddaɗan turarenta mai daɗin ƙamshi, sosai tayi kyau duk da kasancewar ƴar rama ta bayyana ajikinta amma tayi kyau sosai, raman ma saiya kasance yaƙara mata kyau da burgewa.
Cikin takunta mai ɗauke da burgewa tafito daga cikin ɗakin nata, bata samu kowa acikin falon ba hakan yasa kai tsaye ta nufi compound ɗin gidan, cikin nutsuwa taƙarasa jikin motarta, buɗe murfin motar tayi tare da shigewa ciki, maigadi ne ya wangale mata gate sannu ahankali tatura hancin motar tata waje, cikin nutsuwa haka take murza steering motar, azahiri idan kaganta bazaka taɓa tunanin cewa wani abu na damunta ba, amma abaɗini tanajin kusan ma tafi kowa yawan damuwa, sosai takejin kamar zuciyarta zata fashe saboda damuwa, batayi wani tafiya sosai ba taƙaraso gaban gidan na Maryam wanda yake madaidaici mai kyaun gaske, maigadi ne ya wangale mata gate ɗin gidan ta cilla hancin motar ciki.
Da mamaki take kallon motar Yaya Ahmad dake fake cikin compound ɗin gidan na Maryam, sam batasan ma da zuwansa cikin garin na Gombe ba, da ɗan sauri ta bude murfin motar tafito, direct ta nufi cikin gidan, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tashiga, bakinta ɗauke da sallama, Ya Ahmad, Maryam, sune zaune acikin falon yayinda suka juyo da kallonsu gareta, idanunta ne suka sauƙa acikin na Ya Ahmad, saurin ɗauke idanunta tayi tare da turo bakin nata gaba, lokaci guda hawaye suka cika idanunta, sai kawai ta kawar da kanta gefe, cak kuma ta tsaya batare da ta ƙaraso tsakiyar falon inda suke zaune ba.
"Zaleeha!." Maryam taƙira sunanta murya asanyaye, domin tuni ta hango ƙyallin hawaye acikin idanun Zaleehan.
Ɗan juyowa Zaleeha tayi ta kalli yayarta ta, sai kuma ga hawaye zirrr sun ziraro daga cikin idanunta, rumtse idanu Ya Ahmad yayi tare da ɗan cije laɓɓansa, sam baya ƙaunar ganin hawaye a idon ƙannensa, musamman ma ita Zaleeha dayakejinta matsayin shalelensa, cikin son sama mata nutsuwa yace.
"Bansan ƴan matan Yaya Ahmad da saurin kuka haka ba, nasan dai tana da juriya sosai, calm down my lovely sister, zo kigayamin menene damuwar da har tasanyaki hawaye!".
Ae tuni kafun ma yaƙare maganar tasa ta rugu da gudu zuwa cikin falon, faɗawa jikinsa tayi tare da sakin wani irin kuka mai taɓa zuciya, ƙwarai tajima bata samu wanda zata shiga jikinsa tayi kuka haka ba sai yau, hakan yasa ta ƙara riƙe Ya Ahmad ɗin nata tana kuka sosai, shiru Yaya Ahmad da Maryam sukayi, sam sun kasa hanata kukan, domin sunyi imani cewa kuka ma rahamane, sannan wani lokaci yana gusar da damuwa, kana kuma duk cikinsu babu wanda baisan kukan me Zaleehan keyi ba, domin dama ansan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, tayi kuka sosai, aƙalla ta share sama da mintuna 15 tana kuka, sannu ahankali kukannata ya tsagaita, ajiyar zuciya kawai take sauƙewa akai-akai, ɗagota daga jikinsa Ya Ahmad yayi tare da kai dubansa gareta, hannu yasa ya goge hawayen da gaba ɗaya suka dame fuskarta, cikin tausasa murya yace.
"Akullum tun kina ƙarama nakasance ina me horanki da ki-kasance mai haƙuri, Domin shi haƙuri yana maganin abubuwa da yawa Zaleeha, sannan Addu'a tafi kuka don itace babban jigo akan komai, ke ƴar uwata ce kuma jinina, bazan taɓa son ganinki cikin damuwa ba, amma yazamuyi Zaleeha? yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta alamace dake nuna ƙarfin imanin mutum, sannan kada ki manta kowani bawa a duniya da irin jarabawar da Allah yake ɗaura masa, wani mai kyau wani akasinta, shin meyasa bazaki sa aranki cewa aurenki da ake ƙoƙarin yi da Saifuddeen haɗi ne na Allah Ba? babu fa wani bawa aduniya daya isa sauyawa kansa Ƙaddararsa!."
ɗan tsagaitawa da maganan yayi kana ya sanya hannunsa ya shafi kanta, cikin son kwantar mata da hankali yace.
"Kaf cikin ƙannena nafi ƙaunarki Zaleeha, inason duk wani abu da kikeso, banason ɓacin ranki ko kaɗan, dan Allah Zaleeha, kada ki watsawa mahaifinmu ƙasa a ido, kizama mai biyayya agaresa koda yaushe, ita al'barkan iyaye tana da tasiri akan ƴaƴa, har abada Baba Malam bazai taɓayin danasanin zamantowarki ƴa agaresa ba matuƙar kikayi masa biyayya, zai tabbata yana me alfahari dake, ki yi dubi ga ƴar uwarki".
Ya nuna Maryma wanda take zaune itama idanunta sunyi rau rau, kana sun cika da ƙwalla.

"Maryam takasance abun al'faharin Baba Malam, tayi masa biyayya, bata bijiremasa ba, tayarda da zaɓinsa duk da cewa bata so, amma ayanzu ki dubeta, tana zaune cikin jin daɗi, farin ciki, annushuwa haɗi da salama, hakan yafarune kuma duk saboda biyayyan da tayi ga mahaifinmu, sam bata bijire masa ba duk da kuwa bataso, haka yasa muke tsananin sonta kema ki daure ki masa wannan biyayyar."
Hannayen Zaleeha ya kamo cike da kula yace.
"Dan Allah Zaleeha kimin al'ƙawarin zaki yiwa Baban mu biyayya, Insha Allah aurenki da Saifuddeen al'khairi ne, sannan Baba Malam bazai taɓa kaiki inda za'a cutar dake ba!."
Sabon kuka Zaleeha tasanya wiwi kamar wanda aka faɗawa ranar muruwarta, sam kalaman Ya Ahmad basu shigeta ba, inama dazai gane cewa ayanzu idanunta sun rufe, bataji bata gani, inama dabai ɓata lokacin sa ya faɗi waƴannan maganganun ba, zuciyarta tajima dayin nisa wajen tsanan Saifuddeen, bata sonsa, ba kuma ta son aurensa. Haka Zaleeha ta dinga yi musu kuka wiwi, Ya Ahmad da Maryam kuwa sai nasiha sukeyi mata tare da ban baki, saidai kuma ko ɗaya bata ɗaukar nasiharsu, aduk ma sanda sukace da ita tayi haƙuri ta ɗauki Ƙaddara, takuma yiwa mahaifinsu biyayya, saitaji kamar wuƙa suke caka mata agadon bayanta, idan kuwa suka yaba Saifuddeen, suka kuma ce ta rungumi aurensa hannu bibbiyu sai taji kamar narkakken dalma suke watsa mata cikin kunnuwanta.
Haka dai tasha kukanta ta ƙoshi har saida idanunta suka kumbura, daga ƙarshe dai Ya Ahmad ne dayaji yanda jikinta ya ɗau zafi yasakata amotarsa suka dawo gida, yayinda tabar motar ta agidan Maryam ɗin.
Tunda ta dawo daga gidan Maryam tasa kanta aɗaki ta kulle, wani zazzafan zazzaɓi kuwa take yakawo mata ziyara, domin irin kukan da tayi yauɗin nadabanne.

Haka Zaleeha ta kwashe kwana d'ayan cur bata fitowa ko ina, banda kuka ba abun da ta sa agaba, washe garin nema da taji zaman kaɗaici naneman takurata yasanya ta shirya don zuwa aiki ko kewan da takeji zai ɗan ragu, ko wani wadataccen kwalliya yau ɗin batayi akan fuskarta ba, wata bubu gown red colour da red vail kawai ta yafa ajikinta, amma dayake itaɗin ce mai kyau bawai kwalliyan da takeyiwa kanta ba duk da haka saida tayi kyau, cikin ƙunci haka ta nufi gidan redion nasu na Vission FM.
Koda taje banda Rabeel da suka gaisa babu wanda ta kula, kai tsaye tatafi gabatar da shirinta na Mushaƙata.
A kasalance ta gyara zamanta tare dacewa.
"Barkanmu da war haka sannunmu da sake saduwa cikin shirinmu mai taken mu shak'ata.
sai kuma ta d'anyi shiru tare da sakin wak'ar,.
Tattausan lafazi mai dad'i jinshi ya ratsa raina, hadarin so yayi had'owa.
Sai ta kuma d'an rage volume tare da cewa.
"Taken na masoya ne, gareku masoya."
A hankali ta dinga sake zafafan waƙoƙi na soyayya masu taɓa zuciya, wani waƙan idan tasaka har ƙwalla ne ke bin ƙuncinta, domin sosai suke ratsa mata zuciya.
kai ta jinjina tare dacewa.
"Ganin lokaci na hararanmu a gurguje ga zazzafan sak'o na masoyo, wanda shine na kusa da k'arshe.
sai kuma ta saki wak'ar K'anina Hamisu Breaker tare da k'ara volume.
A hankali Wak'ar ke tashi.
Tun forkona duniya an dasa so bisa zuciyar mutun biyu.
kuma har abadan bazai yankeba dan yanada armashi.
sai ta kuma d'an rage volume d'in tare da d'aga muryarta tana bin wakar yadda sautin ke fitowa tare cikin rauni take bin baitukan.
"Soyyyy ruwan zuma inji wasu,
wasuko sukace ruwan gubane." haka tai tabin wak'ar har k'arshe kana tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
"Ganin lokacin da aka d'ibar mana ya k'are ga wak'armu ta k'arshe." wak'ar isa ayagi.
Duk masoyi zai jure karan tsan." sai kuma ta d'an k'ara sautin muryarta tare da bin mawak'in inda yake cewa.
"Zaya jure kai kawo ko ina, zai nufin masoyinsa da hassada. Ba'ason fushi sai dai dangana."
sai kuma ta dai-daita muryarta da mawak'in suka had'a baki wurin cewa.
"Yin fushi a so tono fittina, wanda ya fara so baishiga yak'i na kanganba."
sai kuma tayi maza ta katse wak'ar dan sai taji kamar Saifuddeen take bawa k'arfin guiwa,
tana ƙare shirin nata ta fito.
Balkeesu ce ta karɓa don itace zata gudanar da labaran duniya, bayan tagama gabatar da labaranne ta gyara zama, cikin isgilanci tace.
"Kanun Labaran duniya da ɗumi ɗuminsu.mun samu wani labarin mai cike da al'ajabi daga wata majiyarmu mai taken Babu nakasasshe sai rago, cewa soyayya ta ɓarke tsakanin masu lafiya da kuma nakasassu, inda shahararriyar matashiyar budurwa maiji da kyau, ilimi, wayewa, haɗi da aji tayi gamdakatar da wani nakasashshen kurma, kana gurgu, inda yazo ya bayyana mata soyayyarsa hartakai ga suna ƙoƙarin yin aure, mudai fatan mu anan shine Allah yaƙara danƙon ƙauna da soyayya, domin ai Nasaka ba kasawa bace, kuma babu nakasasshe sai kasasshe!." taƙare maganar tana me ƙoƙarin gimtse dariyarta.

Zaleeha dake zaune aɗakin watsa shirye shirye tanajin abun da Balkeesun ta faɗa, taji ranta yayi wani irin ƙuna, take ɓacin rai ya cika mata zuciya, sam bata tsammaci haka daga Balkeesu ba abinda taketa boye shine take son sanarwa duniya.
Jakarta ta ɗauka tare da miƙewa tsaye batajin zata iya jure zama awajen aikin, saboda haka tafiyarta gida shine kawai zaifi.
Tana fitowa, tayi kiciɓus da Balkeesu, tare da wani Hamza wanda yake shima abokin aikinsu ne, Hamza irin mutanen nanne masu gulman tsiya da kuma shishshigi, gason shiga abun dabai shafesa ba, shiyasa ma sam basa shiri da Zaleeha.
Yana ganin Zaleehan yasaki dariya tare da dubanta da kyau, cikin son ƙarin jin gulma don wanda Balkeesu ta gulmata masa bai ishesa ba yace.
"Zalees fashion amaryar nakasasu, anguji masu lafiya an ƙare a nakasassu."
Cak ta tsaya da tafiyan da takeyi tare da juyowa ta watsa masa wata uwar harara, bata da lokacin tanka masa hakan yasa ta juya taci gaba da tafiyarta.
Dariya suka ci gaba dayi shida Balkeesu, ita kuwa ko sake waiwayosu batayi ba.
Kaitsaye wajen motarta ta nufa, tana shiga ta murza wa motar key tare da cillata kan titi, kanta ne ke mata ciwo sosai, gaba ɗaya damuwa ya cika zuciyarta, har wani ɗaci takeji aranta.

Baba malam ne zaune a falonshi bayan tafiyan iyayen Abdussalam wai sun kawo sadakinsu wa Zaleeha kuma wai masu kawo kayan aurenma suna kan hanya,
Malam Adam ne ke tausarsa da cewa.
"Malam Bashir ka kwantar da hankalinka domin al'amarin yaran yanzu sai du'a'i." cikin tsananin b'acin rai da tarin bak'in ciki murya a hargitee Baba Malam yace.
"Me Zaleeha take son maidani da zatayi ta turomin manyan mutane masu daraja a kanta ita d'aya, da kaifa muka amshi sadakin Saifuddeen a hannun mutane masu kima da daraja, sannan yanzu ta kuma turo min wasu, biyu za'a rabata ne? ga uwarta ita ma sai tayar min da hankali takeyi."
cikin tausasawa Malam Adam yace.
"Kada ka damu tunda su iyayen Abdussalam mun basu hak'uri mun kuma ce musu kada su bari a kawo kayan lefensu ai inaga sun fahimcemu."
kai ya jujjuya tare da cewa.
"Banga alamun hakaba a fuskokinsu, bakaji cewa suke ai dai da fari nine na bawa d'ansu damar zuwa zance wurinta, kanaji har cewa sukeyi wai in dai daure inyi dottaku kaji fa abinda Zaleeha ta jaza min zubewar mutunci da kima da dottaku a idanun mutane."
"Ba komai in sha Allah, bari inje gida anjima zan dawo inyi mgna da ita Zaleeha ka kwantar da hankalinka."
Da haka Malam Adam ya sallami Baba Malam ya tafi ya barshi cikin tarin bak'in cikin abinda Zaleeha da Mama keyi

Please Login or Register in order to submit comment