Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda suka saba
gyara zama Nuruddeen yayi kana ya sunkuyar da kanshi sannan ya kuma d'agowa ya kallesu, cikin sanyin murya yace.
"Bappa Ali, ya batun karatun Saifuddeen ne? kunyi shiru bakuce komai ba, kuma tun kwanaki naketa binku a saida gona d'aya, a saya min machine, tunda na iya na koya a mashidin abokina Adnan,
tunda akwai makarantar kurame a cikin Gombe, kullum da safe sai in tafi dashi in kaishi makaranta ni kuma na wuni yin acabana,
in zan dawo da yamma in d'aukoshi mu dawo tare, kunga baiyi nesa damuba kuma zai samu ilimi, kana mun sauk'e hakkinshi daya rataya kanmu, kuma mun cire mishi nakasar zuciya, kana mun ink'anta rayuwarshi, sannan zai samu k'arin fasaha da basira ta yadda zai k'ara samun experience,
sannan mu rabashi da barace."
shiru yayi ganin duk sun zuba mishi ido,
su kuwa yabawa sukeyi da shawararshi domin sun san gsky ya fad'i.
hakan yasa Bappa Ali gyara zama tare da cewa.
"In sha Allah hakan za'ayi Allah yayi maka al'barka Seyo da yake haka suke kiranshi *Seyoji ko Seyo duk d'aya ne* kakmar fillancine da take nufin FARIN CIKI a hausave.
murmushin jin dad'i Nuruddeen yayi kana ya kalli Abbansu da yake zubda hawayen tausayinsu yace.
"Abba kada kayi kuka, in sha Allah watarana muma zamuyi farin ciki, Allah zai sauqaqa mana zafafan k'addarorinmu ih zuwa dad'ad'aan k'adarori domin dukkan tsanani yana tare da sauk'i,
ku dai kuyita mana addu'a."
cikin sanyin murya Abba yace.
"Allah yasa haka Seyo na Allah ya al'barkaci rayuwarka ya baka damar rik'e k'annenka."
Amin Amin ya rabbil izzati. Suka amsa a tare.

Tofa daga wannan ranar akasa wata yar madaidaiciyar gonarsu a kasuwa cikin ikon Allah a wata d'aya akayi cinikinta aka basu kudin.

A ranar da aka basu kud'i a ranar Bappa Ali ya shiga cikin birnin gombe ya sayowa Nuruddeen mashin d'in bajat sabuwa dal,
kana daga ranar suka fara cuku-cukun nemawa Saifuddeen gurbin karatu a makarantar kurame ta Gombe. Special education Gombe state,
cikin sa'a aka sama mishi takardar shaidar ya zama d'alibinsu zai ci gaba daga JSS two, kasancewar da sa hannun Malam Ashiru abokin Abbansu kuma Saifuddeen kanshi na ja sosai domin nakasarsama kamar k'ara zaburar dashi tayi.

Daga wannan ranar kullu yaumin fisha'i.
Nuruddeen zaiyi sammakon baro Dukku tare da Saifuddeen suna shiga gombe ya kaishi makaranta kana shi kuma ya shiga cikin gari yayi ta kabo-kabonshi tun baisan anguwaninba har yazo ya saba ya goge ya zama idon gari,
sai sun karya suke tahowa kana shabiyu nayi zai kaiwa Saifuddeen abinci duk da ana basu abinci a makarantar kasan cewar sashinta boarding school ne kana kuma akwai yan jeka ka dawo in har iyayenka zasu iya d'aukar dawainiyarka.
A ranar forko Saifuddeen ya had'u da abokinshi Is'haq makaho wanda suka shak'u sosai har yan uwan is'haq sun san Saifuddeen da Yayanshi Nuruddeen, hakama Nuruddeen yasan yan uwan is'haq dan har gidansu yana zuwa,
dan in an bada hutu Saufuddeen kan biyo Seyo gombe ya kawowa abokinshi ziyara su wuni suna hira da yake shi Is'haq iyayenshi a gombe suke cikin anguwar Fada,
shi Is'haq makahone kuma shima k'enda ce sila makantan shi dan ya bawa Saifuddeen lbri suna hira ta hanyar is'haq yayi Magna shi kuma Saifuddeen ya rubuta mishi amsa a wayarshi da yake iyayen is'haq sunada yar wadata sun saya mishi waya.

Haka rayuwa tai ta tafiya mashin d'innan ba k'aramin rufa asirinsu Ummi yayiba,
suna samun komai a wadace, shi kam Nuruddeen ya jingine batun nashi karatun dama dukkan buk'atun rayuwarshi burinshi ya gina rayuwar Saifuddeen.

Tuni rayuwa ta mik'e, sai dai kullum jikin Abba na yawan tashi,
Rahma ta haifin d'anta na fari mai suna Faruq, har ta kuma haifi na biyu mai suna Adam.

Tuni Saifuddeen ya tafi SS 3 shida abokinshi Is'haq da wasu sauran yan ajinsu karatu sukeyi sosai babu kama hannun yaro kuma. Alhamdulillahi kwakwalensu na ja.


Tuni Raihana ma ta fara zama yar budurwa hakama Raliyya Hayatuddeen ma tuni ya tafi primary 3.

Bappa Ali kuwa har yau Allah bai bashi haihuwa ba,
Kuma shike jan ragamar makarantar da mahaifinsu ya bari.
Goggo Dada kuwa tun haihuwanta na fari bata kumayin koda b'ariba tuni d'an nata Ahmad ya girma domin sa'an Saifuddeen ne shi.
Alhamdulillahi su Saifudddeen sun kammala makarantar especial education lfy,
har anyi bikin yaye d'aliban
kana yanzu sunata shirin zana jamb dan samun gurbi a jamir'ar G.S.U wanda shine burinsu.

Ana cikin haka Allah ya yiwa mijin Rahma rasuwa,
dole ta dawo gida da yan yaranta Faruq da Adam daga nan nauyin kula dasu ya dawo kan Nuruddeen,
abu ya had'e mishi gashi yanzu jikin Abba ya tsananta tsawon shekara guda kenan da abun ya tashi bai kuma sakeshi ba koda na dare biyu ne, duk ya rame ya lalace sai tsawonshi daya k'ara fitowa kana farinshi ya k'ara baiyyana
hancin nan nashi har kan baki,
gashi yanzu baifi gonaki shida bane ya rage musu, sai filayen cikin gari,
inda sunada fili a biyu a Sirinkiyo da katafila duk sunada fili anan,
sai kuma nan gidansu na gado da yake Dugge nan kusa da Fadan Dukku d'in .

dole ciwon Abba yasa aka saida gonaki biyu ya rage musu hud'u,
inda suka zuba kud'in wurin nema mishi mgnin.
Sukaje bauchi wurin wani Mlmi irin masu Islamic kemis innan,
nan duk kudaden suka k'are dan magungunansu da tsada,
Alhamdulillahi jikin ya d'anyi sauk'i sosai.
Sai kuma wani mak'ok'o ya fito mishi nanfa, suka fara jinyar asibiti kuma, amman ina abu sai gaba-gaba yakeyi,
ta kai matakin da ko tsawonshi baya iya mik'ewa.
Bappa Ali yace a kuma saida sauran gonakin amman Abba ya hana acewarshi kada su Kuma saida komai a kanshi dan yasan wannan ciwon ba barinshi zaiba kar yazo ya mutu bai barwa yaranshi komaiba,
sun so suk'i bin shawararshi amman sai yace bai yafe musuba in suka kuma saida wata kaddararshi dan jinyarshi,
su bari in ya rasu suyi duk yadda sukaga dama da kaddarorin da suka rage dole suka hak'ura, badon sun soba, haka yasa Nuruddeen zagewa da yin acaba don samo kud'in da za'a nema mishi mgni, wani lokacin sai k'arfe goma na dare yake baro gombe ya nufi Dukku.
Saifuddeen kuwa shike kula da Abban tunda yana gida,
bappa Ali ma yanzu bai fiye zamaba yana tafiye-tafiye dan yana bin kasuwannin k'auye yana aune-aunen kayan abinci. Still kuma dai yana kula da d'aliban sun, dan da safe baya tafiya sai ya karantar dasu na safe, kana in ya dawo da deddere bayan sallan isha za a hura wuta a tsakiyar tsangayar daliban su zazzauna kan itatuwan dake zagaye da wutan ayi ta karatu, sai k'arfe tara da rabi ake tashi,



Yau asabar da sanyin safiya Nuruddeen ya fara shirin tafiya gombe,
sai ya kuma fasa ya dawo ya zauna tsakiyar k'annenshi Raihana nayiwa su Faruq wonka dan Faruq ya fara zuwa makaranta, Abba kuwa yana zaune jingine da pillow,
kana Saifuddeen na gefenshi yana sa mishi sugar a cikin kunun koko da Ummi ta dama musu, kana Rahma kuma tana toya musu kosan da zasu had'a da kunun suyi karin kumallo dashi,
Raliyya kuwa wonke-wonke takeyi.
gefen Ummin shi ya zauna tare da tonkoshe kai irin yadda Saifuddeen keyi sannan yace.
"Na fasa tafiya yanzu yau sai azahar zan tafi."
cikin disashewar murya Abba yace.
"Meyasa?."
ajiyan zuciya yaja tare mik'e k'afafunshi kana ya yayi murmushi tare da cewa.
"Yau dai abincin Ummina zan ci."
Rahma ce ta juyo ta kallesu tare da cewa.
"Kuma dama d'an malele zamuyi yau Ya Seyo nasan kai kana son d'an malele,
ba irin Saifu ba da yake cewa muma mmki muke bashi wai shi baiga abin ciba a dan malele."
Hayatuddeen ne ya tura baki tare da cewa.
"Gskyan shi ai, dan malele fa abincin matane."
murmushi Ummin tayi tare cewa.
"Kada ku damu kowa zaici abinda yakeso, nasan Autana da Hamma Saifunshi da Abbanku suna son d'anwake, ni kuwa da sauran muna son d'an malale shiyasa nace ayi duka biyu kowa yaci abinda yake so."
murmushi sukayi baki d'aya kana sukaci gaba da hira,
sannan Rahma ta gama tuya ta kawo musu tsakiyarsu nan suka zauna sunaci suna hira,
saidai Ummi da Saifuddeen sam basuci wani mai yawa ba,
shi kuwa Nuruddeen sosai yaci kosan nan yana korawa da koko.
cikin kula Nuruddeen ya kalli Ummi tare da cewa.
"Lfy kuwa Ummi naga kinyi shiru da yawa, ko kokon baki shaba, gashi kin san Saifu bazai ciba muddin yaga kina cikin damuwa."
murmushi tayi sai kuma ga hawaye,
da sauri Saifuddeen ya zuba mata idanu lokaci d'aya idanunshi sukayi jazir.
shi kuwa Nuruddeen kasa had'iye abincin bakinshi yayi dan ji yayi ya mishi d'aci ranshi na suya,
tuni shima hawaye suka ciko mishi ido,
Rahma kuwa mik'ewa tayi ta shiga d'akinsu haka nan tausayin Umminsu da kanta da Saifuddeen yasata kuka tuno mijinta daya tafi ya barta, kana ga uba ba lfy. Kuka ne sosai ya rufeta tuno sam Umminsu tunda tayi aure take cikin k'uncin rayuwa.

Shi kuwa Nuruddeen cikin k'arfin zuciya ya sharce hawayenshi, kana ya d'ago kanshi ya kalli Ummi da ta zubawa Abba ido tana kuka,
cikin raunin murya yace.
"Ummi". kai ta juyo a hankali kana ta zuba mishi ido,
shi kuwa murmushi yayi still hawaye na zuba,
cikin k'arfin guiwa da yak'ini yace.
"Ummi ki kalleni, ki cewa k'annena su kalleni."
sai ya kuma share hawayenshi kana ya kalli Saifudden daya zuba mishi ido ko k'ibtawa bayayi sannan yaci gaba da cewa.
"Ummi na kada kiyi kuka, ki meda idanunki da buk'atun rayuwarki dana k'annena dana yaran k'anwata a kaina, dai zan iya kula daku, Ummi na kada kiyi kuka, kin ganniko ni d'innan nine farin cikinku, kin manta wanne suna kuka bani inkiya SEYO fa kike cemin to kuyi imani da Allah ku yarda da kaddara mai kyau ko akasinta, ku kalleni ni zan jure d'awainiya daku iya rai da mutuwa."
sai ya kuma kamo hannun Ummi da Abban su cikin rawan murya yace.
"In sha Allahu Ummi na ni d'innan sai na kaiku makka da madina birnin ma'aiki, insha Allah ni d'innan zan share hawayenku,
Ummi in dai fa ina raye to insha Allah bazakuyi kukaba."
sai ya kuma kalli Saifuddeen kana yace.
"Gamu Allah ya baku zaratan yara kyawawa muminai salihan bayin Allah,
ko ni na gaza zama gatanku in sha Allah Saifuddeen zai zama Garkuwar ku kuma zai saku farin ciki, zai kula daku ya ruggumi buk'atunku."
Raihana ce ta sharte hawayeta tare da cewa.
"Dan Allah ya Seyo kubar kukannan haka kallifa yadda kukasa Abba da Hamma Saifu kuka, please Ummi ki rink'a bamu k'arfin guiwa kada ki bari hawayenki suna zubowa."
jin haka yasa Ummi share hawayenta kana tasa hannu ta share na Saifuddeen da Seyo, shiko Saifuddeen ya share na Abbansu daya gaza cewa komai dan ya lura jikinsu ne ya fara basu zai mutu ya barsu da maraici.

Daga nan sai kuma suka d'an sake,
haka dai sukayi ta hira har Rahma ta gama musu abinci, kowa yaci abinda ransa keso.

Bayan anyi sallan azaharne, Seyo ya biya wurin mai kayan miya ya sayi naman miya dasu tattasai. al'basa, atraruhu. sannan yakuwa da alaiyahu da ganyen al'basa. Kana ya nufo gida a tsakiyan gida ya samu Ummi da Aunty Nina matar Bappa Ali,
nan yazo ya zauna yana dariya cikin yanayinshi na raha yace.
"Yau kam Ummi na k'uruciya takeji, kalli yadda tasha duma."
dariya sukayi baki d'aya kana yaje ya d'auko wuk'a da tire da babban roba ya debo ruwa a ciki kana yasa gishiri sannan yazo ya zauna gefenta ya fara wonke ganyen.
Bayan ya gama wonke ganyen ya tsanesu ya sakasu bisa tiren kana ya mik'e tsaye hannunshi dak'e jik'e har yana d'igar da ruwa, ne ya kallesu kana ya nunawa Ummi su sannan yayi mumurshi kana ya fara yarfasu yana watsar da ruwan yana barin jikin hannun nashi, still yana murmushi ta tare da tonk'oshe kanshi bisa kafad'unshi ya kalli Saifuddeen daya shigo yanzu hannunsa rik'e da carbi,
k'ara yarfa hannun nashi yayi a karo na bakwai sannan ya kallesu dukansu kana cikin yanayinshi na mai matuk'ar fara'a yace.
"Na gama! Ummi na gama!! Na gama!!! Nawa aikin na kammale komai saura kuma Saifuddeen zai k'arisa, kada ku tab'a komai ku barshi da wannan aikin zaiyi komai yadda ya kamata fiyema da yadda ni zanyi ko yadda zakuyi."
Zurui Ummi tayi tare da zuba mishi idanu,
Rahma kuwa murmushi tayi kana tace.
"Kai Ya Seyoji gani ni mace ga Raihana ga Ummi ga Raliyya duk bamuyi aikinba sai Saifuddeen namiji."
matsowa yayi kusa da Saifuddeen Kana ya had'e hannayensu wuri d'aya ya rik'e hannun Saifu gam cikin nasa kana ya kalli Rahma sannan yace.
"Wannan aikin nashi ne daga yau, ai ba aikin mata bane na mazane, shi zai iya ke bazaki iyaba."
Ummi kuwa ajiyan zuciya ta sauk'e kana tace.
"Yau kam bazaka je Gombe bako?."
sakin hannun Saifuddeen yayi kana ya gyara tsayuwarshi sannan yace.
"Zanje Ummi yanzuma zan tafi."
shiru sukayi baki d'aya kana Saifuddeen ya tsuguna a gabanshi yayi rubutu kamar haka.
"Ya Seyoji ka bari mana tunda bakayi sammako ba ka bari kawai sai gobe."
dafa kafad'unshi yayi kana yace.
"Saifuddeen ai tafiyar yau dolece a kaina dolen dole sai naje.
Dan ina son samo maka kud'in hidimar karatunka.
kana ga Faruq ma an kusa neman school fees,
ga Rahaina tace min auren k'awarta ya kusa zasuyi anko kaga dole in dage in isarmuku.
Gashi naga Leda carpet d'in Ummi na ya fara yagewa."
cikin kula Ummi tace to.
"Allah ya kiyaye hanya ya kaika lfy ya dawo da kai lfy, Allah ya baka sa'a."
"Amin Amin ya rabbil izzati." ya amsa kana ya juya ya shiga d'aki inda Abbansu yake, ya dade a cika sannan ya fito,
yana isewa inda suke ya kama hannun Saifuddeen yajashi suka nufi gaban Ummi sannan yace.
"Kin ganshi Ummi yaron kin nan ko yanada wata baiwa ta musamman a jikinshi, kuma ki kula zaki iya ganowa,
shiyasa ni bama zan fara yin aureba sai na fara yi mishi aure."
dariya sukayi baki d'aya kana yace.
"To Ummi na tafi."
Aunty Nina ce matar Bappa Ali wanda tun d'azu batayi mgnaba sai yanzu tace.
"Allah ya bada sa'a in kana dawowa ka siyo min a gwalima."
har ya juya zai fita sai ya kuma juyowa tare da zaro ido kana ya tab'e baki sannan yace.
"Kawai Aunty Nina kice mun kusa mu zama mu bakwai."
kai kawai ta kauda dan ta sanshi da iya zolaya,
daga nan basu kuma cewa komai ba,
yaja hannun Saifuddeen suka fita,
sun dad'e suna tsaye a bakin masallacin dake k'ofar gidansu.
bisa dukkan alamu mgna mai mahimmaci yakewa k'anin nashi,
har ya tada mashin d'in sai ya kuma kashewa ya sauka da sauri kana yayi cikin gida.
Yana shiga gaban Ummi ya d'an rusuna kana yace.
"Na manta Ummi bance miki kada kiyi kukaba shiyasa na dawo,
dan Allah Ummina kada kiyi kuka dukkan tsanani yana tare da sauk'i."
kai ta jinjina tare da cewa.
"To Nuruddeen insha Allah bazanyi kukaba."
mik'ewa yayi tare da cewa.
"To na tafi, hankalina a kwance tunda nasan bazakiyi min kukaba."
yana fita ya kuma tasa Saifuddeen da Hayatudden a gaba yai ta musu nasiha,
kana ya kuma hawa mashin d'in ya kunna,
still ya kuma kashewa ya sake komawa cikin gida kawai sai ya tsaya yayi ta kallon cikin gidan nasu baki d'aya, kana ya kuma dawo da hankalin shi da dubanshi kan Ummi, ya kai 5 minutes yana kallonta tana kallonshi amman babu wanda yayi mgna cikinsu,
hakama yayi da Raihana da Raliya,
Rahma kuwa tana ganin yadda yaketa binsu da kallo sai kawai taji hawaye na kwaranyo mata,
kuma ta kasa cewa komai,
shima Nuruddeen hawayen ne yaji suna zubo mishi, sanin in Ummi taga hawayenshi hankalinta zai tashi,
sai yayi maza ya fita.

Hannun Hayatuddeen ya kamo ya saka cikin na Saifuddeen kana yace.
"Ka rik'eshi fiye da yadda uwa zata rik'i d'anta, ka hanashi kukan maraici, ka hana Ummi kukan k'unci, ka zamewa su Rahma Garkuwa kada ka bari yaranta suyi maraici."
sai ya kuma kalli Hayatuddeen kana yace.
"Autanmu kaga Hamma Saifunka ko to ba Yaya bane kawai a wurinka ubane a wurinka, kayi mishi dukkan biyayyan da d'a zaiwa ubanshi ku had'a kanku, ku had'a hannu ku share hawayen Ummi da yan uwanmu matannan. Ni kam Addu'a kawai nakeso daga gareku."
Duk sun kasa motsi domin shi dai Saifuddeen kalaman Yayanshi ya sakar mishi kasala, shiko Hayatuddeen, ido kawai ya zubawa fuskokinsu ya kalli wannan kana ya juyo ya kalli wannan.
Shi kuwa Nuruddeen, tada mashin d'in nashi yayi sannan ya takata,
ya k'ara masowa gab da Saifuddeen suka kalli juna kana yayi murmushin da yasa hawayen shi kwaranyowa a idanunshi ,cikin zubda hawaye murya na rawa yace.
"Saifuddeen babu nakasasshe sai rago, kuma nasan kai ba rago bane,
Saifuddeen kasa a ranka Nakasa ba kasawa bace."
yana fad'in haka ya ja mashin d'inshi ya tafi, yana woiwoyosu, Hayatuddeen kuwa sai hannu yake d'aga mishi, shiko Saifudddeen addu'a ya rink'a mishi a ransa.


A cikin Gombe kuwa, Nuruddeen yana shiga gari yana bisa babban titin tashan Dukku yana isowa dai-dai Tashan Dukku yazo dai-dai bakin tashar kenan shi yana shirin wucewa, kana wata mota ta fito cikin tashan dai-dai lokacin da Nuruddeen yazo bakin wurin, wannan motar birkinta ya d'an kubcewa matuk'inta.
Cikin rashin sa'ar takan birkin tayi kan Nuruddeen.....!!!





By
*GARKUWAR FULANI*
8/

*NAKASA BA KASAWA BACE*


*PAGE 3*


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


_Wannan page Ι—in nakune gaba Ι—ayanshi Ζ΄an Hukuncin Allah fans Especially Mom Asas, Zee Ya'u, Jannart Salis, ina muku fatan al'khairi._

~Gareku masu buΖ™atan biyan kuΙ—in littafin ,turo katin mtn na Ι—ari uku, ta wannan layin 09097853276 ko transfer ta nan 0005388578 jaiz bank Asha Aliyu Garkuwa~

Cikin tsananin razana da tsoro jiki na rawa mai jan motar ya fara kiciniyar taka birki.
Amman ina abin ya gagara, tuni birkinta ya kubce mishi, ido ya zaro da sauri lokacin da yaga motar tashi ta nufi kan Nuruddeen gadan-gadan
ji kakeyi k'uuuuuiyyyyhh.
motarnan ta bugu machine d'in Nuruddeeen bugu mai tsanani wanda yasa, Nuruddeen yayi tsalle yayi sama kana ya fad'o kan bump d'in tsakiyar titin,
"Innalillahi'wa'illaihi rajiun. Hasbunallahu wani'imal wakil."
Shine abinda tarin mutanen dake zageye da Nuruddeen suke fad'i,
yayinda wasu suka ma kasa mgna sai d'aura hannu sukayi a kai, kana wasu sai jujjuya kai sukeyi.
mai mota kuwa da ker ya samu ya fara sarrafa motar har ya samu ta tsaya,
yana fitowa da gudu ya nufi inda dandazon mutanen suke,
kutsawa yayi tayi tsakiyar mutanen har ya samu ya isa,
ido ya rumtse da k'arfi cikin tsananin fargaba ya sunkuyo kan Nuruddeen da yake konce lib bisa titi, ida nunshi a rufe kirib sai numfashin shi dake korar juna,
da sauri ya tallaboshi tare dagowa ya kalli mutanen cikin tashin hankali yace.
"Ku taimaka min mana in d'agashi in sashi a mota."
wani k'ak'k'arfan matashi ne,
yayi maza ya sunkuyo ya ciccibi Nuruddeen kana cikin, d'aga murya yace.
"Biyoni."
yana fad'in haka ya juya ya tsallaka titin zuwa d'aya hannun kana ya nufi cikin asibitin MUSABA dake fuskantar tashan Dukkun,
cikin rawan jiki mutumin ya mik'e kana yabi bayanshi.
suna shiga Reception suka nufa,
ganin sun shigo hajaram majaram yasa Nurse's yin kansu da tambayar meke faruwa,
cikin kad'uwa mutumin nan yace,
"Accident ne ku taimaka doctor ya dubashi."
juyawa sukayi suka kalli juna, kana d'aya daga cikinsu tace.
"Ko an gayawa doctor bazai dubashi ba sai an nemo police."
jin haka yasa mutumin nan juyawa da sauri ya fita,
gudu-gudu sauri-sauri ya tsallaka titin kana ya nufi wurin motar tashi, yana shiga ya nufi Gombe division yana zuwa ya musu bayanin abinda ke faruwa,
ba b'ata lokaci suka had'ashi da police d'aya, kana suka tafi tare,
suna zuwa Doctor in ya amsheshi bisa sa hannun hukuma kana fara bashi taimakon gaggawa, sannan daga bisani ya ce su tafi Medical Center.
Ba b'ata lokaci suka amshi shawararshi suka tafi can,
suna zuwa aka amsheshi.

shi kuwa police yasa d'aya police d'in yaje ya d'auki machine d'n nashi ya kaishi officensu.
kana sun samu wayarshi y'ar Nokia dake jikinshi tanan aka kira Bappa Ali aka sanar mishi meke faruwa.

Lokacin da aka gayawa Bappa Ali yana cikin garin kurugu da yake ranar larabace,
to yaje cin kasuwa,
ana gaya mishi bawan Allah ya bar duk abinda yakeyi ya nufi cikin Gombe kai tsaye Medical Center din ya nufa, inda yana zuwa fargabarshi ta k'aru domin tunda Nuruddeen ya fad'i bai sake bud'e idanunshi ba kuma uwa uba yana konce tamkar gawa komai sai an mishi ga roba a hanci da baki da k'asanshi wannan abu yayi matuk'ar firgitashi, duk da k'arfin zuciya irin na bappa Ali sai da yayi ta kuka,
mutumin daya bugi Nuruddeeen ma sai kukan yake sabida kukan da Bappa Ali keyi ya matuk'ar karya mishi zuciya sai hak'uri yake bashi da neman yafiyarsu.
Cikin raunin murya yake cewa.
"Ku gafar ceni tsautsayine, nayi iya k'ok'arina inga na tsare motata bataje ta bugeshi ba amman ina Allah ya k'addara faruwar hatsarin bani da tsumi ko wayo bare k'arfin hanawa."
sai ya kuma sharte hawayenshi kana yaci gaba da cewa.
"Tunda nake ban tab'a shiga cikin tashan Dukku ba, sai yau, ashe ashe ban saniba masifa ke kirana."
shi kuwa Bappa Ali ya gaza cewa komai domin da ganin mutumin ya girmeshi kuma bisa dukkan alamu mutum ne mai daraja da ka ganshi kasan mai kamalane,
shi kuwa mutum shirun Bappa Ali sai ya sa mishi rauni yana ganin shike nan ya cucesu,
yana bashi hak'uri yana tuno dalilin zuwanshi tashan,
dan matarshi da ta kasance yar Ngalda to kullum shi ke kaita to yau kuma har ya shirya zai kaita sai kuma motocin kayanshi suka iso, so shiyasa yace bari ya kaita tasha ta shiga motar kasuwa, to shinefa ya kaita kenan yana fitowa wannan hatsarin ya auku.


Bappa Ali kuwa ganin yanata bashi hak'uri ya sashi yin k'arfin halin cewa.
"Ba komai Allah ya bashi lfy, ai shi tsautsayi ba ta inda baya wakana."
sosai mutumin ya d'anji sanyi kana yace.
"Wacce uguwa kuke ne?."
cikin sanyi Bappa Ali yace.
"Har Dukku muke."
da sauri yace.
"Ina mamanshi?."
kai ya jinjina kana yace.
"Mamanshi da babanshi duk basu saniba, suna Dukku ni kuma dama ina Kurugu to da aka kirani sai na taho nand'in.
Yanzu in ba matsala in akwai masu kula dashi zan wuce Dukku inje in sanar musu."
cikin kad'uwa yace.
"To kai waye d'inshi ne?."
"Ni bappanshi ne k'anin mahaifinshi kuma mahaifin nashima baida lfy."
kai ya jinjina kana ya zaro kud'i a aljihunshi sannan ya mik'a mishi tare da cewa.
"Ba matsala zan kula da komai kayi maza kaje ka sanar musu."
k'in amsar kud'in yayi, shi kuwa mutumin ya sashi karb'a a dole.

Haka dai ya amshi kudin badon ya soba ya tafi,
shi kuwa mutumin shida kanshi ya zauna wurin kana ya bada duk abinda ya dace na jinyar Nuruddeen.


Shi kuwa bappa Ali daya koma Dukku jiki a mace yayiwa Ummi bayani sai dai ya boye mata hak'ik'anin halin da Seyojinta ke ciki, yace mata da sauk'i sosai baiji ciwoba an dai mishi allurar bacci ne dan ya huta.
To shiyasa hankalin ta bai tashi sosaiba,
Saifuddeen kuma tun lokacin da Yayan nashi ya tafi sai yaja hannun Hayatuddeen suka tafi gidan Goggo Dada, to shiyasa bappa Ali bai tarar dashi a gidaba,
kuma gidan Goggo Dada nada d'an nisa don ita a Shabewa take.
Abba kuwa baida lfy ba damar yaje,
haka yasa Bappa Ali ya juya shida Adnan babban abokin Nuruddeen d'in,
kana sai Rahma.

Koda sukaje gaba d'aya hankalinsu ya tashi ganin yadda Nuruddeen ke kwance tamkar gawa Rahma tayi ta kuka tamkar ranta zai fita,
Adnan yanata rarrashinta,
Bappa Ali kuwa mutumin ne keta rarrashinsa.

Ganin dare ya fara nisa yasa Bappa Ali cewa Rahma ta koma dan har takwas na

Please Login or Register in order to submit comment