Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai wani fari mai d'aukar hankali da ya k'ara.
Dr Adnan kuwa ido ya zubawa na'urar dake gefen kan Saifuddeen d'in wanda Dr Acash prasat ke kimtsawa,
Dr Malik kuwa hannunshi yasa yana jan yatsun k'afar Saifuddeen sannan ya juyo ya kalli Bappa Ali da ke cikin kid'ima cikin harshen larabci yacewa bappa Ali.
"Ba komai fa da yardar Allah zai samu lfy,
adai tayamu da addu'a in sha Allah zai samu waraka,
kuyi hak'uri komai zaiyi dai-dai amman sai mun hak'ura domin sauk'i a hankali yake samuwa."
kai bappa Ali ya jinjina alamun gamsuwa kana ya juyo da ganinshi kan Dr Adnan dake cewa.
"Yauwa Bappa Ali yanzu mu fita,
dan ba'a son yawanta surutu a kanshi."
Ahmad ne ya motso jikin gadon hannunshi yasa ya shafa fuskar Saifuddeen cikin sanyin lafazi yace.
"In sha Allah zaka samu lfy in Allah ya yarda zamu jure ko wanne wuya zamu kuma dage da addu'a in sha Allah zaka samu lfy."
sai kuma yayi sauri ya juya ya fita dan jin hawayenshi na zubowa.
Da sauri Bappa Ali yabi bayanshi, a wannan wurin suka zauna, shi kuwa
Hayatuddeen a hankali ya bud'e baki cikin sanyi ya kamo hannun Hamman nashi murya can k'asa yace.
"Ummi tace in gaidaka da jiki, Adda Raihana ma tace in gaidaka."
sam baya iya motsa komai na jikinshi shiyasa sai da ido yake musu mgn,
yana son ya d'ago tafin hannunshi ya sharewa Hayatuddeen hawayenshi dake kwaranyowa amman bazai iyaba, hakan ne ya sashi rumtse ido yana mai jin ciwo a duk wani sashi na jikinshi,
ganin haka yasa Dr Adnan yaja Hayatuddeen suka fira.

Bayan fitarsu da kamar 23 minutes su Dr Acash suka fito suma.
Dr Malik yace yana son ganin su da yamma.
to sukace sannan duk suka nufi masauk'insu.

Zaune suke a parlour kowa da abinda ke ranshi,
Dr Adnan ne yayi gyaran murya cikin sanyin sauti yace.
"Bappa Ali munyi yawa anan dole wasunmu su hanzarta komawa gida Nigeria dan zamanmu zai k'ara tada hankalin Ummi,
amman in wasu sun koma sun gaya mata jikin da sauk'i zatafi samun nitsuwa."
gyara zama Bappa Alin yayi tare da cewa.
"Hankali na ya tashi da yanayin jikin Saifuddeen, bana son inyi nesa dashi."
sai dai ko in Ahmad da Hayatuddeen ne zasu koma."
cikin sauri fuska cike da rauni Hayatuddeen yace.
"Bappa Ali in tafi in bar Hamma na kenan?."
shi kuwa Ahmad kai ya jujjuya tare da cewa.
"Kayi hak'uri kawu Ali, komarka nada mahimmanci dan Ummi zatafi gamsuwa da kalamanka, sannan kasuwancinmu yafi buk'atarka akan ni,
kuma kaga shima Ya Adnan ya kusa komawa, in mun tafi yazo shima ya tafi sauran kai d'aya,
bazaka iya d'awainiyar ba,
amman yanzu in kaje ka kwantar musu da hankalin bazai jimaba shima ya Adnan zai komo ya kuma kontar musu hankali ni da Hayatuddeen kuwa zamu kula da komai in munga sauk'in jiki sai nima in koma sai su Ummin suzo su dubashi."
shiru sukayi baki d'aya dan jin ta bakin bappa Ali.
Cikin gamsuwa yace to ba matsala in sha Allah cikin satin nan zan wuce.
sosai Dr Adnan yaji dad'in hakan.

Da yamma Dr Adnan da Bappa Ali suka shirya suka koma cikin asibitin kai tsaye office d'in Dr Malik Khan suka wuce.
Nan suka samu Dr Acash ma a nan bayan sun gaisane Dr Acash ya gyara zamanshi tare da fuskantarsu da kyau cikin nitsuwa yace.
"Jikin Saifuddeen dai da sauk'i sosai, amman akwai buk'atar k'arin kula da jinyarshi,
in da hali nanda wata biyu zuwa uku akwai buk'atar canji asibiti daga nan New Delhi za'a maidaku Mumbai zuwa babban asibitin.
Orthopedic hospital zanyi k'ok'arin hadaku da d'aya daga cikin manyan doctors d'in.
Physiotherapist domin sune suk'eda gwarewa da k'ok'arin farfad'o da aikin lakar jiki ga wad'anda akayiwa aiki dama wanda ba'a samu damar yi musu aikin ba.
To shiyasa nake son turaku garesu in munyi sa'a zai samu sauk'i cikin k'ank'anin lokaci tunda an mishi surgery sannan an sama mishi kular likitocin fisiyo to muna da k'arfin guiwar samun sauk'inshi."
cikin gamsuwa Dr Adnan yace.
"Ba matsala in dai hakan ya kamata ayi duk abinda ya dace kawai."
shima bappa Ali cikin gamsuwa ya gyad'a kai,
sai kuma suka nitsu jin Dr Malik Khan na cewa.
"Alhamdulillahi ko yanzu muna ganin alamun sauk'i sosai a jikinshi alamun aikin da akayi mishi yayi kyau to amman yana da kyau ku kaishi Mumbai d'in domin acan zai samu duk abinda ya dace a sauk'ak'e, likitocin zasu rink'a kula dashi sosai dan canma asibitin mune, munfi zama a canma nan duk wata sa huɗu muke zuwa muyi aiki,
so a can akwai.
Orthopedic surgeon likitocin da suka k'ware a fannin k'ashi, ga kuma neurosurgeon da suka kware fannin k'wak'walwa, to suke kula da masu larurar. So zai samu wadacecciyar kulawa da treatment mai kyau da ink'anci, da taimaka musu wurin movement motsa jiki da da kuma yin exercise a rink'a strengthen muscles d'in manual therapy. koyar dashi duk wani abinda ya dace tare da bashi shawarwari yadda zai kula da kanshi bayan an sallamesh.
Sai dai kam akwai cin kud'i amman in sha Allah zai samu lfy."
cikin gamsuwa Bappa Ali ya kalli Doctors d'in tare da cewa.
"Ba matsala aiyi duk abinda ya dace fatana samun lafiyar d'an d'an uwan na."
murmushi Dr Malik Khan yayi tare da cewa.
"To Alhamdulillahi yanzu dai muna bashi Drugs masu rage mishi symptoms d'in ciwon sosai, kuma Alhamdulillahi yana jin dad'insu, so yana gama shansu zamu yi muku transfer zuwa can d'in."
sosai Dr Malik Khan ya musu cikekken bayanin da zai sama musu nitsuwa har saida yaga hankalin su ya kwanta sannan ya sallamesu suka fita suka tafi.

Daga ranar ba'a sake barinsu sun ganshiba sai bayan kwana hud'u wanda kuma a ranar ne Bappa Ali zai koma gida Nigeria.
Da sanyin safiya suka nufi cikin asibitin bisa jagorancin Dr Malik Khan suka samu suka shiga suka ganshi, kuma Alhamdulillahi sosai suka samu nitsuwa dan sunga alamun d'an sauk'i a jikinshi,
suna fitowa Bappa Ali ya shiga taxi ya nufi airport k'arfe sha d'aya dai-dai jirginsu ya tashi.

Su kuma kai tsaye masauk'insu suka koma.

Bappa Ali kuwa komawarshi ya samawa Ummi nitsuwa sosai dan ya kontar mata hankali ya b'oye mata batun sauyin asibiti ya samu kuma ya hanata tafiyar yafi son sai sun koma Mumbai d'in taje.

Warisu da Mudassir da Bello kuwa suna kula da kasuwancinsu yadda ya kamata.

Bappa Ali ya dawo da kwana biyar Salisu yaje India ya duba jikin abokin nashi kwana biyar yayi ya dawo gida Nigeria shima ya k'ara kontarwa Ummi hankalinta sosai.

Sai dai sunyiwa Ishaq bayanin komai,
yaso yaje sai suka hanashi a kan ya bari sai sun koma Mumbai d'in sai yaje da Ummin dan dole ya hak'ura.

***
Yau watan su Saifuddeen d'aya da kwana goma kwanansu arba'in kenan a can,
kuma yau ne zasu wuce Mumbai tare da jagorancin Dr Acash prasat.

K'arfe biyar dai-dai jirginsu yayi sauk'an ank'ulu a babban filin shige da ficen.
Hilton Mumbai international Airport.

Daga nan Airport d'in kai tsaye asibiti suka wuce.
*Nanavati super speciality hospital*.  
Shine sunan dake liƙe asaman asibitin da akayiwa su Saifuddeen transfer. Asibitine da haɗuwarsa ya zarce misali don ya ƙawatu sosai, komai na cikinsa gwanin burgewa ne, ko ina kakai dubanka zakaganshi ya ƙawatar gwanin ban sha'awa, don sosai haɗuwarsa ya zarce na garin New Delhi.

Mutane ne keta hada-hadan shiga da fice daga cikin asibitin.
Koda suka ƙaraso cikin asibitin ɗaki na musamman aka samawa Saifuddeen tare da taimakon Dr Acash prasat,   Dr.Adnan da Ahmad ne suka ɗaga Saifuddeen daga kan weelchair ɗin da suka turosa akai, kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin wanda yaji lallausan katifa suka shimfiɗesa, ahankali ya maida kyawawan idanunsa ya rufe tare da ɗan sauƙe ajiyar zuciya.  Kafaɗansa Dr.Adnan ya ɗan dafa a hankali, jin an dafa kafaɗansa ya sanyashi buɗe idanunsa ya sauƙesu akan laɓɓan Dr.Adnan,
Dr.Adnan kuwa ganin Saifuddeen na kallonsa ya sanyashi cewa.
"Yajikin naka?" 
Kyakkyawan murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, kansa yaɗan jinjina alamar da sauƙi, tare dakai dubansa ga Hayatuddeen dake tsaye ya kafesa da ido, murmushinsa me kyau yayiwa Hayatuddeen tare da miƙo masa hannunsa, ganin haka yasa Hayatudden cikin tsananin ƙaunar da yake yiwa ɗan uwan nasa yataho garesa tare da miƙa masa hannu shima, damƙe hannun Hayatuddeen yayi acikin nasa hannunsa tare da lumshe idanunsa,  sosai yakejin son ƴan uwansa acikin rai da zuciyarsa, tabbas yasan Allah shine gatan kowani bawa, amma kuma yasan duk wani buri da fatan ƴan uwansa akanshi yake, shi musulmine da ya yarda da ƙaddara me kyau ko akasinta, haka kuma yayi imani cewa komai ya faru da bawa muƙaddarine daga Allah,
Sake rufe idanunsa yayi kirif yayinda zara zaran eye lashes ɗinsa suka kwanta luf aƙasan idanunsa, gashin giransa kuwa sai shinning yake kamar wanda aka shafawa mai, uwa uba ga tohon sabon gashi na tattausan sajen da ya fara yiwa fuskarsa k'awanya, sosai fuskarsa tayi fayau da ita hasken fatarsa yasake bayyana, haƙiƙa Saifuddeen kyakkyawane sosai, sannan duk da nakasar dake tare dashi komai nasa abun burgewa ne da so,  ganin kamar yayi bacci ne yasanya Dr.Adnan duban Ahmad da Hayatuddeen cikin kulawa yace.
"Yakamata ace kuje ku nemi masauƙi tunda Dr.Acash yayi mana komai ya kuma sama mana nurses ɗin da zasuna kula dashi, sannan gani ni zan zauna atare dashi."
Jinjina kai Ahmad yayi tare da duban hayatuddeen da har yanzun hanunsa ke cikin na Hamma Saifuddeen ɗinsa. "Mutafi ko Hayatuddeen, naga idanunsa arufe inaga yasamu bacci".
Ahmad yafaɗa yana me kallon Saifuddeen.

Kallon Hamma Saifuddeen ɗin hayatuddeen yayi,cike da tausayin ɗan uwan nasa ya soma yunƙurin zare hannunsa dake cikin nasa,  har acikin ransa yakejin tausayin Hamman nasa, tabbas shikam da ace ana sauya ƙaddara, to da tuni ya sauya ta hammanshi daga mummuna izuwa kyakkyawa.
  Haka Hayatuddeen da Ahmad suka baro cikin asibitin don nemawa kansu masauƙin da zasu zauna,  taxi suka shiga inda suka ce yakaisu hotel wanda yake mafi kusa.

Tafiya kad'an sukayi kana motar ta ratsa cikin Ƙofar katafaren hotel d'in.
Sahar International Mumbai,  mai taxi din ya sauƙesu, hotel ne ƙawatacce me kyaun gaske wanda yake ɗauke da dogon gine gine gwanin burgewa.
Kallon Ahmad Hayatudden yayi bayan sun sauƙa daga taxi ɗin sun biya me taxi ɗin kuɗinsa, cikin yanayi naɗan damuwa yace.
"Ya Ahmad baka ganin wannan hotel ɗin zaiyi tsada da yawa? ka duba kyawunsa fa".
Ɗan jim Ahmad yayi tare da ɗaga kansa yana ƙarewa hotel ɗin kallo, asanyaye yace.
"To Hayatuddeen ya zamuyi, dole haka zamu kama saboda shikaɗaine zai sauƙaƙa mana wahalan zuwa asibiti, kaga idan bashi ba ko ina muka kama sai munyi ta cacan kuɗin transport, kaga kuma wannan ma ƙarin ɗawainiya ne". 
Kai Hayatuddeen ya jinjina cike da gamsuwa da kalaman Ahmad, atare suka jera har zuwa cikin hotel ɗin inda suka tsaya a receiption.  saida sukayi duk wani abun daya dace kana suka biya kuɗi sannan aka basu makulli da kuma nomban ɗakin da suka kama,   tafiya suke suna me dudduba nambobin ɗakunan har suka iso ɗakin dayake da namba dai-dai da wanda aka basu, Ahmad ne yasanya key ya buɗe ƙofar ɗakin, Hayatuddeen na biye dashi abaya haka suka shiga cikin ɗakin, amatuƙar gajiye hayatudden ya faɗa kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin, wanda ke ɗauke da wata luntsumemiyar katifa me laushin gaske, lumshe idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kallonsa Ahmad yayi tare da girgiza kai aransa yana me cewa .
"Allah Ya shirya mana kai Auntan Ummi".
  kasancewar agajiye suke su dukansu, yasanya Ahmad soma ɗan rage kayan jikinsa kana ya wuce bathroom,  wanka yayi tare da ɗauro alwala don gabatar da sallan magriba wanda daf ake da cikar lokacinta, yana fitowa daga cikin bathroom ɗin yaci karo da wandon Hayatudden daya cire yayi wurgi dashi atsakiyan ɗakin, gefe kaɗan ma rigarsa ce wanda ya cire a yashe, cike da takaicin halin Hayatuddeen Ahmad ya girgiza kansa tare da ƙarasawa gaban mirror, don yasan idan yace da Hayatudden ya ɗauke kayan nasa daga ƙasan ma, wani sabon sakalci ne zai tashi, hakan yasa ya ƙyaleshi yashiga fito da kayansa dake cikin jaka don zaɓan wanda zai saka.
  Haka dai cike da sangarta Hayatuddeen ya wuce bathroom shima yayi wanka tare da ɗauro alwala,  koda ya fito awankan kamar yanda ya saba haka ya zazzage kayansu dake cikin jakan kaf akan gado, shidai Ahmad yana kallonsa bai kulasa ba, don yasan me hali baya taɓa fasa halinsa,  riga da wando na jeans Hayatuddeen yasanya cike da sakalci ya dubi Ahmad dake ƙoƙarin rufe kwalban turaren dake hannunsa, ɗan ɓata fuska yayi tare da shafa cikinsa cikin murya me ɗauke da gajiya yace.
"Yaya Ahmad nifa gaskiya yunwa nakeji, gashi bamu sayawa su Hamma Saifuddeen abinci ba!"

"To acici kai-dai baka da wani zance saina ci, yanzun idan mukayi sallah sai munemi waje mafi kusa musai abinci mukai musu, don tabbas nasan zuwa yanzu dole zasuji yunwa".
 Ahmad yafaɗa yana me ƙoƙarin saka takalmi aƙafarsa.
Shi kuwa Hayatuddeen bai sake cewa komai ba har Ahmad yagama kimtsa kansa suka fice daga cikin ɗakin, cikin harshen turanci Ahmad ya tambayi ma'aikatan dake aiki a hotel ɗin inda zai samu abinci,  dayake babu wani nisa tsakanin hotel ɗin da kuma inda ake sai da abincin hakan yasa ɗaya daga cikin ma aikatan yayi musu kwatance,  saida suka fara zuwa wani masallaci da ke nan kusa suka gabatar da sallan Magriba, daga Hayatudden har Ahmad babu wanda daya kafa goshinsa aƙasa ba tare da yayiwa Saifuddeen addu'ar samun lafiya ba, 
suna idar da addu'o'insu suka nufi inda zai sadasu da inda ake saida abinci. 
Koda suka ƙarisa wajen cin abincin, waje ne me kyau da tsabta sannan babu irin abincin da babu awajen,  cimar Nigeria sukaci, inda Ahmad yaci Fish roll and gas meat, shikuwa Hayatuddeen yaci roasted fish da kuma damammiyar madara me kaurin gaske, daganan takeaway sukayiwa su Dr.Adnan da Saifuddeen, kasancewar tsakanin hotel ɗin da asibitin babu wani nisa sosai hakan yasa da ƙafansu suka shiga takawa har zuwa privet hospital ɗin.
Kaitsaye inda su Hamma Saifuddeen din suke suka nufa,  abakin ƙofar ɗakin da Saifudden ɗin yake suka hango Dr.Adnan tare da Dr.Acash prasat, da alama magana suke mai mahimmanci, tsayawa sukayi daga gefe har saida suka kammala maganan kafun suka ƙaraso, kallon fuskan Dr. Adnan sukayi su duka, cikin yanayi naɗan damuwa Ahmad yace.
"Akwai matsala ne?"
Kai Dr.Adnan yagirgiza tare da cewa.
"No babu wata matsala, sai-dai bayanzu zamu samu ganin doctors ɗinba aƙalla sai munshare kwana biyu kafun mugansu,
  Dr.Anan Mehta, ƙwararren  likitane a ɓangaren  Orthopeadic surgeon, sai kuma  Dr.Mahesh Khurana, wanda shima ƙwararrene afannin neurosurgeon, muna da buƙatan ganin wad'annan likitotin don kuwa sune masu kula da irin lalurar Saifuddeen, fatanmu akullum dai shine Allah yabashi lafiya".
Da.
"Amin Amin". suka amsa su dukansu, ko wanne zuciyarsa cike da tausayin Saifuddeen. 
Ganin rauni nashirin bayyana akan fuskokinsu ne yasanya Dr.Adnan karɓan takeaway din hannunsu kana yace su koma masauƙinsu su huta sai kuma zuwa da safe idan Allah yakai rai,  bazasu musa masa ba domin dama agajiye suke, hakan yasa sukayi masa saida safe, koda Hayatuddeen ya buƙaci ganin Hamman nashi cewa dashi Dr.Adnan yayi yayi bacci sannan ba aso atasheshi, dole haka Hayatuddeen ya haƙura yabi Ahmad suka koma masauƙinsu.

Koda Dr.Adnan ya koma cikin ɗakin nan ya iske Saifuddeen kamar yanda yafita ya barshi wato idanunsa alumshe tamkar wanda yake bacci, shi kuwa Saifuddeen ba bacci yake ba, yayi nisa ne akan tunanin Zaliha, kyakkyawar fuskarta ne keyi masa gizo acikin ƙwayan idanunsa da zuciyarshi, tuno da yanda ta rungumesa ta baya tana me jansa akan su gudu alokacin da yaran Dalla suka kusa cimmasa  yasanya tsikar jikinsa tashi, lokaci guda ya tuno da taushin hannuwanta da kuma yanda daddaɗan ƙamshin turarenta ya zautar dashi,  yanayin da yakejin kansa aciki, ya sanya shi jin tamkar alokacin abun ke faruwa, sake lumshe idanunsa yayi alokacin da ya tuna da yanda bakinta ke motsawa alokacin da take cewa yazo su gudu kada su cutar dashi, wani irin yawu ya haɗiya wanda tuntuni ya tsaya masa amaƙoshi, gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi wani iri, yayinda yakejin wani irin sassanyan yanayi shauƙin sha'awa na musamman suka rufeshi dangane da ita.     "Saifuddeen!".
Dr Adnan yaƙira sunanshi yana me kamo hannunshi, tayanda zaiji ya buɗe ido, jin sauƙan hannu akan nasa hannun yasanyashi buɗe idanunsa ahankali, murmushi Dr Adnan yayi masa tare da cewa.
"Tashi kaci abinci, danajika shiru na ɗauka ma ai bacci kakeyi".
Ɗan murmusawa kawai Saifuddeen yayi, inda shi kuma Dr Adnan yaɗan ɗago saman gadon da Saifuddeen ɗin yake yayi sama, shida kansa ya gyara masa kwanciya inda yayi kamar azaune yake saidai kuma bayansa yana jingine ne da gadon, abinci Dr Adnan ya miƙo masa kana ya koma gefe shima ya soma cin nasa,   cikin nutsuwa haka Saifuddeen ya shiga cin abincin ahankali yake ɗan lumshe kyawawan idanunsa masu matuƙar ɗaukar hankali, haryanzu tunaninta ne kwance aƙasan zuciyarsa, ahaka dai har ya ɗanci abincin kaɗan ya ture sauran gefe, don shi ba mutum bane me yawan cin abinci sosai...


Gombe Nigeria

Dawowarta daga wajen aiki kenan,
aɗan gajiye ta shigo cikin  haɗaɗɗen ɗakin nata, jakar dake hannunta ta aje gefe tare da soma rage kayan jikinta, saida ta cire komai na jikinta sannan ta sanya wata kekyawar rigan wanka baby pink colour, dogon gashinta ta ɗaure da ribbom sannan ta wuce kai tsaye zuwa toilet, wanka tayi da sabulunta me daɗin ƙamshi kana ta ɗauro alwala, kasancewar ankusa ƙiran sallan Magriba, zama tayi agaban tangamemen dressing mirror'n ta wanda gabansa ke cike maƙil da kayan shafa masu kyau da tsada, body lotion ɗinta tashafa wanda gaba ɗaya sanyin ƙamshinsa ya game ɗakin, yanayin yanda takejin kanta agajiye yasanyata miƙewa tsaye, ahankali ta ƙarasa gaban drawer ɗinta wanda cikinsa ke shaƙe tam da kayan sawanta masu kyau da tsada, wanda ita kanta batasan iyaka yawan suturun sawanta ba, wata ƴar doguwar riga marar nauyi ta zaro wanda yake daga ɓangaren kayanta marassa nauyi, rigar irin mai taushin nanne wanda takebin jikin mutum ta lafe, da fararen stones aka ƙawata wuya da hannayen rigan, wanda hakan kuma ba ƙaramin ƙarawa rigan kyau yayi ba, sosai rigan ta amshi jikinta ta lafe, hakan yasa kyakkyawan body structure ɗinta bayyana, wanda da ace lafiyayyen Namiji zai gani to fa tabbas dasai ya rasa nutsuwarsa, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasanyata zura wani dogon hijab ajikinta tare da shumfuɗa sallaya, koda ta idar da sallan magriba bata tashi akan sallayan ba har saida ta sallame sallan Isha, bayan ta tarin addu'ointa wanda mafi yawansu akan Saifuddeen ne, cikin sanyin jiki ta tashi daga kan sallayan tare da cire hijab ɗin ta ninkesa, kana tayi taku uku zuwa biyar ta isa bakin gadonta kwanciya tayi akan lallausan gadonda tare da jawo pillow ta matse a ƙirjinta, rumtse idanunta tayi da tsananin k'arfi tare da fesar da wani zazzafan numfashi me ɗan karen zafi yayinda takejin wasu zazzafan hawaye sun tsastsafo mata cikin jijiyoyin idanunta, cusa kanta tayi cikin hannayenta tanajin akowani bugu na zuciyarta da tunaninsa yake wanzuwa, ina yake!? a ina zan ganshi? wani hali yake ciki? sun kasheshi ko yana da rai? tana da buƙatar sanin waƴannan amsan fiye da komai ayanzu, gyara kwanciyarta tayi tare da buɗe idanunta, kan zanen pop'n dake mamaye saman ɗakin ta tsaida idanunta sun kad'a sunyi jazir cikin raunin murya take cewa.
"Ya Allah kasa ako ina yake yana cikin ƙoshin lafiya, in kuwa sun mishi rauni ya Allah ka bashi lfy!".
tafaɗi haka aɗan raunane, ahankali hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa suka biyo ta gefen kumatunta, haƙiƙa zuciyarta cike take da son jin wani abu daga garesa, yayinda idanuwanta kuwa ke ɗokin sake ganinsa, tunaninsa ya matuƙar tsaya mata azuciya babu dare ba rana ko yaushe bata da sukuni bata fahimtar komai domin duk nazarinta da tunaninta a kanshi yake k'arewa,
sake muskutawa tayi ta gyara kwanciyarta akaro na biyu, kana ta lumshe idanunta da har yanzu suke ɗigan hawaye, da sauri ta buɗe idanunta tare da dafe ƙirjinta dake wani irin bugawa sakamakon tunowa datayi yanda
Yaran Dalla suka caka masa wuƙa abayansa, da ƙarfi ta rumtse idanunta tare da sakin kuka me cin zuciya cikin yanayi mai kama da sambatu tace.
"Ya Allah Kasa ba mutuwa yayi ba, Ya Allah ko sau ɗayane ka ƙara nunamin shi, ya taimakeni alokacin danafi kowa buƙatar taimako, Ya Allah kasa yana cikin halin nutsuwa aduk inda yake ya Allah ka kaddara saduwa ta dashi koda godiya in mishi!!".
Da sauri ta d'ago kanta jin k'anwarta Zahira na cewa.
"Dan Allah Anty Zaleeha, ki bar irin wannan kukan, kici gaba da yimishi addu'a insha Allah addu'arki zata riskeshi."
cikin kuka ta kife kanta bisa cinyar k'anwar tata wacce ita kad'aine tasan da batun. Cikin kukan take cewa.
"Bai sanniba, bai tab'a ganinaba cikin taron maza dake wurin kab babu wanda ya kula da ni bare ya taimaka min dan tsoron Dalla da sukeyi,
sai shi d'aya ya zame min Garkuwata, kuma sun mishi illa gashi ban san ina zan sake ganinshi ba."
shafa kanta Zahira tayi tayi tare da kwantar mata da hankalin.
A haka tacigaba dayin kuka ƙasa-ƙasa tana me fidda shashsheƙa da haka har bacci ɓarawo ya ɗauketa.

***

A gidansu Saifuddeen kuwa.
Ummi ce zaune afalo tayi jigum yayinda tunanin ɗanta kuma farin cikinta Saifuddeen ke kwance acikin ranta, dare da rana bata da wani addu'a sai na nema masa lafiya awajen mai duka, Raliya ce da Adda Rahma da tazo musu tunda safe,
sune suka tafito daga cikin kitchine, hannun Adda Rahma ɗauke da goran ruwa me ɗan sanyi, jingina bayanta tayi da jikin ƙofar kitchine ɗin tare da kafe Ummin nasu da ido, wani irin tausayin kansune ke ƙara ɗarsuwa acikin ranta a kullum, haƙiƙa SAIFUDDEEEN shine komai nasu, Allah Ne gatansu amma Saifuddeen babban jigone agaresu wanda kuma shine gaba ɗaya farin cikinsu.
Raliya kuwa da sauri ta k'araso gefen Ummi ta zauna, ita kuwa Adda Rahma cikin sanyin jiki ta fara d'aga k'afafunda da suka kumbura sabida tsufan cikin jikinta da kyar take tafiya bisa dukkan alamu cikin ya cika wata bakwai ya shiga na takwas a hankali ta ƙaraso cikin falon tare da sanya hannu taɗan taɓa Ummi wanda tayi nisa acikin duniyar tunani.
Ummi kuwa jin sauƙan hannu akan kafaɗanta ne yasanyata ɗagowa da sauri ta kalli wanda ya dafatan, da fuska Raliya tayi arba wacce ta marairaice tuni idanunta sun tara k'walla.
A hankali ta kuma juya ganinta zuwaga Rahma wacce ta fara mgna cike da sanyin murya haɗi da tausayawa tace.
"Dan Allah Ummi kidaina sa kanki adamuwa, Ummi idan kika kasance acikin damuwa akullum natabbata Saifuddeen idan yasani bazai taɓa yafewa kansa ba,
Ummi kinfi kowa sanin Saifuddeen sam bayason damuwarki, dan Allah Ummi kidaina sanya kanki adamuwa Saifuddeen addu'a yake nema daga gareki damu baki d'aya , sannan Ummi kada kimanta addu'an uwa yana da matuƙar tasiri akan ƴaƴa, please ki tausaya mana ki dage da yi mishi addu'a!"

Wani irin dogon Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da ɗan rausayar da kanta gefe tana mai son maida hawayenta amman ina ta gaza tuni sun zubo mata bisa k'unshinta, haƙiƙa shiga damuwa yazame mata dole, tunda ɗanta mafi soyuwa agareta yana cikin wani irin mawuyacin yanayi a hankali tace.
"Ina yimasa addu'a akullum akuma ko yaushe Rahma, sannan nakasa ɓoye damuwata akansa, ke uwace Rahma kinsan irin tsananin so da kuma ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa, wannan ƙaunar fiye da itace ke tsakanina da Saifuddeen, kuma kisani ko ban nuna damuwata afili ba to tana nan kwance acikin zuciyata tana cina!".
ta ƙare maganar murya araunane.

Hawaye ne suka cika idanun Raliya har suna kwaranyowa kan fuskarta yayinda itama Rahma ida nunta suka cicciko da hawaye,
tabbas idan harsu da suke ƙannansa suna tsananin

Please Login or Register in order to submit comment