Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gareshi dashi dama dukkan yan uwa musulmai, ya rabbil izzati ka al'barkaci rayuwar Saifuddeen ka raya minshi ka shirya minshi ka bashi arzik'i mai al'barka wanda musulmai da musulunci zasu al'fahari dashi ya ka bud'a mishi k'ofofin samu ka yalwata arzik'inshi."
kasan cewar tunda ta dafa kanshi ya d'ago kai ya kalleta shiyasa yake gane abinda take cewa,
yana kallonta still yatsarshi na k'asa yana.
Rubuta "Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati".
daga nan suka zauna tayi ta musu nasiha mai ratsa jiki.

Bappa Ali kuwa da matarshi suna side d'insu sam basu san meya faruba.


A daren ranar Saifuddeen yaje ya samu Bappa Ali da fefanshi da biro,
nan yake neman izinin bappan nashi da kuma shawarshi cewa.
A d'auki machine d'in Nuruddeen a bawa wani d'an mak'ocinsu Salisu wanda shima d'an acaba ne to dama na haya yake karba, to kuma an karb'e machine d'in wai mai ita zai saidata ya cikata ya sai sabuwa,
ba musu bappa Ali ya yarda dan yasan ko ba komai balance d'in zai taimakesu,
shi kuwa Saifudden gyara zamanshi yayi kana ya rubutawa bappan nashi cewa.
Kullum da safe in Salisu zai tafi zai bishi su tafi tare,
in yaje zai shiga cikin kasuwan Gombe zai nemi sa'ar da zaiyi."
da fari Bappa Ali yak'i kasan cewar yanaga Saifuddeen d'in kurma ne,
to amman da suka dunguzuma sukaje wurin Ummi sai ta kauda kai yadda Saifuddeen d'in bazai ga bakintaba tace.
"Ba matsala Ali barshi yaje, in mun hanashi zaiga ko dan yanada nakasane, mukuma bamu son hakan to amman ai kasuwa saida jari,
amman tunda yace a barshi yaje,to mu barshin in yaje yaga ba abinda zai ai zai bar zuwa, mu kuma bishi da addu'a Allah ya taimaka mishi."
cikin sanyi bappa Ali yace.
"To shake nan ba matsala Allah ya bashi sa'a."
"Amin Amin." sukace baki d'aya.

Daga part d'in Ummi woje suka fita,
sukako yi sa'an samun Salisu a harabar matsallacin k'ofar gidan nasu.
Nan bappa Ali ya mishi bayanin yadda sukayi, aiko dad'i kamar ya kashe Salisu,
ya kuma yarda da shared'in zaike zuwa da Saifuddeen su kuma dawo tare.
A take bappa Ali ya bashi Key d'in machine d'in.
sannan ya wuce cikin sangayarsu ya fara ratsa tsakiyar d'aliban nasu.
shi kuwa Saifuddeen gida ya koma ya sanarwa Ummi yadda sukayi, ita ko Ummi sai addu'a da samishi al'barka takeyi.
A daren ranar Ummi da Rahma da Raihana da Bappa Ali kusan kwana sukayi sunayi mishi addu'ar samun madafa da sa'a.
Shi kam Saifuddeen baiyi bacci a ranar bare ya rumtsa,
Kwana yayi yana neman yardar Allah da sanya al'barkanshi ya bashi sa'a a cikin k'udurin da yayi.

Washe gari da sanyin safiya Saifuddeen ya shirya bayan ya karya Salisu ya shigo yace su tafi.
gaban Ummi ya tsuguna kanshi ta dafa tare da sa mishi al'barka.
sannan su Rahma suka mishi addu'a baki d'ayansu kana suka fita suka tafi.


Suna shiga Gombe Salisu ya wuce dashi k'aramar kasuwa,
gab da San Hussen mall ya ajiyeshi,
kamar yadda sukayi tun jiya da dare,
bayan ya sauk'ane Salisu ya kalleshi tare da cewa.
"Ana yin sallan magrib kazo ka tsaya a nan, dan zanzo in d'aukeka mu tafi in munyi sa'a bayan isha mun isa Dukku."
cikin nuna alamar ya gane ya gyad'a mishi kai alamar toh.
Salisu na ganin haka yaja machine inshi gaban wata yar budurwa data tsaidashi,
lokaci d'aya suka shirya kud'in da zata bashi kana ta hau yaja ya tafi.

Shi kuwa Saifuddeen juyowa yayi ya zubawa makeken wurin San Hussain d'in idanu a lokacin tun forkon-forkon bud'eshi kana wurin ba'a wani gyarashi sosaiba kamar yanzu ba,
ajiyan zuciya yayi lokacin daya karanta sunan wurin,
sai kuma ya k'auda kai kana yayi tafiya kad'an yazo dai-dai mashigar kasuwan,
inda zai bulla ta babban layin na k'aramar kasuwan.
ida nunshi ya lumshe kana ya bud'esu a hankali hannunshi ya had'e wuri d'aya kana ya fara karanto addu'o'i yayi kusan 16 minutes yana addu'o'in kana ya shafa a fuskarshi kasan cewar da d'an sanyin safiya ne wurin bai cika jama sosaiba kuma kowa sauri yake ya wuce ya isa wurin sana'arshi ya bud'e.
bayan ya shafa addu'ar ne yayi bisimillah tare da d'ago k'afarshi ta dama ya shiga cikin kasuwan.
Sannan ya mik'e gabanshi samb'et, yana tafiya a hankali.
har yazo dai-dai wani babban shagon seye da sayarwa inda mata keta shiga da fita irin masu zuwar sassafen nan shagon kuma cike yake mak'il da atampopi, shadda, laces, material, voyels, su wagbari, gyalulluka. da dai sauransu,
ido ya zubawa yaran shagon kowa na hidiman gabanshi.
a hankali ya kalli saman shagon inda yaga an rubuta.
Alhj Ishaq,
murmushi yayi dan sunan mai shagon ya tuno mishi sunan abokinshi wanda kusan sau biyu kenan yana zuwa Dukku bayan Abba ya rasu.
juyawa yayi d'aya sashin inda yaga wani k'aton shagon mai cike da gyalulluka da dogayen riguna,
kana ya kalli d'aya sashin inda yaga k'aton shagon saida takalma,
sai kuma kusa da inda yake shagon masu saida yadin hijabai ne da masu d'in kasu.
shiru yayi sai ya kuma ci gaba da tafiya ganin ya b'ata kusan 30 minutes a wurin.
A hankali yake taku har ya isa konan shagunan alhaji Yawale,
shiga yayi nanma ya dad'e a tsaye sai kuma yayi baya ganin kusan irin kayayyakin wancan shagon ne daya wuce,
kan babban layin ya dawo kana yaci gaba da tafiya,
Dai-dai shagunan ba mishkila ya tsaya yana kallon yadda mutane ke cike a wurin mazansu da matansu yara da k'anana,
ido ya d'an zubawa yaran shagon ganin kowa da abinda yake aunarwa kuma awu mai kyau irin awunda musulunci ya yarda dashi,
sunan shagon ya kalla sai kuma yayi murmushi ganin sunan shagunan ba mishkila a ranshi yace.
"Eh tabbas kam ba mishkila."

A takaice dai a wanan ranar kam kusan aikin daya wuni yi kenan ya zaga wannan layin ya zaga wancam layin, kana yana bin bakin shaguna yana kallon abubuwan dake ciki da yadda suke mu'amala da costumers insu, yana jin yunwa na k'ak'ularshi amman bai kulaba in lokacin salla yayi ya sayi pure water yayi al'wala yabi jam'in inda duk yaga ana haramar salla.

Kafin magrib ya gaji lik'is.

koda magrib ta kawo kai sai yaga anata rurrufe shaguna hakan yasa ya fita,
bakin inda Salisu ya ajiyeshi,
yana tsaye a wurin ya hango tsallaken titin anata Al'wala haka yasa shima yayi Al'wala kana ya tsallaka yaje akayi sallah dashi.
yana dawowa Salisu na isawa,
babu b'ata lokaci ya hau suka fara tafiya,
sunzo dai-dai wani wurin masu tuwo-tuwo Salisu ya tsaya kana yacewa Saifuddeen.
"Zo muje muci abinci kafin mu tafi naga alamun kamar ba abinda kaci."
juyawa yayi kalli wurin da Salisu ya nuna mishi,
baki ya tab'e kana ya girgiza mishi kai tare da nuna alamar kamar yana kekyamin abincin wurin.
murmushi Salisu yayi dan tabbas yasan Saifuddeen mutunne mai tsananin tsabta da gayu kuma yanada kyakyani,
dan yasan iya tsawon yarintansu bai tab'a ganin ya sayi koda ko kosai ko wani abuba cikin abubuwan da ake kawowa a yar majalisar k'ofar gidansu ba.
So dan haka sai ya hau machine d'in yaja tafiya kad'an suka isa wurin mai shayi, kana yace.
"To mu shiga nan kasha koda shayine."
Still tab'e baki yayi tare da juya kai,
alamun bazai shaba.
ganin haka Sakisu ya kuma jan machine d'in, kai tsaye hanyar tashan Dukku ya nufa dashi,
suna zuwa dai-dai bakin gate d'in Abba bakery yayi parking kana ya sauk'a sannan,
yacewa Saifuddeen.
"Zo muje nan ko zaka iya cin gashin wannan."
a tare suka shiga inda daga mashigar wurin mai naman yake,
ganin wurin fes komai a killacene yasa,
Saifuddeen yarda ya zauna a wurin,
naman d'ari biyar Salisu ya saya musu, kana ya shiga cikin asalin Abba bekery ya sayo musu yogurt k'ananun robabin guda biyu.
nan sukaci duk da Saifuddeen bai wani ci mai yawaba yanka hud'u yaci bai kuma k'arawaba sai yogurt yasha.
Tuni kafin lokacin an kira isha'i haka yasa sukayi sallan
kafin suka nufi hanyar Dukku.


Suna isa gida Ummi tai ta murna ganin ya dawo lfy kuma gashi babu alamun wahala,
shi kuwa Saifuddeen yaki yace mata komai sabida gudun kada ta hanashi zuwa gobe.

Washe garima kamar jiya suka shirya suka tafi bayan Umminshi tayi ta mishi addu'ar samun nasara.

A inda Salisu ya ajiyeshi jiya yauma nan ya ajeshi,
bayan yaja ya tafine shi kuma ya nufi bakin mashigar kasuwar,
yauma kamar jiya saida yayi addu'a kafin ya shiga da k'afan dama.
Kai tsaye layin masu kayan yara ya shiga a hankali yake bin shagunan daki-daki yana kallon yadda suke gudanar da kasuwancin su, mata masu ciki nata shege da fice, a hankali yake taku cikin nitsuwa.
duk wanda ya ganshi sai ya k'ara juyawa ya kalleshi sabida bak'ak'en kayan da ya saka ba k'aramin haskashi sukayiba farinshi ya k'ara fitowa hancin nan har baki, uwa uba sumar kanshi tafi sawa ana kallonshi sabida duk wanda yaga sumar zai tunanin balarabe ne,
fatar k'afafunshi da tafin hannunshi kuwa sunyi jazir, in ya taka k'afar tamkar jini zai tsillo.
Dai dai bakin wani k'aton shago ya tsaya,
yana tsayuwa kenan yaji an.....!




By



*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 4*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Free page

*Wannan page Ι—in kuma nakunw Ζ΄an Hukuncin Allah fans two, ina al'fahari daku,*

*Ga masu son saya turo katin Mtn na 300 ta nan 09097853276 ko ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa*

Yaji An d'an matso kusa dashi har jikin wanda ya matso kusa da shid'in na gogan nashi jikin hakan ya sashi juyowa a hankali ya d'an kalli matashin da bazai zarta sa'anshi ba,
ganin d'an saurayin yana murmushi ya sashi d'an murmusawa,
shi kuwa saurayin cikin fara'a ya mik'a mishi hannu ganin haka shima Saifuddeen ya bashi hannu, fuska cike da fara matashin ya fara mgna cikin bagwariyar larabcin, dan a zatonsa Saifuddeen balarabene,
sosai Saifuddeen ya zuba mishi ido tare da mmki dan ya gane zaton saurayin, haka yasashi k'ara tsurawa bakin matashin ido lokacin daya kuma ci gaba da mgna cikin larabcin shuwa'arab yace.
"Barka da zuwa, shigo daga ciki, me kake so?."
kai kawai Saifuddeen yake jujjuya mishi alamun a a ba abinda zai saya,
shi kuwa saurayin murmishi ya kumayi dan a zatonsa Saifuddeen baya gane irin nashi larabcin ne haka ya sashi juya harshe eh zuwa hausa yece.
"Kai wannan balarabe ba dai kyauba Masha Allah, ko me kakeso ne oho."
wani dake cikin shagon ne yace.
"Jabeer wai me yake sone, jiya mafa na ganshi a bakin shagon Alhaj ishaq."
murmushi wanda aka kira da Jabeer yayi kana yace.
"Ai bai gane larabcina."
cikin zuba mishi ido wancan din yace.
"To yaje gaba wala Allah a samu mai iya mishi irin yarenshi."
daga nan ya juya yaci gaba da sabgogin jera kayayyakin.
Shi kuwa Saifuddeen gane abinda suka cene ya sashi juyawa ya ci gaba da tafiya.
daga nan yayi ta bulayi har azahar koda yaga ana al'wala shima ya zaro goma ya sai pure water yayi al'wala kana ya nufi inda ya hango ana jam'i yana zuwa ana tada ik'a.
Bayan an idar da salla ya d'an jima a zaune yana addu'oi saida yaga an fara nannad'e taburman sai ya mik'e yaci gaba da yawatawa.
kanshi ya kule ya rasa ya zaiyi dan sam cikin kasuwar babu mai kula kowa kowa sabgar gabanshi keyi, kana duk bakin shagon da yaje ya tsaya sai ai ta mishi gwarancin larabci, duk da yana ganewa to amman dame zai basu amsa tunda shi kurmane,
haka yasa ake zaton bai gane larabcin ne tunda yawanci yan koyone ke gwada iyawarsu.
jin ya gaji da yawone yasashi shiga layin masu kayan kitchen nan ya samu inuwa dai dai bakin wani babban shago ya tsaya bencin dake gefe yaja ya zauna,
yana kallon yadda ma'aikatan keta cinikaiya da masu sayyya kasan cewar ramadan ya kusa baifi wata biyu ya rageba shiyasa kasuwan masu kayan kitchen ke gudu,
sabida mata kan sabunta ababen aiki dan samun yalwatuwarsu.
d'aya daga cikin yaran shagon ne ya kalleshi da kyau kana yace.
"Mai gida Allah yasa dai kana jin hausa?."
da sauri ya gyad'a mishi kai alamar. "Eh inaji."
shi kuwa murmushi yayi sannan yace.
"To me kakeso?." da sauri ya jujjuya mishi kai alamar.
"Ba abinda nakeso."
gane abinda yake nufi yasa yaron shagon yace.
"Hutawa kakeyi kenan?." still kai ya gyad'a mishi alamar eh.
ganin kamar baison mgnane yasa yaron ya shareshi yaci gaba da sabgoginshi.
Shiko Saifuddeen gyara zamanshi yayi tare jingina da jikin k'ofar shagon.
mata nata shiga da fita,
sai ya kuma tsargu ganin yadda aketa kallonshi,
har ya mik'e zai tafi sai ya kuma tsayawa ganin wani kekyawan Dottijo fari k'al dashi dake bisa keke bayan keken wani k'aton kwaline dake cike da lododi manya-manya irin k'atti sosai d'innan wanda in kayi sayayya mai yawa ake saka maka kayanka ciki,
sai kuma tsaka-tsakiya sai yan saffa-saffa sai k'anana kana sai masu layi-layin nan sai kuma k'ananu irin mai gida ya kasa d'inna.
hannu ya mik'a ganin wannan kekyawan dottijon yana mik'o mishi kullunan lododin yana ce mishi.
"Tai maka min mana yarona mik'a musu lododin,
ka amso min kud'in na jiya, ba sai na sauk'a bisa motar tawa ba".
ya k'arishe mgnar cikin fara'a,
shima murmushi yayi kana ya amshi ledodin ya juya cikin shagon inda yagga babban ogansu ya zaro kud'i ya irga gudan dubu guda uku kana da d'ari biyar,
yana mik'owa Saifuddeen d'in yana kuma kallon Dottijon tare da cewa.
"Barka da yamma baba Bello, kaga ko kamar kasan lododinmu sun k'are."
cikin sakin fuska dottijon yace.
"Kace nazo a dai-dai kenan?."
shiko mai shagon bayan ya karb'i lododin da Saifuddeen yake mik'o mishi sai ya kuma kalleshi kana ya kalli Dottijon tare da cewa.
"Kai Baba yau kam inaga a bamu na dubu biyar,
sabida kar muzo gobe bakazo da wuriba su gaza mana."
da sauri tsohon yace.
"To ba matsala."
bayan ya amshi kud'in da Saifuddeen yake mik'o mishi ne sai ya kuma bashi wasu banduran lododin,
da sauri ya amsa kana ya bawa mai shagon.
ganin alamun bakin mai shagon yana cewa.
"To Baba bello Allah bada kasuwa sai gobe kuma."
da sauri ya juya, ganin Dottijon na ce mishi.
"Ngd ko d'an saurayi."
kai ya gyad'a mishi tare da zura mushi ido ganin yaja keke nai ya tafi.

A hankali ya juya yaci gaba da tafiya bai jima da fara bulayinba yaga anata shirin Sallan la'asar daga nan shima yayi harama.
Bayan an idarne ya koma layin masu robobi nan yayi ta yawatawa,
hardai aka kira magrib ganin anata rurrufe shaguna ya sashi fitowa, inda yayi sallan magrib jiya anan yauma yayi salla yana dawowa kuma ya samu Salisu ya iso.

Daga nan bakin kasuwan bakin General hospital sukana nufa,
inda daga bakin titin ta d'aya gefen akwai wata mai saida abinci sanin tanada tsabta ne yasa Salisu kawosu nan,
amman Saifuddeen k'in ci yayi,
sai dai Salisu yaci kana ya nuna mishi wani shagon fura da nono,
gane yana sone yasa Salisu shiga ya seyo mishi k'aramar roba saida yasha sukayi sallan isha kafin suka d'auki hanyar dukku.


Bayan sun isa shi Salisu yayi gidansu da machine d'in shi kuwa, Saifuddeen kai tsaye cikin gida ya nufa a tsakar gida ya samesu zaune,
gefen Umminshi ya zauna kasan cewar akwai wuta duk suna ganin juna,
da sauri Rahma ta kawo mishi abinci kana ta kunce bakin zaninta ta kunto 50 sannan ta kalli Hayatuddeen dake tsaye alamar zai fita ganin Saifuddeen dinne ya hanashi fita,
hamtsin d'in ta mik'a mishi tare da cewa.
"Ingo jeka gidansu Ya Adnan ka seyo mishi ruwan sanyi."
da sauri ya amsa tare ficewa.
Ummi kuwa cikin kula tace.
"Ya kasuwa?."
kai ya jinjina mata cikin son boye yanayin da yake wuni a cikin kasuwar.
Rahma kuwa ido ta zuba mishi tare da cewa.
"Saifuddeen gobema zakaje ne?."
da sauri ya gyad'a mata kai dan baya son su karaya.
Raihana kuwa cikin karya wuya tace.
"Hamma Saif me kake sayarwa ne to?."
ido ya zuba mata cikin rashin son yi musu k'arya ya girgiza mata kai alamar babu
da sauri Raliyya tace.
"To me kakeyi?."
sai ya kuma juyo ya kalli Ummi ba tare daya amsawa Raliyya ba,
cikin sanyi take ce mishi.
"To Babana me amfanin zuwan, kalli jiya da yau duk baka wuni damu ka tafi har Gombe kuma kaje ba wani abu kakeyi ba ai gwara ka hak'ura ko?."
murmushin k'arfin hali yayi kana ya fara rubutu a k'asa.
"Ummi wai har kin karaya ne? To ki aro jarumta ki yafa ai komai a hankali yake zuwa,
ai mai nema baya fushi, yoh su masu shagunan da kansu wata rana zasu bud'e ko asi basuyiba kuma haka bazaisa gobe su k'i zuwaba, kedai kiyi ta min addu'a in sha Allah, Allah bazai hanani abin yiba."
sai ya kuma kalli Rahma dasu Raihana yace.
"kuyi tamin addu'a in sha Allah dukkan tsanani tare yake da sauk'i."
cikin samun k'warin guiwa, sukayi mishi addu'a.

Bayan yaga sun saki Randi sunata hirane sai ya mik'e yad'auki bokiti ya debi ruwa a randa kana shiga d'anshi wanda da shida Nuruddeen ne,
farar jallabiyarshi ya d'auka da boxer inshi kana ya fito hannunshi rik'e da kondon wonkanshi ban d'aki ya nufa yaje ya shiga wonka.
Ya jima kafin ya fito daga cikin d'an madaidacin bayan gidan nasu da aka lailayeshi da fulo d'in siminti,
shaddan na can gefe kana wurin wonkan anyishi da mazaunin siminti da kuma inda zaka ajiye sawunka.

A hankali yake tafi bisa dukkan alamu baison kasa ya bud'e mishi sawune,
d'akin nashi ya shiga,
inda yake gyare tsab sai k'amshin turare yakeyi wanda ishaq ne ke saya musu tare,
ko ina a kimtse kodan babu tarkece sosaine,
leda carpet ne a malale a tsakiyar d'akin wanda sai Shek'i yakeyi alamun ya wadatu da tsabta sai katifarshi shimfid'e a gefe wanda yasha gyara sai pillows biyu a
gefen katifar.
can daga k'asa kuma wata yar madaidaciyar durowa ce,
inda gefe d'aya ya jera kayayyakinshi dake wonke a goge, sai d'aya side in kuma littafanshi ne a jere daga sama har k'asa kama dana boko na islamiya dana allonsu wanda wasu tun na kakansu ne, sai wani dogon madubi dake lik'e a jikin ginin daga sama har zuwa k'asa dan zaka iya kallon tsawonka duk ta cikin madubin
sai wani dan abun aje takalma kana sai fankar k'asa da kuma wani d'an k'aramin randar tabo da sai naso yakeyi alamun ruwan ciki da sanyi
sai butarshi a gefe kana can gefen durowar kuma sallayanshi ne ke shimfid'e.
Mai ya shafa sannan ya fito tsakar gidan tuni Hayatuddeen ya dawo har yayi bacci hakama su Faruq.

Gefen Umminshi ya zauna tare da tonk'oshe sawunshi abincin da Rahma ta ajiye mishi ya jawo,
bud'ewa yayi sai ya kuma yi murmushi ganin tuk'ek'k'en tuwan shinkafa da miyar busasshen zogale wanda yasha kifi, gyada, attaruhu, da albasa, wanda aka had'esu da kifi,
kana ga wake dasu kayan d'and'ano
miyar sai k'amshi take, Allah ya sani Saifuddeen nason miyar zogale shiyasa Umminshi ke yawan yin miyar in dai tanada halin yinta da yake miyar tanada cin kud'i.
ledan ruwa d'aya ya d'auka tare da b'ulawa kana ya wonke hannunshi ya fara ci,
ita kuwa Ummi ido ta zuba mishi tare da cewa.
"Yayanka Adnan yazo ya sallameni d'azu wai zai tafi karatu har Zaria."
kanshi ya d'an jinjina alamar Ayyah,
sai ya kuma yi mata alamun Allah ya kaishi lfy.
Amin Amin tace,
bayan ya d'an ci abincin ne ya wonke hannunshi Raihana ta kwashe kwanukan kana ta dawo sukaci gaba da hira.
Suna nan a zaune Bappa Ali da Aunty Nina ma suka shigo yi mishi barka da dawowa nan sukayi ta hira.

Washe gari da sassafe Rahma ta hura wuta tayi d'umame kamar yadda suka saba,
da sauri ta d'auko pillet ganin Saifuddeen ya fito cikin shirin tafiya,
yau k'ananun kaya yasa wanda sukayi masifar yi mishi kyau blue Jeans ne a jikinshi sai bak'ar riga mai farin rubutu a jiki,
kanshi ba hula hakan ba k'aramin haskashi yayiba,
yana shiga d'akin Umminsu tana binshi a baya,
bisa kujerarta irin zauna kaci doya nan ne ya zauna,
ita kuwa Rahma mik'o mishi fillet d'in tayi kana ta jawo kolban man shanun da suke sawa in sunyi d'umame,
bud'ewa tayi tare da tsiyaya mishi kana ta mik'e ta koma kitchen robar dakekken yajin borkono ta d'auko sannan ta dawo barbad'a mishi tayi,
sannan ta d'auki kofi ta nufi d'akinshi ruwa ta d'ebo mishi a wannan randar tashi,
sannan ta kawo mishi tare da cewa.
"Kaci kafin ku tafi."
kai ya gyad'a mata kana ya kalli Umminshi dake shirya Hayatuddeen yanata zumbura baki, murmushi yayi tare da jawo hannun Hayatuddeen yana mishi tambaya irin tasu ta kurame ya tambayeshi me ya sashi fushin.
Bakin ya kuma turawa kana ya rab'a jikin Saifyddeen d'in tare da cewa.
"Hamma Saif ba Adda Rahma bace tayi d'umame kua tasan ni bana cin d'umame hakama Faruq da Adda Raliyya."
murmushi yayi kana ya jawoshi ya ajiyeshi gefenshi,
a hankali yasa cokalin da Rahma ta mik'i mishi ya gutsuri gayan kana ya dandalo miyar da taketa k'amshin man shanu,
bakin Hayatuddeen ya kai,
tura baki yayi tare kwabe fuska kana yace.
"Na k'os. "
bai k'arisa mgnar tashiba yayi shiru,
jin ya sa mishi loman a bakinshi, lumshe ido yayi tare da fara sarrafa abincin,
saida ya had'iye kana ya bud'e idanunshi tare da cewa.
"Dad'i wlh miyar tayi dad'i Faruq zo kaci."
Ummi kam da Raihana dake shirya Faruq tuni dariya sukeyi, shima Saifuddeen dariya yakeyi har saida dimples nashi suka lotse sosai kana fararen hak'oranshi suka baiyana manyan idanunshi ya lumshe tare daci gaba da basu abincin a baki,
aifa sukaci sukayi nak, sannan suka tafi makaranta,
ita kuwa Raihana da sauri ta fita tace.
"Adda Rahma ki samishi wani abincin su Faruq sun cinye wannan,
harda santinsu."
dariya sukayi kana Rahma ta samishi wani yana cikin cine Salisu ya shigo nan sukaci tare kafin suka fita suka tafi.


Yauma kamar kullum Saifuddeen wuni yayi yana yawo da bulayi a kasuwa,
sai da magrib tayi ya fito, kana yayi salla kafin Salisu yazo ya d'aukeshi yau ma fura da nono yasha da zasu tafi.

Haka dai Saifuddeen yayi ta fama yawo da wahala a cikin kasuwar Gombe har tsawon kwana bakwai,
to a ranan ne kuma Salisu ya basu balance ensu kamar yadda sukayi duk sati zaike basu dubu biyar.

Koda ya karbi kud'in Bappa Ali ya kaiwa su,
shi kuwa Bappa Ali k'in amsarsu yayi yace ya kaiwa Ummi kud'in zasu samu abinda zasuke sarrafa cefenen abincin.
da yake har yanzu sunada sauran abincin da baban Arabi ya kawo musu.

Shi kuwa Saifuddeen sai ya zare dubu biyu ya bawa bappan nashi, amman sam yak'i karb'a acewarsa ai da yanada hali shine ya kamata ya basu,
to dai ganin Saifuddeen ya b'ata rai ya sashi amsar 1k yasanya al'barka.
Shiko yaje ya bawa Ummi dubu uku sannan ya d'auki dubu d'aya.
Ummi kam sai sanya mishi al'barka takeyi.

Washe gari kamar kullum suka shirya suka tafi cikin. Gombe a inda ya saba sauk'eshi yau ma nan ya sauk'eshin, bayan Salisun ya tafi shi kuma Saifuddeen sai ya d'anyi tattaki zuwa bakin mashigar kasuwar, addu'a yayi kamar kullum kana ya shiga da k'afar dama,
yauma bakin shagunan yayi tabi har kusa k'arfe shad'aya lokacin rana ta tsala zafi ya fara,
sai ya nufi layin masu robobi,
yana zuwa shagon wani bayerbe sai ya tsaya,
bokatin kand'e tsirara ya saya wanda wasu ke cemai ganta sarai,
bayan sun gama ciniki cikin mgnar kurame ya bashi dubu d'ayannan,
kana bayerben ya bashi canjinshi,
daga nan ya nufi wani layin tafiya kad'an yayi sai gashi a wani babban shago da yake cike da d'ima-d'ima firiji masu tsawo da masu fad'i.

Yana zuwa d'aya daga cikin yaran

Please Login or Register in order to submit comment