Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita inda motarta take,
su kuwa zugan 'yan kalaren nan kansu suka nufo a guje ganin hakane yasa,
yajata da k'arfi sannan ya bud'emata motartata wurin zaman direba ya ajiyeta kana ya meda marfin ya rufe sannan ya sunkuyo kanta tare da kad'a mata yatsunshi biyu kana yayi mata alama dataja motar ta gudu, gane abinda yake nufine yasa ta jujjuya kai tare da zubda hawaye cikin haki tace.
"Mutafi zasu kasheka fa 'yan kalarene fa yaranshi ne."
ganin zata b'ata lokaci har suzo su sameta suyi mata illane yasashi buga marfin motar da k'arfi tare dayi mata gurnani irin nasu na kurame wanda in bawai ka saniba sai kayi zaton tsawa ya buga mata hakance ta kasance ga Zaleeha dan jin sautinshi tayi a sama haka yasa ta figi motarta a guje, tana jan motar suna isowa inda yake, yayinda shi kuwa yake kallonta so yake yaga fitanta a wurin, su kuwa suna isa inda yake ba tare da ya juyoba don shi dai kurmane bazaiji sautin takun k'afafunsu ba,
suna isa d'aya daga cikinsu ya narka mishi k'aton katakon dake hannunshi a tsakiyar gadon bayanshi kafin, yayi wani yunk'urinma
d'aya daga cikinsune ya dab'a mishi wuk'a a tsakiyar bayanshi kana ya zaro wuk'ar wanda tuni sun farka mishi rigarshi
wani irin razanennen ihu Zaleeha tasaka tare da zubawa bayanshi ido sabida tana ganinshi ras dan hasken motoci dake haska wurin da hasken fitulun dake zagaye da farfajiyar wurin
cikin tsananin tsoro da firgici taja motarta ta bar sitadiyon d'in,
tana fita kai tsaye gombe division ta nufa.

Shi kuwa Saifuddin tuni sun mishi illa sun daddatsa mishi kataki a tsakiyan bayanshi.
yayinda duk da haka bai bar kare kanshiba sai dai ance sarkin yawa yafi sarkin k'arfi gashi sun zomishi ta bayanshi kuma sunzo tare da makamai yayinda shi kuwa babu ko allura a jikinshi,
haka yasa sukayi mishi illah mafi muni a jikin d'an adam, haka suka rink'a hankad'ashi kan k'arafun wurin suna buga bayanshi a kai
saida sukaga yabar motsi kana suka dauki uban gidansu da Saifuddeen ya daddaga mishi jelershi sukaja motocinsu suka tafi,
yayinda tuni mazauna wurin kuwa sun watse don kowa yasan rashin mutuncin Dalla.

Shiru cikin sitadiyon d'in ba ko tsuntsu sai Saifuddin dake yashe tamkar mamaci,.

Ita kuwa Zaleeha bayan ta sanarwa hukuma, ganin ita macece kuma sananniya kana yar babban Malamin da akeji dashi a fad'in jihar dama k'asar bak'i d'aya yasa aka had'ata da police officer d'aya ya rakata gidansu dake New G.R.A...



A haka police officers na station d'in gombe division suka iso,
yayinda aka had'a da sosojin Anty kalare,
kana
suna isowa ganin halin da yake ciki ne yasa suka d'aukeshi,
kai tsaye general hospital Gombe suka nufa dashi, kai tsaye aka wuce dashi o,p,d. suna isa ma aikatan wannan sashin suka turo irin yan wannan gadaje na d'aukar marasa lfy,
tare dasa hannun hukuma aka karb'eshi bayan an duddubashi ganin aikin babbane ya kuma ji rauni sosai ne sai aka basu takarda wacce zata sadasu da babban likitan dake Medical Center.

Kan hanyarsu ta zuwa Medical Center d'inne d'aya daga cikin police d'in yayi saurin zaro woyar dake al'jihun wondon Saifuddin
ganin tanata kawo haske alamun shigowar sak'o,
text ne aka turo kamar haka.
```"Babana Saifuddin Kana ina? ka dawo kayi bud'a baki mana, ka sani duk muna jiranka kasan hankali na bazai kontaba in baka ci abinci ba."```
shiru police d'in yayi yana jujjuya kalaman, a ranshi yake cewa.
"Bawan Allah azumi ma yakeyi kenan."
sai kuma ga wani sak'on da yaga suna no daya turo text d'in Hayatuddin inda yake cewa.
```"Slm Hamma Saifuddeen ka dawo gida muyi dinner yunwa nakeji kuma kasan bazamu iya cin abinci ba in baka nan please ka dawo da wurin shalelen Ummi kaga ta k'i kula kowa sai cekiyarka takeyi kamar kaine autanta."```
haka nan yaji tausayin ahlin wannan bawan Allah ya kamashi,
dai-dai lokacin suka shiga harabar Medical Center Gombe,
kasan cewar da jami'an tsarone lokaci d'aya aka karb'eshi, aka fara bashi taimakon gaggawa
d'aya daga cikin doctors da sukayi kanshi ne domin bashi taimakon gaggawa don ceto rayuqarshi yayi saurin matsoshi ido ya zazzaro woje Cikin tsananin kad'uwa da tarin tsoro da tausayawa yace.
"Saifuddeen!."
sai kuma yayi maza ya fara had'a na'urar dai-daita nufashi wato oksijin kana yayiwa sauran doctors guda biyun alama dasu fara aikinsu,
mazuk'in numfashin suka manna mishi,
kana suka kunna wani wuta mai tsananin haske sannan suka matso da dukkan abin buk'atan aikin suka fara, duddubashi ciki da woje sam babu wani yanka ko karta a sauran sashin jikinshi sai na bayan nashi kawai, sai kuma alamun duka da katako dake tsakiyar k'ugunshi da bayanshi.
Kana sai suka koma duba kwokwon kanshi inda suka samu buguwar guda uku, amman iya karsu woje basu shiga ciki yadda zasu shafi hankalinshi da tunaninshi ba.

Sosai suka duk'ufa dan ganin numfashi sa ya dai-dai ta,
amman abin yaci tura,
sosai suke aikinsu cikin iyawa da gwarewa da sanin makaman aikinsu,
shiru kakeji ba motsi sai body language da sukeyi a tsakanin su.
Tsawon awa biyu sukayi a kanshi kafin suka samu nasarar dai-dai tuwar numfashi sa,
canza mishi gado sukayi kana Doctor Adnan ya turo gadon da kanshi ya nufi I, C U inda nos guda biyu suke biye dasu,
bayan ya dai-dai ta mishi komai sai ya fito kai tsaye office nashi ya nufa.
Yana shiga ya zame bisa kujerar dake mazauninshi, idanunshi ya rumtse da azabar k'arfi yana jin wasu hawaye masu azabar zafi suna tsatsafo mishi cikin jijiyoyin idanunshi,
sai ya kuma mik'ewa da sauri kanshi ya kifa da jikin bongon office enshin yana mai zubda hawayen.
cikin rauni da tausayawa murya na rawa yake cewa.
"Astagfurillah Allah na tuna ya Allah nasan ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah nasan kafi ahlinshi sonshi, ya Allah ka sauk'ak'awa Ummi wannan jarrabawa dake shirin sauk'a gareta ya rabbil izzati ka duba larurar Saifuddeen ka yaye mishi ka bashi lfy."
sai ya kuma koma ya zauna kan kujerar kana ya kifa kanshi bisa babbn table dake gabanshi,
dai-dai lokacin Doctor Arabi ya shigo tare da police officer biyu,
da sauri ya matso wurin abokin aikin nashi ganin yana kuka cur-cur tamkar yaro,
cikin kad'uwa yace.
"Doctor Adnan meke faruwa?."
kai ya jijjiga jikin son tsaida hawayenshi yace.
"Dr Arabi wannan da aka kawofa k'anin abokina Nuruddeen ne."
cikin firgici Arabi yace.
"Innalillahi Saifuddeen! to kuma me yayi musu meya tsare musu, meyasa zasu cutar da bawan Allah shida baya mgna meyasa suke son sa ahlinshi a rana Allah sarki Ummi da Rahma wayyo Hayatuddeen wayyo Raliyya da Raihana."
cikin kad'uwa police d'in yace.
"Alhamdulillahi abu yazo da sauk'i tunda kun sanshi."
cikin rauni Arabi yace.
"officer kun kama wad'an da sukayi mishi dukan ne su waye ne ina suke me ya musu?."
cikin kauda kai officer d'in yace.
"Ina bamu kamasu ba asalima bamu san su waye bane,
domin kafin mujema shi kad'ai muka samu a wurin babu ko mutun d'aya,
itama wacce ta sanar damu cewa tayi wucewa tazoyi ta gefen sitadiyon d'in ne so sai taji ihu shiyasa ta kawo rahoto,
to ganin a firgice take yasa muka had'ata da d'aya daga cikinmu ya rakata gida don ta gaza yin draving dan tace itama sun biyota ne ganin ta d'an tsaya shiyasa har suka samu daman fasa mata glass d'in gaban mota, so kunga bamu da hanyar samun wata shaida, abu mafi sauk'i a bashi taimakon gaggawa kana ga woyarshi ku nemi yan uwanahi ku sanar dasu."
cikin rauni Dr Adnan ya rink'a jujjuya kai tare da cewa.
"Innalillahiwainna'ilaihirajiun wayyo ni Adnan ta yaya zan tinkari ahlin Saifuddeen da wannan mummunan lbri da wanne baki zancewa Ummi Saifuddeen d'inta na asibiti cikin d'ayan biyu mutuwa ko rayuwa taya zan sanarwa Rahma halinda k'aninta ke ciki?."
ganin haka Dr Arabi yayi saurin cewa.
"Please officer ga adireshin gidansu kuje ku sanar dasu kana ku d'aukosu ku kawosu nan d'in."
da wannan shawarar police d'in suka nufi federal lowcost
babu wuya ya gane kwatancen da Dr Adnan yayi mishi,
a k'ofar wani babban gida sukayi hon minti uku tsakani mai gadin ya lek'o, ganin motar jami'an tsarone ya sashi bud'e k'aramar k'ofar ya fito cikin hausarsa ta buzaye yace.
"Sannunku lfy kuwa?."
cikin saisaita fuska mai jan motar yace.
"Wurin masu gidan mukazo bud'e mana gate."
cikin sanyin jiki da d'an tsoro ya bud'e gate d'in kana ya rab'a gefe suka shigo,
bayan sunyi parking ne biyu daga ciki suka fito,
hannu suka bashi bayan sunyi musabaha ne police d'in yace.
"Kayi mana sallama da Hayatuddeen."
to yace jiki a mace har ya juya zai nufi cikin asalin gidan sai ya kuma juyowa tare da cewa.
"Dan Allah ku gaya min lfy dai ko?."
ganin alamun rashin gamsuwa a gareshi ya sasu ce mishi,
"Saifuddeen ne tsautsayi ya ritsa dashi so ana neman danginshi."
cikin tsananin firgici da tsoro buzun nan ya kama kai tare da cewa.
"Innalillahi! Saifuddeen meya sameshi ina yake?."
cikin mmkin waye Saifuddeen menene nagartarshi shi wayene da Doctors ma suke kuka kan cutarshi kana kalli yadda ma'aikatan gidansu ma suka firgita jin yana cikin matsala, jiki a mace yace.
"Kaga yi maza ka mana sallama da k'aninshi."
cikin rawan jiki ya kusa kai cikin gidan nan mai azabar kyau.
A cikin gidan kuwa Hayatuddeen ne da Ummi suke sauk'owa daga benen ,
cikin shek'iyanci Hayatuddeen ya zame ya zauna kan last step kana ya manna kanshi da k'afafun Ummi dake tsaye a gefenshi cikin shogwab'a ya kalli Raliyya kana yace.
"Yaseen yau a bedroom d'in Hamma Saifuddeen zan kwana, nine auta amman anfiji dashi, komai nashi na dabanne Ummi da kantafa take gyara mishi side nashi, ni kuma nawa ko oho."
cikin wasa sukayi mishi dariya, Ummi ce ta shafa kanshi tare da cewa.
"Yoh kaida kake cewa ka fini sonshi ni uwar data haifeshi ma."
ido ya lumshe tare da cewa. "In banso Hamma Saifunaba to waye zanso a duniyarnan?, amman dai duk da haka nima ina son a gyara min d'akina yayi ta shek'i da zuba k'amshi koda rabin na Hamma na ne."
dariya Raliya tayi tare da cewa..
"Hayatuddeen waya isa ya medaka irin Hamma Saifuddeen ko Allah ma bai halicceku iri d'aya ba Hamma Saifuddeee mutun ne mai tsabta, kaikuma irin kune ake cewa kai dai kaga gaye a titi karkaga ma koncinsa, kaida inda ka tub'e wondonka nan kake tsallakeshi."
dariya sukayi baki d'aya dan shima yasan halinshi kenan.
Raihana kuwa cikin dariya tace.
"Karka damu autan Ummi shalelen Hamma Saifuddeen daga yau zan rink'a share maka side d'inka."
Dariya yayi cikin jin dadi kana yayiwa Raliya gwalo,
cikin raha tace.
"Au nanda yaushe zata koma ka dawo kana min k'aramar murya."
dariya sukayi baki d'ayansu banda Ummi da zuciyarta ke yawan tsinkewa yana fad'uwa ras-ras.

Shi kuwa buzun nan
wata k'ofa ya bud'e tare da kusa kai cikin wannan corridor d'in, wucewa yayi ba tare daya tsayaba cikin wannan had'ed'd'en parlour mai azabar kyau ya kuma baiyana wanda yakeda tsananin girma da fad'i kana ga steps d'in da zai sadaka da sama, sallama yayi tare da duk'awa gefen Ummi kekkyawar mace wacce zata iya kai 49 years to 50 kekyawace wacce yawan shekarunta bai samu nasarar b'oye kyantaba, Ummi kenan sai wannan d'an matashi autan nata da banzai wuce 17 years da yan watanni ba, Hayatuddeen,
Raliyya matashiya yar duma-duma wacce zata iya kai 23 years.
Sai kuma Raihana da zata iya kai 26 year da d'anta Affan wanda bazai wuce shekara biyu ba.

Cikin maida hankali kan buzun Ummi ta juyo cikin wani yanayi da takeji tun da yammacin yau d'in tace.
"Baba ila ya akayi ne?."
cikin sanyin jiki yace.
"Wasune ke sallama da Hayatuddeen."
mik'ewa Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Muje wata k'il Zakariya ne."
kai ya jujjuya mishi cikin sanyi yace.
"A a bashi bane folisawa ne, sunce Saituddeeen ne ya samu d'an hatsari yana asibiti shine akeson yan uwanshi suje."
wata iriyar zabura Ummi tayi kana ta rumtse idonta da azaban k'arfi sabida wani irin duhu da jirin da ya rufe mata ido a take,
wani irin rawa jikinta ya fara har cikin hanjinta takeji suna hautsinewa zuciyarta kuwa tamkar zata faso k'irjinta ta fito fili sabida tsananin razana da kad'uwa lokaci d'aya wata zazzafar zufa ta yanko mata
hakama Raliyya da Raihana shi kuwa Hayatuddeen gaba d'aya idanunshi ya zazzaro woje.
kusan gaba d'aya a tare suka fito Ummi kam duk jikinta rawa yakeyi tamkar mazari.

Hayatuddin ne yayi saurin isa garesu kana cikin tsananin kad'uwa da firgici yace.
"Ina Hamma Saifuddee ina yake meya sameshi ku kaimu wurinshi waya bugeshi?."
Raihana kuwa kuka takeyi mai cike da fargaba,
ita kuwa Raliyya direbansu taketa rabkawa kira cikin firgici da d'aga murya take cewa.
"Sule taho mu tafi wurin Hamma Saifuddee."
a hamzarce Sule direban ya taso wanda yayi ta bai jima da dawowa ba dan shi yana Ζ™ofan Baba bello lokacin da abin ya faru kuma yayi ta kiran Saifudddeen alamun yana nemanshi baiga amsaba, to sai yayo zaton ko yayi wani wurin ne shiyasa ya dawo shi Ι—aya,
Motarnda ke harabar gidan ya bud'e ya shiga tare da jawota zuwa gabansu,
dai-dai lokacin kuma police officer d'in yake cewa Hayatuddeen .
"Shiga mota muje yana asibitin Medical Center ne."
firgici da kad'uwan Ummi ya tsananta jin k'irjinta takeyi yana buguwa da azaban k'arfi wata fargaba da razani ya rufeta,
jiki na rawa ta shiga motar da Sule ya kowa gabanta sam ta kasa furta ko k'ala domin harshenta ya mata nauyi jiki na tsuma ta shiga motar, wonda tuni Raliyya da Raihana sun shiga
shi kuwa Hayatuddeen cikin kaifin basira da zurfin tunani irin nasu na maza yace.
"Ummi kuje, bari in d'auko kud'i zan taho a U.D. d'ina."
jin haka yasa Sule jan motar yabi bayan motar police d'in kana suka fita suka nufi Medical Center Gombe.

Shi kuwa Hayatuddeen , a guje ya koma cikin gida sam bai lura da Affan ba d'an Raihana wacce itama Raihana ta mance da d'an nata sabida firgincin halin da d'an uwanta ke ciki,
to bare kuma Hayatuddeen da Ummi,
cikin sassarfa ya haura matakalan benen har yana take steps bibbiyu,
direct d'akin Hamman nashi ya shiga bayan wasu yan mituna sai gashi ya fito,
yana gyara zaman kud'i a cikin al'jihunshi still bai kula da Affan ba ya wuce yana fitowa harabar gidan ya figi mashin nashi cikin azama ya nufi asibitin.

Su Ummi kuwa bisa jagoran jami'an tsaron suka isa k'ofar d'akin da Saifuddeen yake,
sai dai ba damar shiga kanshi.
suna isowa bakin k'ofar Ummi ta rumtse idonta da k'arfi cikin tsananin hargitsin rayuwa tace.
"B.......


Hmmmmmmm. Wasa farin girgi karfa ku manta na gaya muku labarin sashi-sashine, littafin yana tafe da ababe masu tarin yawa,
Salon Saifuddeenfa salone da zai sanyaku shauΖ™i bage farfaΙ—o da tsohuwar soyayya hmmmmmm dafa sauran rina a kaba, ku dai ku biyoni a baya.

By
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*NAKASA BA KASAWA BACE*


*PAGE 14*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



~Har lau dai kuna samun garaΙ“sar free page ne kafin a tsaya Ζ™oΖ™arta ka/ki turo kuΙ—in karantar littafin har Ζ™arshe~

_Turo katin mtn na Ι—ari uku kacal ta wannan number 09097853276 ,ko kuma ka/ki turo Ι—ari ukun ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki_

Cikin tsananin firgici da kad'uwa jiki na tsuma murya cike da taraddadi Ummi tace.
"Bayida rai ko Raihana? Raliya baya numfashi ko!? yamutu ko shikenan Saifuddeen shima yatafi yabarmu inna'lillahi wa'inna'ilaihirraji'un,!sai ta kuma fashe da kuku mai matukar ban tausayi.
jiki a mace tasulale kasa ta ta zauna kan kujerar dake gefen k'ofar cikin muryar kuka mai cike da taradaddadi takefad'in.
"Ya Allah karufamin asiri kakara rufamin, kad'aga kafad'ar wanna bawan naka, Saifuddeen idan katafi kabarmu yazamuyi da rayuwar mu ina rayuwa zatata kaimu Saifuddeen kadawo garemu."
sai ta kuma kalli yadda Raliya ta kife kai jikin k'ofar tana wani irin narkekken kuka,
cikin matsanancin tashin hankali Ummi tamike tsaye kamar anzabureta.
Da sauri su Raihana suka rungumeta suma suka fashe dakuka mai sanyin sauti nan gurin yakacame da koke-koke duk wanda yagansu saisun bashi tausayi.

Dr Adnan dake zaune acikin offece inshi kuwa shima sai sharar kwalla yake time to time sai kuma yamike da sauri jin hayaniya a waje, dasauri yafito.
kana Dr Arabi yamara masa baya,
ganinsu Ummi ne yasa Dr Adnan saurin saida hawayenshi, yanufi inda suke.
A hankali yasa hannu ya Yajanye su Raihana ajikin Ummi,
dasauri Ummi tariko hannunsa tare da zuba mishi ido murya a raunace tace.
Adnan Saifuddeen yarasuko!? dan Allah ka kaini naganshi."
wasu zafafan hawayene yaji nakokarin zubo masa dasauri yamaidasu dan gudun kada takuma shiga wani tashin halin,dukda shima hankalinsa amatukar tashe yake sai dai ya fahimci bata cikin haiyacinta matar da take tsananin jin kunyarshi ko sunanshi bata fiye kira iya gaisuwa ke hadasu sabida fulakun fulanin gaske tunda ya zama surkinta suke kunyar juna, amman gashi yau ciwon Saifuddeen yasa ta mance komai har tana rik'e hannunshi cikin sama musu k'arfin guiwa yace.
"Ummi ki kwantar da hankalin ki.
Saifuddeen yana raye, babu wani abunda yasame shi natashin hankali, illa d'an buguwa kadan kuma duk anyi settling d'in komai yanzu haka yasamu bacci.
Ummi addu'arki kadai Saifuddeen yake buk'ata, kidaina kukanna dan kinsan bazaiji dad'iba idan yatashi ya taddaki ahakan."
da sauri tasa tafin hannunta bisa fuskarta hawayenta tashiga sharewa cikin hanzari, dan tasan abinda yafada gaskiya ne.
Dan a duniya idan dakwai abinda Saifuddeen yafi tsana arayuwarsa, baiwuce ganin bacin ran mahaifiyarsa ba in yaga tana zubda hawaye hankalinshi tashi yake ya birkice mata, tuno hakan yasa ta tsagaita kukan,
dai-dai lokacin kuma
Dr Arabi ya k'araso inda suke nan suka hadu sukayita k'arfafa wa Ummi guiwa, harsaida sukaga tad'an sami nutsuwa kafin, suka juya suka nufi office d'in Dr Adnan kasan cewar shi babban doctor daya ke kula da masu irin matsalar da Saifuddeen yake ciko.

Shi kuwa Hayatuddeen gudu yake akan U.D. d'inshi tamkar zai bar garin batareda bata lokaciba ya'isa Medical Center,
dasauri yafaka mashin d'insa acikin harabar asibitin,
kana yanufi cikin asibitin inda Raliya ta kwatanta mishi.

A tsaye yataddasu Ummi ganinsu tsaye cirko-cirko yasa zuciyarshi bugawa da azaban k'anrfi ido ya tsura musu tare da sassarfa cikin kid'ima ya'isa inda suke,
jikinsa nab'ari ya kalli Umminsu cikin tsoro yace.
"Ummi ina Hamma Saifuddeen?."
kai ta sunkuyar cikin son samawa yaran nata nitsuwa tace.
"Ba matsala fa ka kontar da hankalin ka ya yana bacci ne."
sai ta kuma sa hannu ta share hawayenta kana ta nuna mishi inda su Dr Adnan sukayi tare da cewa.
"Kaje ka Adnan na son ganinka."
ba tare da yace komai ba yabi inda ta nuna mishi kasan cewar yasa ofishin Adnan d'in so kai tsaye ya shiga,
in da ya samu Dr Arabi yana nunawa dr Adnan wasu takardu da sukafi kama da hoton k'ashin bayan mutun da jijiyoyin.
Da sauri ya k'arisa gabansu jiki na rawa yasanya hannunsa acikin aljuhu yaciro kud'ad'en daya d'ebu,ya mik'awa Dr Adnan tare da cewa.
"Ya Adnan gashi dan Allah ayiwa Hamma Saifuddeen duk abinda yadace in bazasu isaba in k'aro wasu, mu dai lafiyarshi muke buk'ata in Allah yasa yanada sauran rayuwa."
cikin kulawa Dr Adnan yace. "Ay an mishi komai duk abinda yadace duk wani taimakon da ya kamata abashi anbashi yanzu dama numfashinsa mukeso ya dai-dai ta,
kuma Alhamdulillahi munsami nasarar ceto numfashinsa yanzu jira muke zuwa gobe muga abinda Allah zaiyi,"
Cikin sanyi Hayatudden yace.
"Ya Adnan ina tsoro, kar mu rasa Hamma Saifuddeen."
kafad'arshi Adnan ya d'an bubbuga kana yace.
"In sha Allah bazamu rasashi ba,
sannan kacewa Ummi kada a gayawa Rahma abinda ya faru a bari in na koma zan san yadda zanyi in gaya mata."
Shiru Hayatuddeen yayi fuskarsa d'auke=da matsanancin damuwa, saikuma yace.
"Ya Adnan yanzu zamu'iya ganin sa?".
girgiza kai Dr Adnan yayi,
tareda fadin.
"No yanzu yana buk'atar hutu so bazai yuwu kugansa yauba."
komawa dabaya Hayatudden yayi yajinginu da jikin garu
tareda dafe kansa da yayimasa nauyi, a hankali ya rumtse idonunsa yanajin zuciyarsa nayi masa kuna wasu zafafan hawaye na zubo mishi,
tausayin Hamman nasa dasu kansu yacike ilahirin zuciyarsa afili yafurta.
"Ya Allah kabashi lfy ka d'aga mana kafad'unshi ka rufa mana asiri."

Tare suka fito wurinsu Ummi bayan sun isane.
Dr Adnan yadubi agogon dake daure a hannunsa, kana yadubi Ummi cikin girmamawa yace.
Ummi kuje gida dan dare ya fara nisa yanzu inyaso saimu zauna da Hayatuddeen kafin zuwa goben muga abinda Allah zaiyi,
dasauri Ummi tace.
"A a sudai sutafi ni subarni anand'in nakwana."
Raihana ce tace.
"Ummi muma bazamu iya tafiya ba tareda munga farkawarsa ba."
kai ya jinjina dan yasan dama hakan bamai yuwuwa bane, dan yasan k'auna da shak'uwar da ke tsakanin ahalin,
dan haka saiya kyalesu yace su shiga office inshi, kana shi ya koma office d'in Dr Arabi.
ya rasa meyasa tun d'azu Rahma keta kiranshi gaba d'aya sai ya rasa me zaice mata lokacin daya amsa kiran nata dan a zatonshi ko taji abinda ya farune,
ita kuwa Rahma cikin sanyin jikin da takeji tunda yamma tace.
"Ya Adnan kana lafiya kuwa inata kiranka baka amsawa?."
numfashi ya d'an fidda kana yace lfya lau Rahma meya hanaki bacci har yanzu?."
gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"Ji nake zuciyata nata tsinkewa gabana nata fad'uwa shine nace bari in kiraka inji lfyarka."
cikin son sama mata nitsuwa yace.
"Kiyi baccinki ni lafiyata lau, in kuma wani abu kikeso ki gaya min gsky Baby in dawo in miki kona 30 minutes ne in dawo bakin aikina."
cikin jin kunya tace.
"A a ni bance wlh."
da sauri yace.
"Kin ce mana tunda du du du fa bayan sallan isha na baro gida kuma wuni mukayi tare amman yanzu har kwadayinki ya tashi ko?."
da sauri tace.
"A a wlh to kayi zamanka, kaga saida safe."
kafinma yayi mgna ta katse kiran.


Ance bacci b'arawo ne mesace idon kowa,
to yaudai baisami damar sace idanun wanna ahalin ba.

Acan d'aya sashin kuwa cikin New G. R. A.

Hargida police d'in da aka had'ashi da Zaliha yakaita, abakin makeken gate d'in gidansu tatsaya,
kana yafita amotar tayimasa godiya yatari abin hawa yatafi,
dasauri tafita takoma gefen driver tunkan takarasa zama tadanna horn dan har'alokacin amatukar tsorace take,
da gudu maigadi yataho dan jin yadda aketa danna hon ba sassauci da sauri ya wangale mata get d'in,
da sauri ta kutsa hancin motarta cikin farfajiyar gidan nasu da gudu,
asakar farfajiyar gidan tayi parking tafito,
maigadi nakokarin rufe get
wata lafiyayyiyar mota mai azabar kyau da tsananin shek'i ta danno hancinta cikin gidan,
Zaliha kuwa har tajuya zata shige cikin gidan,
ganin shigowar motar yasata tsayuwa, yayinda gaba d'aya zuciyarta da tunaninta ke can wurin kelyawan mutumin daya taimaketan
har aka faka motar tana nazari asannu akabude marfin motar yazuro kafafunsa yafito,da murmushin sa yanufi inda Zaliha take,
itako kwabe fuska tayi tareda langwab'ar dakai gefe,
yakaraso inda take waro idanu yayi ganin galashin motarta afashe cikin mamaki
yace.
"Hatsari ki kayine Zaliha?." cikin muryar shagwaba ta tura baki tare da yarfa hannu tace.
Ya Ahmed ba y'an kalare bane na taddasu a hanyata ta dawowa sunata fad'a shine suka fasamin gilashin mota, badon a mota nikeba nima da sun fasa min kai."
takarasa maganar kamar zatayi kuka dan tausayin Saifuddeen da ta baro suna shirin kashewa,
dasauri Ya Ahmed d'in nata yace.
"Ina dai ke basu ji miki rauniba ko?."
kai tagyad'a masa tare da cewa.
"Amman dai ai sunyiwa motata illa ai."
cikin kula da shak'uwa yace. "To Alhamdulillahi da Allah yasa akan motace ba kan 'yar kekyawar k'anwata aka fasaba,
gobe ida Allah yakaimu zamuji kizabi motar da kikeso.
Amman fa mai sauk'in kud'i Hajia na sanki baki san zafin neman kud'iba sai son ayi ta kashesu ba sassauci."
bayanshi tabi tare da cewa.
"To Ya Ahmed duk yadda kace

Please Login or Register in order to submit comment