Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinci sai dai Abu me ruwa,Mimi taga duk ya canja kullum sai taga ya zauna Yana ta tunani abinci baya ci,duk ya rame sosai,Tayi tunanin rashin Basma ne ta tafi Makkah,Bmbata San me akeyi ba,Ya samu kwangila me tsoka amma ya kasa zuwa ayi aikin kudi zai samu miliyoyi na kirki,daga lokacin idan yayi ya Zama hamshakin gaske amma tunanin Hamida yasa Office dinma ya daina zuwa,idan yaje gidan Mimi ta daina Fitowa yana ganinta Sam dakinta take kullewa idan har yaga Hamida to Doctor dinta ne yazo ta fita kofar gida tayi zance tun Yana masifa har ya dawo ya gaza,ya zaci abinda doctor ya Mata na gori zata daina kulashi amma sai yaga ya lallabata sun koma sun jone.

Mimi ce ta tasa shi a gaba Nabeel Wai meke damunka mene ne ka fada min? Baka da lafiya kake boye min ko wata cutar ce ta kamaka,abinci ka daina ci nasan dai matarka Bata nan dole a nan zaka ci abinci me ya faru? Ya rasa inda zai sa Kansa in banda Ammar ba Wanda yasan zancen yasan Yana fadawa Mimi za a samu matsala,Affa Kuma yace sai in Nabeela ta yarda sannan zai aura Masa ita, ko me zaiyi Matukar Hamida bata sonsa bazai same ta ba,shi Kam rayuwa babu Hamida gwara ya mutu ma da yaga bakin ciki,Shuru yayiwa Mimi, Hamida tana jinsu tana kitchen kin Fitowa tayi,Mimi tace dan ubanka baza ka fada min meke damunka ba gashi Nan sai tunani kake Yi,Nabeel ya wayance tare da sakin murmushin yake yace ba komai fa Mimi a wajen aiki ne wata kwangila nayi asara,to ba Allah ne ke badawa ba Mene na damuwa haka,idan baka da jari ga gida na Nan na Kano nasan zai Kai Million hamsim yanzu tunda a g.r.a yake Kuma babban gidane sai ka siyar,wancan ma dana siya kwana nan duk ka siyar ka hada na bar maka,Ko a dawo da Fadila ta dinga tayaka Hira? Murmushin karfin hali yayi yace no ba sai an siyar ba,to kayi Hakuri ka fawwalawa Allah,Nabeel ya kalli Mimi yace hmm Kawai,rabon ma da yaga Hamida har ya manta sai dai ya hange ta a wajen Doctor,wucewa tayi da plate din Indomie tana waya da Saurayinta tace gashi na dafa Indomie zanci ka daina damuwa,Nabeel kamar ya kurma ihu haka yaji ta shige bedroom ta kulle,Mimi tana ta Murna tace Hamida doctor har ya siya Mata form din School of nursing yace kafin ayi biki zata Fara zuwa makaranta in anyi aurensu taci gaba a can kaga mun huta da Kaya,Affa Kuma ya amince ta nuna Masa komai da yardar sa akayi komai sun kusa kawo kudi ma,Bari naje na dakko ma form din ka gani Mimi ta tashi tana rawar kafa ta haura sama,Nabeel bai San Yana hawaye ba sai da yaji laima sannan ya shafa fuskarsa kafin Mimi ta dawo ya Shiga kitchen yayi sauri ya wanke fuskarsa ya dakko ruwan sanyi Yana Sha kamar bai damu ba.

A hannun Mimi ya gani ko karbar form din bai iya Yi ba,hankalinsa ya tashi da yaji za a kawo kudi,yace Mimi Kuma iyayenta sun sani? Tace yaro har yaje kauyen ya gaishe su da danginsa da komai Kai abinfa ba na Wasa ba ne wallahi yaje can itama Hamidan ana kawo kudi zata tafi can, Nabeel mikewa yayi yace bari na karbi number dinsa ma dinga gaisawa Mimi tace ya kamata,ya nufi dakin Hamida, Yana knocking gabanta ya Fadi ta bude kofa tace mene ne? Yace magana za muyi,Fadi a Nan,Hamida Ni kike fadawa haka? Kallon tara Saura quarter ta Masa tace da kasan yanda na tsan....kasa karasawa tayi kallmar ta Mata nauyi, daurewa tayi tace Malam ka fita Ni ba Yar Iska ba ce irinka,mashayin giya mazinaci ka cuceni ta fashe da kuka,a zahiri Hamida fakewa take da kukan an cuceceta amma har ranta kukan son Nabeel takeyi ta kasa cire shi a ranta tayi tayi ta kasa kullum kaunarsa karuwa take a ranta Kuma kullum son ganinsa take tana son kasancewa da shi amma dole ta hakura ta tursasa zuciyarta.

Durkusawa yayi har kasa a gabanta tana kuka,hawaye kamar ya zubowa Nabeel yace please Hamida kome kike so a duniya Zan Miki,matarka fa in ta dawo me zaka ce? Mufa musulmai ne Allah ya halatta min Mata Hudu,ya narkewa Hamida tace ka rike matarka Ni wallahi bazan.....bakinsa taji cikin nata Ido ta lumshe ta sa karfi ta ture shi tare da shigewa toilet ta kulle kofa barshi a Nan durkushe ya kifa Kansa a saman bed dinta,a toilet din ta durkeshi tana rusa uban kuka kasa kasa yanda bazai ji ba Kuma tayi ma kanta alkawari baza ta auri Nabeel ba duk son da take Masa, sai da Nabeel ya gaji da Zama sannan ya mike ya bar dakin ko Mimi baiwa sallama ba ya wuce gida direct.

Shigarsa gida ke da wuya ya fada saman bed dinsa ya kifa cikinsa da kyar ya iya tashi yayi Sallar Isha ya kwanta bacci ya gagari idonsa,In banda Hamida ba abinda yake tunani,da komai nata shi yake tunawa,Mimi a cikin dare ta Kira Ammar akan yaje yaji abinda ke damun abokinsa,Ammar yasan komai amma Kawai yace to,Bai je wajen Nabeel ba sai da safe ya iske Nabeel Yana kwance zazzabi ya rufe shi ko motsi bai iyawa tsoro ne ya kamashi,Bargo ya lulluba Masa.
Da sauri ya Kira doctor aka Masa gwaje gwaje hawan jini ya kamashi da karfi,an bashi magunguna da allurai an Masa Karin ruwa amma Nabeel babu sauki a abin nasa,Ammar duk iya kokarinsa yayi kasa hakura yayi yace mu tafi asibiti Kawai Nabeel yace bazai je ba,Lele so kake ka kashe kanka Kar ka manta Hamida yanzu Bata sonka gwara ka kyaleta ka fuskanci gaskiya ka rabu da ita sai kace Yar gwal,Nabeel baya iya Maganar kirki,Ammar yace to gaskiya Zan Kira Mimi,Nabeel ya girgiza Masa kai hawaye Kawai ya fara sakkowa Nabeel,tausayi ya bawa Ammar yace Kai Hamida kake so? Ya daga Masa Kai Wai ae,yace to tsaya naje na lallabota Allah yasa tazo ta kula da Kai,Ammar gidan Mimi yaje da sauri ya iske kamar kullum duk suna wayen Aiki sai Hamida,hankali tashe yace Hamida ga Nabeel can zai mutu sai abinda Hali yayi yace kije gidansa zai bar Miki wasiyya,Gaban Hamida ya fadi ta dora Hannu aka tace na shiga uku me ya sameshi yace ciwon zuciya,nayi nayi muje asibiti yaki yanzu ma kamar kakin jini ya fara Mimi ma ta tafi can kiyi sauri,Hamida tsalle tayi ta saki kuka ta fara tumami tana birgima Ammar ya saki baki Yana kallon ikon Allah yace ba kuka zakiyi ba kije ki bashi agaji idan Yana da sauran rayuwa to idan ya mutu duk munyi Rashi,Hamida ta daga hannaye sama tace bazai mutu ba...bazai mutu ba...in Allah ya yarda bazai mutu....bakin ka sari motar tantan ...bakinka ya sari tsohuwar tifa,tana kuka tace muje ka kaini,Ammar yace ni asibiti zanje karbo magani,mayafi ta figa ta Dora saman silk doguwar rigarta dark blue,ta fice da gudu takalman ma a Hannu ta eba,Tana Fitowa taga Doctor Ahmad dama sunyi zaizo ya fito da sauri ya ganta a hargitse.

Yace Honey lafiya? Da bala'i tace karka isheni dan Allah zanyi rashi,Ya sake cewa Hamida...karka dameni Malam ka tafi sai na kiraka a waya,Ahmad yaji haushi ya figi motarsa a ransa yace ki gama wulakancin wallahi Kika shigo sai na Rama Zaki Gane kurenki baki San waye Ni ba dama kwadayi ne ya kawo ni in aura na gurjeki.

Hamida Kuwa taxi ta shiga ta Masa kwatance kudi ta Mika Masa dubu Daya,yace Hajiya canjin tace na bar maka ta fyalla da gudu cikin gidan, dama tasan har room dinsa Kawai Shiga tayi lokacin ma duk ya jigata bai ma San me yake ba,Hamida tana hawaye kasa kasa ta ganshi cikin bargo,gefen fuskarsa dake waje ta taba taji mugun zafi Yana ta rawar sanyi,kumatunsa ta tallafe da Hannu biyu tace Yaya kyakyawa,tana fadan haka sai da yasan itace yaji wani sanyi a ransa duk da jikin da yake ji,yace sanyi nake ji kimin wani abin,Hamida tace ban San me Zan maka ba,Yana numfarfashi yace dumin jikinki dan Allah tace tab ba ruwana bamu da aure ai nayi hankali nida Namiji haihata haihata,wallahi... ba.. abinda Zan Miki kinji na rantse,Ya sake narkewa Kamar ransa zai fita harda tari, Hamida tsoro ya kamata,taji yace Hajiya Bilki me kosai tana bina bashin naira dari idan Allah yayi min rasuwa kije ki Bata,Ido ta zaro ta saki kuka,ya sake cewa sannan....Jamilu me dinki shima Yana bina dari hudu da hamsim ki bashi cikin abinda Allah ya hore min,...ya sake yin tari...muryarsa na rawa kamar zai sheka lahira yace Lawan kwalli me aski na shima Yana bina dari uku ,akwai wasu maza biyu ban San inda Zan same su ba amma idan na rasu a dauka cikin abinda Allah ya hore min ayi musu sadaka ta naira dari dari bazai wuce haka ba,Kimin Addua Allah ya min Rahma kinji..

Kafin ya rufe baki Hamida ta shide barkosa jikinta na rawa tana lallashinsa tana baza ka mutu ba Inshaallah baza ka mutu ka barni ba, Nabeel ya sake lumewa a jikin Hamida ya maida Kansa saman kirjinta yayi wani lamo Yana sake shigewa jikinta,gashinsa ta shafa da yake birgeta tace abinci Zan maka ai da sauri yace ban warke ba ya sake narkewa,yace Ammar ma Yana bina dubu uku nasan zai yafe min amma a bashi dai,,Hamida a ranta tace wannan shine final next week Ahmad zai kawo kudin aure dole ma ka hakura da ni,Nabeel a ransa murna yake Hamida ashe tana dan sonsa Allah yasa ta aure shi haka yake fata, ya wani makalkaleta



Sharhi pls



AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮

8

Official

By
AsmaBaffa


Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM



Page naku ne Yan albarka

KHADIJA DEEY
GIMBIYW DIYAR KATIBI
HAUWA J
MAMAN AHMAD
OUM NU'AIMA
M DEWU
MRS NAZIR
XARA
UMMY MANGA
HABEEBAH HIBBAT
MMN SADEEQ
MUMMY NEEMRAH





Tunawa tayi da abinda ya mata a farko tuni ta fisge jikinta ta dirgo kasa tace bari na ma girki ka lallaba ka tashi kayi wanka,Ido ya zura mata kawai amma hakan ma yaji sauki sosai ya samu nutsuwa,da farko yace bazai iya tashi ba sai gashi ya mike ya shige toilet wanka yayi ya sake yin brush ya fito sanye da jallabiya blue mayen turare duk cuta yake amma komai nasa kamshi ko me ya taba sai yayi kamshinsa me sa nutsuwa.

Kitchen ya bi Hamida ya tsaya tare da zura mata Ido kamar tsohon maye,juyowa tayi ta ganshi a tsaye a kofar kitchen ya harde hannaye a gaban kirjinsa bata ce komai ba kunya ma yake bata ta dan dafa Masa dankali da miyar kwai kamar ba shine ranga ranga ba,ba ruwanta tana gama Masa girkin ta ajiye a dining sannan ta hau gyara Masa gidan sai binta yake da kallo duk inda ta matsa idonsa Yana kanta,ko kallonsa Hamida bata Yi aikinta take Yi har bedroom dinsa sai data gyara ko Ina fes sannan ta gyara jikinta ta yafa mayafinta sosai ta fito.

A Palo ta iske shi kwance a saman kujera duk ya Zama abin tausayi,nesa da shi ta durkusa a nutse tace abincin fa? Shi Kam mamaki take bashi kamar aljana har ta canja Masa gaba daya lokaci guda,idonsa ya lumshe tare da cije pink lips dinsa na kasa, hannunsa daya ya daura saman goshinsa ya dafe sabo da yanda Kansa ke Sara Masa,satar kallonsa takeyi Jin bai magana ba,ta mike jikinta a sanyaye ta zubo Masa abincin a plate ta ajiye a gabansa,komawa tayi kitchen ta dakko Masa fresh milk da ruwa ta tsiyaya Masa milk din a glass cup,tace abincin fa kaci dan Allah,Hannu ya daga mata da kyar yace dakko min magunguna sauri kaina,da sauri ta mike ta haura sama sai gata ta dawo da magungunan ta bude Masa ledar ya balla Wanda zai iya Sha ya Sha,ta tsura Masa Ido a tsorace.

Wayarta ta zaro ta mike ta Shige kitchen,da kallo ya bita ji yake kamar zuciyarsa ta fashe,tunani yake ta wacce hanyar zai shawo Kan Hamida yasan ma Doctor Ahmad ne ya Kirata kishinsa Ahmad ma Yana da kudi Kuma gashi matashi duk da Nabeel yasan ya fishi komai amma yasan shima bashi da makusa.

Hamida Kuwa number Ammar ta Kira wacce ta karba yace idan da matsala ta neme shi,Yana dagawa tace Hamida ce,yace ya ake ciki? kazo ka kwana da shi da dare gaskiya baiji sauki ba ya kamata ma a kaishi asibiti idan baza ka kaishi ba ni sai na kaishi da kaina,maralafiya haka an barshi a gida ta furta Kamar zata Yi kuka,Ammar yana sani yace aiki ya min yawa kuje asibitin zanzo anjima amma karki Kira su Mimi ya Mata kwatancen asibitin da zata kaishi yace amma karki biya kwandala za a biya,Hamida tace to ta kashe wayar, fitowa tayi Yana Palo tace na tafi Allah Kara sauki,Yana kiranta ko juyowa bata Yi ba ta wuce abinta tana Fitowa taga Doctor Ahmad Yana kallonta a tsaye jikin mota a ransa yace taje ya gama eban banza wannan Yarinyar sai na kure mata karshen malejin jarabarta ashe tana lallabawa,Hamida ta kalle shi ya kalleta.

Ya kalleta shekeke yace me ya kaiki gidan Namiji bayan matarsa bata Nan? ran Hamida ya baci tace ka daina bin kwakwafi na kana zargina Kai din wani na kirki ne ko Kai baka wa Allah laifi zaka fada min magana,tana gama fadan haka tayi maza ta karasa mainroad idonta cike da hawaye tana tafiya tana magana ita kadai tace na cuci kaina dana tonawa kaina asiri yanzu wa zai yarda Dani?a zuciyarta tace Allah shi Yana gani tace hakane Allah shi yasan namijin hankaka..

Me taxi ta Nemo tunda Bata iya tuka mota ba sannan Kuma taga Nabeel baison a San baida lafiya,a gate me taxi ya tsaya ta shiga abin Mamaki Ahmad Yana cikin mota yayi parking daga baya yanda Hamida baza ta ganshi ba.

Hamida tana shiga ta iske Nabeel idonsa yayi jajir Kamar Wanda yayi kuka,Hankalin Hamida idan yayi dubu to ya tashi ta kalle shi zata Yi kuka Fuska a kwabe ta riko hannunsa tace tashi mu tafi asibiti tunda baka so kowa ya sani,Kai ya girgiza mata shi bazai je ba,Hannunsa ta Kama ta dinga jijjiga shi tana rokonsa ka tashi muje dan Allah,ganin yaki tashi tasa karfinta wai zata daga shi kamar me Jan akuya,ganin baida niyya gashi ta kasa dagashi tace haba Leleluwa,Dan Leleluwan Mimi... Lelen gayu... Lelen kamshi...ko ba Lelen kamshi bane? Kallonta yayi ta bashi dariya ya girgiza Kai Wai ba Lelen kamshi bane shi,Tace to Lelen mene? Ko Lelen Kashi ne? Fuska ya daure tace ahhh shagwalliya to Lelen mene? da shagwaba kamar yaro yace naki, da sauri tace Lelen Pipi Hamida,kallonta yayi Jin sabon suna wai Pipi,tace Malam Shehu ne yace sunan gayu ne Nick name Pipi,Murmushi yayi tace taso to Hannu ya Mika Mata ta tallafa Masa ya mike hannunsa ta riko ta rufe ko Ina na gidan Suka fito,Ahmad Yana kallo takaici ya kamashi yace sai na dau mataki duk ya gama kwashe Mata albarkatu Ni Kuma sai dai na auri kankaren kanzo Yaja kwafa ya fisgi motarsa ya bar wajen.

Hamida da sauri ta bude Masa mota ya Shiga baya itama ta shiga ta zauna gefensa,ta yiwa me taxi kwatacen asibitin suna zuwa Ammar yazo shima shi ya tsaya aka yiwa Nabeel duk abinda ya kamata sannan akace ba sai an bashi gado ba.

A gidan Mimi Ammar ya sauke Hamida yaja shi da Nabeel Suka tafi tana shiga ciki ta iske Mimi da Affa suna dining ta gaida su,Affa yace Ina Kika je ne? tace wani shago naje Zan Nemo wani littafi da Malam yace na siyo ban samo ba amma na bawa Uncle Inuwa ya siyo min,Okay that's good cewar Affa, Mimi Murmushi Kawai tayi tace ai Hamida ta fara hankali Naga sai gogewa take kullum gashi ta Kara haske sosai tayi kyau da kiba,Hamida harda rufe Fuska taji kunya ta juya ta Shige bedroom dinta.
Alwala tayi lokacin magriba tayi ta gabatar da Sallah a nutse Shehu duk Yana koya Mata yanzu ta iya abubuwa dai dai gwargwado.

Bayan kwana Uku Nabeel yaji sauki sosai har ma yazo gaida Mimi amma bai samu ganin Hamida ba ta kulle ma kofarta da key suna ta waya da Doctor Ahmad akan maganar turo kudin aure sabo da Ahmad ya danne duk abinda ya gani sai Hamida ta shiga hannunsa sannan zata gane shayi ruwa ne,Lele har ya tafi bai ga Hamida ba yasan shine bata son gani haka ya shiga motarsa ya koma gida.

Da dare bayan ya dawo daga masallaci Basma ce a harabar masallacin dakin ka'aba ta gaji yau satinta kusan uku kenan a Makkah idan tace zata dawo Lele yace ta Kara kwanaki ta Masa addua,Wayar Nabeel ta Kira Suka gaisa tace Honey gobe Zan dawo fa,Nabeel Yana kwance ya mike zaune yace no akwai adduoin da nake so ki min a dakin ka'abah dawafi bakwai sau bakwai kullum har kwana bakwai kice abinda Nabeel mijina ke so a ransa Allah ka bashi Allah ka cikawa Nabeel mijina burinsa haka Zaki dinga fada a dawafi kinji my wife.
Basma tace wallahi bazan zauna ba na gaji haka kawai ka turoni Makkah Umrah ba watan Ramadan ba ba komai ba,Addua kana ta sani Ina maka kala kala kullum kace abinda kake so a ranka Allah ya baka Wai me kake so ne haka,Nabeel a ransa yace Hamida a fili yace calm down Ni da akwai Hali ma dan Allah ki zauna ki min aikin hajji,Wallahi bazan zauna ba kwana Nan fa aka Yi karamar Sallah ni ba takari ba ba komai ba Haka Kawai daga Nan Kawai na zauna nayi takarci mana to wallahi gobe i yanzu Ina gida kazo airport ka daukeni 5pm na gaji,Nabeel yace ke kullum idan zakiyi magana bakya taba cewa Inshaallah sai dai Kawai ki fada direct,Yo me zai hanani dawowa gobe bazan zauna ba wallahi,Wayarsa ya datse sabo da zai iya fusata.

Nabeel ya fara murmurewa tunaninsa Hamida zata so shi tunda yaga ta damu Sanda baida lafiya,5pm ya manta ma Basma zata dawo sai Wayarta yaji tace Ina airport kazo ne? Yace au yau dama fa Zaki dawo na tuna,Basma tace bazan jiraka ba ni gani Nan na shigo airport car...kafin ta karasa ya datse Kiran sabo da ta fiye fadar magana yanda taga Dama sabo da ta taso cikin kudi,15mnt sai ga Basma ta dawo Yana kallon ball ta shigo kallonta Kawai yayi ya dauke Kai sabo da yaga tana ganin damarsa.
Itama ganin haka ko kulashi bata Yi ba ta haura sama da kayanta.

Key din mota ya dauka ya fice zuwa gidan su Ammar estate din su Ammar ba kowa haka yayi parking a bakin gate ya fito yasha kyau Yana taku dai dai kawai Yan daba ya gani sun zagayeshi da makamai,abin ya bashi mamaki dole mutum ya furgita,Nan take Suka ce koma cikin mota ba musu ya koma ba tare da ya nuna ya razana ba,mutum uku ne suka Shiga motar biyu a baya Daya a gaba sauran Yan daban ma suka shiga motarsu daya suka tafi da gudun tsiya,Daya daga ciki yace tuka muje,Nabeel ya fara driving suna zuwa inda ba gidaje ba ababen Hawa suka ce wait Nan take ya tsaya da mota yayi parking Yana ta karanta adduoi a ransa abinda suke nufinsa da shi Kar ya same shi,yana parking mazan biyu suka shake Nabeel ta baya ta yanda ba zai iya motsi ba,Wanda yake gaban motar Kawai Hajiya babbar Nabeel ya damka ya kafta Mata Sara da wuka Nan take jini ya balle ta gaban Nabeel,ya saki wata azababbiyar kara,su Kuwa da gudu Suka fice daga motar suka shiga tasu Suka bar layin a tsiyace.

Nabeel kukan ma ya gagareshi sabo da tsananin bala'in da yake ciki, Affa Yana can tare da Papan Hamida sun karbi kudin auren Hamida,Ahmad ya Kai kudin aure Saura a sa rana ya rage,har ya shiga social media shafukansa ko Ina ya rubuta got Engaged ana ta Masa fatan Alkhairi,Hamida haka kawai ta fara nadama da tace a kawo kudi amma ya ta iya.

Affa Yana zaune ya raka Papa ya hau mota kenan zai wa motarsa key yaga Kiran Nabeel,dagawa yayi kukan Nabeel yaji Kawai da Nishi Kamar ana zare Masa rai, Affa yace Lele lafiya Kai Lele,da kyar Nabeel yace Affa kazo Zan mutu,Affa mutuwa zanyi wallahi wasu Yan daba ne Suka yanke min Naja'atuta,Affa yace wacce Naja'atun? ta gidan su Muhseen? Yana Nishi jikinsa na rawa yace Affa..Affa...Ya Allah...Affa... Naja'atu fa Affa Naja ta,Affa duk ya rude yace kana Ina yanzu? Da kyar ya Masa kwatance nan Affa ya Kira Ammar da Mimi duk kafin kace me sunje wajen,Affa motar ya leka yaga gaban Nabeel jini yayi faca faca da farar rigarsa,Ido Affa ya rufe ya juya baya sai hawaye,Ammar Kuwa kuka wiwi take,Mimi zubewa tayi a kasa Kawai,Affa Yan Uwansa ya Kira Alhaji Ubaid da Alhaji Abbas,kafin kace me sojoji sun cika wajen su Alhaji Ubaid sun iso ba bata lokaci suka tafi katafaren hospital kafin su Isa asibitin Nabeel tuni ya sume tuni,Suna shiga hospital din taimakon gaggawa aka bashi likitoci sun dade suna aikinsu kafin babban likitan ya fito,Affa suka Yi Kansa yace Alhmdllh rabi Suka yanka Allah ya tsare basu raba jijijiyar jiki ba,yanzu zuwa gobe ku shirya komai Zan hada ku da likita a paris a kaishi can sun kware a wannan fannin idan ba Haka ba za a iya samun matsala ko ya warke yazo ya kasa haihuwa ko ya kasa biyawa matarsa bukata kuyi sauri kuje can amma gaskiya wallahi ko sun Masa Aiki sai ya dade Yana jinya zai kwashe watanni ko shekara ma dick dinsa bai dawo normal ba amma Inshaallah zai warke abin da sauki.

Sai lokacin su Affa Suka danji dama dama,Sanata Alhaji Abbas ya Kira yaronsa yace a Fara musu Shirin tafiya paris,Hamida Bata San me ake ba tana kwance taga Affa ya shigo da sauri cikin tashin hankali ya fito da wasu takardu da international passport hankalinsa a tashe Hamida hijab dinta ta gyara ta fito har kasa ta durkusa tace Affa lafiya Kuwa?

Affa yace Ina lafiya Hamida Nabeel wasu Yan daba sun yanke Masa Wai Naja'atunsa Affa shima bai San yanda zai fadawa Hamida ba kunyar fadar sunan abin yake a gaban yarinya,da Mamaki sai yaga Hamida ta gane Yana Fada ta dafe kirji tace Naja'atu? Affa yace ita,Hamida sai ta kwalla uban Kara sai kace wacce junnu Suka shigeta ta dinga wayyo Allah na Shiga Uku na lalace ta Fadi a kasa tayi birgima tayi burburwa Affa ba ta ita yake ba tuni ya bazama ya koma asibiti,Hamida ihu take da kururuwa kamar ance mutuwa yayi ta fito da gudu ta nufi wajen su Sale su dama sunji labari duk sunyi tsumu tsumu,Jama'a ku ceceni Ni yau Ina Zan sa kaina....ta wuce su Sale ta fice kofar gida,wani Almajiri yace Hajiya a taimaka min da sadakar yaji da Mai zanci kanzo mm,Hamida tana kuka ta cakumi Almajiri ta kifa Masa mari ya juya da sauri zai cika rigarsa da Iska ta tallafe Masa keya sai da ya kusa faduwa,ko me ta tuna oho gida ta shiga da gudu duk Yan aiki sunyi cirko cirko ta dakko waya ta Kira Ammar tana shesheka ta tambaya Kuna Ina? Ammar yace ba sai kinzo ba da Sauki,Ni ka fada min ta sake tambaya cikin kuka me ratsa zuciya,Kawai asibitin ya fada mata,ta fice ko wacce mota tarewa takeyi ba sai taxi ko napep ba,Wani me napep ya tsaya ta fada ciki Yana

Please Login or Register in order to submit comment