Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma Suka zazzauna,masu kida suna ta cin abinci Suma,Angwaye basu Fara ci ba sai da sukayi hotuna da Amarya da kawaye sannan dangi ma kowa sai aka zauna ana cin abinci banda Nabeel da akace nasa daban,Yana zaune Suka ga ana ta girke Masa girki iri iri nama kala kala abokai Suka ce bai Isa ba Suka cinye nasu Suka dawo Kan nasa shi bai ci ma da yawa ba,Yana ganin Hamida ma bata da nutsuwa sabo da mutane ana ta kiranta ana hotuna.

Bayan duk mutane sun tafi saura kawaye da Angwaye da Dangin ango Mata da maza,Dj ya saki Sauti Su Nabeel mamaki ya Kama su ganin matan aure ba kunya kowacce ta botso duwawu baya suna wani karkada harda masu yin goho suna rawar kwankwaso dattijai ,Yan Mata Kuwa inda kasan karuwai,Sanda Karima ta shiga Nabeel Nan ya tsinke da lamarin wakokin fitsara ake sa musu,Hamida Amarya tana gefe tana ta dariya tace Ni wallahi haushi ma suke bani a dinga barin takashi a gaban maza duwawu na tashi,Hamida ta jawo Karima tace ke Aunty idan mijinki ya gani sai ya tsine Miki wlh Duwawu haka ki ta zazzage shi a gaban mutane maza,Karima ta fisge ta koma abinta,idan sukayi wani abin Nabeel har rufe Ido yake sabo da kunya,Sakina ita Duwawun ma Kamar tsinke Hamida tace ke Sakina sunan naki duwai bai Kai darajar duwawu ba ki fito kayan takaici.

Duk Yan birni kasa rawar sukayi sunga an fisu fitsara ma Nabeel yace ashe Hamida ba banza ba amma duk da Haka na Kauye suna fita na birni Suka shiga

Kawayen Karima Suka fada ciki Suma na birni ne amma Ina rashin albarkar tayi yawa samari Kuwa abin nema ya samu sai barin kudi suke,Hamida tana daga gefe cikin Yan kallo kamar ba itace Amaryar ba,Tace wuhuhu Sannu Takashi sannu,Nabeel yace tazo ta karbi kudin liki ta makale kafada tace nidai bazan je ba Allah.

Ihsan ganin Amarya taki ta musu liki tace a sa Mata tsohuwar wakar Shakira Shakira Dangin ango da Suka San da zance suna ta dariya Hamida ta gudu wajen Nabeel,Suka zo zasu jata ta karfi Nabeel yace baza tayi ba kuje ku kuyi,kudin liki Nabeel ya bata yace je ki musu liki shima ya mike ance Amarya da Ango ake bukata Suka shiga fili su kadai hannunsa cikin na Hamida sun Sha ruwan kudi ba Wanda ya kada ko kafa Kawai tsayawa sukayi aka dinga zuba musu ruwan kudi sannan Suka yiwa mutane liki sannan gaba Daya Angwaye Suka tafi sai Dangin ango mata iyaye da Yan Mata zasu taho da Amarya sabo da yawan Yan Kai Amarya kawai a tafi a motoci, basuyi booking flight ba Papa da Ummi suka ce su dai a Dangin Amarya ya zabi iya mutum biyar su zasu je Karima,Sakina kawa,sai dattijai guda uku,Dangin ango ma Yan Mata tuni sunyi gaba sai masu tafiya da Amarya su Uku kwata kwata mota biyu aka dauka sauran motocin empty Suka koma da ace sun San baza aje da yawa ba da flight zasu bi.

Amarya kayan da abubuwan gyaran jikinta duk an zuba a mota komai tayi wanka tasa lace hadadde maroon mayafinta adon jikin lace blue takalmi da jaka blue,Hamida harda kuka,aka kaita gaban Ummi da Papa zasu Mata fada,Papa bai iya fada ba shi Sam tana gabansa tana kuka tana shesheka fuskarta a cikin mayafi tace

Papa ayi Mana Addua Ina fargaba ban San wacce rayuwa zanyi ba,Papa yace ta alheri zakiyi Hamida Inshaallah Allah bamu sa'a sai Watarana,Allah ya bada sa'a ita Kawai papa yake maimaitawa Hamida,Hamida tace papa Kamar na dakko talla taci gaba da kuka, akayi dariya aka tafi da ita wajen Yaya Sulaiman shine yayi fadan yace rayuwar baya ta wuce sabuwa Zaki shiga me Dadi Inshaallah Hamida,ki nutsu kiyi hankali,ki kula da mijinki ki Masa biyayya duk abinda yace kiyi kinji,ki daure ki samu ilimin addini dana boko Banda shirme nasan kin samu nutsuwa ki Kara akan nada,ki koyi rike sirri banda bankada Hamida tace Inshaallah Sulenmu,Dariya yayi Wai Dan ta tsokaneshi.

Wajen Ummi aka kaita Nan ma Ummi ba laifi tayi kokari ta gaya Mata gaskiya ta Mata Nasiha karshe tace aure sai anyi hakuri banda Raina Iyayen Miji da Yan Uwa a rage surutu marar ma'ana tace to,har zasu tafi tace tayi mantuwa wajen papa,ta koma ciki tace papa motar Sadakina na barmaka ita,kudin Kuma a bawa Yaya Sulaiman dubu dari uju yaja jari ya fara sana'a,a..papa ne ya dakatar da ita yace tunda kin bashi har dari uku ai ya isa,mota Kuma kice mijinki ya turo a daukar Miki,Hamida tace wlh tunda Ni ya bawa na bar maka ta dinga rokon Papa ya karba sai da ta hada da harda kuka da kyar ya karba mota ta million biyu da rabi,sauran dubu dari biyu Kuma a hannunta Papa ya bata ta zuba a jakar Karima sannan Suka tafi a motoci.

Sun dau Hanya sun bar garin Adamawa sosai sun shiga daji ana tafiya Daya motar su Karima dama sunwa motar Amarya nisa Bama a hango su,sunzo wani gurin rami Kawai Suka ga manyan bishiya an datse Hanya da Yan daba dauke da makamai iri iri,Hamida kuka ta saki tayi maza ta zaro Wayarta jiki na bari ta Kira Nabeel Yana dauka yaji tana kuka tace Yan fashi sun tare mu,Innalillahi ya Shiga ja ta Wayar yaji ana durawa su Hamida ashar wani kato ya leko tare da karewa motar kallo Mata sai kuka jiki Yana Bari,wani cable Suka zaro Wanda ake shake mutane da shi,Nabeel Yana Jin kukansu sabo da Wayar ta fada kasan kafafunsu.

Yana ta kwala Kiran Hamida,ai Kuwa suna zuwa Suka bude mota tare da fisgo Amarya waje ita kadai Suka dauka ku tafi ko mu hada da ku,Hamida ihu da tsalle.

Take tana Kiran sunan Nabeel....driver jiki na bari yaja mota Suka daga musu hanya Suka wuce suna kuka suna kallon Hamida aka hankada keyarta cikin dajin.






AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮

21-25


Official
By
AsmaBaffa



Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM




PAGE NAKU NE

Hjr murja kankara
Mk Hussein
Ummu Zahyed
Mrs Aminullah
Khadijatul Kubrah
Faiza
Ummi H
Ummul Ihsan








Motar da aka sace Amarya sune suke ta buga waya dangin Amarya dana ango ana sanar da abinda ya faru duk sun firgice suna ta kuka,Driver me tuka motar sai Innalillahi yake furtawa Yana cewa da Mata kuyi Hakuri ku dowa Allah mun kubuta babu mu Allah ya taimakeni iyalaina Allah ya musu gyadar dogu da tuni Ina ciki shike nan su da cin taliya sai dai su gani a makwsta, sai da wata dattijuwa Maijidda ta zazzage shi tukun sannan yayi shuru

Nabeel a haukace ya Kira jami'an tsaro ya sanar musu Nan take Suma Suka aikawa Wanda suke kusa da wajen har sojoji Su Affa sun sanarwa,Gaba daya su Affa sunyi jungum jungum a palo sabo suna karasowa gidan Affa aka wuce da su Kawai suna ta faman kuka sun rude,Affa yace ba kuka zamuyi ba gaba daya Addua za muke a tayata da shi itace mafita kawai kowa yaje yayi Alwala azo ayi saukar Qur'an ayi addua Allah ya kubutar da ita,Nabeel shi Kam kwata kwata ma ba a ganshi ba an Neme shi an rasa kwata kwata.

Abinda basu sani ba Nabeel mutanen Unguwarsu duk ya bada sanarwa a tayasu da Addua sannan duk ya tattaro abokansa Suka shiga wani Palo kowa yayi Alwala sukayi Nafeela tare da mikawa kowannensu Qur'an da inda zai karanta da Niyyar Allah ya kubutar da matarsa,Affa bai San ma Su Ammar sun dauki mataki ba na gayawa Allah ya kirasu Yana Neman Nabeel ya fada musu abinda sukeyi Yace Alhmdllh kunyi dabara haka ake so muma gashi zamu dukufa duk abin ya samu bawa abu na farko ya tuna da Allah ya Kai kukansa wajen Allah ba wajen wani boka ba,ko mutum ya zauna ya dinga bakin ciki Yana kuka ya kasa bacci amma ya gagara tashi ya kaiwa Allah kukansa,duk abinda ya damu mutum to ya Kai kuka wajen Allah Suma can Su Yayan Affa sun bada a taya su da Addua a masallatai da Yan uwa,Ammar Yana ta karfafawa abokinsa gwiwa cewar Inshaallah ba abinda zai sameta.
Bangaren su Papan Amarya ma haka suke ta kai kuka wajen Allah.

Nabeel lokaci guda duk yayi wani iri duniyar ta Masa zafi,Kowa abokai da Yan Uwa da iyaye sai kwantar masa da hankali akeyi ana Masa addua,ko magana ma ba yayi sai ta zama dole sabo da tunaninsa kar su cutar masa da Hamida,duk Sanda akace an sace mace ana Shiga firgici sabo da raping da ake musu ko a aure su Kawai sun zama nasu musamman mace irin Hamida zukekiya.
Bayan sun gama adduoi Nabeel part dinsa ya koma ya kwanta Yana ta tunani ko wanne Hali Hamida take oho,kwanciya yayi a saman bed ya kasa kwanciya ya Mike zaune ya zuba tagumi,Zama ne ya gagareshi ya mike tsaye sannan ya dakko Wayar Hamida data sullube a cikin mota ya kalli wallpaper dinta Wanda pic din Nabeel ta dora akai Yana Murmushi,tunano abubuwanta yake kawai bai Sanda hawaye ya taru a idonsa ba a fili yace kidnapping mutum da ciwo yake da ace mutuwa mutum yayi kasan Allah shi ya karbi abinsa amma Yana hannun wasu baka San a ya mutum yake ba Allah ka saka Mana ka kubutar da matata Ya Hayyu ya qayyum.

Mimi ce ta shigo dauke da abinci tana kwantar Masa da hankali amma kasa cin abincin yayi ruwa Kawai ya iya Sha dole Mimi ta koma da abincin.
Yayan Yan uwan Affa ma waya suke ta bugowa Nabeel suna kwantar Masa da hankali tare da karfafa Masa gwiwa zata fito Inshaallah shi dai Nabeel jinsu Kawai yakeyi.

Bangaren Hamida Kuwa tafiya me nisa Suka dinga kwararawa da ita cikin dajin Wanda yaki karewa Hamida tun tana kuka har ta gaji ta daina ga yunwa ga kishirwa tafiya taki karewa,su Kuwa dukkansu da bindigunsu zafafa sun sa Hamida a tsakiya har dare yayi tafiya suke Hamida ta lullube jikinta da mayafinta sosai sabo da Kar ma su kalli surarta wani Abu ya darsu a ransu, Wasa wasa har akayi Sallar Isha,karfe goman dare ta hude suna ta zuba uban tafiya,12am tayi duk ana uban tafiya kafafun Hamida duk sun kumbura sosai da sosai sabo da bala'in tafiya,su Kuwa sai ihu suke suna wani irin yare Wanda bata gane wanne yare ne,sai wurin 2am taga wasu Yan daban a ciki yawansu ya baci da machine,tsawa Suka bugawa Hamida hau daya,Hamida bata ko uhum haka ta gyara skert din lace dinta ta hau Suka bi wata siririyar hanyar a dajin sukayi ciki gaba daya ana gudu ana ihu ana daga bindigu,Hamida ta fashe da kuka tana karanta duk abinda yazo bakinta tana rokon Allah ya kubutar da ita ana wuta ana fyalla uban gudu.

Sai da Suka yi nisa sosai sannan Hamida taga mutane ta ko Ina duk gasu Nan a daure fululu da su kowa ya galabaita Yana cikin wani hali,ga Mata masu girki suna ta aikin girki da kantama kantaman tukane,suna tsayawa Hamida ta sakko,wasu Suka cafki hannayenta ta kwalla Kara tace zanyi fitsari cikin yaran wani ya Rakata can wani waje me uban nisa gaba daya kashin mutane ne da futsari Kamar zatayi amai ta dan yi yanda mutumin bazai ga tsaraicinta ba ta fara fitsari chaaaaaaa Yana tsaye a kanta da bindiga,

mutumin sai da ya kusa Dariya bai taba Jin fitsari me karfin na Hamida ba kamar an kunna pampo da dan wani ruwa da Suka bata a jarka tayi tsarki ta fito da sauri daga bayan dutsen mutumin yana bayanta da bindiga,Tace zatayi Sallah wani ciki ya dura mata zagi sannan da kyar ya bari aka bata ruwan Alwala,ita dai bata ce komai ba bata kula kowa ba,har tayi Alwala ta fara gabatar da sallolinta tana sane da gayya ta dinga lankanji raka'a daya ma kafin tayi aikine ga dakaru suna jira tana ta kaiwa Allah kukanta ko adduar bata gama ba duka Suka tasa keyarta gaban Ogansu gaba daya

A gabansa ta durkusa Yana zaune a Kan saman wani dutse Kato Yana bulbula wiwi ya kalleta sosai yace ke cikin tsawa ya furta ya sunanki? da Sauri Hamida tace Shakira wani mahaukacin Mari ya zuba mata ta fashe da kuka tace wallahi sunana Hamida na dawo Hamida ta,yace mu ba a raina Mana hankali a Nan yanzu Zan dauke kanki da bullet.

Hamida tace kayi Hakuri bazan sake ba,yace ke nan Amarya ce ko? tace ae sunan mijina Nabeel Lele Kuma Yana so na sadaki na million Uku ya biya amma kuyi hakuri wallah bani da kudi na bayar kyauta dubu dari biyu ce ta rage Kuma yaranka sunyi shashanci basu ce a basu ba aka bar jakar a mota yanzu da sunce kudi tun a can ai da ka samu na siyen Sigarinka ko ta kwana Uku ce irin wannan bulubawar da Naga kunayi cikin nishadi yo ai sai dai ta dubu dari biyu a kwana Uku.

Sai da ya gama Jin surutun Hamida tsaf yace ke daga wanne garin kike naga alama baki San a gaban wa kike ba,da sauri tace a gaban Uncle Me Imani nake,dariya ta bashi Wai shi zata wa wayo

yace kalli wancan mutanen Hamida ta juya tana kallon wasu maza da Mata siraran gaske Kamar Kashi da rai yace to mutanen can Manyan alhazawa ne masu kiba da tumbi sosai cikin sati daya Suka koma kwarangwal,Hamida ta fashe da kuka tana magiya dan Allah Yaya ka min rai Kar na koma haka mijina ya tsaneni,Baki ya bude gani ba a taba kawo mutum gabansa Yana Magana shima yana magana ba sai Yarinyar na,da alama bata da tsoro sosai

mutanensa ya bawa umarni Nan take Suka dinga Jan Hamida a kasa har suka daureta a jikin wata bishiya Kamar yanda sukewa kowa haka suka daure Hamida ta ko Ina,Hamida tace sai kace goro irin wannan dauro Jin abinda ta fada wani ya taho da Niyyar dukanta sai ga wani matashin wanda fuskarsa tasha nadi idonsa Kawai ake gani ya dakatar da mutumin tare da furta ka manta banda taba lafiyarta, yace sorry oga.

Abincin da suke bawa sababbin zuwa shi aka sauki Hamida da shi wato tuwon dusar masara da miyar kuka wacce ba Maggi ba gishiri sabo da zalunci wai mutum ya barke da zawo komai kibarka ka rame ka dawo duk Kashi amma babu yanda mutum zaiyi haka Hamida ta lashe tuwo sabo da yunwa,idan baka ci bama ka Sha Mari da duka,Babban Oga Yana zaune da tarin wayoyin mutane a katon buhu a gabansa tunda aka kamo Hamida yake kallonta,matarsa itace shugabar masu girki na wajen..

Hamida taci tuwo cikinta Yana ta uban kugi da rugugi duk wajen Addua kowa ke yi har dare yayi gari ya waye Hamida kwana tayi tana zawo itama har gari ya waye,masu aikin abinci suna ta fama wata Mata dauke da goyon yaro a bayanta wace ance itace matar oga wacce ya aura ta karfi ya maidata matarsa.

Yaron Yana bayanta ba dai muni ba Hamida tunda take bata taba ganin yaro me munin Dan gidan ogan kidnappers ba iya tsawon rayuwarta,wata mace dake kusa da Hamida tunda ta fahimci Kamar ogan ya fiye kaunar yaron da yawa sabo da duk auren da yayi dai akan wannan yaro ya samu haihuwa shi yasa yake tsananin kaunar yaron Kamar ransa.

Hamida dan yaron ta kalla ta fara masa wasa Kai dan baba,Dan yaro kana goye,Allah sarki uwar yaro da fara'a ta juyo ta kalli Hamida tare da cewa kin ganshi sai rigima,dama duk bala'in mace kana yiwa danta magana sai kaga farin cikinta, Hamida tana yiwa yaron wasa daga nesa tace kai dan kyakyawa kamoshi nan kamoshi nan....kamoshi...yan Yan Yan...yaro da shegen muni y wani bangale baki Hamida harda cewa me sunan baba nane ko Salisu ne me Sunan kakana,Mahaifiyar yaron tana faman washe baki ta matso inda Hamida take daure da goyonta tace wannan sulaimam ne, ahhh ashe Yaya nane ma shi yasa kake kyakyawa da kai cewar Hamida a ranta Kuwa tace tab tunda uwata ta kawoni duniya ma na taba ganin yaro Haka Kamar aljani Aljani mutum mutum.

Ogan Yan ta'addan ne ya kalli Hamida Yana murna Yana Jin dadi ta yabi dansa shi a duniya duk Wanda ya kula yaron Nan to ya gama masa komai a rayuwa Nan take yace Kai ku kwance wannan yarinyar nan take suka kwance Hamida,sauran mutanen wajen Kuwa wasu ma sun kusa mutuwa sabo da wahalar yunwa da kishi ga duka da azaba iriri kullum da ake musu, Allah ya rufawa Hamida asiri ance a daga Mata kafa zawon tuwon dusar masara ma ya isheta data kwana yinsa.

Ogan ne ya kalli Hamida yace ke daga Ina kike, Hamida tace Yar asalin wani Kauye ne dake Adamawa shine anyi bikina za a kaini Kaduna gidan Lelen Pipina ko ka sanshi ne? Dariya ta ba mutumin shi Ina zai San wani Lele,yace da yau a dinga bata abincin da mukeci da ruwa albarkacin kaunar yarona da takeyi,Hamida farin ciki ya kamata ba shiri ta mikawa matarsa Hannu Miki min shi na tayaki Reno,Matar tana farin ciki ta mikawa Hamida yaro wanda ya fara tsaiwa ma,Hamida tana Masa rawa tana yaro dan kyakyawa Yana ta dariya,Hamida tsabar neman gindin Zama yaron a hannunta yake yini,duk Yan ta'addan kowa uncle take kiransa ogansu Kuma ya koma Abba shikenan ta samu yanci a cikin wajen sai abinda taga dama takeyi mutanen dake wajen ma taimakonsu takeyi Wanda taga Yana wani Hali sai dai Matsalar Daya ba wanka ko zaka shekara dari baza kayi wanka ba Hamida gaba daya duk sunyi futu futu tsoro takeyi Kar ta fara period brush ma Sai dai su balli abin bishiya suyi aswaki ga masu tsafta.

Akwai Wanda ya nade fuskarsa sai dan iya idonsa Hamida tayi ta kallonsa kamar ta sanshi ta rasa waye har ta cika kwana biyar cif a cikin dajin.
Nabeeel kam sai Addua ya rame damuwa ta Masa yawa a hakan ma Dan ko yaushe a Addua yake ne shine ma yake samun dan sauki sauki,kullum wayarsa tana kusa jira yake kawai a kirashi a nemi kudin fansa ko nawane zai biya

Hamida ma kullum a Addua suke ba dare ba rana,Wanda fuskarsa take a nannade shine yasa azo wajen Hamida ta bada number mijinta za a sanar Masa ya bada kudin fansa Wanda dama shine dalilin kamota,Ogan yace a'a wannan sakinta za ayi baza mu karbi kudi ba tayi min abinda babu Wanda ya taba Yi wato Bata kyamaci dana ba me nadin fuska ya fara masifa ai ba haka mukayi da Kai ba mun riga munyi kasafi nawa zaka samu nima nawa Zan samu

Oga fusata yayi ba a nuna Masa yatsa nan take ogan ya mike tare da bada umarni a ladabtar da shi,Nan yaran Suka kama shi shima aka daureshi suka fara jibgarsa kamar Allah ya Aiko su yace ku cire Masa nadin nan yarinyar ta san waye mun daina rufa ma asiri,Nan take Suka fisge Masa nadin fuskar Shehu teacher din Hamida ta bayyana.

Hamida tace Malam Shehu kaine dama kasa a satoni ogan yace fada Mata gaskiya ko yanzu nasa a yanke min kanka,Nan take Shehu yace wlh ni dama sana'ata kenan tunda naga Nabeel Yana sonki nasa a sace ki idan ya aureki sabo da nasan zamu samu kudi amma ainihin sana'ata kenan na kashe mutane da dama,Hamida bata Yi mamaki ba sabo da yanda taga suna kashe mutane ba Imani ba tausayi,kafin kiftawar Ido Kawai karar bindiga taga bullet ta ko Ina duk a jikin Shehu aka juye bullet din nan take yace ga garinku nan,Ogan ya kalli Hamida yace tafi gida,Hamida ta kalli gabas da Yamma ta wacce Hanya zata bi Amma haka tayi ta kanta ta dinga uban gudu a dajin nan duk uban gajiyar dake tare da ita bata ji ko hutawa bata tsaya ba a dajin ma ko Ina tafiya take bata San inda ta nufa ba tun safe har dare yayi mayafinta da takalminta duk ta watsar da su,Wasa Wasa har gari ya waye bata hango titi ba ta fashe da kuka kafafunta duk sun kumbura taji rauni a kafafunta,faduwa tayi a gindin wata bishiya ba gida gaba ba gida baya ga yunwa da kishirwa kwanciya tayi tana kallon sama tayi flat tayi kuka tayi kuka tare da tsinewa Shehu ta daga hannu sama tace Ya Allah badan hali ba Allah ka nuna min hanyar da zan fita daga dajin Nan,Allah ka kawo min agaji yunwa da kishirwa zasu kashe ni ya Rahman ka ciyar dani

Mikewa tayi da kyar take taka kafarta haka taci gaba da tafiya sai data sake yini Yamma likis tana tafiya a cikin dajin sannan ta sake Zama a wata bishiya tana hawaye tana Addua tare da Kiran sunan Allah ta koma Kiran Lele,Nabeel,Yaya kyakyawa tun tana Yi ta koma papa da Yaya Sulaiman yunwa taci karfinta baza ta iya tashi ba.

Tana kwance taji wasu maganganu a kanta lokacin da kyar take gani dishi dishi taga wasu mafarauta su biyu da kayan harbinsu,a hankali tace ku taimaka min sace ni akayi daga wajen Yan kidnapping Allah ya kubutar dani,ruwa Zan Sha dan Allah,Wani a ciki ya tausaya Mata yace ai kin kusa bakin titi ma tashi ga ruwa hannunta na rawa ta karbi robar ruwan da ya Miko mata ta shanye tas,dayan ma ya bata tasa robar ta karbe ta shanye,wani a ciki ya zaro fura a cikin leda da yayi guzuri da ita ya mikawa Hamida ta karbe tunda ta kafa Kai a ledar sai da ta shanye tas duk yawanta bata rage ba tace bawan Allah bazan muku Kara ba ta jefar da ledar sannan ta koma ta kwanta sai data huta sosai taji karfi a jikinta ta mike tace ku nuna min Hanya naji garau yanzu na gode wayyo naga duniya

Suka ce muje sai mu saki a motar garinku,Tace na gode Suka tafi gaba dayansu tace amma dan Allah idan akwai waya a wajenku Zan Kira mijina ince na kubuta,dayan yace ki bari mu Isa bakin titi sai a Kira shi tace to suna tafiya tana basu labarin komai

Basu dade ba sai gasu a gefen babban titi Hamida murna Kamar zata yi me itace a gaba tana tafiya zungwi zungwi sannan Suka zaro waya ta karba tana Murmushi ta saka number Nabeel tayi dialing lokacin Nabeel Yana kwance Yana tunanin Hamida yaji wayarsa na Kara tunaninsa jami'an tsaro ne da sauri ya daga,Hamida tana Jin muryarsa yayi sallama ta kyalkyale da dariya Kamar yana ganinta tace Lele pipinka ce na fito Allah ya kubutar dani ka ganni za a sani a motar gidanmu ayyiriri Chaka lubaye chasss gani a bakin titi kaji karar motoci ta sake tuntsurewa da dariya tana murna,Nabeel ma har wani dan ihu ya saki yace yau yau zanzo garin zanbi flight gamu Nan zuwa.

Su dai Hamida dariya take basu ba takalmi ba mayafi a haka Suka sata a mota Suka biya kudin motar,dankunnen Gold dinta me tsada da Lele ya siya Mata shi ta cire a kunnenta ta mikawa mafarautan tace gashi ku siyar na baku kyauta sabo da taimakon da kuka min,kin karba sukayi Hamida ta dirgo daga motar bus tana rokonsu da kyar Suka karba sabo da sunga passengers suna jira,Hamida Yan motar sai tayata murna suke ta dinga basu labari kuwa Ana ta mamakin tabarbarewar

Please Login or Register in order to submit comment