Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri ka fada min kafin a tarfa mu,Lele shima ya karkato da rada yace sai a nan Zaki tambayeni ba a surutu fa,I miss you shike nan,Hamida ta dan kalleshi tare da cewa me too to muyi Shuru cikin rada duk ta fada.

Sharia aka gabatar da hujjoji komai a gaban Alkali, Alkali yace kinji duk hujjojin da aka gabatar kin gamsu ke Kika aikata Basma tace kwarai kuwa nice na aikata Kuma har yanzu Ina Kan bakana,Haka su Nabeel kowa sai da ya bada sheda Yan daba da komai sun tabbatar Basma ce,Hamida a kotu tayi hankali ta bada shedar iya abinda ta sani,duk da haka Alkali yace sai Nan da sati biyu za a dawo bayan an sake bincike Kuma za a Kai Basma gwajin kwakwalwa,Suna fitowa Nabeel ya dauki kanwarsa Fadila wacce ya dade rabonsa da ya ganta sai dai waya tana can Abuja gidan Senator,Dariya takeyi tace Yaya an kawoni Hutu munyi Hutu gidanka Zan zauna,yace to ga me gidan Nan ai,Hamida dake yin magana da su Anwar suna ta surutu ta juyo tace ga Fadilanmu ga Fadilanmu,Fadila ta dinga dariya taje wajenta tare da rike Hannun Hamida,Mimi ce ta Mika musu jakar kayanta da aka kawota da su tace kuje da ita can dama ai tafi son Yayanta,Anwar yace sai munzo gidan kafin mu wuce tace Ina jira,Fadila tana zaune a cinyar Nabeel,Hamida itace ke driving,Anwar yace ashe mutuniyar an goge,Dariya Hamida tayi tare da danna musu mahaukacin horn sai da Mimi ta Mata dakuwa sannan taja mota Suka nufi gida.

Bayan sun koma gida wanka ta yiwa Fadila ta canja Mata Kaya marasa nauyi Yan kanti,itama wanka tayi ta hade cikin Atamfa Riga da skert ta Sha kyau,Me zakici Fadila? Fadila tace koma Mene Aunty Ina ci ai,taliya da Miya ta zuba Mata Tasha nama ga lemo da ruwa su Fadila an Kara girma da kanta taci bata bata jikinta ba,suna kallo tana cin abinci,Nabeel ya fito Yana baza kamshi cikin jallabiyya arsh,Zama yayi gefen Hamida lokacin Fadila tana kasa ta kwanta tana kallo,Nabeel sai ya faki idon Fadila sannan yake wani shafa Gorar Madarar Hamida,Hamida tana kwance a cinyarsa,Harda wani cewa Fadilata Kai cartoon chanel mu kalla,to ta furta da sauri ta kamo Channel hankalinta ya tafi gaba daya kallon cartoon.

Har dare Hamida sannan ta musu girki Suka ci ta yiwa Fadila Shirin bacci itama ta shirya cikin kayan baccinta masu kyau,Fadila ta kwantar a bed dinta amma ta saka fitina ita a wajen Yaya Nabeel dinta zata kwana,Hamida tace a ranta yanzu ya Zama nawa yarinya,hannunta ta rike muje to na kaiki dakinsa,Lokacin Yana danna laptop suka shigo yasan dama haka zata faru, Fadila tace Yaya a wajenka Zan dinga kwana yace to Fadila hau bed,Kawo min tea yace da Hamida

Hamida taje ta hado Masa tea lokacin Fadila ta dawo jikin Nabeel ta kwanta sai surutu takeyi Taki bacci,har ya gama abinda yake tana surutu Hamida tana gefen bed tana latsa waya,Fadila ya daura a saman bed Yana mata Wasa tana ta dariya kamar me, Hamida tana jinsu har 12am Fadila taki bacci Nabeel yace maza kiyi bacci,Fadila tace Aunty ke baza ki kwanta ba,Murmushi Hamida tayi tace yanzu Kuwa ta koma gefe ta kwanta itama,Nabeel Yana gefe ansa Fadila a tsakiya ta makalkale Nabeel sai gani sukayi tayi bacci,Nabeel yace Yi Mata shimfida a kasa,Hamida tace akwai sanyi ka sata a bayanka Kawai

Aka tura Fadila can karshen gado Hamida ta koma jikinsa ta shige Yana shafa kanta Yana lumshe Ido zaiyi bacci yau an gaji bacci za ayi Hamida tace bata San zance ba, bacci ya fara daukansa ta fara kissing dinsa sai kace mayya,idonsa ya bude a hankali ya kalleta Kawai jaraba ke addabarta,kayi min Hidima Lelena Ido ya zaro bata taba tambaya ba sai yau yace to an gama ni dama Hakurin dole nayi, Suka Fara sarrafa juna Nabeel ya rude ya zauce sabo da irin sakonnin da take aika Masa bazai iya hakura ba,Pipi kullum gogewa takeyi da Harkar yau Kam itace me riding dinsa itace a samansa kullum sai anyi sabon style,ihu take sun manta Fadila na dakin, sai da sukaji mutsu mutsunta Kamar zata farka Nabeel ya maza ya toshewa Hamida baki da tafin hannunsa har Suka samu gamsuwa bai bar bakinta a bude ba bare tayi ihu,suna kwance Fadila ta tashi zumbur tana ruwa Zan Sha,Hamida suka fada cikin bargo ba shiri suka Yi Kamar suna bacci.

Fadila ta tsallako tsakiyarsu ta fashe da kuka tana tashin Hamida wai Auntyn Lele ruwa,Nabeel yace dan ubanki Aunty na ce? nine Yayanta dai kanwar Lele ce,Hamida ta rada masa Miko min kayana na saka cikin duhu ya jawo Riga da wondon baccinsa ya Miko Haka ta zurma su Kawai ta Mike tare da kunna haske,Fadila ta bude Ido ta tashi zaune ta kyalkyale da dariya Aunty kayan Yaya ne fa kin manta,Nabeel yace ke zanci ubanki Kuma kina Shan ruwa kiyi bacci ko na ballaki,Fadila ta cuno baki gaba Wai tayi fushi tace tunda ka samu sabuwar kanwarka ni ka tsaneni wlh sai na fadawa Mimi Ni in nace ka bani nasa kayanka sai kaki yarda ga Aunty ka bata sai na fadawa Mimi Kuma shine ka jefar dani ka koma wajenta,Dariya Nabeel yayi a ransa yace kaga yaran yanzu da wayo,a fili yace Sorry sis karki fada kinji na daina,Fadila ta fada jikinsa can wajen cinyoyinsa da sauri ya riketa kafin ta kwanta a jikinsa zata iya jinsa ba Kaya,yace bani da lafiya fa, Shagwaba ta fara ta fashe da kuka ta kwala uban ihu, ihu take zundumawa Kamar wacce aka sokawa Allura.

Hamida ta shigo da sauri dauke da ruwa tace Zaki tara Mana mutane Fadila Yi hakuri,yarinya ta makale kafada naki ta fashewa da sabon kuka, Nabeel ya bata rai yace Zaki ci ubanki gobe kije can wajen Mimi na daina kulaki tunda baki da kunya dukanki akayi,Shuru tayi Jin ance za a kaita wurin Mimi ita tafi son Nabeel ruwa aka bata tace ni ba shi ba tea nake nufi,Nabeel kamar ya mareta haka yaji ya kalli Hamida yace gidan su Anwar ne wlh suka batata Wai da dare yaro in ya farka Nanny sai ta hada musu tea haka sukeyi,Hamida tace ga ruwan zafin dana tafasa ba kayan Hadi na juyeshi nayi tsarki dazu,baki ta rufe da sauri ta manta,Fadila tace Aunty Sannu baki kone ba tab,Nabeel ya kalli Fadila Kawai yace to ba tea kinji,Bari na Mata wani ya na iya da jarabar dangin miji cewar Hamida.

Dariya Nabeel yayi yace dangin nawa ne jaraba,to kaki yi a tsaneka ba dole kayi biyayyar dole ba,au ta Dole kike? ae Mana idan a gidan mu ne ba sai nayi ball da yarinya ba,Fadila ta kyalkyale da dariya ance za ayi ball da yarinya,tashi ki dakko min towel a toilet,ta Saba dama can Watarana Yana aikenta toilet dinsa ta dakko Masa towel bata gane komai ba ,yace to jeki wajen Aunty zanyi wanka,da gudu ta Bude kofa ta fice,da sauri ya fito ya daura towel ya kwashe tissue da wives din da sukayi amfani da su ya zuba a dustbin,ya gyara bed din tare da duba lafiyar bedsheet yaga baza a gane ba sai Yar alamar laima kadan a wani wajen,wanka yayi tare da tsarkake jikinsa ya saka jallabiya Yana cikin Sallar nafeela suka dawo da tea,Hamida tace ai kin iya Sha ko? a'a Ni a baki ake bani,haka ta zauna ta dinga bata a baki tace biscuits fa Yana Ina mu da shi muke Sha,Hamida ta bude fridge ta dakko wani kala tace gashi,mu ba irin wannan ba butter milky shi muke ci,Nabeel ne ya sallame Sallah yace to Kisha haka gobe Aunty zata kaiki Shopping mall,Murna ta fara kafin kace me ta shanye taje tayi fitsari ta dawo ta kwanta,Hamida ma wanka ta shiga tare da tsarkake jikinta ta fito ta busar da gashinta ta gyara kanta sosai tana kamshi ta haura saman bed,Fadila tuni ta koma bacci Suka sake maida ta karshe.

Washe gari suna zaune a Palo bayan Hamida ta dawo daga school Exam Suma sukeyi an kusa musu hutu,Bayan Sallar Isha suna kallo Fadila tana wajen Habiba,Wayar Hamida ce ta Shiga ruri Nabeel ya Mika Mata yace Sakinanki ce dagawa tayi Suka gaisa Sakina tace ke an sani School fa zanyi NCE, Wow na miki murna cewar Hamida,Iya fa aure zata yi jibi za a daura da wani,Hamida ta bude baki tace Iyanki duk tsufanta bata hakura ba,Wai ta gaji da tallan Masara cewar Sakina,Hamida tace wani tsohon ne amma Allah kiyaye Kawai jinya ta tafi yi Wanda Iya zata iya aura ai karewar tsufa ya kusa mutuwa,Sakina tace Wai tace da Dan kwari kwarinsa,ahh kice Kawai zuba ruwa a buta zata je tayi Sakina tana dariya tace aikuwa shi zataje tayi ya samu me zuba Masa ruwa a buta,Wai matarsa ce ta mutu wani tsohon bafulatani ne,Allah Sanya Alkhairi ko banza taci kajin kiwo,Nabeel ta bawa Suka gaisa tace Ango kasha kamshi ya mutuniyar tawa,Nabeel yace gata tayi bulbul ta kumbura kumatu subu subu,Sakina tayi dariya tace ai na ganta a Online ta turo min pics ta Whatsapp ka iya kiwo,na gode ya furta Sakina tace ka tayani godiya fa ta tura min dubu hamsim Wai Naja jari,Nabeel yace an gode Mata to ta kyauta ya mikawa Hamida wayar,Sakina tace Su Sulaiman Ashe an samu Offer shi da Karima nayi murna wlh Yar uwa,Bayan sun gama waya Hamida ta Kira Papa Yana ta yiwa Hamida godiyar aikin data samowa yaransa yace ai Ummi harda kukan murna haka suka gama wayar.

Nabeel yace a Ina Kika samu kudin bawa Sakina? Kudin break da kake bani nake Tarawa da Wanda kake bani idan Zan siyi Abu na hada na bata, yace amma baza ki tambayeni ba Mene amfanina? Nan gaba zaka Yi ne karka damu
Bayan Sati biyu anyiwa Basma duk wani gwaji kwakwalwarta fes take sannan hujjoji sun tabbatar ita ta kashe Basma sannan ta Kara tabbatarwa itace ta kashe Alkali hukuncin daurin Rai da Rai ya yanke mata, Yayarta ta rushe da kuka da danginsu amma Basma mirsisi tayi ta kalli Hamida tace sai naci Uwarki Allah ya tsine Miki,Hamida ta Mata gwalo yayin da matakan tsaro Suka fita da Basma tana ta durawa Hamida ashar Hamida ta kwantar da kanta a jikin Nabeel tana ta faman yiwa Basma gwalo,Alkali ya nuna Hamida yace ke Zan yanke Miki hukunci bulala dari akan gwalon da Kike ta yi kullum ina kallonki indai an shiga kotu kin dinga yiwa Basma gwalo kenan,Dariya akayi Alkali ya mike kowa ya fito ana murna dangin Basma ne kadai ke kuka.

Yau Mimi ta karbi Fadila ta koma wajenta.
Hamida tana dawowa daga Islamiyya ta damu Nabeel sai ya bata labarinsa da rayuwarsa, suna kwance bayan sunyi Shirin bacci tana jikinsa Yana Wasa da gashinta yace

Kamar Yanda Kika sani sunana Nabeel Al'amin Lele,asalin fulanin bakwalo ne masu jajayen shanu,mu kaf zuriyarmu basa kiwon fararen Shanu sai jajaye wasu ma Jajaye ake cewa irin wannan fulanin,Fulanin Cameroon ne mu Wai inji manya amma asalinmu dai baki ne har Cameroon zuwa kakanni Suka yi,Hamida tace lallai to da ganinku kunyi Kalar larabawa,Nabeel yace oho dai, Nigeria kuma Wai ance asalalin zuwan kakannin mu to kakannin kakannine wata a ciki Wai tayi kambun baka sunyi fada da wata tace Zaki gani shike Nan Wai washe gari aka ga matar ta kwanta cuta shine a kauyen Suka hadu zasu kasheta tana ta kuka tace wlh taka San barawo tayi,Hamida kirji ta dafe Kar dai ace Dangin mayu na shigo Naga ta kaina gwara ka auri barawo akan maye,Nabeel ya tintsire da dariya yace ke Kika sani ita dai data ce zata gani ance ba abinda ta Mata Kawai ta fada a akasi ne, ganin haka Dangin da yawa Suka gudo Suka dawo Nigeria Wai Suka zauna a tudun wada Kano,Suka dinga hayayyafa wasu Kuma suna mutuwa har aka haifi kakanninmu Sara da Malam Adamu suma auren dangi aka hada suka haifi Iyayenmu

Kawu Ubaidu Suka fara Haifa Sai Al Amin Affa sai Kawu Senator Abbas su Uku kenan rak, su kawu sun taso Suma kakanninsu duk sun mutu iyayensu suna son boko suka tsaya musu har Suka gama secondary da Diploma sannan aka zaba musu Mata a dangi aka hadasu auren Zumunci,Affa ne kadai yake da budurwa a Dangin Mimi Kawai aka bashi ita,aka musu auren gata kowanne aka gina Masa gida a cikin garin Kaduna sunce can suke son rayuwa kowanne da gidansa.

Kawu Ubaidu sai da ya haifi Yara uku,Kawu Senator ya haifi Yara biyu sannan Mimi ta Samu Ciki ta Haifeni shi yasa dangi suka sa Min Lele,aka Haifeni santalele nafi kowa kyau a zuriyar mu sabo da tsananin kyawun Mimi ga Affa ma me kyau shi yasa yasa nazo a a zizana Nima,Hamida tayi dariya,a shekarar Kuma Iyayen su Affa Suka rasu motace ta bigesu sunje unguwa wajen tsallaka titi mota tayi gaba da su.

Lokacin da aka sakani a primary lokacin Affa Suka siyar da gadonsu me uban yawa Suka tafi turai Karo karatu,har Suka gama degree lokacin na kusa Gama primary,Suka koma Masters lokacin Kuma na shiga Secondary,suna dawowa Ubaidu ya Zama babban likita ya gina katon asibiti a Abuja ya tashi da iyalansa ya koma can,Alhaji Abbas tuni ya shiga siyasa amma duk da haka da sun samu dama suke komawa school su Karo karatu komai nasu boko,Indai Kai ba dan Boko bane baka birgesu,rayuwar turawa sukeyi,Amma akwai zumunci sun Zama tsintsiya madaurinki Daya,sun tarbiyyartar da iyalansu akan haka,damuwar Dan Uwa ta Dan Uwa ce Kuma kowa baya abu Kai tsaye sai yayi shawara da Dan Uwansa.

Ga rike sirri basa fadawa ko matansu suji wani sirrinsu bare 'ya'ya su Haka su binne Kuma haka Suka koya Mana Muna kaunar juna,babu kyamar talaka ko wani,ba wulakanci nine ma na Dan fita daban ban son surutu,Alhaji Abbas ya fito takarar chairman yaci lokacin Affa tuni Yana lecturing a university, bayan chairman lokacin ya fito takarar dan majalisar tarayya Allah yasa yaci ai Kuwa da shi da Kawu Doctor sune Suka daukewa Affa nauyin komai ganin sun fishi samu,karshe ma Kawu Abbas a gidansa na girma a Nan ya hadamu da yaransa ya turamu kasar waje karatu akan Ni nayi Medicine sabo da na fisu kwakwalwa amma da naje can Ni nafi son Engineering,na karanta shi,mahaukatan kudi suke tura Mana Kawai saving muke.

Lokacin Mimi ta haifo min kanwa Fadila,Ina Uk Nasha murna,tun kafin mu gama karatu Allah ya hadani da wani company na Yan China masu aikin titin kwalta,muna Hira Haka Suka ga Ina da basira sukace nazo company dinsu zasu gwada kwazona,naje Allah ya bani Nasara,Suka bani aikace aikace na dinga nunawa yaransu suna aiki Kuma abin yayi daidai na samu kudi a wajensu na hada na zuba shares dina daga Nan Muka fara
Ina dawowa kasar Nan na mallaki wasu motocin aikin wasu Kuma su suke bani haya da komai dai da Kika sani nazo kasata Ina samun Kwangila har Allah ya hadani da ke
Hamida tace gaskiya ne Alhmdllh Yanzu gashi Kawu Senator yayi Senator har sau biyu ga kawu Ubaidu shima ya bunkasa asibitoci ne da shi kala kala Allah ya baku, suna Hira har bacci yayi gaba da su.

Lokaci na ja Hamida har ta kwashe wata biyar a gidan Nabeel suna zuba love ta goge sosai ta Kare wani irin wayewa in kaga Hamida sai ka rantse ba ita bace,ta Zama me aji lokacin ne Kuma ya maidata Ss3 ta zana waec da Neco ganin yanzu tana kokari ta iya karatu da rubutu,turancin ma tana Dan tabawa sai dai ba irin me yawa sosai ba wannan sai a hankali, Islamiyya ma kanta ya bude matuka
Yau final Exam Suka zana tana ta faman Murna ta shigo gida shima bai dade da dawo ba congratulations my wife washe baki ta furta thanks yau nayi candy sai hutu da Hidima wa Naja'atu cikinta ta shafa ta kalli Nabeel dake zaune Yana kallon News Yaya Kyakyawa wlh cikina sai kumbura yake Yana tauri kullum har motsi nake ji,Nabeel ya murmusa nace Miki tun Rannan ciki ne da ke kince ke Allah ya kiyaye baki da komai yanzu Kika Fara harkalla da Naja'atu kina ta cin abinci kullum Kamar hauka gashi Nan cikinki ya fara Fitowa,Hamida da sauri tace a'a kiba ce teba ce har yaushe aka fara Amarcin za ace ciki Ni wlh Indai Muka je asibiti akace cikine to idan na haihi tsarin iyali zanyi gaskiya bazan iya ba,Harkalla da Naja'atu ta yanzu na fara kullum a zandamo min abata

Kallonta Nabeel yayi yace to Sannu Mijina,Dariya tayi ta fada jikinsa yace maza ki zubar da cikin shima garin tsalle tsallenki,

Naja'atun Nabeel ta kalla dake wando tace Najancy ana ta hutawa? Dariya ta bawa Nabeel yace Naja'atu dadi kenan?inama ana ajiyeta a gida idan zaka tafi unguwa,Allah ya shiryeki Pipi amma farko Kika dinga kuka, yace Yunwa nake ji kinga tafi kitchen Kawai Madam,kitchen ta shiga ta kyalkyale da dariya Yana jiyota ta Palo,Bread ta dakko da lemo Cock tana girki tana ci,Nabeel ne ya shigo ya ganta yace Kinga ta kanki,tana cinyewa ta hada cornflakes ta shanye sannan taci gaba da girkinta Nabeel Yana ciki Yana tayata suka Gama da wuri.
Nabeel washe gari 10am Bayan sun karya kowa ya zuba gayu ya fito Yana daura agogo yace muje asibiti dakko mayafi,Ni bana so naje ba ciki bane wani kallo ya mata ta mike zunbur ta dakko mayafi yace koma kisa hijab kina gani duk hips a waje muje ana ta kallonki

Hijab ta saka me kyau da jaka sai yaga tafi kyau ma haka yace Kai baki da nikaf ne? Hamida tace ae yace muje haka ya rike hannunta suka Shiga mota Yana driving private hospital suka je,Suna zuwa Nabeel yaga Doctor Ahmad a can a nan ma aiki yakeyi,Nabeel Suka shiga dai Yana Fitowa ya gansu Ahmad sai bin Hamida yake da mayen kallo ganin tayi uban kyau ta wani goge gwanin sha'awa,a ransa yace a haka ma a hijab kenan,Nabeel tsaki yaja,Hamida tace bari na gaisheshi,wlh kina gaisar da shi sai Kinga abinda Zan Miki wanne irin Iskanci ne wannan Zaki gaida da shi mene hadinki da shi dalla tashi mu bar asibitin wlh ko a Hanya kuka hadu Kika kulashi ban sani ba ban yafe Miki ba na fada Miki tashi ya fisgi hannunta Suka fice tare da Shiga mota Suka koma wani Hospital din daban.

Hamida cikinta wata hudu ma da aka gwada,murna Nabeel yake sosai itama haka,tace dan Daddy ya dawo ahayye dadi Zan samu dan aike idan aurensa yazo ni Zan hada Masa Lefe,Idan macece ni Zan Mata kayan kitchen in gyara yata mijinta yajita zakwai,Dariya ta ba Nabeel tun ba a Haifa ba har an kawo zancen auren da ko 'ya

Gidan Mimi Suka wuce suna shiga Mimi tace Naga Kuna ta fara'a yau lafiya? Nabeel yace jika Kika samu fa shine,Hamida tace 4mnths harda kunya Wai ta Shige kitchen,Mimi Tace gwara ma ki fito min a kitchen ke dai in kin Haihu Naga yaro tsakanin ke da dan naki

Tuwo ta gani anyi ta ebo ta fito,Mimi tace tuwon Affa ne fa,in yazo kice surukarsa taci cewar Nabeel , Affane ya shigo yace naji ana gulmata,Dariya sukayi tace tuwanka dai Saura kadan rumbu ta kwashe tana ci,Affa yace Shakira Alu takwashe,Dariya sukayi Mimi tace sunan ya dace da ita Alu takwashe girki,Hamida ta kalli Nabeel tace Lele na fada?
Nabeel yace a'a, Affa yace me zata fada?Hamida ta kwabe Fuska yace Kar na fada Kuma Ina so na fada,Affa yace Fadi,Nabeel yace no Mimi zata fada ma,to ku bar min gida na karku takura min cewar Affa,Hamida sai da ta cinye tuwo Mimi ta zuba Mata a flask Kato da yawa miyar kubewa danya Suka dauka sai gida.
Mimi Affa ta fadawa Maganar ciki ce fa Hamida ta samu,Murmushi yayi yace shine ake ta yayatawa Kai Yara da shiririta in ya girma ma kowa zai gani ai,Mimi Tace naji dadi wlh inaso a Tara min jikoki tunda Ni Allah Bai bani da yawa ba Affa yace Allah yasa.

Akwai wata marainiya Dana gani lokacin da Muka Kai ziyara da Yan Uwana Suka taimaka musu yarinya ce me Hakuri ga hankali 16yrs take Zan dakko Miki ita ki riketa Kawai a Nan a bata ilimi ai taimako ne abin,in kin ganta Zaki so ta kyakyawa ce kamar Hamidan Lele Ni suna min Kama sosai wlh.
Mimi Tace Ina so a kawo min ai taimako ne dama an kwace min Fadila tana can ya na iya,Dariya sukayi Kawai.

Su Anwar da su Ihsan duk sun fitar da matan da zasu aura matan ma sun kawo mazajensu wasu a dangi wasu Kuma a wani wajen Suka samu,shirye shiryen biki akeyi za a tafi Abuja asha bikin yaran Yaya Ubaidu Dana Senator Abbas.
Hamida sai Murna takeyi zasu tafi da Lele dama ba school jiran Exam suke yi,Maza hudu Mata Hudu za a aurar sauran masu tasowa ne sai Nan gaba.

Nabeel ya musu dinkuna na Alfarma,biki Saura sati daya Mimi tuni ta tafi can ita,Affa Kuwa Saura kwana Uku a fara ya tafi can
Su Hamida ana gobe za a fara Event Suka sauka a Abuja ita da Nabeel dinta.

Hamida ta kalli gidan senator Wanda har family din Ubaidu can Suka koma gaba Daya a gidan za ayi shagalin sabo da girmansa, Hamida an dau wanka ansha takalmi me tsini,Nabeel ta gani ya karbi key a hannun wani me aiki a gidan,masu Aiki sun daukar musu Jakar kayansu sunbi bayansu wani part da ba kowa Nabeel ya bude hadadden part yasha gyara sai kamshi da sanyi ke tashi Kawai,yace Pipina a Nan na zauna Sanda Ina gidan Nan,Gashi Allah yayi Zan shiga Nima ta furta,Kasancewar a jirgi Suka Zo ba gajiya Kawai kayan suka ajiye Suka fito zuwa wani part inda manyan suke iyaye kenan har Affa Yana can da matansu a Nan Suka kwashi gaisuwa sannan Suka tafi inda dangi suke suna Shiga katon Palo Hamida taga su Anwar maza da Mata ana ta labarin duniya ana Dariya harda dattijai dangi suna tsokanarsu,Hamida tana shiga suka hau ihu ga Shakira ga Shakiran Lele, Dariya Hamida ta saki ba shiri ta shiga ciki suna ta kallon dan cikinta.

Fatima tace Pipin Lele ashe an hadu da abin Hamida tace wlh Allah ya nufa suka dinga dariya,Lele ne ya shigo Suka Yi tsit ana Masa Sannu da zuwa Suka gaisa yace ana ta surutun shirmen ne,wajen Hamida ya karasa tare da Mata rada zanje wajen wasu friends Dina sai dare Zan dawo,a dawo lfy tace ficewa yayi abinsa mota ya hau,Suka Dora surutunsu ana ta abin dariya Hamida tace bayin Allah Zan zirarawa cikina abinci yanzu Ni bana jurewa a nuna min kitchen,ai Kuwa aka nuna Mata ta Shiga abinci iri iri gashi Nan abinda take so ta eba.

Akwai wani yaro Dan gidan Senator ne Fauzan baya son magana bai wuce 24yrs ba, duk gidansu yafi kowa kyau in ka cire Nabeel Wanda shi na daban ne amma Fauzan ya hadu sai girman Kai duk Family yafi su nuna Isa da mulki Yana Jin kansa,tasu tafi zuwa Daya da Nabeel,Nabeel sai yace ai yafi kowa hankali
Sai bayan an gama biki Suka dawo gida anji Dadi anyi zumunci biki ya kayatar an kashe Naira.

Bayan watanni Hamida cikinta ya tsufa sosai ga maitar Nabeel baya bari ta huta,tana kwance ta ya fara rabata da kayan jikinta wani dadi take karawa Yana ta

Please Login or Register in order to submit comment