Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Isa ganin Naja'atu ba,Budurwar tace Indai Naja ce gata can a class din Nan itace monitor,Hamida tayi dariya sosai tace an taba drinking din gorar Madara a gabanki? Suka ja Tsaki to ba gora ake cewa ba yogurt gashi ma mun gama sha,what of Koko an taba tiltila Miki a baki? Wata a ciki tace Kai dalla muci gaba da hirar mu, basu gane me Hamida ke nufi ba, ta sake ce musu ko Naja'atu ta taba kawo burkutu a gabanku Suka Mata banza ba ganewa suke ba,Lele ta tuna tana note ta ajiye biro tayi tagumi tace Lelena Yan matan Suka juyo suna kallonta suna kallon Hamida, wacce ta tsani Hamida sai hararta takeyi wata Jamila,Hamida ko ta kansu bata bi ba ta dauki biro taci gaba da note har teacher ya shugo

Hamida duk magana ko Abu zatace da hausa sai ta jefo ko kalma daya ce ta turanci Yan class Suka dinga gulma da gani wannan daga yanda take magana komai sai ta jefo turanci maybe tana da kokari nan Suka sallama Mata, nan kuwa basu San dan abu kadan ta rike ba Wanda ta tsinta a wajen Shehu,har wani kulata akeyi irin an kawo me kokari Pipi a ranta tana ta dariya tana Adduar Kar Allah ya kawo malamin da zai kureta.

Sai da period ta Kare aka tashe su,Hamida ta tattara littanta ta gyara hijab dinta ta fice daga class tana fita Kuwa Lele yazo Fitowa yayi tare da bude Mata motar kawai ta shiga tana wakar I'm coming home..lele dai ya rufe sannan ya zaga ya Shiga sai kallonsa akeyi har Malaman gaba daya,Hamida an dakko yunwa da rana baki ya mutu tayi tsit tunda ta gama wakar murnar komawa gida har Suka karasa gida bata ce komai ba tana fitowa tayi cikin kitchen direct ta zubo abinci sai lokacin Nabeel ya shigo yayi Dariya yace sai da nace a kawo miki abinci Kika ce aya da kwakwa sun isheki,rabu dani banyi zaton haka nake ba ulcer ce ta kamani wannan shekarar maybe bazan iya azumin watan Ramadan ba idan ya zagayo

Sama ya haura ya shiga wanka,Hamida tana gama ci ta cire uniform dinta ta bawa Habiba ta wanke su ta goge,Sallah ta gabatar sannan bedroom dinta dana Nabeel ta gyara neat har toilet sannan sauran Kuwa duk Habiba ta gama,Wanka tayi tasa Yar karamar gown iya cinya me gajeren hannu tayi kyau, kitchen ta Shiga ta danyiwa Nabeel girki me sauki sannan tayi Shirin Islamiyya dake kusa da gidan ne ba nisa sosai, nan ma sanye da uniform milk and dark brown ta fito ta iske Lele a dining,muji girkin naka ta danyi cokali daya sannan ya Mata kiss a kumatu yace a dawo lfy a kula da waya da Kinga ba daidai ba ki kirani tace to yace dan security zai rakaki kuje.

Tana fitowa cikin securities din guda daya ne ya rakata har School ta Shiga sannan ya koma gida,Yan daban da suke ta bibiyar Hamida waya Suka sake bugawa Basma Suka ce yanzu fa Yarinyar Nan an bata tsaro sosai gaskiya,Basma ta dinga bala'i karfa ku min Wasa da kudi na,na biyaku kudi me yawa taya zaku dinga raina min hankali ku yanka Yar Iska Kun kasa,Dan daban yace idan aka Kama daya cikinmu wlh kema asirikin ya tonu kibi a hankali zamu sheketa ne duk inda take Muna kusa.

Ana tashin su Hamida daga school Nabeel yaji hankalinsa bai kwanta ba da Kansa yaje ya dakko abarsa,zuwa dare ya koya Mata karatu sosai da sosai sannan Suka kwanta bacci,zai Fara tabe tabensa taki yarda Kar yace sai yayi haka ya hakuri sukayi bacci.
Washe gari da safe ya sauketa a school ya wuce office,ana Fitowa break again ta sake ganin mazan Nan suna lekenta ta katanga wajensu ta matsa suna daga waje tace bayin Allah da aure na an siyar dani ni kayan wani ce,wata budurwa ta fisgo wacce ita bata kula da maza na lekowa ba Hamida ta juya bayanta sosai da yatsa ta nuna musu Duwawun budurwar tace ku kalli na wannan nawa an siyar da shi tuni akwai me shi ta Kara gaba,Budurwar kafin ta kalli katangar sunyi kasa basu sake lekowa ba.

Nabeel Yana zuwa daukanta lokacin an tashe su suna Kan Hanya ta shagwabe tare da cewa Lele wasu ne kullum idan akayi break suke lekowa ta katanga Kuma ni kadai suke kallo ko duwawuna suke kallo oho nidai ban gane musu ba gaskiya,Nan take Nabeel hankalinsa ya tashi Yana tuki ya kalleta yace ba nan suke kallo ba,ki nutsu karki sake fitowa break ki dinga Zama a class Zan dau mataki kome kike so ki bayar a siyo Miki kinji,to ta furta jikinta yayi sanyi Islamiyya ma karki na Fitowa sai securities sunzo kinji ko? yanzu Ina da aiki da zanyi securities ne zasu dinga kaiki suna dakko ki,tun 7 Zan dinga fita sai dare,aikin kwangila ne? ta tambaya yes ya furta, Allah ya bada sa'a,Gefen fuskarta ya shafa a hankali sannan ya dauke hanyar layinsu har gida, abinci ta ci tayi Shirin Islamiyya yace muje na ajiyeki zanje gidan su Ammar muna Shirin bikinsa,Uhm kace shima ya kusa shiga layin ganin duwai,Dariya yayi yace sai kin girma kin koyawa yaranki fitsara naga alama,haba tarbiyya Zan musu zaka gani zagi yaro yayi sai dai kaji fas na kwade shi,a son yaranku Mata Allah ya kaimu Zan gani.

Yana ajiyeta ya Mika Mata dari biyar,tace kana shagwaba Ni ta safe dubu ta Yamma dari biyar sai kace matar gomna a rayuwar Nan so kake ta Allah idan ta kasance babu Kai na Sha wahalar rayuwa ta window ta shigar da kanta ciki Kamar zata Yi kuka tace Lele Allah ya baka tsawon rai da lafiya Ina sonka wlh kayi lafiya kaji, Lele yau dadi kamar an Masa bushara da gidan Aljanna bai taba ji tace tana sonsa ba sai yau yasan dai tana sonsa ga yanda take nuna Masa,gemunsa taja kadan tace a kara bari yafi haka, Lele harda wani yin fari kamar mace shauki ya kwasheshi,Hamida ta kyalkyale da dariya ta sake tsura Masa Ido Kamar zata Shige Masa Fuska tace Lele kamshi Lelen kyau Lelen Pipi.

Lele Yana ta dariyar Jin dadi sai ya fasa tafiya ma ya fito ya jingina da jikin motarsa ya wani harde kafa hannayensa rungume a kirjinsa yana dan Jan gemunsa yana karewa Hamidansa kallo.

Sai Murmushi take zubawa tana dan kallon gefe gefe sabo da Lele ya kafeta da ido,Yace kin hanani tafiya you are so cute lips dinta ta wani gyara, ganin ba kowa a wajen ya dan zaro harshensa waje in a sexy way, Lele ji yake kamar ya dauketa su koma gida ,Ganin lokaci zai kure ya bude mota ya shige ciki tace sai na dawo ya daga Mata hannu tajuya ta wuce ta danje bakin gate ta juyo ta kalle shi bai tafi ba Yana ta faman kallonta alama ta Masa da Hannu Wai ya tuka mota ta Shige school sannan yaja mota ya wuce.

Duk abinda sukeyi akan idon Basma wacce ke cikin mota tare da Yan dabanta,wani kishin Hamida ya sake ninkuwa a ranta suna baya sun buya a cikin mota suna kallo,Basma hawaye ya zubo mata,cikin Yan daban dayan yace gaskiya suna birgeni Yana son matarsa itama tana sonsa ni in ba a radio ba ban taba ganin so irin wannan ba,Ki daina kuka Basma karki ga wai Mata suna kuka a cikin film kice kema zakiyi akan Namiji karya ne wasan kwaikwayo ne Yi suke ana biyansu kudi,Kuma ba kukan gaskiya suke ba karki ga suna yi,su yi suke ana biyansu Kamar baki San me duniya take ciki ba ai su kudi ake biyansu Kuma ba hawaye suke ba ruwa ake zuba musu suyi bana gaske bane,Baku da aiki yanzu sai kwaikwayon Yan Film to Suma duk karya ce Kawai kudi suke samu ke gashi Zaki kwaikayesu ki bata hawayenk....tas kakeji Basma ta kwasheshi da Mari tace baka San so ba an fada ma kwaikayon wasu nakeyi na gaske nakeyi ni,dayan yace ah to ko mai yanzu ba su ake kwaikwaya ba daga anga Yan film sunyi abu sai a ara a yafa,Basma tace Baku San aikinku ba wlh kuje na fasa ni zanyi da kaina,Suka ce ah Indai kin bar Mana kudin ai shike Nan dama mu bamu taba kisa ba shaye shaye Muka iya ayi lafiya Kuma ki sani mun San kece Kika kashe matarsa ta farko Kika dakko Yan daba tun daga Lagos hausawan Lagos Kika yo haya Zaki sani,Basma taji tsoro amma ta fuske tunda tunaninta basu da hujja ko kotu aka je sabo da haka ko zata mutu itama sai ta kashe Hamida.

A Nan Suka rabu da Yan daba Basma bindiga ta Nemo aka ce za a kawo mata ta biya kudin tana jira Kawai a kawo.
Saurayin da zata aura Alhaji Sa'edu hamshakin me kudi ne Yana da Mata Daya da Yara biyar Basma gidanta daban ya kankara Mata shi a Abuja amma Sam ba shine a ranta ba Kawai ta gaji da rashin auren ta fiso tayi auren tunda me kudin gaske ne ko an gano tayi kisan Kai shi zai fita ya Shiga ya bada rashawa a saketa sabo da kasar haka take shi yasa ma take so Kawai ayi a daura auren ranar da za a kaita gidan miji ita Kuma ranar ta dauki alkawarin ranar zata gama da Hamida,Motarta ta ja ta koma hotel kafin gobe ta bi jirgi ta koma gidansu Wanda babu Wanda yasan me take kullawa duk anyi zaton Shirin auren takeyi,kudin ma idan an bata na gyaran jiki Yan daba take bawa.

Ammar tare suke da Nabeel suna ta zuba hira da yanda za hada komai na auren Ammar, Nabeel agogon dake daure a hannunsa me tsada ya duba yace 5pm yanzu an tashi wifey zanje na dauki abata,Ammar yayi Dariya yace to wa yace tasa ce, Nabeel yace yaro tawa ba irin taka bace baza ka samu irin tawa ba,har mota Ammar ya rakashi Yana dariya sosai sannan ya wuce direct school din su Hamida ya wuce ya ganta a tsaye a ciki tana jiransa su da wasu Wanda suma suke jiran azo a dauke su, wata Khadija wacce ta damu sai tayi kawa da Hamida duk da ba ajinsu daya ba haka Kawai taji tana kaunar Hamida tace ya sunanki dan Allah? Hamida Kabir Nabeel,nice name sunana Khadija,Hamida harda cewa nice to meet you,itama tace nice to meet you too bye,Hamida tace bye itama ta nufi motar Nabeel Fitowa yayi tare da bude Mata yace Sannu Pipi yawwa Lelena ta Shiga ya rufe ya koma ya shiga mota yaja suka tafi Hamida tace Yar gata ni ba nisa amma sai an kaini an dakko Ni Allah ya daukakani thanks Lele.
Hmm Kawai ya furta gobe za a fara kaiki ai,kafadarsa ta dafa tare da furta oh I will miss your driving,Dariya take bashi da mamaki Jin tana yawan kokarin yin turanci yace ashe dai Shehu yayi kokari Hamida tace hmm ai Shehu wlh Yana da baiwar koya karatu duk daskarewar brain dina sai da ya tasheta,Yana lailaya mota yace yayi dan abin kirki,hmm banji dadin da Shehu ya Zama haka ba ta wani bangaren Yana da Hali me kyau duk lalacewar mutum baya rasa wani halin kirki,Nabeel bata Rai yayi yace nifa? Why kike yabon wani? Murmushi ta saki tace sorry na manta mijina me kishi ne,Bmbai kulata ba ta girgiza kafadarsa I'm sorry Lelena ta wani kashe murya tare da kwanciya a saman kafadarsa,Ice cream ya tsaya ya siya Mata da kayan makulashe yace yau ba girki ki huta kinji my love.

Wayarta ta jona ta kunna wakar hausa ta soyayya tana bi tace Sadaukarwa zuwa ga Lelena tana bin wakar tana kallonsa,yace zakisa nayi hatsari fa,Murmushi ta saki yaji wani baitin soyayya yace nine nace wannan zuwa ga ke,Hamida harda dafe kirji ta lumshe Ido ya shigeni tace,Hannu ya Mika Mata suka tafa,Yazo wajen danger suna tsaye sai ga Basma itama da motarta ta tsaya a saitinsu tana kallon Hamida ji take Kamar ta dauketa da bullet amma ba a kawo Mata bindigar ba,Nabeel ne ya dan leke fuskar Hamida Yana dariya, hannaye biyu tasa tare da rufe fuskarta,Yana kallon dayan hannun yayi Ido biyu da Basma,Kallonta yayi yanda ta kafe su da Ido,Hamida ma gefen ta kalla ganni ya kalli wajen sai taga Basma,Hamida taji haushin Nabeel ko tsohon so ne ya motsa shi yasa ya tsaya Yana kallonta,Glass ta sauke Kamar yanda Basma ta sauke nata,Hamida taga Basma ta Lula tunani ta Dan bigi mota ta dawo firgit ta kalleta taga ta rame sosai Hamida tace ga kwandalata a ajiyemin a cikin kashin wuyan, Baki da lafiya? ko Tamowa ce ta kamaki?Ana ba da gyadar Yara masu tamowa, danger ta bada hannu Nabeel yaja ya wuce itama Basma ta canja road inda zata koma Hotel,Hamida ta bata rai taki Masa magana,Maganar duniya taki kula Nabeel,Yana shiga gida kafin ya fito a mota ta riga shi ficewa da sauri ya gano kishi takeyi yace Pipi Ina magana Palo ta wuce tare da wucewa sama,a steps ya cimmata daukanta yayi tare da maidata bayansa ya goyata,Hamida sai ta daina fushin tace kaini dakinka ya kaita tace karka saukeni kaini dakina Nan ma ya kaita,ya dawo da ita ya dauketa suna facing juna sai ya Kai kanta kasa sai ya dagota sama sai Dariya takeyi,Sai da ya gaji yace to sakko,uhm uhm ni kar a saukeni Kamar Yarinyar yaye haka tayi,Saman bed ya kwantar da ita ya zare Mata katon Hijab din tare da Zama a gefen bed din ya cire mata rigar daga ita sai guntun pant da bra,kirjinta ya kifa a saman cinyoyinsa sannan ya balle Mata hook din bra din ya janye tare da jefar da ita,har ga Allah bada niyyar Mata wani abu yayi ba ganin boobs din nata da yake mugun kauna bazai iya kyalesu ba,Hamida Bata hanashi ba sosai ta bashi hadin Kai Suka fara murza juna suna sakin Nishi,ganin zai wuce gona da iri ta fara nokewa nan fa yace bai San zance ba Suka dinga kokawa,har ya samu nasarar danneta ta ko Ina Wayarsa tayi Kara Yana dubawa yaga Mimi,tana danne a kasansa ya daga wayar Mimi tace Ina Hamidan bani ita dama ita nake Nema yace ta shiga wanka idan ta fito Zan bata,Hamida tasan shirinsa da karfi tace gani Mimi na fito,Dariya yayi ya shake wuyanta da Wasa ta fara tari,Mimi tana ta hello hello Kawai tarin Hamida ta ji da dariyar Nabeel,Sai lokacin Hamida tace hello Mimi Ina yini ya gida ya...Dariya ta saki ta sake cewa sorry Mimi ya Affa na Kira bai daga ba,Mimi tace kowa lafiya Nima na jiki kwana biyu shuru bamu gaisa ba,Hamida tace uhm Mimi School ce wlh shi yasa.

Yan makaranta ai naji Alama har sorry ake ce min dariya Kawai Hamida tayi sai Jin kunya takeyi tana wani ladabi ka rantse a gaban Mimi take,Nabeel sai Jin Dadi yake pipinsa tana ta hankali ko yaushe Kara canjawa take Yi,Mimi ce ta jaddada Mata karfa ta biyewa Nabeel ya karya dokar likita,Hamida harda rufe Fuska tare da cewa to Mimi,dama Kiran da na Miki kenan na tunatar dake,tace to a huta lafiya ta kashe wayar,Nabeel ya tallafe haba tare da zubawa Hamida Ido harda wani a huta lafiya,Wayo tayi Masa ta Shige toilet ta kulle Wai sai sunyi wankan tare shi yasa ta kulle da key, Bedroom dinsa ya koma ya zuba wanka sannan ya fito suka ciki kayan tande tandensu ya koya Mata karatu.

Haka abin ya kasance har Hamida tayi sati biyu kullum baida lokaci yanzu securities ke kaita su dakkota daga Nan bai sani bama tace kumma zasu na koya Mata mota, a dan wannan lokacin take dan koya tana koya duk Nabeel bai sani ba,haka idan ba Islamiyya sai tace zata unguwa wajen mimi sai ta gama koyon motarta sai ta wuce can,har ta iya mota cikin kankanin lokaci sai dai hannunta bai gama fadawa ba.

Lokacin Kuma bikin Basma Saura wata daya,Alhaji Sa'edu ne yaje zance ta hada Masa girki na alfarma suna hira yace My love ba abinda bazan Miki ba a rayuwa Matukar Zaki nuna min kauna,katon tumbinsa ta kalla ta dan tabe baki sannan tayi murmushin dole sabo da me kudine tace kome nake so zaka min? Yace kwarai kuwa tace ko kisan Kai nayi? Yace shi yafi komai sauki case nawa na kashe irin wannan yarona ma ya kashe wani na fita na Shiga nasa aka sakeshi ya kashe banza,Ni kaina mutane Nawa na kashe Kuma ba abinda aka iya Yi min ai yanzu in kinji hukuma ta kashe wani to talaka ne marar galibu,duk abinda kike so kiyi kanki tsaye ke idan ma so kike a kashe Miki a gabanki Ina da shahararrun Yan daba,Basma taji Dadi tace a gabana nake so ayi watace ta zalunceni taci amanata ranar da za a kaini gidanka ranar nake so a gabana a kasheta,Alhajin Sa'eedu yace karamin Aiki ne ma Ashe mace ce karki damu My love,Basma tace I love you ta fara bashi abincin a baki harda gyara Masa Karin hula Yana ta wani washe baki Yana murna ya samu budurwa zukekiya.

Yau Saturday Nabeel Yana wajen da yaransa ke aiki Hamida tana gida sai ga wasu mata su Uku sun shigo da wata jaka katuwa da kayan Aiki Kamar Yan polio, Security ne ya sanar Mata tace ace su shigo,har Palo aka rakosu duk da Yan birni ne amma sunga hadadden gida yasha kudi sai kalle kalle sukeyi ko Ina kamshi na tashi Yana kyalli ga ac,Hamida Suka kalla ta zuba kyau cikin wata Riga Yan kanti marar nauyi me siririn Hannu Maroon da gani kasan me tsada ce,sunyi zaton irin Yan wulakancin matan birni ne,Hamida ta kallesu duk wasu a jigace sunsha Rana da ga yunwa suke ji,Hamida Murmushi tayi tace bayin Allah me kuke raba Mana ne gomnatince ta aiko maganinta kullum baza a rana abin arziki ba sai magani maganin ma bana kirki ba duk Kun jawo yaranmu sun kangare sabo da kwayar da ake Basu yaro ka zare Masa Ido ya zare maka,Dariya Suka dinga Yi Suka ce masu kananan ciki muke aunawa idan an tabbatar da cikin sai a bada maganin karin lafiya dake da jaririnki,Ahaf nasan bazai wuce wannan ba da wannan maganin da tallafe tallafe gwara a sakko Mana da Kaya mu daina Shan tsadar rayuwa.

Tace Amarya ce ni banda ciki,dayar tace taya Kika sani Indai ba gwadaki ba,Ke karki min tambayar ya uwata ta haifeni bani da ciki amarci muke Sha Naga dai yunwa kuke ji bayin Allah ku zauna na zuba muku abinci kuci ku koshi gashi Nan duk Kun fita a hayyacinku,Dariya sukayi ta wuce kitchen suna ta yabon Hamida ta kinkimo musu wani hadadden flask da plate ga ruwa da lemo tace ku saki jikinku Gomnati tana ta wahalar daku wallahi kuyi aurenku Naga alama Yan Mata ne ku,Suka ce ai ance aure Rahma ne Allah ya bamu me son mu,Hamida tace Ameen Rahma kai ai Ni ban gane ba sai da na shigo daga ciki suna ta dariya tana ta basu dariya Kuma ita bata dariyar.

Ta zuba musu Fried rice da soyayyar kaza Haba Malam baki dama yunwa ta ishesu Suka share girki,tace a kara muku Suka ce sun koshi tace don Allah Kar kuyi Kara yanzu an waye an daina wannan ta sake zuba musu Suka lashe kadan suka rage Suka Sha ruwa da lemo sannan suka dinga Mata godiya Suka ce zasu tafi tace ku gaida gida.

Suna fita kofar gida Suka tsaya can nesa suna shawarwari,Daya a ciki tace wannan mutuncin data Mana ta ya zamu iya yaudararta a kasheta ki duba kwana Nawa bama samun abinci mu koshi haka sai yau a gidanta,gashi ta bamu shawara muje muyi aure muma mu samu farin ciki kullum muke Nan bara a Kan titi Muna neman abinda zamu sa a bakinmu yunwa ita tasa Muka karbi aikin nan sabo da mu samu kudin abinci,wallahi bazan iya ba iya abinda ta mana ya ishemu ishara,ki duba masu kudi gidajensu idan ka shiga Yanda ake wulakanta mutum kallo baka ishesu ba amma ita bata Sanmu ba ta karramamu har palonta ga abinci me dadi da nama ga ruwa da lemo haba ai wallahi mu samu miji ko talaka ne muyi aure Kuma Nan gaba muzo mu dinga gaisheta duk da cewa mun girmeta ita Kuma Basma mjn cinye kudin baza muyi aikin ba Suka kara gaba suna ta sawa Hamida Albarka.

Lele sai magrib ya dawo lokacin tana kitchen ta Masa wani girkin na daban Wai bazai ci girk tazarce ba,kitchen ya shiga direct Jin motsin abar kaunarsa ta baya ya rungumeta Yana shakar kamshinta ta juyo a hankali tare da shigewa jikinsa ta kwanta a kirjinsa tana Masa Sannu da zuwa,Kanta ya dago da hannaye biyu ya hade bakinsa da nata ya fara tsotsa Yana cewa I love your lips, Hannunsa ta rike tace bari na karasa shirya dining kafin Nan kayi wanka,kafada ya makale yace yunwa nake ji,Lemon kwakwar data hada ta zuba Masa a glass cup ta Mika Masa ya shanye ya Masa dadi yace bari nayi sauri nazo naci girkin Amaryata me dadi yau wankan ma bazan iya na kirki ba sabo da girki me dadi zanyi ta tunani,Dariya ta dinga Yi tana lekensa ya wani haura sama da sauri,da dan karfi tace kayi a hankali Lelena,bazan iya ba kamshin girki ya cika min ciki,Yana shigewa daki Hamida harda tafin Jin Dadi ta ajiye abin juya girkin tace ahayye chass inji dan daudu,tayi wani takun yanga ta kalli kanta ta dan juyo ta kalli bayanta tace Lele zai Sha Dadi gaskiya Abu lunguna lunguna Dawas Kara taji girkin zai kone ta koma jikin gas da sauri ta sauke oh Zan bata rawata da tsalle

Basma bindiga ta iso ta siyi abarta sabuwa an kawo Mata daga lagos ta boyeta tana jiran rana,gashi sunyi da Alhaji Sa'eedu tana kasheta Kawai zata bar kasar kafin lokacin zai musu visa da shi da Basma a ranar zasu bar kasar su wuce inda zasu kwashi love.


Masu sharhi Wanda basa gajiya da min sharhi Ina Matukar godiya





AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮

41-45

Official
By
AsmaBaffa


Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM



Page naku ne

Nimcyluv
Nanahkhadii
Rayys
Mom aneesa
Fatima Umar Adams
Madame Souley Aicha
🥰🥰🥰
Maman Sultan
Ummu Jiddah
Maman Murtalah
MamaZee Ddm
Maman Raiz





Washe gari Sunday Bayan ta raka Nabeel mota ya fita Palo ta zauna tare da Kiran Karima bayan sun gaisa tace Aunty Karima ya za ayi ne?da me fa karima ta tambaya,Hamida tace Wai da Zan fara zuwa gyaran jiki kafin Lelena ya dawo normal sabo da time ya kusa,Karima tace ai ya kamata ki fara amma karki ta Shan magunguna Kar a samu matsala amma jikin Kam ki gyara sai maganin Infection kiyi kin San ba a rasa mata da shi kina da su duk an kawo Miki su suna Nan bedroom dinki,yes na gansu ai,to ai kowanne an rubuta yanda zaki amfani da shi ki fara amma banda siyen jike jike banza kina Sha Kar ya Haifar Miki da wani ciwo a internal organs ki kula in baki San Abu ba karki dinga shayen banza,okay ta furta Suka gama tattaunawa sannan ta ajiye Wayar tare da haurawa sama.

Wankin Nabeel da aka kawo su Hamida ta zauna ta shirya Masa su tare da gyara komai ta tattara Inners ta wanke Masa a washing machine tayi drying dinsu bayan ta gama abinci ta goge su ta

Please Login or Register in order to submit comment