Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yana sex da ita sai da ya gaji sannan ya wulakantata wannan bakin cikin yasa ta koma karuwanci iyayenta sun mutu sai uwar daki itace tazo ta zauna tare da Maman Zee lokacin bikina,su peace Kuwa gaba daya su Uku Ra'ayinsu ne da son karya dole sai sun sa suturar da Yar Gomna zata saka,Kawai su dai karya suyi kudi shine ya kawo su Abuja Wanda karya Suka yiwa Iyayensu cewar Aiki suka samu a Abuja sakamakon duk sunyi Degree sun bar iyayensu sun dawo Nan

Fauzan yace tab dama can lalatattu ne a kansu aka fara talauci ki shirya gobe muje da Mummy,washe gari haka suka tafi gidan su Zee suna zuwa suka iske su suna Shan kida ana rawa ganin Mummy da Fauzan suka kashe tare da Basu wajen Zama harda ruwa da abinci,Bayan sun gaisa Ramcy tace Jannat murna muke Zee ta samu mijin aure Nima Haka,Jannat ta dinga murna,Zee ta kalli Mummy tana kunya tace Yana da Mata Daya da yaransa biyu custom ne a Kano gidana daban bikin bazai dade ba Inshaallah za ayi,Ramcy Kuma wani dan uwan Mamansu ne a Nan Abuja,Sannan Peace da Merry sun Musulunta shekaran jiya,Kuma a masallacin Suka samu wasu musulmai zasu aure su mun tuba gaba dayan mu rana daya muka tsara bikinmu,Mummy tace Mashaallah Muna tayaku murna,Fauzan ya kalli peace harda hijab yace Kun Musulunta duk abinda kuka Yi na zunubi babu yanzu gobe kowacce zata koma wajen Iyayenta,Fauzan yace Alhmdllh mu Kuma Inshaallah zamu dauki nauyin komai naku,Mummy tayi ta musu godiya sun dade suna hira kafin su musu sallama su tafi.

Bayan Sati Uku Jannat ta fara laulayin ciki sosai lokacin bikin su peace Yana matsowa,Anne Kuwa tana nan rai a hannun Allah babu Wanda yake lekata,har ta mutu ba a San ta rasu ba sai da Me kula da ita tazo ta iske Anne ta mutu gawarta har ta kumbura, mutane aka dan tattara tare da Kai Anne makwancinta kusa da danta,Jannat suna can akayi janaza kowa ya guji Anne,Jannat tana zaune Hamida ta shigo da Dan karamin cikinta Lele Yana kofar gida tare da su Fauzan,Hamida waje ta samu ta zauna anci shadda me tsadar gaske ta gaisa da mutane tayi musu gaisuwa ta kalli Jannat tayi Narai narai da Ido zata Yi kuka tace oh Jannat kina ganin Iftila'in rayuwa sai ta fashe da kuka,a ranta tace karya nake kukan karya nake ai mu duk gidan mutuwa sai mun taya Wanda aka yiwa mutuwa kuka,Jannat ko ita bata Yi kuka ba sai Pipi,Murtala Kuwa da yazo gaisu tabarma Guda ya dauka ya ware can gefe daya azo a dinga Masa gaisuwar tsohuwar matarsa Anne,Fauzan bai gane nufin Murtala ba yaje ya zauna a tabarmar

Murtala yace Anne baiwar Allah ga iya tuwo da Miya,Sanda hakoranta na karshe turmi zai fice tace Murtala sa kibiya ka banbro min shi,Amma matar Nan Haka ta soye min Gilala ta,ba komai Allah yaji kanki amma tooooo na dai Yi shuru amma da kyar ne idan ba a fara Jibgar Anne a kabari ba,watakil tana can an Mata butar Malam,Fauzan yace ka Fadi Alkhairi ko kayi Shuru,Murtala yace an gama Oga amma gaskiya Anne zai wahala ta tsallake siradi,Jannat ce ta fito ta rako wasu Murtala ya Mata gaisuwa,Fauzan kuwa suna hada Ido ya kashe Mata Ido daya saura kadan tayi dariya.

Da rana ana ta kawo abinci kala kala Hamida ta tashi ta koma wajen Abinci duk wani abinci me dan dadi sai ta juye a wuri na daban,a kitchen take buya taci ta cika cikinta sai ta fito ta zauna idan ance abinci tace sai anjima,Kunu aka kawo na daka lafiyayye Hamida ta mike ta karba tayi can wajen wata Amarya a gidan dake gidan yawa ne,a can tayi Sallah ta Sha kunu ta koshi ta dawo kusa da su Jannat tayi malaho harda sadda Kai,Jannat tace Aunty tun safe baki ci komai ba ga aikin juye abinci da rabawa kina ta Yi ki samu ki sa wani Abu a cikinki,Pipi tace hmm wa zai baka cin abinci a babbar mutuwa irin wannan,Ni kaina iyayena nake tunowa sai tsusayin Anne ya Kama Ni,idan aka yi mutuwa dole sai kaji ba dadi bazan iya cin komai ba kyale abincin Nan jannat.

Tana zaune taga makwafta sun kawo Dambu me rai da lafiya Yana tiriri tace bari a juye sai a hada da na dazu a sallami bayin Allah,Jannat tace Sannu Pipi Muna godiya tace ai an zama daya,tana karba tayi kitchen da dambu plate Guda ta zuba taci ta koshi ta rage ta dawo ta rabawa wasu da Yamma gaf da zasu tafi sai data Kara cin dawake sabo da Hamida ita laulayinta cin abinci da yawa take yi, da su Fauzan suka tattara suka tafi Abuja,Jannat sai da akayi Uku ta dawo,Fauzan ya dakko abarsa a airport Yana ta zumudi kwana Uku baiyi komai ba,Bayan Yan kwanaki suka Shiga bikin su Zee dukkansu sun shiryu,anyi biki na gagara ko wacce an kaita dakin mijinta.

Hajiya Amatullah tun tana damuwa har ta hakura da auren Mummy suna zaune lafiya sai dan abinda ba a rasa ba,Mama Kuwa shiri suke sosai da Jannat.
Itama Jannat ta shiga University.
Bayan wata shida Hamida ta haifo yarta mace kyakyawar gaske taci suna ummussalama kyakyawar gaske Kamarsu daya da Lele wata biyu tsakani Jannat ta haifo twince dukkansu Mata zuka zuka,Fauzan sai Murna duk ya rasa inda zai da kansa ranar suna aka sa musu Fuad da Fudhal.

Bayan shekara biyu Mummy cikinta ya tsufa sosai ba a dade ba ta haifo 'yan biyu itama duk maza,Jannat sai Murna take tayi kannai,ba Wanda bai taya Mummy murna ba,lokacin Pipi ta gama degree abinta,Jannat ma tayi nisa,Arzikin Nabeel ya Kara bunkasa,ga Affa yayi retire Lele shike komai na gidan,Fadila ta girma ta shiga primary 5,Fauzan lokacin Jannat ta samu wani cikin shima arziki sosai ya bunkasa,kowa Yana cikin Jin Dadi da kwanciyar hankali sai abinda ba a rasa ba kasancewar dan Adam baya rabuwa da jarabawa kala kala ta rayuwa.

Aslam Yana yawonsa ko Ina sai rigima,yau Sunday Nabeel Yana gida babu inda yaje,Pipi tana kitchen tana tsantsarawa me gida girki kamshi ya cika gida,Aslam ya shigo da gudu su Fuas sunzo Mum Yana Jan rigar Pipi,to je ka fadawa Dad,da gudu ya fita har da faduwa Lele yace sai ka Fadi baza ka taho a hankali ba sai kace mamanka a Kauye,Aslam yace cikin gwarancinsa Fu'as ne ya Jo,sai ga su Jannat sun shigo tare da Fauzan da yaransu abin sha'awa,Hamida tace Alhmdllh sai ku tafi min da Aslam,da gudu ya fada bayan Nabeel yace Daddy ni wajen Mimi zanje,Fauzan yace wa zai dauke ka dama ka damemu da kuka.
Zama sukayi suna ta hira anci an koshi a gidan Suka yini.
Suna kallon news suka ji an Kama wata Mata Yar asalin Niger tana safarar miyagun kwayoyi,ana hasko matar suka ga Hajiya Talatu ce ashe ,an yanke Mata hukuncin daurin Rai da Rai a kasar China.

Hajiya Talatu duk abinda ta kwashe na Abba ya Kare ta kashe su wasu sun damfareta millions of Naira karshe shine ta koma safarar kwayoyi da ragowar kudin Abba.
Yaranta biyu mace da Namiji Kuma aka dawo da su Nigeria.
Su Nabeel na gama ji Suka dunguma hukuma aka shigar da komai sai da aka tabbatar kannen Jannat ne sannan aka Basu yaran,Mimi ce ta karba zata rike su,Affa sai Murna ya masu Yara zai rike ya samu Lada.

Ita Kuwa Talatu sai kuka sai nadama gashi abinda ta tara cikin kankanin shekaru sun Kare, karshe anyi gidan yari da ita,dama China su akan harkar kwaya basa dagawa kowa kafa kisa suke yi,Talatu tun tana kuka har ta daina,ta fita a hayyacinta gaba daya.
Basma ware Baiko Kuwa ta hada kungiya guda ta mata itace shugabar Mata ta gidan yari sai abinda tace da Mata ga zalunci,duk ta addabi Yan prison kowa ya tsaneta a ciki.

Wata tantiriya aka kawo gidan yari wacce ta gagara ita Yar daba ce ta gagari ware Baiko a Iskanci tana zuwa Basma ta mata wani kallon banza,ai Kuwa matar ta Kama Basma Ware Baiko ta lakada mata dukan tsiya ta farfasa mata jiki,sai Murna akeyi ana Allah ya kara.
Yan matan Basma ne Kawai suka ji haushin dukan Basma da akayi sabo da gaba dayansu Yan matan sunfi su ashirin Lesbian sukeyi,Basma duk amfani take da su a boye a prison din.
tunda ma'aikatan suka gano sai aka dauketa aka maida ta prison din Lagos acan ake cin ubanta gaba daya wahala tasa tayi ladab Kamar ba ita ba,tana zaune sai kace an tonota daga cikin toka kanta ko dankwali babu ta rakube a jikin wani karfe ga aikin wahala,a wajen ta tsuguna tare da fashewa da Kuka abin gwanin tausayi tana na cuci kaina sai ta sake rushewa da kuka,Wata Igbo me karfin tsiya tazo ta sharara mata Mari ta bata aiki taki yi ta zauna tana uban kuka,Kafa Igbo tasa tare da yin ball da ware Baiko ta sake rushewa da kuka ta rarumi cuttlas ta tafi aikin sassake ciyawa tana bawa Igbo hakuri ba shiri ta fara aikin tare da wasu yaran matan Suma.

Pipin Lele ce ta dau wanka ta fito tana jiran mijinta a jikin galleliyar mota,Daya Yar tana kafadarta, Lele ya fito tare da Aslam rike a hannunsa sun zuba gayu wata dalleliyar mota Suka shiga driver yaja su tare da tafiya yawon shakatawa.
Jannat Kuwa da Fauzan suna Bedroom suna zuba Hidima Kamar zasu kashe kansu.



(END) karshe

Nan na kawo karshen Ware Baiko Allah yasa muyi amfani da darasin Dake cikin wannan Novel

Kuskuren da muka Yi Allah ya yafe Mana.

Masu sharhi Ina Matukar godiya da jinjina

Wanda ban bawa page ba ayi min afwa na gode

Sai Allah ya kai mu mun hadu a sabon Novel

🥰💕🥰🥰zanyi missing naku fans

Copy By Zainab Butalawa




AsmaBaffa


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment