Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa lafiya my love? Hannunta ta fisge tana kuka wiwi tace shike Nan nasan nayi ciki ma,karfin jini ne da Kai Yi kadan sai na samu ciki wlh bazan taba yafe maka ba har kabarinka yana ci da wuta ta tsuguna a wajen tana ta kuka,baki bude yake kallonta tace Kuma gidanka Zan bar maka bazan taba Zama a Nan ba gidan Mimi Zan koma ta mike a fusace tana kuka ta jawo Jakarta data jariri ta figi kayanta ta maida jikinta ta Suri mukullin motarsa shidai Yana tsaye mamaki ya kashe shi yace ko dai Aljanu gareta?

Aslam ta karbo su dai masu aiki sunga tana ta kuka ta fice da kayanta Dana jariri ta hau mota ta bar gidan,Nabeel ransa ya baci yace tab za ayita sabuwa ashe Ni Kuma kinyi da dan halak bazan je biko ba kada Allah yasa ta dawo,gashinsa ya shafa ya juya Yana huci yace ga masifar Ina sonta sai kace Wanda aka yiwa asiri Ni zata rainawa hankali,gashi na daina Shan giya bare na kora,ruwa ya dauka ya tiltilawa cikinsa yace Zaki sani yarinya,Zama yayi a bakin bed din ya sake mikewa yace Mata ba Yan goyo bane Yarinyar Nan fa ta rainani Ni to na zauna Ni Daya a gidan nayi uban me

Hamida Kuwa a gidan Mimi tayi parking ta fice jaririnta na hannunta tana kuka ta shiga sai taga wata yarinya gidan Yar kyakyawa da ita ta rakube a gefe ta hade rai kamar an aiko Mata da mutuwa,ita Yarinyar Bata da fara'a ko miskala zarratin kafin ma tayi dariya Aiki ne itace wacce Affa ya dakko daga gidan marayu 17yrs take,Mimi da Affa Suka Mike tsaye suna tambaya Hamida lafiya,Bata ce komai ba tana ta faman share hawaye,Baza ki magana ba wani abin ne ya faru? Hamida Tace Yaya Kyakyawa ne Ni gaskiya garinmu Zan koma,Affa yace Mene yayi miki to? Tace Mimi banfa Dade da haihuwa ba Nasha wahala gaskiya Ni gida Zan koma.

Nan take su Mimi suka Gane har Mimi ta bude baki Affa ya Mata alama da tayi Shuru,da Kansa yace a'a ke da kike da gata Hamida ai ke Yar gata ce ki zamanki karki koma zauna a nan,da sauri ta kalli Affa tunaninta zaice a Kira Nabeel a Masa fada ta koma gidanta sai yace ta zauna ai ita ba Zama tazo Yi ba me zata Yi a Nan ba Nabeel a kusa.

Sarkin Fushi ce tayi magana ba wani alamar fara'a ko Wasa tace mu Muna layi Muna jira idan wata ta saki nata zamu damke mu,Hamida ta kalleta Tace ke nayi Miki saurayi akwai irinki family din Nan wlh idan Kika kalli Lelena Sai na koma gidan mijina,Mimi suka Kama dariyar Hamida sun zaci wani mataki zata dauka suna Haka sai ga Fauzan yazo gidan an shigo da akwatinansa bautar kasa yazo a Nan zai zauna Dan gidan Senator.

Sarkin Fushi ta zaci shine mijin Hanifa a ranta tace dole a kirashi da Yaya Kyakyawa sai ta tafi waje Fauzan ta tari gabansa Kamar zata shiga jikinsa ta kwalalo Masa Ido sai da yaji tsoro ma shi,gata ba Fara'a ko digo a fuskarta, fari ta Masa farrrrrr farrrr Wai duk Dan ta bawa Hamida haushi ta tashi ta koma gidan mijinta, Bata iya Dariya ba ta yake hakora kamar me tallan toothpaste,Fauzan ma sarkin Fushi ne ga saurin Fushi ga rashin magana,Hamida ta kyalkyale da dariya tace algunguma to ba Nabeel bane wannan Fauzan ne,Fauzan Hannu yasa ya hankadeta gefe ya kalli Affa yace Can you Imagine wannan yarinyar tana kwalalomin ido, sai fa na fasa Zama a gidan Nan daga Ina aka kawota? Affa yace daga gidan marayu Allah sarki marainiya ce sunanta Jannat,Mimi tace kace me hankali ce Ina hankali a nan? To gwara ita dai akan Hamida da farko,Hamida tace Kai Mimi nafa Yi hankali,Ina hankali kinyi yaji,Affa sama ya haura sai ga Nabeel ya Fado dakin.

Lokacin sarkin Fushi sai da taji tsoron kyansa da kwarjini da haibarsa,wajen Hamida ya nufa yace Ina key din motata tace oho,Mimi tashi tayi itama ta barsu Yana ganin ba kowa ya fara lagude kirjinta da wayo Wai neman key yake, sarkin Fushi tuni ta bar wajen ta Shige dakinta jikinta na rawa, Nabeel baiga key ba ya karbe Baby ya ajiyeshi gefe ta cikin kafafu ya zura hannu ta kasan skert ya bige da shafa cinya duk neman key yakeyi,Hamida taji kamar tana son Hidima tace mu je gida na fasa yajin yace karki sake ki dawo gidana kiyi zamanki Kuma bai fasa mutstsika Gorar Madara ba Wai key yake Nema har yanzu Hamida taji tsoro Kar a fito a gansu ta dakko a jaka tace ga abinka Kiri Kiri yasan shine Yace ba shi bane wannan ai key din kofa ne yaci gaba

Dama zuwa yayi ya kunyatata yanda da kanta zata bar gidan,na shiga Uku Kar a kamamu da yarinya a gidan Nan yace muje bedroom nayi searching ko na Miki tsirara a Nan,tashi tayi ba shiri ta shiga wani daki harda da sa key,Suka bar yaro Yana ta kuka a palo.

Dakikantar Hamida ta motsa tana kallo ya cire Mata Kaya Yana ta Murzata ta biyewa Jin Dadi sai da Suka sake Yi a dakin sannan Suka maida kayansu,ta fashe da kuka shike Nan ciki,Kinga wallahi ki bini mu tafi gida ko na Miki abinda Baki zato ba,suna fitowa Suka ga Mimi tana jijjiga yaro Hamida tayi sauri tace banga key din ba mun duba dakin ma babu muje gida mu gani kunya ta kamata ko Dan Bata iya karba ba ta figi kayanta ta fice,Nabeel ne yayi karfin halin karbar yaro Mimi ta Mika Masa ta dada Masa duka a baya ku tafi marar kunya,Nabeel dai ya fice Sarkin Fushi tana ta lekensu ta kofa Nabeel ya tafi da imaninta,Nabeel take kauna gaskiya tana so ko a ta biyu ya Kara da ita.

Jannat Jin sun tafi sai ta fito tana Fitowa Fauzan ya sakko shima da sauri,Jannat ta kalleshi da sauri tare da dauke kanta tace ko wannan Zan aura ne? Wa Zan aura duk gasu masu kyau Kai wancan yafi gwara wancan wannan bashi da mutunci,a ranta ta sake cewa Kai gwara wannan amma ban sani ba ko shima Yana da Mata bari naji,Fauzan ya zauna cin abinci a dining ya kashe gayu cikin kana Nan Kaya Jannat ta karasa inda yake tare da durkusawa har kasa a gabansa ta sadda Kai kasa tace dan Allah Ina da tambaya babu fara'a ko digo shima haka,tace dama wata magana nayi a cikin zuciyata Kawai Dan babu damar da zaka ji ne amma Zan dai Yi tambayar please kana da Mata kaima?

Baki Fauzan ya bude spoon a hannu ya kasa cin abincin tace karka Yi Fushi tambaya ce ance matambayi baya bata wani Abu nake so na tantance,are you normal? Fauzan ya tambaya tace yes I'm normal please yace Ina da Mata what's your problem? tell me ya furta da karaji,Jannat ta Sosa gashinta ta fara masifa itama Kamar sa'anta Wai ku Mene Haka ne ae wannan da Mata wannan da Mata shima duk Yara daku baku taru kunyi mutum Daya daya kwakwara ba,ae Haka akeyi a rayuwa, Fauzan ya fusata ya mike zai mareta Affa ya fito Yana tsawa Kai Kai lafiya?

Me tayi maka Dan Iska dama Kai duk yaran Nan Kaine ba mutumin kirki ba kullum sai zafin zuciya Kai da Lele baku da kunya yarinya me hankali,Affa yanzu wannan abin ce me hankali wallahi bata da hankali ka kaita asibitin kwakwalwa,Mimi tace sai da na fada ga masifar Fushi yarinya ba faraga a Haka Kuma baza ta taba magana akan abin kirki ba sai shashanci zaka ji tayi magana ga bala'in kyuya wannan ba irin Hamida bace gwara Hamida tana Aiki gata tana da ilimi na banza,Affa yace Kai ku daina Haka wlh a gidan marayu na dakkota, Mimi tace Hmmm ai sai kayi ta koma daki tana cewa yaje ya kwaso Mana Yar shege wa ya sani ko cikin shegece aka jefarta aka kaita gidan marayu bazan iya ba a kaita wajen Alhaji Abbas baban Fauzan shine sarkin dakko marayu ya Raine su idan sun girma ya musu aure ya musu gida da komai Kawai a kaita can ta hadu da halin Maman Fauzan Bata kaunar marasa asali Nan gaba can Zan kaita taci ubanta a gidan bazan iya ba Ni ban iya zalunci ba

Jannat Jin irin masifar Fauzan ta yanke a ranta Nabeel zata aura Kawai,Amma Kuma taji ance suna da yawa, washe gari a Palo ta shimfida Sallaya tayi Sallar azahar tana idarwa lokacin Fauzan Yana kwance a palon yaji ta sallame Sallah maimaikon yaji Addua sai Jin tafi yayi tana rera kasidar manzo Ya manzon Allah Sayyadil wara yaaaaaaa.......Manzona manzon Allah Sayyadil wara.. ta rera harda da Kara volum,Fauzan ya juyo a fusace tana sani zata kashe Masa dodon kunne,tayi mugun tsorata Amma Bata tashi ba tunaninta kasidarce baya so sai ta fara Na kusa Na kusa in Mari soja... sai Dan Sanda ya Kare Kai Dan Sand Yi a uwarka Ubanka tana nuna Fauzan da Hannu ai Kuwa Yana tashi yaga shi take nunawa Ni kike Zaki dan ubanki a gidan marayu ba manya ta kwashe da gudu,Affa ne ya fito yace Kai ka kiyaye ni Yarinyar Nan wlh ba a agidan marayu ta girma ba da girmanta aka kaita can Zan baku labarinta nan gaba,ko wata Bata Yi ba a gidan marayu Kuma da iyayenta ku daina Mata wulakanci karku zo Kuna Jin kunya.

Waya Fauzan ya Kira Nabeel yace matarka tana gida? Yace ae Mana yace bari naje can wannan jarabar Yarinyar da Affa ya kawo daga gidan marayu ta dameni,Nabeel yace au wata aka kawo Kuma gidan? Kai baka ganta ba da kazo daukan matarka,Allah me iko ban kula da ita ba ma ni matata nake hangowa Kawai.
Fauzan tashi yayi ya tafi gidan Hamida,Hamida tana ganinsa tace yau a gari,yace uhm Kawai tare da daukan kyakyawan Annur dinta Yana Masa rawa Hamida tace karka tsinke Masa hanjin ciki baka San wahalar haihuwa ba kwata kwata kwanansa Sha biyu a duniya wannan wacce rawa za a Masa bani Dana gaskiya Hamida ta karbe danta,Aunty Hamida Wannan son Dan fa ai gaskiya ne,me zaka ci? Allah kiyaye naci girkin me jego cewar Fauzan ai daga juice na kwali sai lemon da Zan balle da kaina sai ruwa su Zan iya ci

Hamida tayi Murmushi tace na Jannat dama kana labari Haka,Shuru yayi Mata Yana canja channel,Nabeel ne ya fito an zuba wata gezna arsh kamar ango yace na tafi,Hamida tace a gaida Amaryar Ammar kafin naje yace zata ji ai ya Miki afwa tunda kina jego.

Sai ka dawo ta mike ta rakashi yace ki shirya dausayi kafin na dawo a Kansa Zan huce gajiya Nima angwanci make,Dariya tayi tace to Kawai ya tafi ta dawo Suna Dan magana da Fauzan Jefi jefi ta kawo Masa lemo da ruwa.

Affa ne ya Kira Nabeel yace idan ka Gama kazo Ina nemanka,Bayan Nabeel ya Gama abinda yake ya wuce gidansu Bayan sun gaisa da Mimi yaga Jannat ta zauna Fuska ba Rahma Tace Ina yini daga Haka bata Kara ba ko kulata Nabeel baiyi ba ya haura sama Yana zuwa Suka gaisa da Affa,Affa yace kasan me yasa nace kazo? Yace a'a Alfarma nake Nema me zai Hana ka auri Jannat yarinya baiwar Allah in kayi Haka kayi taimako zaka samu Lada Ina maka kwadayin wannan ladan Nabeel,yarinya Yar sunna ce Nan gaba Zan baka labarinta Mai ban tausayi,Nabeel Nan take ya bata rai yace Affa ba Wai bazan ma biyayya ba Amma Ni gaskiya bana sonta Haba Affa Hamida fa,Affa yace Allah ne yace a Kara ai Kuma Hamida nasan bata da matsala zata Amince Ni da kaina Zan Mata Maganar, Nabeel murmushin bacin rai yayi yace Hamidan ce zata hakura? Kamar baka santa ba to wallahi ko ta yarda a gabanka Ni na fada maka sai ta bar min gidana,Ni Kuma Ina son matata wlh bana son bacin ranta farin cikin Hamida shine Nawa, in ba Hamida babu rayuwata,ko wace bazan iya sonta ba,Ni za'a sa na dinga aure aure ko wacce ace Ni bags dangi Nan ba a jona su Mana sai Ni za a ruguza min farin ciki wlh bana sonta ko an daura sai na saketa Ni tun yanzu ma na saketa saki Uku Kuma wallahi idan aka fadawa matata ta tafi ta barni Nima baza ku sake ganina ba.

Mari Mimi ta kifawa Nabeel wacce shigowa tayi ta tsinci zancen,Bata so itama ayiwa Hamida kishiya sam,Tace baka da hankali kasan a gaban Wanda kake mahaifi ya wuce Wasa so hauka ne bai Isa ya baka umarni kabi ba Ashe yanda yace Haka za ayi,ko dan kaga Kai kadai ne damu sai Fadila tashi ka tafi karka sa na maka baki, Nabeel mikewa yayi yace Kuma wallahi bana sonta wallahi ko an daura sai na saketa na rantse da Allah gwara ma ku bawa wani ita,Kofa ya bude ya sake juyowa yace bana sonta ai Allah yace sai kana so zaka auri mutum ya fice abinsa ya koma gida,lokacin Fauzan ya bar gidan,Hankalin Nabeel a tashi ya shiga palonsa,Hamida taci uban kyau cikin Nighty dinta tana kamshi,Annur Yana wurin Nanny,ganinsa Haka sai jikinta yayi Sanyi Tace lafiya? jikinsa ya jawota tare da rungumeta Kam bakinsa ya daura a kunnenta yace kishiya za a miki,Affa Yarinyar daya kawo Wai ita zai sake aura min nace bana so wlh da alamu baza su yarda ba,abin Mamaki sai yaga Hamida tayi Murmushi tace to menene ba Allah ne yace Ayi ba,lokaci ne Allah ya kaddara ba yanda za ayi.

Ka daina damuwa Indai dan nice tunda iyayenka ne Suka ce,Kuma ba a Wasa da iyaye kullum kokari ake a musu biyayya sabo da a Gama lafiya da su,Aljanna kake Nema fa haba Lelena ya za ayi kace baza ka musu biyayya ba taya Ina kallo Zan bar mijina ya nufi wutar jahannama Ni da nake so mu dawwama a Aljanna.

Duniyar kanta Nawa take yanzu zakaji ance babu mutum amma a kanta a zauna ana bata lokaci gaskiya baka kyauta ba,yanzu ka Kira su Affa kace ka Amince Nima na Amince mu basu hakuri Saura kadan kuka ya kwacewa Hamida za ayi Mata kishiya amma dai ta danne abinta su Hamida anyi hankali bai zaci haka daga gareta ba yanda take Yar daru.
Gefen bed ya jata suka zauna yana karewa fuskarta kallo tana murmushin karfin hali fuskarta ya shafa yace kin San dalilin da yasa nake kaunarki? Hamida tace sai ka fada? Yace sabo da Kawai kece Hamida Pipin lele duk a yanda kike Ina kaunarki,Kamar bakya kishina ke Why? Me yasa bakya min son da nake Miki? baki cancanci Haka ba a wajen iyayena,Wacce mace ce a duniya ta gagari a Mata kishiya duk wacce ta sa Rai zata zauna ita Daya ta yaudari kanta,Fiyayyen halitta ma ya auri mataye sannan matansa da Suka fimu daraja sunyi zaman kishi to mu su waye

Wayarsa ta dauka ta Kira Affa Saura kadan tayi kuka ta sake dannewa tana murmushin dole Yana dagawa yace Lele me ka kirani ka min bayan ka nuna bani na haifeka ba,Hamida tayi magana Affa kayi Hakuri Dan Allah Hamida ce,Oh Hamida sai Affa yaji wani kunyarta Kamar me,Tace Ya tuba Affa kayi Hakuri ka yafe masa ka bawa Mimi ma Hakuri ya amince Nima Haka na Amince Allah ya bamu zaman lafiya ya bashi ikon Yi Mana adalci,Mimi tana gefe tana ji tace yanzu abinda kayi ka kyauta kenan? Yau da Lelene yaga wata yace Yana so ba ruwanmu a Haka Kuma ku maza kullum kuce kunfi Mata hankali,Affa yayi Murmushi yace da kinji tarihin Yarinyar Nan da kin San da Lele ta dace,bani da shakku da Lele wlh zai riketa Amana ko da baya sonta,to yanzu Mene ribar ashi wacce baya so Kai wa ya maka dole? akidarka ta boko ma ku ai ba a Baku shawara kuji sai kayi wlh ba hannuna a ciki,Kuma Ni Hamida nake so sai dai kayi Kai kadai.
Ni kuma Zan nuna muku Ina da iko,Iko sai Allah shine me Iko Kuma idan Allah baiyi ba baka Isa ka daura auren ba ta fice fuuuu.

Bangaren Hamida Kuwa Lele ta taimakawa ya cire kayansa Yana ta faman tunani,toilet ta kaishi sannan ta kulle Masa ta fito,tana fitowa dakinta ta wuce ta kulle tare da fadawa saman bed ta fashe da kuka Hamida harda jiniya Idan tayi tayi karshe tace Lelenaaa...ta sake ci gaba,Har ya shirya Yana jiranta yaji Shuru Shuru dakinta ya nufa,Jin kamar ta fiya ta mike tare da fadawa toilet ta rufe kofa ta shafawa fuskarta sabulu tana wankewa tana daura alwala ya shigo toilet din direct yace I thought wanka kike,Kasa magana tayi sabo da tana bude baki kuka ne zai kwace Mata.

Tashi tayi kanta a kasa sabo da Kar yaga alamar kuka,kiranta yayi Pipi...uhm Kawai ta amsa,yace Hamida ajiyar zuciya tayi tace na..na"am...hannunta ya riko Suka fito room din,fuskarta ya leka yace kuka kikayi? A'a ta furta tana girza Kai sai hawaye ratatata tafin hannunta tasa tare da rufe bakinta da fuskarta kuka ya kwace Mata me karfin,Amma Kika amsawa Affa?ban taba saninki da boye boye ba bakya boye abu me yasa kika lallaba Affa,Ni nasan wlh ba haka bane a ranki,ba...baf...bafa komai Kawai iyayena na tuna,Ina Kika sansu har da Zaki tunasu Pipi.
Saman bed din ya jata suka kwanta Yana ta lallashinta har ya dan samu tayi Shuru.

Bacci ya fara daukansa sai kukanta yaji ya tashi da sauri ya hangota a saman Sallaya ta daga hannu sama ana addua shine kuka ya kwace da Alama Nafeela tayi,Shuru yayi Yana kallonta ranar a haka ta kusa kwana sai da ya gaji yazo ya dauketa Yana ta lallashi bakin ciki ya isheshi suna zaune lafiya da matarsa anzo an ruguza musu farin ciki.


Nan na kawo karshen Part 1

Saura part 2
Idan na huta kwana Uku ko sati daya zanci gaba

Ina godiya fans da masu godiya da masu sharhi,Wanda ban bawa page ba suyi hakuri abin sai a hankali Zan Basu a part2 Inshaallah


Ayi Hakuri banyi editing ba yau.


WARE BAIKO GROUP page naku ne






AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮
(JANNAT)
Part 2.

66-70


Official
By
AsmaBaffa


Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM



Page naku ne mutanena

BESTYNBEELAT
AUTA
UMMI DEEJAT
AUNTY NICE
MAMAN SAMHA
UMMIN SADEEQ
UMMIN NAJWA
QUEEN MEENAT MHD




Washe gari Jannat da asuba ta tashi tayi Brush da Alwala ta fito Sallah ta gabatar ta zauna tana ta azkhar Allah ya hore Mata Addini har rana ta fito sannan ta Mike tayi wanka ta shirya cikin wata kodaddiyar atamfarta ja Riga da zani,Hijab ta saka baki fuskar Nan a daure ta fito ,tana fitowa Fauzan ya Sha wanka cikin kayansa na NYSC zai fita,Mimi da Affa suna dining dake da wuri suke fita aiki,har kasa ta tsuguna ta gaida Affa ya amsa da fara'a ta gaida Mimi itama ta amsa,Fauzan ta dan kalla tace barka da asuba ko jiran amsawarsa bata yi ba ta mike zata bar wajen

Garin sauri ta dan bigeshi bata kula ba,Mari ya kwada mata Yana masifa naki da hankali Zaki bata min Kaya,a fusace ta kalleshi dafe da kumatu Shuru tayi ta juya ta tafi Kawai a ranta tace wlh sai na rama.
Affa ne ya lullube shi da fada ya kamata kusan darajar dan Adam sabo da yanda Allah ya karrama dan Adam,bana son irin wannan ka kiyayeni tam,Mimi tace Fauzan bai kamata ba gaskiya ka gyara,Shuru yayi ya zauna Yana cin abinci,Bacci ta koma sai 11am ta tashi ta fito taga ba kowa duk sun tafi wajen aiki sai masu Aiki, tace ana yiwa boko baurta a gidan Nan,abinci taci itama ta koshi sannan ta koma dakinta ta dakko Qurani tana tilawa,tana gamawa ta koma sauran littafan addini tana bita sai data gama sannan ta fito bakin gate

Har kasa ta tsuguna gaban su Sale tace Ina yininku suka amsa da fara'a tace Wai a gidan Nan ba cinnaka Kuwa nemansa nakeyi zan hada maganin Ulcer,Inuwa da Sale suka kalli juna cike da mamaki,Inuwa yace tab ai sai dai kije Garden jikin fulawoyi da bishiyu maybe ki samu,na gode tace ta nufi garden tun 2pm take neman cinnaka a garden din bata samu ba har Allah yasa ta ga wasu birda birda a kasan bishiyar mangoro harda masu tashi, farar Leda ta dakko tayi ta zubawa sai da ta tara da yawa sannan ta daure ledar ta koma ciki
A dakinta ta ajiye tazo taci abinci tayi sallah.

Sai da asuba tana Jin fitar Affa da Fauzan masallaci tun kafin tayi Sallah ta fito sannan ta haura sama a hankali Kamar barauniya da sauri ta Bude dakin da taga Fauzan Yana shiga,Bedroom dinsa ta shiga ta hango takalmansa guda biyu na nysc sai ta cire dankwalinta ta goge Masa shi tas ta zuba cinnaku a ciki da yawa,ta koma wajen dayan ma ta goge ta zuba cinnaku incase of duk Wanda ya saka akwai cinnaka ciki,gashi sun Sha wahala a leda kasa fita sukayi daga takalmi,ficewa tayi tayi Sallah tare da wanka Sannan ta fito ta iske Mimi,Fauzan da Mimi suna breakfast duk sunyi Shirin fita,Fauzan yasha kayansa na nysc yau ma akwai abinda suke Wanda dole sai sun sa kayan shi yasa ganin takalmisa fes fes bai ko goge ba ya saka abinsa

Tun Yana cin abinci yaji Kamar abu na bin kafafunsa haka dai ya fita compound da key din mota a hannunsa,Yana bude motar yaji abu ta cikin wandonsa ya galla Masa cizo a jere, tsalle ya buga cizo suke bashi ta ko Ina a cinyoyinsa,Su Inuwa suna kallo,Dan fuskewa yayi ya tafi zai shiga mota ya saki Kara tare da dawowa baya ya fara cire takalman Ina cinnaka har cikin duwawunsa suke ta gallawa cizo da sauri ya shiga zare belt din wandon ya zuge zip tare da yin kasa da wandon Boxers dinsa suka bayyana azaba ta isheshi gashi wandon wani tight na daukan wanka sai an nutsu ake cirewa, wandon ya sutale kasa iya dunduniya gashi yaki cirewa ga azaba ta isheshi Yana ta Sosa cinyoyinsa da Suka yi rudu rudu abinka da me haske.

Su Inuwa ne Suka Zo Alhaji lafiya? Fauzan ya daura hannunsa a bayan duwawunsa Yana ta Sosa wajen ga cinnaka a ciki Kara cizonsa yake,duk ya hada zufa Ya dafa sale yace Inuwa karasa tsige min wandon Nan Inuwa da sauri yace Alhaji ai cinnaka ne ga wasu Nan suna yawo a jikin takalminka,dan Allah ka cire min Ni cewar Fauzan,Inuwa ya fara kici kicin cire wando ya kasa Fauzan ganin haka yace matsa dalla ya zauna a kasan Interluck dirshan cinyoyi duk a waje ga dan guntun boxers Sale sai kunshe dariyarsa yake ya tabbatar sabuwar bakuwa ce me kunci itace take neman cinnaka jiya,idan ba haka ba Ina za a samu kwari a gidan Nan,Shidai Fauzan da kyar ya samu ya zare wando sannan ya mike Yana zazzage boxers dinsa Kamar zaiyi tsirara,Sale ya karbi wandon ya karkade sai ga cinnaku sun zubo kasa,da sauri Fauzan yace jefar da shi ya koma ciki da sauri,Mimi da Affa suna zaune Jannat tana gefe tana karyawa ya shigo da Yar Riga sai boxers,Mimi Tace lfy Kai Kuma? Cinnaku ya iya furtawa ya haura sama,Suka dinga dariya Cinnaka ne

Please Login or Register in order to submit comment