Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taba ce muku Ina zuwa ba sabo da idan na fada nasan Zaku hanani shi yasa nake zuwa a boye,Amma sau daya Yaya kyakyawa yayi min nidai ya fara tattaba min dangerous part Ina Jin Dadi na biye Masa baki gani ba Ummi ya dinga taba min Nono wallahi Dadi tunba ya fara shansu ba Ni Kuma sai na kasa hanawa har ya samu ya sa min wani Abu me zafi ya fara Haka kingani ta dinga gwadawa Ummi Tace Ina Jin zafi Ina Jin Dadi Dadi,nace Yaya kyakyawa ka daina yace da Dadi,Kuma yace Yana so na zai Zo ya daukeni mu tafi birni, har ma yace Ina da dadi, Takaici da kunya ya kashe Ummi tace yaushe yace Yana sonki tace Sanda Yana yin abin ya fada min ta furta ko a jikinta Kamar cikin sunna har wani Murmushi take.

Ummi sai ta Nemo Napep ba Wanda ta gayawa tasa Hamida a gaba har asibitin Dake birni akayiwa Hamida test har sau Uku an tabbatar ciki ne na wata hudu,suna dawowo ta Kira Karima Tace tazo gobe da meeting lallai,Sannan ta sanarwa su papa tare da bashi result ya gani,washe Gari da safe Karima tazo sai Suilaman, Papa da Ummi,Papa yace Hamida duk naji komai,Hamida Tace kayi hakuri Papa mun tuba ban San Haka ake cikin ba,Ummi tace dabbar Ina ce Baki San ko ya aka samu matsala ba ciki Zaki dauka mahaukaciya dabba,karamar yarinya ce ke a'a tunda yarinya ce ke mahaukaciya Zo kici gaba da Shan Nonon uwarki.

Sulaiman yace yanzu ta Bamu number a kirashi Kuma dan Allah mu binne zancen Nan iya mu Kar wani ya fidda Maganar nan ta bazu a Gari abin kunya ne, Karima har da kuka ta tashi Kawai ta koma birni gidan mijinta,Yaya Sulaiman shima dakinsa ya shige ya rage Saura Papa da Ummi,Ummi tace munafuka kullum ki damemu da Yaya kyakyawa Yan Yan Yan.... Ashe abinda kike kenan.

Papa yace Dan Allah Abu ya Riga ya faru kema Hadiza kinfi kowa laifi bakya sa Ido a kanta na fita Ina Nema Ni Zan zauna na lura da gida,mace itace jigon tarbiyyar Yara,da ace kin Mata tarbiyyar da haka baza ta faru ba,Amma kin watsi da ita ta taso Bata San komai ba a zamanin Nan ace Hamida kamarta Bata San Mene Zina ba,Ummi Tace ohhhh yanzu wato ta kwabe zaka dora min laifi sanda nace a lura kar ta dakko masifa me kace Nan Papa da Ummi suka Fara fada,Hamida da sauri tace duk kowa yayi Shuru Dan Allah ta dafa kafadar Ummi da Papa tace karku yi fada akan abinda nayi,Ummi kiyi hakuri ba fada ku zauna lafiya kamar yanda na sani na dauki laifi,zanji da komai kuyi Hakuri na dauki kaddara magana ta Kare ba abin damuwa bane,Papa yace bani number da ya baki,Hamida ta dakko number tace gata Tsautsayi ne Papa wallahi Yaya kyakyawa ba fan Iska bane Kawai tattaba Ni ya Fara na Fara Jin dadi daga Nan ya as min Abu.. Papa ne ya make Mata Baki tayi shuru,Ummi Tace kaji da kunnenka fitsarar da take iya fada ku karke na barku Kai da ita Ummi ma ta fada dakinta tabar Papa da Hamida suna kokarin kiran number Hamida tana cewa nasan kana so na Papa ka yarda dani zaka yarda da zance na wallahi sau Daya mukayi,shima cewa yayi Ina da Dadi...Papa ya sake bige Mata Baki Amma bata hakura ba Tace Naga duwawunsa ma fari tasssssss Papa tana dariya,yace Zan tattakaki ,sannan tayi Shuru.

Lokacin Basma an fito Palo ana kallo Kamar gidan ubanta ko kunya kullum ana gidan Saurayi Dan Kawai ana da dangantakar da abota da maman saurayi,waya tana Ringing ta Mike ta daga yace hello da iyayi,Ai Kuwa Hamida Tace aloo...aloo...Yaya kyakyawa nice Hamida ta kauyen Hamdala dake Adamawa samu ciki,cikin gaske sabo da abin Nan da ka min a hotel...aloooo Yaya kyakyawa Ina da cikinka tana fada tana wani Jin Dadi tana farin ciki taci gaba Ina da cikinka na wata hudu abin Nan daka min a hotel to ciki ya shiga na samu cikinka na gaske gashi danka Yana ta motsi yace a gaisheka...Basma tasan sunan garin da yaje aiki tabbas wannan ba karya sai ta sandare a Nan.

Papa ne ya kwace wayar yace nine Baban Hamida na kauyen Hamdala Adamawa ki fadawa dan uwanki 'yata tana da cikinsa ki isar Masa da sako,Basma sakin wayar tayi jiki na rawa hawaye na bin fuskarta mami tazo ta sameta,Tace lafiya? Nan Basma tana uban kuka ta zayyanewa Mimi komai itama Mimi sai kuka,Affa na shigowa Mimi ta sanar Masa komai.

Yace bari a Kira Nabeel Affa ko a jikinsa, Nabeel Yana Office bai San me ake ba ya dawo yayi parking ya shigo Basma ba Hakuri Nan take tarbeshi tana kuka Tace mayaudari azzalumi,mazinaci to ka sani Hamida ta kauyen Hamdala Adamawa tana Nan da cikinka na wata hudu,azzalumi macuci,mayaudari,mazinaci,bani ba Kai na fasa aurenka,Shima Nabeel Yana ji ya tabbatar akwai matsala hankalinsa ya tashi karya ta kare palon ya Koma ya samu Mimi Na sheka Kuka,Affa yayi tagumi.

A gabansu ya durkusa Mimi tace kayi mamaki ne marar tarbiyya, yanzu tarbiyyar kenan duk addinin naka to sun bugo waya,Affa ya dagawa Mimi hannu tare da cewa dakata,Nabeel ya Kira sunansa ya amsa a hankali yace tambaya Zan maka tsakani da Allah fyade kayi ma yarinya ko Kuwa dama itama tanso kuka aikata? Nabeel cike da kunya yace ba fyade bane tana so,Affa ya saki ajiyar zuciya tare da furta Alhmdllh wannan to da love za a kirashi,mu a matsayin mu na masu ilimi Love da ace fyade kayi da an samu matsala amma tunda tana so ya Zama love yaro ya Zama jikina,Kuma Ina sonsa.

Mimi tace haba Affan Fadila sai kace ba musulmi ba,yaro ya aikata laifi Babba kace love ne, Affaa yace sai ya shirya Aurenta in ta Haihu,Kuma zamu dakkota a gobe Matukar kayi aure a gidanka zata zauna har sai ta Haihu ka aureta muma baza ta zauna a gabanmu ba sabo da gidana na mutane ne akwai tonon asiri a gidan aurenka zata zauna da ku tana haihuwa dole ka aureta.

Nabeel ya zaro Ido hankalinsa ya tashi yace Ni gaskiya bazan iya auren matar da bana so ba,gata Yar Kauye,Bata waye ba,gaja da ita,Kuma ga rashin ilimi,kasan da hakan ka kwanta da ita ka Mata ciki,ai tun kafin ka yara da ita ya kamata ka tuna wannan Affa ya furta,karyar banza yake cewar Mimi kasan da Haka ka kulata algungumi,Ni dai Dan Allah a dakkota na yarda ta Haihu amma babu batun aure idan ta Haihu sai ta samu Wanda take so ta aura,Nima ba Sona take ba,Affa yace tunda kace haka shike Nan zamuje da Kai a rufawa iyayenta asiri mu dakkota Amma wallahi baza ta zauna a Gaban mu ba sai dai ku zauna gida Daya da Kai da ita da Basma.

Basma tayi zuciya amma haka ya dinga bata hakuri har ta hakura zata aureshi a Hakasu zauna tare da Hamida kafin ta Haihu ta koma Gidan Affa,ranta Kuma ta kulle cin uban Hamida idan tazo.

Basma washe Gari ta koma garinsu,ranar Kuma Affa da Mimi sai Nabeel suka tafi dakko Hamida tunda sun Kira Papa sunyi magana sosai shima yaji badi baya son ya tozarta a Kauye.

Abin Mamaki Nabeel sai kace Bai San Hamida ba Haka ta fito sanye da katon Hijab har kasa ta tsuguna ta gyaida su ta zaci Nabeel ne na da tace Yaya kyakyawa Ina yini ka tafi ka barni tun Sanda kamin abin Nan ka tuna? Papa ne ya galla Mata harara sannan ya shigar da su Nabeel Palo aka sauke su da ruwa da abinci Hamida ta kawo musu tana rawar jiki sai Mimi da Affaa ta birge su yanda duk akan dansu take haka bayan abinda ya mata maimakon su ganta cikin damuwa sai Suka ga gidan ba Wanda ya nuna ko a Fuska sun dauki kaddara,Hamida kusa da Nabeel taje Yana Kan kujera ta zauna a saman hannun kujerarsa sabo da ta Saba da shi Su Affa suna magana da Papa da Ummi,Hamida tace Yaya kyakyawa cikinka ya girma Yaya kyakyawa in Bude kaji kamshin danka,Nabeel kunya ta sake rufe shi sai kunyatashi take zancen ma baya so na cikin amma ta dame shi da Iskanci a gaban Iyayensa.

Mami taga alamar Yarinyar tarbiyya ce na Uwa bata samu ba shi yasa ta Zama wata kamar bata da Kan gado,Nabeel ne ya harareta tayi Shuru Wai,Tace to nayi Shuru bari na baka labari na Bayan tafiyarka yo ba sai cikina ya dinga girma ba kullum kullum,nace a'a Mene Haka ciki ka koma Amma yaki ji girma yake kullum gashi in ta cinye abinci yo ba sai motsi ba naji Ana hargitsi da yamutsi a cikin kina,Su Suna jinta dariya ta basu tace yo Kuma abu yaci tura naji Kura na tashi Ana Kai ruwana Ana wata walankeluwa a ciki,sai aka koma sufa a suuuuuu sai daram dam dam,Nabeel dariya ta kamashi ya danne da kyar su Mimi sai dariya suke su Kam,Hamida Tace Wallahi sai na Fara bacci na me dadi sai a farkar dani naji Ana birgima da alkafira a ciki,Mimi tace to munji dakko kayanki mu tafi a can birni Zaki haihu,Dama Papa ya fada Mata komai Murna fal ranta,Papa yace Kar ta dauki komai a can za a siya Miki duk abinda kike so ai Kuwa tace to,taje ta canja sabon doguwar rigar Lace dinta da Papa ya dinka Mata a birni,dinkin buba ne bazai takura Mata ba sai ta sa hijab dinta har kasa ta fito Tace na shirya,Dama nayi wanka Papa ya fada min komai,Mimi tace bakya shafa ko powder kenan?Ummi yace wannan shashashar ce zata Yi ai bata taba ko shafa man lebe ba,wanka Kawai take tasa kaya,Sulaiman yace gayu ai ya ma Kare dama ba Yi take ba bare yanzu data Zama bazawarar dole,kiyi a hankali dai can birni ne,Sule sule Sulele yayiwa Sulaiman Waka tasan ya tsani ace Masa Sule shine take tsokanarsa,Har mota suka rakasu,Baya ta shiga Nabeel ma ya shiga baya gefenta Mimi tana gaba Suka dauki hanya,Nabeel yace yanzu a mota zamu koma gaskiya Ni jirgi zanbi,Papa yace mu a mota zamu dawo Muna tafiya Muna kallon Gari ko 'yata,Hamida tafi so tabi Nabeel amma ya daure Fuska sai Kawai Tace ae, airport suka sauke Nabeel yabi flight sure kuma Suka tafi a mota,Hamida sai labarin Kauye take basu tana kalle kalle a mota,tana ta Bawa su Affa Dariya.

Ko ya akayi tafiya sai an siya Mata abinci ciye ciye take a mota kafin suje Kaduna Nabeel ya koma gida har yayi wanka yaci abinci yana hutawa sai dare Suka Iso gida Hamida duk ta gigice tana kalle kalle,taga hadadden gida sai kallo bata taba ganin gida me kyau Haka ba sai yau,Nabeel Bai fito ba bacci ma yake abinsa.




Sharhi fans


AsmaBaffa
[6/28, 1:46 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮


5

Official

By
AsmaBaffa


Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM



Page naku ne

NO LOVE
THUWAIBATUL ASALAMIYYA
RUKYALY
SHAHRY
AYUSHER UMAR YARO
FATIMAMUHAMMADINUWA
MADAME LAMINE
AYEESHART
MMN MEENAT
MAMAN AHMAD
UMMU KHALEEL
SAFEEYAT
MAMAN YUSRAH




Hamida Tace kallo sai gobe da safe tana Shiga ciki ta daga Kai sama tana ta juye juye baki bude haka tayi sai da Mami ta jata Sama part dinsu tace kin fiye kallo muje kiyi wanka kici abinci ki huta.
Haka ta kaita wani bedroom tace wannan ne dakinki ta nuna Mata toilet a ciki tare da gwada Mata komai sannan ta barta ta tafi nata dakin,Wanka tayi ta maida kayan jikinta ta fito,Mami ce ta kawo Mata wasu Abaya har kala Uku sababbi tace cire kayan Nan kisa wannan sabuwa ce tsaraba nazo dasu naga zasu miki,karba tayi Tace na gode Allah ya saka,Ni Guda ukun ma sun isheni bana son wani Kaya a Bari sai na Haihu a siya min naci bikin suna da sababbi,Mami tace to tunda jaka kike bukata ai ba matsala,Yar Aiki tasa ta kaiwa Hamida abinci har daki,Hamida ta kalli Yar aikin tace ke iceko Kun rage min abinci cikin dare nakan tashi cin abinci,me aiki tayi Dariya Tace akwai a flask Mimi tace a ajiye miki tace yawwa ta zauna ta fara dura abinci ta cinye tas.

Ta fito tace bazan lamunci wannan dan plate ba ke me Aiki ta kwala Kira Me Aiki ta fito yace Wai ya sunanki ne? Matar tace Asabe,Hamida Tace Sannu Asabetutuwayye, Asabe tayi Dariya sabo matashiyar budurwa ce,Hamida tace Karo min abinci Yar Asaballiye ,Asabe ta sake shako Mata plate,a Palo ta zauna tv nayi tana kallo tana ci ta zauna a kasa ta Mike kafafu kwanon a tsakiyar cinyarta tana ci,Nabeel ne ya dauro Alwala zai fita Sallar Isha Hamida ta kalle shi yanda ya zuba kyau cikin dark blue jallabiya kamshi na tashi,Bai ko San da zamanta ba ya sakko kasa,Hamida tace Yaya kyakyawa yaushe Zan Fara zuwa awo kaga ya kamata musan me zamu Haifa a fara siyayyar kayan yara Kuma Dan Allah ka siyo Masa gado me lilo,ita ko kunyar cikin shege bata ji sai kace wacce ta girma a kudu garin arna,wato son cikin ma take haka ya furta a ransa ko kallonta baiyi ba ya bar palon.

Hamida ta turo lips gaba tana gama cin abinci jaririn cikinta ya hau motsi tace jaba dan babansa ka dinga tausaya min kaji,yaro Yana motsi abu ya ishi Hamida haushi taji da masifa ta shafa cikin Tace wanne irin Iskanci ne wannan Dan wulakanci da rashin mutunci sai ka dinga hanani sakewa kaci Babanka Yaya kyakyawa, nace ubanka Yaya Kyakyawa,Yaro Yana ta motsi yaki ji,Nabeel ya shigo Palo yaji tace Kai Dan maye dan giya dole kayi ai giya muka Sha aka sameka dole ka dinga tambele na gane ka bugu da giya shi yasa,to dan uwarka Ni Hamida makwalwa Daya na Sha Babanka shine yasha cikin cup ta Nan ma gado tambele da maye.

Wani zunkuli taji ta saki Kara tace wannan shine hukuncin Allah ya sauka a kaina fushin Allah ne ya jarabceni da yaro Dan Giya ba komai Allah na tuba,sai da Nabeel ya hama Jin haukar Hamida ta bashi Dariya sai gashi ya shigo Fuska ba Rahma ya zauna a kujera shima, tana sani tace yawwa Alhmdllh ga babanka ya shigo Yaya kyakyawa ta Kwabe Fuska zata Masa kuka tace wallahi giyar da Muka Sha tabi jinin yaron Nan tambele yake Kawai Yana tayi Marisa a ciki na,Tayi Marisa ta Sha Kafso Kawai yake, dariyarsa ya danne shima haka Kawai yaji Yana son dansa,yace tashi ki dan jijjiga shi,Mami ta fito kenan taji me Nabeel yace jijjiga yaro a ciki lallai Nabeel,Mami labewa tayi taji yace Yi Masa Waka,Hamida ta fara Dan tsalle tana baaaabanka Yaya kyakyawa yaci Dadi yaci bala'i,Nayi cikin shege a garinmu nayi cikin shege... a garinmu tana Waka harda tafi,Mimi yau ta tabbata wannan Yarinyar bata da hankali,Nabeel ta kalla tace taso muyi Enter Yaya,Harara ya galla Mata ko a jikinta tace Yaya ka tuna abin Nan da mukayi a hotel Ina cewa zafi tunda na samu ciki shi nake so a Kara min Kullum da kyar nake bacci,Ai zumbur Nabeel ya Mike ya rufe Ido da bala'i yace idan ke dabba ce jahila Ni Ina da hankali da dinma tsautsayi ne na tuba ga Allah,sannan baki da ajin da Zan saurareki dakikiya jahila bagidajiya,Kinga Nayi kala Dake ko na Dace da ke? To na kusa aure ki sani ba Ni ba ke karki sake min magana in ba dole ba, Fasika marar tarbiyya,Hamida bata taba sanin haka yake ba sai yau sai tsoronsa ya shigeta Amma sabo da Bata ji kallonsa tayi ta Masa signa da Ido tana kashe Masa Ido Daya tare da daga Masa gira.

Palon ya Bari fuuuu cikin Fushi Mimi taji Dadi sabo da bata son komai ya sake faruwa tunda taga Hamida bata da hankali tabbas ba lafiyayya bace kwakwalwarta da motsi Tace Allah yasa ki Haihu sai mu maida ke garinku ki karata a fili Mimi Fitowa tayi ta ga alamar taji zafin kalaman Yaya kyakyawa tace je ki kwanta,Ranar Hamida bata Yi baccin kirki ba tana tuna maganganun Nabeel da ya yaba mata,tunda take a rayuwa yau ne karon farko da aka yaba Mata magana taji zafi har ta kasa baccin kirki.

Washe gari Mimi tace kaje ka Kai Hamida awo ya kamata ta fara ganin likita,to Kawai yace zai fita Office ya dau mayen wanka Hamida ta kalle shi kadan a ranta tace ashe acan ba Wani gayu yake ba a Nan yake gayun,Hamida tasha abayarta ta tsala kyau sai ciki ya girma ya fito das dashi,Ko data gaisa shi ko amsawa baiyi ba Haka ta fuske da fara'a Tace muje kayi kyau,wani uban Tsaki ya buga Mata yayi waje tabi bayansa tana Siiiiiiiii minti Daya gaye siii...sii....Yana juyowa ya kwasheta da Mari ya nunata da yatsa yace wallahi duk ranar da kika sake kulani sai na kasheki na fada Miki last warning masu Aiki suna kallo,Yana zuwa mota ya Bude ya ebo kudi ya Watso Mata dauki ki tafi a kafa Kika fadawa Mimi bani na kaiki ba sai na yankaki, a kafa Zaki tafi har sai kinfita daga estate dinnan sannan kije ki Sami taxi stupid girl ya shiga labebiyar motarsa ya Kara gaba,Hamida tayi Dariya ta kwashi kudin ta samu me gadi yace dan Allah muje ka rakani asibiti Zan fara ganin likita.

Me gadi Musa ya bita Suka tafi babu Wanda yasan zancen a gidan sai iya su Mimi amma Hamida suna tafiya da Musa dake matashi ne suna ta Hira a kafa tace Kai Musa cikin shege aka min fa a kauyen mu Musa ya kwala ihu tare da dora Hannu a Kai yace Ashe ke Yar Iska Ce Yar uwar su Mimi ce dole a kawo ki birni Ashe abin kunya Kika tafka yanzu sai Kika bude Masa cinyoyi wanne shegen ne wannan? Tace Yaya Kyakyawa ne,Oganku Nabeel,Musa ya sake kurma ihu yace shege karamin Alhaji ashe Kawai harka yake bajewa,yanzu ke in Banda shashasha ce sai ki bude Masa ai gashi Nan ya cuceki kece a ruwa Musa ya dinga tir Yana tsinewa Nabeel,yace nima da Zaki bani sai na Dan wake.
Da sauri ta daure Fuska Tace koma gida bana so ka rakani zanje da kaina,Ashe kaima Dan iskan ne wallahi Zan durawa iyayenka zagi koma gida ka barni,Musa ya tsaya cak ita Kuwa turtsi turtsi taci gaba da tafiya ga Rana ga nisa ta hada zufa Musa yace to kardai ki hadu da wani Yaya kyakyawan ya Kara Miki ciki na biyu ki dawo Mana da double ciki,Tace sai dai ayiwa uwarka ba dai Ni ba,Musa Yana ji ta fara danno Masa zagi ya juya sai gida ita Kuma da tambaya take har asibitin Gomnati aka Mata duk abinda ya Dace ta dawo gida duk ta jikata haka napep ya ajiyeta ta bashi kudi ta dawo da takardunta da magunguna,Mami ganin da Nabeel Suka fita ko duba takardun bata Yi ba tace ya cikin naki tace komai lafiya ga magunguna an bani sunce duk laraba na dinga zuwa sai Nan gaba zayi min sauran test,Mimi tace a kula da Shan magani a ka'ida Tace to,Sai da taci abinci ta watsa ruwa sannan ta fita kallon gidan tana jinjina kyan gidan.

Tunda Haka ta faru,Basma ta raina Nabeel Affa Yana Office din Nabeel suna tattaunawa sai ga Basma fuuuu ta Fado a gaban Affa har office taje taci kwalar Nabeel tace saura idan munyi aure ka dinga zagawa wajen karuwarka a boye ta zuba Masa maruka biyu tana zaginsa,Shi kuma sabo da yasan yayi laifi sai ya kyaleta.

Affa yace baka haifu ba Lele mace tun baka aure ta ba tana cin kwalarka ta mareka,Nan take Affa yace wallahi baza ka aure ta ba na soke komai gwara ka koma wajen Basman kawunka Yar uwarka ta jini wacce zamu Haka mu rufe,Basma tace tafi nono fari ta kalli Nabeel tare da nuna shi da yatsa tace you fool sai na dau fansa zaka gani daga Haka ta juya fuu tayi waje..

Affa takaici yasa Kawai a daurawa Nabeel aure da Basma Yar dan uwansa tunda an gama kera Masa gida,Haka Affa ya sake rushe auren waccen Basma ya dawo da Basma Yar dan Uwa,da Yan Uwansa aka shirya komai,Suka rufe zance ko matansu ba Wanda Suka fadawa Haka Basma ta dinga murna dama tana son Dan uwanta duk da an fada Mata a sirri tare zasu tare da Hamida,Suka ce kaddara ce tunda tana sonsa tayi Hakuri ayi auren tunda an Gama komai,Haka aka daurawa Nabeel aure ba shiri Wanda shi Kansa a cikin nishadi yake zai auri Yar uwarsa dama suna shiri da Basma sabo da shi gani yake ai farko duk soyayya take da Basma Yar uwarsa da daya Basman,Dan ya rasa Daya ciki ba abinda ya dame shi

Ana daura aure aka Kai Masa Amarya Affa yace tsuntsun da Yaja ruwa shi ruwa Kan duka Nan da sati Daya za a kawo Hamida ta zauna a gidanka Kai da ka Mata ciki ku zauna tare ka kula da Yar mutane har ta haihu,Bashi da zabi yasan yayi kuskure haka yayi Shuru shi yaji Dadi ma da aka ce ba sai ya auri Hamida ba.
Basma tana mararin Ango shima Haka Bayan sun gabatar da Nafeela Suka ci abinci sannan sukayi Shirin bacci Amarya ansha kyau cikin kayan bacci gaba Daya Nabeel baya Jin wani sha'awar matarsa ya rasa dalili,Sam Sam baida feeling a kanta Haka ya tsinci Kansa,Haka abar tasa ma taki tashi tayi kwanciyarta lakaf abinta,mamaki da tsoro ya kamashi, Haka yayi wayo yace hutu zasuyi su baza suyi gaggawa ba Romancing Basma yayi sosai sai da ta gamsu Amma shi komai baiji na Sha'awa ba,abinda Ya daurewa Basma Kai kenan amma dake budurwa ce sai ta hakura,Haka suka kwashe sati guda sai dai romancing ya kasa komai Nan ya tabbatar baida lafiya,Basma ya fadawa gaskiya tace bari su Fara Neman magani yace to,Basma tace maybe Yar kauyen Nan ce Suka maka asiri,Nabeel yace oho Ni ban sani ba.

Sati na cika Mimi da Affa da kansu Suka kawo Hamida gidan Nabeel sai Murna take ko banza zata dinga ganin abin sonta, Suka yiwa Basma da Nabeel Nasiha Haka Hamida ma,Basma sai kuka take Nabeel Yana Bata Hakuri yace karki damu na dan lokaci ne tana haihuwa zata koma garinsu ba sonta nake ba ke nake so haka ya lallaba Basma tace ba komai ai tana da amfani a gidan Nan ta Zama Yar Aiki na ba ruwana da cikin dake jikinta,Nabeel a ransa bai so Haka ba Amma ya zaiyi da matarsa baya son rabuwa da ita akan wata banza Hamida.

Hamida tana jinsu ita ko a gyalenta Dariya ma take ta kalli Basma yanda taci kwalliya ta zuba kyau tana kamshi da gudu ta fada jikin Basma bayan su Mimi sun tafi,Ai Basma wani ihu da tsalle ta buga tare da komawa gefe tace oh my God Baby kana gani wannan kazamar ta taba min jiki,Ni ajikinki ce Dan uwarki nayi Kama da sa'ar ubanki,Nabeel yace ke me yasa jahila ce kalleki kazama ki hada jiki da matata kalleta fa,Hamida ta washe Baki Tace Naga tayi kyau ne gata kyakyawa ta H
hadu shi yasa na rungumeta kina da kyau Aunty kin iya wanka,wata uwar tsawa ya daka Mata ke dalla rufe Mana baki,Basma tace Kinga kazama shiga kitchen gashi can akwai wanke wanke ki fara,in kin Gama kizo ki share ko Ina ki goge maza Kuma ki tabbatar yayi kyau,da Murna tana tsalle Hamida ta fada kitchen ta fara abinda akace dama ta iya tana Yi a gidan

Please Login or Register in order to submit comment