Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zirga zirga Yana binta da Ido ta fito tace na hada ruwan zafin me jego,kallonta yayi ya murmusa Kawai ya wuce toilet,ganin Ana ta cin abinci a gidan ta zuba tuwon a flask ta kawowa Mimi har dakinta ta iske Yan Uwan Mimi Mata makil a dakin ta gaishe su sannan ta Kira Mimi gefe ta bata harda rada Mata tuwo nayi karki bari a cinye Miki suje suci shinkafa ta kullum kullum,Mimi tace to Kai dakin Affa,Hamida ta kai dakin Affa ba kowa duk suna kofar gida a Nan ta ajiye ta koma dakin Nabeel taga har ya shirya cikin brown jallabiyya ya dauki gajeren wando zai saka Wai sai yaje wajen zaman makoki , Hamida tasan a dokokin likita Banda sa wando,tace karka sa wallahi baza ka bi doka ba dan Allah karka sa,tsayawa yayi Yana kallonta ta Masa kyau bai ma San kyanta ya Kai haka ba,yace sai na sa tunda Ahmad kike so bata da amfani a wajena,Hamida cikin dakewa tace please Yaya karka karya doka ka Mata Addua a daki Dan Allah ba sai kaje ba,nasan zuwa zaka Yi,duk duniya ko Mimi bata gane abinda ke damunsa sai Hamida tun kafin ta fara hankali ko kallo ya Mata tasan me yake nufi Yana tunani ta kwace wandon ta maida ma'ajiya tace Jego fa kake zata Yi waje ta tsinci muryarsa yace abincin fa, dawowa tayi ta fara serving dinsa yace harda yin wani tuwo? Me jego ai sai da tuwo ta furta ba tare da ta kalle shi ba muryarsa taji yace dan Allah karki auri Ahmad,mikewa tayi ta fice abinta ya bita da kallo Kawai.

Tana fita wanka taje tayi ta canja kaya tayi Sallar Isha sannan ta take cikinta da shinkafa da Miya harda salat ta sake sabon hijab ta fito cikin Yan makoki a palo,tayi jugum tana jan carbi, ana ta fadar halayen Basma na kirki Hamida tana cikin su Ihsan ka rantse dama a gidansu ta taso,Fatima kanwar Basma ce ta Dora hannunta a cinyar Hamida tace naji su Daddy suna cewa idan mutuwa ta lafa ranar arba'in din Basma za a daurawa Nabeel aure da Ihsan ko Ni wai,Hamida bata San Sanda tace Innalillahi wa inna ilayhirrajun ba,Mene ne Yar uwa? Hamida ta wayance tace Basma ce ke Fado min sai naji gabana ya yanke ya fadi,wata tsohuwa dake kusa da su tace Yar Nan haka mutuwa take mutum Yana Fado ma zaka ji gabanka ya Fadi sai hakuri duk mu na hakane kowa jiranta yakeyi,Hamida kuka ya kwace Mata za a aure Mata Lelenta kuka na sosai takeyi ana ta bata Hakuri ana yar Nan haka mutuwa take sai hakuri,Hamida Sam bata mutuwa take ba ta Lele takeyi tashi tayi ta koma bedroom dinta,Yan Uwan Basma dattijai Suka ce wannan Yarinya ta shaku da wannan baiwar Allah.

Hamida saman bed dinta ta fada tana kuka sai ga Kiran Doctor Ahmad tsaki taja sannan ta daga yace ya Hakuri? Tace Alhmdllh,Allah yasa ba Murna kike ba ta mutu ta bar Miki mijinta,Takaici ya Kama Hamida dama kadan take jira tace na fasa aurenka kai zo ka karbi kudin aurenka wallahi bazan aureka ba ko sama da kasa zata hade ka turo a karbar ma kudinka,Hakuri ya fara bawa Hamida tace bazan hakura ba na gaji da zarginka kazo ka karbi kudinka wallahi ko na rotse ma kai banza Jaki,Dr yana gadara shi llikita ne yace da ilimi na da wayewata da kudina babu Yar da zata zageni na aureta ko wacece wallahi na barki har abada Ni da Zan rufa Miki asiri fa zaki zageni, gobe zanzo da kaina na karbi kudina,Hamida waya takashe tace maza zo ka karba dan me bakar takashi na huta da Kaya.

Washe gari Ahmad ba mutunci ba kunya ana zaman makoki Affa ya zaci gaisuwa ma yazo amma ba Wanda ya gaisar Yana zuwa yace kudin aure na za a bani dana kawo na fasa yarinya bata da tarbiyya Wanda ya Mata cikin shege yaje ya aureta,su Papa da Sulaiman sunzo suna wajen,Ummi tana ciki wajen Mimi,Affa ya mike tare da rike hannun Ahmad yace muje gefe Ahmad ya fisge hannunsa ya fatalar da hannun Affa gefe yace dalla sakeni cikin dubban mutane yace kaje ka aurawa danka Wanda ya Mata cikin shege ta Haihu a bani kudina na fasa,mutane aka fara gunaguni,Alhaji Ubaid yayan Affa shi ya mike tare da kwashe Ahmad da mahaukacin mari Ahmad ya daga hannu zai rama Sulaiman ya tashi ya Masa wani mugun naushi a Fuska Nan take jini ta hanci ta bakin Ahmad,Su Anwar yayan Kanin Affa Dana yayan Affa Suka Mike zaratan maza sunkai su goma Suka yiwa Ahmad laga laga sai da kyar aka kwace shi,Muhseen shi ya zaro kudi masu yawa yace Nawa ne kudin Affa? Affa yace dubu hamsim ne,Muhseen yace kacal wannan ai kudin Yar budurwar akuya ce,Nan ya irgo kudi ya sawa Ahmad a Aljihu tare da tankada shi gaba gaba Daya family din tsabar hadin Kai Shuru sukayi Suka fuske Suka nuna Basu San ma zancen ba aka ci gaba da zaman makoki.

A Haka sai da labari ya Isa wajen matan cikin gida Mata Basu San Kan zancen ba Suka dinga tsinewa Ahmad,Nabeel zai je dakin Affa kenan ya tsinci zance Nan take farin ciki da murna Suka cika Masa zuciya Kamar ba matarsa ce ta mutu ba,Wanda Suka ganshi ranar cewa sukayi yaron Nan da tawakali yake,yaro yayi tawakali.

Anwar duk kwanakin da suke a hannun Hamida suke karbar Abinci duk sun santa ba Wanda bai santa ba,dama Anwar shi ya Santa yayi mamakin ganin wayewarta da hankalinta sai yaji kaunarta tana shigarsa shi Kam ya samu matar aure,Kowa in ya shigo sai dai kaji ana Ina Hamida bata Zama sai hidimar dangi takeyi dama gata ba kuya ai ta sata girke girke tayi suna ta Zama wata star Mata da maza Hamida Kawai,Muhseen ne shima fa yaji kaunar Hamida tana Neman kamashi birge shi take ga abin dariya,Ihsan ya Nemo yace Ina Hamida kice ta dafa min Indomie da kwai,Ihsan tace to ta Fara Neman Hamida,Yayinda Hamida ke dakin Nabeel tana hada Masa tea,Ihsan dakin tayi knocking, Nabeel yace come in, ta shiga tace Sannu Yaya Nabeel tace Hamida kizo inji Muhseen ki dafa Masa indomie,mugun tsoron Nabeel suke sabo da baya Wasa da kowa baya sabgar kowa,muryarsa taji yace get out baza ta dafa ba kowa Hamida, a girki zata Kare da aiki ku dama baku iya samun waje ba,Ihsan ta fice ba shiri,Hamida ta Mike zata fita yace wallahi kina fita zaki ga true color dina koma ki zauna yau ba inda Zaki,shike Nan kowa ya saki aiki ga masu aiki Nan,Shuru Hamida tayi ta dauki tea din ta Mika Masa ta koma gefe ta kwanta a kasan tiles,mikewa yayi ya koma saman resting chair yace hau bed din ki kwanta Kuma kiyi bacci,Fuska ta kwabe yace ba abinda Zan Miki Ni kin San Banda lafiya,tunawa tayi sai ta haura saman bed din ta kwanta ba Bata lokaci bacci ya kwashe ta,Shi Kuwa Yana gama Shan tea din ya fice tare da sa key ta waje ya kulleta gam ya koma dakin Affa ya kwanta a saman bed.





Sharhi pls




AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮

10-15


Official
By
AsmaBaffa


Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM



Page naku ne Yan kirki

Safiyya Nabebe
Ummulkhair
Maman Alamin
Habeebah Heebat
Maryam T Baliya
Maryam






Ba Wanda bai nemi Hamida ba an rasa Ina take,dare har la'ar tayi Sallah Kawai tayi ta koma baccinta sai magrib ta tashi ta nufi kofa tare da murda handle taji gam gam,komawa tayi ciki tayi Alwala tare da yin Sallar magriba har Isha tayi ta mike tayi lokacin Anwar Yana so ya ganta su danyi Hira ya samu ya yada Manufa amma Nabeel ya boyeta, Muhseen ma ya nemeta Shuru ba a ganta ba har sai da sukayi bacci 11pm sannan Nabeel yasa key tare da Bude dakinsa tana gani ya bude tayi sauri zata fita ya riko hannunta ta fisge tare da karawa gaba.

Washe gari sadakar Uku Allah yasa duk mutane sun watse sai iya dangi, matasa su Anwar suna zaune Kawai
Sai ga Ahmad tare da kannensa su biyar matasa sun tsaya akan mutane yace zuwa nayi a bani dukkan kayan sawar da na siya Mata,Hamida sai ranar taji me ya faru tsaf ,wata ce ta shigo tace gashi can mutumin jiya ya dawo za ayi fada again, kofar gidan Hamida ta fito ta kalli Dr Ahmad,

Mata sun fita suna ta kallo,Ahmad Yana ganin Hamida yace yawwa rigar ma dake jikinki tawa ce a hado min kayan Dana siya Miki akwai dubu biyar biyar dana baki sau hudu,Banda su ice cream da snacks duk Ina son kudina,Hamida ganin ba wasu mutane duk su Affa basa wajen ma Sai yaransu,tace zakkar Soyayya ka fitar nayi tunanin ma cikon kudin ka kawo min ai baka gama biyana ba Nike binka bashi ma,ba Kaine a zuciyata ba in ba kirana kayi ba ko tunawa da Kai banayi,kudi da Kaya Kuma Allah ne ya rubuta Kaine zaka siya min Kuma ka bani kudi Nasha Alawa,kudinka Alawa ma Nasha da su kaga basu da Albarka ya zaka Yi Allah ya rubuta.

Ahmad yace tonon asiri ai ya Kare Miki ke da kikai cikin shege,Hamida tace danayi cikin ubanka ne ya min ta daga hannu biyu ta zageshi tace sharri zaka min sabo da zaka fasa aure kace nayi ciki Kuma tunda ka min kazafi sai na dakko ma Yan Sanda sai munyi Sharia da kai kayi min kazafin ciki, Hamida a ranta tace yo ko banza ai na kafa tarihi a dangina nice na Fara cikin shege Kuma banji kunya ba,? ke malama a hado min kayana,Hamida ta girgiza kai tace bani da lokacin ka dan tukunyar babarka kullum ka dakko bakar Fuska kazo duk a banza Zan fito.
mu a jikin maza Allah ke fitar Mana da arzikinmu Kuma Allah ya baka har da kaso na a jikinka dole ka bani sabo ba yanda za kayi rabona na ci hakkina nane Allah ya baka ajiya,shawarmar ma na zaci wani dan faten yakuwa ne haka,da nasan ba fate bane Zan bika ba ai ni na zaci faten yakuwa ne, ficika baza a baka ba iya kudin aure ne an baka Kuma kayanka wallah akan na baka gwara na yayyafa musu fetir na kone su.

wannan har wani kudi ka kashe,ni Murmushi million Nawa nayi har ce min kake na iya murmushi idan nayi sai kace Murmushi na Kai kosar da Kai yake kaji ba sai kaci abinci ba karka dauka ban San karya kake ba kana tafiya zaka narki abinci.

Lele da ace ya warke da tuni ba sai buzunka ba,Kuma wallahi kana magana Zan sa ko wacce mace a gidan makokin Nan sai ta lakace ma tabilallen hancinka,Su Anwar suna ta dariya Hamida tayi Masa tas Kuma yayi shuru,kannensa matasan samari sunga Yan hutu masu kudi Shuru sukayi,Ahmad yace kuyi Mata dukan kudina suka ce mudai Yaya ba ruwanmu wallahi baza ka ja Mana ba daga Haka sukayi tafiyarsu,Muhseen ne ya mike ganin haka Ahmad ya fada motarsa yace akwai magana a gaba sai na hanaki zaman lafiya a duniya ai Zan ganki a hanya Watarana,Nabeel ne ya fito sanye da jallabiyarsa dark blue,ya kalli Ahmad yace Indai haka kace to ka tanadi likkafaninka,Muhseen kafin kyafta ido ya sace Masa tayar mota da wani karfe,Anwar da Zain Suka fisgo Ahmad daga mota sai ya Shiga basu Hakuri,Muhseen dama dan kwaya ne Kamar Allah ya aikoshi haka ya dinga jibgar Ahmad sai guduwa yayi a million ya Sha kwana Ya bar motar a Nan.

Anwar yace wannan anyi jahili marar mutunci sai kace jahilin Kauye,Nabeel yace Wai doctor ne,please karku sake wani ambatar doctor jahili dai cewar Anwar.

Nabeel ne ya nufi cikin dangi zai zauna a saman carpet din da suke,Hamida tasan ba short a ciki sabo da lalurar, tace Yaya Nabeel matsowa yayi da kunnensa saitin bakinta yace fadi a hankali ta rada masa Banda wawan Zama mutane na sintiri a layin Nan ato,Murmushi yayi yace tafi gida kinzo kinwa your love masifa Ahmad dinki, gida tayi tafiyarta,Anwar ya kalli Muhseen yace kai gaskiya sauri zanyi na fadawa Yarinyar Nan Ina sonta,Muhseen takaicin Anwar ya kamashi yace ku duk bakuwa idan kuka ganta sai kunce Kuna so to ance an Mata miji,Anwar yace ko kaima kana ciki ne? Zain yace gaskiya beb din ta hadu Kan bala'i komai Excellent gata social ba ruwanta da wani Jin kai,Anwar yace Ina kaunar hancinta da kalar lips dinta wow,gata doguwa skin dinta me Jan hankali tana da Fara fara amma me dan duhu duhu haka,Anwar yace sai kaga gashinta ma,Nabeel hade rai yayi Kamar yau ance Mimi ta mutu tunda yazo wajen yaki magana hirar duniya Bai ce musu kala ba karshe ma tashi yayi ya koma cikin gida.

Bayan an sallami baki Saura iya family din su Affa Yan Mata da maza da dare sun cika palon damkam wasu a kasa wasu a saman kujera suna ta hira Hamida tana ciki amma bata sa musu baki a hirarsu sai dai duk Wanda yayi magana ta kalleshi,Nabeel Yana dining shi kadai Yana cin abinci,Mimi da Affa suna bedroom.

Sale ne yayi sallama tare da neman izini ya shigo palon daga kofa yace ance ana sallama da Shakira,Kallon kallo aka fara wace Shakira Kuma a dangi ba wacce ta mike sai aka ga Hamida ta mike tace Uncle Sale kace Ina zuwa aka kwashe da dariya gaba daya palon har Nabeel ya dara yaushe ta koma Shakira basu da labari.
Ita kanta Hamida sai data ji kunya,Anwar yace Shakira a Ina aka samo sunan? Hamida tace Nick name nayi sab...kafin ta rufe baki Nabeel yace sunan arniya ce fa mawakiya,Hamida tace ni Ina son abina Malam Shehu ne yace idan na waigo Zan kalle shi sai yaga kamar Shakira,su Ihsan dariya harda jefar da waya,Wanda yake kiranki fa? Nabeel ya tambaya tace me voters card ne Wanda Affa yace naje nayi tana da amfani shine yazo kawo min,tana fada ta fice ta tafi karbowa Yana kofar gida a Kan lifan

Suna gaisawa ya bata voters card ta dawo gida,tana shigowa Nabeel yace mu gani,Mika Masa tayi yaga ansa Shakira Kabir Tahir,Kai ya dafe yace Hamida Oh my God yanzu dan kanki ya kwance Shakira Kika je Kika sa? Kowa ya fara dariya,Yace dole sai an canja wata,Hamida tace Ni Allah bana so ni na canja suna na tashi daga Hamida ta furta da shagwaba,Nabeel a ransa yace me hali baya fasawa dama yasan Hamida kafin ta dawo normal sai ta shiga school dole yace dole na kaita school a week din Nan.

Hannunta ya rike ya jata palon sama ya bar su Anwar suna ta dariya,paper ya dauka ya Rubuta mata sunan bank U.B.A yace me ake cewa wannan a turanci yanda ake ABCD kin tuna? tace ae yace to fada naji karanta maza,Hamida ta karbi takardar ta gyara zamanta a kujera harda harde kafa tana karkada kafafu ta karanta abinta da Hausa tace Uba Kamar baban mutum Uba amma ba Ubana ba gaskiya wannan ai wayon ka zagi banana ne Yana kabari Kuma ta kwabe fuska,harara ya watsa mata yace bani school Zan kaiki shehu baya aikinsa Kuma wlh a primary Zan saki cikin yara,Hamida ta fashe da kuka yanda bata son makaranta za a maidata baya tace Allah Zan dage Shehu ne Ni kwalliya yake koya min,Nabeel yace ai dama wannan ba malami bane korarsa zanyi na kaiki school suyi ta zaneki a can.

Hamida tace ai ya bani assignment na mathematics bari na kawo ka koya min Dan iskan maths din Nan ne me Find X wlh na gaji Ni bana iya nemota,Nabeel ma anyi rashin sa'a a duniya bai iya maths ba a school da kyar yake tsallakewa,sai yayiwa Hamida wayo yace tab Nemo x ai sai anje Taraba Hamida tace Allah dama acan take? Yace a school can ake kaimu a motar makaranta idan Muka ganta a cikin yayanta sai ta ba kowa daya shike Nan mun samo ta,Hamida tace dan Allah ka rakani,Ihsan tana da ita kije ta nemota ta miki assignment din dama yasan Ihsan ta bala'in iya maths, Hamida tace to gobe kafin su tafi zata min.

Hamida ta bar zancen Assignment ta Mike zata tafi
Yace ki zauna ki tayani hira tace a'a Ni dai bacci zanyi ,Kai ya jinjina yace Wai me yasa yanzu Kika tsaneni ne kin rainani fa? Hamida tace ka manta Sanda ka dinga wulakantani kana hantarata Kai da matarka ka mareni ka zageni duk sabo da kaga Kalar Dausayina bani da daraja sai yanzu gwara na auri Wanda banga Kalar tasa ba baiga tawa ba,ka je ka auri Virgin dinka ba ruwana,Nabeel yace haka Kika ce? tace ae ta juya tayi tafiyarta,tagumi yayi Kawai tare da furta ya Allah ka kawo min agaji Yarinyar Nan Bata San son da nake Mata ba tun farko Allah ka ganar da ita,Allah ka shiryi Pipi

Fitowa yayi ya ganta zaune kusa da Anwar da wayarsa tana tura film Wai zata kalla,Nabeel yaja kwafa ya wuce ciki shi duk ya matsu su tafi Abujansu ya huta,Har ya kwanta ya sake Fitowa ya leko palon yace wai bakusan ku kwanta bane dare yayi,Muhseen yace Kai Lele duk Nan fa Zain ne da mata kannenka mun girmeka amma sai wani Raina Mana hankali kake yi,Tsaki Nabeel yaja ya koma bedroom Hamida bata ma San me yake ba hankalinta na Kan waya amma tana jinsa,room din Mimi ya shiga ya iske ta tana gyara Kaya yace Mimi kice Hamida taje ta kwanta tana can tana sakin layi wajen su Anwar,Allah sarki Hamida bata yi surutun komai ba ma, Mimi tace me Hali baya fasawa sai tayi tunanin gaske ne tace naga ta fara hankali fa Kai wannan Yarinya Mimi ta sauka da sauri tace Hamida zo.

Hamida mikewa tayi tabi Mimi Sama,tana Shiga bedroom Mimi ta rufeta da fada Lele yana zaune Yana murna,Mimi tace Zaki je kiyi zancen Duwawun da kika Saba ne wallahi ki kiyaye Ni,Hamida tayi rau rau zata Yi kuka tace wallahi Allah bana fada tun yaushe na daina tun Sanda Kika ce na daina kula Yaya Nabeel na daina fadan komai Kuma Ina kiyayewa na gane gaskiya na gane ba mutunci na bane sai fa yau kadai Kuma daga Ni sai Nabeel na fada Kuma ban ambaci takashi ba wallahi Kawai dai nace Naga tasa yaga tawa Kuma ai shine Yace Yana s....Nabeel ne yayi sauri yace jeki Kawai duk ya hana aji karshen zancen Hamida sabo da Mimi Kar ta ji,tana Jin yayi Shuru taci gaba sai yace Yana so...da sauri ya dan bigi mudubin Mimi da Hannu ya saki Kara,Mimi tace maganinka kenan gashi Nan kayi famu,Hamida ta rufe bakinta da tafin Hannu sabo Dariya taci karfinta Wai yayi Famu kamar dan kaciya,Mimi ta kalleta tace fita ja'ira duk abin fitsara kina ciki kaima fita munafuki,Hamida tana sauka daga last steps ta juyo tana kallonsa shima Yana sakkowa a ranta tace sai na Rama,Tafi ta shiga Yi Masa tana wakar da akewa Yan kaciya a kauyensu Wai Lele takwa takwa....ah Lele takwa takwa...Yan Palo Suka kece da dariya kamar me,Nabeel shi kanshi da kyar ya shanye dariyar sabo da Kar ta Raina shi da yawa,fisgota yayi tare da murde hannunta ya kwace Wayarta ya wuce masallaci.

Washe gari da wuri duk Suka shirya Suka tafi har Anwar sun ga alama kamar Nabeel son Hamida yake shi yasa Suka hakura Kawai,gidan ya dawo sai iya su ya su Yan gidan sai Fadeela da aka kawota hutu,bayan komai ya lafa Nabeel ya samu Affa a room dinsa yace Affa ka canjawa Hamida teacher wlh in Banda kwalliya ba abinda yake koya Mata bata iya komai ba,Affa yace naga hakan nima Inshaallah gobe Zan kawo Mata wata Zainab babbar mace ce me hankali in yaso sai a sata a Islamiyya bana so ta shiga secondary ss3 bata San komai ba rainata student zasu yi a dinga wulakantata Kai kasan Yan makaranta,yace hakane kam yace yawwa kaima ka dinga dan koya Mata abubuwa,Nabeel ya sake cewa to amma Affa Ina son Nabeela dan Allah ka aura min ita,Affa yayi Murmushi yace bayan ka gama wulakantata Lele,dama Ina sonta Affa lokacin ban gane sonta nake ba tun farko,bazan baka ita ba kaje sai Zama yayi Zama ka Fara Mata gori wani dan abokina Zan bawa ita.

Nabeel sai yaji haushi yace Affa kafi son bare da ni? Affa yace kwarai tunda baka ganin darajarta ba ai gwara a bawa me hankali Kai ka hakura ka auri Yar uwarka Fatima ko Ihsan munyi magana da su Yaya mun yanke hukunci Hamida Wanda ta zaba zata aura,Nabeel yace Ni bana son su gaskiya da na auri Fatima ko wata gwara na Kare rayuwata a haka,Affa yace Kai ka sani kuma,Nabeel ya sake cewa please Affa,Affa yace karka dameni Lele tashi ka bani waje Hamida ko ta aure ka kana da tabbacin zaka Haihu sannan ma idan baka warke ba fa ya zakayi da Yar mutane wajen bukatar Aure? Nabeel yace Inshaallah ma Zan warke Nan da 5-6mnth Affa Ina da karfin jini,gwara Yar uwarka inda zaka samu rufin asiri,Nabeel yace ita Basma da aka aura min ita kalli fa abinda ta min Haba Affa,yace to dawo da daya Basma ka aura,Nabeel yace Ni duk me Suna Basma bana kaunarta yanzu, to tashi ka bani waje Allah ya hadaka da ta kirki amma ba Hamida ba.

Mikewa Kawai Nabeel yayi ya fice cikin bacin rai,Hamida bata San me akeyi ba karatunta take Yi sosai wajen sabuwar malamarta Aunty Zainab ta fahimci Hamida a hankali take bi da ita tana koya Mata har abubuwan rayuwa sannan tana zuwa Islamiyya sosai,kwana biyu taga Nabeel Sam Bai da walwala,kullum baya fara'a da sauransu Kamar yanda aka Saba,Sabgarta ma ya daina shiga kwata kwata,hakan yana damun Hamida sosai tayi zaton ko wata cutar ce kuma,tana so ta tambaye shi amma ba fuska.
Karatunta takeyi sosai ta nuna bata damu da shi ba amma a zahiri hankalinta na wajensa.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya zancen auren Nabeel ya kankama tabbas ranar arba'in din Basma za a aurawa Nabeel wata matar,Hamida sai ana gobe ta tsinci labarin,Kamar tayi hauka kasa daurewa Hamida tayi ta dauki biro da takarda ta Kira Shehu a waya tace mu hadu dan Allah a bayan gidan Affa,Shehu 5pm yace ta fito yazo,bayani tayiwa Shehu tace abinda yasa bazan rubuta wasikar da kaina ba nafi son rubutun kwari Wanda yafi Nawa kyau,Hamida ta shiga fadawa Shehu abinda zai rubuta a takardar har ya gama tace sa ayar tambaya a can,Shehu ya saka,Tace sa coma again,Shehu yace to ya saka ta karbi paper ta Masa godiya ta koma gida tana shigowa room dinta ta wuce ta saka a sabon envelope ta manne ta kaiwa Mimi tace gashi inji wani mutumi yace a bawa Affa,Mimi ta karba tace bai fada Miki sunansa ba tace ae yace shima aikoshi aka yi ya kawowa me gidan,Mimi tace to idan ya dawo Zan bashi Hamida tace to ta juya ta koma palo.

Kwanciya tayi tare da yin rub da ciki tana rubutu da karatu Nabeel ya fito shi fa Ammar,dama sun gaisa Ammar ya kalleta yace Sannu da karatu tace yawwa ta dago ta kalli Nabeel,yaga tayi kyau taci kwalliya cikin wani material black me adon red Riga da skert shi kanshi Ammar sai da ya kafeta da Ido sabo da ta fita ba karya,Haka suka wuce suna barin palon Hamida ta ajiye biro ta dafe kanta tare da lulawa tunanin Nabeel,a hankali tace dole in shiga in fita Ina Zan bar wannan inyi

Please Login or Register in order to submit comment