Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

falo su sameshi .

Cikin kankanki lokaci kowa yazo , nan daddy yake shadamusu abun da juwarriya tace," nan duk aka hauta da masifa kowa na zaginta , ita ko banda kuka ba abun da takeyi , dan hakan ma baya damunta dan bai hana ta sauya ra,ayi ba , ban daddy yace kowa yayi shuru, tunda haka tazaba taje Allah bada zaman lafiya , zan miki duk abun da ya dace a matsayina na mahaifinki, ki ce su tura sati mai zuwa za,a daura muku aure amma kusani babu ni babu ke kin amince ko? Kada kai kayi alamar eh tana fadin haka ta tashi ta nufi dakin da gudu tana kuka .......

*Muje zuwa*


*SHARE & COMMENTS*


*STORY & WRITTEN BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 40 & 41*

Da kallon mamaki kowa ya bita .

Tana Shiga daki cikin kuka ta dauki waya ta kira Khalil ,nan ta shaida mishi ya turo iyayanshi tare da sadaki , Abbanta yace nan da sati daya za,a daura musu aure.


Murna sossai yayi kamar ya zuba ruwa a kasa yasha, jikinshi na rawa ya kashe wayar batareda ya bata amsa ba .

Da sauri ya nufi dakin Hajiyanshi , jikinshi na rawa yasameta tana kishingide taba lazumi yace,"Hajiya Kitayani murna mahaifin juwarriya ya amince da Auren mu.

Wani kayataccen murmishi hajiya tace da gaske ? Kad'a kai yayi yace," wallahi da gaske hajiya ,masha Allah , hajiya tafada .

Cikin zakuwa yace," uhm yace wai a turo da komai da komai in mum shirya nan da Sati mai zuwa za,a daura auren .

Mamaki sossai hajiya tayi tace," to fa da wuri haka anya ba wani Abu kuwa? Sosa keya yayi yace," Hajiya ba komai kar ki damu nidai tunda ya amince shikenan , da Addu,a Hajiya ta bishi cikin murna tace," to barin kira kawunnan naka sai sukai sadakin ko koda zuwa jibi ne , in an kwanan biyu kuma sai su Hajiya HAUWA sukai akwati ,dama akwati kadai ya rage baka siya ba ko ?da eh ya amsa , tace," to sai a siyo ai tunda ance za,a gama komai , da haka HAJIYA tayi farin ciki nan ta fara kiran danginta da abokan arziki tana shaidamusu auren.

mamaki kowa yakeyi da jin haka , nan ta bashi umarni akan suyi magana da juwarriya abuga I .V ayi duk abun da ya dace , hade da shawarwarin yanda bikin zai gudana.


Nan Khalil ya fita yafara shirya _shiryen da yakamata , nan yafara kiran abokanai da yan uwa da abokan arziki yana shaidamusu daurin aurenshi mamaki kowa yayi .

A banganren juwarriya kuwa farin ciki da bakin cikin duk suntaru sun mata rufdugu, kuka sossai takeyi ita kadai a daki yana jin takaicin yanda aurenta yazo ,ta wani ban garen kuma tana jin dadi zata auri abun sonta .


Wunin ranar bata fito ba tana daki komai a daki takeyi , mommy da daddy ma basu damu da Sanin halin da take ciki ba .

Washe gari da safe jiki a sanyaye juwarriya ta fito tayi break fast ta gaida su daddy suka amsa ciki_ ciki batareda da sakin fuska ba .

Bayan ta gama ta koma daki Takara kukanta har kanta yafara ciwo.

Mommy ce ta shigo dakin fuska ba yabo ba Fallasa nan ta zauna a gefen gadon juwarriya tace," hakika juwarriya banso aurenki ya zo a haka ba , amma Na barshi a matsayin kaddara kuma haka Allah ya shirya , amma ina so kisani juwarriya kinyi babban ganganci , ni bazan miki mummunan fata ba ,amma ina miki fatan Allah ya zaunar daku lafiya keda abokin rayuwarki da kika zaba ma kankii.

wata yar karamar gora ta mika mata tace," ga wannan kishanye shi yau dinan in kin shanye kizo zan baki wani .

kad'a kai tayi alamar toh, wasu hawaye nlmasu zafi suka zubo a idonta , mommy ma hawayena kesan zuboma ta tayi saurin gogewa ta tashi ta Fita jiki a sanyaye .

Uhmmm Allah sarku tsakanin da da mahaifi sai Allah .

A gugurje.

daddy ne ya kira family meeting, nan yake kara shaida musu cewa za,a kawo sadakin juwarriya jibi talata in Allah ya kaimu , wani mummunar faduwar gaba haidar yaji yayi saurin dago kanshi .

Nan daddy ya dago kai ya kalleshi yace," haidar kayi hakuri, Allah yasani nayi iya kokari na babu yanda Na iya , naso juwairriya ta amince da aurenka amma ta watsamun kasa a ido, babban abun dake damuna ma rashin cika alkawarin da muka daukan ma iyayenmu, hakika in na tuna abun yana mun ciwo hakika da ba,a kusan Auren husna ba da Nlna musanya maka ita ,amma lokaci ya kure, ina me baka hakuri ,ka kuma kwantar da hankalinka , inshallahu Allah zai musanya maka da wacce ta fita komai da komai inshallahu .

Numfasa daddy yayi yace," nayi mamaki da juwairriya ta bijiremun, kuma kasan Annabi S A W Yayi hani ga auren dole abun da yasa ban matsa mata ba kenan , sannan kai kanka bazaka sami kwanciyar hankali ba , da haka nake baka hakuri Allah ya baka wacce tafita ,ko nima zan tayaki neman Yar mutunci matukar tayi maka ni zan tsaya maka akan komai , inshallahu ,sannan kasani duk abun da Allah ya tsara bawa bai isa ya kwauce mishi ba,mungode matuka da biyaiyyar da kayi mana Nlna amincewa da kudurin mu.

Nasiha sossai da ratsa jiki daddy yayi mishi, da haka duk mai magana ma yayi mishi, nasiha.

Take yaji sanyi a cikin zuciyarshi , ba tareda daya saka damuwa cikin ranshi ba .

Take aka rufe gurin da addu,a kowa ya watse .

Washe gari iyayyen haidar suka kawo sadaki naira dubu Dari biyu.

A gurguje .

duk wani abun da uba yakeyi ma yarshi Na gata daddy yayima juwairriya , haka ma mommy tayi mata duk abun da tasan hakki ne na uwa akan 'yarta tayi kokari ta sauke wannan hakkin .

Waya sossai juwairiyya da Khalil suke a harkar bikinsu cikin kwanciyar hankali .

Su Anisa ne akan komai na harkar bikin juwairriya, duk da kuwa Anisan taso tayi ma juwarriya fada akan hukuncin da ta yanke , saidai ganin ran juwairriya zai baci kuma ranta naso yasa taja bakinta tayi shuru batareda da tace komai ba ta cigaba da tayata murna .

Ana jibi daurin aure aka kawo akwati dosin daya , ba laifi Masha Allah Amarya tasha kaya .


A yau ne dubbanin jama,a suka shaida auren Ibrahim Khalil Da Amaryar sa juwairriya ........✍️✍️


*muje zuwa*

*sorry for the late update*


*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 42 & 43*

Murna wajan haidar ba,a magana ,da ka ganshi kasan yana cikin farin ciki marar musultuwa.

A bangaren amarya juwairriya kuwa ba laifi tayi kyau sossai , inda mommy takira mai kwalliya ta can cadamata kwalliya .

Saidai da ka kalli fuskar Amaryar zama gane babu walwala ko farin cikin a cikinta , domin zuciyarta nayi ma radadi da zafin rabuwa da mahaifanta ta hanyar da bu so ba.

Gud'a ake ta rangada mata itako banda wasu siraran hawaye da take fitarwa ba abun da takeyi.

Misalin karfe Biyar motocin daukan Amarya juwairriya suka karaso, wani irin faduwar gaba juwairriya taji jin ana gud'a ana fadin ayi a fito da Amarya .

Kuka mommyn ta fashe dashi ta jawota jikinta tana kuka mai tsuma zuciya .
Cikin matsanancin kuka juwairriya tace,"mommy mommy ki yafemun dan Allah hakika nasan ban kyauta muku ba .

Dago fukarta tayi ta kalleta , cikin kuka mommy take fadin," 'yata banso ace aurenki ya kasance a haka ba naso a ce anyi aure Wanda dukkaninmu zamu kasance cikin farin ciki , amma nasan haka Allah ya kaddara , ina miki fatan Alkhairi, Allah yayi miki Albarka ,Allah yasa gidan zamanki ne , Allah yasa yazame miki abokin rayuwaki na har Abada kita hakuri ,kita hakuri ,na yafe miki duniya da lahira kuma in Allah ya yarda zan san yanda zanyi na lallashi mahaifinki har ya saukko daga fushin da yakeyi dake ,ki kwantar da hankalinki kinji ko .

Tunda mommy tafara magana juwarriya take wani kuka ma tsuma zuciyar _,hakika masu karatu ko Ku in ku ka kalli juwairriya sai ta matukar baku tausayi._

Kuka take sossai hade da Ajiyar zuciya .

Husna ce ta karaso da gudu ta rungumeta tana kuka tace," yar uwata ,Allah ya sa gidan zamanki ne kiyi hakuri , rugune juna suka 'karayi suna kuka sossai hade da shasheka .

Nan mahaifiyar haidar ta zo tafara kokarin 'ban 'bare juwarriya a jikin husna amma Sam juwairrriya taki sakin husna sai kuka da sukeyi , dakyar aka aka rabasu .

Yaya suhail da Yaya Al_Amin ne suka shigo cikin dakin ,suna fadin," ayi a Fita da itaa mana suna ta jira fa .

Gurinsu juwairriya ta karaso da sauri ta rungumesu tana kuka tace," yaya Ku yafemun, Suhail ne ya shafa kanta yace Allah ya sanya Alkhairi juwarriya , Allah ya Blbaku zan lafiya , nan Al_Amin ma yace ," Allah ya Sanya Alkhairi juwairrah , suna fadin haka suka janyeta a jikinsu suka fita, jikinsu duk a sanyaye .

Nan mommy tabada umarni tace a kaita dakin daddynta suyi sallama .

Nan mahaifiyar haidar da Yayar mommy suka riketa suka nufi dakin daddy da ita .

Tun bayan da daddy ya dawo daga daurin aure ya shiga daki ya kwanta , banda tunani ba abun da yakeyi zuciyarshi na mishi zafi matuka yana aiyyana cewa wai yau juwairriyan da ya daurama son duniya ita take aure da wani can ba Wanda ya zaba mata ba ,lallai yayi Mamaki , ko a mafarki bai taba tunanin haka zata kasan ce ba , wata iska mai karfi ya furzar yace hmmm juwarriya ! Juwarriya ! Juwarriya !nan , take idonshi yakada yayi jajir, hakika yanasan juwarriya sossai , bazai iya cewa ya daina sonta ba amma bijiremishin da tayi lallai tayi babban kuskure kuma zata gane kurenta , murmishin da yafi kuka ciwo yayi, cikin ranshi yake fadin," naso ace ni nakai juwarriya da hannuna gidan mijin ta amma hakan bata kasance ba ,Allah sarki yafada gamemida runtse idanuwanshi ,tunani sossai ya cigaba dayi cikin ranshi .

Sallmar da yaji ne ta dawo dashi daga dogon tunanin da yakeyi .

Dago kai yayi yaga ana taho da juwairriya da fuskarta take a rufe .

Saurin dakatar dasu yayi da hannu yayi musu nuni yace," A,a basai kun karaso ba , ina anzo daukanta ne taje kawai Allah yabada zaman lafiya bana bukatarta anan , wani kuka juwairriya ta fashe dashi ta durkusa akasa tace" dan Allah dan Annabi daddy kayi hakuri kanyafemun ka taimakeni kasamun Albarkarka ..

Cikin bacin rai yace," juwarriya da kina Neman Albarkata da baki watsamun kasa a ido ba hakika kin bani mamaki, sabida haka Allah ya Sanya Alkhairi ,ki tashi kitafi kafin yammah tayi kinsan ke akejira .

Haba Alhaji kayi hakuri mana ka sassauta zuciyarka kuyi sallama mana ai aikin gama ya riga ya gama .

Murmusin da yafi kuka ciwo yayi yace," dan Allah kuje Alla ya bada zaman lafiya kawai ,yana fadin haka ya juya bai kara waiwayo wa ba .

Daga juwairriyan sukayi suka fita daita tana kuka sossai kamar ranta zai fita .

Sossai take kuka su mommy da husna suna tayata da sauran Yan uwa masu saurin kuka domin kuwa duk Wanda yaga juwarriya zai matukar tausayamata .

Fita da ita akayi tana kuka, daidai lokacin da za,a shigar da ita mota haidar yayi saurin karaso yace juwarriya !

Juyowa tayi takalleshi, yayi murmishi yace," ina miki fatan Alkhairi ,Allah ya Sanya Alkhairi a cikin sabuwar rayuwarki , yadaga mata hannu yana mata ban kwana da hannu, yana fadin haka a juya ya tafi , idanshi sun dan cicciko da kwalla yayi saurin sharewa ya dane zuciyarshi .

Ai ganin haidar yasa kukan ta yakara karuwa sossai , dakyar aka turata a cikin mota ,suka dauki hanyar zuwa gidan Khalil .........✍️✍️

*Muje zuwa*

*Hakika wannan page din ya bani tausayi matuka wallahi* 😩😩😩

*COMMENTS & SHARE*


*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


*PAGE 44 & 45*

Murna da d'oki a gurin Khalil ba,a magana .
misalin karfe bakwai aka kai Amarya juwarriya gidanta , inda taci kuka ta koshi , sai da tayi mai isarta.

Bayan an gama gyara mata komai ,dangita da suka rakota sukayi mata sallama daga bisani kowa ya watse ya barta sai Ita kaidai a cikin dakinta duk tsoro ya kamata .

Shuru_shiru bataji motsin kowa ba hakan yasa duk tsoro ya kara kamata neman guri tayi ta gefen gadon ta rakebe, tana ta sharar kukan .

Misalin karfe takwas motar Ango khalil ta faka a Sabon gidanshi, Inda ya hana ko wani abokinshi ya rakashi gurin amaryarshi, a cewarshi bayasan hayaniya , badan sun soba suka hakura da rakiyar .

Sanye yake cikin wata lafiyyaiyar dakakkiyar shadda kirar BUWA , kalar light bleu yasha malum_malum hannunshi sanye yake da light bleu din tsadadden agogo, yatsunshi sun sha zobuna na azurfa sai she'ki suke suma kalan light blue , hular kanshi kuma dark bleu ce mai dan ratsi_ratsin light bleu, kasancewar aiki jikin malum_malum dinshi dark bleu ne , takalmin kafarshi ma light bleu , sajen nan yasha gyara ya kwanta luf_luf a fukarshi , sanye yake da light bleu din gilashi , banda tashin kamshi ba abun da jikinshi ke fitarwa , hannuwanshi rike suke da bakaken manyan ledodi.
Masha Allah Ibrahim Khalil , hakika duk yanda zan baiyyana muku irin kyawun da Khalil yayi bata lokaci ne , domin khalil yayi kyau iya kyau .

Shiga cikin gidan yayi , kai tsaye ya nufi part din da Amaryarshi take ya turo kofar a hankali .
kukan da juwairriya takeyi a hankali ne irin nasu Na amare ya doshi kunnuwanshi .

Sallama yayi cikin daddad'an muryarshi , firgit tayi ta dago kanta ta kalli kofa, ganinshi yasa ta sauke wani Ajiyar zuciya ,karasowa yayi gurinta ya zauna kusa da ita yana sakin murmishi da ya baiyyan kyawawan hakwaranshi .

Kukan shagwaba tafashe dashi hade da kwantowa jikinshi ,tace," shine kaje ka dad'e kabarni ni kadai kuma ina jin tsoro.
Nan yasa hannayenshi biyu ya rugumeta yana shafa bayanta a hankali yafara magana cikin sassanyar muryar yace," haba my happiness kukan ya isa a haka mana ko so kike ki illatamun kanki ne pls kidaina kukan nan banaso kiyi shuru haka kinji my wife goslow ne yasa na dade haka .

'Dan tsagaita kukan tayi ta dago ta kalleshi , wani kwarjini ya karayi mata , nan take takara jin wutar sonshi na kar ruruwa cikin zuciyarta da ilahirin gangar jikinta .

Nan ya sakar mata murmishi yace," amm tashi ki rage kayan jikinki ko? Sai muyi Alwala muyi sallah, cikin sanyin murya tace toh ,nan ta tashi ta shiga toilet tayi Alwala , shima rage kayan jikinshi yayi kafn ta fito, tana fitowa shima ya shiga yayi alwalan .

Bayan sunyi ya shimfida musu dardduma juwairriya tasa katon hijabinta sukayi sallah raka,a biyu .

Bayan sun iddar ya dafa kanta yayi mata Addu,a irin yanda addinin musulunci ya tanadar yakuma yimata tambayoyi irin yanda addinin musuluncin ya tanadar .

Bayan sun gama nan Khalil ya dauko ledar da ya shigo da shi ya bude ya Ciro lafiyayyun kaji , tashi yayi ya tafi falo ya bude fresh ya daukko Sassanyan Rufaidha yoghurt ya kawo musu hade da fanta.

kitchen ya nufa ya daukko plate da cup.

Daki ya dawo ya zauna ,kallanta yayi da kanta dake a durkushe yace," juwairrah please kar kicemun kin koshi ki zo kuci .

Cikin sigar shagwaba murya a sanyaye ta langwabar da kanta tace," A,a nifa nakoshi , hararar wasa yayi mata yace" amma nace miki kar kicemun kinkoshi ko ? Hmmm tace," ta dan dauki tsoka 'yar karama tasa a baki, tace," gashinan naci kuma na koshi , jawota jikin shi yayi batareda yace mata komai ba .

Nan yafara zuba rufaidha yoghurt din cikin cup din , itako da kallan mamaki take binshi, tana San ganin ikon Allah , kallanta yayi yace," bude bakin banason kimun gardama , badan taso ba ta bude baki ya bata rufaidhan tashan nan ya yagi katuwar tsoka yabata taci .

Bata ya dingayi badan taso ba haka taketa ci .
Ganin cikinta na barazanar fashewa ne yasa ta saurin mikewa kamar zatayi kuka tace," ni wallahi na koshi fa , dariya taso bashi nan ya girgiza kai yace," to shikenan ai ko ba komai dai kinci .

Tashi tayi ta nemi gefen gado tadan rakube , tashiga tunanin gida da iyayenta da yan uwanta , hawaye na bin fuskarta .

Bayan Khalil yagama cika cikinshi , tashi yayi ya dauke kayan ya kai ya ajiye .

Gurinta ya nufa yace," ammm in kina jin barci mu kwanta kawai nasan kingaji da yawa ko? , nan fa kirjin juwairriya yafara dukan uku_uku tana jin faduwar gaba da tsantsar tsoro jin yace su he sukwanta , dkyar ta iya tattaro nutsuwarta yace," uhm Bana jin barci , dariya yasa yace,"a haba baby karya kike ba wani nan Allah kina jin barcin da ganin idonki , ki kwanta kawai .

Drawer ya bude ya daukko wasu kayan barcin Kallan dark pink masu tsantsi ya mika mata yace," gashinan kisaka yanzunan fa Sai Mlmu kwanta, ba tareda da ta musa ba ko gardama ta tashi sumi_ sumi ta canja kaya cikin jin kunya .

Shima kayan barcin ya dauka Kallan nata dark pink riga da wando .

Ba laifi kayan sun musu kyau sossai , musamman ma juwairriya kayan ya amshi coca cola shape din jikinta , ga suman kanta da yasha gyara yaketa tashin Kamshi ya kwanta luf_ luf a gadon bayanta.

'Kura mata ido yayi yace," masha Allah , nuni yayi mata da ido gamida d'aga kanshi sama Alamar tazo, jiki a sanyaye ta karaso gurin shi tana jin faduwar gaba , riketa yayi ya daurata akan gadon , shima ya koma ta gefen ta ya kwanta ya juyo da jikinshi yana karema halittar jikinta kallo musamman dukiyar fulaninta da suke a cike kamar zasu fasa riga , a hankali ya kai hannunshi Kansu Inda yafara shafasu cikin salo da kwarewa , tuni juwairriya ta rasa samun nutsuwarta wani bangaren tana jin dadin sakon da yake Isar mata Inda gangar jikinta yake amsar sakon da khalil ke Isar mata sabanin wani 'bangaren tsoro ne fal cikin ranta.

Ganin yafara wuce Gona da iri yafara bata good romance yana shafata ko ta ina yasa juwairriya tafara sakin kukan shagwaba tana fadin," waiyyo pls baby kayi hakuri kabarni dan Allah wallahi nagaji tsoro nakeji dan Allah kayi hakuri , duk maganganun da juwwairriya takeyi sam Khalil baya jinshi domin rabin hankalinshi baya jikinshu , banda rawa ba abun da jikinshi keyi , hakika yaga mata kala _kala ,amma bai taba ganin mace mai cikar sura irinta juwairriya ba domin ji yake kamar bai tanlba ganin jikin wata mace ba inba ita ba .

Ganin bazai iya hakuri ba yasa ya tashi ya kashe wutan dakin , bed side lamp kawai ya bari kasancewar bata da haske sossai .

_uhmmmm nima tunda naga ya kashe wutar na tattara inawa_ inawa nabar _dakin dan kar naganema idona abunda yafi karfina , kafin na fita najiyo ihun juwairriya ,tunda naji kuwa nasan brahim Khalil ya cika aiki ,nasan ko ba a fada ba yau kam ya maida da juwarrriya tazama cikakkiyar mace_......✍️✍️

*Muje zuwa*

*COMMENTS & SHARE*


*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN

Please Login or Register in order to submit comment