Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu ke karuwace.
kutumar uba , nikike fadawa magana to dan ubanki da mijin ki muke karuwancin in baki sani ba kisani , wani faduwar gaba juwairriya taji , danne zuciyarta tayi cikeda karfin hali tace," ai mijina yafi karfi ya hada jiki da ke domin ke a karuwanma ke kazamace kuma kucaka ... kafin ta gama rufe baki ta dauki hannu zata mari juwairiya ..

karar mota Khalil ne yasa ta juya tana kallanshi gamida sauke hannun.

Tun kafin Khalil yagama parking yayi saurin fitowa a motar yanufo gurinsu da Sauri....✍️✍️

*MUJE ZUWA*

*COMMENTS & SHARE*

*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 52 & 53*

Da sauri ya karaso gurin , cikin tsantsar bacin rai yace," amm juwairriya shiga gida ......

Da kallon mamaki ta bishi tana fadin," taya za,ayi kace na Shiga gida , wacece ita?

Wata uwa harara ta wurgamata tace," baki bukatar sanin ko ni wacece , amma in kinaso zan iya fada miki ko wacece ni!!!
Wata razananniyar tsawa Khalil ya daka mata yace," juwairriya nace ki Shiga gida kawai yafada cikin Bacin rai ....

Dariyar shakiyanci heavy baby tayi tace," amm in fa bazata Shiga ba ni zan iya fada mata ko ni wacece a gurinka .....

Tsayawa kyam juwairriya rayi tanason Sanin ko wacece .

Cikin tsantsar masifa juwairriya ke fadin," ni wallahi tallahi bazan bar nan ba har sai naji ita wacece a gurinka ?

Caraf heavy baby ke fadin ' karuwace ni , karuwarshi ba , ai dama da kika cemun karuwa na fada miki da mijinki nake aikata zinar , amma kinki yarda sabida haka gaskiya, yanzu ki tambayeshi wala alla ya baki ansa ......

Wani irin faduwar gaba juwairriya taji , nan take wasu hawaye masu zafi suka zubomata cikin muryar kuka ta kallashi tace," da gaske ne? da gaske ne abun da take fada? Dan Allah ka karyatata kace ba gaskiya bane , kunnuwana baza su taba iya jin wa inna mumnanan kalaman NATA ba , dan Allah kace ba gaskiya bane , nasan mijina ba fasiki bane ,kuma ni ce mace ta farko da ya fara Sani , kuma nasan son da kake mun bazai sa ya ci amanata ba , sabida haka karya kike munafuka hakan bazai taba faruwa ba ....

Dariya ta tintsire dashi tace," to in karya nayi miki bagaki gashi ba , ai sai ya miki bayani ai , ba,a karya kusa da gida ai , amm ni zan barku haka zan tafi sabida haka sai na kara kawo muku ziyara ta gaba , amma ziyara ta gaba inaso ku san da cewar zan tattaro kayana na dawo nan na zauna matsayin sabuwar Amaryar Khalil , tafada gamida da tuntsurewa da wata shu'umar dariya .
Daga musu hannu yayi hade da fadin," byee , ta juya ta tafi tana rangwada.

Da gudu juwairriya ta juya ta shiga cikin gida , cikin hanzari shima yabi bayanta .... .

Kai tsaye daki ta nufa ta zauna a kan gado tana kuka mai cin rai da tsuma zuciya ....

Dakin ya shigo yace," juwairiya kar ki yarda wannan magana yasa ki daga ma kanki hankali , to in ma karuwatace menen a ciki?
Cikin nuna Alamun ko in kula yace," in har kika je kika sama kanki damuwa ni baruwa sabida haka garama ki yi hakuri kawai , dan ta ce miki ita karuwatace ke sai ki yarda ? Lallai kina da aiki ,ai na da ma ace kingamu kwance da ita akan gado shine zaki Yanke wannan hukuncin amma baki gani ba zakizo ki na damun kanji .

Dago rinannun idonta tayi tace," yanzu amsa daya yadace kabani kenan ? madadin kamun bayanin da zai gamsar dani har hankalina ya kwanta amma kazo kana kokarin kare kanka batareda wani kwakwararan bayani ba ?

Cikin fada yace," to ya kike so nayi miki , yana fadin haka ya tashi ya fita yabar dakin gamida Jan dogon tsaki yafita hankali kwmace ....

Da Sauri ta tashi ta bishi a baya tana dan dingisawa , tace," ka tsaya kaji , amma nasankaji abun da ta fada kafin ta tafi, tace zatazo a matsayin amaryarka ne fa ? Haka fa ta fada , wata dariya ya tuntsure dashi yace," to menene , ai Allah ya hallatamun yin mata uku ne bayan ke , so in ma tazo ai ba matsala bane so karkidamu ....

Tsuro tayi tana kallanshi tace," Khalil anya Kaine kuwa? Anya kaine? ko fitar da kayi an canjamun Kaine , ni nasan bazaka tabamun magana irin wannan ba .....

Dariyar gefen baki yayi yace," amm karkidamu nine , kece kika kasa fahimta , shuru tayi batareda da ta kara cewa komai ba , ta juya ta nufi daki ......

Zama yayi akan gado tana ji abun kamar a mafarki , cikin ranta take aiyyana cewa", karfa ace na fara fuskantar wulakancin d'aa na miji tinda ga yau? Girgiza kai tayi tana fadin," A,a A,a Khalil bazai mun haka ba yayi alkawari zai rikeni amana sabida haka nasan bazai saba alkawari ba,tunanin haka yasa hankalinta yadan kwanta ...

Shugowa dakin yayi kai tsaye , ganin yanda idonshi ya kad'a yasa juwairriya tadan tsorata tace," lafiya , cikin wata kasalalliyar murya yace," ke nake bukata .

Cikin matsanancin tashin hankali tace," nikuma? Dan Allah kayi hakuri wallahi gurin ciwo yakemun , magana take amma yana kara nufuta ,batareda ya ji abun da take fada ba .
Caraf bakinshi ya sauka akan nata yafara tsotsa kamar mayunwacin Yaro , hawaye ne ke fita a fuskar juwairriya , tana tuna irin Azabar da zataji .

Batareda bata lokaci ba Khalil ya fita haiyyacinshi har ya rabata da kayan jikinta ya biya bukatarshi .

Bayan ya dawo haiyyacinshi yadinga rarrashinta ,Ita ko banda kuka da azaba da take ba abun da takeyi , da haka har ta hakura, dan kanta... .

*A gurguje*

Wasa wasa yau Satin Khalil da juju daya da aure... ..

A bangaren gidansu mommy kuwa , hakika sunyi matukar damuwa a yan kwanakin nan , a koda yaushe maganar mommy bata wuce tace juwairiiya ba..... .

Shima daddy ya danu sossai akan yar tashi , saidai kuma in ya tuna da abun da tayi mishi yakanyi burus da Al_ amarin.... .

Zaune mommy take a falo tayi tagumi , husna kuma na danne_ dannen wayar , Kallan husna mommy tayi tace," husna inason jin muryar juwairriya ina San ganinta bansan a wani halin take ciki ba husna ya zanyi ? tafada cikin tsananin damuwa ......

Kallan mommy husna tayi tace," uhmmm to ke mommy juwarriyan ta damu da kune , ai da ta damu daku wallahi tallahi ko me daddy zai mata sai ta zo ta ganku ko kuma takira wayarki amma bata taba wanan ba , ai kuwa kinga hakan na nuni da cewar Itama tana fushi da ku kenan tunda a matsayinta ta 'ya ai a kalla zata iya kira a waya ko ta tako kafa tazo ko YAYA amma batayi hakan ba , kekuma kin zo kinaso kisama kanki damuwa ni wallahi ko a jikina , daa na damu amma wallahi banda yanzu , shuru mommy tayi batare da ta kara cewa komai ba ,tana me nazarin maganganun husna... .


Kwance juwairriya take akan gado tana tunanin rayuwarta ta baya rayyuwar jin dadi da kulawa , tabbas tayarda namiji bashi da tabbas , Ashe hakurin da ake cewa kayi da gaske ne Ashe duk abun da ake fada maka a gidan aure tabbas hakan zai kasance , hakika in aka ce Khalil dinta zai daga mata muryar ko yayi mata tsawa ko a mafarki bazata taba yarda ba , yanzu a zamatakewarsu , babu soyaiyya ko kadan, sai in yana bukatarta ya zo mata ko tanaso ko batason, in kuma ya biya bukatarshi shikenan , hawaye masu zafi ne suka zubo a idonta , lallai duk abun da ke faruwa da ita yanzu *A Sanadin kuskurenta ne* amma ta dauki hakan matsayin kaddarar rayuwarta , kwata_kwata watansu daya amma har ta fara samun matsalolin aure , kuka me karfine ya kubuce mata....

A hankali ta fara jin tashin zuciya,ganin tana cigaba da ji yasata ta mike da gudu ta nufi bayan gida , amai tafara kwarawa kamar kayan cikinta zai fita, hakki ta fara yi tana numfasawa dkyar, gawani jiri dake dibanta kamar zata fadi , a hankali ta bude famfo ta wanke fuskarta , bayan ta gama ta lallaba dakyar ta iya fitowa tana daddafa bango.....

Shame shame tayi akan gado , wani barci yayi awun gaba da ita .

Tunda khalil ya shigo gida yaketa rafka sallama , jin bata amsawa yasa ya nufi dakin. ta cikeda bacin rai .....

Shiga yayi cikin fadaa yace," Ke !! Juwairriya ! firgit ta farka , tana mutsuka ido tace," sannu da dawowa , yauwa yafada a takaice"ina ta sallama bakya jina ne?

Cikin Muryar barci tace," wallahi banda lafiya ne , tunda nayi amai dazu na zo nadan kwanta shikenan barci ya kamani , yanzu haka Kaine ciwo yakemun , ga kasala da nake ji da jiri.....

Too Allah ya sauwwake , barin gama nayi wanka Sai mutafi Asibiti ko? To tace gamida kokarin komawa barcinta...... .

Ha,a yazaki koma barci bayan baki kaimun abinci ba ? kayi hakuri yana kan dininng na ajiye maka , tana fadin haka ra kara komawa barcinta ....

Tsaki yaja ya nufi dinning .

Bayan ya kammla ,ya nufi dakinta ya tasheta , yace ta shirya su tafi ....

Tashi tayi ,ta yi wanke fuskarta ,ta dauki hijabinta suka nufi Asibiti...

Kai tsaye asibitin suka nufa , inda gwajin farko likita ya tabbatar musu da cewar tana dauke da cikin sati hudu.....

Murma sossai juwairriya tayi sabanin Khalil da babu yabo ba fallasa....
bayan sun kammala suka nufi gida.... .

Bayan sun isa gida ,sun zauna , cike da farin ciki juwairriya tace," uhmmm my love kaga rabo ko , gaskiya naji dadi sossai wallahi tafada hade da shafa cikin nata .

Mai da hankalinshi yayi gareta ya fuskanceta cike da mai da hankali yace," juwairriya , da murmishi a fuskarta ta amsa da Na,am , kara mai da hankali yayi akanta kafin daga bisani yace," amm gaskiya ban shirya haifan da ko 'ya yanzu ba, kwata kwata auren namu wata daya ne fa , taya zaki yi saurin daukan cikin haka ?

Cikin rashin fahimta take kallanshi tace," kai Khalil me kake nufi kenan? Haihuwa ai Allah ne yake badawa , wasu fa ko da dukiyarsu zata kare basu ki su sami haihuwa ba , sunanan suna nema shekara da shekaru amma shuru babu ,amma mu cikin kankani lokaci Allah ya bamu Ai yakamata ace mun gode mishi da kyautar da yayi mana ko?

Kallan raini ya bita dashi yace," to kin fini sani ne ? nidai na fada miki ban shirya haihuwa yanzu ba.... .

Numfasawa tayi tana kare mishi kallo tace," to ya kakeso ayi kenan?

Batareda da nuna damuwar komai ba yace," a cire cikin kawai ina nufin a zubar dashi.... .

Zaro ido tayi tana kallanshi tace," kana nufi Abortion?? in zubar da cikin jikina?......✍️✍️

*MUJE ZUWA*

*COMMENTS & SHARE*

*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 54 & 55*

Cikeda nuna Alamun ko in kula yace," yehh Abortion that's what I mean .

Hawaye masu zafi ne suka fara gangarowa a fuskarta tace," haba Khalil karfa ka manta hakan babban kukskurena a garemu baki daya , dan Allah kayi hakuri ka barni na Haifa , kasani ko rabonmu kenan a duniya wasu fa da kudi nema suke amma basu samu ba .......

Wata tsawa ya daka mata yace," kee!! Kin fini Sanin abun da zanyi ne , an fada miki ni dakikine kwata_ kwata auren namu watanawa wata daya fa shine har zaki dauki ciki kuma kiyi tunanin zan karba A,a ina wannan ai abun kunya ne a gurina , bazan taba yarda ba in kuma kince sai kin Haifa to tun wuri ki nemi Inda zaki je ki haife abunki amma wallahi tallahi ba a gidana ba ya fada a fuskace gamida mikewa......

da sauri ta rike rigar jkinshi , tayi murmishin da yafi kuka ciwo gamida sa hannu to goge hawayen fuskarta tace," A,a Khalil kayi hakuri basai anyi haka ba wallahi na amince a zubar da cikin basai ta kai ga wanan ba kaji kayi hakuri ......

Zama yayi yace," to shikenan ki shirya gobe muje akwai likitan da zai cire miki, to tace," gamida da tashi ta nufi daki da gudu hade da fashewa da kuka mai ban tausayi.... .

Daki ta Shiga ta zauna a kan gado tana cigaba da matsanincin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro........

Kuka take sossai tana fadin," nashiga uku anya Khalil dina ne kuwa ? Meyasa zaimun haka meyasa zai rabani da cikin jikina ,kar dai ace *Sanadin kuskurena* zai haifar mun da illah ko wace mace in ta sami ciki a gidan mijinta fari ciki kowa yakeyi ,mussaman ma shi mijin , amma ita yau tasamu ciki na Sunnah mijinta yace ta zubar lallai rayuwa , tabbas ko a mafarki bazan taba tunanin Khalil dina zai aikata mun haka ba amma kuma ba komai , sonshi shi ya rufe mun ido na nagarara hango aibunshi , wani matsanancin kuka ta fashe dashi , kafin daga bisani barcin wahala yayi awun gava da It .......

Zaune hajiyan Khalil take a shingide , yarinyar kanwarta na zaune suna hira , gyaran murya mahaifiyar Khalil tayi tace," hmmm Raudat kinsan Allah ni fa har yau ban je gidan yaron nan ba , kuma itama bata zo ba , ko kunje?

Tabe baki Raudat tayi tace," hmmm Hajiya ai ni wallahi banje ba , kuma ban zantaba zuwa ba kuma bazan je ba........

Tabe baki itama Hajiyan tayi tace," hmmm ni kaina ta yar bata mun ba fa , tunda suka mana rashin mutunci ni da kannen mahaifin shi yasa naji duk na tsani yarinyar , nifa gani nake ma ba dan Allah yarinyar take sanshi ba , Shiyasa duk na tsaneta.......

Caraf Raudat tace," hmm Hajiya ai kuwa kinga hakan bazai yuyu ba , kawai kisa YAYA Khalil yayi aure , tunda kinga wanan din ba Santa kike ba sabida haka wallahi ki aura mishi wacce kikeso kawai...

Cikeda da gamsuwa Hajiya tace," gaskiya raudatu kin bani shawara mai kyau kinsan miye? zan yi tunani akan wannan maganar taki kuma zanyi tunani , sannan zanyi bincike akan wacce zan aura mishi , to tace gamida sakin wani kayataccen murmishi a fuskarta ..........


Washe gari da safe juwairriya da Khalil suka shirya, basu zarce ko ina ba sai Asibiti...... .

Kai tsaye kiran doctor yayi ya shidamusu cewa sun iso , kasancewar jiya yafada mishi zasuzo .

Fitowa likitan yayi daga office dinshi ,suka gaisa daga bisani ya nuna ma juwairriya lab yace taje a gwada ta gamida rubuta mata wani abu a paper yace ta kaimusu....

Ba musu juwairriya ta karba kai tsaye ta tafi lab din.......

Bayan sun kara tabbatar da cikin sati hudu ne , ya rubuta mata wata yar takarda ya ceta ta kaima doctor office dinshii..........

Bayan ta kai mishi ya duba , gamida tashi ya nufi phamarcy din Asibitin ya daukko wasu magungunan....... .

Dawowa yayi ya bata gamida da fadin," Amm na ga cikin naki sati hudu ne so ba bukatar na miki aiki wajan cireshi , wa inna magungunan in kika sha zai sa cikin ya fita da kanshi , yafada gamida mika mata, yace," gashi nan gobe in Allah ya kaimu zaki sha , bayan wani lokaci zaki fara bleeding to shikekan cikin zai fita , to tace rai a bace ta tashi ta bar office din cikeda bakin cikin da tsananin tausayin kanta.,..... .

Bayan ta fito khalil ya kalleta yace," kai har angama? Gigiza mai kai tayi Alamar A,a yace," to me kika fito yi?
Nuna mishi maganin tayi tace," ga abun da yabani nan yace wai shi zan sha in nakoma gida..............

Cikeda farin ciki yace," okay okay to ina zuwa barin je na sallameshi kije moto kijirani kinji ?

To tace gamida da tafiya ta nufi mota .......

Kai tasye office dinya nufa yayi mishi godiya gamida bashi kudi masu yawa kafin daga bisani ya fito shima ya nufi motar suka tafi gida .........

Bayan sun dawo gida , sun zauna batare da kowa ya ma dan uwanshi magana ba .....

kai tsaye juwairriya ta nufi daki cikeda takaici............ .

Wayar Khalil ce tayi kara , bayan ya dauka wayar yaga sunnan hajiyanshi ya baiyyana akan screen din wayarshi , dauka yayi cikin biyaiyya yace," Hajiya ina wuni , amsawa tayi tace lafiya ya matar taka amsawa yayi da lafiya kalau , in ba ka komai kayi maza kazo yanzu ina San magana dakai , Hajiya ta fada cikin Isa......
Cikin girmamawa ya amsa da to ganinan zuwa ,gamida kashe wayar .........

Tashi yayi, yayi saurin fita ya nufi gidan Hajiya .......

Cikin mintuna kadan ya isa gidan da sallama ya Shiga yace," sannun da hutawa Hajiya , yauwa ta amsa a takaice.........

Gyara zama Hajiya tayi tace," yauwa yaro abun da nakeso dakai shine , ba komai ne yasa nace kazo ba illah inaso mu tattauna wata muhimmiyar magana dakai , ka nutsu ka fahimceni gaskiya ni fa Kasan tun da iyayen matarka sukamana rashin mutunci Shiyasa naji duk na tsaneta , sabuda haka abun da nakeso dakai shine ka kara Aure !

Kallonta yayi cikeda mamaki yace," Hajiya aure kuma?amma ba yanzu ba ko? da ni wallahi banda niyyar aure yanzu , amma in kin ce nayi zanyi amma bayanzu ba..

cikin murnar samun nasara Hajiya tace," eh dama ni bance yanzu ba in an kwana biyu nace maka , tunda dai ka amince shikenan duk sanda ka shirya sai naji , to yace," gamida yi mata godiya daga bisanii ya nufi gida ........

Koda ya koma gida a ranar haka suka wuni ba tareda kowa yayi ma dan uwanshi magana ba............

Washe gari da safe Khalil ne zaune a kan fining ya gama musu break fast , jiki a sanyaye juwairrya ta fito, zama tayi gamida da kallanshi tace,"ina kwana , cikin sakin fusaka ya amsa yace," lafiya kalau kin tashi lafiya , amsawa tayi da lafiya , batareda da takara cewa komai ba ta janyo flask tafara zuba abun karyawa ..........

Bayan ta gama Khalil ya kalleta yace," kinsha maganin kuwa ?
Kada kai tayi Alamar A,a kallanta yayi cikeda mamaki yace to meyasa?

Cikin rashin nuna damuwa tace," bakaga yanzun nagama karyawa ba ai yanzu zan daukko nasha ,tafada gamida tashi ta nufi daki ta daukko maganin.........

Zama tayi akan dress mirror ta dafa kanta tana Karema maganin kallo tana hawaye kafin daga bisani ta dauki ruwa tasha maganin .....

Bayan ta gama sha ta tashi ta koma falo ta kwashe plate din da suka ci abinci ta je ta wanke tadanyi aikin gidanta da basu da yawa ......

Bayan ta gama ta koma falo ta zauna a gefen gadon, da Sauri ta tashi ta daukko pad kasancewar tasan zatayi bleeding yasa ta daukko pad din ta saka a jikinta gudun kar jinin ha bata mata kaya.... .

Bayan ta gama ta tashi ta nufi kan gado ta kwanta ta rafka uban ta gumi tana tunanin rayuwarta na baya ,hawaye ne ke fita a fuskarta tana tunanin rayuwar su ta baya da Khalil Inda ko a mafarki in akace mata haka zasuyi zaman aure da Khalil to tabbas basa ta yarda ba ,gashi tun ba,a je ko ina ba tafa ganin *kuskurenta* hmmm auren mu wata daya dashi har na fara fuskantar kalu bale , gashi a bangare daya tana fargabar zuwan heavy baby da tace zata dawo mata gida a matsayin matar Khalil , gashi ta wani bangaren khalil ya juya mata baya ,ba kamar daa da ta sanshi ba , gashi kuma uwa uba iyenyenta suma ba sa tare da ita ,iita kam tashiga uku , ga mahaifiyar Khalil ma har yau bata santa ba , kuma da da dukkan Alamu basanta take ba, babu mai zuwa gurinta daga ita sai ita garama Anisa takan dan bullomata ta duba halin da take ciki ,sanan ta fada mata halin da iyayenta suke ciki, tunanin ta dingayi iri_iri cikin ranta tana me tausayin kanta........

Da kadan _ kadan tafara jin ciwon ciki , tun tanaji yanayi mata a hankali har tafara jin azababen ciwo , wani ihu tasa tafara murkususu a kan gado tana kuka , da rarrafe da murkusuwa ta saukko a kan gadon tana jin azababben ciwo........ .

Da kadan Kadan jini yafara fita ,tun yana fita kadan har ya fara fita mai yawa da yasa pad din ya jike jagab har ya fara bata kayan jikinta.

Jin ciwon cikin na kara karuwa yasa ta tsala ihu tace," Khalil! Khalil! Kazo zan mutu ..........

Jin ihunta yasashi saurin tashi ya nufi dakin kai tsaye ..

Ganinta kwance cikin jini yasa ya tsorata yana me yi mata sannu, a rikice yake kallan ta ganin yanda jini ta bata mata jiki yasa shi kara rikice gamida fadin," subhanallahi garin YAYA haka?

Kasa magana tayi tana numfashi dakyar , numfashinta Na fita a hankali hannunta rike da cikinta ,a hankali tafara rufe idonta ta fadi sumammiya .......

Akidime Khalil ya jijjigata yace," juwairriya! Juwairriya!ganin bata motsa yasa hankalinshi ya kara tashi , jikinshi na rawa ya ciro wayarshi ya fara kokarin kiran likitan da ya bata maganin, gamida yi mishi bayanin halin da juwairriya take ciki .........


Please Login or Register in order to submit comment