Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Cikin kankanin lokaci lilitan yazo , cikin hanzari yafara dubata gamida da bata taimkon gaggawa , cikin ikon Allah likita yayi nasarar tsaida jini ......

Drip yasa mata gamida yi mata Allurai , bayan ya gama ya ba Khalil wasu magungunan yace," in ta tashi ya tabbatar taci abinci kafin ya bata maganin , ya kuma tabbatar mishi da cewar cikin ya zube gaba daya , bayan ya gama ya yi mishi sallama yatafi Yakuma shaidamishi in akwai wata matsalar zai iya kiranshi , godiya sossai Khalil yayi mishi , daga bisani doctor ya tafi.....


Bayan doctor ya tafi , kaya Khalil ya daukko kaya a drower juwairriya , ya debo ruwan dumi a baf, ya goge mata jiki ya canza mata kayan jikinta , yanayi yana tabe fuska hade da tsaki , bayan ya gama ya kara gyara mata kwanciyarta ........

Bayan ya gama kai tsaye ya nufi kitchen yana shiryamata abun da zatji ci...

Indomie da kwai yayi mata , yasa a kula, ya kai kan dining ya ajiye.......

Tsaki ya dinja cikin ranshi yana fadin," badan Allah yasa nine silar faruwan haka ba ko, da wallahi babu abun da zai sa nadinga wannan bautar ,da yin aikin kazanta , yafada kamar wani na ganinshi .......

Bayan ya ya gama komai ya dawo daki ya kura mata ido yana kallanta,Inda tayi rama cikin kankanin lokaci, tayi yar fayaut sai wani haske da tayi hancinta ya kara fito wa , zuru yayi yana kallanta ........

Falo ya dawo ya dauki wayarshi ya kira Hajiya yace," ta dan turo mishi mai aikinta .....

Cikin kankanin lokaci laure mai aiki ta zo gidan Khalil.....

Nuna mata aikin da zatayi yayi batarreda bata lokaci ba tafara aiki tukuru ta gyara gurin da jinin ya bata ta wanke mata kayan jinin tas , sai da takammala komai kafin daga bisani ta tafi gida........ .

Bayan ta koma gida nan Hajiya take tambayarta abun da tayi musu ?

cikeda gulma laure tace," hmm Hajiya inaga fa Juwairriya 'bari tayi dan wallahi aikin jini nayi ,gata akwance tana ta barci, dakin duk ya baci da jini ita kanta ta yi wani rama gashi da gani tana jinjiki....

Subahanallahi 'bari kuma? Shine yaranan bai fadamun ba? kai amma banji dadi ba naso cikin ya zauna Nima nadan ga jikana duk da bana san Uwar amma ai uban d'aa na ne , to ina yi mata fatan ta samu wani , in kuma ba ita bace mai rabo shikena , Hajiya tafada gamida tabe baki , itama laure tabe baki tayi gamida tashi tanufi kitchen dan daura ma Hajiya Abinci.....,. .


Bayan awanni biyu juwairriya ta farka .....

A hankali juwairriya take bude idonta,jin wanj nauyi akanta kamar an daura mata dutse ,hannu tasa a kanta tana runtse idonta tana jin wani irin jiri , kanta na juya mata, ga ciwon cikin da takeji........ .

A hankali tafara bude idonta , ganin ta bude ido yasa Khalil fadin," sannu ko ?

kada kai tayi Alamar yauwa , zaki iya tashi?

Yafada yana kallanta, shuru tayi batareda da tace komai ba ,a hankali ya fara kokarin rike mata hannu ya dagota ya taimakamata ta dan shingida a kan gadon..... .

Kuka ta fashe dashi muryar a sanyaye tace," khalil ka gani ko?
ka ga abun da ka jawomin ko na kusan rasa raina akan wannan abu, Khalil yanzu da na mutu fa me zamuje mucewa Allah , ni kadai nasan azaba da radadin da naji , takarasa maganar hawaye na zuba a fuskarta...... .

Shuru yayi ya kallanta yace," inshallahu baza ki rasa ranki ba , kinji .....

Sannu yakeyi mata , yayi saurin mikewa yace," barinje na kawo miki abinci kici kinji?

tashi yayi ya daukko mata abincin , ya dawo ya fara kokarin zubamata , ya hada mata tea .......

Bata yayi yace gashi kici kinji?
Girgiza kai tayi muryarta sanyi sanyi da bata fita sossai tace," na koshi ....

Taya zakice kin koshi ai dole sai kinci abinci dan ko likitan ma yace," ki fara cin abinci sai kisha maganin sabida haka ki daure kici kinji?

A hankali ya fara bata abici kadan_Kadan tanaci yana bata tea din.
sai da ya tabbatar da ta ci da yawa kafin ya barta , ya ballo mata magungunan ya bata tasha ......

Bayan tasha ya Kara gyara mata kwanciya , ta kara komawa barci ....

Kayan ya kwashe ya Kai kitchen , ya fito falo ya zauna .....

Ringing wayarshi ta fara ganin sunnan heavy baby ya baiyyana akan screen dinwayar yasashi jan tsaki yace," kai wanan bazata barni ba ....

Dagawa yayi cikin fada yace," kai wai miye ne? ba mun gama magana ba kuma?.
Zaro ido tayi kamar yana ganinta tace," tsawa kakemun!!
Uhmm ,ta tabe baki tace," ko dayake ma kai kasani dama ba komi ne yasa na kira ka ba dama kasan kai kace nayi aure , so zanyi aure kuma ina bukatar kudi daga gurinka dan yin shirye shiryen bikina dan auren saura wata daya yanzu .....

Cikin Bacin rai Khalil yace," lallai ni ne mijin da zan dauki nauyin bikin?
Bura uba ne, ba kai kace inyi aure ba? Ohh ko dan kaga na amince da bukatarka wallahi kasa wasa sai na fasa , da sauri yace," A,a kar ayi haka zan turo miki zuwa karshen watanan yana fada ta kashe wayarshi .

Hannu ya daura akai yace," kai ! duk laifinane da nashiga rayuwar yarinyar nan , da bani na fara lalata ta ba da batazo tanamun wannan haukan ba yafada gamida Jan dogon tsaki .......✍✍

*MUJE ZUWA*

*SHARE & COMMENTS*

*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 56 & 57*

*A gurguje*

Bayan sati daya juwairriya taji sauki sossai ta samu lafiya....

Inda take dan samun kulawa ba laifi ta bangaren Khalil...........

Zaune take tana kallan TV shi kuma hankalinshi nakan wata yana dannawa, kallanshi tayi , cikin girmamawa tace," dear , mai da hankali gareta tayi yace," ya akayi ina jinki , Amm dama dan Allah ina Neman wata yar Alfarma ne ? hankalinshi na kan wayar ya amsa mata da ina jinki , amm dan Allah dama so nake kadan kaini gidan Hajiyanka , naga ban taba zuwa ba kuma kaga Baka taba bani mun gaisa ko a waya ba , shine naga tunda na samu sauki dan Allah kataimaka naje na dubata , kaga yanzu kai da ita kune dangina , tunda na rabu da nawa iyayen, duk da suma inaso naje na dubasu na roko ya yafiyarsu ko zasu yafemun , amma kafinan inaso naje na gaida hajiyanka kaji tafada murya a sanyaye..... .

Tunda juwairriya ta fara magaba Khalil bai jiyo ya kalleta ba , sai da yaji ta ambaci iyayenta ya mai da hankali yana kallanta .

Bayan taga ya fara yimata kallon rainin wayo yace," Amm kinajina ?
cikin jin dadi tace," eh ina jinka tafada gamida sakin murmshi ......

Had'e rai yayi yace," ke nifa banasan muna furci banzan da hofi ni zaki nuna ma wayo , munafuka kedai kawai kice kinaso kije ganin
Iyayenki ba Hajiya naba , in zaki fito mun a mutum ki fito mun , kinasan iyayen naki kika rabu dasu ? Suna sonki suka rabu dake? Ohh shine yanzu zaki kawomun iskanci ko ?to sai ki zaba ko nan ko can , sannan in kinje kar ki kuskura ki dawo mun gida na tunda bana ubanki bane ko da yake na ubankin ma ya gagareki , karkisake kidawo kinjin koh yafada cikin tsantsar rashin mutunci da rashin ta ido...........

Tunda Khalil yafara magana juwairriya ke fitar da hawaye masu matukar zafi...

Kasa ta saukko ta durkusa a gabanshi cikin muryar kuka take fadin," haba Khalil meyasa kakemun haka ne ? Meyasa kazama mugu maras tausayi , meyasa Abu dan Kadan sai ka fara mun kora da hali, Khalil wallahi tallahi kaci amana ta, kwata_kwata watan Mu daya ne da kwanaki ni dakai amma duk ka sauya duk ka canza Ashe haka kake, Ashe Alkawarin da kayimun na karya ne , Ashe duk Son da kake nunamun na karya ne , tabbas nayi wauwuta kuma hakan ya faru ne *A SANADIN KUSKURENA* Shiyasa kake mun haka , numfashi taja tace," Khalil A lokacin da na fada maka cewar babana ya bani zabi na zaba ko shi ko Kai , a lokacin da sai kacemun in hakura dakai , kai bazaka rikeni ba , bazaka auren ba ,ko naki ko naso zan hakura ,ko da kuwa zan rasa raina sanadin sonka amma Khalil bakayi hakan ba , sai ka ansamun da cewar zaka rikeni amana , fashewa tayi da matsanancin kuka tace," Amanar kenan ? Amanar kenan da nake gani yanzu , aure tun ba,aje ko inaba anfara samun irin wannan matsalolin?
to wani irin zama zamuyi kenan dakai ? Ya rayuwarmu zata kasance lallai nasan sai ciwon zuciya ya kamani , Khalil ka rabani da iyayena sanadiyyar soyyaiyarka , Khalil naki dan uwa na jini sanadiyar sonka ,duk da son da yaya haidar yake mun ban damu ba na nuna ko a jikina , nace sai kai , Khalil babu Wanda yake zuwa Inda nake daga dangina har naka , ka rabani da cikin dake jikina wala Allah shi kadai ne rabona a duniya , ta yuyu shine Wanda zai dinga debemun kewar dangina, Khalil ka rabani da shi , son da kake nunamun a baya yanzu duk ka daina , babu koda kwatan san da ka ke nunamun a daa, Khalil ya kakeso nayi dan Alllah tafada gamida fashewaa da wani matsanancin Kuka mai ban tausayi.... .

A zafafe ya mike ya dagota tsaye , ya tsinketa da wani gigitaccen mari , yana huci cikin tsantsar bacin rai ........

A gigice ya dago fuskarta idonta kar akan nashi , tana kokarin hadiya kukan dake kokarin zubo mata , amma hakan baisa hawayenta dake makale a donta suka zuba ba.....

Bakinta na rawa ta kara kallan Khalil tace," Khalil! mari ? Mari? Nii? Wani matsanani kukan da ta gagara hadiyewa ta fashe dashi tace,"nagode, tafada muryar ta na rawa .......

Cikin fada da bacin rai yafara magana yana fadin," how dear you! daza kizo kina far fadamun magana Sun ranki , ni sa,anki ne , ni na rabaki da iyayenki ? ni nace dole sai kin aureni , shine zakizo kina mum iskanci da rashin kunyar da kika saba a gidan iyayenki , nunata yayi da yatsa yace," kuma ke bari kiji na fada miki abun da baki sani ba ,kinga wannan yarinyar da tazo kwanaki gaskiya tafada miki karuwa tace karuwa tace karuwatace in kin ga dama bakin ciki ya kashe ki mutum ke kikayi asara bani ba, kuma ciki ne NASA kin zubar din ,kuma ko yanzu kika kara samun wani cikin to tabbas abun da zai kara faruwa kenan na fada miki , sannan in kin ga dama ga hanya nan kar ki kara ko minti daya a gidannan ki tafi gidan ubanki bani da asara na fada miki .........

Girgiza kai juwairriya tafara cikin kuka tace," kai wallahi ina tantama anya Khalil anya Kaine kuwa Khalil dina bazai mun haka ba bazai mareni , dan Allah na farka in barci nake , naso ace wannan abun a barci ne da wallahi idan nafarka bazan sake komawa ba , wani mari ya kara sauke mata a dayan fuskar yace," yauwa yanzu nasan kin farka in barci kike kalleni da kyau dakyau nine ibrahim Khalil fatan kin gane ni, yana fadan haka ya fara kokarin fita.....

Da sauri tasha gabanshi tace," Khalil dan Allah dan Annabi kayi hakuri , batareda ya kulata ba ya wuce ya fita abunshi rai a bace .......

Bayan ya fita faduwa tayi a kasa ta Kara fashewa da wani matsananci kuka gamida fadin," nashiga uku na lalace na tabbata ban ga Komai ba wannan kadan kenan daga illar bijirema iyaye dole na nayi hakuri na dauki kadara , kaddarata kenan kuma hukunci na kenan , waiyyo Allah tafada cikin muryar tausayi......

Haka taci kukanta ta koshi ta tashi ta nufi dakinta ta kwanta barcin azaba yayi gaba da ita, ga matsanancin cion kai..... .

Misalin karfe Tara na dare Khalil ya shugo...

Daki ya nufa yaga juwairriyan tayi barci...

Kallanta yayi ya tabe baki , gamida Jan tsaki shima ya kwanta abunshi.......

Washe gari da safe , da fara,a juwairriya tagaida Khalil shima ya amsa ba yabo ba fallasa .

Misalin karfe tara juwairrya tafara kokarin shirya musu break fast...

cikin yan mintuna ta gama , takai kan dinnig ta ajiye ,tana jiran fitowarshi , jin shuru shuru bai fito ba yasa ta nufi dakin ta Tatarar dashi yana kwance yana danne_dannen waya..

Murmshi tayi cikin sakin fuska tace," sannu da hutawa , yauwa yafada a takacie .
Amm dama nagama haa mana break fast ne yana kan dining juwairriya tafada cikeda lallabi....... .

To ganinan zuwa ya fada gamida mikewa akan gadon , fita tayi shima ya bita a baya , suka nufi dining ........

Abincin ta zuba mishi ya fara ci itama ta zuba ta fara ci .

Bayan sun gama cikin sakin fuska juwairriya tace," amm dan Allah ya maganar zuwa gidan Hajiyan , in zakafita sai mutafi tare ko? In ba damuwa kaji ?

Ba yabo ba fallasa yace," shikenan in kin shirya shikenan , Barin yi wanka sai mutafi , cikeda farin ciki tace," to shikenan nagode barin gama kafin kayi wankan , tafada gamida tashi tafara hada kayan plates da cups din .....


Misalin karfe 11 na rana suka gama shiri , kai tsaye gida Hajiya yafara kaita ......

Shiga cikin gidan sukayi.
Ita kam juwairriya jiki a sanyaye tana me fargabar irin halin da Zata riski Hajiyan Khalil akanta .......

Zaune take tana kallon TV a kasaitaccen falonta .....

Cikeda mamaki take kallanshi tace," A,a to fa yau kune a gidan sanunku , Ai da kun fadamun zakuzo Ai.......

Neman guri sukayi suka zauna ,Khalil yayi murmshi yace," wallahi kuwa Hajiya na yau da safe tace in kawo ta shine muka shirya muka taho , Allah Sarki Hajiya tafada ......

Cikeda girmawa da risinawa juwairriya ta saukko kasa cikin ladabi , gyalenta ya dan rufe fuskarta , tace," Sannu Hajiya ina wuni , cikin sakin fuska hajiya tace," lafiya kalau ya jiki? nagama jikin yayi kyau sossai to Allah ya kara sauki , Allah ya bada mai zama , tunda wancan mun rasashi.... .

Kara sunkuyar dakai juwairriya tayi ta na me mamakin yanda akayi Hajiyataji labarin cikinta , to ko Khalil ne yace tayi 'bari ?eh kam shine ya fada mata tabbas dan kuwa babu yanda za,ayi ta sani, in har ba shi ya fada ba... ..

Tashi ki zauna akan kujerar mana ai bakya zauna a kasa ba ko Hajiya tafada .......

Dariya juwairriya tayi tace," to nagode , gamida tashi ta zauna akan kujerar .....

Minti talatin Khalil yayi ya tashi yafara kokarin tafiya yace," Amm zan tafi , so anjima da daddare zanzo na daukeki kinji , to tace , gamida fadin," adawo lafiya .....

A daddafe dai juwairriya take a gidan Hajiya , in da babu wata kwakwarar hira da ta shiga tsakaninsu....

Bayan yan mintuna larai mai aiki ta zuba mata abinci , ta kawo mata taci, ta tashi tayi sallah ta Kara komawa ta zauna batareda da ta sake ba kasancewar Hajiyan bata ba ta wani fuskar sakewa ba ,hasalima Hajiyan dakinta ta tafi ta barta ita kadai a falo tana kallo ,Laure kuma na aikinta....

Hakan yasa juwairriya tafara Allah Allah Khalil yazo su tafi gida dan kuwa duk a takure take, ta kosa taje gida ......

Misalin karfe takwas na dare juwairriya ta iddar da sallar isha'i , jin karar motar Khalil yasata sakin Ajiyar zuciya tace," Alhamdulillah nagode Allah tafada cikin ranta......

Yana shigowa itama Hajiya ta fito a cikin dakin..
Cikin sakin fuska tace,"Yaro kadawo?

eh nadawo yafada cikin sakin fuska , yanzu zamu wuce gida ne ...

Tashi juwairriya tayi ta fara kokarin daukan Jakarta tana shirin tafiya ..
Sallama sukayi ma Hajiya gamida tafiya gida.....

Bayan sun iso gida , cikin sakin fuska Khalil yace," kin gajiko?
murmishi tayi tace," A,a ba wani gajiya , okay shikenan kinci abinci ? Ehh tace," yace okay nima naci a waje , yanzu me yarage?.

Dariya tayi tace," nikam barci kawai zanyi , okay to muje mu kwanta kawai , to tace gamida tafiya suka nufi bedroom cike da farin ciki.......

*A gurguje*

Bayan sati biyu , ba laifi juwairriya da Khalil basu yi wani hayaniya ba ,domiin kuwa,tunda juwairriya ta fuskanceshi hakan yasa take kiyaye duk wani abun da zaisa ya ci mutuncinta....

Hakan yasa duk abun da zaiyyi sai dai ta kalleshi ta jure , batareda da ta tanka ba , amma hakan bai hanashi yin rashin mutuncinshi ba in yaso . ......

In yan rashin mutuncin suka tashi haka zai rufe ido ya mata rashin mutunci , sai dai tayi kukanta ta share ........


A bangaren su mummy kuwa!! duk yanda mommy taso daddy ya yarda akan batun juwairriya amma fur daddy yaki amincewa...

Hakan yasa ya yanke hukuncin cewar duk randa ta kuskura ta sake mishi maganar juwairriya to tabbas a bakin aurenta...

hakan yasa mummy ta yi ma kanta alkawarin bazata karayima Abban juwairriya maganar ba tunda har ya yanke wannan mumunan hukunci ...

Saidai ta zauna shuru tana hawaye tana tunanin yar tata .......

Su yaya suhail ma da yaya Al_Amin tun abun na damunsu har suka fara share wa, kasancewar shima daddyn nasu sunga alamar bai damuba...

Hakan yasa suma suka mai da hankalin akan Neman aurensu da sukeyi , dan kuwa an tsaida cewar rana daya za,yi musu aure su uku , suhail Al_Amin da husna , Inda daddy kullum yake matsa haidar akan cewar yayi kokari ya nemi mata shima dan son samunshi ya hadasu su hudun yayi musu Auren gata.......

Ita kam husna duk da a cikin zuciyarta hakan baya mata dadi na rashin yar uwar ta amma hakan bai hana ta jin dadin hukuncin da daddy ya yankemata ba,hakan zai sa tayi hankali nan gaba......

hankalinta kwance take shirye _shiryen bikinta , kasancewar ya rage sauran watanni biyu da kwanaki......

A bangaren haidar kuwa ,duk yanda yan mata suke kawo mishi Kansu Sam basa gabanshi ,dan shi har yanzun ya gagara cire juwairriya a ranshi ,hakan yasa ya dauki aniyar cewa ba yanzu zai yi aure ba sai ya tabbatar da cewar juwairriya ta fita a ranshi kafin yaba zuciyarshi gurbin wata 'ya mace ba ......

Duk yanda mahaifiyarshi taso yayi aure yaki a cewarshi aure lokaci ne .......

Bayan wata daya wani cikin yakara baiyyana a jikin juwairriya.....

Da murnarta a wanan karan ta fada mai a tunaninshi zai yi na,am da cikin , sai taga sabanin haka..

Haka ya kara tursasata takara zubar da cikin a cewarshi akwai abun da yake jira tukunna kafin ace ya haihuwa , haka ta yi kuka ta share hawayenta , ba dan taso ba ta amince aka zubar da cikin....

Sai dai wanan karan tafi wahala akan wancan ,sabida cikin sati shida ne , tayi bleeding sossai harda guda guda kamar bazatayi rai ba .......

Bayan sati biyu ,taji sauki sossai ..

Zaune take tayi shuru tana tunanin rayuwa .

firgit ta mike ta dauki gyalenta kasancewar Khalil baya gida ya yi ya fita.....

Hakan yasa ta yanke shawara zuwa gidansu ko Allah zai sa mahaifinta ya saduda in ya ganta yace ya yafe mata......

hakan ko tayi cikin karfin hali batareda da ta karaya ba , takuma tabbatar da cewa mahaifinta zai yafe Mata in taje ta rokeshi, kuma tasan zuwa yanzu tasan ya saukko.......

Kai tsaye ta fita ta bar gidan ta rife gidanta , ta taro mai adaidaita ta nufi hanyar gidansu .......

Tunda ta fita gabanta ke ta faduwa tana tsoron yanda zata Tarar da daddynta , gamida da Addu'ar Allah yasa ya yafe mata ........

Cikin 'yan mintuna ta isa gidan Inda ta sallami mai Napep din ...

Gabanta na faduwa jikinta na rawa ta fara kokarin tura gate din gidansu , cikin sand'a take kokarin Shiga , cikin gidan......

Daidai lokacin da daddy ke kokarin fita mommy na rakoshi a baya ne juwairriya kuma tana nufo hanyar......

Turus tayi ta tsaya, ganinshi a gabanta...

ganinta kai tsaye yasa daddy ya hade rai lokaci daya sabanin daa dayake cikin farin ciki da annashuwa .. .....

Wata razananniyar tsawa ya dakamata yace! Ke daga ina ,me yakawo ki gidana waya baki izinin kizo mun gida?
dan ubanki ya mukayi dake wallahi tun wuri ki ficemun daga gida tun kafin nayi miki mahaukacin duka....

Da Sauri mommy ta karaso dan ganin ko waye haka?

duk da cewar jikinta yaso yabata juwairriya ce , amma saida ta matsa ta kara gane ma idonta....

kallanta tayi amma Sam ta gagara magana , ganin yanda tayi rama yasa ta jin ba dadi a zuciyarta .....

A tananin ta zata ganta tayi kyau tayi bulbul abunta , amma sai taga sabanin hakan , hakannne ya tabbatar mata da cewa juwairriya ba ta cikin yanayi mai dadi a gidan aurenta ......

Durkusawa tayi a Kasa ta hada hannayenta guri daya tana kuka tace," daddy dan Allah na rokeki ka yafemun daddy nasani nayi kuskure kuma *SANADIN KUSKURENA* shi ya jazamun duk halin da na Shiga , daddy na tuba kadubi Allah ka yafemun kayarda kaddarata kenan tafada gamida Kara fashewa da matsanacin kuka gwanin ban tausayi.....

Ranga_ranga daddy ya nufi kanta ya kwada mata mari yana huci, idanuwanshi sunyi jawur, yana tunawa da bijire mishi da tai, hakan kuma na kara hura wutar tsananta cikin ranshi , yanaji ma kamar ya kasheta ya huta dan kuwa baya San ganinta , baya kaunar ganinta ....

Cikin matsanancin bacin rai yace," juwairriya ni ! Wallahi ban haifi dan da zaifi karfina ba , kuma na fada miki babu ni babu ke kije ki nemi wani uban amma bani ba , juwairriya babu irin rokon da ban miki ba ,amma kika watsamun kasa a ido ,shine yanzu zaki zo kina nadamar munafurci ,sai da lokaci ya kure ....

Cikin bacin rai yakara mata wani marin a fusace yana huci ..

Wani kara tasa ,ta kara fashewa da wani azababben kuka ......

Jin hayaniya da kuka yasa husna ta fito da gudu ,su suhail ma suka fito...

Ga mamaki suke kalan juwairriya .

Cikin kuka juwairriya ta nufo momy gwaiwowinta akasa tace," mommy dan Allah ki cema daddy ya yafemun dan Allah...
Hawaye kawai mommy ke fitarwa zuciyarta cike fal da tausayin yar tata amma ta gagara cewa Komai sai kuka da takeyi .......

Ganin mommy ta gagara magana yasa ta kara jaa

Please Login or Register in order to submit comment