Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sauri dan taje taga muradin zuciyarta .

Duk da cewa tanajin dacin mutuwar Abban haidar sossai , amma wani zuciyar na tsananin bukatar khalil kusa da ita, ita kanta taso tafiya Maiduguri , Amma Sam zuciyarta bazata taba iya jure rashin ganinshi ba na 'yan kwanaki , dan ita kanta tana mamakin San da take mishi ..

Ganinta tana dosawa daukeda da fara,a A fuskarta yasashi tunanin cewa kamar ba ita aka ma mutuwa ba ?, da kallan mamaki ya bita har ta iso gurinshi .

Bude kofar motar tayi , sassanyan turarenta ne ya doshi hancin shi dayasashi lumshe lumsasaun idanunshi .

Ganin yanda ya dauki wanka yasa juwairriya ta kara narkewa a sanshi , cikin zuciyarta tana me kara ma Allah godiya da ya bata khalil a matsayin mijin da zata aura , kuma dole ta rikeshi hannu bibbiyu bazata ta taba sakacin rasashi ba domin khalili mijin nunama sa,a ne .

Cikin sanyin murya juwairriya tace," Assalamu Alaikum !!, Amsawa tayi da muryarshi mai dadi yace," was,alaiki salam ,gaisheshi tayi cikin sakin fuska , amsawa yayi daukeda murmishi a fuskarshi , kasancewarshi me fara,a ne , numfasawa yayi cikin sigar tausayi yace," juwairriya ya hakurinmu kuma?? .

Cikin sanyin muryar ta kad'a kai tace," Alhamdulillah ! mungode Allah , toh Allah ya jikanshi yayi mishi Rahama Allah kuma yasa ya huta , da Ameen ta Amsa .

Numfasawa yadanyi yace," Ai nayi tunanin bazan sameki ba dama na zo miki gaisuwa ne ina ne gidan rasuwar?.

Ai ba anan garin yake ba shi a garin borno yake da zama , su mommy sun tafi ni kadaice a gida ni banje ba .

Zaro ido yadanyi yace," bakije ba ? amma meyasa bakije ba kuma kince kowa ya tafi?.

Kaii!! Nii !! nikuma ??, eh Kaine dalilin dayasani banje ba , da mamaki yake fadin," juwairriya taya zan zama dalilin rashin zuwanki Gidan mutuwar yayan babanki ??.

Juyowa tayi ta kalleshi ido cikin ido tana Kare mai kallo tace," khalili!! Amsawa yayi da Na,am!! .

Kara juyawa tayi tana kallanshi ,gamida tattaro dukkanin nutsuwarta da hankalinta tace," wallahi inasanka , naki zuwa ne kawai dan bazan iya deban kwanaki batareda ganinka ba , ina sanka ina kaunarka dan Allah kaima kace kana sona kaji!? tafada kamar zata yi kuka .

Tunda juwairriya tafara magana Khalil ke Kallan dan karamin bakinta , yanda take magana yasa yaji ya kara Santa matuka ,domin yanda take magana yayi matukar bigeshi , ji yake tamkar kar ta daina .

Wani kayattacen murmishi yayi da ya baiyyana lotsatsun dimples dinshi yace," juwairriya wallahi Nima inasanki so na hakika , ina matukar kaunarki duk da cewa bamu dade da sanin juna ba amma ina sanki ina kaunarki , nima kimun Alkawari dagani bazaki kula kowa ba sanan bazaki taba rabuwa dani ba .

Da Sauri tace," nayi maka Alkawari nima inaso kamun Alakwari dan Allah , Na miki Alkawari yafada cikkn zallar soyaiyya .

Zaka Aureni!!?? tafada tana kallanshi , eh zan aureki juwairriya matukar kema zaki aureni , jin yace zai aureta takara jin farin ciki marar misultuwa ,toh yaushe ? yaushe zaka aureni , dariya yayi yace," yaushe kika shirya? "Ni ina tunanin daddy bazai miki aureba yanzu juwairriya duk da , bansan tsarin gidan Ku ba amma sai nake tunanin kamar baza su aurar dake ba yanzu .

Dariya tasa tace," waya fada maka sai dai in in nace banaso domin duk abun da nakeso to shi daddy na yakeso , nasan bazai hanani yin duk abun da nakeso ba , ni kaina bani da niyyar aure yanzu a tsarin rayuwata sai na gama jami,a kafin in yi aure amma zuwanka ya ruguza wanan hasashen kwata _ kwata , na canza shawarar auranka koda kuwa a yanzu ne .

Cikeda da mamaki yake kallanta cikin ranshi yana me mamakin irin San da juwairriya take mishi , duk da cewa ba abun mamaki bane domin 'yan mata da yawa sun haukace akan sanshi , amma Sam su basa gabanshi , juwairriyan dai kawai yakeso , ya kayi shuru yaushe zaka turo Gidan mu?.

Saurin dawowa yayi saga dogon tunanin da yakeyi , yace," inshllahu nan da wata daya zakiji kwakwarar magana kafinan daddy na yadawo daga Abroad sai in sameshi miyi magana , Nima banaso abun ya dauki lokaci mai tsayi batareda da kin zama mallakina ba , cikin jin kunya tayi dariya hade da farin ciki fam cikin ranta shima dariya ta bashi .

Hira sossai suka ci gaba dayi kamar ba ita akama mutuwa ba , nan yayi magriba yayi isha,I , sai misalin karfe goma saura ya tafi, a hakan ma dan ya matsa zai tafi ne amma juwairriya ta hanashi fur wai ya yi wuri , badan taso ba ya tafi , bisa Alkawarin zai kirata , itama ta fita ta Shiga gida ya barta cikin kewa da tsananin kaunarshi , da soyaiyyarshi .

Tunowa tayi da mutuwar da aka mata tayi , nan jikinta yadanyi sanyi tana mejin zafin rasuwar Abban haidar.


Misalin karge goma da Rabi haidar ya kirata , farin ciki sossai tayi ganinan kiranshi , nan suka dan taba hira daga bisani sukayi sallama badan taso ba sai dan ya bukaci hakan .

Tunowa tayi dasu mommy bata kira taji ko sun sauka lafiya ba , itakam shaf ta manta , cikide da damuwa tafara kokarin Kiran wayoyinsu amma Sam yaki Shiga , haka taita trying numbansu har barci ya kwasheta , kasancewar tana tare da khalil har ta manta ma bataci Abincin dare ba sai cikin dare da tadan ji yunwa ta tuna da bata ci Abinci ba , da haka tadanyi barci a daddafe tana me tunanin halin da su mommynta suke ciki ....✍️✍️✍️.

*MUJE ZUWA*

*KUYI COMMENTS KUGA TYPING.....*🤷‍♀️


*COMMENT*

*SHARE*

*LIKE*

*&*

*VOTE*

*BY MUM FU,AD*


💐💐💐💐💐💐💐

*A SANADIN KUSKURE NA*💐💐💐💐💐

*MALLAKIN*👉 *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
*AND NOW*👇
💐💐💐💐💐 *A SANADIN KUSKURENA*💐💐💐💐💐

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*Page 17&18*

*Gaskiya rashin comments dinku na karyarmun da guiwa, hakan yasa na fara tunanin ko littafin baya muku dadi ne?? In baya muku dadi gara kawai na hakura na daina ba kaina wahalar typing , amma da yawanku suna karantawa amma babu dogon sharhi gaskiya Ku gyara*.

***************

Misalin karfe biyar na yamma su mommy suka isa garin mai duguri , sunso Kiran juwairriya ,kasancewar babu caji yasa basu kirata ba .

Tarɓansu akayi cikeda jimami .

Ganin basa tare da juwairriya dadyd ya Shiga tambayarsu tana ina?? .

Nan mommy tamishi bayanin duk yanda sukayi .

masifa yayi tayi akan anbarta ita kadai a gida , yana me jin haushin hukuncin da Hajiya luba ta yanke na barinta a gida .

Duk yanda Hajiya luba taso mishi bayani Sam ya ƙi yarda, duk ya dauki laifin ya ɗaura mata , kamar ita ta hana juwarriyan zuwa .

Wayarshi ya daukko ya faro ƙoƙarin kiran juwairriya .

Ganin daddynta ne yake kiranta yasata jin sanyi cikin zuciyarya , dan tasan su mommynta sun isa lafiya duk da cewa bata tabbatar da hakan ba .

Dauka tayi da sallama, batareda ya amsa mata sallamar ba yace," Haba juwairriya yazaki ki ƙi zuwa , bayan kowa yazo ke kadai ce baki slzo ba meyasa ??.

Cikin muryar shwagwaɓa tace," daddy muna da exams a school ne Shiyasa ban bisu ba , but I,am very sorry kamun Afwa .

Cikin ɓacin rai yace," gaskiya banji daɗi ba naso ace kinzo kowa ya ganki , amma Allah sa hakan shi yafi Alkhairi , da Ameen ta Amsa daga bisani ya tambayi lafiyarta ko da abun da take bukata , da haka sukayi sallama tace," ya gaida da momynta .

Duk Wanda yaga Hajiya luba sai ya. tambayi juwairriya , sai dai Hajiya luba tace," Suna da jarabawa ne Shiyasa bata zo ba .

Haidar ma ya tambayeta , amsa daya kawai take bayarwa cewa sukna da jarabawa a makaranta .

Da haka aka gaggaisa akayi gaisuwa cikeda jimami da sanyin jiki .

Tunda Hajiya luba suka zo garin maiduguri batareda da shalelenshi daddy ba hakan yasa kwatakwata hankalinshi na kanta, kullum tunani shi wani hali juwairriya ke ciki .

Hakan yasa kullum cikin kiranta a waya yake , ba dare ba rana domin duk hankalinshi ba a kwance yake ba , burinshi ayi ayi ayi sadakar uku ya tafi gida , saɓanin da,a da yake da niyyar bari har sai anyi bakwai , amma baya tunanin hakan zai yiyu .



Hankalin juwairriya a kwance yake , batada wata damuwa kasancewar tana samun kulawa daga gurin khalil dinta , kullum soyaiyyarshi kara bunkasa take a cikin ranta , domin ba karamin so take mishi ,kullum sai Khalil yazo sunyi hira , ko watarana su dan fita hankalinta kwance , makaranta da school ma duk ta rage zuwa ba kullum ba , a layinsu har sun fara sa mata ido suna gulmarta , amma Sam hakan bai dameta ba .

Yau akayi ukun Abban Haidar , dalilin juwairriya yasa babanta san komawa gida , sai dai daƙyar Hajiya luba ta shawo kanshi akan ya bari sai anyi bakwai, badan yaso ba ya hakura dan ba yanda zaiyyi .

Cikin kwanakin kullum tunanin juwairriya yake , hakan yasa ya yanke shawarar cewa suhail da Husna su koma gida su zauna tare da juwairriya ,dan Sam hankalinshi bai kwanta ba barin ta ita kaɗai a gida.

Hakan kuwa ba dan su Husna da suhail sunso ba suka koma gida .

Misalin ƙarfe shida suka dawo gida , ganin rantsatsiyar mota a kofar gidansu yasa suhail da Husna suka haɗa ido suna san hango ko suwaye a ciki , kara gaba sukayi suka ga juwairriya da khalil zaune suna hira cikin farin ciki .

Kai tsaye gida suka nufa , saurin fitowa khalil yayi yaɗan duƙar da kai a ƙasa yace," sannu da dawowa , wani kallo suhail ya bishi dashi yace," yauwwa rai a haɗe, yana faɗin haka ya wuce gida batareda ya kara juyowa ya kalleshi ba , ita kuwa husna har ta wuce gida domin bata ma bukatar ganinshi .

Jiki a sanyaye ya dawo cikin mota , ita kuwa juwairriya na zaune , ganin yanda yaya suhail ya amsa ma khalil yasata jin haushi , kallanshi tayi tace," uhm karkadamu da yanda yaya suhail ya maka, daɗin abun ba shi zai baka aurena ba ehee., daddy na ne zai baka aure na sabida haka kar wanan abun abun ya dameki , kaji masoyina , murmishi yaɗan kwakulo da baikai zuci ba yace," to Allah yasa , Yakamata kije ko ?kinga sun dawo daga tafiya , Yakamata kije kimusu sannu da dawowa tunda sun dawo ko?, Cuno karamin bakinta tayi cikin sigar shagwɓa tace," har ka gaji dani kenan ? yanayin yanda tayi , dariya yaso bashi yaɗan gimtse ta yace," A,a baby ba haka bane , wallahi a kullum ina matukar san kasancewa dake , kawai dai ya kamata kije kkyi ma su yaya sannu da zuwa , ba dan taso ba ta ta buɗe kofar motar ta fita rai a bace , dariya ta bashi sosai yana me mamakin son da take mishi , da wanan tunanin yaja motarshi ya tafi cikin farin ciki .

Ko da ta shiga gida kai tsaye daki ta shiga , ta tarar da suhail da Husna suna zaune suna hira , turo baki tayi .

Kai tsaye cikin daki ta nufa batare da ta kulasu ba .

Wata razananniyar tsawa suhail ya dakamata yace," kee!!dan ubanki baki ga mutane bane da bazaki musu sannu ba , bakida hankali ne , ko kuma tsabar rashin kunya ce datake damunki , kuma ma waye wancan da muka gani dashi a waje ?? har kina Shiga cikin motarshi tsabar baki da hankali , dama nasan tunda kikace bazaki bimu barno ba nasan akwai abun da kike shirya , Ashe kinshirya sheƙe a yarki ne koh??,tunda suhail ya fara magana juwarriya ta juya mishi keya , murya kasa_ kasa take kunkuni tana harare _ harare, ba magana nake miki ba juwarriya ?yafada cikin faɗa da bacin rai kallanshi yayi ta harareshi , ta wuce dakinta da sauri .

Tashi yayi ya bita , ya tokari ƙofar dakin , a tsorace ta kalleshi .

Curo ƙatan belt din dake manne a cikin lafiyaiyyan jeans dinshi yayi ,cikin matukar bacin rai yafara zuga mata , ihu takeyi sossai tana fadin," Allah ya isamun ,mugu Azzalumi , wallahi sai dai ka kasheni , in Har dadday ya dawo wallahi sai na fadamishi , mugu , zuga mata belt dn Ya cigaba dayi , yana haki yake fadin," dan ubanki har ina miki magana kina wani banza dani tsabar kin rainani , ko dan kinga ina barinki ne, kin raina kowa a gidanan , ke koh mutuwar Abbban haidar ma bata dameki ba , tsabar kin raina mutane baki da mutunci Har kina kawo mana ƙato kofar gida , kina abun da kikaga dama , toh wallahi baki isa ba na fadamiki , kuma daga yau inn na sake ganin wani a kofar gidanan kinsamln Allah sai na miki dukan da sai kin kwanta a asibiti , yana faɗin haka ya fita yabar ɗakin yana huci , kuka sossai juwarriya takeyi ,kamar ranta zai fita, cikin ranta ji take kamar ta kama yaya suhail ta caka mai wuka dan ta huce bakin cikinta , da sauri ta miƙe kamar an zabureta ta yi saurin ɗaukko wayarta , goge hawaye fuskarta tayi ta fara dailing numbern daddynta .

Ganin sunan da ya sama juwairriya ya baiyyan akan screen din wayarshi yasa shi saurin ɗauka ,yace," juwairriya lafiya ??, wani wawan ihu tasa , tana faɗin," waiyyo daddy!! waiyyo daddy!! na shiga uku!! daddy yaya suhail !!yaya suhail yaya!! suhail!! zai kashenk!, daddy wallahi gidanan zan bari daddy , yaya suhail ya tsaneni .

A matukar rikece muryarshi na rawa yayi saurin faɗin," juwarriya make damunki ki nutsu kimun bayani me suhail din Yayi miki??, kara wage karamin bakinta tayi tace," daddy ni dai kawai gidanan zan bari daddy in ba haka ba yaya suhail kaheni zaiyyi ,wani dogon numfashi yaja, yace," juwarriya ki nutsus kimun bayani me suhail din ya miki ??, nan taɗan tsagaita kukan tace," daddy babu abun da nayi mishi yana dawowa ban mishi komai ba ya fara duka na wai dan ban bisu mun taho Maiduguri ba yafara dukana kamar zai kashe , yanzu haka a kwa ce nake na kasa tashi .

Cikin ɓacin rai da tashin hankali dadday yace ," kuyi hakuri ina zuwa zan kira ki kinji ki share hawayen ki , to tace cikin sigar shagwɓa ta kashe wayar tana me jin daɗi cikin ranta ,dan tasan ko ba komai tasan yaya suhail ya shiga uku , da haka ta tashi ta kwanta tana me jiran kiran daddynta.....✍️✍️

*Muje zuwa*

*Ina kunyi comments mu cigaba ina bakuyi in kara tafiya hutu , har sai randa ta rayamun in dawo💁‍♀️*

*Dan Allah kusa kawata a Addu,a da bakuna ku masu Albarka, Allah ya fitar da ita daga cikin damuwar da take ciki.*


*COMMENTS*

*VOTE*

*&*

*SHARE*

*BY MUM FU,AD*


💐💐💐💐💐💐💐

*A SANADIN KUSKURE NA*💐💐💐💐💐

*MALLAKIN*👉 *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
*AND NOW*👇
💐💐💐💐💐 *A SANADIN KUSKURENA*💐💐💐💐💐

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*Page 19&20*

*Walllahi tallahi duk Wanda bata comment zan cireta, ko kuma indinga bin wa Inda suke min comments ina turamusu ta private, mutum zai zauna ya bata lokacinshi yana muku typing dan nishadantar da Ku ,da rubuta abun da zai amfanemu amma kwata _kwata Ku ba kwa gani , rashin comments dinku shi ya kara kashemin jiki , Shiyasa bana typing akai akai , abun da duk Ku kuka ja hakan , sabida haka wanan shine na farko kuma na karshe , Wanda zaiyi comments to Wanda bazaiyyi ba to fa tabbas zai jishi a waje , mutum zai shafe kusan awa nawa yana rubuta , amma comments din minti Biyu ya gagara daga ace tnx sai mungode ko kuma a wani turo sticker ko emoji sign, gaskiya Ku gyara , kuma labarin nan bai fara zafi ba chakwakiyar tana gaba , dan duk yanda labarin yake muku dadi baikai na gaba ba , kudai kuyi comments in cigaba da muku posting , naso ace littafin nan mungama shi kafin sallah amma rashin hadin kanku yasa hakan bazai yuyu ba , amma in naga kuma comments inshallahu zan Dage mugama kafin sallah , dan Allah kuyi comment*


***********************

Cikin tsantsar ɓacin rai daddy yafara kokarin lalubar lambar wayar suhail .

Ganinshi a fusace da ɓacin rai yasa Hajiya luba fadin," Alhaji wai make faruwane me yayi zafi haka ? Nasan juwarriya ce ta kiraka me tafaɗa maka ? ta jero mai tambayar cike da damuwa .

Bai tsaya bata amsa ba , sai sa6iling number suhail da ya farayi .

Ringing wayar suhail tafarayi , ganin sunan daddy ya baiyyana akan screen din wayar shi yasa gabanshi yayi mummunan faduwa , cikin ranshi yake faɗin," wanan munafukar nasan ta fada mishi wata magana da ma nasani kwace wayarta nayi a hanunta .

Ƙirjinshi Na dukan uku_ uku ya dauki wayar , bakinshi na rawa yace," Assakamu Alaikum .

Wata razananniyar tsawa yadaka mishi yace," bana bukatar sallamarka , suhail meyasa baka da mutunci ne , daaa ina tunanin fahad ne kadai ya takurama yarinyar Nan ahse kaima mugun kanka ne , wai dan Allah me yarinyar nan taimuku haka kuka tsaneta , amma dad...... Saurin dakatar dashi yayi yace," kamun shuru kar ka yarda inji bakinka in ba haka ba ranka zai baci , abunda nakeso dakai shine , gobe gobe kadawo garin mai duguri, in yaso sai mu dawo tare , dan bazaka zo kadinga takuramata ba bayan bananan , kuma bana san inji wata magana , yana fadin haka yakashe wayar yana huci yana me jin haushin suhail cikin ranshi ,sanadiyar taba mishi shalelenshi da yayi .

Ko da daddy ya kashe wayar wata 'yar iska suhail ya furzar cikin bakin ciki yace_" kai!! kai!! kai !daday why !!why! meyasa ?? Meyasa! daddy yakesan lalata tarbiyar yarinyar da ya Haifa ta cikinshi ?wani irin so ne haka har daddy ya yankemun irin wanan hukuncin haka , bai ma tsaya na mishi bayanin abun da tayi ba zaimun haka , Yanzu a sandiyar juwarriya zankara wahala in koma garin borno bayan yau dinan na dawo amma wallahi yarinyar nan kin cuceni.

damuwa sossai da ɓacin rai ya Shiga , yana me jin haushin juwarriya cikin ranshi .

Cikin matukar mamaki Hajiya luba ke fadin," Alhaji wai meke faruwane , yana ji kana maganar cewa suhail ya dawo nan meyasa ? Wannan Ai wahala ne yaza,ayi yau yaranan ya tafi, kuma ace gobe ya dawo ?.

Cikin ɓacin rai yace," ehh gara yadawo din dan bazaiyuyu ya dinga takura ma yarinya ba daga dawowarshi , har yana sa hannu a jikinta yana dukanta dan mugunta .

To amma Alhaji ka tambayeshi dalilin shi na dukanta da yayayi , ? gaskiya Alhaji wanan hukuncin da ka dauka Sam baiyyi ba , kafasan juwarriya bata jin magana ta yuyu wani Babban laifin tayi, har yasa suhail ya daketa,kasan shi ko harkar ta ba shiga yake ba .

Ganin bazai iya cigaba da sauraran maganarta ba yasashi tashi ya bar dakin ba tareda yace komai ba .

Da kallan mamaki ta bishi tana me mamakin irin yanda Alhaji mansur he shagwaɓa juwarriya da yawa .


Washe gari da safe,suhail ya fara kokarin shiryawa dan tafiya garin borno , samun su yayi suna zaune husna na kallo juwarriya na danne dannen waya batareda ya kalli Inda juwarriya take ba yasa ya maida kallanshi zuwa husna yace," Husna zan tafi mai duguri , cikeda da faduwar gaba husna tace," amma yaya suhail lafiya?? me ya faru a mai dugurun bayan jiya jiyannan muka dawo , murmishi yayi yace hmm ba komai husna kawai daddy ne yace lallai in dawo , in yaso so mu dawo tare dasu , to amma daddy akan me yace hakan ? tafada cikeda mamaki , hmmm wai akan dukan da nayi ma wanan 'yar ya nuna juwarriya datake kwance tana chart abunta hankali kwance tana taunar cingum , kai !! shine zai sa ka koma ? Eh wai zan ta kura mata yafaɗa cikin sigar shagwaɓa .

wata shu,umar dariya juwarriya ta kwashe dashi tace," uhmm kadan ma mutum

Please Login or Register in order to submit comment