Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafara gani , Indai nice , tana fadin haka ta mishi gwallo ta kwasa da gudu ta Shiga dakinta ta rude kofa.

Girgiza kai gaba daya sukayi.

Nan suhail yayi ma husna sallama ya tafi cikeda jimami da bakin ciki .


Bayan suhail ya isa mai duguri fada sossai mahaifinshi yayi mishi kamar zai dakeshi dan kuwa kiris ya rage ya dokeshi , dan kuwa Sa,arshi daya gidan mutuwane da tabbas zai iya dukanshi .

Dakyar mommy da sauran mutanen gidan suka bashi hakuri ya hakura .


Bayan kwana Biyu kullum husna da juwarriya cikin fada suke, matukar husna zata fadamai gaskiya to fa sai sunyi fada , hakan yasa husna taja bakinta tayi shuru , ta zuba mata ido , duk abun da zatayi bata taɓa mata maganar balle har tafaɗama daddy , Shiyasa take jan bakinta tayi shuruu.


Yau akayi ukun Abban haidar Inda 'Yan uwa har sun fara tafiya , suma Abban juwarriya ƙoƙarin ta fiya Suke .

Nan ya roki mahaifiyar haidar Alfarmar tafiya da haidar gurinshi dan ya cigaba da zama acan , ya kuma shaida musu cewa ya bashi juwarriya halak malak zai aura mishi ita da zaran ta gama karatun secondry, in yaso sai ta karasa karatun ta adakinshi, yayi haka ne badan komai ba sai dan ya kara kulla zumunci , yakuma cika Alƙawarin da sukayi ma junansu da yayanshi , nacewa ko bayan ransu zasu bar wasiya cewa a kulla alakar aurataiyya tsakanin yaransu , yakuma yi Alƙawarin cika mishi wanan buri nashi , yakuma kara dacewa , duk abun da mahaifiyar haisar take da bukata ta faɗamun mishi , kar taji kunyar hakan, ta sanar sashi .

farin ciki sossai sukayi gaba dayansu suna me jin daɗin wanan Al_amari , sossai haidar yaji daɗin hakan domin kuwa tun kafin juwarriya takai haka yake Santa , sai kuma Allah yasa akwai al ƙawarin aure tsakaninsu .

Sossai mahaifiyar Haidar tayi farinciki da hakan , takuma Amince da tafiyar haidar kasancewarta mace ce mai hakuri da saukin kai .

Nan Haidar yafara kokarin shirya kayanshi, ya farfadama duk Wanda ya kamata ya faɗama .

Suma shiryawa sukayi suka fara kokarin tafiya .

Godiya sossai Mahaifiyar haidar tayi musu , bayan ta ma haidar fatan Alkhairi , nan mahaifin juwarriya ya daukko kudi masu yasa ya bata , yana me kara mata godiya , itama godiyar tayi mishi , daga bisani sukayi sallama suka tafi, cikeda kewan junansu ......✍️✍️


*Muje zuwa*
*Kuyi comments in cigaba in bakuyi ba wallahi bazan kara typing ba sai bayan sallah*



*By mum fu,ad*


💐💐💐💐💐💐💐

*A SANADIN KUSKURE NA*💐💐💐💐💐

*MALLAKIN*👉 *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
*AND NOW*👇
💐💐💐💐💐 *A SANADIN KUSKURENA*💐💐💐💐💐

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*Page 20&21*

*ALHAMDULILLAH I AM BACK*

*INAYIWA DUKKAN DAUKAKIN MUSULIMI BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITA MANA, AMEEN*

*RASHIN COMMENTS ME YAWA SHIYASA JIKINA YAYI SANYI BANA MUKU TYPING , AKAI AKAI , AMMA MATUKAR ZAKU DINGA DOGON SHARHI TO INSHALLAHU ZANYI KOKARIN TYPING DAN MUYI SAURIN GAMAWA.*



Misalin ƙarfe shida na yamma su ka sauka .

Farin ciki da murna sossai Husna da juwarriya sukayi , musamman juwarriya ma , domin dawowar mahaifinta ne Yakara sanyata cikin farinciki matuka , domin ko ba ko mai zata cigaba da cin karanta babu babbaka .

Ganin Haidar yasa juwarriya jin wani kololon bakin ciki , cikin ranta tana faɗin kai wanan mayen sai da ya kara dawowa nifa bansan takura .

Ba yabo ba fallasa juwarriya tace", yaya Haidar sannu da zuwa ya ƙarin hakuri mu kuma? da murmishi dauke a fuskarshi ya amsa da Alhamdulillah juju fatan kina lafiya.

Taɓe karamin bakin ta tayi tace," Lafiya kalau , Allah ya kara hakuri , tana faɗin haka bata jira cewar shi ba ta maida kallanta zuwa gun Babanta tace," daddy me ka siyomin?.

Dariya yayi yace," haba jujun daddy kiyi hakuri kin san daga gidan rasuwa nake , kinga kuwa bazaiyuyu in siyo miki tsaraba ba , amma ki faɗa mun me kike so na siyomiki gobe inshllahu zan aika a siyo miki .

cikin sigar shagwaɓa tace," no dadday ba damuwa ai

Nan suka huta suka ci Abinci daga bisani sukayi sallah .

Bayan daddy yayi Sallah nan ya kara musu nasiha sossai game da kara basu labarin irin rayuwar da sukayi da Abban Haidar , yakuma kara shaida musu cewa Haidar yazama dan gidan nan , nasiha sossai yayi musu daga bisani kowa ya watse , sukayi isha'i kowa ya nufi ma kwancinshi .

Bayan Daddy da mommy sun Shiga dakinsu, nan mummy tafara tambayar daddy tace," Abban juwarriya Amma meyasa baka fada Alakar da za,a kulla tsakanin yaranan ba, yanzu da kayi magana fallo ? ni sai nake bani gara ayi gaggawar fada kafin ace juwarriya ta kawomana wani a matsayin mijinta koh ?.

Murmishi daddy yayi irin Nasu Na manya yace,"hmmm Hajiya kenan juwarriyan da bata kula kowa Ai baza ta taba kawo wani a matsayin miji ba , yarinyar da tace karatu zatayi kinga kuwa babu maganar miji , kuma bazata taba watsamun kasa a ido ba nifa bana shayin hadata da haidar domin kuwa nasan zata Amince , sanan inaso sai ta kammala karatunta kafin in fada mata , kinga da anyi auran sai kuma taci gaba da karatunta , wanan dalilin ne yasa ban fada mata ba .

batareda damuwa ba mahaifiyar juwarriya tace," toh shikenan Allah sa hakan ,Allah kuma ya tabbatar mana da Alkhairi , da Ameen ya amsa mata , daga bisani suka cigaba da hirarsu cikeda Annashuwa .


Kwance take tunanin Khalil take can cikin ranta , kallan sama take tana murmishi sossai a fuskarta , tunawa da fuskar masoyinta da tayi , yasa taji sanshi na kara ratsa dukanin ilahirin jikinta ,murmishi take sossai hade da far in cikin .

Jin ringing din wayarta na nema yankewa yasata saurin daukan wayan ,domin sam ita bataji ba kasancewar hankalinta baya jikinta , sai tunanin khalil dayake ratsa zuciyarta.

Ganin sunan da ta saving number khalil dashi ya baiyyana akan screen din wayarta yasata sakin wani kayatacen murmishin da ya tafito da kyawawan Hakoranta , da sauri ta dauka, jin daddaɗan muryarashi yasata lumshe idanunta, hade da jan dogon numfashi tace" Royalty!! Jin ta kirashi da daddɗan suna yasashi sauke Ajiyar zuciya yace" na,am babyna , yakike fatan kina lafiya , ya su dad & mom fatan sun dawo lafiya , dan naji kincemun yau zasu dawo koh? Uhm eh sun dawo dazunan wallahi , sun dawo lafiya kalau , Masha Allah , to yanzu ya maganar turowa na gidanku tunda daddy ya dawo , kuma Yakamata inzo in musu gaisuwa koh ? Murmishi tayi da farinciki jin khalil yace zai turo , nan ta ce," eh to ba damuwa zan fara fadamishi inyaso sai in fadamaka ranar da zakazo koh? Sossai yayi farin ciki da hakan daga bisani suka ci gaba da hirarasu cike da tsantsar soyaiyya da kaunar juna.

Ganin dare yayi sossai yasa Khalil yayi mata sallama batareda da ranta yaso ba , domin kuwa ko kwana ,zasuyi a waya juwarriya bazata taba gajiya da jin daddaɗan hirarshi mai dauke da sasanyar muryarashi na ratsa dukanin sanshi ilahirin jikinta .

Sallama sukayi cike da kewar junansu .

Tun juwarriya na waya da Khalil, Haidar keta dailing numbernta yana jin busy , sossai hankalinshi ya tashi , cikin ranshi yana Aiyya cewa ko juwarriya nada wani saurayi ne bai sani ba , shi dai a sanin da yayi mata bata da wani tsayaiyyan saurayi , amma kuma dawaye take waya haka , shine tambayar daya rasa me bashi amsa, daukan wayar ya karayi ya dailing numbern , da sauri ta daga wayan a tunaninta Khalil ne ya kara kira , ganin suna yaya haidar ne ya baiyyan a kan screen din wayan yasa murnarta ta koma ciki , tazumburo karamun bakinta tayi tace," kai Ni wanan mutum akwai shegen naci, ya wani kirani a dare an kome zaimun oho , tsohon maya kawai , ni wallahi yafara takuramun , wani dogon tsaki taja ta kalli wayar , taga har kiran ya tsinke , wani kiran ne ya kara shigowa wayar , ta ja tsaki ta dauka ,tace," hello yaya Haidar lafiya ? Kira a darenan?.

Murmishi yayi yace," lafiya kalau juju Inadai San Jin sassanyar muryarki ne , kuma tun dazu nake ta kokarin kira ki amma call waiting , dawa kike waya , haɗe rai tayi tace," kai yaya Haidar yada tambayana da wanda nake waya , Ni da classmate dina nake waya , shikenan? Batareda yaji ya gamsu ba yace," hmmm to naji shikenan Allah ya kyauta , da Ameen ta amsa , daga bisani shiru sukayi gaba dayansu , numfashi Haidar yaɗan ja yace, jujun daddy ki dan bani labarin mai daɗi mana ,harara taɗan galla kamar yana ganinta tace," uhm nikam banda wani labari , to in tambayeki mana , inaji ! Ta bashi amsa , shin ko kina da wanda zaki Aura in kin gama karatu?? Taɓe fuska tayi tace," ni bani da wanda zan aura , ni ba aure ma zanyi yanzu ba , jin tace bata da wanda zata aura yasa Haidar jin sanyi cikin ranshi yace," to amma meyasa bazakiyi aure yanzu ba ? Ni kawai ba yanzu zanyi ba , tana faɗin haka tafara kwakulo hamma karyar tace," yaya Haidar barci nakeji barin kwanta , marairacewa yayi yace," haba juju bayan bamu gama hiran ba zaki kwanta , eh barci nakeji sossai , gobe in Allah ya kai mu sai mu cigaba da hiran, to yace badan yaso ba yayi mata sallama yace kiyi barci mai daɗi , yana faɗin haka ya kashe wayar , sauke wayar tayi da ga kunanta ta turo baki ta cillar da wayar tace," uhm ko miye na tambayar nan oho , kai kasani, taja bargo , ta kwanta cikin farin ciki cike da tunanin khalili ɗinta .

Washe gari da safe suka hadu akan dining ana karyawa , sauri sauri juwarriya tayi tace," daddy nikam Sauri nakeyi barin tashi in shirya nakusan yin latti , tafada hade da tafiya dakinta dan shiryawa okay kiyi Sauri daddy yafada .

Kallan haidar daddy yayi yace," haidar ka dauki Keyn moto ka kaimun juju , kuma kayi driving a hankali , dariya yayi yace," okay daddy ba damuwa .

Nan haidar ya tashi ya dauko key .

Fita yayi ya tsaya yana jiranta a jikin Moton .

Fitowa tayi tace," daddy mommy Na tafi, to Adawo lafiya suka amsa , haidar Na jiranki a moto nace ya kaiki , wani kololon bakin cikine ya tsaya cikin ranta jin daddy yace haidar zai kaita , dariyar yake tayi tace," ok daddy ba damuwa , badan ranta yaso ba tafita cikin Bacin rai .

Ganinshi ya kame a cikin mota yana jiranta yasa ta galla uban harara tace," dubeshi dan Allah uhm , gurin ta nufa ta fara kokarin bude motar rai a bace ta zauna .

Kallanta haidar yayi yace," juju lafiya naga ranki a bace dazu fa naga kina fara,a ko an bata miki rai ne ? Ba komai tafada a takaice.

Nan yaja motarahi suka fara tafiya .

Duk yanda yaso janta da hira Sam juwarriya taki bada wanan damar , domin kuwa tunda ta hadu da khalili taji batasan haidar kwata kwata , musamman ma da Anisa tace taga Alama yaya haidar Na Santa , hakan yasa taji duk ya fita a ranta , sabanin daa da suke kaunar juna .

Haka dai ba yabo ba fallasa a haka har suka iso makaranta , kallanta yayi yace," in zo in daukeki ne in an tashi? A,a shine amsar da ta bashi , tana fadin haka ta bude kofar moton tashiga cikin makaranta .

Mamaki sossai haidar yakeyi na sauyin juwarriyya a gareshi , ko meyasa kwana Biyu take sha mai kamshi oho ? Amma dai zai cigaba da bibiyarta har Allah yasa ya gano komai , da haka yaja motorshi ya koma gida .

Gab da lokacin tashinsu daddy yakara cewa haidar ya je ya daukkota , cikeda ladabi haidar yace," daddy ai tace wai kar inzo daukanta , dan Na tambayeta , ama in kace naje sa naje .

Cikin fad yace," ita har ta isa ta zartar da hukunci da kanta , rabu da ita kaje ka daukkota kawai , tafison taita hawa adaidaita sahu yana kawota gida nikum bana San hakan , sabida haka kaje ka daukkomin ita kawai .

Batareda ya musa ba yace OK daddy Barin tafi yanzu in daukko ta.

A dawo lafiya daddy ya bashi amsa......✍️✍️


*MUJE ZUWA*


*kUYI COMMENTS INYI TYPING..*✍️✍️


*COMMENTS*

*&*

*SHARE*


*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


💐💐💐💐💐💐💐

*A SANADIN KUSKURE NA*💐💐💐💐💐

*MALLAKIN*👉 *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
*AND NOW*👇
💐💐💐💐💐 *A SANADIN KUSKURENA*💐💐💐💐💐

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*Page 22&23*

*Ku cigaba da comments in muku typing , in bakwa comments sossai zan kara tafiya hutu*💁‍♀️


Tunda juwarriya ta hango motar gidansu, Haidar na zaune a cikinta taji wani kololon bakin ciki cikin ranta .

Cikin ɓacin rai ta nufi motar , ta cuno karamin bakinta ta buɗe kofar ta zauna tace uhm yaya haidar ai da bakazo ba tunda nace kar kazo koh?

Murmishi yayi yace," Haba jujun daddy kinsan dai bazan taɓa saɓa umarnin ki ba , saidai kuma umarnin daddy yafi naki muhimmacin domin kuwa shine yace lallai sai nazo na daukeki .

Shiru tayi takara zumburo baki tace," uhm to muje , yanda tayi yaso bashi dariya , yakuma birgeshi sossai domin santa ne ma yakara darsuwa cikin ranshi matuka , da murmishi yaja motarshi suka tafi .

Kai tsaya bata tsaya ko ina ba sai dakinta , domin kuwa haushin kowa takeji a gidan .

Tunda daddy yaji bata zo gurinshi ba cikin ranshi yake Aiyya na cewa lallai yau an batawa shalellenshi rai kasancewar kullum ta dawo daga makaranta sai ta fara zuwa gurinshi kafin ta shiga daki , rashin zuwa ya takara tabbatar mishi da cewa ranta a ɓace yake .

Tashi yayi nufi dakinta dan jin ko wa ya taɓa mishi ita ?.

Samunta yayi kwance dauke da waya a hannunta tana chartting murmishi yayi yace," haba jujun daddy , yau kuma fushin a kaina zai sauka kin dawo ko kizo in ganka in San da dawowarki ? laifin me nayi miki ,ko ince laifin me muka yi miki? .

Dan shagwaɓa fuska tayi ta cuno baki tace," babu komai kawai na gaji ne kuma yau class din yau ya bani wahala , murmishi yayi irin nasu na manya yace," Aiyya to kiyi hakuri yanzu Kinsan miye? Anjima da yammah ki shirya zakufita shopping mall ki siyo duk abin da kikeso, tashi tayi cikin murna tace kai daddy gaskiya naji daɗin wanan good news din Nagode sossai sossai , murmishi yayi ya nufi hanyar fita .. juyowa yayi yace," Af na manta da Haidar zaku tafi , in Husna zata rakaku to in baza take ba shikenan ku dai ku tafi abunku, jin ya ambaci Haidar yasa murnarta ta koma ciki , domin kuwa a tunaninta driver ya kaita daganan ta kira khalil ɗinta dan su haɗu ,amma daddy zai kwafsa mata , ganin yanayi ta ya canza yasa daddy faɗin juwarriya yana ga mood ɗinki ya canza ko bakyasan ku tafi da Husna ne ? Na san dai baza kice bakyaso Haidar ɗinki ya kaiki ba koh? Murmishi yaƙe tayi tace," uhm A,a daddy ba haka bane , ina so mana, barinyi sauri in gama abun da zanyi sai in fara shiri .

Cikin farin ciki yace ,"to shikenan Allah yayi miki Albarka , yana faɗin hakan ya fita , cikin ranshi yana Aiyyana Abubuwa da dama , wata zuciyar na raya mishi cewa Anya juwarriya zata Aminta da auran Haidar kuwa domin in ya fuskancin yanayin ta , a duk lokacin da ya ambaci sunan Haidar ranta yakan ɓaci , ko meyasa ?? Wani sashi na zuciyarshi kuma yana raya mishi cewa eh babu tantama Juwarriya zata amince da auran nan ɗari bisa ɗari domin kuwa na farko yana tunanin juwarriya zata iya sadaukar da farin cikinta dan biyan buƙatar shi yayi imani ko da bataso zata Amince sabida irin san da yake nuna mata , sanan na biyu juwarriya bata da wani tsayiyyan saurayin da suke soyyaiyya dashi , na uku Haidar bashi da wata makusa domin kuwa Haidar mijin nuna ma sa,a ne, Abun da yafi tasiri cikin zuciyarsu shine , bazata taɓa watsa mishi kasa a ido ba ko dan irin san da yake nuna mata , da wannan tunanin ne yaji zuciyarsu tayi sanyi hankalinshi kwance baya kuma shakkar tunkarar juwarriya da wannan batu, domin yasan tabbas zata amince .

Kiran Haidar yayi ya shaida mishi cewa zasu fita da juwarriya , cikin girmamawa da farin ciki Haidar ya amsa da to daddy .

Ko da daddy ya fita haushi sossai juwarriya taji cikin ranta badan taso ba ta fara kokarin shiryawa rai ɓace...

Kiran Husna daddy yayi ya tambayeta ko zata je itama , kai tsaye Husna tace," A,a ita kam bazata je ba , cikin rashin damuwa daddy yace," to shikenan ...


Misalin ƙarfe hudu juwarriya tafito , tayi kyau sossai, ta saka less riga da sikel , ligt pink me Adon milk colour a jiki , tayi kyau sossai , ta murza daurin ture kaga tsiya , tasa gylenta milk colour ,da takami da jaka milk , tayi kyau sossai , zai dai kuma daka ga fuskarta kasan cewa cikin ranta ba daɗi yake mata , babu yanda zata yi kawai ,domin kuwa haushin Haidar takeji , taso ace fitar nan ita kaɗai ce da ta kira masoyinta Khalil yaga wanan lafiyaiyyan kwalliyar .

koda Haidar yaga fitowar juwarriya sai da ya kure mata kallo cikin ranshi yana faɗin Allah ka mallaka mun juwarriya a matsayin mata , kallanta sossai yakeyi har ya karaso inda yake , yanda yake kallanta yasata kara jin wani kololon bakin ciki , kai tsaya bayan moto ta buɗe ta shiga ta zauna , da kallan mamaki khalil ya bita yace," juwarriya nazama drivern ki ne? a baya fa kika zauna miye haka ? Yatsine fuska tayi ta cuno karamin bakinta tace," uhm nikam yau anan nake da ra,ayi zama , da kallon mamaki ya bita yace," to ni nace bazaki zauna a baya ba dan kuwa ni ba drivern ki bane, sabida haka ki dawo gaba batareda ta kara cewa komai ba ta taso ta buɗe gaban mota ta zauna , badan taso ba , yanda takeyi yaso bashi dariya , sai takara birgeshi, sossai motan yaja suka tafi........


Zaune yake cikin lafiyaiyyan dakinshi me dauke da sassanyan easy ta na rastsa dakin , tsayawa fadan irin kyan dakin da tsaruwarshi bata lokaci ne yana zaune yana danna laptop , cire tsaddaden gilashi fuskarshi yayi yana kara mai da hankali akan system dinshi , gefen bedsite drawer shi dauke da lafiyaiyyan Rufaida yoghurt, mai sanyi ɗauka yayi yana sha yana lumshe ido,yana kara maida hankalinshi kan system dinshi..

Da sallama wata 'yar dattijuwa ta shigo a ƙalla zata kai kimanin shekara 75 ,amma da ka ganta zaka ce batafi 55 ba ,tsabar hutu da ya ke ratsa ta yasa sam tsufanta bai baiyyana ba , da sallama ta shigo cikin murmishi tace," Ibrahim , da sauri ya dago fuskarshi dauke da murmishi yace na,am hajiiyata barka da shigo , murmishi tayi da ya bayyana kyawawan hakwaranta wanda yake sanye da golden din hakorin Makkah , tace," yauwwa sannu Ibrahim aiki kakeyi ne? .

Sosai keya yayi yace," eh wallahi amma nakusa gamawa Hajiyata, kinasan wani abu ne? da murmishi ta masa tace," eh dama na duba Freezer dina ne naga fura ta ta kare ,kuma inasan sha , kasam banaso in ba Musa ya siyomin dan shi shirme yake mun ,shiyasa nace in ba ka komai kaje kasoyimin mana , cikin sauri ya mike ya rufe laptop ɗinshi ya mai da gilashi fuskarshi ya mike cikin hanzari yace," Kai Hajiyata ai da kin faɗamun kafin ya kare da nasoyi miki da bakizo kina nema ba ai .

Dariya tayi ganin inda duk ya rikice yake sauri taɗan kallashi tace," Khalil ka kwantar da hankalinka ,ni ko bayanzu ba ma ba damuwa naga duk ka rikice da yawa , dan Allah Kabi a hankali , kokarin daukan keyn motarshi yakeyi yana faɗin A,a Hajiiyata badamuwa yanzunnan zanje in siyo miki ki kwantar da hankalinkak yana faɗin haka ya fita cikin sauri da hanzari.

Kai tsaya shopping mall din ya nufa nufa da sauri yafara biyawa gurin abubuwan da Hajiyan shi take so yafara deban duk abun da yasan zata so shi .


Parking motar Haidar yayi a daidai kofar shopping mall din , fitowa juwarriya tayi cikin takun isa , ganin mota khalil a gurin yasa gabanta faduwa , dan kuwa ko shakka babu wanan motar khalil ce , duk da cewa bada mota daya yake zuwa gurinta ba , amma tabbas tasan wanan tashi ce .

Daidaita kanta tayi ta fara kokarin shiga , kiranta Haidar yayi yace," ko inzo mu shiga tare ne? Wani kallo ta wurga mishi tace," A,aka barshi kawai banaso , tana faɗin haka ta juya tashiga ciki ,tana shiga ta tarar da Khalil yana kokarin dossowa dan fita , wani irin farin ciki ne ya mamaye zukatansu lokaci guda , da sauri Khalil ya karaso cikin sauri yace," lallai na yarda zukatansu 'yan biyu ne tabbas domin kuwa haduwa a irin wannan gurin ba karamar nasara bace a gun masoya , dariya take sossai cikin ranta tana faɗin ashe

Please Login or Register in order to submit comment