Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai kowa dakinshi ya nufa jiki duk a mace .

dakinta mommy ta kaita bayan ta zauna a gado, mommy ta zauna tace," juwarriya wallahi kin bani mamaki , bantaba tunanin haka daga gareki ba ,hawayene yafara gangarowa daga fuskarta , ta bude baki zatayi magana ... Mommy tayi saurin dakatar da ita tacce," yimun shuru ai babu abun da zaki fadamun , mommy na fadin haka ta Fita tace," Allah bamu Alkhairi.

Tana fita juwarriya ta fashe da matsananci kuka .

Tashi tayi da kyar ta dubo wayarta ta daukko , nan taga About 30 missed call din Khalil, wani marayan kuka ta kara fashewa dashi , ta rungume wayar a kirjinta .

Hannunta na rawa ta tafara dailing number khalil , ringing tafari amma ina yaki dauka .

Shikuwa ganin kiran juwarriya ne yasa yaki daukan wayana zuciyatshi na mishi zafi .

Ganin taki daina kiranshi yasa ya dauka yace," inajin ,wani kukan Takara fashewa dashi tace," meyasa zakamun haka inata kiranka kaki dauka .

Da sauri yace ki kwanta kiyi barci gobe inshallahu zanzo da iyayena kamar yanda daddy ya umarceni , batareda ta yi musu ba ta amsa da to , sanan ki tayamu da Addu,a Allah yasa daddy zai Amince da auranmu ne tunda yace Nazo da iyayena , da Ameen ta Amsa nan yayi saurin kashe wayar.


Gaba daya zuciyoyinsu na musu zafi , dukkaninsu sun gagara barci , sai dai dan barci barawo , da ya sacesu

Washegari da safe , Khalil ya shaida ma Hajiyanshi duk halin da ake ciki, Hajiyan Khalil dai bazace komai ba, dan taga samu taga rashi, cikin ranta tana farin ciki da danta daya tilo ya bijiro da maganar aure , sabanin dayar zuciyarta da take takaici da dayan labarin cewa anyi mata miji, cikin zuciyarta ta danyi sanyi Kadan domin kuwa tayi tunanin ko mahaifin juwarriya zai yarda ya aura ma Khalil ita ne .

Batareda bata lokaci ba ta kira yayan mahaifin khalil ta shaidamishi duk halin da ake ciki .

Batareda bata lokaci ba yazo gidansu Khalil .

Misalin karfe shadaya suka nufi gidansu juwarriya .......


*MUJE ZUWA SHIN KUNA GANI DADDY ZAI AMINCE DA AUREN NE KO KUWA ? KODAI KUBIYONI A NEXT PAGE*

*COMMENTS & SHARE*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*✍️✍️


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 34 & 35*

******************

Washe gari da Safe , jikin kowa a sanyaye, ya tashi .

Misalin karfe goma ne kowa ya fito kan dinning dan yin break fast , sabanin juwarriya datake daki bata fito ba.

Kallan husna mommy tayi tace ," husna kije ki kira juwarriya tazo muyi breakfast .

Saurin dakatar da ita daddy yayi ta hanyar fadin," ke karkije ko ina , ai jiki magayi , dan ubanta sai an kirata tazo tayi breakfast , wazata nuna ma zuciya , tayi ta zama a daki kar ta fito .

Badan ran mommy yaso ba haka ta hakura .

Kwance take abun duniya duk ya isheta , wasu hawaye masu zafi ne suka sauka akan kuncinta , cikin zuciyarta tana ta tunani.

Wani sashi Na zuciyarta tana tunanin ta sadaukarta da burinta dan cika ma mahaifinta burinshi , amma in ta tuno dawa zatayi zaman aure sai taji ina bazata iya auran Yaya haidar ba .

Tunowa tayi a lokacin da suke tsara rayuwar auransu da Khalil, hakan yasa ta saki wani dan murmishi mai kunshi da kuka a cikinshi, zubowa hawayen fusktar yayi tace,"Kai Khalil bazan iya ba bazan iya auran wani bayan kai ba , Inshallahu daddy Na zai fahinta .

Tashi tayi ta fita jiki a sanyaye ta fita gurin da su daddy da suke break fast , jiki a sanyaye ta durkusa tace ,"daddy ina kwana , ba yabo ba fallasa yace lafiya ,dady dan Allah....., saurin dakatar da Ita yayi ta hanyar yimata nuni da hannu yace banaso inji komai kimun shuru kawai , shuru tayi ta koma gun mommy tace ina kwana mommy , amsa was tayi tace lafiya kizo kiyi beak fast , to tace.

Nan ta zauna ta gaishe da suhail da Al_ amin batare da ta kalli husna ba .

Jim kadan kowa ya cigaba da bareak fast ba tareda kowa yace komai ba .

Bayan yan mintuna mai gadi ya shigo yace Ana sallam da Abban juju .

Nan yace ace waye ,bayan mai gadi yaje ya tambaya , ya dawo yace , wai ance su Khalil ne .

Jin mai gadi ya ambaci khalil yasa gaban juwarriya yayi mummunan faduwa, ba shiri ta tashi ta Shiga daki .

Nan mommy itama ta tashi ta shiga daki ta saki hijb , gaba daya kowa tashi yayi akan dining din.

Nan daddy ya tafi babban falo l bayan ya Sanar ma baba mai gadi akan su shigo .

Jim Kadan suka shigo , mahaifiyar khalil ce sai Khalil da yasa manyan kayan da suka kara yi mishi kyau matuka , sai yayan mahaifinshi da kanin mahaifi shi , sai Abokin mahaifinshi .

Da sallam suka shiga falon , Inda sukatarar da Abban juwarriya yana zaune akan kujera.

Da fara,a Abban juwarriya ya tarbesu yace kushigo , Neman guri sukayi suka zauna , nan suka gaggaisa , mahafiyar juwarriya ma ta fito ta nemi guri ta zauna suka gaisa.

Shuru ne ya biyo baya kafin daga bisani Abban juwarriya yafara magana yace," to nasan zakuyi mamakin kira da nayi muku , duk da cewa bansanku ba kuma kuma baku sanni ba , to ina neman Afwan hakan , dalilin yin hakan shine akwai wata muhimmiyar magana da zamu tattauna daku ne yasa Har nace ya Fada muku ina San ganinku , nasan dai danku yayi muku bayanin abun dake tsakaninsu da juwarriya .

Nan yayan mahaifin Khalil yace eh hakane yadan fada mana a takice , yanzu sai muji cikakken bayani daga bakinka .

Kallan mahaifiyar juwarriya daddy yayi yace," kije ki kiramun juwarriya
Tashi tayi dan kiranta.

Fitowa sukayi a tare , zama juwarriya tayi a kasa a gefe a dan ruku'be .

Nan mahaifin juwariya yaci gaba da magana yace," to in ba damuwa zan so inji waye shi wannan yaro ???.

*hmmm nasan kuma masu karatu zakuzo kuki waye Khalil ko?.*

*To kubiyoni a next page dan jin wanene khalil ???.*


*COMMENTS & SHARE*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


*PAGE 36 & 37*

*Dan Allah kusaka my kawas maman Hajja a Addu,oinku , mijinta da yaranta duka ba su da lafiya , Allah ya basu lafiya Ngode*

A gurguje

Ibrahim sultan kazaure shine cikakken suna Khalil, mahafinshi sannanen mutum ne , yana da kudi ba laifi domin kuwa cikaken dan kasuwa ne .

Matarshi daya tilo wato Hajiya Kulsum , itace mahifayar Khalil.

Khalil shine da daya tilo a gun mahaifinshi , bayan shi basu kara samun haihuwa ba .

Duk san duniya Alhaji sultan ya daura akan Khalil , haka ma Hajjiya kursum , ta daura San duniya akan danta daya tilo.

Kasancewar Hajiya kursum taga Alamar mijinta nasan haihuwa yasa ta bashi shawarar kara yin aure, amma Sam yaki Amincewa da shawararta , yace shi ya danganawa Allah haka Allah ya nuafa .

Cikin haka ne Har Khalil ya fara zama saurayi , tun yanaka karami bai taba nema Abu ya rasa ba , hakan tasa yazama baya jin magana kasancewer shi kadai ne a gun iyayenshi .

Yaro kyakyawa black beauty , hakan yasan tun da yafara zama saurayi yan mata suke yawa binshi , tun baya kulasu Har yafara kulawa .

Khalil Na da shekara 20 a duniya Allah yayi ma mahaifinshi rasuwa sakamakon hatsarin mota da yayi , Hajiya kulsum tayi kuka matuka da matuwar mijin nata haka Khalil ma da sauran yan wan Alhaji sultan .

A gugurgjur .

Bayan rasuwar mahaifin Khalil , nan aka raba gado Khalil ya mallaki kusan Rabi da kwatan dukiyar mahaifinshi , hakan kuwa bai dami sauran yan uwan Alhaji sultan ba , domin kuwa abun duniya bai rufe musu ido ba kasancewar suma suna da nasu rufin Asiri .


Bayan shekaru Bakwai Khalil yakara zama saurayin matashi , inda yan mata suka binshi , sannan kullum kara shagwabashi Hajiyan shi takeyi , hakan yasa matukar yaga mace to zaiyyi kokari yaso suje su gama shashancinsu da ita .

Ba da kowa wace mace Khalil yake harka ba , Yana da tmyan mata sossai amma sai wacce ajinta yakai yake harka da ita.

Ganin irin rayuwar da yakeyi yasa mahaifiyarshi fara yi mishi maganar aure , amma a duk lokacin da mahaifiyarshi tayi mishi sai yace wai shi ba yanzu ba shi Yaro ne .

Bayan sheka daya halaiyyar Khalil dai bata gyarru ba sai dai ya rage saba,in a cikin Dari , tun mahaifiyarshi na mishi maganr aure da yan uwan mahaifinshi Har suka daina , tun mahaifiyarshi na hadashi da yaran yan uwa ko Kawaye ,Har ta daina dan duk wacce aka kawo sai yace batayi mishi ba.

Khalil Na matukar girmama mahaifiyarshi , dan yana matykar Santa bayasan ganin Bacin ranta ko kadan , saidai yakasa cika mata burinta Na ganin aurenshi .

Ganin mahaifiyaramshi ta damu da maganr aure Har ranta yafara baci yasa ya yarda zaiyyi auren in ya samu matar da yakeso , cikin hakane Har ya hada da juwarriya ....

Wanan kenan , shine takaittacen labarin Khalil .

Cigaban labari .

Yayan mahaifin Khalil ne yafara jawabi , nan ya fada mishi cewa shi ne yayan mahaifin Khalil da kaninshi da kuma Abokokin mahaifinshi.

Bayan Abban juwarriya ya sauraresu nan yayi gyaran murya yace hakane naji duk abun da kuka fada , inaso zan kuma kara yi muku bayani abunda ke faruwa .

Maganar Gaskiya ni bansan wata Alaka dake tsakqnin Khalil da juwairra ba , hasalima ban taba sanin yana zuwa gurinta ba , maganar gaskiya tun iyayens mu suna raye suka umarcemu da mu hada yaranmu aure tsakani , ganin juwarriya bata gama karatu bane yasa ban Fada mata hadin da za,a yi kusu da dan uwanta ba , sai lokacin da nafada mata cewa zamu hadasu shine ta fadi sai a Asibiti ne take fada mana ga Wanda takeso Wanda mu bamusan da zancen ba .

Na zabi na fadamuku maganar nan ne , dan nasan ku zaku fi mishi bayani yanda zai fahimta Shiyasa ma ban fada mishi ba .

To da wannan nake baku hakuri nake kuma ba danku kakuri akan yayi hakuri yaje yanemi wata amma juwarriya nabama dan uwanta ita .

Gaban juwarriya ne yayi mumunan Faduwa Jin numfashinta na Neman daukewa yasa tadan daidaita nutsuwarta , ta sunkuyar da kan ta kasa wasu hawaye masu zafi Na zuba a kuncinta, kakkawarwa bakinta kawai yakeyi , Khalil ma hankalinshi yayi matukar tashi , ji yake kamar ma ba zai iya taka kasa .

Yayan Abban Khalil ne yayi karfin halin cewa , amma Alhaji kana gani a marrannan ana auren hadi , ni a tunani na tuni an dade da huce wannan gurin ai , ina Baka shawara karkuyi ma yaranan dole .

Murmishi yayi yace," hakane amma ni wannan abun kamar Alkawari ne da muka dauka tun yayana Nada rai , sanan burin iyayenmu ne fa , sabida haka nasan yarana bazasu taba watsamun kasa a ido ba zasu Amince.

Magana Abokin mahaifin Khalil yayi yace," to shikenan Alhaji mu bari mutafi , mungode.

Cikin fara,a da sakin fuska daddy yace," Ah da wuri haka bakuci komai ba ?.

Tabe baki mahaifiyar Khalil tayi tace," A,a mungode , dan kuwa ita Hlhar cikin ranta haushinsu takeji dan bataji dadi ba kwata kwata .

Tashi sukayi dan tafiya , dakyar Khalil ya iya tashi idanshi nakan juwarriya da kanta yake a dukufe , juya wa yayi tana tafiya jiki a sanyaye .

Bayan sun tafi mahaifin juwarriya ya dawo da kallanshi zuwa gareta yace," juwarriya ! Kasa dago kai tayi dan kallanshi , kira ya kara kwallamata ta," juwarriya bakya Jine?cikin muryar kuka tacce," daddy ina ji .

Magana yafara yi cikin sanyin murya yace," juwarriya kinsan dai bazan tanlba zabamiki abun da zai cutar da rayuwarki ba , ke shaidace kifi kowa sanin irin San da nake miki,juwarriya kiyi hakuri ki daure ki amince da kudurina mana .

Wasu hawaye masu zafi suka zubo ,dago idanta tayi da sukayi ja jawur , tafara girgiza kai , cikin muryar kuka take fadin," daddy wallahi bana sanshi daddy bantaba ji ina San yin aure da YAYA haidar ba , daddy dan Allah Dan Annabi daddy kabarni Na Auri Khalil wallahi shi nakeso , tafada cikin muryar matsanancin kuma.

Jin kukan juwarriya yasa dukkan mutanen gidan suka fito .

Ganin hakan yasa mahaifiyar haidar fadin," wai lafiya kuwa ? , da sauri juwarriya ta zo gurinta tace," Hajiya dan Allah ki mishi bayanani yabarni aa aura Wanda blnakeso dan Allah.

Gurin Abban juwarriya Hajiya ta karaso tace," Abban suhailu, kayi hakuri kawai ka bar hadin auren nan kabarta ta auri Wanda kakeso , tunda batasan haidar din .

Jaa idan Abban juwarriya yayi fuskarshi a murtuke da ka ganshi Kasan yana cikin damuwa da bacin rai , shuru yayi batareda yace komai ba , tashi yayi dan Shiga daki gameda kamo hannun juwarriya ya shige da ita .

Da kallo kowa ya bisu yanasan ganin ikon Allah .

Suna shiga ya sake ta yayi mata nuni da hannu yace," zauna ba musu ta zauna a gefen gadon dakinshi .

Shima kan gadon ya zauna , nan yace," dago idonki ki kalleni ......✍️

*HMMMM MUJE ZUWA FANS*

*AMMA BANGA KUNA COMMENTS BA FA*πŸ˜’πŸ˜’

*COMMENTS*

*&*

*SHARE*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 38 & 39*


Nan yace dago ldo ki kalleni, dago rinannun ldanta tayi dasuka yi ja ta dago ta kalleshi .

Cikin sanyin murna yace juwairiyya tunkina karama na raineki,karkimanta na nuna miki so kuma kinsan bazan taba zabamiki abin da zai cutar da keh ba duk cikin yarana babu wanda nafi nunawa kauna kamarki dalilin San da nake miki Shiyasa har na zaba miki haidar a matsayin mijin auranki.

Numfasawa yayi yace ," Juwairriya meyasa bazakimin biyayya ba na dauka ldan kikayi la, akari dasan da nake miki zaki amincemin da duk abin dana cemiki, ko da bakyau so .

Hawaye masu zafi keh zuba a fuskarta.

Cikin muryan kuka take fadin," nima naso ace nabi zabinka dady na amma San Khalil yagama shiga zuciyata nima kaduba San danake maka kabarni na auri zabina.

Cikin zafin nama ya mike a zafafe ,yace," juwarriya! Yafada da kakkausar murya , cikin hanzari ya daga hanu ya tsinketa da wani gigitacecn mari ,

Arikice tadago ta kalashi hade da rike kuncinta , muryar ta na rawa race," daddy tunda nake baka taba marina haka ba , daddy kayi hakuri , amma wallahi bazan iya rayuwar aure da YAYA haidar ba .

Cikin kakkausar murya idanshi yayi jaa yace," tashi ki ficemun a daki, jiki a sanyaya ta tashi ta fita , tana kuka .

Babban falon ta fito ta Tarar da sauran mutanen suna falo .

Nan daddy ya biyo bayanta nan ya nemi guri ya zauna , cikin fushi yace," juwairriya! nan ta dawo ta zauna tace na,am .

Cikin rashin fahinta kowa yake kallansu .

Nan mummy tayi karfin halin cewa Abban suhail menene yake faruwa ne?.

Cikin bacin rai yace," na yanke hukuncin aurama juwarriya zabinta , amma bisa sharadin babu ni ba ita sanan karta kara kirana a matsayin mahaifinta , in ta amince da haka shikenan .


Cikin matukar tashin hankali mommy tace," Abban juwarriya wacce irin magana ce haka , yazaka ce haka, karka yanke hukunci cikin fushi mana, yakamata ka fahimta kayi mata uzuri har yanzu ita yarinya ce dole sai anyi mata magana ta nutsuwa da fahimta .

Cikin Bacin rai yace," wani irin bayani zan mata bayan Wanda nayi mata a daki, na yi mata nasiha nayi fadan amma taki ji ya takeso nayi mata .

Cikin sanyin murya mahaifiyar haidar tace,"Abban juwarriya kayi hakuri ka kwantar da hankalinka , komai zaiyyi daidai inshallahu .

Murmishin da yafi kimuka ciwo yayi yace," to shikenan, yanda kukayi , yana fadin haka yatashi ya fice cikin bacin rai.

Bayan ya fita mummy tayi sauri tazo gurin juwarriya tace," juwarriya ban taba Sanin Baki da hankali ba sai yau , tsabar Baki da hankali har ki bari mahaifinki yafara furta irin wanan furucin a kanki , kuma kina ganin hakan zai fi miki ne? Kinsan illar hakan kuwa?yazama dole ki sadaukar da farin cikinki da biyan bukatar mahaifin ki ko kinki ko kinso kinji na fadamikii .

A,a luba ba haka yakamata ki fada ba muyi mata magana ta fahimta , da nutsuwa mahaifiyar haidar ta fada cikin sanyin murya, nan takalli juwairriya datake ta kuka hade shasheka tace, juwairrya, yakamata ki gane kisan meyake miki ciwo ni bawai ina magana wai dan haidar dana bane ko kuma inason lallai sai an hadaku a,a kawai inasan nabaki shawara, kinga bin iyaye sune gaba da komai na ruyawa , meyasa bazaki amince ba juwarriya zamu baki lokaci kije ki zauna kiyi nazari yakamata ki san cewa baza,a taba zaba miki abun da zai cutar dake ba .

Cikin Bacin rai husna tace," dallah Shasha , in ba baki da hankali ba har kibi zabin ki kiyi burus da na mahaifinmu wallahi kin bani mamaki .

Cikin tsiwa da kuka juwarriya tace," ina ruwanki ke ba zabinki a ka barki zaki aura ba meyasa ni ma baza,amun wanan halacin ba na auramun zabina meyasa ,ke ki hakura da auran Jamal din ki auri yaya haidar din mana....bata karasa rufe Baki ba mommy ta tsinketa da lafiyaiyyan mari, tace dan ubanki duk abun da kika ga dama kiyi , tana fadin haka ta tashi ta tafi a zuciye.

Wata Harar husna ta wurgamata ta tashi ta fita .

Nan duk sauran suka watse akabar juwarriya ita kadai takara fashewa da matsanancin kuka.

Tunanin maganar tasu ta farayi , da Sauri ta share hawayenta ta mike tashiga daki , daukan wayarta tayi tafara dailing numbern khalil,.
Kwance yake zuciyarshi nayi mishi zafi , ganin kiranta yasa shi saurin dagawa a tunaninshi ko zata ce mahaifinta ya amince da auren ne .

Dauka yayi cikin sanyin murya yace," juwarriya ya akayi ?.

Kuka tafashe dashi race," khalil zan aureka amma ina so kamun wani alkwari guda daya, da sauri khalil yace," fada fada naji juwarriya ina jinki nayi miki aljwari zan miki shi ko menene , nan ta sharehawayenta kamar yana kallanta tace," ina so kayi mun alkawari bazaka taba wulazkantani ba , da Sauri yace," eh juwarriya nayi nayi namiki alkawarin bazan wulakantaki ba , ddady ya amince da Auren ne? ya tambayeta

Murmishin da yafi kuka ciwo yayi yace," A,a bai Amince ba , yace in har zan aureka bani ba shi nikuma nazabi na rabu da shi akanka dan Allah karka juyamun baya girgiza kai yayi yace," eh eh baby kiyi hakan na amince bazan wulakantaki ba , nan taji sanyi cikin zuciyarta .

Hira suka dan yi sossai da haka Har taji zuciyarta ta danyi sanyi .

Bayan sallar Azahar daddy ya shigo , ganin yashigo yasa juwarriya yanke shawara samunshi .

Zaune yake a fallon shi da mommy suna hira .

Nan tazo sumi sumi ta tsugunna a gefe tace," daddy dama Nazobnafada maka wata magana ne, nan daday ya tattaro hankalinshi yace," to inajinki , a tunaninshi hakuri zata bashi akan ta janye maganar, zata amince da zabin da ya mata

Kan ta sauke a kasa taca," Daddy na Amince zan auri Khalil bisa sharadin da kace na amince duk abun da yabiyo baya ka cire hannunka , wani mmumna faduwar gaba daddy da mommy sukayi jin wanan maganar daga bakin juju , da Sauri daddy ya mike yace," haka kikace ," kada kai tayi Alamar eh !

Da Sauri mommy ta karaso ta jawota ta tsinketa da mari tace," juwairiyya meke damunki? baki da hankali ne? , cikin muryar kuka juwarriya tace," mommy na Amince mommy tunda daddy yaki amincewa da zabina nima na hakura bazan iya auren YAYA haidar ba ni Khalil nakeso .

A take daddy ya kira kowa da su suhail akan duk suzo

Please Login or Register in order to submit comment