Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su koma din .....
Alfarma daddy ya roka kan haidar ya dawo su cigaba da zama a gidanshi , hakama mahaifiyarshi, dakyar Mommyn juwairriya tasa baki mahaifiyar haidar ta yarda da sukoma gidansu da zama ....

Hada kayanta sukayi gamida shiryawa suka koma gidan Abban juju ......

Koda suka dau hanya daddy ne ya kira suhail da Al_Amin da husna kan cewa ga sunan suna hanyar dawowa , sossai sukayi farin ciki da jin hakan , domin har sun rigasu Isa gida ma suna jiran isowarsu ......

Bayan wasu awanni suka karaso ,murna a gurinsu ba'a magana , sai dai Sam basu ji dadin ganinin juwairriya ba sakamakon ramar da tayi ....

Kwana sukayi gaba dayansu a gidan , Inda aka basu labarin rayuwar juwairriya a gidan mijinata ....
sossai ransu ya baci gamida Alawadai da hali irin na su haidar, suka ce sai sun dauki fansa ...

Dakyar mommy ta basu hakuri suka hakura domin kuwa sunce Sai sun dau fansa akan abunda akayi ma yar uwarsu

badan ransu yasoba haka suka hakura , Sune me tausayin kanwar tasu.....

Washe gari da safe kowa ya koma gidanshi badan sun soba Sai dan bin umarnin daddy ......

Sossai juwairriya take samun kulawa a gurin Abbanta da mommy, uwa uba kuma yaya haidar .....

Wata shakuwa ce ta kulle sossai tsakaninsu , kullum suna tare suna hira gwanin ban sha'awa...

Mommy ce ta bukaci da aje gidan juwairriya a debo mata kayanta,amma Sam daddy yaki yarda wai babu da zai kara hada yarshi da Khalil ya yafe ,zai sake yi mata sabo in zatayi are .....


Bayan wata daya , sossai juwairriya ta samu lafiya tadawo da kyanta da kibarta ba laifi....

Ganin yanayin shakuwarsu yasa daddy nuna bukatarshi ta sake hada su aure a karo na biyu matukar in sun yarda ...

Sossai sukayi farin ciki da hakan ,shima haidar yanason yayi magana amma kunya ta hanashi sai gashi daddy ya fahimci hakan da kanshi , haka itama juwairriyan ,domin San da take ma haidar yanzu ya ninka son da takeyi ma Khalil a daa .....

Batareda bata lokaci ba aka tsaida lokacin aurensu bayan Wata daya....

Bayan wata daya aka daura musu aure , farin cikin a gurinsu ba'a magana .....

Kula da ita yake sossai kamar me ..
baya so yaga abun da zai bata mata rai kwata_kwata ..

Watarana in juwairriya ta zauna tana tunani sai tayi ma Allah godiya, hakika rayuwarta yanzu tayi kyau matuka , tana kuma me gode ma Allah a koda yaushe da Allah da ya mallakamata haidar a matsayin mijin aurenta na har Abada , hakan yasa tamanta da rayuwar Khalil bata ma so ta tunashi......


A bangaren Khalil kuwa tun bayan rabuwarshi da juwairriya aka daura misshi aure da raudat ..

Hakika zuwa yanzu duk Wanda yaga Khalil Sai ya tausaya mishi ,domin raudat tasa duk ya fita haiyyacinshi ,Inda suka shiga bokaye ita da mahaifiyarta sai yanda sukayi da Khalil ...
Haka yasa duk ya susuce ...
Hatta mahaifiyarshi baya zuwa gurinta ta rasa gane kan dan nata ,hatta ita kanta raudat ba barinta tayi ba ......

duk abun da raudat tace to fa jikin Khalil na rawa zaiyyi mata....

Cikin hakane ta sa dukiyarshi tafarayin kasa , har yazo yanema ya rasa ....

Bayan komai ya Kare raudat tanemi da ya saketa, ba yanda ya iya haka ya saketa...
hatta gidan da yake cikin raudat ta kwashe takardun ..
hakan yasa ya koma zama da mahaifiyarshi....

Rayuwa ta yi mishi zafi , watarana sai ya nemi naira Biyar ma ya rasa hakan yasa mahaifiyarsu ta fara fita Neman nakanta .....
kullum cikin zagin Khalil take tana jin tsanarshi a cewarta duk shi ya ja musu halin da suka Shiga yanzu ......

Gidan da suke ciki suka siyar suka kama gida mai daki daya ...
A hankali suna zarar kudin har Sai da ya kare.....

Hakika rayuwar Khalil ta koma abun tausayi tazama kamar ba shi ba duk ya lalace ya fita haiyyacinshi......

Tafiya yakeyi a hanya shi kadai yana sake_sake iri_iri cikin Ranshi , bayan yadawo daga guraren da yasan zai sami taimako amma ina bai dace ba.....

shuru ya yi ,yana tafiya ,damuwa tayi mishi yawa kamar zautacce...
Horn moto take tayi mishi a bayanshi amma tunani da tsananin damuwa tasa bai ji ba ....
Da gudu motar ta yi ciki dashi ya fadi a Kasa ...

A kidime me Motan ya fito , ganin khalil kwance a kasa yasa haidar fadin," juwairriya fito ki gani wanan ba tsohon mijinki bane?
jin haidar ya ambaci tsohon mijinta yasa gabanshi yayi mugun faduwa , ta fito a rikice...
Ganinshi kwance cikin jini yasa ta karajin wani tsanarshi ta kalli haidar tace," darling bro mutafi kawai mubarshi , dama sakamakon sharri kenan , tafada hawaye na fita a fuskarta , share hawayen, fuskatta tayi taja numfashi tace," Darling bro , kabarshi mutafi , wallahi ko tantama banayi sakaiyya Allah yamun cikin sauki , ka kalleshi fa ka kalli yanda yadawo , mutafi kawai .....
Jiki a sanyaye haidar yace," no darling sis kiyi hakuri , tunda muma asibiti zamuje Mlmu tafi dashi kawai kinga fa akwai hakki akanmu, shida Allah ....
badan juwairriya taso ba haka ta hakura suka kamashi dakyar da taimakon mutane suka sashi a moto suka nufi asibiti dashi , gamida da biyewa ya dauki police gudun samun matsala ....

Cikin hanzari suka nufi Asibitin suna shiga aka nufi emergency dashi , aka fara bashi taimakon gaggawa ....

Kai tsaye suma suka wuce bangaren masu awu , kasancewar ta na dauke da cikin watanni shida ...
bayan angama suka nufi gida , bisa da niyyar zasu dawo gobe su dubashi ....

Washe gari Khalil ya farka,ba laifi jikinshi da sauki kasancewar yasamu kulawa mai kyau daga asibitin ....

Misalin karfe sha daya na rana juwairriya da haidar suka iso asibitin....

Dakin suka Shiga, rai a bace juwairriya ta Shiga dakin .....

Ganin juwairriya yasashi jin faduwar gaba yana me tsananin mamakin ganinta..
kokarin mikewa yayi yana fadin," juwairriya! Wata uwar harara ta gallamishi tace," karkiyi tunanin nazo dubaka ne, A a saidai dan mijina ne ya bigeka , sabida haka ina maka fatan samun sauki , mun rigada mun biya duk kudin da ake bukata, in natafi bazamu sake zuwa dubaka ba ...
Na barka lafiya tafada gamida juyawa , juwairriya! yafada kamar me shirin yin kuka , juyawa tayi tagalla mishi harara tace," karka sake kirana , murya Na rawa yace," juwairriya dan Allah ki yafemun hakika nasan hakki kine yake bibiyata , ni naga rayuwa naga jarabawa , sanan naga tashin hankali, hakika Allah yana sona da rahma ne tunda har Allah yasa na ganki kuma ina Neman gafararki , kiyi hakuri ki dubi Allah , kiyafemun , nasan Na cutar dake Na ci amanarki banmiki hallaci ba kamar yanda kikamun , kiyi hakuri ...

Kuka sossai juwairriya takeyi , tace," Khalil bazan iya ba bazan yafe maka ba dan ka cutar dani ka lalatamun rayuwa nayi ma Alkhairi kasakamun da sharri gashi tun ba'aje ko inaba Allah ya faramun sakaiyya....

Haidar dayake gefe yana kallansu ya karaso gurin juwairyiyan yariketa yace," darling sis kiyi hakuri ki yafemishi tunda har yayi nadama , Allah ma ana mishi laifi kuma ya yafe ,kiyi hakuri kinji matata ....

murmishi tayi tace," shikenan darling bro zan ya femishi ko dan Albarkacin ka inshallahu ......

Maida kallanta zuwa Khalil tayi tace," shikenan Khalil na yafemaka , Allah ya shiryaka , mu mun tafi , tafada gamida juyawa suka tafi .. ....

Kuka sossai Khalil yayi yana me cike da nadama, hade da jin son juwairriyan a ran shi amman yasan yanzu tayi mish nisa....
da haka ya fashe da kuka mai cin rai yana me tsanain nadama da tsanar kanshi .. .......

Bayan kwana biyu juwairriya suka je gida suka musu yanda duk sukayi da Khalil, Inda sukace hakkinta ne yake bibiyarshi , suka bishi da Addu'ar samun lafiya ....

Bayan raudat ta kwashe dukiyan ita da mahaifiyarta sun , gudu, suma dukiyar bata tsinanamusu komai ba , illah tashin hankali da suka Shiga ,inda suka hadu da yan damfara suka kwashe musu komai ,suma suka wulakanta sukadawo abun tausayi .......

Bayan watanni uku , juwairriya ta haifi katon danta .....
itama husna ta haifi mace , tsirarsu kwana daya , hakan yasa aka hada sunan a tare inda akaci a kasha , aka sanya ma yarinya sunan mommy, shima aka sanya mishi sunan daddy .....

Suma su Al_amin da suhail matansu duk sun haihu sun haifi maza dukkansu , akayi farin ciki matuka ...

Zuwa yanzu juwairriya tana cikin farin cikin ,inda takeji kamar ta fi ko wace mace sa'a.....
tama zaune cikin so da kauna da kulawa ita da masoyinta wato darling bro dinta ,haidar ..

A kulum kara son junansu suke , tare da yaronsu , gwanin ban sha'awa ....

Kullum cikin yima Allah godiya take a kan sauyin da yayi mata , tana me farin ciki matuka , tana kuma kara tuba akan kuskuren da ta aikata a baya .........


Bayan wasu shekaru familyn Alhaji mansur mai tala ne kewaye da shi da 'ya'ya da jikoki ...
farin ciki sossai familyn suke cikin suna me yima Allah godiya kan hadin kan da suka samu a familynsu .....


*TAMMAT BIHAMDULLAH*

*SUBHANAKALLAHUMMA*
*WABI HAMDUK,*
*NASH HADU ANLA' ILA HA ILA ANTA,*
*NASTAGFIRUKA WANA TUBU ALAIK*


*ALLAH NAGODE MAKA DAKA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN NAWA MAI SUNA A SANADIN KUSKURENA.*


*KUSKUREN DA NAYI A CIKI ALLAH YA YAFEMUN ABUBUWAN DA NA FADA DAIDAI ALLAH KABAMU LADA BAKI DAYA ....*

*DAGA NI ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU'AD) NAKE CEWA, KU KASANCE DANI A SABON LITTAFINA MAI SUNA , 🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA ....*

*INASONKU SON SU FISABILILLAH*

*DAN NEMAN KARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUBATA AKAN LAMBAR WAYA KAMAR HAKA 09066386347*

*MA'ASALAM...*

*SHARE IT PLS👏👏👏👏👏*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment