Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai kwalliyar da tayi batayita a banza ba , gaisawa sukayi cikin marin juna , cikin jin dadi Khalil yace," kinki bani dama inzo in ganki gashi Allah ya nuna mun ke!

Dariya tayi tace," hmm ba haka bane wallahi daddy na ne kasan baisan Alakar mu da kai ba , nafiso sai baya gari ne sai kazo gidanmu amma kaga yanzu bazai yuyu ba domin kuwa yana gari , cikin sigar so ya kalleta yace," to kinki sa lokaci in aiko gida bansan meyasa ba ko bakyaso nane ? Saurin toshe bakinta tayi da kyawawan hannayenta tace," nashiga uku dan Allah ka rufamin asiri kar ka kara aikata wanan mummunan zunubin , kar ka yarda kyawawan bakinka sukara furta irin wa, ina munanan kalaman kaji, dariya sossai ta bashi yace," to shikenan baby na ,na daina bazan kara ba amma yanzu ki fadamun yaushe zan tura ?? Kayi hakura lokaci kankani , cikeda da jin dadi yace," to shikenan Allah Nuna mana , amma keda wa kikazo nan? Ya tsine fuska tayi tace," ni da yaya haidar ne cousin brother na Wanda Abbanshi ya rasu shine suka taho tare da su daddy, OK aiyya ko Zan iya zuwa mu gaisa dashi? zaro ido juwarriya yayi yace," kai karufamun Asiri ka bari kawai , ni kam ma barin Shiga in siya abun da zan siya na tafi , OK to muje na rakaki , nan suka fara tafiya , sai da Khalil ya ya cika mata babban basket da kaya , ko bata yi niyyan dukan Abu ba sai ya daukan mata ,da haka har suka zo gurin counter akayi musu lissafi take Khalil yabada ATM dishi ,suka cire kudi godiya sossai juwarriya tayi mishi ,nan suka tsaya suka dan kara taba hirarsu mai cikeda da soyyaiya .

Shuru shuru haidar yanata zuba ido juwarriya bata fito ba Kallan agogon hannunshi yayi yaga har shida saura , zuba ido yayi ko zata fito...

Ganin lokaci na nema kurewa yasa juwarriya fadin," kai dear lokaci na kurewa kar wanda mukazo dashi yaji shuru ,kar ya fito , dan zai iya shigowa , badan haidar yaso ba yasa sukayi sallama cikeda kewar juna .

juwarriya ce ta fara fitowa gudun kar haidar ya gansu a tare da khalil, ganinta dauke da murmishi yasa haidar mamakinta , mamaki sossai haidar yayi cikin Ranshi yana aiyya meyasata farin ciki haka sabanin da ta Shiga cikin shopping mall din rai a bace.

Bude kofar tayi tashiga cikin farin ciki tace muje koh? batareda yace komai ba haka yaja motarshi suka tafi ....

Ganin suntafi yasa Khalil shima ya fita yaja motarshi cikin Sauri ya tafi dan kaima Hajiyanshi furarta .......✍️✍️

*MUJE ZUWA*

*GASKIYA NAJI DADIN COMMENTS DINKU A LAST PAGE, KUCIGABA DA SUBURBUDO COMMENTS IN SUBURBUDO MUKU RUBUTU.....*✍️✍️✍️

*COMMNETS*

*&*

*SHARE*


*STORY &WRITTEN BY MUM FU'AD*


💐💐💐💐💐💐💐

*A SANADIN KUSKURE NA*💐💐💐💐💐

*MALLAKIN*👉 *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
*AND NOW*👇
💐💐💐💐💐 *A SANADIN KUSKURENA*💐💐💐💐💐

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*Page 24&25*

*Rashin comments dinku mai yasa shi yawa Shiyasa jikina yin sanyi banna muku typing akai akai amma matukar zaku dinga comments sossai to inshllahu nayi muku Alkawarin typing akai akai , Allah ya wuce mana gaba.*


************

Da sallama Khalil ya shigo cikin sauri , kawo ma hajiyanshi furar,.

Kishingiɗe take tana lazumi ta maida kallanta zuwa kantafaren tv bangwantan dake manne .
Ganinshi yasata sakin kayatacen murmishi da tace," yaro ! Kadawo ? da murmishi ya amsa yace," eh nadawo Hajiiyata , gashinan na yimika siyaiyya sossai duk abin da nasan zaki soshi shi nasiyilo buɗe ledodin tayi ta zato ido tace," yaro? Ni da nace ka siyomin Fura shine ka kahado kaya haka ? Haba Hajiyata na dan kwana biyu fa ban miki siyaiyya ba , kuma ma ai ba yawa, to nagode yaro Allah saka da Alkhairi , Allah ya nuna mun lokacin da zan Aurar da dan daya dayana , sosa keya yayi cikin jin kunya yace," hmm Hajiiyata , ai kinkusa aurar dani inshallahu kwannan, dariya tayi tace," hm to Allah yasa .

Nan ya tashi ya shiga daki dan karasa aikin shi , da kallo ta bishi tana girgiza kai cikin ranta tana faɗin Allah kanuna mun Sanda zan aurar da khalil da hannuna , tana faɗin haka ta fara kokarin shan furarta .

Tunda Haidar suke tafiya da juwarriya yake santa kallanta , domin takawa ɓoye farin cikinta nahaɗuwa da Khalil , kallanta yayi yace," Juju wai lafiya kuwa naga tunda kika fito a shopping mall din kike ta murmishi faɗa mun wani abun Alkhairi ne ya sameki? .

Wani kallo ta wurga mishi tace,"uhm yaya haidar nifa babu komai ni kawai tsintar kaina nayi cikin farin ciki .

Girgiza kai yayi batareda da yarda da maganar ta ba .

Tun a mota juwarriya take ta tsake tsaken yanda zata tunkari mommynta da zancen , batareda da ta Sami mafita ba ta cigaba da shirya yanda zata tunkari momynta , da haka har suka isa gida ...

Koda suka isa kai tsaye dakinta ta nufa kasancewa daddynta ya tafi masallaci , tana zuwa ta ajiye kayan ta nufi dakin mommynta dan faɗa mata tasami mijin aure domin a tunaninta , mommynta zatayi farin ciki da hakan matuka kasancewar tana san tayi aure .

Da sauri tashiga dakin ta fada jikinta cikin fara,a tace, mommy! Kai! juwarriya meyasa ke har yanzu baki girma bane? Ji yanda ki ka fada a jikina so kike ki karyani ? Shwagwaɓa fuska tayi tace ", kai mommy to in bankwanta a cinyarki ba a wunyan wa zan kwanta ? Cinyar daddynku mana dan kin fi sanshi , mommy tafada cikin sigar wasa da zolaya , yanzu dai miye ke faruwa naganki cikin farin ciki Albishirinki , mai da hankali mommy tayi a kanta tace," uhm goroo ,buɗe baki juwarriya tayi zata yi magana , amma sallama Husna yasata yin shuru , ta amsa mata sallamar , mai da hankalisu sukayi ga ba dayansu suka kalli Husna , karasowa tayi tace,Mommy barin dan fita in dawo ina zuwa , jamal yazo barin je in dawo , to Adawo lafiya husna sai kindawo mommy ta fada cikin sakin fuska , tabe baki juwarriya yayi tace," uhm mommy nifa natsani wannan Jamal din dayake zuwa gun husna , harara mommy ta bita dashi tace," lallai ma juwarriya haka Kawai kice kin tsani mutum me yayi miki toh? Turo baki tayi tace", uhm oho ni kawai bai mun bane , to kar yamiki tunda ita yamata ai shikenan , kuma kwananan zai fito In aurar da ita in huta kafin kee,maganar da mimmy tayi yasa juwarriya tunawa da abun da ya kawota gurin mommy , zatayi magana kenan sai wata zuciyar taraya mata cewa kai tadan kara jinkirtawa zuwa wani lokaci , ko da zuwa lokacin da zata gama candy dinta ne sai ta fadama mommy , da wanan tunanin ymtayi na,am cikin ranta , hakan yasa ta fasta fadama mommy maganar , ganin ta lula tunani yasa mommy fadin," ke juju ! Miye haka kika fada cikin tunanin nasan bai wuce tunanin kema ki samu mai sanki ba koh? Mummy tafada cikin sigar wasa ,Shagwaba fuska tayi tace," A,a nikam mommy ko Kadan ba haka bane , ni barin ma tashi in tafin, to dama ban gaiyyaceki ba kikazo sabuda haka sai anjima Allah raka taki gona, tashi juwarriya tayi ta fita da gudu tana dariya......✍️✍️


*MUJE ZUWA*

*kuyi manage da wanan pls*


*STORY & WRITTEN BY MUM FU'AD*✍️✍️✍️✍️


💐💐💐💐💐💐💐

*A SANADIN KUSKURE NA*💐💐💐💐💐

*MALLAKIN*👉 *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
*AND NOW*👇
💐💐💐💐💐 *A SANADIN KUSKURENA*💐💐💐💐💐

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 26 & 27*

*_KUYI HAKURI BAYAN HUTUN DA NA TAFI , TO YANZU NA DAWO DA ZAFINA INSHALLAHU IN KUNYI COMMENTS KUGA TYPING IN BAKUYI BA IN KARA TAFIYA HUTU , NAGODE_*

***************

Bayan juwarriya ta shiga daki kai tsaye wayarta ta dauka , ganin bar missed call biyar yasa gabanta faduwa musamman ganin sunan Khalil ne ya baiyyan akan screen din wayar .

Da Sauri ta fara kokarin dailing numbernshi har tafara ringing , bugu Biyu ya dauka yace," haba Baby kinsan halin da kika sani kuwa ,yanzu haka ina shirin inzo in ganki ne tunda nakira wayanki baki daga ba , ajiyar zuciya juwarriya ta sauke tace am sorry dear bana kusa da wayan ne ina dakin mommy , murmishi yayi yace," to shikenan bazan yi fushi da gimbiyata , yaya kike? Kin koma gida lafiya? ,murgunawa sossai tayi tana jin magannshi na ratsa dukanin jijiyon jikinta ,rintse ido tayi tace," uhm lafiya kalau my heart beat ya hajiyanmu ? HAJIYA tana nan lafiya , kulum dai burinta taga aure na amma haryanzun kin kasa bani dama in turo a ayi magana wai meyasa ? Dear ba haka bane nafiso in gama karatu ne kafin acee anyi kwakwarar magana , karfa ka manta akan ka ne fa na haura da Burina na cigaba da karatu na hakura na bari sai a gidan ka , kuma ma saura kwanaki nawa ne kayi hakuri very soon kaji my *NOCSOL* jin ta kirashi da da nocsol yasashi yayi suman tsaye yace ,"baby sunan nan fa ? daga ina yayimun dadi sossai wallahi repeat it pls dariya tayi harda rufe ido kamar yana kalanta tace," NOCSOL, wani dadi ne yakara ziyartashi yace," thanks you baby , hira sossai sukayi mai cikeda da shawa, da soyaiyya hade da kulawa da tarairaya , kafin daga bisani sukayi sallama suka kashe wayar , cike da kewar junansu .


Bayan sun gama wayar juwarriya tafara kokarin nemi hanyar da zatabi dan fadawa mahaifiyarta , domin kuwa Tabbas a yanzu babu abun da take bukata Sama da auren Khalil, cikin wani bangare na zuciyarta tana da yakinin cewa tabas mahaifinta zai aminita da aurenta da khalil domin abun da takeso Shiyakeso , da wannan tunanin taji zuciyarta Takara Santa tana me farin ciki matuka cikin ranta .


Haka rayuwa take tafiya a gidansu juwarriya , kullum soyaiyya kara kulluwa take tsakanin Khalil da juwarriya , rashin jutuwa nakara shiga tsakanin juwarriya da khalil , tunda juwarriya ta fuskanci manufar haidar akanta yasa take kokarin Jan baya dashi , domin ko ba,a fada ba ,da ganin yanda haidar yake ma juwarriya to fa tabbas kasan dawani abun a cikin ranshi , haka daddy ma iya kokarinshi yanayi ne dan ganin yakara kullla shakuwa da jituwa da kusanci tsakanisu , amma Sam juwarriya bata ba da wannan kofar ba , mommy ce kadai ta fahimce yanayi Juwarriyan akan haidar domin ta fauskanci in dai haidar na guri to juwarriya bata bukatar zuwa inda yake , ama tunaninta bai kawo cewa akwai wanda takeso ba .

A Kullum burin Khalil bai wuce yaga juwarriya ta amince ya tura gidansu ba , domin kullum cikin tambayarta yakeyi , akan ya maganar turowa gidansu , hakuri take bashi akan lokaci yakusa .


Wasa wasa wata daya ya rage juwarriya tayi candy , hakan yasa daddy murna sossai yana me farin cikin ganin juwarriya ta gama karatu tafara jam,i,a , saidai wani Abu da bai sani ba , juwarriya kam Sam Jami,a bata gabanta yanzu khali kadai take hangowa cikin ranta .


Abubuwa da dama sun Faru kafin wata dayan ,ciki kuwa harda tambayar Auren husna da akayi inda aka yanke sadaki naira dubu Dari biyub, aka kuma sa ranar auren nan da wattani uku masu zuwa , murna sossai juwairriya takeyi tana murna husna zata barmata gidan tayi abun da takeso son ranta , amma wani sashi na zuciyarta tana ji inama ace itace zata yi aure ta Auri Rabin rantq Tabbas farin cikin da zata shiga mara misultuwa ne .


Kullum soyaiyya Khalil kara yawaita take cikin zuciyar juwarriya , sabanin tsana dake kara Shiga tsakanin haidar da juju , duk yanda dady da mommy suka so Suka shakuwa cikin zuciyar juwarriya , ina abun ya gagara , domin juwarriya tayi nisa sossai kuma balallai taji kira ba, hakan yasa mummy tafara fahintar cewa akwai wani a cikin zuciyar juwariya , duk da cewa bawai ta gane sossai bane , amma kasan tsakamin Uwa da daa .

Kansancewar mommy bata Fiye sa ido akan masu zuwa gun juwarriya ba yasa bata wani damu kanta ba in dai juwarriya zata fita , sai dai tace Adawo lafiya , haka ma yayunta .

Wasa wasa an Shiga satin graduation din juwarriya , sossai suke shirye_ shirye, naira tayi kuka sossai ,domin kuwa Abban juwarriya yakashe misalin miluyan daya akan bikin gama makarantar juwarriya.

Ranar lahadi akayi candyn jujun Abba , Alhmdulilh tafito da sakamako mai kyau , hakan yasa daddy murna matuka da momy , misalin karfe biyu kowa ya watse bayan anci ansha daganan aka rankaya gidan Daddy aka kara wata walimar da haka kowa ya watse cikin farinciki .

Bayan kowa ya tafi gidan , masu aiki sun gyara ko ina da ko ina , aka kara hutawa , misalin karge takwas Na dare dady yakira kowa Na cikin gidan yace yana buktar kowa yazo yasameshi a babban falonshi , har mahifiyar haidar da yayanta , kasancewar itama tazo walimar juwarriya Na gama makaranta da sauran Yan uwan na na nesa .

mamaki juwarriya da husna sukeyi suna me tunanin abun da daddynsu zai fada da ya kira meeting kowa da kowa , Allah dai yasa lafiya .

kasancewar mommy yasa akan abun da za,a tattauna hakan bai bata wani mamaki , da haka kowa ya hallara a falonn dadaly ana jiran karasowarahi .

Fitowa yayi yayi gyaran murya yanemi guri ya zauna , yana karema kowa kallo , gyara muryar ya karayi iron nasu Na manya yace .......... ✍️✍️

*Muje zuwa*


*Mu hadu jibi insha'allahu muji yanda zata kaya*
.

*COMMENTS & SHARE*

*BY MUM FU'AD*

💐💐💐💐💐💐💐

*A SANADIN KUSKURE NA*💐💐💐💐💐

*MALLAKIN*👉 *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
*AND NOW*👇
💐💐💐💐💐 *A SANADIN KUSKURENA*💐💐💐💐💐

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 28 & 29*

*******************

Gyara murya yakarayi irin Nasu Na Maya yayi yace," to Assalamu Alaikum nasan cewa zakuyi mamakin yanda na taraku a nan gurin ..

Kara gyara zamanshi yayi yace," to bakomai ne yasa ba illah wani babban Albishir da zan muku dakuma sauke nauyin da iyayenmu suka barmana da kuma Alkawarin da zan cika musu da burinsu , hakika abun da zan fada yanzu duk Wanda yaji zaiyii matukar farin ciki musamman ma wa,inda wannan lamarin zai faru a kansu .

Jin daddy nata Jan maganan yasa cikin juwarriya duran ruwa tana tunanin karfa ace daddy zai hadata da haidar ne can kuma sai ta sauke a jiyar zuciya bayan tunawa da tayi cewa daddynta bazai taba yi mata abun da ranta bazaiso ba , kuma bazai taba aura mata Wanda bata so ba , kuma tasanda ace zai hadata da yaya haidar dole zai nemi shawararta , balle ma shi yasan cewa ba aure zatayi ba karatu zatayi, da wanan tunanin taji wani sanyi cikin ranta .....


Muryar daddy ce tadawo da ita daga dogin tunanin da ta lula , jin daddy ya ambaci juwarriya , saurin dago da kanta tayi maida hankalinta gun daddy dan jin abun da zaifada .

Juwarriya da Haidar duk yarana ne a guna kuma basu da wani banbanci , sanan bazan taba fifita daya ba a tsakaninsu , duk da cewa juwariya itace 'ya mafi soyuwa cikin raina , kasancewarta sunan mahaifiyata ne , dalilin da yasa Santa yake karuwa cikin raina kenan ,domin nima mahaifiyata ta nunamun so matuka , indai naji sunan juwarriya nakan girmamwa wanan sunana , to dalilin ne yasa har kuke tunanin San da nakeyi Mata yayi yawa , amma ba wai yawa yayi ba ni san ta a zuciyata yake ,kuma itama nayi imani yanda nake Santa haka take sona kuma Sam duk hukuncin da na yanke akanta bazata ba bijirewa ba domin tasan bazan taba zaba mata abun da zai cutar da ita ba , kuma ina da yakinin cewa zata Amince da bukatarmu ....


Tunda daddy yake magana juwarriya taji gabanta Na mugun faduwa tana tunanin wani irin zabi daddaynta zai mata, itakam ta matsu taji me daddynta yake shirin aikatwa akanta .

Shikuwa haidar cikin zuciyarshi ji murna ce fam, dan yana matukar murna da hadin da daddy zai yi mishi .

Cigaba da magana daddy yayi yace," Na yanka hukunci a matsayin Na uba a gun haidar kuma mahaifi a gun juwarriya na ba haidar auren juwarriya halak malak ko bayan ba raina banyarda juwarriya ta auri wani ba bayan haidar domin in mune yau gobe ba mu bane , wannan shine burin iyayenmu tun mahaifin haidar Na da rai ,kuma munyi musu Alkawarin cika musu burinsu kuma mun cika inshallah ina fatan kuma baza Ku watsa mana katsa a ido ba , zaku Amince da kudirin mu?.

Tunda daddy ya fara magana juwarriya tanemu nutsuwarta ta rasa , zufa ce ke fita a jikinta ta ko ina , duk da sanyin essyn dake busowa a falon bai hana juwarriya jin zafi ba ,irinta tashin hankalin da tashiga ba,a magana , bakinta yakasa furta komai illa rawa dayakeyi , cikin ranta tana Ambato sunan khalil tashi tayi dan Shiga daki dan baza iya cigaba da zama ba dan komai zai iya faruwa ,bayan ta mike taji wani irin jiri na dibanta yana barazanar kayarda da ita ,kafafuwanta na mata rawa kanta ta rike tayi baya sai timmm tafadai a kasa sai suma....

Cikin tashin hankali kowa ya nufu gun juwarriya , da Sauri daddy ya dagota ya Na fadin" juwarriya!!

Ina juwarriya batajin me yake fadi Sam , da Sauri yace," Ku fito da mota a kaita Asibiti , dakatar dashi Mommy tayi tahanyar fadin," A a, Alhaji basai ankaita asibiti ba suma tayi inaga tadan shiga rudu ne Shiyasa ta fadi amma in tadan huta aka yaiyyafa mata ruwa zata tashi.. .

Cikin zafin rai yace," wani irin maganin kike haka , kina gani yarinya tayi irin wannan mummunar faduwan kuma kina cewa a kar akaita Asibiti , dole mukaita Asibiti ,kallan suhail yayi yace kayi maza ka fito da motar mu kaita Asibiti , da sauri ya Fita ya daukko key yayi ya fitar da mota , daukan juwarriya sukayi suka sakata A mota suka nufi Asibiti da ita ......✍️✍️✍️


*muje zuwa fans*

*bari muji yanda zata kaya tsakanin juwarriya da Abbanta shi kuna gani zata yarda ayi auren ko kuwa bazata yarda ba ,Ku biyoni a next page ,amma fa sai naga ruwan comments*😍😍


*COMMEMTS & SHARE*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*✍️✍️✍️


💐💐💐💐💐💐💐

*A SANADIN KUSKURE NA*💐💐💐💐💐

*MALLAKIN*👉 *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
*AND NOW*👇
💐💐💐💐💐 *A SANADIN KUSKURENA*💐💐💐💐💐

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 30 & 31*

*****************

Gaba daya hankalin kowa a tashe yake.

Cikin kankanin lokaci suka iso Asibiti da ita , cikin Sauri likitoci suka karbeta suka nufi da ita emergency .

Kokarin binsu dakin daddy yayi , wani likita yayi saurin dakatar dashi yace," Alhaji am sorry to say but you are not Allowed to enter , am sorry ,just few minute everything will be Alright , yana fadin haka ya juya ya shige dakin .

Badan Daddy yaso ba haka ya dawo jiki a sanyaye yana Addu,a cikin Ranshi Allah ya farfado da jujun shi .

mamamki sossai daddy yayi domin yana tunanin. Yanda ta fadi lokaci guda batareda wani matsalan ba , tambayar kanshi yafara yi , to ko juwarriya batasan wannan hadin ne ?? Can kuma wani sashi na zuciyar Na raya mai cewa kai ina juwarriya bazata ki Amincewa da zabin sa ba kodan son da yake yi mata dole zata Amince da zabinsa , sanyi yaji a ranshi , cikin zuciyar na damuwa

Please Login or Register in order to submit comment