Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, ya tambayeta ko ina kawarta Anisa ? nan take shaidamishi cewa sunyi fada , nan ya roketa akan taje ta bata hakuri su shirya , batareda tayi mishi musu ba ko gardama ta amsa da toh , nan suka cigaba da hirarsu irin ta dad'd'adun masoya , kafin
daga bisani sukayi sallama badan ranta yaso hakan ba sai dan khalili din ya bukaci hakan .

Washe gari da safe Juwaiiya ta shirya dan tafiya makaranta ,tun bayan rabuwarsu da khalil a waya tasa a ranta dole taje gidan su Anisa dan cika umarnin khalil , domin bazata taba watsa mishi kasa a ido ba dole ta cika umarninshi da gudun bacin ranshi .

Da sallama tashiga gidansu Anisa , kaitsaye dakinsu ta shiga.

Shiryawa Anisa takeyi dan tafiya makaranta , ganin juwairriya a gidan yasata fadin," hummm kekuma daga ina? Ai na dauka bani bake!, dariya juwairriya tasa tace," hummm dallah ni na tashi cikin farin ciki kar ki batamuun rai , to yanzu gashi mutumin da kika tsana shi da kanshi yace inje in baki hakuri akan abun da na miki jiya , da na bashi labarin yanda mukayi , shine fa yace maza_ maza inzo in baki hakuri , kinga yanda yake yawan tambayarki kuwa ? amma sabida baki da kirki kike Adawa dashi wallahi ki daina haka ba kyau .

Tunda juwairriya take magana Anisa ke wurgamata kallan mamaki , dogon numfashi taja tace," kingama? to tashi mutafi zamu makara , ya zakice mutafi zamu makara na miki magana kin mun banza shine zaki ce wani na tashi mutafi , Juwairriya tafada cikin fada .

Dariya Anisa tasa tace hmm juwairriya kenan mutafi mana zamuyi magana akan hanya kinga yanzu in muka tsaya zamu makara , kitashi mu tafi kawai ..

tashi sukayi suka tafi .

Ko da suka tafi a hanya babu Wanda yace komai , nan juwairriya takarayin gyaran murya tace," lallai Anee ni zakima wulakanci ? Abun har ya kai haka? in miki magana kiyi banza dani ?.

Haba juwairriya toh ni me kikeso in ce miki , ai Sai dai ince Allah ya tabbatar muku da Alkhairi , amma ni kam baruwana bazan kara magana akan khalil ba , illah Addu,a da zan dinga binku dashi Allah ya barku tare Yakuma bar kauna , tana fadin haka tayi shuru bata kara cewa komai ba .

Kwafa Juwairriya tayi tace," uhmm Ameen in ma ba da zuciyarki daya kika fada ba oho dai , da ma tun tuni haka kika fada ma da yafi , amma kintsaya kina wani magana har kina cewa wai wani yaya haidar ne yake sona ,yaje ya nemi husna amma badai ni juju ba dan ni mutuwace kadai zata mun shamaki da Shiga gidan khalil dina ...

Tunda juwairriya take magana Anisa bata ce komai ba illa binta da kallo da takeyi da haka har suka isa makaranta .


Sauri daddy yake yana kokarin hada jakar tafiyanshi , cikin damuwa Hajiya luba take fadin," Alhaji ni fa tafiyar nan ta tsoratani lokaci daya a kiraka ace kazo yaya ba lafiya , wallahi duk tsoro ya kamani Allah dai yasa jikin da sauki ...

Cikin hanzari yake fadin," luba ni kaina fargabar tafiyar nan nake wallahi ina tsoran zuwa in tarar da halin da dan uwana yake ciki ina tsoro ,amma nasan duk yanda Allah ya yi shine daidai .

To ko zaka tafi da haidar din ne ? in yaso Sai kawai ka fada mishi mahaifinshi ba lafiya kaga daga nan ma ya Ganshi , tunda Kasan bai sani ba , kuma in yazo yaji daga baya bazai ji dadi ba , Hajiya tafada cikin damuwa .

Cikin damuwa Alhaji mansur yace," eh to badamuwa kiramun haidar din sai in fada mishi yayi Sauri mu shirya mutafi dan wallahi babban burina in ganni a gaban dan uwana in duba halin da yake ciki kinsan shi kadai yaragemun , Shiyasa duk hankalina ya tashi nake muradin ganinshi , hakane kam ! Hajiya ta fada , gamida fita dan kiran haidar .

Koda ta fita nan daddy ya kira yaya suhail yace maza ya shirya shima zasu tafi tare , da to ya amsa gamida shiryawa .

Samunshi tayi yana zaune yana kallo , Inda tadanyi gyran murya tace," uhm Haidar kazo daddynku nasan ganinka ,da toh ya amsa gamida tashi yabi bayanta.

Samun daddy tayi zaune a kan kujera yace," haidar kayi Sauri ka hada kayanka yanzu aka min waya yayana ba lafiya , yanzu ka shirya zamu tafi maiduguri , nakira suhail na fada mishi shima zamu tafi tare .

Cikin matukar damuwa haidar yace," daddy me yasameshi??, lafiya kalau na barshi fa ko ciwan shine ya tashi .

Ka kwantar da hankalinka haidar jikin nashi ai da sauki sossai , kawai abun da zakayi kaje ka shirya yanzu mu bi jirgi sai mutafi .


Batareda da ya kara cewa komai ba ya tashi jiki a sanyaye ya tafi dan shiryawa .

Bayan sun shirya nan suka fito suka tafi basu zarce ko inaba sai garin borno...............


Bayan juwairriya ta dawo daga makaranta , nan ta Shiga tambayar mahaifiyarta ina daddy ??.

Nan ta shaida mata cewa ya tafi borno Abban haidar ba lafiya .

Nan ta jimanta hade da Addu,ar samun sauki .


Da yamma khalil ya danno hancin motarshi layinsu juwairriya bai fakata a ko ina sai kofar gidansu juwairriya .

Sanye yake cikin shadda geznal Ash colour , kanshi sanyi da hula light Ash sai takalminshi manne a kafarshi shima Ash colour , hanunshi sanye da Agogo da zobe duk Ash colour , sai dan karamin glass din dake manne a fuskarshi daya kara baiyyana sirrin kyanshi ,sanjenshi baki kirin da dan kasumbanshi da ya kwanta luff yana daukan ido hade da kyalli da sheki , gawani daddad'an kamshi dayake fitarwa .

Nan ya daukko tsadaddiyayar wayarshi ya fara lulubar numbernta ya kirata , bugu uku tayi t saurin dauka , cikin sassanyan muryarshi dake kashe mata jiki yace," gani a kofar gida gimbiyata , a fito lafiya ....batareda yaji amsar da zata bashi ba yayi saurin katse wayar gamida yin wata yar karamar dariyar da takara baiyyana lotsatsun dimples dinshi .

Murna sossai juwairriya takeyi jin khalili yace yana kofar gida , sauri _ Sauri tayi ta fada toilet tayi wanka, tafito , nan ta bude drowern kayanta tana kalla tana tunanin kayan da zata sa .

Nan idanta yakai kan wani dankareraren less dinda da daddynta ya siyomata daga garin kwatano , nan ta fito dashi tasaka ta danyi light make up tasa pink din jambaki , da dankunne pink takalmi pink , ta murza daurin ture kaga tsiya ,sai gylenta fari kasancewar akwai touches din fari a less din nata, turare ta dauka ta fesa da sauri.

Nan ta kara Kare ma kanta kallo a madubi ta juya ta kara juyawa tace," Wow tabarakallah Masha Allah !! ni ma mum Fu' ad ganinta sai da nakasa rufe baki domin kuwa juwairriya tayi kyau iya kyau sai dai ayi mata hass.

Bayan tagama kalla kanta ta fita, samun maifiyarta tayi da husna suna zaune suna jimamin ciwan Abban haidar .

Ganinta ta fito yasa mahaifiyar tasu ta kalleta tace," juwairriya ina zakije da yammanan baki fadamun ba ?.

Cuno dan karamin bakinta tayi tace," mommy fita fa zanyi kuma ma kofar gida zanje yanzunann zan dawo .

Juwairriya kofar gida gun wa?? Mahifiyarsu ta fada cikeda tuhuma .

Cikin Inda _Inda tace," uhm mommy fa class mate dinane yazo yanzu zan dawo kar yace na bata mishi lokaci barin tafi tana fadin," haka ta fita da sauri , da kallo mahaifiyarsu ta bita da shi tana me mamakin halin juwairriya .

Ita kuwa Husna tunda ta kalleta ta tattatra ta watsar bata kara kallanta ba bare ma taimata magana .

Cikin yanayin yanga Juwairriya ke tafiya tana karairaya hade da lumshe ido .

Saurin fitowa yayi ganin fitowarta a gida.

Ganin yanayin yanda take tafiya yasa Khalil kara jin Santa cikin ranshi domin yanda takeyi ya birgeshi .

Da sallama ta karaso gurinshi tace," Assalamu Alaikum, cikin murmishi ya amsa da wa ,alaiki salam .

Shuru tayi batace komai ba , tsaye yayi yana karemata kalllo .

Nan ta dan kallasahi tace," uhmm wai wanan kallon fa ?.

Dogon nnumfashi yaja yace," uhmm ai yau dinne kinmin kyau sossai wallahi fiyeda yanda kike tunani .

Dariya ta kyalkyale tace," kai ko wallahi kafiye zolaya , wallahi ba zolaya bane da gaske nake kinmin kyau sossai .
Uhmmm tace," tayi shuru tana kallanshi .
Ko zamu shiga mota sai miyi hirarmu ??.
Toh tace," nan ya bude mata motar ta shiga shima yashiga .

Cikin tattausar murya yace," to yasu mama da baba da kowa da kowa fatan duk suna lafiya ?
Cikin sanyin murya tace," lafiya kalau .
Nan ya juyo ya kura mata ido yace," juwairriya??, dago kai tayi ta kallashi tace," na,am !!, Cikin maida hankali yace," zaki aureni!?.
Samun bakinta tayi da fadin," zan aureka in zauna dakai na har Abada matukar bakai ka juyamun baya ba tafada cikin zallar soyaiyya da kauna ...................✍️✍️

*Hummm An ya juwairriya baki za'ke da yawaba ??????*

*Hummm muje dai zuwa sannu a hankali*


*IN BANGA COMMENTS BA BAZAN YI UPDATE GOBE BA KO JIBI*

*COMMENTS*

*SHARE*

*LIKE*

*&*

*VOTE*


*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


*page 13&14*


*KUYI HAKURI KWANA BIYU KUN JINI SHURU WALLAHI WAYATA CE TA SAMU MATSALA SHIYASA KUKAJINI SHURU , AMMA YANZU KAM ALHMAMDULILAH ZAMU CI GABA INSHALLAHU.*


*INA MIKA GODIYATA GA SUK WANDA YASAMU DAMAR KIRANI DAN JIN LAFIYATA GANIN YANDA NADAN KWANA BIYU BAN HAU ONLINE BA , NAGODE NAGODE SOSSAI ALLAH SAKA DA ALKHAIRI ALLAH YA BAR KAUNA. AMEEN YA ALLAH*


******************

Jin kalaman juwairriya yasashi cikin matukar farin ciki hade da kayataccen murmishin da ya kara biyyana kyawun fuskarshi .

Nan ya kura mata ido yace, " nagode sossai jujuna wallahi Nima ina sanki ina matukar kaunarki , bazan taba juya miki baya ba nayi miki Alkawari .

Cikin farin ciki juwairriya tace,"nima haka nayi maka Alkawari .

Hira sossai sukayi cikeda da soyaiyya da jin dadi , da farin ciki ....

Misalin karfe Tara mahaifiyar juwairriya taji shuru Juwairriya bata dawo ba.

Nan ta aika husna ta duba ko juwarriya na kofar gida .

Badan husna ta so ba ta tashi ta fita .
Bude gate din tayi ta dan leka gudun kar juwairriya ta ganta tamata rashin kunyar da ta saba .

Ganinta zaune cikin mota suna hira hankalinta a kwance yasata komawa gida ta tasanar da mahaifiyarsu.

Cikeda da damuwa mahaifiyarsu tace," Husna dan Allah je ki kiramun ita , meyasa juwairriya takesan bani Matsala ne , wallahi ni hankalina ma duk a tashe yake , tunda mahaifinku ya tafi har yanzu shuru bai kirani ba nakira wayoyinsu gaba dayansu a kashe wallahi , amma sabida ita bata da hankali kinga ko a jikinta .

Badan husna taso hakan ba tace," mommy nifa bansan abun da zaisa juwairiiyya tamun rashin kunya wallahi kisan juwairiyya bata da kunya yanzu sai ta mum rashin kunya.

Hakuri mahaifiyarsu ta bata , nan ta tashi tafita badan ranta yaso ba .

Kwankwaso murffin motar ta farayi , nan juwairriya ta wurga mata wani banzan kallo ta bude kofar tace," ke lafiya miye ??, batareda ta bata amsar tambayarta ba tace," in kin ga dama kizo mommy na kiranki , tana fadin haka ta juya ta tafi rai a bace .

Nan khalail ya kalli juwairriya yace," juju!! Waye wanan haka tazo batasan yanda zatayi lafazi mai kyau ba , balle kuma ta gaisheni ko bata ganni bane ??.

Ta'be baki tayi tace," hmm ta ganka wallahi rashin mutuncin ne kawai da wulakanci amma kayi hakuri zanyi maganinta .

To wao waye ita ma a gurinki ?.

Kara tabe karamin bakinta tayi tace," uhm yayaa ta ce.

Zaro ido yayi yace", Haba dai yayarki shine baki fadamun ba nafito na durkusa na gaisheta ba
tunda ya yaraymu ce.

Dariya tasa tace," tab wa zaka gaisar din? husnan ?? Lallai kuwa .

Ha,a to miye abun dariya a ciki ai ta cancanci a gaisheta, in akwai ma abun da yafi gaisuwa ai zan mata , ko kinmanta itadin ta dabance, yayar masoyiyata ce fa masoyiyata!! kinga dole in yi gaisuwa in kwashi Albarka , yafada gamida yin dariya ,gaskiya karki karamun haka , ai da sai
ki fadamun, yanzu kinga zaki sa ta fadama mommy race," bani da kirki , yakarasa maganar hade da kangwabar da kai .

A,a karka damu zan yi musu bayani bakada matsala ..., nan suka cigaba da hirarsu .

Koda Husna fa shigo gida a fusace ta shigo , cikin fada take fadin," mommy nikam gasakiya karki kara sakani a shirgin juwairriya king a inda ta yarfani a gaban mutum , mommy karki ga yanda yarinyarnan tamun , Na fada mata saqonki , in taga dama ta shigo gida to in ba ta shigo ba to ?! ruwanta .

Dogon numfashi mahaifiyarsu taja , batareda tace," komai tai tagumi da ta rafka .

Cikin damuwa Husna tace," mummy yadai ya kikayi shuru ina fada miki magana kinyi shuru?, hmmm to husna mai zance , saidai kawai ince Allah ka shirya min juwairriya shine kawai, da Ameen husna ta bita.

wayar Hajiya luba ce ta fara ringing , ganin sunan Abban juju ya baiyyana akan screem din wayar yasata saurin dagawa tace, " husna babanku ne , dauka tayi ta sa a kunne tace," Assalamu Alaikum , murya a sanyaye ya amsa da was, alaiki salam , jin yanayin muryarshi ya yi matukar fadar mata da gaba, nan ta dan daidaita nutsuwarta tace," uhm Abban Juwairriya lafiya??.

Murya a sanyaye yace," saidai miyi hakuri Allah ya yi ma yayana rasuwa .

Wani irin salati Hajiya luba ta rafka tasa kuka tace," *innalillahi wa inna illaihir raju,un* yaya ya rasu?? Cikin matukar damuwa yace," yarasu naso tun dazo na kiraki tunda muka isa wayoyinmu babu caji sai yanzu na samu caji , gobe in Allah ya kaimu za,ayi Jana izar shi .

Jin muryarshi ta fara rawa yayi saurin katse wayar , kwalla ta fara zuba a fuskarshi.

Cikin matukar tashin hankali mommy ta fadawa husna suka fara kuka sossai hade da jimami da tashi hankali .....

Ganin dare yayi yasa khali fadin," baby Anya baza ki Shiga gida ba dare yayi sossai kinga to 10 fa yanzu.

Shagawba fuska tayi , ta dan cuno karamin bakinta tace," har ka gaji dani kenan koh? Shine zaka ce in tafi gida ?.

Dariya yasa yace," A,a baby ba haka bane dare yayi banaso mama ta yimiki fadane kar in jama wanan beautiful face din bacin rai yafada hade da kashe mata ido , but na miki Alkawari gobe inshallahu zan dawo zan dade sossai har sai kin gaji dani .

Sa hannu tayi a baki tadan zaro ido tace," kai rufamun Asiri taya za,ayi in gaji dakai , wallahi bazan gaji da kai ba sai dai in Kaine zaka gaji dani , tafada hade da kara cuno karamin bakinta cikin sigar shagwaba.

Dariya taso bashi sossai yace," uhmm baby in na biyeki zamuyi dare , kiyi hakuri I promise u gobe zaki ganni early .

To ta ce ta fara kokarin bude kofar , Saurin. dakatar da ita yayi yace," dan tsaya , nan ya ciro kudi a Aljihu ya mika mata .

Langwabar dakai gefe tayi cikin sigar shagwaba tace," wallahi bazan karba ba , da sauri ta bude motar tafita hade da yimishi bye_ bye ta Shiga gida da sauri.

Dariya kawai yayi ya girgiza kai yaja motarshi ta tafi .

Misalin karfe goma juwairriya ta shigo gida .

Jin karar kuka da shasheka yasa gabanta yayi mugun faduwa , da Sauri ta karasa cikin dakin .

Ganin husna da mommy suna kuka yasata zubewa a kasa murya na rawa tace," mummy lafiya??? .

Cikin kuka mommy take fadin," juwairriya Abban haidar ya rasu !!! .

Cikin tashin hankali juwarriya tace," ya rasu!!!.??.

Kada mata kai mahaifiyarsu tayi Alamar ehh
Nan ta fara kuka mai cin rai da ban tausayi , dukkansu kuka sukayi sossai babu me rarrashin wani a cikinsu .

Kuka sossai sukeyi , Ringing wayar juwairriya tafara yi , ganin sunan da tasama khalili ya fito a sensor din wayarta ne yasata saurin dauka, sabanin daa da batayi niyyar dauka ba .

Tashi tayi to dan goge hawayen fuskarta ta shige daki da sauri .

Mommy da husna kuwa ko ta kanta basuyi ba suka cigaba da kukansu .

Cikin Murya kuka tace,"Assalamu Alaikum .

Cike da fargaba yayi saurin fadin," juju lafiya naji muryarki haka meke faruwa ??.

Cikin kuka tace," bayan mun rabu na dawo gida na tarar an kira waya ana fadama mommy na cewa yayan babana ya rasu dazu .

Cikeda damuwa yace," Allahu Akbar innalillahi wa inna illaihir raju,un to Allah ya jikanshi ya mishi rahama yasa ya huta , da Ameen ta amsa cikin sanyin murya .

Numfaawa yadanyi yace," toh Barin barki sai da safe , badan taso hakan ba tace," Allah ya kaimu , kara bata hakuri yayi daga bisani ya kashe wayar.....

Fallo ta koma suka cigaba da kukansu hade da jimami .

yan da dai suka ga dare haka suka ga rana , babu Wanda ya runtsa a cikinsu sai dai barci barawo......✍️✍️


*MUJE ZUWA*

*KU SUBURBUDO COMMEBTS IN SUBURBUDO TYPING...βœοΈπŸ™„*

*COMMENTS*

*SHARE*

*LIKE*

*&*

*VOTE*


*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*Page 15 &16*

Washe gari da sassafe Hajiya luba da husna da fahad suka nufi hanyar garin borno , duk yanda sukayi da juwairriya akan ta bisu su tafi amma Sam taki yarda a cewarta sun fara jarabawa a school hakan yasa bazata bisu ba .

Ba yanda Suka iya haka suka barta amma badan sun so ba , sai dan juwairriyan ta bukaci hakan , cikin ran mommy sam zuciyarta bataso barin juwarriya a gida ba domin barin 'ya mace budurwa ita kadia a gida matsala ne , dama yaya!? juwairriya take a gabanta ma balle kuma batanan sai dai kawai tace Allah ya tsare Allah kuma ya shirya , da ma husna ce da sauki , sa,arta daya cewa da tayi zasuyi jarabawa amma da ko taki ko taso sai ta tafi , amma ba yanda ta iya da ita .

Duk yanda fahat yaso tursasata akan taje amma fur juwairriya taki duk da cewa Kasan zuciyarta na San taje, amma wani sashi na zuciyarta bazata iya jure kwananki batareda ganin khalil dinta ba , Shiyasa ta gwammaci ta hakura da zuwan .

Ba yanda suka iya haka suka barta badan ranso yaso ba .

Bayan sun gama shiryawa suka kama hanyar zuwa mai duguri.

Murna sossai juwairriya tayi da tafiyansu , hakan zai kara bata damar soyewa da khalil dinta cikin kwanaciyar hankali .

Ringing wayarta ta fara ,yi ganinan sunan da ta Sama khalil ya baiyyana akan screen din wayarta yasata sakin wani kayataccen murmishi .

Da sallama ta dauki wayar, jin dadd'an muryar ta yasashi lumshe idanunshi ya amasa da wa,alaiki salam , Anjima zanzo , yana fadin," haka ya kashe wayar .

Da kallo juwairriya tabi wayar tana mamakin kashe wa dayayi lokaci daya .

Saidai kuma jin yace zaizo anjima yasata sakin jiki hade da zumudin zuwanshi .


Misalin karge biyar na yamma Khalil yayi parking lafiyyaiyar motarshi a kofar gidansu juwairriya.

Tsayawa fadin irin kyawun da khalil yayi bata lokaci ne.

Daukko wayarshi yayi yafara kokarin kiran layin juwairriya , bugu biyu ta dauka , ina kofar gida , yana fadin haka ya kashe wayar .

Cikin sauri juwairriya tafara kokarin shiryawa , Atamfa ta sa ta danyi light make up ta Murza daurin ture kaga tsiya , dan karamin gyalenta tadan yafa , Takara Kallan kanta A Mirrow tana me kara yaba irin kyan da Allah yayi mata .

Turare ta daukko mai dadin Kamshi ta fesa a jikinta ko ta ina .

Fita tayi da

Please Login or Register in order to submit comment