Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gwaiwarta ta nufi gurinsu YAYA suhail da suke tsaye suna kallo sun gagara cewa Komai amma zuciyarsu na tausayama kanwar tasu .......

Cikin kuka tace," YAYA dan Allah na rokeku kusa baki daddy ya yafemun dan Allah....

Kuka take sosaii muryarta ,har tafara dashewa ,ta nufi gurin husna tace," husna kisa baki dan Allah daddy ya yafemun kinji , tafada gwanin ban tausayi ......

Ganin kowa ya gagara mata magana yasa jikinta yayi sanyi ta Kara fashewa da kuka , kanta a kasa tamkar me neman gafara, duk da cewar Neman gafar take ....

A zafafe daddy yayi mata wani figa ya nufi hanyar fita da ita .......

Ganin haka yasa mommy ta gagara jurewa ,kukanta ya tsanata cikin muryar kuka tace," Alhaji! Alhaji dan Allah Kayi mata a hankali karka illatata zata fita da kanta ka kabarta haka , dan Allah Dan Allah badan halinta ba ka yafemata mana tunda har ta gane kuskurenta Alhaji Kayi hakuri .......

Wani kallo yabi mommy dashi cikin tsantsar bacin rai yace," wallahi tallahi in kika sake kika sake magana wallahi sai kin bita, keda ita gaba dayanku ...

Ai jin maganar daddy yasa husna fadin," tab daddy Kayi hakuri baza,ayi haka ba mommy bazata bar gidanan akan wanan ba , miye laifin mommy a nan daddy ?

juwairriya kiyi hakuri ki lallaba ki tafi kar ki jama mahaifiyarmu .....

Goge hawayen fuskarta juwairriya tayi ,murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace," A,a baza,a ayi haka ba inshallahu kuyi hakuri ni zan tafi , sanadina mommy bazata bar gidanan ba .
nagode zan tafi , takarasa maganar gamida fashewa da kuka ,ta karasa da gudu ta fita a gidan.........✍✍

*MUJE ZUWA*

*COMMENTS AND SHARE*

*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER 1122@GMAIL.COM*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 58 & 59*

Bayan ta fita wani jiri ne ya fara dibanta..
Da kyar ta iya lalabawa ta taro abun hawa ya nufi gida da ita......

A bangaren daddy kuwa bayan juwairriya ta fita, cikin tsananin bacin rai ya koma dakinshi, batareda ya kula kowa ba , suma ganin haka yasa suka tafi suka bar wajan jiki a matukar sanyaye .....

Mummy ce ta bi bayanshi, ta Shiga daki, muryar a sanyaye tace," kafasa fitan ne kuma ?

Shuru yayi batareda yace mata komai ba sai cire hularshi da yayi da babbar rigar jiki shi , hannu yasa ya dafa kashi cikin zuciyarshi na mishi zafi , yana me kara jin haushin juwairriya , amma tabbas wani sashi na zuciyarshi na bala'in tausayi ta, yasan tana cikin damuwa yanzu haka , amma girman laifin da tayi mishi ne yasa ya danne tausayin ta da yake ji ...

Cikin ranshi yake aiyyan cewar wannan hukunci shine dai dai da ita, amma Allah ha sani har yanzu zuciyarshi na tsananin son juwairriya , shi yasa da ta bijire mishi yake jin zafin abun matuka domin ba haka yayi tsammani daga gareta ba...,

Tsugunawa mommy tayi a a kasa tana kuka tace," Alhaji dan Allah..... batareda yaji abun da zatafada ba yayi saurin daga mata hannu ya dakatar da ita ta hanyar fadin," indai akan juwairriya zakiyi mun magana toh tun wuri gara ma kimun shuru , in kuma ba haka ba wallahi tallahi zakisha mamakin abun da zai biyo baya nafadamiki , ni yanzu hakama nafi bukatar zama ni kadai a dakinan kije kawai bana bukatarki a halin yanzu nagode....

batare da mommy Takara cewa komai ba ta tashi cikin ladabi da girmamawa tace," Allah baka hakuri , tana fadan haka ta fita jiki duk a sanyaye .......

Bayan ta fita tunani sossai daddy yacigaba dayi zuciyarshi fal da bakin ciki da bacin rai , domin abun da ya fara mantawa yau antuno mishi dashi ........

Ita ko mommy bayan tafita dakin ta nufa taci kukanta mai isarta, tana me tsananin tausayin yar tata kamar me..

Ita kanta Mommyn tasan juwairriyan ce ta jawo , duk da cewar kaddarar tace hakan babu yanda za,ayi, kuka tayi sossai zuciyarta cike fall da tausauyin jujun ta.... ....

Bayan mai Napep din ya ajiyeta a gida kai tsaye ta Shiga gidan hannunta na rike da kanta sakamakon jiri da takeji , idanuwanta sunyi bula bula suyi jajir , tana tafiya tana layi ........

Ganin motar Khalil a parking space din gidan yasa gabanta yayi mugun faduwa , bugun zuciyarta ya Kara tsananta , tana taka kasa a hankali kamar me tsoron takawa , jiki a sanyaye ta runtse idonta ta Shiga cikin daki kirjinta na dukan uku_ uku .......

Ganinshi zaune a kujera yana Kare mata kallo yasa ta nufeshi tana tafiya a hankali , tsugunnawa tayi a gabanshi tace," sannu da dawowa .....

wata harara ya wurgamata yace," daga gidan uban wa kike?
Cikin tsoro tace," Khalil kayi hakuri wallahi kewan gida nake , Shiyasa naje na dubasu , kuma suka wulaka tani suka koreni dan Allah Khalil kayi hakuri , ka tausaya.... bata karasa magana ba taji saukar wani gigitaccen mari da yasata jin wani jiri na barazanar kayar da ita , banda Allah yasa a tsugunne take da tabbas ta fadi a kasa......

Mikewa yayi cikin fushi yaxe," tashi ki barmin gida na ,ki komai can gurin iyayen naki tunda su kika zaba , har zaki iya fita ba tareda izini na ba , da can kina San kasancewa da iyayen naki amma kika zabe ni , to baki Isa ba , nabaki mintuna kadan ki bar min gidana kafin ranki yabaci .......

Jin ya fadi haka yasa gaban juwairriya yakara faduwa kukanta ya tsananta , zubewa tayi a kasa tasa hannayenta ta rike kafofinshi ,tafara magana cikin da shashiyar muryar ta da kuka ya dashar da ita tace,"Khalil dan girman Allah karkamun haka in ka koreni yanzu ina kake tunanin zan je kar kamanta na bar kowa sabida da kai , karkamun budulci kayi Mum halarci ko dan soyaiyaiyar da na nuna maka dan Allah,...

Jan kafarshi yayi ya tureta gefe , ya fita abunshi...

itako tsabar tashin hankali ma kasa kukan yayi Sai kallo da ta bishi dashi .....

Mikewa tayi tana tan gyadi wani jiri na dibanta ,ta nufi dakinta ta na Shiga ta fada gado a sume....


Bayan ya dawo gida kai tsaye ya nufi daki , ganinta kwance a gado yasa ya tabe baki , cikin ranshi yace," mara zuciya dama nasan ba iya tafiya zatayi ba......

Ganin nononta da ya baiyyana yasa ya hadiyi yawu , gamida da jin wata sha'awa ta kamashi ...

Nan take ya cire kayan jikinsh ya nufeta gadan gadan ,ya biya bukatarshi Akanta ......

tunda yafara sex da ita ko motsawa batayi ba ...
sai da ya tabbatar ya biya bukatatshi akanta sossai , har yayi mai isarshi kafin ya batta .......

Ganin har ya gama yaje yayi wanka amma bata farka ba yasa ya tabata ya kai hannunshi daidai hancinta yana son ji ko tana numfashi , amma shuru bai ga Alamar hakan ba , jijjigata ya farayi ko zata tashi amma ina bata ko motsawa ......

Kayanta ya maida mata ya daukko hijabinta yasa mata .....

Cikin hanzari ya dagota ya nufi moto da ita sai Asibiti .......

Bayan sun sun iso asibitin ya kira abokinshi likita ,bayan ya kirashi ,Likita ya shaida mishi da ya shigo asibiti .......

Fitowa likitan yayi daga office ,ya jegurin Khalil din dan ganin halin da juwairriyan take ciki......

Da Sauri aka nufi emergency da ita aka fara bata taimakon gaggawa .......

Bayan yan mintuna likitan ya fito gamida Kiran Khalil office ......

Bayan sun zauna nan likita yajefa ma Khalil tambaya yce," Khalil ! Khalil ya dago kai gamida amsawa yace," na,am siririn gilashin fuskarshi likitan yacire yace," amm me ke damun yarinyar nan ?

Cikeda da nuna amalun ko in kula Khalil yace," doctor ina zan sani, ina zan San mai ke damunta ..

kada kai doctor yayi yace okay, amma ya akayi damuwa tayi mata yawa haka garin YAYA?
har take nema ta illata mata zuciya bayan jininta da ya hau , kuma ga dukkan alamu ka making sex da a ita A lokacin da bata cikin haiyyacinta Wanda shima ya ja mata matsala,, and bayan nan ma kayi mata na karfi dan kaga bata motsi ,kuma ka dade akanta sossai meyasa kayi hakan?

Cikeda jin kunya Khalil yace," am sorry doctor nakasa controling kai na ne Shiyasa , amma bazan kara aikata hakan ba Inshallahu........

Dogon numfashi doctor yaja ya kakara mai da kallanshi zuwa Khalil, cikeda nustsuwa yace," okay naji wanan , amma wani damuwa yake ciki bar ya keso ya bata mata matsala a kwakwalwarta da zuciyarta?
Uhmm to doctor wanan dai bansani ba , amma in ta farfado zanyi kokari in tambayeta ta fadamun damuwar ta ,Khalil yafada cikin sigar rashin gasjiya , hmmmm doctor yace" gamida mikewa yace," "amm zaka iya tafiya in naga da yuyuwar ka Shiga ka dubata sai na fadamaka in kuma babu sai kajira lokacin da zakashiga ka dubatan , okay Khalil ya fada gamida mikewa ya tashi ya fita a office din cikeda jin kunya ......

Bayan likita ya Shiga dakin hutun da aka dawo da juwairriya , yaga tana barci , sai rama da fuskarta da tayi fuskarta duk juruwayen hawaye yasa tausayinta ya kamashi ya girgiza kai ya fita.........

Bayan ya fito ya shaida ma Khalil zai iya Shiga ya ganta har sanda zata farfado , yafada mishi gamida tafiya dan cigaba da aikinshi na duba marasa lafiya ........

Dakin Khalil ya Shiga Inda ya zauna yana Kallan juwairriyan da take ta barci , ganin haka yasa yadan tausa taya mata......

Bayan minti talatin juwairriya tafara bude idonta a hankali , wani nauyi kanta yayi Mata, tana jin dakinn na juyamata ta runtse idonta ......

Ganin ta farka yasa Khalil fadin," sannu ko? Allah ya sauwake , shurutayi batareda da tace komai , tunawa da abun da ya faru da ita tayi , nan danan kwalla masu zafi suka fara sauka a fuskarta ....

Ganin haka yasa Khalil fadi," me kinsan Allah karkijama kanji damuwa daga farkawa sai kuka , ai gashi likita yace jininki ya hau , so in kika kashe kanki babu Wanda kikayima asara kinji na fada miki , a hankali ta bude bakinta tace," yunwa nakeji , harara ya gallamata yacre" yunwa kikeji shine sai kin ma mutane kuka , yafada gamida tashi ya fita dan siyo Mata abinci....

Bayan ya fita tafara kokarin mikewa , amma jikinta yayi mata tsami sossai ..

Jin wani ruwa na gangrowa ta kssanta yasata jin mamaki , cikin ranta tace," garin yaya? Khalil yayi sex dani kenan, ba a haiyyacina ba , jin babu pant a jikinta ya kara tabbatar mata da hakan dan kuwa tasan bata taba zama ba tareda da pant a jikinta ba , jin hakan yakara tabbatar mata da cewar Khalil ya yi amfani da ita a lokcin da bata haiyyacinta .....

Wani kuka ta fashe dashi mai matukar cin rai tace," Kai kai kai wani irin mutum ne wannan maras imani ,me nayi mishi haka yake azabtar dani haka , lallai rashin imanin ya kai rashin imani, amma ba komai duk *sanadin kuskurena ne* har hakan ke faruwa dani tafada gamida kara fashewa da matsanancin kuka..
tasan cewa tabbas da tayi biyaiyya ga mahaifinta da duk haka bai faru da ita ba , hakika da tabi zabin abbanta da bata fuskancin irin wannan ba , rana zafi Inuwa kuna, runtse ido tayi tana tunawa da irin yanda suka wanye da mahaifinta ,tana fadin," kaicona,haka ta kasance zuciyarta nayi mata sake_ sake iri _iri , tana me cike da nadama , amma hakan bai hana son Khalil ya fta cikin ranta ba .......

Bayan yan mintuna Khalil ya dawo yayi mata take away ya bata..
sossai taci abincin kasancewar yunwan da takeji ,ga shi sex din da khalil yayi da itama kadai ya isa yasa taji yunwa sossai .....

Bayan tagama cin abincin ya dan tsurgamata , tadan kishingida tana ta tunani iri_iri cikin ranta .....

Kallanshi tayi murya a sanyaye tace, Khalil! dago wa yayi ya kalleta yace," ya akayi ?
Amma Khalil kayi sex dani ne a lokacin da bana cikin haiyyacina ko?
Cikeda Nuna alamun ko in kula yace," eh menene? hmmm ba komai shikenan kawai dama na tambayeka ne , tafada cikin sigar ,mamaki , okay yafada a takaice

Amma Khalil meyasa kayi hakan kasan bana cikin haiyyacina ?
tafada cikin muryar sanyi sanyi ..
Ha,a miye dan na bukace ki a wannan lokacin , ai matata ce ke ina da damar da zan biya bukata ta akanki a duk lokacin da naso ai.....
hakane tafada a takaice batareda da takara cewa komai ba , ta kwanta abunta ......


ba laifi a Ranar tasamu kulawa agun Khalil,domin indai zatayi abu yana taimaka mata ,bai fita ko ina ba wunin ranar suna tare dan har kwana ma yayi a asibitin ,amma ba ,a san ranshi ba , sai dan gudun kar wani yasan halin da suke ciki ne yasa hakan, da ya kira mai aikin Hajiya ta kwana da ita....

Washe gari juwairriya ta nemi da a sallameta a cewarta ita tagaji da zaman asibitin, kuma taji sauki tanaso taje tayi wanka , bazata iya wanka a asibiti ba , nan likita ya rubuta mata sallama ya bata maganunguna ,yakuma kara shaida mata ta da ta kiyaye sa damuwa a ranta ...

Cikeda da gamsuwa tace," inshallahu nagode ..

godiya sossai sukayi mishi, bayan sun biya kudi a gun reception din daga bisani suka nufi gida ....

Har suka isa gida babu Wanda yayi ma kowa magana a cikinsu .

Bayan sun shigo gida kai tsaye juwairriya dakinta ta nufa ta Shiga bayan gida tayi wanka kasancewar tsamun da jikinta yayi mata , ga kuma wankan tsarkin da yake kanta , hakan yasa ta kasa samun sukuni ta dage ta dawo gida......

Bayan ta fito tayi sallolin da ake binta .. ..

Bayan ta iddar tasa kaya , ta kwanta akan gado tayi shuru tana tunanin , hawaye na bin gefen fuskarta.....

Dakin yashigo ganinta a kwance yasashi zuwa kusa da ita ya zauna a kan gadonta , hannunshi ya kai kan fuskarta yana share hawayen fuskarta yace," bazaki daina kukan nan ba?yafada cikin sigar rarrashi ..
shuru tayi batareda da tace komai ba?

kamar an tunzurota ta mike tace," la kayi hakuri wallahi tallahi na manta ne, kayi hakuri bari na hada kayana na tafi , tafada gamida tashi ga nufi gurin drawer kayanta ..

Da sauri ya tashi ya rike hannunta yace," ke miye kike yi haka ai komai ya riga ya wuce kardai ki karamun haka kinji ko ? in ma kintafi ina zakije yanzu ? murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace,"nasani babu Inda zanje ,amma hanyar Allah da yawa take ,Allah bazai ta ba bari na wulakanta ba tafada hawaye na bin fuskarta ..

Kiyi hakuri amma yanzu babu inda zakije, kina nan kinji ko?
To tace gamida share hawayenta , ta zauna tayi shuru , tashi yayi yayace," barinje in kawo mana abun da zamuci ko , yanzu lokaci ya kure bazaiyuyu muyi girki ba , dare ya farayi ,to tace, tafada murya a sanyaye .....

Nan ya tashi ya fita yayi musu take away ya dawo , suka ci abincin daga bisani sukayi kallo ...

Misalin karfe goma na dare suka kwanta cikin farin ciki , suka farantama junansu rai ,kamar su dore a haka ......

A 'yan kwanakin nan ba laifi Khalil na farantama juwairriya rai , sai dai abun da ba,a rasa ba , amma duk da hakan ba wani sake mata yake sossai ba , hakan yasa kullum cikin tunani take iri_iri.....

*A gurguje*

bayan watanni biyu , abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda shirye_shiryen bikin husna Al_Amin da kuma suhail....

shirya _shirye ake sossai , amma cikin zuciyoyinsu suna matukar jin zafi da radadin rashin yar uwarsu a harkokin bikin su ..

mommy ma komai takeyi a sanyeye takeyi domin duk wani bugun zuciyarta juwairriya sai ta fado mata a rai......

Biki ya rage saura kwana biyu yan uwa da abokan arziki suka fara zuwa gidansu Husna dan fara gudanar da shirye_ shiryen biki.....

A bangaren su juwairriya kuwa ?

A yan watannin nan
Kullum munanan halayen Khalil kara yawaita suke matuka....

Juwairriya duk ta rame ta fita haiyyancinta.......

A na hakara ta kara samun ciki, haka yakara sa ta zubar da cikin da ta Kara samu...

A wannan karan sam taki yarda ta zubar hakan yasa ya shaida mata cewa Indai har bata amince ba to tabbas sai ya sake ta tsoron hakanne yasa juwairriya ta yarda badan taso ba sai dai dan babu yanda ta iya.....

Haka ta na kuka haka aka cire cikin.

A wanan karan cikin sirri likita ya tabbatar mata da cewar matukar ta kara zubar da ciki a jikinta toh maihaifarta zata iya samun babbar Matsala domin mahaifarta bata da karfi sossai ....

Tsoron sossai juwairriya taji gamida yima likitan godiya ta tafi .........

Hakika zuwa yanzu Juwairriya na dumbin da nasanin auren Khalil ....

Dan kuwa da za,a bata zabi tsakanin rayuwarta da mutuwarta babu shakka mutuwarta zata zaba .......

Domin Khalil yagama fita a ranta domin yanzu har tsoronshi takeji..
bata san ganinshi , sannan in yadawo in dai yana bukatarta to ko taki ko taso haka zai danneta yayi batareda da ya damu da halin da zatashiga ba .....

A kullum in ta zauna takanyi tunanin cewa anya Khalil ne musamman in ta tuna rayuwarsu ta baya, da kuma dangin ta, da soyaiyyar da mahaifinta ya nuna mata , hankalinta na matukar tashi tana ji kamar ta mai da rayuwarta koma kamar ta daa , amma ina babu halin hakan....
Cikin ranta take aiyyana cewa zata ci gaba da zama hakan har taga yanda hali yayi .......


A bangaren gidansu mommy kuwa ..
A yau Asabar a ranae ne dubannin jama,a suka shaida daurin auren , husnah, Al_amin da kuma suhail .....

Inda akaci akasha , daga bisani aka kai amarya husna gidanta , husna da mommy sunsha kuka domin kukan nasu da biyu sukeyi tunawa da juwairriya .......

Sukuma angwayen suka nufi gidajansu gurin Amarensu ......


Bayan kwana biyu da biki kowa ya watse a gidan , anbar daga mommy sai daddy , sai mai aikinsu da take zuwa tamusu aiki ta koma ........

Toh fa !!anan ne gida yayi ma mommy fadi , saban kewan juwairriya yakara dirar mata.....

kuka sossai tayi , tana tunanin yaran nata , amma ta wani sashin tana jin dadin hakan domin ta aurar da yaranta da hanunta , sai dai akasin da aka samu na auren juwairriya , kuma ta daukeshi kaddararta , da haka hankalinta yadan kwanta , sai dai tunanin halin da juwairriyan ta take ciki a gidan aurenta , domin kuwa jikinta na bata ,cewar kamar bata cikin yanayi mai dadi , hakan yasa ta yanke hukuncin zataiyita binta da Addu'ar fatan Alkhairi a duk halin da take cikin ......

A bangaren Hajiyan Khalil kuwa?ta tabbatar ma da Khalil cewa dole zai kara aure , a cewarta wai ya auri juya , tunda haryanzu babu alamar ciki tun bayan 'barin da tayi har yanzu ,shuru ba wani labari , hakan yasa ta zaba mishi mata , raudat yar kanwarta, batareda yayi musu ba yayi na,am da zancen cikin farin dama yana san karin aure , kuma yana San raudat din Sossai ........


Cikin kan kanin lokaci Khalil yafara zuwa gurin raudat haka har suka fahimci junansu sossai.... .

Batareda da sanin juwairriya ba aka tsayar da bikin Khalil da raudat , bayan watanni uku , murna a gurinsu ba,a magana .......

Bayan watanni biyu , juwairrya ta kara jin alamar shigan wani cikin , jin hakan yasa ta aika aka siyo mata PT script a boye .....

Gwada wa tayi Inda gwaji daya ya nuna mata Alamar positive wato akwai cikin , ganin haka yasa gabanta yayi mummunan faduwa matuka ....

Ba shiri ta fara neman hanyar da zatabi gudun kar Khalil ya gane cewar akwai ciki.... .

Nan ta Shiga sake_ saken yanda zata bullowa Al_ amarin ...

Cikin hakane ta fara laulayi kadan_kadan ta fara laulayi a tsatsaye , amma tanata kokarin boyewa gudun kar Khalil ya gane..


Duk da wanan cikin yazo mata da kwadayi, haka take dane kwadayin da takeji ta gwammace ta hakura .........

Wani lokaci in taji amai , haka take boyewa da kyar , sai ta tashi a dabara ta nufi bayan gida taje tayi batareda Khalil ya fahimta ba .....


A cikin watanin juwairtiya tadan canza, kuma tadanyi rama kadan , kasancewar bata yawan zama da Khalil yasa sam bai kula da ramar ta ba ......

A Kwance ya sa meta tana ta sharra barci , tashin ta yayi a hankali yace," juwairriya ! fifgirta ta mike tace,"na'am kura mata ido yayi, sai a lokacin ne ya hango ramar da ta karayi yayi yace," juwairriya wai meke damunki ne naga kin rame anya lafiya kuwa ?

Cikin muryar barci tana rafka hamma tace," wallahi kwana biyu ina fama da ciwon kai ne mai zafi ....
kallo ya kara kura mata yace," to ko dai ciki ya shiga ne ?

gabanta ne ya fadi , ta zaro ido tace," ni rufa min asiri ciki ana zaune kalau ba ciki bane ni yanzu haka ma jini nake bana sallah....
cikeda gamsuwa race," okay fine ,kitashi ki kawomun abinci naci , to tace," gamida tashi ta ta fita ......

*A gurguje*

Wasa wasa cikin juwairriya ya kai watannin uku , tana lalaulayi , amma karfin hali da dauriyanta bai sa Khalil ya gane cewa akwai cikin ba , domin duk rashin dadin da take ji a jikinta bata bari Khalil ya fahimci ko bata da lafiya ba , dan kuwa tana iya kokarinta, sanan duk wata takan mishi karyan Alada(mensuration) da haka ne take share mishi tan_tama.

Zaune suke suna kallo a TV suna kallan shirin akushi da rufi na arewa 24 ganin sunyi spring rolls yasata jin sha'awan ci ya wunta ya mugun tsike kewa ....

Bakinta ne ya subuce tace," kai dan Allah a ina zan sami wannan abun ta fada gamida nunawa da hannu....

Wani kallo ya bita dashi yace," tab a ina zan samo miki yanzu , mikewa yayi cikin rashin fahimta ya juyo ya kalleta yace," ke wai make damunki ne ina fa lura dake a yan kwana kin nan kin tabbata

Please Login or Register in order to submit comment