Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda ta ji muryan Arab sai ta fito tana cewa, "Oh Auta wai ina kika je ne yanzu aka zo neman ki? Kinga baƙo a waje?"

"Eh na ganshi Inna, mun je kasuwa ne Ni da Besty mun yi siyayyar tafiyana."

"Tafiya kuma?" Cewar Innar tana isowa wajen itama ta zauna, yayinda ta bi kayan da Ummu take fitowa da su suna gani

Zahra tace, "wanne tafiya kuma kika samu za ki yi?"

Dariya tayi tana ɗaukar wayanta tare da latsawa tace, "Abuja zan je."

"Abuja Autana? Ke kuwa me ya haɗa ki da Abuja da za ki je? Me za ki yo a can?"

"Uhm ai Inna wani Alhaji na samu wlh me kuɗin gaske, ina faɗa miki idan har na samu shiga a wajen shi to kakar mu ta yanke saƙa, wlh ina tunanin ma sai dai in Yi wuff dashi don ina ji a jikina kin kusa zuwa Makka Inna."

"Don Allah da gaske kike yi?" Innar tafaɗa cike da washe baki

"Wlh kuwa Inna, shiyasa nake son in je saboda ya gayyace Ni, but ba wani daɗewa zan yi ba yakamata dai in je inga masaukin sa ne."

"Kai wannan ganganci ne wlh, taya ya za ki bi mutum har wani uwa duniya don kawai yana son ki? Har yaushe farashin naki ya sauka haka haba Arab? To makarantar naki fa ko kin manta kuna da Exams ne?"

Arab kallon Ummu da ke maganar tayi tana waro mata idanu da cewa, "lallai Aunty Ummu ba ki san waye Alhaji Bashir ba shiyasa kike wannan zancen, wlh ko ke ne kika samu damar nan sai kin je, to meye a ciki don na je can mun fahimci juna? Ba ki san irin kuɗin da ya tura min bane lokacin muna gidan Aunty Firdausi, wlh bazan zauna ba don na san arziƙi ke kirana."

Baba da ya fito daga ɗakinsa domin duk yana jin abubuwan da suke tattaunawa a kai, sai ya tsaya daga bakin ƙofan yana cewa, "akul ɗinki A'isha da wannan banzar shirmen, wato abun naku ya kai har ki bi namiji wani garin tsaban gantali ko? To babu inda za ki je, baza ku mayar da Ni mutumin banza ba duk kun hana Ni saƙat a gari, ko ina zancen ku ake yi na gagari baku tarbiyya, wannan abun da me yayi kama? To zan ɗauki mummunan mataki a kan ku wlh idan har baku gyara ba, kowaccen ku ta samu Miji tayi aure don bazan iya wannan shirmen naku ba, na gaji wlh."

Inna kamar jira take yi ya ajiye numfashi sai ta hayayyaƙo mishi tana cewa, "wlh bazai saɓu ba, ai zancen ka zancen banza ne tunda ba kai kaɗai kake da yaran ba, baka isa kayi musu aure a wannan marran sabida kana min baƙin ciki ba, na gode Allah ya bani ƴaƴa mata masu share min hawaye amma kai baƙin ciki yayi maka katutu kullum so kake yi kaga bayana, to wlh na rantse da Allah ba ka isa ba Iro, tun wuri ma ka canza tunani idan zugin ƴan gari zaka bi can ta matse maka, mu kuwa ba yau muka saba da su ba kuma maganganun su bazai mana komai ba, yara dai nawa ne sai abun da suka yi ninya zasu yi babu takura a rayuwar su, su ba Bayi bane balle ace za'a hana su ƴancin kansu, duk abun da suke so shi zasu yi tunda dai basu tarewa uban kowa hantsin gaba ba."

"Yanzu Ni kike faɗawa haka Harira? Ni Mijin ki?" Yayi maganar yana nuna kansa

"Yo yau ka soma ji dama? Ai idan har baka fita a harkan yarana ka dena takura musu a kan mutanen gari ba; wlh daga kai har su sai dai aniyar ku ta ƙare muku, yarana nan gari nan bari kurwan su kurr, kuma insha Allahu da su zan yi kuɗi, sai zaman anguwan nan ya gagare mu don mun fi ƙarfin zama a kwata."

Kanshi kawai ya gyaɗa yana juyawa ya shige cikin ɗakin sa zuciyarsa kamar zata yi bindiga ta fashe, sai dai bazai iya amayar da abubuwan da ke ransa ba, Harira ta rigada ta fi ƙarfin sa bai san ya zai yi ba, bai san ta wanne hanya zai bi domin ya ceto rayuwar ƴaƴan shi ba, haƙiƙa yana kaicho da wannan rayuwar, yana tur da Allah wadai da samun Harira a matsayin Matar sa, ga shi yanzu ba shi da wani ikon da zai iya tsawatar musu a matsayin waɗanda suke ƙarƙashin ikon shi, bai da wannan fawan. Har hawaye yake sharewa sabida yanda ya ji sun ci gaba da shewa da maganganu wanda ko alamu bai nuna sun ɗauki zancen shi da wani muhimmanci ba, inda yana jin Inna tana sake zuga Arab ɗin sosai

"Duk yanda za'a yi ta damƙo mutumin ta ɗaura shi a tafin hannunta, akwai ma maganin da zata bata zuwa gobe sai ta sake yin farin jini fiye da ko yaushe, kuma duk abun da ta buƙata ya bata sai ya bata a nan take, bari dai ta je ta ga yanda zai susuce a kanta."

Ƙarshe dai rediyo ya sa a kunnen sa ya dena sauraron baƙin cikin da suke ƙunsa mishi.





             Zuwa washe gari kuwa Arab tayi sammako ta gama shiryawanta tsab. Ibrahim ya zo da motan abokin sa zai kaita tasha ta samu abun hawa, tare da Ummu suka je tayi musu rakiya. Zahra kuma na gida suna aiki da Inna

Bayan sun kaita tashan har ta hau Mota sannan suka juyo.
[15/07, 9:25 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

    *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍


*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*










_________________________


*BABI NA TARA*
_______________  *ABUJA STATE*
            Tun shigowar Nawwara cikin falon Mummy ta washe baki tana cewa, "iyee ƴan matan Yayanta, wannan cancaɗi haka! Kwalliya yayi kyau."

Dariya tayi tana isowa wajen, yayinda ta samu wuri kusa da Ikhlas ta zauna tana cewa, "Mummy good morning?"

"Morning Nawwara, har kin fito? Ga shi mutumin naki har yanzu shiru nake ji ya ƙi fitowa."

Ikhlas tace, "ai yanzu Mummy za ki ganshi, naga ya shiga part ɗin Abba but maybe ya fito." Sai kuma ta kalli Nawwara tana cewa, "Aunty kin Yi kyau wlh, sosai da sosai."

Baki Nawwara ta washe tare da cewa, "thank you sister, Ina Zainab?"

"Tana school, yanzu ta fita."

"Ok Mummy bari in je in duba shi ko ya shirya." Nawwaran tafaɗa tana miƙewa

Mummy tace, "to, but tell him don't waste time please, you should go now, gwara ku tafi da wuri zai fi ai.. Ikhlas tashi ki je ɗaki na ki ɗauko min baƙin ledan nan dana ɗaura a kan gado, ki riƙo da kyau fa kar kiyi min ɓanna."

Miƙewa tayi da sauri tana cewa, "kai Mummy sai kace wata yarinya?" Sai ta ruga a guje kuma ta hau steps ɗin benen

While Mummy na cewa, "ai na san halin ki ne tunda ba kya abu da hankali".








                   *****

         Nawwara kuwa tana shiga ɗakin Malik ta hange shi zaune a gaban gadon shi yana ƙoƙarin saka shoes ɗin sa

Shima ɗago kai yayi ya zuba mata idanuwansa masu shegen haske da ɗaukar hankali, sai ya sakar mata murmushi kawai yana bin ta da kallo tare da ƙarewa shiganta kallo

Doguwar riga ce a jikinta kalan ruwan hanta, me gajeren hannu da igiyoyi, rigan ta lafe mata daga sama har ƙasa babu wani shafe sai na jikinta, ƙam ta kama ta, stones ne kawai aka yi kwalliya dashi a gaban rigan while ta ɗaura farin gyale a saman attachment ɗin kanta; yayinda ya rufe mata har zuwa kafaɗun ta, kasancewarta fara rigan tayi mata matuƙar kyawu musamman yanda ta sha makeup a fuska, sai sheƙi fuskar nata take yi tana glowing, sai tayi using da farin hill shoes tare da Hangbag ɗinta me ɗaukar hankali

While shima Malik farin yadi ya saka wanda aka yi mishi ɗinki dai-dai da jikinsa na zamani, yayi masa kyau matuƙa ya fito da ainihin kyawu da kamalansa, kyakykyawar fuskarsa yana zagaye da ƙasumba da dogon gemu da ya ƙara ƙawata face ɗin nasa, duk wata Mace idan ta kalle sa dole ta sake kallonsa sabida haɗuwar sa, kana kallon sa zaka hangi irin tsantsan tsaftar shi da gayun shi, shiyasa Mata suke mishi rubuti sabida ya iya wanka matuƙa Malik, duk inda namiji ya kai Malik ya kai, ga iya soyayya da ba wa Mata muhimmanci, shi dai a rayuwa yana bala'in ƙaunar Mata, ko ya ya suke yana matuƙar girmama su kuma yana jin daɗin mu'amala da su, shiyasa ba ya rabo da su a koda yaushe

Nawwara tahowa wajensa tayi tana murmusawa tare da cewa, "Wow! My prince charming you look very well, honestly can choose."

Hannu ya miƙa mata yana kama nata tare da cewa, "ai ban kai ki ba, anya zan iya tafiya da ke? Kar azo a samu matsala kuma wani yayi min ƙwace." Ya ƙare maganar yana ɗaura ta a saman cinyan sa, tare da kai fuskarsa kan nata yana shinshina ta cike da tsantsan shauƙi

While itama haka, sai dai murmushi ne a kan fuskarta, inda ta sauke mishi hot kiss before ta janye bakinta tana cewa, "babu wanda ya isa ya ƙwace maka Ni, Ni an yi ni ne saboda kai kaɗai, I'm yours, don haka ka dena saka wani abu a ranka, idan ba kai ba sai rijiya, rijiyan ma mai kwalabe." Ta sake kai bakinta ta lashe saman laɓɓansa

Shi kuma sai ya ɗaura hannunsa a ƙeyanta ya haɗe bakunansu waje ɗaya, tsawon lokaci suna kissing junan su before su janye wanda har sun soma fita cikin hayyacin su. Hakan bai ishe su ba sai da suka sake romance din juna sannan suka haƙura ganin suna shirin manta a inda suke da kuma abun da zasu yi

Ita ta ƙarisa saka mishi takalmin sannan suka fito tare da ɗan ƙaramin Jakar sa kasancewar kwana zasu yi

Mummy da Ikhlas har yanzu suna zaune a Falon, inda Ikhlas har ta kawo mata saƙon da ta aike ta

Mummy tuni ta soma koɗa su don ba ƙaramin ƙaunar Nawwara take yi a ranta ba, tana matuƙar sonta da ɗanta saboda wayewanta da ƙaunar ɗanta da take yi, shiyasa take ganin kamar duk duniya ɗanta ya fi dacen Mace ta gari idan ya auri Nawwara

Nawwara ɗiya ce wajen ƙanwar Abban su Malik. Gidan su a farkon anguwa ne duk da akwai nisa da gidan su Malik, but komai na rayuwar Nawwara a gidan su Malik take yin sa tun tana ƙarama, babu wanda bai san soyayyar su a family ba har dangin Mummy da suke Kano, kasancewar ita Mummy ɗiya CE wajen Sarkin Kano, ita ce ƴa ta biyu a yaranshi da ya mallaka, tana aure a nan Abuja tare da mijinta Alhaji Atiku Nera, shahararren ɗan kasuwa da yayi suna a faɗin Nigeria da kewayen ta, babu abun da bai mallaka ba sabida tsaban kuɗin sa, yaran sa uku Allah ya ba shi, Abdul Malik sai Zainab sannan sai Ikhlas mai sunan Mahaifiyar shi da ta rasu, Habiba

Alh. Atiku su biyu ne iyayen su suka haifa, daga shi sai Mahaifiyar Nawwara. Itama a Abuja take Aure kuma abokin Alhaji Atiku ta aura. Nawwara kaɗai suka haifa ita kenan musu, suna sonta kamar ransu domin ba sa son abun da zai ɓata mata rai, shiyasa ta tashi cikin sangarta tunda ƴar gata ce gaba da baya, duk abun da take so shi take yi. Allah ya ɗaura mata ƙaunar Malik tun tana yarinya bata san meye rayuwa ba, shiyasa ya soma koya mata duk wani rayuwar wayewa da tanbaɗewa, kuma shi ya soma sanin ta a ɗiya Mace bayan yayi mata wayau ya amshe mata budurcin ta tare da yin mata alƙawaruka kala-kala, shiyasa take ganin babu wata Mace da ta isa ta mallake shi face ita, ita kaɗan ta, shi nata ne domin an yi shi ne don ita, tana da tsananin kishi zata iya komai domin shi

Don haka shi kansa yana taka-tsan-tsan saboda shegen kishin ta, but hakan bai hana shi yin mu'amala da mata kala-kala ba duk da ya san halin ta, sai dai har a zuciyarsa bai taɓa son wata ɗiya Mace ba bayan Nawwara. Amma yanzu kuma ƙaddara tana neman canza mishi akala, duk da a baya yayi mata alƙawarin ita kaɗai ce matar shi a duniya, to bai taɓa tunanin zai iya cin karo da wata wacce zuciyar shi zata faɗa da kogin ƙaunar ta a nan take ba, sai dai abun haushin ma bai san inda zai ganta ba, a kullum da hoton ta yake kwana yake tashi, shi kaɗai yake gani ya ji daɗi a ransa, soyayyarta ta shiga cikin jikinsa ta zame mishi jini da hanta, abun da yake ji a kanta bai taɓa jin makamanciyar irin sa a kan kowacce Mace ba har Nawwara da yake tunanin yana matuƙar ƙauna, sai dai kuma bai san ya wannan soyayyar tashi zata kasance ba domin yana ganin makauniyar soyayya ce wacce zata iya kai shi ga halaka, bai san ya zai yi ba duk da yana fatan ace wata rana ya haɗu da yarinyar, koda hakan zai zama silan mutuwar shi ce sai ya mallake ta, dole ne ya mallake ta, sai dai idan Nawwara zata haƙura amma dole ne ayi ɗayan biyu, ko ya aure su duka biyun ko kuma ita kaɗai, amma babu fashi bazai taɓa iya cire soyayyar ta ba, kuma ko nawa ne zai iya kashewa don samun ta a cikin rayuwar shi, amma taya ya hakan zai faru? Abun da kamar wahala domin bai san ta inda zai soma ba, aina zai ganta bare har ya bayyana mata irin soyayyarta da ya kamu da ita? Tabbas idan aka ci gaba da tafiya da yiwuwar ya rasa tunanin sa gaba ɗaya saboda bege da tsananin shauƙin haukan soyayyarta.









                 *******

             Har suka gama sallama da su Mummy suka rako su haraban gidan, gaba ɗayansu har Abba da shima ya fito daga part ɗinsa. Sannan suka hau Mota suka tasarwa hanya ɗoɗar

Duk da Malik ba ya cikin walwala sakamakon damuwa da tunanin yarinyar da take ƙarƙashin ransa, amma haka ya biyewa Nawwara da ke mishi hira, suna zantawa sama-sama yayinda yake kwasa gudu a titi. Wayan sa ne tayi ƙara sai ya ciro ta daga aljihu yana dubawa, ganin sunan wani friend ɗinsa sai ya ɗauka yana karawa a kunne. A haka suka ɗauki lokaci suna waya before ya kashe yana kallon Nawwara tare da kashe mata ido ɗaya yace, "ƴan Matana zamu wuce Zaria kafin mu je Kano, akwai Aboki na da zamu haɗu a can, yace min yana Zaria so ina son mu haɗu tunda muna kan hanya. I want to say hello because we haven't met in a long time."

Murmushi tayi tace, "babu komai my Prince, ka san yau ina matuƙar farin ciki sabida kasancewar mu tare, so duk inda zamu je bazan gajiya ba Ni dai fatana mu kasance tare, ba don kar su Mummy su kira waya ace musu bamu ƙarisa ba da yau kawai mun hutawar mu a wani hotel, hakan zai faranta min rai sosai."

Hannu ɗaya yasa ya kamo nata yana mata murmushi da cewa, "nima haka nayi tunani, but ki bari zamu samu time zamu kasance tare har sai mun gaji, duk sanda zamu dawo gida zamu yi yawon mu before mu koma."

"Yauwa my prince, haka nake son ji, Allah ya barmu tare." Ta furta tana kai mishi kiss a kuncin sa

Dariya yayi yace, "ki bari fa kinga tuƙi nake yi kar ki ja min matsala."

Narke fuska tayi da cewa, "uhm kai ne ka san ba na gajiya da kai, ban ƙi ba mu dauwama manne da juna a koyaushe, ina matuƙar ƙaunar ka Malik, na mallaka maka komai nawa sai yanda kayi dani."

Murmushi yayi yana sake tamke hannunta a cikin nasa, tare da sakar mata kyakykyawar kallo mai tsananin shauƙi da shiga jiki, a hankali cikin raɗa-raɗa da jan hankali irin nasa yace, "na san da haka Princess ɗina, nima ina tsananin ƙaunar ki, but baza ki gane hakan ba sai a nan gaba."

Dariyan farin ciki ta saki itama tana mishi kallon soyayya. Cike da shauƙi da ƙaunarsa take ƙara narke mishi tana jan shi da hira me shiga jiki

Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa Zaria tunda yana zuka gudu, kafin karfe biyar sun kai. Sai ya kira Abokin nashi ya sanar mishi inda suke

Babu jimawa abokin ya taho a motansa. Parking yayi ya fito ya isa wajen motan Malik

Sai shima ya fito daga cikin motan nashi, da dariya a fuskokin su suka cafke hannaye cikin tsananin farin cikin ganin juna

Itama Nawwara fitowa tayi tana kallon su ganin suna gaisawa

Sai Abokin yace, "ah my Man wannan kuma kyakykyawar fa?"

Murmushi Malik yayi yace, "Ƙanwata ce kuma wacce zan aura, Do you remember Nawwara telling you time muna school?"

"Yeah! Yeah! I remember, kana nufin ita ce still?"

"Yes ita ce. Nawwara ga Aboki na, my classmate his name is John."

Hannu John ya bata don su gaisa. Sai ta miƙa mishi nata tana murmushi tare da cewa, "hello."

"I'm glad to meet you. The truth is you are beautiful. My friend deserves to have you."

Duk dariya suka yi, inda ita kuma Nawwara tace, "Thanks." Cike da farin ciki a fuskarta

"Ok amma zaku je gidana ku huta zan ji daɗin hakan, yau ina da manyan baƙi." Yafaɗa yana washe baki

Malik yace, "no John muna kan hanya ne, let sometimes we meet again, I will come especially for you but now we are in a hurry."

"Ok babu yanda na iya ai, nayi farin ciki duk da haka ma." John ɗin yayi maganar yana murmusawa tare da ba shi hannu suka sake gaisawa. Daga nan suka yi sallama ya wuce nashi motan

Su ma suka shiga nasu Malik ya ja suka wuce. "Bari mu nema abinci ko Baby?" Yayi maganar yana kallon Nawwara

Sai ta gyaɗa mishi kai tana cewa, "Yes because I'm hungry now." Hannunta ɗaya a kan cikin ta tana shafawa

"Ok ga bank can, let me withdraw money, I have no money in my pocket." Yayi maganar yana yin parking a gefen titi, "ina zuwa yanzu zan dawo." Ya buɗe motan ya fice zuwa tsallaken titi inda ya ga kamar wajen cire kuɗi ne. Yana zuwa ATM card ɗinsa ya zaro yana shirin tusa wallet ɗinsa da ta biyo baya, sai kuma ta faɗi a ƙasa, juyawan da zai ɗan yi ya ɗauka sai suka ci karo da Zahra da ta taho da sauri tana waya itama bata kula dashi ba, bata san zai dawo baya ba shiyasa suka ci karo har goshin su ya haɗe da juna. Da sauri suka furta, "oshhh!" Suna ɗagowa the same suka kalli juna. Waro idanu sosai Malik yayi yana kallonta saboda ganin yanda lokaci ɗaya tayi mishi kama sak da yarinyar da ya kamu da soyayyarta da bai san inda zai same ta ba, sai ga ta a gabanshi for surprise

Ita kuma Zahra tuni tace mishi, "sorry." Tana ƙoƙarin janye jikinta ta wuce

Sai yayi saurin dakatar da ita yana cewa, "ba ki ji ba don Allah." Lokaci ɗaya ya kai hannu ya kamo nata hannun ba tare da ya san yayi hakan ba

Shiyasa ta tsaya tana kallon shi itama, sai dai bata yi yunƙurin janye hannun nata ba illa kallon kyakkyawar fuskarsa da take yi

Murmushi yayi mata yana janye hannun sa da cewa, "kiyi Haƙuri na taɓa ki."

"No babu komai." Ta furta itama tana murmushin har da canza tsayuwa cikin yanayin jan hankali

Shi kuma sai a lokacin ya gama tantance ba ita bace domin suna da bambanci da wancan, amma tsananin kaman nasu yayi over a jikinsa yana ji duk yanda aka yi suna da alaƙa da juna, kamannin ta sak yake gani a jikin wannan dole suna da alaƙa, zai iya yiwuwa, shiyasa yayi saurin cewa, "idan babu damuwa ki bani Numban ki mana, don Allah kar ki ce na tsayar da ke a kan hakan, and ina son..." Shiru yayi sabida ganin Nawwara a gaban su tamkar kububuwa ko wacce aka hankaɗo

  

Lokaci ɗaya idanuwanta suka rikiɗe tsaban jaraba saboda duk abun da ya faru tana hange daga cikin mota, shiyasa lokaci ɗaya ta fito ta isa gaban su, kuma bata yi wata-wata ba ta kwashe Zahra da maruka har guda biyu, cikin tsananin kishi da ɗaga murya take cewa, "ke dan ubanki wace ce da har kika samu damar yin magana da Mijina? Karuwan banza karuwan hofi ba'a faɗa miki mijin wata bace...?"

Tsawa Malik ya daka mata yana cewa, "ke Nawwara kina da hankali? Wannan wanne irin hauka ne?"

A zuciye ta kalle shi tace, "hauka kace ko? Dama abun da kake son zuwa kayi kenan shiyasa ka taho damu nan? To asirinka ya tonu wlh zaka ga hauka yanzu." Kafin su farga har ta ciro takalmin ta me tsini ta kwaɗawa Zahra da ke tsaye ƙiƙam al'ajabin abun da Nawwara tayi mata ya cika ta, sai ji tayi ta sake buga mata takalmi a saman goshi


Lokaci ɗaya ta saki ihu tana duƙewa a wajen; nan da nan jini ya soma tsatstsafo mata

              
Salatin mutane ya karaɗe wurin; har Malik da jikinsa lokaci ɗaya ya soma rawa tsaban ya rikice.
[17/07, 10:35 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

    *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍


*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*










_________________________

*BABI NA GOMA*
_______________Da sauri Malik ya duƙa yana kamo hannun Zahra cikin tashin hankali, yayinda ya kai dubansa kan goshin ta da ke fitan jini, ya kasa ma furta komai sabida halin da yake ciki illa bin wurin da yake yi da idanu

Nawwara kuma na tsaye a kansu ta ƙi mayar da takalmin sai huci take yi

Yayinda wasu daga cikin jama'ar wurin har sun iso sun tabaibaye su suna faɗin, "subhanallah.. meyasa zata yi mata haka? Me ya faru?" Duk laifin sun ɗaura a kan Nawwara tunda a kan idanuwansu suka ga komai, sai faɗa suke mata a kan, "bata kyauta ba, idan wani abun ya haɗa su ai ba sai ta kai ga haka ba."

Sai dai ita bata damu da jama'ar ba kuma bata damu da surutun nasu ba, baƙin cikinta yanda Malik ya duƙa yana taimakon Zahra, shiyasa cikin zuciya da ya ɗebe ta kamar wata me Aljanu ta soma hauka a kan, "sai ya saki Zahra sun wuce, bai isa ya taimake ta ba wlh." Ta riƙe shi gam tace, "ta rantse da Allah bai isa su wuce ta a nan wajen ba sai dai su tafi su bar Zahra, bazai taimake ta ba." Har da kukan ta

Abun fa ya ba wa mutane mamaki ganin kishin hauka ƙiri-ƙiri da ake yi a gaban su, tamkar bata da tausayi

Shi kuwa Malik da ya san halin Nawwara kuma ya san me zata iya aikatawa, bai yi mamaki ba kwata-kwata, sai dai bai san cewa rashin imani da baƙin kishin nata zai iya rufe mata idanu ta aikata wannan haukan a kan abun da bai kai ya kawo ba, sai ya daka mata tsawa yace, "ta sake shi ko ya illata ta."

But wlh ta ƙi, sai buɗe masa idanu tayi cikin nuna tijara tace, "na rantse da Allah babu inda zaka matsa da ita, baza ka taimake ta ba, kawai ka kama hanya mu tafi."

Zahra taga abun da ya fi ƙarfin ta wajen wannan sheɗaniyar yarinyar, ita abun ma sai ya zame mata t.v don ta kasa kataɓus, yayinda zafin ciwon ma ya dena shigan ta sabida tsananin mamakin Nawwara, ikon Allah kawai take kallo a wajen ta. Ganin abin zai zame musu matsala sai ta ƙwace hannunta da Malik ya riƙe gam ta ratsa mutane ta wuce da sauri, domin idan ta zauna ganin wannan bala'in zuciyarta ce kawai zata buga jininta ya ƙare a banza, gwara ta soma taimakon kanta wajen tsayar da jinin before ya ƙare, a ranta sosai ta ji haushin Nawwara da ta kasa mayar mata da martani ko kuma ta rama abun da tayi mata, tabbas da ace kanta

Please Login or Register in order to submit comment