Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi magana da masu tsaron gidan babu ke babu fita, don haka kiyi shawara rayuwarki ko kuma kuɗi. Mu je Hajiya." Yayi maganar yana kallon Jameema. Kana suka fice a ɗakin suka barta a nan

Sai ta kwatsa ihu tana faɗin, "na shiga uku Ni A'isha! na kawo kaina inda zan kashe kaina da kaina." Sai kuma ta tashi cikin rawan jiki sabida ganin ƙofan a buɗe, bata yi wata-wata ba ta fice da gudunta, tana taɓa ƙofan falon nan ma a buɗe ta ji, sai ta fice da gudu jikinta na rawa sosai, har zata sauka kan benen sai ta hango su a ƙasan falo suna magana, sai kuma ta ga shi ya nufi ƙofan waje riƙe da waya, ita kuma Jameema ta bi hanyar part ɗinta, da sauri ta gangara ta sauka itama ta bi bayansa, tana ganin ya nufi haraban gidan yana waya, ita kuma sai ta lallaɓa ta jikin flowers tana ta tafiya a duƙe a hankali yanda baza a ganta ba, duk da akwai duhun dare amma gidan tarwai yake da fitilu masu haske, still jikinta sai rawa yake yi duk a tsorace take, burinta kawai ta samu kuɓuta daga gidan nan. Tana jin sanda ya gama wayan ya soma kiran securityn gidan har mai gadi, dole ta dakata sabida ganin sun nufo wurin, kuma idan tace zata yi ƙoƙarin fita dole zasu ganta sabida ta kai ƙarshen flowers ɗin. Daga inda take tana jin maganganun da yake faɗa musu

Yana basu umarnin, "kar su bari ta bar gidan, idan suka bari ta bar gidan daga yau kashin su ya bushe." Sai da ya ja ma mai gadin kunne domin shi ne a bakin ƙofa

Mai gadi yace, "an gama ranka ya daɗe! Yanzu ma zan soma aiki na, babu mai shiga da fita sai da iznina domin kwaɗo zan sa a ƙofan."

Jin hakan shiyasa ta lumshe idanunta tana sake buɗewa tana kallon tazaran inda take da Gate ɗin gidan, tabbas idan ta bari ya sallame su bata bar gidan nan ba shikenan kuma bata da damar fita, gwara tayi shahada idan Allah yasa zata iya tsallakewa. Shiyasa ta fito a guje ta nufi ƙofan fita, zuciyarta na wani irin tsalle da bugawar da take tunanin ƙiris ya rage ta fito daga ƙirjinta, tamkar zata ci kai sabida irin gudun da ta kwasa a wurin

Tuni sun hange ta. Nan da nan Senator ya basu umarnin, "su kama ta kar su bari ta fita." Hankalinsa a matuƙar tashe don ba ya fatan ta bar gidan basu kama ta ba

Tuni sun bi umarninsa daga su har karnukan gidan suka bi bayanta

Sai da ta kai bakin ƙofan Gate ɗin tayi wani irin zamewa fuskarta ta bugi jikin Gate ɗin. Bata tsaya tunanin wani abu ba bare buguwan da tayi, burinta kawai ace ta fice daga gidan, tuni ta saka hannu ta buɗe ƙofan tayi wuff ta fice. Gudu take yi kamar zata tashi sama, gudun ceton rai. Ko waiwayan bayanta ba tayi duk da tana jin gurnanin karnuka a kusa da ita, amma inaa ta ƙi tsayawa da iya ƙarfin ta take gudun

Ga layin masu kuɗi ne babu kowa, sai haushin karnukan da suke biye da ita da kuma na cikin gidan mutane, garin yayi duhu sosai duk da akwai hasken fitila na sauran gidaje da ya haska wurin

Wani siririn hanya ta gani ta shige da gudunta, nan da nan ta ɓilla ta wani ƙaton kwalbati, bata tsallaka ba sai ta bi hannun dama, juyawa tayi ta ga basu ɓullo ba sai ta faɗa kwalbatin kawai ta ɓuya, hannunta duka biyu a bakinta ta danne saboda nishin da take saki, ƙarfin nishin dole ne zai tona mata asiri, shiyasa ta ɓame bakin tare da runtse idanu; zuciyarta na wani irin bugawa tamkar zata faɗo ƙasa saboda tsoron kar su ganta, ga numfashinta kamar zai cire daga jikinta sabida yadda ta liƙe bakinta magudanan iska ba ya shiganta sosai

Ai kuwa suna ɓullo wa wurin karnukan suka tsaya suna ta haushi mai firgitar wa. Su ma tsayawa suka yi Ogansu na cewa, "duk yanda aka yi tana wurin nan dole mu bincika kafin mu bar wurin..."

Wayansa da tayi ƙara shiyasa ya dakata daga maganar ya ɗauka, "Hello Ranka ya daɗe!"

Dayake a handsfree ya saka shiyasa maganar Senator Ƙasim ya fito duk suna ji; har Arab da ke cikin kwalbati ta kasa motsawa tsaban yadda ta tsorata jikinta nata rawa

Tana jin muryan shi yana basu umarnin, "duk inda take su kamo ta, kar su bari ta bar garin Kano basu dawo da ita cikin gidan shi ba, and duk yanda zasu yi su tura wasu su riga ta zuwa can gidan su, tana zuwa don't let her into the house su kama ta..."

Iya abun da ta gama ji kenan ta soma rarrafe a cikin kwalbatin, bata damu da irin abun da zai same ta ba, burinta kawai ta tsira, sai da tayi ɗan nisa kaɗan kafin ta fito ta ruga aguje, haka ta dinga canza hanya har sai da tayi nisa daƙyar take iya ɗaga ƙafarta tsaban galabaitar da tayi, a wani lungu ta rakuɓe inda baza a iya ganin ta ba, dirshan ta zauna a wurin tare da dafe ƙirjinta tana ta faman haki, har ƙwallan wahala tayi tsaban jigata, sai da tayi ta ƙaƙarin amai kamar zata amayar da abun da ke cikinta, amma babu abun da ya zuba sai yawu, ga idanunta da suka kaɗa suka yi jawur. Daga ƙarshe kwanciya tayi a wurin tana jin duniyar tana juya mata; domin tunda take bata taɓa ganin bala'i irin wannan ba, gudun da tayi ba shi da maraba da bala'i, don idan aka ce tayi baza ta taɓa iyawa ba sai dai bala'in da ta gani dole yasa tayi

Tayi kusan mintuna ashirin a wurin tana hutawa tare da mayar da numfashi sama-sama tamkar zata shiɗe, daƙyar ta tashi ta bar wurin sabida gudun kar su biyo wurin su kama ta, don ta tabbata zasu iya riskar ta idan har suka biyo hanyar da take, da sauri ta dinga tafiya duk da dare yayi yanzu sosai amma ana ganin abun hawa suna wuce wa, sai kuma fitilu na kan hanya, shiyasa ba ta bari hasken ya haska ta; can gefen titi take tafiya da sauri da sauri tana dafe da cikinta. Ko yanzu suka biyo ta ta tabbata baza ta iya gudu ba a halin yanzu sabida azaban da take ji a cikinta, wanda gudun nan da ta sha shi ya haddasa mata hakan, ko iya tashi tsaye sosai ba tayi, ga azaban da ke ratsa mata gwiwoyi da fuskarta da ta faɗi ta buge, ta rasa inda zata je ga babu shaguna a buɗe, dole ta soma tare abun hawa domin barin wurin da hanzari, gwara tayi nesa da wurin ta samu mafaka idan ba haka ba zata koma gidan jiya. Ta fi kusan mintuna sha biyar tana tafiya tana tare abun hawa amma ba sa tsayawa, ko don dare yayi ne ko kuma don ganinta a haka kamar wata mahaukaciya ne oho, daga ita sai riga da wandon jikinta na Fakistan da ta sanya tun safe, babu takalma bare ɗankwali a kanta, gashin duk yayi baja-baja ya tuttuge daga ribom ɗin da ta ɗaure, ga kwatan da ya ɓata mata jiki, daga ƙafafunta har wandon ta zuwa gwiwanta da ƙasan riganta ya jiƙe sharkaf da kwata, haka ma gwiwowin hannayen ta duk sun ɓaci, ita kanta warin jikinta take ji amma bata bi ta kai ba, fatanta kawai ta tsira. Daƙyar ta samu wani mai napep ya tsaya, bata yi wata-wata ba ta shige ciki tace, "mu je Malam."

Shima bai tsaya tambayarta ba yayi gaba, sai da ya soma tafiya before ya tambaye ta inda zai kaita

Shiru tayi tana tunani don bata san inda zata je ba, koda gigi baza ta iya komawa gida ba tunda ta ji wayan nan da suka yi, kuma zamanta a garin Kano tamkar ta gudu bata tsira bane, Senator Ƙasim ba ƙaramin attajiri bane, komai zai iya yi domin ya nemo ta, ko don sirrinsu da ta sani zai iya kashe ta ma, wannan tunanin kawai take yi a ranta yayinda take ƙara shiga cikin tashin hankali da tunanin mafita

Har mai keken ya gaji ya sake tambayarta jin shiru bata yi magana ba, "Malama ke fa nake tambaya? Ina zan kai ki kina ɓata min lokaci? haka kawai ma bamu yi ciniki ba kin kame kin shige min mota; ga shi duk kin cika min wuri da wari." Sai ya ja tsaki yana mitan, "bai ma san dalilin da yasa ya tsaya ba." har a ransa tsoro ya fara ji yana dana-sanin ɗaukar ta tunda bai ga alamun gaskiya a tare da ita ba, shiyasa ya soma ƙoƙarin tsayar da keken, gangarawa yayi gefen titi

Sai a lokacin Arab tayi magana daƙyar da cewa, "ah ah ya za ayi ka tsaya kuma?"

"Kinga saukar min a mota ki nemi wani, Ni iyakana wannan kwanan daga nan zan tsaya, bani kuɗi na."

Fita tayi daga cikin keke napep ɗin, sai ta dube shi duk da ba wani ganin shi sosai take yi ba; haka shima ɗin, tace, "bani da kuɗi."

"Ba ki da kuɗi kuma? Kin san ba ki da kuɗi taya za ki hau min keke?"

Bata ce komai ba tayi mishi banza tana kalle-kalle don tunanin hanyar da zata bi

"Ke ki sallame Ni in tafi mana kina ɓata min lokaci."

Dawo da kallonta gare shi tayi da cewa, "bani da kuɗi nace, idan kuma baza ka haƙura ba ka sauko ka ci na kuɗin ka sai ka ware."

"Kamar ya?" Yafaɗa yana zubura cike da mamakin furucin nata

"Eh kamar yanda ka ji nace, ai na san ka gane tunda ba kurma bane kai, sai dai ka fanshe kuɗin ka a jikina ka biya buƙatarka na kuɗin ka domin Ni bani da kuɗi." Sai ta ja tsaki tayi gaba ba tare da ta bi ta kansa ba

Shi kuma sai ya tayar da keken yana zaginta da cewa, "shegiya ƴar tasha, an gaya miki kowa ma irin ki ne ɗan iska? Can ki je ki samu abokan shashancin naki, banziya jaka ƙazamiya, sai wari take yi ashe Karuwa na ɗauko."

"Ka zagi uwarka Ni ban rama ba." Tayi maganar da ƙarfi yanda zai ji domin har ya ja keken shi ya tafi

Cikin anguwa ta shiga duk da bata san inda zata je ba, tafiya kawai take yi, sauƙin ta ɗaya tana haɗuwa da mutane jefi-jefi kasancewar cikin anguwa ne. Wani teburin mai shayi ta hango ta nufa ta je ta zauna kasancewar babu kowa a wurin, hannunta ɗaya dafe da cikinta tana zazzare ido sabida tsoro, har leƙe-leƙe take yi idan ta ji kamar motsi ana tafiya, sai kuma ta juya ta ga babu kowa

Machine ne ya zo ya tsaya a wurin ya sauke wata budurwa. Ta ciro kuɗi a jaka ta miƙa mishi sannan ya tafi, ita kuma sai ta taho zata wuce ta kalli inda Arab ke zaune, dayake sanda suka sauka hasken Machine ya gama haske ta tass, so ta ganta shiyasa tayi mata sallama tare da cewa, "baiwar Allah lafiya kike zaune a nan?"

Arab tace, "Ni baƙuwa ce, ina buƙatar wurin da zan zauna ne da safe sai in tafi."

Shiru budurwan tayi, sai kuma tace, "amma wa kike nema a nan arean da kika zo cikin dare kika zauna? Kin san mutane ba abun yarda bane, nima don naga kamar kina buƙatar taimako ne."

"Eh ina buƙatar taimako, wasu suka biyo NI kuma Ni ba a nan nake ba, ina buƙatar wurin fakewa idan kina da ki taimaka min."

"Shikenan, mu je ai Ni ina da wurin ajiye ki, tashi muje."

Hakan yasa ta miƙe suka wuce, tana biye da ita a baya duk da tana a cikin tsoro amma baza ta ƙi tayin da tayi mata ba, a haka ta bi bayanta suka shiga cikin wani gida

Babban gida ne domin ɗakuna ne a ciki sun kai ashirin, koda ganin tsarin gidan ka san gidan Karuwai ne. Babu kowa a tsakar gidan duk da wasu ɗakunan a buɗe ne, kuma ana jiyo surutan mutane a ciki; wani ɗakin ma har shewa ake yi

Kai tsaye ɗaki mai number takwas suka shiga, sai da budurwan ta tura ƙofan sannan suka shige

Arab na biye da ita a baya tana ta kalle-kalle

Ƴan mata biyu ne a cikin ɗakin sa'annin budurwan, dukkansu babu mai kaya a cikinsu, ɗaya ta ɗaura zani ɗaurin ƙirji, ɗaya kuma breziya ce a jikinta sai guntun skirt na ciki tana waya

Mai ɗaurin ƙirjin ne take kwance tana latsa waya, ita ce wacce ta soma magana ganin shigowar su tace, "Ke da wace ce haka Shahy?" Ta ƙare zancen tana leƙen fuskar Arab

Wacce itama kallonsu take yi, but tana tsaye a bakin ƙofa ta ƙi ƙarisa shigowa

Shahy kallon Arab ɗin tayi tace, "shigo mana ki zauna."

A hankali ta tako ta shigo amma ta ƙi zama sai bin ɗakin take yi tana yatsina, duk da ba wani abu ta gani ba a ciki, komai tsaf yake a muhallin sa

"Wai Shahy aina kika samo ta? Wace ce ita?" Wacce tayi mata tambyar ɗazu ta sake yin mata bayan ta tashi zaune a yanzu

Haka itama wacce take wayan tuni ta kashe tana kallon Arab

Shahy zama tayi tana zame Hijabin jikinta, sai ga ta daga ita sai wata ƙaramar riga da leggings a jikinta, gashin kanta kuma an saka attachment mai kalan ja. "Nima kun ganni ban santa ba, ganinta nayi a waje tana zaune shiyasa nayi mata magana, kuma tace tana buƙatar wurin kwana ne shiyasa na kawo ta. Ki zauna mana ko tsoro kike ji?" Ta ƙare maganar tana kallon Arab ganin har yanzu tana tsaye

Zama tayi ba tare da tace komai ba, tana zaune a kan carpet ɗin ɗakin, while su kuma suna zaune a saman ƙaton katifan da ya mamaye rabin ɗakin

Sai Shahy ɗin tace, "ki saki jikinki babu wanda zai cutar da ke a nan, Ni sunana Shahida, but ana ce min Shahy ko ƴar lalli, wannan kuma Sha'ira, ita kuma wannan Walida, tare muke kwana a ɗakin nan, za ki iya zama har lokacin da kike son tafiya, ke kuma ya sunan ki?" Ta tambaye ta dukka idanunsu a kanta

A taƙaice ta bata amsa, "Arab."

"Masha Allah, shiyasa na ganki kyakykyawa, alamu ya nuna ke balarabiya ce kenan?" Shahy tayi maganar tana murmusawa

Ita kuma sai tayi yaƙe batare da tace komai ba; bini-bini ta bi ɗakin da kallo

Walida ce tace, "amma gaskiya kin san akwai matsala Shahy, Magajiya idan ta san da zuwanta ba tare da an faɗa mata ba zai zama wata fitinar, kin san halinta ai, bare akwai ƴan sa ido duk da ba zama take yi ba zasu faɗa mata."

"Haka ne, zan faɗa mata bari tayi wanka ta canza kaya, kinga tana buƙatar yin wanka kayanta ya ɓaci, idan ta gama sai in je in faɗa mata." Sai ta kalli Sha'ira tace, "ina butar ruwan zafin nan in saka mata ruwan wankan?"

"Ga shi can saman drower." Ta bata amsa tana nuna mata da hannu

Ita kuma ta tashi ta ɗauko tare da fita, sai ga ta ta dawo da ruwan ta jona a socket tunda akwai nepa

Suna ta surutu amma Arab tana jinsu bata ce komai ba, sabida ganin ba ta son magana shiyasa su ma basu sake tambayarta ba, har ruwan yayi zafi Shahy ta sake mata ta kai mata bayin ɗakin. Ita kuma ta shiga tayi wankan

Bayan ta fito Shahy ta bata kayanta tace, "ga shi nan ki saka waɗannan, kiyi haƙuri da yanayin kayanmu; duk da ban sani ba ko kina sa irin su."

"Ba komai." Cewar Arab ɗin tana amsan kayan, riga da wando ne duk da basu kama ta sosai ba kasancewar Shahy ta fita girma da shekaru

Tunda ta saka kayan suke bin ta da kallo sabida yanda suka yi mata mugun kyau, musamman yanda suka sake ganin diri da tsarin halittar ta da ya ruɗa su

"Wow! Gaskiya ke kyakykyawa ce, Allah ya ba ki kyawu, kin burge Ni." Shahy ta furta tana mata murmushi

Itama murmushin tayi sai dai ta ƙi magana

Sha'ira tace, "amma ga shi ba kya son magana, zamu so mu san inda kike, ko kuma mai ya fito da ke daga gida?"

Zama Arab tayi tana kallonsu, sai tace, "Ni ƴar Zaria ce, na zo Kano ne sai kuma wasu mutane suka biyo ni, daƙyar na samu na ceci kaina."

"Allah Sarki! Maybe irin waɗannan ɓata garin ne, koda yake sun ga kyakykyawa." Walida tayi maganar tana dariya

Su ma duk dariyan suka yi ban da Arab ɗin da tayi murmushi

Sha'ira tace, "gwara ki je ki sanar da Magajiya kar wani magulmacin ya riga ki zuwa wurin ta."

"Ai babu wanda ya ga shigan mu ma, ina zuwa bari in je in dawo." Tayi maganar tana miƙewa ta fice a ɗakin. Bata jima sosai ba ta dawo tana kallon Arab da cewa, "taso mu je in kaiki wurin ta, wai zata ganki."

Miƙewa Arab tayi ta bi bayanta suka fita

"Ki saka takalman nan." Shahy ta nuna mata wasu takalma da ke bakin ƙofa

Haka ta zura suka wuce ɗakin Magajiya da ke can ƙarshen gidan. Suna zuwa suka shiga ciki

Wata Mata suka samu a zaune a kan kujera, gabanta kuma da ƙaramin faranti tana zuƙan taba tana kakkaɓe tokan a ciki. Shigowar su sai ta ɗago kai tana kallonsu a kaikaice tana hura hayaƙin bakinta

Arab kuwa tuni ta rufe hancinta da bakinta har ta soma tari; sabida yanda hayaƙin taban ya cika mata baki ya wuce mata ta maƙogwaro, ɗakin gaba ɗaya ya kaure da hayaƙin ko ganin Mutum ba a yi sosai

"Aunty Magajiya ga ta nan na kawo miki ita, kwana ɗaya tace zata yi gobe zata tafi shiyasa na taimaka mata." Cewar Shahy tana kallonta

Hankalinta na a kan taban tana kashewa tace mata, "ta basu wuri."

Fita tayi a cikin ɗakin kamar yanda ta buƙata

Ita kuma Magajiya sai da ta gama kashe taban tana kore hayaƙin da ya gauraye ilahirin inda take, shiyasa ko gani sosai ba tayi, sai da ta gama hure wurin yayi ɗan sauƙi sannan ne ta ga fuskar Arab da ke tsaye liƙe da hanci har yanzu, "ke ce baƙuwar da Shahy ta kawo?"

Shiru tayi mata sabida ta ƙi buɗe hancinta da bakinta da ta liƙe bare tayi magana

Tasowa Magajiya tayi ta ɗage labulen sannan ta dawo kusa da Arab tana ƙare mata kallo, sai ta sanya hannu ta cire mata hannun da ke fuskarta ta sake ganin fuskarta da kyau, ita kanta ta jinjina da ganin kyawun Arab ɗin, musamman da ta kama hannunta ta ji taushi, ko da kallon yanayinta ka san akwai hutu da jin daɗi a tare da ita, uwa uba kyawun da take dashi. Sai ta riƙo ta suka zauna a saman kujera tare da cewa, "amma ke bafulatana ce ko?"

"Eh." Ta amsa mata a taƙaice tana zame hannunta a nata domin ji tayi gabanta na faɗuwa sakamakon tunawa da Jameema, kar ya zo itama Magajiyan haka take shiyasa ta sake ja baya cike da fargaba

Murmushi tayi ita kuma tace, "kar kiji tsoro babu abun da zan miki ai, sai dai zubin ki ya nuna min ke ƴar gidan masu kuɗi ne, babu wahala a tare da ke amma kika fito yawon karuwanci?"

Kallon da Arab ɗin tayi mata ne yasa ta sake cewa, "ko ƙarya nayi ne? Ai duk Macen da kika ganta a nan gagaran iyayenta tayi ta taho nan, ke ma ga shi kin taho da alamu guduwa kika yi daga wurin iyayen ki, dama mun sha ganin ire-iren ku da suke zuwa neman mafaka, daga ƙarshe muna basu wuri shikenan sun zama cikin mu, sai su kama haya mu haɗa su da customers, Ke kuma ga shi kin zo a Sa'a domin yau insha Allahu zan haɗa ki da wanda za ki samu kuɗi ba kaɗan ba, Allah yayi miki diri mai kyau, ko Ni Mace na susuce da kyawun halittar ki bare namiji." Sai tayi murmushi ta kama hannun Arab ɗin tare da cewa, "kar ki wani ɗaga hankalin ki domin ke kyakkyawa ce, na tabbata shigowar ki cikin mu tamkar ɗaukaka ce a wuri na, idan kin amince anjima kaɗan idan ƙarfe sha biyu ta cika akwai wani Soja da zai aiko a ɗauke ki, a rana ɗaya 30k yake ba da wa, kawai buƙatar sa a kai mishi Mace ya kwanta da ita, da asuba zai sallame ki da kuɗinki ki dawo, dama irin ku kyawawa yake so na tabbata zai ji daɗin harka da ke, ƙila ma ki samu kuɗin da ya fi haka daga gare shi."

Shiru Arab tayi ta kasa cewa komai but tunani ne a ranta

Sai Magajiyan ta sake cewa, "kin amince kina bukata ko kuwa? Baza ki samu damar da ya fi wannan ba, in dai irin su ne ina da mutanen nan masu kuɗi da yawa, kuma zan haɗa ki dasu, kin kwanta min a rai shiyasa na ji ina son taimaka miki, daga yanzu ma ɗaki na za ki dawo da zama, zan ɗaukaka ki a gidan nan fiye da yanda kike zato."

Arab gani take yi tamkar dama ce ta same ta, duk da ta raina kuɗin amma a yanzu tana buƙatar su, gwara ta amince idan yaso daga can inda za'a kaita sai ta ƙara gaba, baza ta taɓa dawowa gidan nan ba tunda ita irin zaman gidan Karuwai ba burge ta yake yi ba, hasali ma baza ta iya sharing gida da mutane da yawa haka ba, kuma ba ka da ƴancin kanka kana ƙarƙashin wani sai abun da aka ce kayi, ta fi ƙarfin hakan domin ita ba ƙaramar yarinya bace, tana da kuɗin da zata kama gidan kanta ita kaɗai babu takura, sai dai tana buƙatar kuɗi domin barin garin nan, musamman idan ta tuna babu wayanta bare ATM ɗinta a hannunta, komai yana gidan Senator, sannan bata da damar cire kuɗin ta dole sai ta koma banki domin samun mafita yanda zata iya ciran kuɗin ta.




_Tom mai zai faru? Wacce ƙaddaran kuma Arab zata sake koma wa? Yanzu ne za a fara._
[17/08, 9:43 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍


*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*













_________________________

*BABI NA TALATIN*
_______________"Na amince." Arab ɗin ta furta tana kallonta

Murmushi Magajiya tayi tace, "yauwa ko ke fa, bari in ɗauko miki kayan da za ki shirya saboda lokaci ya kusa, babu jimawa za ki ga ya turo a ɗauke ki, kar ki bani kunya kinji ko? Duk da dai kin yi ƙanƙanta amma na san zai ji daɗin ganin ki, don Allah duk abun da yace kiyi mishi ban da gardama, da sannu za ki saba, Shahy zata koya miki komai abun da yakamata kiyi, zan kira miki ita ku tattauna." Sai ta tashi ta fita daga ɗakin

Arab ta bi ta da kallo kamar wata sokuwa, sai kuma tayi murmushi kawai, wai yau ita ce za'a koya wa barikanci da yanda zata tafiyar da naMiji? Sai ta kalli kanta kawai tana mamakin meyasa ta kira ta da ƙanƙanuwa? taɓe bakinta tayi tana lashe ƙasan bakinta

Magajiya tare da Shahy suka dawo tare

Magajiya tace, "ki tabbatar kin ɗaura ta a hanya kuma kin shiryata da kyau, na san yanzu Soja zai aiko a ɗauke ta."

"To Aunty." Shahy ta amsa mata da girmamawa. Tana fita daga ɗakin sai ta matso kusa da Arab ta zauna tana cewa, "Arab kina sane cewa wurin wani za'a kaiki? Ko dama kin fito yawon Bariki ne?"

Girgiza kanta tayi tana taɓe baki batare da damuwa a fuskarta ba

"To ke da za ki tafi gobe kuma shi ne za'a kaiki wurin wani? Gaskiya rayuwar bariki bai dace da ke ba Arab, ina ganinki tamkar ƙanwata ce domin kin shiga raina matuƙa, zan so ace muna tare da ke a gidan nan amma Ni ban ga amfanin zaman ki a nan ɗin ba, sabida za ki ɓata rayuwar ki a banza ne, kinga mu bamu da inda zamu zauna ne dole sai nan, dukkan mu da kika ganmu yaudaran ɗa namiji yayi sanadin fitowar mu gida, iyayen mu suka kore mu muka shigo duniya bamu da inda zamu je, sai da wannan rayuwar zamu iya kula da kanmu, amma ke kina

Please Login or Register in order to submit comment