Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiye maka."

Sa'id ɗin da ya miƙe sai ya narke fuska yana kallon ta, tare da cewa, "haba Arab sai kace ba ki sanni ba? Zan ba ki mana kar ki damu ki zuba min."

Taɓe baki tayi sai a lokacin itama ta ɗago manyan idanuwanta tare da zuba mishi su tace, "ka san hali na, a kuɗi bani da mutunci ka san da sani, Allah bazan ajiye maka ba idan har ba ka bani kuɗi ba, Ni na dena wannan gangancin."

"Ibrahim ka sanya baki mana, wai kamar bata sanni ba? Yawa ne wannan wlh, kin san hali na nima na san naki, bazan miki wasa da kuɗi ba, don Allah ki ajiye min yanzu babu kuɗin ne a hannu na, kuma idan nace sai na dawo zan siya zan zo in tarar da layi, ƙarshe in rasa, kuma so nake yi in wuce da wuri saboda akwai inda zan je."

Tsaki ta ja da faɗin, "zancen kake so, bani da lokacin ka wlh." Ta mayar da hankalinta a kan abun da take yi bata sake bi ta kanshi ba

Yayinda shi kuma yana ta roƙon ta tare da ce ma Ibrahim, "ya saka baki ta ajiye mishi don Allah, wlh zai bata kuɗin."

"Kaima da tuni ka je duk inda zaka je ka dawo, ka san halin Besty tunda tace baza ta ajiye ba, to; baza ta ajiye bane, ka je ka dawo Ni zan ajiye maka."

"Ok. Shikenan sai na dawo." Yayi maganar yana juyawa zai tafi tare da sanya hannu a aljihu yana zaro wayansa

Sai da ya tafi Arab ɗin tace, "bar ɗan iska, wlh bazan ajiye ba sai ya bani kuɗi, da ma ace ban san halin sa bane."

Dariya Ibrahim yayi yace, "ke ma ba ki da dama Besty a kan kuɗi."

Tura baki tayi tana tsikaro ɗankwalin ta a gaba tace, "Ah to, wa ke wasa da kuɗi? Ai Ni duk inda aka ce kuɗi, to; ba na wasa dashi, a kan kuɗi zan iya yin komai."

"Gaskiya ne Besty." Yafaɗa yana ƙyalƙyale wa da dariya, sai kuma ya sauko ƙasa ya duƙa setting kunnen ta yana raɗa mata, "kamu nayi miki fa, wlh wani babban Alhaji na samo miki me shegen maiƙo."

Waro fararen idanunta tayi da cewa, "kai don Allah? Ba na son wasa fa me sunan Baba?"

"Ah to, wanne wasa zan yi miki? Kin san bamu saba haka ba, wlh da gaske nake miki, irin waɗanda kike so, bari ki ga." Sai ya ciro wayansa ya danna kana ya nuna mata hoton wani ƙaton Mutum tulele wanda da ganin sa ka san ba ƙaramin Mutum bane, kuɗi ya zauna masa sosai, don ma a inda ya ɗauki hoton kana gani ka san waje ne na alfarma

Amsar wayan tayi da sauri tana dubawa

Sai shi kuma ya ci gaba da cewa, "a Abuja yake zaune, amma shi mutumin Bauchi ne, a can iyalan sa suke, ɗan hannu ne wlh sosai, nima ɗan small ne ya haɗa Ni da shi sabida ya san Mutumin, yace wlh ba ƙaramin kuɗi zamu samu a hannun sa ba idan har na tura ki wajen sa, shiyasa da gaggawa na amsa tayin nasa saboda Ni kaina sai da nayi bincike before in zo wajen ki."

Ci je baki tayi tana ɗauke idanunta a kan hoton da ta kafa masa, ta mayar a kan Ibrahim tana cewa, "Ni ba wannan nake son ji ba. Ka tabbatar akwai samu a ciki sosai? Don ka san hali na ba na son harkan ƙaranta."

"Haba tawan, kin san na fi kowa sanin halin ki, akwai nace miki, but kinga mutane sun soma yowa nan, ki bari zamu ƙarisa zancen idan kin koma gida, ko kuma muyi waya kawai."

Baki ta washe cikin farin cikin da ya bayyana a kan kyakkyawar fuskarta tace, "ok. I would also prefer that."

"Yauwa Besty na."

Da haka suka ci gaba da magana suna dariya, yayinda wurin sai cika da jama'a yake yi, duk maza ne manyan samari da magidanta, har da masu kuɗi ƴan hannu zuwa siyan awaran nata suke yi don kawai suyi harƙalla da ita

Nan da nan sai awaran nata ya ƙare ko kiran sallan magriba ba'a kai ga yi ba, shiyasa ta tattara kayanta ta ba wa wani almajiri yayi mata gaba da su, sannan suka tako da Ibrahim zai raka ta gida

Wani saurayi ne a mota ya bi bayan su, ya tsayar da motan a kusa da su yana cewa, "ƴan mata ji mana."

Tsayawa suka yi yayinda suka zuba mishi idanu. Gaba ɗayan su kallon yanayin tsarin zubin motan nashi suke yi tare da hasashen yanayin sa; kuma ba tare da tayi yunƙurin amsa shi ba

Sai ya sakar musu murmushi tare da cewa, "Aboki na ɗan bamu wuri mana, zan yi magana da ƙanwar taka."

Shima murmushin Ibrahim yayi tare da shafa kansa yace, "ok ba damuwa Alhaji." Sai ya kalli Arab yace, "Besty Ni zan wuce gida, zamu yi waya kawai."

"Ok bye." Ta furta cikin yanga tana ɗaga masa yatsu

Bayan wucewan sa ne sai saurayin ya buɗe mata ƙofan mazaunin banza yace, "shigo mana Gimbiyya."

Sai da ta kalle sa ta tura baki cikin jan hankali kana tace, "a nawa?"

Murmushi yayi yace, "duk farashin da kika yanka min Ni na amince."

"But ban yi tunanin da sauƙi hakan ba." Tayi maganar tana kafe shi da kallon ta da ke rikita su

Still murmushin yayi yace, "ai ke ce kin fi ƙarfin hakan, ko dukiyata kika ce in ba ki domin mallakar ki; da gudu zan aikata hakan."

"Allah ko?" Tayi maganar tana zaro ido waje kaɗan mai nuni da mamakin maganar sa, yayinda fuskarta ke ɗauke da shu'umin murmushin ta da ba kowa yake iya gane ma'anar sa ba

"Da gaske, kin wuce haka a wuri na, but na san tsokanata kike yi ke ma kin san da haka, ba Ni ne farkon faɗa miki ba."

"No you were the first to tell me, in your mouth I began to hear, kuma kaga dole in yi shakkar amincewa da kai At the same time, bare yanzu da kidnappers suka yi yawa."

Dariya yayi saboda yanda tayi maganar, cike da burgewa yake kallon ta yace, "haba Princess ban zaci haka a gare ki ba, anyway idan ba ki sanni ba Ni na san ki, cuz na daɗe ina bibiyan ki, kuma ina zuwa wurin nan sosai, but sai dai ba ki taɓa kula dani bane, but idan ma Ni kidnappers ne ai ba laifi bane, a kanki zan iya sace ki idan har hakan zai saka zuciyata ta samu natsuwa."

"Ko?" Tayi maganar tana sake ware mishi kyawawan fararen idanuwanta a kanshi

"Yeah, please ki shigo ba don hali na ba, wlh na ƙosa in ji ki a cikin motata, idan ba haka ba zuciyata zata fashe." Sai ya ɗaura hannun sa a setting zuciyar nasa tare da ƙarisa zancen da cewa, "saboda ba ki ji yanda take bugawa bane, saura ƙiris..." Sai ya cije leɓe yana sake faɗin, "wash Allana!"

Dariya tayi kaɗan cike da jan aji, sai tayi wal da idanunta cike da yanga tace, "afwan kyakykyawar saurayi, bari in shigo."

"Yauwa ko ke fa." Yafaɗa yana washe baki, "wlh bazan iya jure jan ajin nan naki ba, gwara ki taimaka min."

Sai da ta shiga ta zauna before ta juya tana kallon sa da kyakkyawar murmushinta me shiga rai tace, "to kayi haƙuri na ce ai, gani na shigo."

"To amma zan nemi wata alfarma."

"Why not." Tace tana ɗage kafaɗa

"Zan ɗan gyara parking sabida naga kamar a hanya nake."

"Ok ba damuwa."

Sai ya yiwa motan key ya ja zuwa gefe sannan ya faka, tare da juyowa kacokan yana kallon ta cikin tsantsan sha'awa da nuna zalaman sa, inda kyakykyawar murmushin sa ke gudana a kan fuskarsa

While itama yanda yayi tayi, ta zuba mishi narkakkun idanuwanta masu shegen kaifi da ratsa ɓargon Mutum, wanda lokaci ɗaya suke sake zautar da ma'abocin kallon su

Shiru suka yi babu mai cewa uffan a tsakanin su, inda suke sakarwa juna wani irin kallo me tattaro saƙonnin zuciyoyin su suna aikawa juna. Yayinda murmushin farin ciki ke kwance a kan fuskartasu cikin shauƙi; tamkar sun san juna da daɗewa a yanayin kallon da suke yiwa kansu

Tsawon mintuna biyar before ya ja wani irin dogon numfashi yana lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta, sai ya buɗe baki cikin wani irin yanayi yace, "Gimbiyyata."

Ɗan waro idanu tayi cikin salo da guntun murmushin ta tace, "har na zama taka?"

"Eh mana, wace ce Gimbiyyata idan ba ke ba? Ai babu wata mace kyakykyawa a faɗin duniyar nan kamar ki, ba ki san jimawan da nayi ina bibiyan ki ba ko? Uhmm zuciyata ta jima da makancewa a kanki, ban yi tunanin zan iya kaiwa har wannan lokacin ban sanar da ke abun da ke raina ba, sai dai kuma ɗan wata tangarɗa da aka samu wanda ya hana Ni bayyanuwa a gaban ki, amma yanzu gani na dawo." Sai yayi shiru yana sake zuba mata idanu kamar yanda itama take mishi wani irin kallo me saka shi a wani irin ɓigirin da be taɓa tsintan kanshi ba, "na san za ki yi mamaki idan nace miki na san komai game da ke, Arab zuciyata ta makance a tun sanda idanuwana suka soma tozali da kyakykyawar fuskarki, na kasa natsuwa tun sanda na ganki, wlh ban taɓa jin wata ɗiya Mace ta shiga raina kamar ki ba, na so in jure amma na kasa, don Allah na zo da ƙoƙon barata ki taimaka ki amshe Ni a matsayin masoyin ki na gaskiya, ina ƙaunar ki! I love You A'isha Humaira, i love You with all my heart!"

Lumshe manyan idanuwanta tayi sabida jin sunan da ya kira ta, ba kowa yake kiranta da sunan ba sai mahaifin ta, shi kaɗai ne ba ya kiranta da suna Arab sai A'isha Humaira. Buɗe idanun tayi ta zuba mishi tana kallonsa da shu'umin murmushin ta da a koda yaushe yake saman fuskarta. Bata yi magana ba illa kallonsa da take yi tamkar zata cinye sa babu wani ɗar ko jin kunya a tare da ita, hasali ma tsantsan gogewa ne irin nata na bariki

Shi kuma sai yace, "kin yi shiru Gimbiyyata? Ko so kike yi zuciyata ta buga?"

Wani guntun murmushi ta sauke before tace, "Ina wani tunani ne a raina that's the reason da ka ji nayi shiru."

"Amma ba ki yarda da Ni bane? Wlh ina ƙaunar ki! Don Allah kiyi min magana ko ya ya ne inji daɗi." Sai ya saka hannayen sa biyu ya kamo nata da take faman shafa fuskarta dasu, ƙurawa junan su idanu suka yi na ƴan seconni before yace, "ina sonki! Me kike so in yi miki da za ki yarda?"

Still murmushin tayi tana cije baki tare da sake narke idanuwanta tana wani luuu dasu tamkar zata rufe sai kuma ta buɗe su, cikin wani irin kallonta me sake zautar da duk ma'abocin da tayi masa tare da fitar dashi a wani yanayi lokaci ɗaya

Wanda hakan ne ya soma tasiri a jikinsa har be san sanda ya sake damƙe hannayenta a cikin nashi ba yana wani irin murza mata cike da wani irin feelings da ya taso mishi

Hakan yasa tayi murmushi kaɗan tana cewa, "har yanzu ba ka sanar da Ni kai wane ne ba balle in so ƙulla alaƙa da kai."

"Haba idan har don wannan ne kar ki wani damu, na sha'afa ne, suna na Tariq... Tariq Muhammad Auwal, Ni mutumin Samaru ne, ina zaune tare da iyaye na da ƴan uwana, kuma abun farin cikin bani da Mata." Ya ƙare maganar yana mata murmushi

Yayinda ita kuma ta saki dariya kaɗan wanda ya bayyana haƙoran ta, still idanuwanta a cikin nasa, sai kuma ta sake sakin murmushinta tana janye hannayenta a cikin nasa tace, "meyasa za ka taɓa min jiki ba tare da mun yi farashi ba? I'm an expensive girl."

"Don't worry, I have the money to pay you until you say it's enough."

"Really?" Tayi maganar tana ɗan waro idanu waje wadda ya zame mata ɗabi'a; kuma yake ƙara mata kyau ainun

"Yeah. You just give me a chance."

Leɓen ƙasan bakinta ta shigar cikin bakinta tana tsotsa cikin salo da jan hankali, sai kuma ta cire tana ɗage kafaɗa tare da faɗin, "fine. I answer you both hands."

Dariya yayi cikin farin ciki tare da cewa, "gaskiya ke ta daban ce, na ji na ƙara sonki matuƙa, but yanzu kin bani damar taɓa hannun ki ko?" Ya ƙare maganar yana kashe mata ido ɗaya da murmushi a fuskarsa

"Me kake ci na baka na zuba? kar ka damu, har sai ka gaji da taɓawa."

"Haba idan ko haka ne bazan taɓa gajiyawa da taɓa kyakykyawar halitta kamar ki ba, ba ki san yanda kike da matsayi a cikin raina ba."

Bakinta ta ɗan turo gaba before ta ja numfashi tace, "ok. Zan tafi, ka ga dare yayi."

"To, babu ko ɗan kiss haka zamu rabu?"

Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa na ɗan wani daƙiƙu, sai ta saki wannan shu'umin murmushin nata kafin tace, "me kake yiwa sauri haka? Za ka samu abun da ya fi kiss ma, but not know."

Langaɓe kai yayi, yayi mata fuskar tausayi tare da cewa, "Please Princess."

"No. Zan ta fi." Ta furta tana ƙoƙarin buɗe ƙofan

Sai yayi saurin kamo hannun ta da cewa, "haba Gimbiyyata kar ki tafi, I'm sorry to, na daina maganar."

Hannunta ta zame tana kallon fuskarsa

Sai yayi mata murmushi yace, "to ki bani Numban ki mana."

"Ok." Kawai ta furta tare da karanto mishi numbern

Sai ya rubuta sannan ya buɗe lockern motan ya ciro kuɗi 20k ya miƙa mata
     

Ta sanya hannu kuwa ta amsa ko jan aji bata yi ba, sai ga kyakykyawar murmushin ta ya bayyana a kan fuskarta, yayinda take bin sa da kallo me ban sha'awa tace, "tnx. Bye."

"Bye dear." Sannan ya ɗaga mata hannu yana mata murmushi har ta fice, sai da ya ga tafiyar ta before ya ja motan ya bar wajen cike da farin ciki a zuciyarsa.


            

_Don't forget to follow me on Wattpad, and voted 🙏🙏. Tnx._
[07/07, 11:27 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

    *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍


*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*










_________________________

*BABI NA UKU*

_______________A bakin ƙofan gidan su ta ci karo da mahaifinsu, wanda yake zaune tun dawowar shi masallaci sallan isha'i, ya shimfiɗa tabarma yana shan iska. Ganinta ne yasa ya kira sunan ta yana cewa, "A'isha Humaira daga ina?"

Yamutsa fuska tayi tana ɗan sosa kanta tace, "Baba daga wurin saurayi na."

Shiru yayi yana kallon ta don ya san halinta ba kunya ne da ita ba, bata da ɓoye-ɓoye abin da ke ranta shi take faɗa. Ganin zata wuce ciki sai yace mata, "dawo ban sallame ki ba."

Dawowa tayi tana faman tura baki tare da ƙunƙunai

"yanzu A'ishah Humaira abun da kika ɗaukarwa kanki kenan? Ban hana ku yawon dare ku kai war haka baku dawo gida ba?"

"To Baba ai nace maka wajen saurayi na naje, ba fa yawo na je ba ina nan bakin layi."

"Shikenan. Allah ya shirya, idan kin shiga ki kawo min abinci na in CI a nan."

Wucewa tayi ba tare da ta amsa mishi ba ta shige gidan

Yayinda shi kuma ya girgiza kansa a ransa yana takaicin wannan rayuwa na yaranshi, ya rasa yanda zai yi ya gyara su, ko yayi ma a banza tunda uwarsu tana warware wa, duk halin su ɗaya gaba ɗaya babu me kallonsa da wani ƙima, sun riga sun taso ba sa shakkar shi bare tsoron shi, tamkar shi ba mahaifinsu ba saboda yanda suka ɗauke shi, ko ince yanda uwar su tayi musu tarbiyya, Firdausi ce kawai ta fita zakka a cikin su, kuma duk hakan yana faruwa ne kasancewar sa me tsananin haƙuri kuma mara faɗa, yana da sauƙin kai ko kaɗan be iya faɗa ba bare ya ce zai ɗauki mataki a kansu, yana ƙaunar yaranshi shiyasa a kullum fatan shiriya yake musu, duk da abun yana matuƙar damun shi domin yanzu babu inda gidan shi bai zagaya ba a faɗin arean nan, kowa ya san yaran shi basu da tarbiyya, wasu ma don rashin ta ido har taren shi suke yi a hanya suna mishi zancen Yaran shi basu da tarbiyya, ya kan yi kuka wani lokacin saboda be san yanda zai yi ba, yayi nasihan duk wani abu da ya kamata uba yayi; yayi musu, amma uwar su ta ɗaure musu gindi, bai da wani fawa a gidan, bare yanda ta mallake shi sai abun da tace, shiyasa be da kataɓus a gidan, ko ya so ɗaukar mataki mummuna ba ya iyawa, sai dai ya zira musu idanu yana musu addu'ar shiriya, ya san wata rana Allah zai dubi maraicin sa ya shirya mishi su, fatansa kenan a rayuwa. Numfashi kawai ya ja yana ci gaba da jan carbin shi.






             *******

       Arab kuwa tana shiga gidan ko sallama bata yi ba

Yayinda su Inna suna zaune a tsakar gidan a gindin bishiyar Mangwaro da ke dirke a tsakiyar gidan suna shan iska, kasancewar garin akwai zafi sosai. Daga ita har su Ummu suke zaune suna cin abinci a cikin faranti ɗaya, tunda haka suke yi a koyaushe, Inna Harira Mace ce mai tsananin ƙaunar yaranta, akwai sabo mai ƙarfi a tsakanin su, ta ɗauke su tamkar ƙawayenta ne, a rayuwa babu abin da take ɓoye musu nata haka su ma, suna rayuwar su ne cikin ƙaunar juna da tsantsan shaƙuwa a tsakanin su, tun farko haka ta sabar musu cin abinci tare a kwano ɗaya, sai dai idan ɗaya ba ta nan ne ko tayi dogon zango shine zasu ci babu ita, ko kuma su jira ta idan ta dawo su ci tare, amma duk runtsi dole sai kaga cikin su wasu sun ci tare, shiyasa shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakanin su, su kansu yaran suna ƙaunar junan su matuƙa, kuma basu yarda wasu sun shigo rayuwar su ba, kaf ɗinsu babu mai ƙawa sai junan su, su ne ƙawayen juna su kashe tare su binne tare, shiyasa duk da babu tarbiyya a tare dasu amma suna rayuwar farin ciki a gidan su, basu damu da surutun mutane a kan rayuwar su ba, a ganinsu rayuwar su ne babu wanda ya isa ya hana su tafiyar da ita yanda suke buƙata, duk wanda yace zai taka su sai inda ƙarfin su ya ƙare, kaf ɗinsu basu da haƙuri suna rayuwarsu tamkar ƴan tasha, musamman Arab wacce duk ta fi su sheɗananta, ita abun kunya gaba ta ba shi ba baya ba, ba ta shakkan kowa sannan babu wanda zai mata a duniyar nan bata mayar mishi ba, komin tsufan shi komin girman shi, wannan sun sha a nonon uwar su ne. Domin idan wani ya taɓawa Inna Harira yara abu me sauƙi ne ta bi Mutum har gida ta ci mishi mutunci ta uwa ta uba, kowa ya sansu a kaf anguwan su har da maƙota, ba a taɓa su su ƙyale, an sha yin dambe da Inna a kan yaranta, bata da mutunci ko kaɗan a kan ka taɓa mata Yara, musamman zata saka wandon dambe ta bi ka har gida ku caku. Shiyasa yanzu da yaran nata suka girma wani lokacin tare suke zuwa ayi ta dambe ana faɗa a anguwa, in dai aka tayar da husuma a anguwan nan to kowa ya san ƴan gidan Malam Iro mai kifi ne, su ne ba sa barin anguwan ta zauna lafiya, an sha kaisu police station a kan husuma, su yanzu har sun saba da kowacce fitina ba sa tsoron ko wanne shege, bare yanda kaf ɗinsu Yaran suna da samari a station ɗin, ana kaisu za'a sako su, wani lokacin ma ƴan sandan ba sa jirgawa ko nan da can da su, a wajen zasu kashe maganar, shiyasa ma ƴan anguwan suke musu kirari da gidan Fitina. Wannan kaɗan kenan daga rayuwar iyalan Malam Iro.


         Kai tsaye wajen su ta nufa tana cewa, "Inna wai Baba yace a aika mishi da abincin sa waje."

"Ga yi can a ƙofar ɗakina ki ɗauka ki kai mishi."

Gyalenta ta cire ta jefa a saman tabarman da suke kai, sannan ta nufi coolarn abincin Baban nasu ta ɗauka ta fita da gudu ta kai mishi. Tana shigowa nepa suka ɗauke wuta, dogon tsaki ta ja tana cewa, "ka ga ƴan iskan mutanen nan, daga shigowa kuma sai ɗauke wuta? Ga shi ina son saka caji."

"Haka suke yi matsiyata, yanzu suka gama wasa dashi, ga shi kuma sun ɗauke, idan ba wasa ba kuma sai tsakar dare su dasu kawo wutan nan." Cewar Ummu bayan ta haɗiye abincin bakin ta

Inna kuma tace, "Auta kunna mana Gen ɗin kafin ki zauna, Allah yasa ma muna da ishashshen mai a ciki."

Wucewa tayi ta kunna sannan ta wuce ta wanke hannu ta zo ta zauna, ta saka hannu a abincin tana cewa, "wai Aunty Zahra aina kika samu wannan guy ɗin ne?"

Zahra kallonta tayi tace, "wai Salisu? Ba ki sanni dashi bane? Shi ne fa wanda nace miki mun haɗu a bikin gidan Jamila ƴar gidan sanata da muka je mata, Ni ban ma san waye ya nuna mishi gidan mu ba, muna dai waya dashi kusan kwana biyu, sai yau kuma na ganshi ya zo."

"To shi ɗan gidan waye ne? Ba ki bani labari ba Mamana?" Inji Inna tana washe baki

Dariya suka yi gaba ɗayansu

Yayinda Zahra take basu labarin Salisu da aikin da yake yi

Itama Arab kuɗin da Tariq ya bata ta ciro ta miƙa wa Inna duka tana cewa, "nima kamun wani nayi wlh, duk da ban san ɗan waye ba amma da alamu yana da fararen." Ta ƙare maganar tana dariya cike da farin ciki

Haka su ma suna taya ta

Inda Inna tace, "ai na san ki Autana babu wasa a lamarin ki, sai dai idan ba ki fita ba, Allah yayi muku albarka baki ɗaya, haƙiƙa na haifi yara masu farin jini, hakan a jini na yake wlh, Ni na san da haka, duk wani me baƙin ciki sai dai ya mutu, ga shi yara mata suna share min hawaye."

Dukkan su murmushi suke yi suna sauraron Innar tasu. Da haka suke ta hira abin su

Yayinda Arab ta tashi ita ta nufi bayi, bata jima ba ta fito ta ɗaura alwala ta wuce ɗakinsu ta rama sallan da ake bin ta na magriba da isha'i. Sai ta zauna a ɗakin tana waya da Ibrahim

A nan yake sake bata labarin Mutumin da ya samo mata, da komai nashi sai da ya faɗa mata, sannan yace, "ta kira shi su soma magana yanzu."

Tace, "a'a sai zuwa gobe."

Dariya yayi yace, "ai girman ki ne Besty na, ina jin daɗin jan ajin nan naki, gaskiya ke ta daban ce a cikin mata, har yanzu ban ga kamar ki ba, kina lokaci ƴan mata na, kin fi ƙarfin Yaro sai dai baban Yaro."

Itama dariyan tayi tana cewa, "Besty kana fasa min kai da yawa."

"Ai matsayin ki ne My Besty, ke ɗin ce ban san yanda zan kwatanta ki ba, amma wlh kin kere duk wata Mace da na sani a rayuwata, Allah ya barmu tare."

"Amin." Tayi maganar tana dariya, "shiyasa nake ƙara sonka Besty na."

"Nima haka Besty, i love You wujiga-wujiga, ba don kin fi ƙarfi na ba da tuni nayi wuff da ke."

Dariya take yi sosai

"Allah kuwa My Besty, yanzu meye tukuici na?"

"Oh Besty! Ba ka yin abu don Allah fa na lura?"

Kashe murya yayi tare da cewa, "haba dai, Ni na isa? Ai duk abun da zan miki don Allah ne, kin san Ni na sanki, Ni da ke ba ta ɓaci, Allah ne ya haɗa jinin mu, abun da kike so shi nake so, haka kuma abun da kike ƙi shi nake ƙi, ke ma kin sani ai.. kawai dai kwaɗayin nawa ne ya tashi wlh."

"Uhmm shikenan. Let's meet tomorrow."

"Ok. But ba ki bani labarin Mutumin da kuka haɗu ɗazu ba?"

"Ai yanzu zan faɗa maka ka san ba na ɓoye maka komai." Daga nan ta ba shi labarin yanda suka yi. Basu jima suna wayan ba ta katse sabida ganin baƙuwar number tana kiran ta. Bayan ta ɗauka sallaman Tariq ya doki kunnen ta, rage murya tayi tana kwanciya a kan gadonta, yayinda ta juya baya ganin Ummu da Zahra

Please Login or Register in order to submit comment