Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun shigo ɗakin. Haka tayi ta wayanta baza ka taɓa cewa waya take yi ba. Sun raba dare suna tare da Tariq before su yi sallama ta kwanta

A time ɗin su Ummu su ma har sun yi barci.

         Zuwa washe gari kuma suka ta fi makaranta. Dayake ita Arab text suke yi a school, saura two weeks su fara Exams, daga nan kuma sai su shiga S.S 3. Ƙarfe sha biyu ta dawo gida

A lokacin Baba yana gida domin dawowar shi kenan daga wajen suyan kifin sa; yake sanar da Inna halin da Firdausi take ciki. Mijinta Nafi'u ya kira shi yace mishi, "bata da lafiya, yanzu haka suna asibiti an kwantar da ita, duk da dai yace jikin da sauƙi yanzu."

"To Allah ya sauwaƙe." Cewar Inna tana wucewa cikin kichen tare da cewa, "Auta har kin dawo?"

"Eh Inna." Ta furta itama tana shigowa tare da zama a kan kujeran zuƙuno, sai kuma ta kalli Babansu tace, "sannu Baba."

"Yauwa Aisha Humaira. An dawo?"

Fitowar Inna tana kallonta tace, "wai ba karatun ne kika dawo da wuri?"

"Akwai mana, muna yin text ne kuma ba wani abu ake yi ba shiyasa na dawo."

Baba ya kalli Innan yana cewa, "yanzu babu wanda zai je a cikin ku ne? Ai ya kamata ko ɗaya daga cikin yaran ne ya je ya zauna da ita, itama zata ji daɗi idan ta ga ƴan uwa, Mijin yace min idan da hali wata ta zo ta zauna da ita tunda kullum damuwar ta yaran nan ne, ta ce a tura mata ɗaya a ciki."

Mitsitstsike baki Inna tayi da cewa, "a tura wa? Ai babu inda zasu je tunda kowacce ba zaman banza take yi ba, in ba iya shege ba ai ta san babu wanda zai je yayi mata bauta tunda ta san suna makaranta, kuma sana'ar nawa ubanta zai yi min?"

Shiru Baba yayi be iya cewa komai ba illa kallonta da yake yi, sai kuma ya girgiza kanshi sabida takaicin Inna

Arab tace, "Inna ni zan je domin dama ina son zuwa, yakamata ace ko sau ɗaya ne mun je amma har yanzu bamu ƙara zuwa gidanta ba tun auren."

"To makarantar naki fa Auta? A'a babu inda za ki je."

"Allah Inna zan je, ai Ni nace miki ina son zuwa, kuma makaranta bani da matsala da hakan tunda Exams ya rage kuma ba yanzu zamu yi ba, har zan je in dawo, zan mata kwana biyu sai in dawo."

Baba washe baki yayi yace, "yauwa A'isha, ai zata ji daɗi idan ta ganku, to yaushe za ki tafi in ba ki kuɗin mota?"

"Ka bar shi kawai Baba ina da kuɗi, idan rana tayi sanyi sai in wuce."

Inna tace, "don dai kin matsa ne babu yanda zan yi amma wlh da baza ki je ba, har wani ciwon ne sai an je an ganta?" Sai ta ja tsaki tana wucewa

Baba kuwa girgiza kansa kawai yayi, sai kuma ya kalli Arab da ta miƙe zata wuce yace, "bari in koma wajen sana'a na, kafin ki tafi zan dawo sai muyi sallama."

"Sai ka ce wani tsiya za ka bata idan ka dawo ɗin? Aikin banza aikin hofi." Inna tafaɗa bayan ta fito daga ɗaki tana dallawa Baban harara

Baba kuma bai ce komai ba ya wuce ya tafi

"Arab ki zo ki ɗibi abincinki ki ci, sai ki zo ki amso min ƙanƙara wajen Lantana in sa a kunun nan. Na san yanzu zasu dawo tunda sun ce ƙarfe ɗaya zasu gama karatun."

"To ina zuwa." Arab tafaɗa daga cikin ɗaki, kayan makarantarta ta cire ta saka wani doguwar rigan Abaya wanda ya fito mata da kyakkyawar shafe ɗin jikinta, sosai rigan ta kama ta saboda yanda aka matse mata dai-dai jikinta, sai ta ɗaura ɗankwalin Abayan a saman kanta da ke ɗauke da ƙananun kitso da aka yi mata, sun zubo har kafaɗunta, kana gani ka san ta haɗa jiɓi da Fulani saboda yanda gashin suka nannaɗe gunin sha'awa, sai dai ƙarshen kitson duk ya tsefe duk da kuwa kasancewar kwana biyu kenan da Ummu tayi mata, kasancewar ita tana son kitso shiyasa ko yaushe za ka ganshi a kanta duk da gashin nata ba ya zama da kitso, yanzu idan ma ta bar shi kafin sati ya tsefe da kanshi don da kanshi yake tugewa, shiyasa bata da wahalan ta sake wani kitson tunda tana da masu yin mata, har Inna tana yin mata, ita kaɗai ce me son kitso a cikin su, don su Zahra ma bai dame su ba sun fi son barin kansu a haka tunda su ma nasu gashin ba ya son kitso, ko sun yi warware wa yake yi, duk Innarsu suka biyo. Flat shoes ta saka a ƙafanta sannan ta fito

Inna tace, "nace ki bari ki ci abinci sai ki wuce."

"A'a ba na jin yunwa, bari in amso miki, idan su Aunty Ummu sun dawo sai mu ci tare."

"To." Innar tafaɗa tana wucewa kichen ta sauke abincin siyarwan da take yiwa su Ummun

Itama kuma Arab ta sa kai ta fice. Bata jima ba ta dawo tunda a maƙotan su Lantanan take

Time ɗin su Ummu sun shigo su ma. Shiyasa suka zauna suka ci abincin tare

A nan Arab take sanar da su, "zata je gidan Aunty Firdausi."

Zahra tace, "ai da na bi ki kuwa, amma babu hali tunda karatu yayi zafi, sai dai ki gaishe ta, nima zan kira waya in Yi mata ya jikin."

Itama Ummu tace, "Auta ki gaishe ta don Allah, ko zuwa weekend ne zamu zo, amma yaushe za ki dawo?"

"Kwana biyu kawai zan yi, tunda kun ce zaku zo sai in tsaya mu dawo tare."

"Eh hakan yayi, Allah ya kaimu Asabar zamu zo sai mu dawo a ranan."

Inna dai na jinsu bata ce musu komai ba. Sai da ta gama abun da take yi sannan tace, "ga abincin nan na gama don Allah ku tashi ku wuce, kunga har biyu tayi."

"To Inna." Duk suka amsa mata

Yayinda Zahra CE ta soma tashi tayi alwala ta shige ɗaki

Itama Ummu alwalan tayi; tayi sallan sannan suka shirya suka fita

Arab tace, "Inna bari in Yi wanka kawai in wuce, ki bani dubu goma a kuɗin jiya saboda babu kuɗi a hannu na."

"Ki shiga ɗaki ƙasan Matashi na suna nan na ajiye a wajen."

"To." Tace tana wucewa. Sai da ta ɗauki kuɗin ta je ta saka a jaka sannan tayi wanka ta shirya. Riga da wando ta saka masu tsantsi, rigan milk color da flowers a dai-dai setting ƙirjin ta da aka yi da kalan maroon color kalan wandon, wanda shima ƙasan wandon aka yi flowers da milk color, kayan sun yi mata kyau ainun sabida kasancewar ta me sura me kyau wanda duk namijin da ya kalle ta sai kyawunta ya bizge shi, bare uwa uba yayi arba da kyakykyawar cuty face ɗinta, fuskar nan nata ta sha makeup me ɗaukan hankali, bakinta sai shaining yake yi, gyalen kayan ta ɗauka kalan milk ta yafa a kanta sannan ta jefa jelan a gefe da gefen kafaɗunta, sai ta saka takalmi masu shegen tsini white color, sai da ta jefa chewing gum a bakinta domin ita mayyar cin chewing gum ne, ya zama sabon ta ba ta rabo dashi, Hangbag ɗinta ta ɗauka na takalmin shima kalan fari ta rataya, sannan ta fito cikin yauƙinta ta wuce ɗakin Inna

Inna na ganinta ta washe baki saboda farin ciki, "ga farar zinariya alkyabbar Mata, kin kerewa kowacce Mace sai dai su biyo bayan ki, kinga yanda kika haɗu kuwa?"

Dariya tayi tana taunan chewing gum ɗinta ƙas-ƙas-ƙas, sai tace, "na san haka Innata, amma nayi  zam-zam ko babu wata mishkila?" Ta ƙare maganar tana juyawa a gaban Innar

Inna tace, "babu abun da yayi saura, ai ke me kyau ce Autana, ko ba ki yi kwalliya ba komai yin miki kyau yake yi, Allah yasa ki samo mana wani me gwaɓi-gwaɓi wanda zai kai ni Makka da Madinah."

Arab tayi dariya tace, "Inna kar ki damu insha Allahu zan cika miki burin ki wata rana."

"Kai Allah ya amsa addu'ar ki Autana, amma ki kula fa don bazan so wani abu ya same ki ba, Allah ya tsare."

"Amin Inna." Sai tayi dariya tana cewa, "to Inna ba ki ce in gaishe da Aunty Firdausin ba?"

Taɓe baki tayi tace, "to har sai na ce? Ai ta san ina gaishe ta".

Sosai Arab take dariya a wannan lokacin, tace, "Innarmu na Aunty, Allah ya bar ku tare, zan ce kina gaishe ta sosai, zan biya sai in Yi sallama da Baba a kasuwan. Babu wani abun da zan kai mata ne?"

"To me nake dashi da zan ba ki? Gaisuwar ma ta isa."

"To Inna na tafi, bye." Sannan ta fice ta shiga ɗakin su, jakarta da ta zuba kayan sakawanta ta ɗauka, ƙaramar Trolley ne, ta janyo ta fito. Har waje Inna ta raka ta suka sake sallama sannan ta tafi.
[07/07, 11:29 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍


*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*










_________________________

*BABI NA HUƊU*
_______________ *KADUNA STATE*
            Bayan Arab ta sauka a tashan Kawo da ke Kaduna; sai ta kira Numban Nafi'u tunda sun san da zuwanta, time ɗin da Baba ya je kasuwa ya kira ya sanar mishi, "Arab na nan zuwa."

Babu jimawa kuwa sai ga Nafi'u ya taho a motan shi, bai sha wahalar hango ta ba, sai ya faka motan nashi ya fito ya nufi inda take tsaye riƙe da waya a hannu tana faman latsawa, kanta na sunkuye tana tauna chewing gum ɗin da ke bakinta. Yana isowa yayi mata sallama

Sai ta ɗago kai tana kallonsa da manyan idanuwanta da suka sha tozali suka sake haske tarr masu ɗaukar hankali, murmushi ta saki tace, "Yayanmu."

"Na'am Autanmu. Barka da zuwa."

Dariya tayi sai tace, "yauwa. Ina wuni?"

"Lafiya ƙalau, ya mutanen gidan?"

"Alhamdulillah duk suna gaishe ku."

"Masha Allah muna amsawa. Mu je to ga motan can, kawo akwatin." Ya saka hannu ya karɓa sannan suka taho wajen motan suna magana suna dariya. Bayan sun shiga ne yake cewa, "bari in kai ki gida inyaso sai in je ɗauko Auntyn naki tunda an sallame ta ma."

"A'a Yaya, mu je tare sai ka ɗauko ta."

Murmushi yayi yace, "ke da kika sha hanya? Ki bari kawai in ɗauko ta ɗin kar ki sake shan wahala, suna tare da Ummana ne ma, bari in kai ki sai in je in ɗauko su."

"Ok shikenan."

Daga haka suka wuce gidan Nafi'un. Ƙaramin gida ne flat ya gina abun shi, bai jima da tarewa ba bayan auren da suka yi. Mahaifiyarsa kuma tana babban gidan su ne tare da kishiyoyinta; tunda Matan Baban Nafi'u su huɗu ne, kuma Nafi'un shi ne kaɗai ɗa a wajen Mahaifiyar sa. Bayan ya kaita ya sauke ta tare da bata makullin gidan, sai ya tafi asibitin

Ita kuma ta shige ciki abun ta, a falo ta samu waje ta zauna tana zare gyalenta ta ajiye. Tsarin gidan take bi da kallo tunda yau ne zuwanta na farko, lokacin da suka kawo Firdausi a babban gidansu aka soma ajiye ta before ya gama ginin sa, babu laifi gidan ya ɗan birge ta, but sai yatsina fuska take yi tana tunanin, "idan ita ce baza ta iya zama a ciki ba, gida kamar kurkuku wai ace a nan zaka ƙare rayuwarka." Sai ta sake taɓe baki tana tashi tsaye ta nufi ƙofofin da ta gani, ta soma buɗewa tana leƙawa, da kichen ne da Toilet, sai kuma ɗakuna biyu masu kallon juna, ɗaya na Nafi'u ɗaya na Firdausi. Ɗakin Firdausin ta shige da akwatin ta, ta shiga toilet ta ɗaura alwalan magriba da aka kira, kasancewar bata yi sallan la'asar ba sai ta haɗa

Tana cikin sallan ne suka dawo gidan. Daga Firdausi sai Nafi'u tunda sai da ya wuce da Ummansa gida sannan suka nufi nasu gidan. Kasancewar ya faɗa ma Umman nashi, "akwai ƙanwarta ta zo." Shiyasa tace, "to ya sauke ta a gida kawai."

Jikin Firdausi da sauƙi sosai, dama ciki ne take dashi kusan watanni biyar kenan, kuma tunda ya fara girma sai ciwo ya sako ta a gaba, ko lokacin da yake ƙarami bata sha wahala irin yanzu ba, sosai take ciwo shi ne har aka dangana ga asibiti, kuma ta tashi hankalin ta tana kukan, "tana son ganin ƴan uwanta ko Innarsu." Gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake musamman yanda suka yi watsi da ita kusan seven months basu zo sun ganta ba

Dalilin da yasa Nafi'u ya kira Baba ya sanar mishi kenan. Kuma shi kansa bai yi tunanin zasu iya zuwa ba tunda ya san Innarsu ba ta son shi, amma kuma sai ga shi Arab ta zo

Gaskiya sun yi murnan ganin ta sosai. Musamman sanda Firdausi ta shiga ɗakinta ta hange ta, ai sai ta washe baki tsaban farin ciki, bata taɓa yarda da gaske Nafi'u yake mata ba wlh, domin ta san ko kowa zai zo Arab baza ta zo ba, in fact ma Inna baza ta barta ba tunda ta fi ƙaunar Arab, baza ta so ta matsa a kusa da ita ba, bare ta san halin Arab sai abun da taga dama take yi, sai ga shi kuma ta ganta a ɗakinta. Da sauri ta nufe ta tana rungume ta tare da cewa, "Auta ke ce? Ashe za ki zo?" Sai ga hawaye sharr sun soma bin kuncinta

Ita kuma Arab kallonta kawai take yi saboda yanda ta sauya mata, ta zama wata ƙatuwar Mata, ko don tana da ciki ne oho. Sai kawai ta ɗage kafaɗa alamun hakan bai dame ta ba, dariya tayi tace, "Aunty da kuka kuma? Kai! kai! Kar kiyi abun kunya a gabar ƙanwar ki mana."

Yanda tayi maganar ne dole Firdausi tayi dariya tana kai hannunta ta ɗan buge ta, sai tace, "kin raina ni ko?"

Murmushi ita kuma tayi tace, "a'a ina girmama ki, ke ce fa babbar Yaya, ina Ni ina raina ki?"

Still dariyan Firdausi tayi sai tace, "idan na biye miki ko; za ki mayar dani mahaukaciya, ya su Inna da kowa da kowa? Ina su Ummu meyasa baku zo tare ba?"

"Hhmm ke ma kin san Inna baza ta barmu gaba ɗaya mu taho ba, da ya ya ta bar Ni nima? Sai dai sun ce suna gaishe ki sosai, su Aunty Ummu ma zasu taho ranan Asabar sai mu koma tare."

Sai Firdausin ta washe baki cikin farin ciki tace, "kai naji daɗi, Allah ya kaimu rai da lafiya, gaskiya kin faranta min da zuwan nan naki, wlh duk naji babu daɗi yanda ku ka manta dani, sai nayi tunanin ko Inna ne ta hana ku zuwa tunda ko a waya ba kwa nema na."

"Ayya ba haka bane Aunty, kin san makaranta ga kuma sana'a, so bamu da lokacin kanmu."

"Shi ne kuma har da lokacin ƴar uwanku baku dashi? Kar ki manta Ni fa ƴar uwanku ce." Tayi maganar cikin rauni har da hawaye suke son zubo mata

Sai dai sallaman Nafi'u ne ya tsayar da Arab yin magana. Ya shigo ciki bayan sun amsa mishi, hannunsa da ledoji har guda uku yace, "to Autanmu ga abinci na siyo miki tunda me yi ba lafiya, ke kuma daga baƙunta baza mu wahalar da ke ba."

Dariya tayi tace, "Ayya Yayanmu, wlh da baka siyo ba ka bar Ni inyi mana, ai ba wani abu bane don na shiga kichen."

"A'a, gwara dai ki huta tunda yanzu kika zo." Sai ya kalli Firdausi yace, "kin yi sallah ne?"

Girgiza mishi kai tayi da faɗin, "a'a."

"To tashi kiyi mana sai ki ci abincin ke ma, kin san abun da likita yace ai. Bari inje falo idan kun gama sai ku same Ni."

"To." Firdausi ta amsa mishi

Sannan ya fice a ɗakin

Kallonta Firdausi tayi tace, "buɗe ledan ki duba abun da ke ciki, bari in Yi sallah."

"Ok." Arab ta furta tana ajiye wayan da ke hannunta, sannan ta jawo ledojin ta soma dubawa. Takeaways ne a ɗaya, sai kuma fruits sannan ledan tsire. Tana ganin tsiren ta ciro ta hau ci tana kaɗa kanta

Firdausi da ta fito ta ganta a haka sai tayi dariya tace, "har yanzu kina nan da halin ki Auta, baza ki bar kwaɗayi ba."

"To me ya fi hakan daɗi? Kowa fa na son daɗi Aunty sai dai idan bai samu ba, Ni duk abun da zai sa Ni jindaɗi a rayuwata shi nake yi bazan ƙwari kaina ba."

Murmushi kawai tayi mata sai ta saka Hijab ta tayar da sallah

Lokacin wayan Arab tayi ƙara, ganin sunan Besty ɗinta sai ta ɗauka tana cewa, "Ya ne Besty?"

"Bazan amsa ba tunda kika yi tafiya ba ki sanar dani ba, na zo gida Zahra take sanar dani kina Kaduna."

Dariya tayi tace, "oh! Sorry my Besty, wlh I have not forgotten you, right now I want to call you."

Yace, "ai kin kyauta, kin san ba na fushi da ke, to ya Kadunan? Ya su Aunty Firdausin?"

"Lafiya ƙalau. Hope kaima kana lafiya?"

"Uhmm ina fa lafiya kin tafi kin bar Ni cikin maraichi, bayan kin san yau akwai alƙawari a tsakanin mu."

Dariya tayi sosai tana siɗe hannunta, sai ta sauke ledan tsiren daga jikinta ta ajiye ma Firdausi, still tana ci gaba da wayan da cewa, "i Know. Amma ka san bazan manta da kai ba, Let me be with you when I return."

"Fine. Ya na iya haka nan zan jira, but zan yi kewar ki sosai wlh, ba ki ga yanda ake tambayar ki bane yau a wajen sana'a, kowa yana tambayana ina kika je? Ni kuma sai na kira wayanki maybe network problem did not enter, after na je gidan ku ake faɗa min kin tafi KD."

Taɓe baki tayi tace, "you just delete them and I don't have time for them. Ya labari?"

Dariya yayi yace, "ok Gimbiyyar Mata, girman ki ne ai. But labari ke za ki bani, You have not spoken to Alhaji Bashir yet?"

Yatsina fuska tayi sabida kallon da Firdausi take mata. Sai ta kawar da kanta tana kwanciya a kan gadon tare da cewa, "I spoke to him on WhatsApp, but I have not been able to go online again."

"Haba Besty kina wasa da Mutumin nan ko? Zuwa yanzu yakamata ace har kun gama fahimtar juna, na san ki ba kya wasa da irin Alhazawan nan, amma da alamu har yanzu ba ki san ko shi waye bane."

Murmushi tayi me sauti sai tace, "ka bari zamu yi maganar daga baya, yanzu ga Tariq nan yana kira na zan amsa call."

"Ok when you're done I'll call you."

Daga haka suka yi sallama ya kashe wayan

"Kar ki ɗauki wayan nan please ki bari ki gama." Firdausi tayi maganar tana kallonta

Itama sai ta ɗago tana kallonta. Sai kuma ta ɗage kafaɗa before tace, "ok." Ajiye wayan tayi ta sauko ƙasan inda Firdausi ke zaune tana cin abinci. Itama ta buɗe ɗaya takeaway ɗin ta sanya Robber spoon ɗin tana ci

Sai da Firdausi ta ɗago ta kalle ta sannan ta kawar da kanta tana girgiza shi, ko kaɗan halayen ƙanninta ba sa mata daɗi, tana shiga ƙunci da baƙin ciki duk sanda ta tuna yanda suke rayuwarsu kuma bata da halin hana su, musamman ma Arab wacce take tsananin tausaya mata kasancewarta ƙaramar yarinya amma ta fi su hatsabibanci, ba ta jin magana ko kaɗan, yanzu tana buɗe baki don tayi mata nasiha zata iya jawowa kanta, sai ma tace mata, "zata koma gida tunda ita ba wa'azi ta zo tayi mata ba." Shiyasa tayi shiru ta ƙyale ta. Bayan ta gama cin abincin sai ta miƙe da gudan takeaway ɗin, sai drinks guda biyu tace, "idan kin gama muna falo, bari in kaiwa Nafi'u abincin shima ya ci."

      

"Ok." Tace mata kawai tana ci gaba da cin abincinta. Bayan fitan ta ne ta ɗauki wayan taga Tariq yayi mata three missed calls. Sai bata bi kiran ba ta miƙe ta shiga toilet. Bakinta ta kuskure sannan ta fito ta ɗauki wayanta zata fice sai kuma kiran Tariq ɗin ya sake shigowa. Zama tayi a bakin gadon tana amsa call ɗin. Sallama yayi mata ta amsa

"Baby ina kika shige ne ina ta kiran wayan ki but ba ki yi peacking ba?"

Ɗan muskuta zamanta tayi tana kwanciya sosai a kan gadon. A hankali cikin yanga tace, "ina cin abinci ne."

"Oh. Har kin sa na ji sanyi a raina, nayi tunanin laifi nayi ko kuma babu lafiya. Yau ban ganki a wajen suyan wara ba? Allah yasa lafiya?"

"Ƙalau. I just Traveling."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!." Ya furta cikin wani irin yanayi da ya faɗarwa da Arab da gaba

Da sauri ta furta, "lafiya dai?"

Sai da ya ɗan ja numfashi before yace, "ina fa lafiya, shikenan Baby bazan samu ganin ki ba kin yi tafiya?"

"Wai saboda haka ne kake jan wannan salatin?"

"Eh mana. Ai babu abun da zai ɗaga min hankali a yanzu sama da rashin ki a tare da Ni, wlh ba ki san yanda na kwana da tunaninki bane jiya, na ƙosa yau tayi in zo in ga kyakykyawar fuskarki but sai ga shi na rasa ki, kuma kina faɗa min kin yi tafiya, yanzu shikenan sai yaushe zan ganki?"

Murmushinta me kyau tayi kafin tace, "kana da abin dariya gaskiya, but I will be back soon, only four days."

"Ki ce zan mutu kafin lokacin nan, Please kar kiyi min wannan horon na rashin ganinki, zan iya mutuwa ba ki san yanda na kamu da soyayyar ki ba ko? Please Aisha help me to give me a chance to show you how much I love you, ki bani dama don Allah in aure ki wlh I really love you."

"Meyasa kake min maganar aure yanzu daga haɗuwar mu jiya? Ko nace maka zan yi aure yanzu ne?"

"A'a, amma Baby ki fahimce Ni, ƙaunar da nake miki ne bazan iya jure tsawon lokaci ba na tare da ke ba, zan so ace Ni na mallake ki a matsayin Mata..."

Katse shi tayi da faɗin, "kaga Malam Ni babu aure a gabana a yanzu, a tunaninka daga haɗuwar mu sai kawai in ba ka damar da zaka iya aure na? Duka-duka nawa nake da zan yi aure yanzu? Don haka ka dena min maganar aure yanzu sabida babu shi a raina kuma ban shirya yi yanzu ba, now ina gaɓar yarintana ban shirya tsufa da wuri ba, and sannan ba na son takura gaskiya idan ka san wannan maganar zaka riƙa min kar ka sake kira na." Sai ta ja tsaki ta kashe kiran. Ai kuwa ko ajiye wayan bata yi ba ya sake kira, kamar baza ta ɗauka ba sai kuma ta ɗaga

Cikin sauri da tashin hankali da ya nuna a kan muryansa yake magana, "don Allah kiyi haƙuri, ban san haka zai ɓata miki rai ba, but I will not do it again."

Yanda ta ji muryansa kamar zai yi kuka don har idanuwansa sun soma kaɗawa tare da ruwan hawaye, duk ya susuce yana ta roƙon ta, shiyasa tace, "is ok ya wuce."

Ajiyan zuciya ya sauke me ƙarfi tare da furta, "thanks Baby, kiyi haƙuri don Allah, Ina sonki."

"Ok. Ni zan kwanta, bye." Bata jira cewarsa ba ta katse kiran

Sai ya bi wayan da kallo zuciyarsa babu daɗi, haƙiƙa yana tsananin ƙaunar Arab a zuciyarsa, tsaban ƙaunar da yake mata ya rasa inda ke mishi daɗi a yanzu, bai san haka take ba sai a jiya da ya soma mu'amala da ita, yayinda tarin ƙaunar ta me tsanani ya ninku a zuciyarsa wanda yana jin bazai taɓa iya rayuwa ba tare da ita ba, dole ko ta halin ƙa-ƙa ne ya mallake ta ta zama tashi ta har abada. Numfashi ya sauke yana ajiye wayan a saman kujeran da yake zaune, a hankali ya furta, "na zama mahaukaci a kan ƙaunar ki A'isha, bazan taɓa samun sukuni ba har sai kin zama mallaki na, ina sonki da yawa!" Sai ya kama setting ƙirjin sa yana shafawa a hankali tare da lumshe idanuwansa.





              Ita kuwa tana kwance bata tashi a wurin ba sai ga Firdausi ta shigo

Tace mata, "wai kina nan ba ki yi barci ba? I thought kin Yi barci tunda na ji ki shiru."

"No ina nan ban kwanta ba."

"Ok to ki kulle ƙofan, Ni zan wuce ɗakin Nafi'u sai in kwanta a can, sai da safe."

"To." Kaɗai ta furta tana

Please Login or Register in order to submit comment