Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar wanka tayi dasu. Kallon kanta tayi a madubi, ita kanta ta yaba da Kyan da tayi. Ta fito a Queen Basma.

A can kuwa cikin gidan hankalin kowa ya tashi ba'a ga Basma ba, an duba duk inda ya kama ta amma ba'a ganta ba, gaba d'aya gidan ya hautsine cikin tashin hankali, a cikin wannan yanayi ne Basma ta fito cikin taku na k'asaita, yau Queen Basma ta fito a sunanta, ai sai kallo ya koma gunta cike suke da mamakin ganinta a rinin wannan shiga, nan take suka fara murna, Basma tayi kyau sosai, masu d'aukan hoto suka fara d'aukanta, Ammi ce ta tawo da gudu ta rungemata tace
"Basma ina kika shige ne haka?" dariya tayi tace ina d'akina, nayi bankwana da Yaya Aryan shine barci ya d'aukeni, yanzu na kimsha nace bari na fito a cigaba da shagalin Biki dani" ai baki bud'e Ammi ta bita da kallo tana mamakinta tare da tausayinta.

*Rahma Ce*
[8/7, 8:33 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *15.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Da dare*

An shirya kayataccen Dinner a katon hol mai d'aukan mutane dubu, manyan mutane sun halarci wannan Dinner, harda wasu yan k'asashen waje sun halarta, Amare da Angwaye sunsha kyau, ko wanne zaune yake da Amaryansa, Safeena na zaune cikin mutane ranta ya gama b'aci, zuciyarta yana mata zafi dan tsananin kishi, tunani ta shiga yi, ita fa Auren sirri aka mata sam ba'ayi irin wannan shagalin ba, haushi ya k'ara cikata, amma tasan matakin da zata d'auka akan Shureym, dan taga yana ta rawan jiki akan Basma.

Kowa ka ganshi a wannan lokacin yana cikin farin ciki, amma banda Basma da take cikin damuwa na rashin ganin Aryan agun, dan batasan yayi tafiya ba, sai kuma Safeena da take jin haushi akan mijinta. Anyi taro lafiya an watse lafiya, cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

*Washe gari*
An kai ko wace Amarya gidan Mijinta da misalin larfe hud'u na yamma, Deeja an kawota gidan president a side d'in mijinta, haka Meena ma an ajeta acikin gidan president, part d'insu na gefen nasu Yaya Ahmad, Leema kuma an wuce da ita Kaduna zuwa gidan Jamal da Dady ya siya masa, sai Yaya Adam an wuce da matarsa Munayah, an kaita part d'inta dake cikin gidan Sarki, Basma ita ce tayi saura a gida, itama part d'inta yana gidan Sarki kusa dana Yaya Adam, kasantuwar Yaya Shureym bai gama aikin da suka d'aukeshi ba na shekara biyu, yasa zasu wuce America, su cikasa sauran shekara d'ayan daya rage. Sauran baki kuma suna nan basu soma tafiya ba.

Sai Washe gari ko wani Ango ya shiga d'akin matansa, suka fud'e faifan sabon rayuwa cike da So da K'auna.

Da safe su Basma suka wuce airport, da kyar aka raba Basma da jikin Ammi, tasha kuka kaman ranta zai fita, Shureym kuwa sai wani kamata yake yana lallashi, sun shiga jirgi Basma na d'agawa iyayenta hannu, ji take kamar in ta tafi bazata dawo ba, haka suka zauna wuri guda, sannan aka rufe k'ofar jirgi, ana rufewa Shureym ya tashi kusa da ita ya kowa gefen hagunsa, kusa da Safeena ya zauna, ta cika ta batse dan haushi, Basma ta bishi da kallo ganin ya zauna kusa da wata mace cike da mamaki, bata iya cewa komai ba, Safeena ce da taga Basma na kallonsu, sai tayi saurin sakin fusha ta juyo fuskanta tana kallon Shureym, sai ta had'a bakinsu guri guda, ai da sauri Basma ta kauda kai, zuciyarta na dukan uku-uku, bakinta na fad'an
"Inalillahi wa inna ilaihir raji'un" kwantar da bayanta tayi jikin kujera, ta runtse ido, tsananin radad'i zuciyarta yake mata, bawai kishin Yaya Shureym taji ba, tsabar bak'in ciki da irin tsanar hayayyansa take, a tunaninta k'aruwansa ce, Safeena tana ganin Basma ta kauda kai, sai ta janye jikinta ta fara magana k'asa-k'asa tace

"Baby wlh ka b'ata min rai cikin kwanakin nan, naga sai wani rawar jiki kake akan wancen yar iskan Yarinya, to wlh ka sani bazan tab'a raba kwana da ita ba, alkwari ka d'aukan min cewa kai mijin mace d'aya ce, dan haka kai nawa ne ni kad'ai, tunda kace had'in zumunci ne shiyasa na yarda da auren, dan haka da kanta zata gaji da zaman gidanka, harta nima saki tayi gaba"

Gaban Shureym ne ya fad'i, hankalinsa ya tashi, amma sai ya dake ya wayince yace

"Love ke kad'ai ce a guna, me zanyi da Basma, had'in zumunci akai mana dan bana sonta"

Cike da murmushi tace
"yauwa Babyna, kamin alkwara ba raba kwana da ita" murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace

"na miki alkawari, ai bana son b'acin ran ki, ko me kike so zan miki domin in saki farin ciki" Safeena farin ciki ya rufeta, take nan ta manta da b'acin rai data shiga.

Basma kuwa kuka ta shiga yi mara sauti, a haka har barci ya kwasheta.

*America*
Bayan sun kai, mota biyu ke jiransu, d'aya wanda zai d'auki kayan su, d'aya kuma wanda zasu shiga, Basma jikinta a mace ta bud'e k'ofan bayan mota zata shiga, sai Yaya Shureym ya daka mata tsawa yace
"Karki kuskura ki shiga nan, ki shiga gaba ki zauna da driver, ko baki ga ina tare da matata bace?" cikin tsoro Basma ta bar jikin mota cike da tsiwa tace
"Matarka ko Karuwa?" Ai bata rufe baki ba ya tawo da sauri ya wanketa da mari, a razane ta dafe kuncinta tace
"Ni ka mara akan wannan yar iskan, to Allah ya isa mugu fasik'i kawai" tana gama fad'an haka tabar wurin da gudu, ta shige gaban motan daya d'auki kayansu ta zauna, driver ya tukasu suka wuce. Cike da k'unar rai Yaya Shureym ya girgiza kai yayi kwafa, iya ka k'uluwa Safeena tayi, amma ta share suka shiga mota  tana sake-saken irin matakin da zata d'auka akan Basma, Lallai dole saita fahimtar da ita cewa ita matar Shureym ce.

Suna isa gidan, ta shiga babban falon gidan Driver ya shigo musu da kayansu, d'akuna uku ne a cikin falon, ko wanne da kaya aciki wanda President yasa aka sanya musu komai na buk'ata aciki, Basma ta zauna akan kushim tana jiran su Shureym su shigo, koda suka shigo sai suka zauna suma, Yaya Shureym ya kira wani kuku, sai gashi da gudu yazo, da yake gidan ai'nahi anan Shureym yake zama, ya Umarcesa daya kawo musu ruwa, da sauri yaje ya kawo musu ya dire musu goran ruwa biyu da cup, yaje zai aje goran ruwa a gaban Basma, sai Safeena ta dakatar dashi cikin turanci tace
"kai zonan" jikinsa na b'ari ya isa gurin ya risina, tace

"daga yau Ni zaka rik'awa aiki amma banda wacen 'yar iskan, domin Mijina ni kad'ai yake aure" tana kaiwa nan tayi shuru, jiki na rawa Kuku ya amsa mata yabar gurin.

Cikin ko in kula Basma ta mik'e tace
"Yaya Shureym ina ne d'aki na?" Hararanta yayi yace

"ban sani ba mara kunyar banza, wlh nan ba Nigeria bane da zaki min iskanci na d'auka, koda kika ga ina lallab'a ki, dama ina yi ne dan ayi auren, saboda kar in b'atawa Iyayena rai, kuma ki sani bana son ki, biyayya ga Iyayena yasa na aureki"

Gaban Basma ne ya shiga bugawa da sauri, saboda tashin hankali, ya cigaba da cewa
"kinga wannan sunanta Safeena, itace zab'ina, kuma munyi aure da ita wata guda daya wuce cikin sirri, ba tare da kowa ya sani ba, daga ni sai Mami na data goya min baya, dan haka in kina son zaman lafiya a gidan nan, to dole sai kin bita sauda k'afa, inba haka ba wlh na lahira saiya fiki jin dad'i"

Basma durkushewa tayi a gurin, saboda k'afafunta bazai iya d'aukanta ba, ta shiga rera kuka wiwi, sai ya kwashe da dariya yace
"wawuya nasan kin d'auka son ki nake ko, tashi dalla ki bani wuri, ki wuce d'akinki shine na gefen hagu, na tsakiya kuma nawa ne, na gefen dama na Safeena ce, kuma na haramta miki shiga d'akina" yana kaiwa nan ya mik'e ya kama hannun Safeena suka wuce d'aki.

Basma cikin tashin hankali taja trolley kayanta, ta shiga d'akin daya gaya mata, katon d'akine mai d'auke da katon gado, sai daga gefe an jera kujeru set, sai bayi da kicin a ciki, kalan d'akin da kayan ciki purple da ash color ne, rufe d'akin tayi da key, ta shiga wanka, kanta ta sanyawa ruwa sosai, saboda zafin da yake mata, tayi kuka kamar zata shid'e, daga bisani tayi wanka ta d'auro alwala ta fito, kaya ta sanya mara nauyi, ta sanya hijab ta tada sallah, sai da ta rama duk Sallolin da ake binta kana tayi Addu'a, ta mik'e ta shiga cikin d'in d'akinta, komai data ke buk'ata akwai aciki, dan akwai k'aramin store a ciki, ruwan tea ta dafa, ta zo ta diba cin-cin d'in data tawo dashi a plet, ta zauna taci kana ta d'aura da danbun Namam kaza, bayan ta gama sai ta kwanta akan doguwar kujera, ta runtsa idonta ta shiga tunanin wani irin rayuwa zatayi yanzu, kuma wani mataki zata d'auka akan Yaya Shureym da Safeena wacce yake ik'ira rin matarsa ce, hawaye ne ya sauka a kuncinta, a fili tace cikin kuka
"babu wanda ya jamin wannan rayuwa sai ku Abbana, dan haka ba wani matakin da zan d'auka ma, domin ko me ya sameni kune sila"

Ta goge hawayenta, ta d'auko wayanta ta shiga kiran Momy, ta sanar da ita sun sauka lafiya, nan sukayi sallama, ta kira President ta sanar masa da sun sauka lafiya shima, haka kuma ta kiranl Ammi ta sanar mata da sun sauka lafiya itama, bayan ta gama wayan, sai ta tuna da Umma, sai tayi murmushi, itama ta kira ta suka gaisa, Umma tayi mata nasiha sosai akan biyayyan aure, kana suka yi sallama, saita kashe wayen gaba d'aya ta gyara kwanciya, bata dad'e ba barci ya d'auketa.

*A Nigeria*
Mutanan Biki duk sun watse sai dai-dai da suka rage, ta b'angaren Amare kuwa sunata cin Amarci hankalin su kwance, kowa yana cikin farin ciki. Ta b'angaren Yaya Jalal ya samu Leema ta yanda bai yi tsammani ba, domin gaskiya tasha gyara wajensu Momy, duk da dai bata isa ta maida mudurcinta ba, amma dai ya gamsu sosai da ita, Leema ta kasance cikin murna da yanda Jalal ya saki jiki da ita, tamkar babu wani abin da ya faru a baya.

*A K'asar Monaco*
Yaya Aryan ya cigaba da rayuwa shi kad'ai, da Umma kawai yake waya su gaida, da sun gama saiya kashe wayan. Kullun soyayyan Basma k'aruwa yake a zuciyansa, yanzu da baya ganinta yafi shiga tashin hankali da damuwa, ya k'ara ramewa sosai, burinsa yanzu bai wuce Basma ta kwantar da hankalinta ba, tayi rayuwan Aure cikin farin ciki da annatsuwa. Ya duk'ufa sosai wajen karatunsa, yana k'ok'arin kafa sabon rayuwa.

*Bayan mako guda*
*A America*
Basma tunda ta kulle kanta a d'aki, bata kuma bud'ewa ba har tsawon mako guda, komai a cikin d'akinta take yi, hatta girki da kanta take yi, taci ta wanke kayan data b'ata, tun yin aikin na bata wuya kasantuwar bata saba yi ba, har ta fara sabawa, Allah yasa ta iya girki, domin Momy ta koyawa Basma girki dan gaba zai mata amfani, kamar yanda yanzu ya soma mata amfani.

Yaya Shureym suna falo suna hira, Safeena tayi pillow da cinyansa, hankalinsa na kan k'ofar d'akin Basma, hira take mishi amma sam baya tare da ita, sha'awan Basma na d'awainiya dashi, sannan ya fara damuwa da rashin ganinta da baiyi ba, tun ran da suka zo, bai sake tozali da ita ba, Safeena ganin baya tare da ita ya barta tana ta surutu, sai ta d'ago kai tana kallon direction d'in da yake kallo, gabanta ne ya fad'i cikin jin haushi tace

"Baby tunanin me kake yi haka? Ko ka fara sonta ne?" Firgigit ya farka, cikin inda-inda yace
"ba komai, me zanyi da Basma, Allah ya kyauta" cikin fushi tace
"k'arya kake yi, d'akinta fa kake kallo, kana ce min ba komai" murmushin ta kaici yayi domin ya soma gajiya da yawan k'orafinta, kawai ba yanda zaiyi da ita saboda yana sonta, kuma baya son b'acin ranta yace

"kedai kin cika kishi, kawai ina tunanin yarinyar nan ne, akan tunda muka zo ban ganta ba, ina tsoron kar wani abu ya sameta, domin in wani abu ya sameta wlh zamu shiga cikin matsala, kinsan *YAR SHUGABA* ce, gwara na rika duba lafiyan ta domin president ya bani amanarta, ko ba komai kuma 'Yar Uwata ce"

Safeena cikin nuna ko in kula tace
"wannan kaita shafa" tana gama fad'an haka ta mik'e ta shiga d'aki tana jan tsaki, binta yayi da kallo yace a fili
"Safeena sarkin kishi" sai ya mik'e ya nufa d'akin Basma...

*Rahma Ce*
[8/7, 8:34 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *16.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_

Yana isa d'akin ya shiga bugawa, kwance take bisa gadonta tana kallon tv, koda taji bugun k'ofan, ta d'auki kusan minti uku kafin ta mik'e ta nufi k'ofar ta bud'e, tsaye ta ganshi yana k'are mata kallo, miyau ya had'iye da k'arfi, gaba d'aya hankalinsa ya tashi da ganin Basma cikin k'ananun kaya, hararansa tayi cikin tsiwa tace

"Malam lafiya ko da matsala ne"

guntun murmushi yayi bai ce komai ba, sai yabi gefenta ya kutsa kai cikin d'akin, zama yayi kan kujeran zaman Mutum d'aya, ya shiga k'arewa d'akin kallo yana shakar kamshin d'akin, wanda ya saukar masa da kasala had'e da tsananin sha'awar Basma, ita kuma tura k'ofan tayi ta koma cikin d'akin ta zauna gefen gadonta ta cigaba da kallon tv, sun kai minti biyar a haka ba tare da wani yace wani abu ba, Yaya Shureym ne ya katse shurun yace

"Basma meyasa bakya fitowa falo ki zauna?"

Cikin nuna ko in kula tayi banza dashi, yace
"magana nake kinyi banza dani" Cikin yatsina fuska tace

"naga cewa wannan ba matsalan ka bane, ka je ka cigaba da zama da karuwanka, don ni ban yarda aure ku kai ba, kyamarka nake ma, da zaka taimaka ka tashi ka fita da ka kyauta min"

"Iya b'acin rai ransa ya baci, mik'ewa yayi da sauri zai isa inda ta zauna, ai da sauri itama ta mik'e tana ja da baya harta isa jikin bango, kankame jikinta tayi ta runtse ido domin yanda taga ransa ya b'aci ta sadakar zai duketa, gabda ita ya tsaya wanda hartana jin hucinsa, hannunta ya shiga b'amb'arewa a jikinta, a razane ta bud'e ido tana kallonsa, ba tayi aune ba ya rungumeta da k'arfi ya matseta a jikinshi, tirjiya ta shiga yi tana k'ok'arin kwatar kanta, ganin ya rik'eta gam yak'i sakinta, saita gantsara masa cizo a damtsan hannusa, da sauri ya saketa yana yarfe hannu, saita maza ta matsa a gun, yana jiyowa ya nima k'ara kamota, da sauri ta ruga, guje-guje suka fara a cikin d'akin, yana k'ok'arin kamata tana kaucewa.

Safeena shiganta d'aki da tayi, tana tsammanin Shureym zai biyo bayan ta, sai taji shuru, ganin haka yasa ta lek'a falo sai taga wayam baya gun data barshi, cike da masifa ta fito ta nufi d'akin Basma, tana bud'e k'ofa sai ta cimmusu suna wannan wasan guje-guje, ai sakin baki tayi tana kallonsu, shiga ciki tayi rai b'ace, Shureym yana ganinta yayi sauri ya tsaya yana sosa k'eya, mugun kallo Safeena tabi shi dashi bata ce masa uffan ba, sai nuna masa hanyar waje tayi alaman ya fita, sum-sum ya fita yana murmushi k'asa-k'asa, yana fita ta gyara tsayuwa tana kallon Basma tace

"A hir d'inki da Mijina domin ba sa'anki bane, in kuma ke mayya ce to Mijina yafin k'arfinki, ki shiga taitayinki domin wlh inna kuma ganin haka zan d'auki tsastsauran mataki mafi muni a gareki" tsaki Basma tayi tace cikin fad'a

"ai ko wlh da kinga yanda zanyi k'asa-k'asa dake, ke d'in banza ke wacece da zaki zo ki nima shiga tsakanina da Mijina kuma d'an Uwana, kefa ba kowa bace face karuwa mara lasisi mara mutunci, ki gaugauta fita sabgata domin had'uwata dake bazai yi kyauta, kibar ganin ina miki shuru-shuru, jaka kawai"

Ai tuni Safeena ta cika ta b'atse, magananun Basma sun tunzurata, bata san lokacin da tayi kukan kura ba ta nufi Basma gadan-dagan, Basma na ganin tayo kanta sai ta shige bayi da gudu tare da sanya key, tana maida numfashi, iya tsoro ta tsorata da Safeena, dan ta girmeta kuma ta fita girman jiki, tace a fili

"ko banza nasha dakyar muguwa kawai" Safeena tana ganin ta shige bayi sai tayi kwafa, ta fita da sauri.

Ta tada Shureym a d'akinsa, ta shiga surfa masa masifa shi dai uffan bai ce ba, da ya gaji da jin haya niyarta sai ya shige baya danyin wanka ya barta tsaye baki na kumfa, a ransa yace

"Safeena akwai masifa, ta dage ta hakikance akan abin da yake halal d'ina, gaskiya bazan d'auki wannan sakarcin ba, domin ko ban son Basma ai ina feeling d'inta, balle ma ina sonta kawai kauda kai nake ina miki biyayya, saboda ina tsananin sonki, amma nasan hukuncin da zan d"auka"

Basma sai da ta tabbatar ta fita a d'akin saita fito da sauri ta rufe k'ofarta, ta haye gado tana kwasar dariya, ko ba komai ranta ya mata dad'i tunda ta bak'anta ran Safeena, Jakarta ta jawo na kayan gurinta,  lollypop ta d'auko, ta bud'e sweet ta sanya a baki tare da lumshe ido dan dad'in ya fara ratsa ta, nan take ta tuna da sunanta Queen Basma 'yar rawa, tashi tayi ta kunna radio tare da sakin sauti, ta shiga cashewa son ranta tare da tuno rayuwanta na makaranta cike da nishad'i.

Yaya Shureym ya fito zai fita, jin wakar da Basma ta sanya yasa shi girgiza kai, a fili ya furta
"Basma dangin k'uruciya" sai ya fice, Safeena ma fitowa tayi cikin shirin fita tabi bayansa da sauri ta taddashi harya kunna mota zai wuce, da sauri ta cimmasa ta bud'e gaba kusa dashi ta zauna, tana mai kallonsa cike da shagwab'a tace
"haba baby shine zaka tafi ka barni" murmushi yayi yace
"ai naga fushi kike dani shiyasa nayi shirin fita in je in wayata kona sarara" kamo hannunsa tayi tace
"sorry Baby, d'azu raina ne ya b'aci bazan sake ba" gyad'a kai kawai yayi alaman ya gamsu, sai suka fice daga gidan.

*Washe gari*
Shureym ya tashi da sassafe yayi shirin office, haka ma Safeena tayi shirin fita, nan suka had'u suka fice a gidan.

Basma tana jin k'aran fitan motansu, saita bud'e k'ofa ta fito, d'akin Shureym ta shiga ta gama kallon komai, yanda akayi decoration d'akin yayi mata kyau, kalan fentin coffee brown da milk color, haka ma kalan furniture d'in, d'akinsa ba kitchen sai dai akwai toilet babba wanda yafi nasu Basma.

D'akin Safeena ma yanayin d'akin Basma ne, sai dai itama ba Kitchen sai toilet kamar na Basma, kalan fentin d'akin ash da pink ne hakama furniture d'inta, fitowa tayi ta shiga cikin babban kitchen na falo, nan ma ya tsaru sosai, kuku guda biyu ta gani a ciki, cikin ladabi suka gaisheta tare ta tambayan abinda take buk'ata, da murmushi tace
"bata buk'atar komai" shiga tayi store d'in ta shiga diban abinda ba tada shi ta kai kitchen d'akinta, kana ta fice farfajiyan gidan, baya ta nufa inda shukoki na furanni suke, ta tsak'i iskan wurin sai taji dad'i a ranta, nan take ta tuno da wurin shak'atawan da suke zuwa ita da Yaya Aryan, idonta ya ciko da kwalla, zama tayi kan wani kujera na katako mai lilo, runtse idonta tayi ta shiga duniyan tunanin Aryan, ta kai kusan rabin awa agun kana ta bud'e ido, ta shiga rera kuka, istigfari tayi ta nima yafiyan Allah akan tunanin da tayi na Aryan Alhalin tanada auren wani akanta, tashi tayi ta nufi d'akinta ta fad'a bayi dan watsa ruwa, ko jikinta zai mata dad'i.

Yaya Shureym yana office amma ya kasa aiwatar da komai, gaba d'aya tunanin Basma ya cika masa kai, burinsa bai wuce ya samu Basma ba, agogan hannunsa ya duba yaga k'arfe 11am na safe, mik'ewa yayi da sauri ya d'auki wayansa, jakansa da key d'in mota ya wuce gida.

Basma ta fito wanka d'aure da towel a k'irjinta, tana zaune gefen gado cike da damuwa a ranta, tunanin iyayenta da family d'inta takeyi, tunawa tayi da tun ranar da suka sauka ta kashe wayarta bata kuma waiwayan sa ba, murmushi ne ya sub'uce mata data tuna dasu Meena, tunanin ya sukaci amarci ne ya fad'o mata, tace a fili

"guys nayi missing d'inku sosai, anjima zan bud'e waya muyi chart"

Tana gama fad'an haka taje kusa da dressing mirror ta soma Shafa mai, jin motsin k'ofa tayi sai ta juya da sauri, dan shaf ta manta bata rufe ba d'azun, Yaya Shureym ne tsaye yana jefo mata mayen kallo, gabanta ne ya shiga fad'uwa sam bataji k'ugin motansa ba, takowa ya fara yi yana mata wani shu'umin murmushi, Jada baya ta shiga yi, k'ok'arin isa Waldrop d'inta tayi da nufin d'auko hijabi dan ta sanya, da sassarfa ya cimmata a gurin, jikinta ne ya soma b'ari, hannu ya kai saman k'irjinta inda ta d'aura towel d'in, ta rik'e gam ta shiga kuka tana cewa

"meye haka Yaya Shureym dan Allan ka fita"

Murmushi kawai yayi ya sanya k'arfinsa ya fisge towel d'in, da sauri ta zukunna k'asa ta shiga kuka da k'arfi, d'aukarta yayi ya jefata kan gado, zanin gadon ta jawo ta rufe jikinta dashi, cire kayansa ya shiga yi, vest da gajeran wandon kawai ya rage a jikinsa, sai ya hau kan gadon, Basma ganin haka ta kuma rushewa da kuka, bai hanashi fasa k'udirinsa ba, zanin gadon ya shiga yayewa amma Basma ta cukukuye jikinta da shi, wani wawan mari ya sakar mata, sai ta tsandara uban ihu, duk da haka baisa ta saki ba, cikin fushi yace

"wlh ko ki so ko kar kiso yau saina karb'i hakk'i na"

Wani marin ya kuma sakar mata, duk da haka tak'i saki, da k'arfi ya finciko zanin gadon, sai ta k'ank'ame hannunta a k'irjinta, kuka take kamar ranta zai fita, magiya ta shiga yi masa cikin kuka

"Yaya Shureym dan Allah ka kyaleni karka kasheni, me nayi maka ne da zaka yi min mugunta"

Bige mata baki yayi, bakin ya fashe sai jini, abinda yake son aiwatarwa bai fasa ba, Basma kuwa gunjin kuka take yi, a wannan lokacin tariga ta sadak'ar, cizo ta ganna masa a kunne sai ya saketa ya kai mata naushi a baki, ya shiga dukanta ta ko ina

Basma wani wahalanlan ihu ta saki wanda yayi dai-dai da shugawar Safeena falon, dama ta shigo falon da mamaki, saboda ganin motan Shureym da tayi a gida, da sauri ta nufi inda take jin kukan, harta isa d'akin Basma, ta tsaya a bakin k'ofar, dai-dai lokacin Shureym yana k'ok'arin kai ga cika k'udurinsa Basma ta saki wani wawan k'ara, ai da k'arfi Safeena ta tura k'ofan ta buga garam, ta fad'a d'akin ta tuna huci....

*Rahma Ce*
[8/8, 5:38 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *17.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

K'aran bugun k'ofar shine yayi dai-dai da Shureym ya dawo hayyacinsa, da sauri ya sauka akan gadon, cikin jin haushi da borin kunya ya kwaci kayanshi a hannu ya fita a d'akin, da gudu-dugu ya fad'a d'akinsa tare da sanya key. Basma kuka take tana cewa
"Allah ya isa bazan yafe maka ba, mugu azzazulumi insha Allah harka mutu baza ka cimma burinka a kaina ba" furucin Basma na k'arshe shine ya sanya Safeena ajiyan zuciya, dama fargabanta shine ace ya samu Basma, tasan lallai kashinta ya bushe, gashi Basma ta fita komai na kyawun sura, sannan ta tabbatar Basma bata bin maza lallai zai sameta a budurwa, kallo Basma tayi cikin tausayawa, da sanyin murya tace cikin tsoratarwa

"Kad'an kika gani in dai Shureym ne, mugune shi sosai haka yakemin nima, karki k'ara yanda haka ta faru in ba haka ba wataran zai kashe ki, maza tashi ki gasa jiki a toilet, kuma karki sake barin k'ofarki a bud'e, dan Shureym ya wuce yanda kike tunani" tana gama fad'an haka ta fice a d'akin.

Basma wani sabon kuka ta saki, da kyar ta iya sakowa daga gadon, tana bin bango harta shiga bayi, ruwa ta had'a mai zafi ta shiga ciki, ta kai kusan rabin awa tana ciki, kana tayi wanka ta fito, mirror taje ta tsaya tana kallon yanda fuskanta ya kummbura, hawaye ne ya sauka a kuncinta mai zafi, fuskan ta tayi ja sosai, gashi

Please Login or Register in order to submit comment