Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaci karo dasu momy, nan ya kewaye su ya wuce da ita part d'in president, a falon ya ajeta duk suka shigo ko wanne ya rufa a kanta, Ammi ne keta kiran sunanta amma shuru, da gudu Meena ta kawo ruwa aka yayyafa mata, lumshe ido tayi tare da sauke ajiyan zuciya mai k'arfi, President da kansa yazo ya d'auketa cak ya haye da ita sama, ya kuma yi gargad'in kar wanda ya biyoshi, a zata yayi akan gadonsa ya d'auki wayansa ya kira likitansu.

Baifi rafin awa ba sai gashi, ya haura sama ya dubata, allurai yayi mata a ciki harda na barci, yayi wa Abba bayanin
"damuwa ce ya haifar mata da suma, yanzu nayi mata alluran barci domin kwakwalwanta ya huta" nan Abba ya mishi kyauta ya fice yana godiya.

Su Ammi duk suna falon sun kasa tafiya, Yaya Ahmad ne ya zauna jugum yace
"Ammi dan Allah kusa baki a jenye maganar Auren nan, lamarin Basma ya fara bani tsoro" Ammi tace
"nima abinda na gama tunani kenan, amma kasan Abbanku baya sauya magana in yayi" Momy ce tace
"uhum nikam ina bayan Abbanku, aure kuma da Shureym ba fashi" tana gama fad'an haka ta mik'e tace
"Husnah zo muje na had'a miki turarukanki kan ki tafi" Cikin sanyi jiki da damuwa Anty Husnah tabi bayanta cike da tauyawa 'yar uwanta.

Sai bayan Sallan Isha'i ta farka, Abba da kansa ya kira Ammi tazo tayiwa Basma wanka ta shiryata, Abinci ta bata da kanta, da kyar take iya cin kad'an, bayan sun natsa Abba ya kira su Meena dasu Momy, dasu Yaya Ahmad duk suka had'u a falon sa, ya soma magana

"na taraku a nan ne domin in kuma jaddada muka akan zancen Auden ku, saboda wasu dalilai mun k'ara kwanakin bikin zuwa bayan wata Uku, lokacin Basma ta samu lafiya sosai, Meena tasha maganin Islamic akan kwayoyin da tasha, ke kuma Leema ki samu yin istibra'i" Leema saita sunkuyar da kai k'asa, cike da dana sani, yanzu kowa yasan ita fasik'a ce wa'iyazu billah, maganar zuci takeyi hayawa na zuba a kuncinta. Abba yakai dubansa ga Basma data rakub'e gefe d'aya kusa da Ammi yace

"ke kuma Basma ina so ki sani tun da muka haifeki, ban tab'a saki abu kin k'i yimin ba, to ina niman alfarma a gunki a matsayina na mahaifinki, kiyi hak'uri kiyi min biyayya insha Allah zaki nasara a rayuwanki, Basma ke mai biyayya ce a garemu, akwai abubuwa dana auna na tabbatar da yin aurenki ga Shureym shine dai-dai, zumunci ba abun wasa bane, dan haka ki sanyawa ranki salama ki tabbatar min da nine mahaifinki kuma na isa dana saki Abu kiyi min"

Kuka ta soma yi amma mara sauti, tashin hakanli ta shiga, domin yau ta riga ta sadak'ar an rabata da Aryan, kwantawa tayi a jikin Ammi tace cikin kuka mai karya zuciya

"Abba ina son Aryan ne wlh shi nake so, burina in muku biyayya, Abba kamin komai a rayuwata, k'arshe na sab'a muku, na aje tarbiyyan da kuka bani na soma yin wata rayuwa mara tushe, mai dinbin dana sani aciki, nagodewa Allah da kune kuka ganni da idonku, na tabbatar da labari aka baku baza ku yarda ba, saboda kun bani dukkar yardanku, Abba saboda haka na hak'ura da soyayyar Aryan, amma ku sani zan auri Shureym bisa ga biyayya a gareku ne, domin in cire muku rad'ad'in sab'a muku da nayi, Na amince zan auri Shureym, Aryan ka yafemin"
Sai ta k'arasa maganar da wani matsanan cin kuka, da gudu ta mik'e tabar falon, ta nufi d'akin Abba, ta fad'a gado tana rera kuka mai tsuma zuciya.

Gaba d'aya illahirin mutanan falon jikinsu yayi sanyi, hatta Abba ya tausayawa 'yarsa abin sonsa, sunyi shuru ko wanne da irin abin da yake sak'awa a ransa, sautin kukansu Meena da Leema ne ke tashi a falon, Kaka Ma'u ce tace
"ni kam wannan lamari yana bani mamaki, waye wannan Aryan d'in da yake son raba zumunci" Yaya Ahmad ne yace cikin wasan kaka
"ke kuma tsoguwa ina ruwanki, ana Abu na yara kin tsomo baki, sai ki mana shuru" Abba ne ya masa dak'uwa yace
"kai ungo naka uwata kake cewa hakan" su Ammi duk suka yi murmushi, nan take fara'ansu ya dawo, damuwan da suke ciki ya ragu, Abba yace
"Ahmad ina so gobe in Allah ya kaimu ka tattaro min dukkan takardu da makullan abubuwan da Basma ta mallaka" Cikin dalabi yace
"to Abba insha Allah zanyi, Allah ya kaimu"

Nan Abba ya sallami kowa, Momy ce mai girki Abba ya cewa Ammi, ta wuce da Basma d'akinta, ta bata kyakkyawan tsaro saboda karta fita cikin dare ba'a sani ba.

Shureym bayan sun isa Kano, ya samu Maminsa ya matsa mata akan shifa lallai sai an aura masa Basma in ba haka ba akwai Matsala, Hajiya Sa'a tayi murmushi tace masa
"Ka kwantar da hankalinka, aurenka da Basma kamar anyi an gama, ita d'in banza harta isa tace bazata aureka ba, zanje in samu Mai Martaba na k'ara hura masa wuta akan lamarin" dariya yayi na farin ciki yace
"to Mami ya maganar aurena da Safeena? Kinsan fa so nake a fara d'aurawa da ita kan na Basma" tace
"Karka damu cikin satin nan zan had'aka da sarkin gida da wasu, domin su jagoranci aurenka da Safeena, a cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba, kaga sai a d'aura muku aure kafin bikin su Basma da wata guda, ka ajeta a gidan gonarka, da an d'aura aurenku da Basma ku tarkata ku wuce America, bazaku dawo ba sai ka kammala komai da shekara guda, kaga lokacin komai yayi dai-dai" dariya yayi harda tafawa yace
"Gaskiya Mami kin gama min komai in kika min haka, zanyi murna sosai" tunowa da yanda Basma ta nuna masa tsantsar kiyayya yayi, yasa ya cije leb'e yayi wani shu'umin murmushi.

*Bayan kwana biyu*
Aryan ya lalace yayi duhu, hankalin Umma ya tashi sosai dan kwanan sa biyu ko k'ofar gida baya iya zuwa, sallah ma a gida yake yi, baya iya cin komai sai abu mai ruwa, sai yawan barci. Deeja ce take sanarwa Yaya Ahmad halinda suke ciki domin sam Yaya Aryan yak'i yarda suje asibity kuma yace shi lafiyansa kalau, Ahmad ya shirya yazo, ya samu Umma ya sanar mata abin da ke faruwa game fa Basma da Aryan, bai b'oye mata komai ba, hankalin Umma ya tashi sosai ta tausaya musu, dama tasan za ayi haka, Deeja d'aki ta shiga ta fara kuka, Yaya Ahmad ya sanar mata da zuwan iyayensa nan da ranar Juma'a akan maganar auren Deeja, Umma ta sanya albarka tayi murna koba komai hakan ya rage mata damuwa, nan ya shiga wurin Aryan da kyar ya shawo kanshi suka tafi asibity tare.

Likita ya duba shi ya rubata masa magani da allurai, haka akai treatment d'insa, Yaya Ahmad yayi masa siyayyan kayan ciye-ciye, kana ya dawo dashi gida, ya yiwa Umma sallama ya tafi.

*Bayan wata guda*

Bikinsu Basma saura wata biyu, Yaya Aryan ya warware ya cigaba da zuwa aikinsa, sai dai yanzu miskilanci ya k'aru, baya magana saiya kama dole, baya cin abinci sosai duk ya rame yayi fari, Umma tayi mita da lallashi harta gaji ta kyaleshi, kullun dare baya iya barci sai yayi kuka sosai, kana yayi Nafila ya rok'i Allah kan ya sassauta masa akan lamarin.

Abba ya wakilta Abokansa wajen nimawa Ahmad auren Deeja, da yake Ahmad ya sanar da Abba komai tun farkon had'uwansu, Abba ya jinjina lamarin kuma yayi farin ciki da 'ya'yansa, da suka kasance masu tausayi da taimakon na k'asa dasu, hakanne ya k'ara bashi k'arfin gwiwan ya amince da Auren Ahmad da Deeja, a ransa baiji dad'in raba Basma da Aryan ba, Amma yayi alkwarin zai d'aukaka darajan Aryan yanda duniya da 'yan uwansa zasu amfana dashi.

Mak'otan su Deeja da mai anguwa sune suka amshi maganar Auren Deeja, iyayen Ahmad da suka zo sun boye asalin Ahmad, suka sanya biki dai-dai dana su Meena, a haka suka gama taron cikin mutunci, kowa ya koma gida.

Deeja farin ciki ya lullub'eta, amma inta tuno da Yaya Aryan sai damuwa ya rufeta. A haka suka fara shirye-shieyen biki, Yaya Ahmad ya sanar musu da, shifa Deeja kawai yakeso a bashi, baya buk'atar komai, hatta abincin biki Abbansu ya d'auki nauyi, dan haka kar su takurawa kansu, Umma saboda murna har kuka tayi.

B'angaren Basma kuwa, lamura sun dagule mata ta lalace tayi bak'i, duk ta rame inka ganta sai ka k'ara kallonta ka tambaya anya itace Basma 'yar kwalisa kuwa? domin duk ta fice a hayyacinta, kowa na gidan yana tausaya mata, hatta Momy tana jin tausayin 'yarta haka yasa take jawota a jiki, tana lallashinta da maganganu masu dad'i da nasiha, yanzu Basma ta saduda ta kuma hak'ura da lamarin, burinta bai wuce ta k'ara tozali da Aryan ba suyi magana na bankwana.

Su Meena an natsu, ana ta bata magunguna na Islamic wanda zai wanke mata dattin kwayoyin data sha. Leema kuwa Momy musamman takwo mai gyara, domin a gyarata, yanda zata dawo kamar budurwa, koda dai ta riga ta rasa budurcinta.

*Ni kam nace anbaro shiri tun rani*

Shirye-shirye ake ta ko wani b'angare, Abuja, Kano, Kaduna, duk sunata shirye-shieye, biki ne na 'ya'yan manya.

*Biki saura wata guda*

President ya kira Ahmad suka gana dashi a d'akinsa. Yaya Ahmad ya fita da sauri domin aiwatar da ummarnin Abba. Abba ya kira Momy da Ammi, ya kira duk yaran gidan, kaka Ma'u ita ta koma Kaduna dan tafi jin dad'in zaman can.

Yaya Ahmad ya nufi gidansu Aryan, ya samu duk suna gida da yake weekend ne, Yaya Ahmad ya shiga ya zauna a shinfid'an da Deeja ta masa, suka gaisa da Umma, ya kalli Aryan ya kalli Umma yace
"Umma mahaifina ne yace inzo in tafi daku gidanmu, domin yana buk'atar ganinku, yace in baku hak'uri akan hakan, yasan shine ya kamata yazo amma bisa wasu dalilai yace da kuje ku same shi" Yaya Aryan ne yace
"ok badamuwa yaushe yake son ganinmu?"

"Yanzu yake son ganinku" Umma tace
"to shikenan bari mu tafi" ta k'ara maganar tana mik'ewa, komawa d'aki suka yi duk suka canza shiga mai kyau, suka rufe gidan suka gida mota.

Aryan na gaba Umma da Deeja suna kujeran baya, sun kama hanya suna tafiya, Aryan suna hira da Yaya Ahmad, tafiya sukai mai nisa, tun suna arean talakawa har suka gota arean masu hannu da shuni, Yaya Ahmad yana zullumi a zuciyansa yanda in suka san Abbansu ne Shugaba k'asa ya zasu d'auki lamarin , Yaya Aryan ne ya katse masa tunaninsa yace
"Ahmad naga mun doshi hanyar gidan Shugaba k"asa ne, kasan fa ta arean akwai check point kuma ga yawan security" murmushi Yaya Ahmad yayi yace
"eh gidanmu dole sai tanan zamu bi, karka damu" haka suka fara ratsa check point ba tare da an tare su ba, security suna d'agawa Yaya Ahmad hannu, mamaki ne ya fara cika su, basu tsinke ba saida suka ga security na bud'e musu hanya suna sarawa Yaya Ahmad, katon tangameman gate d'in fadar shugaban k'asa suka dosa, wanda kan su k'araso an bud'e musu gate, a tsorace Yaya Aryan ya kalli Ahmad bakinsa yana yawa yana nuna shi yace.....

*Rahma ce*
[8/6, 9:03 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *14.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Yace
"Ahmad kasan inda ka kawo mu kuwa?" Ahmad murmushi kawai yayi, sai yayi parking mota, ya fito tare da cewa
"Umma mun kawo Ku futo" a sanyaye suka fito suna k'arewa gidan kallo, cikin kulawa Yaya Ahmad yace
"kumu je" Umma tace
"Kai Ahmad wai ina ne nan, gaskiya a tsorace nake" murmushi yayi yace
"Umma Ku kwantar da hankalinku bakomai fa" a tsorace suka bi bayansa, direct part d'in president ya kaisu, suna shiga duk mutanan falon suka zuba musu ido, jikin su Deeja sai ya d'au rawa, ido suka saki suna kallon kayan alatu da aka zuba a falon, har suka isa tsakiyan falon, Basma ne ta rugo da gudu ta rungume Umma, ai sai ta fashe da kuka, Umma ta rik'eta gam tana lallashinta, a haka suka k'arasa cikin falon suka zauna a kan kafet, Ahmad yace su zauna a kujera amma suka k'i hawa, Su Ammi da Momy suka bisu da kallo, su Meena ma dasu Yaya Naufal kallonsu suke yi da mamaki, sun gaisa gaba d'aya sai falon ya d'auki shuru, baifi minti goma da zuwansu ba President ya fito, cikin shiga na manya kaya, yana tafiya cike da izza tamkar Baba Buhari ya bayya a cikin bainar Jama'a, sai dai shi Abba bai yi tsufan Baba Buhari ba, lol.

Su Aryan suna arba dashi sai cikinsu ya d'uru ruwa, kamma ace Umma da tayi mutuwar zaune, Deeja ko kamar ace mata ket ta ruga a guje dan tsoro.

Zama yayi a kan kujeransa na alfarma, Ahmad ne yace
"Abba gasunan nazo dasu" Abba ne ya kalli inda suka zauna yace
"barkanku da zuwa" baki na rawa suka amsa gami da gaisheshi, Abba yace

"Nine mahaifin su Basma, Ahmad shine Babban Yaro na, nasan za kuyi mamaki da haka, Ahmad ya sanar dani labarinku, sai dai Ku bakusan nine Mahaifinsu ba sai a yau" a razane Aryan yake kallon Abba yana magana, ya juya kallonsa ga Yaya Ahmad da Basma, murmushi Yaya Ahmad yayi masa ya gyad'a masa kai alaman eh, Basma Kuma ta sunkuyar da kai k'asa, tunda tayi tozali da Yaya Aryan hankalinta ya tashi, taga ya rame sosai tausayinsu ya kamata tasan lallai an yiwa rayuwansu gib'i.

Nan Abba ya cigaba da bayani yace

"Aryan nasan komai dake tsakanin ka da Basma, kayi hak'uri da abinda ya faru, ba zan iya hana Auren ta da Shureym ba, domin ina martaba zumunci, dan haka ne na amince da Auren Ahmad da 'yar Uwanka saboda in sanya muku farin ciki, ku tabbatar da bama kyamar talaka, sannan yanzu nayi maka alkhawarin ka kawo duk yarinyar da tayi maka, insha Allah zan zame maka Uba na jagoranci lamarin, sannan nasan a company na kake aiki, yanzu na baka MD na company, sannan zaka Zab'i k'asar da kake so domin kaje ka k'aro karatunka a can"

Aryan kuka ya fara yi, yace cikin ladabi,

"Yallabai nagode kwarai da karamci, ban tab'a kawowa a rayuwata zanga Shugaban k'asa da idona ba, sai gashi a sanadin soyayyan Basma na ganka, Basma ke haske ce a rayuwanmu, Yallab'ai nagode da duk abinda ka bani, amma ina so ku sani, ba zai iya siyan soyayyan Basma ba a zuciyana, domin an riga an halittamin shi a zuciya, na hak'ura da soyayanta dan nariga na sadak'ar Basma tafi k'arfi na, mun gode sosai da karamci" yana gama magana sai yayi shuru.

Shasshek'an kukan Basma ke tashi a falon, kowanne yayi shuru suna zancen zuci. Umma itama tayi godiya tace
"lallai Basma da Ahmad kunyi gadon halaye na kwarai wurin mahaifinku, nayi mamaki sosai da yanda kuka shigo cukinmu kuka zauna damu duk girman matsayinku, kun rungume mu tamkar jininku" saita k'arasa maganar da kuka, Deeja ma kuka ta soma yi, falon ne yayi shuru na 'yan dak'ik'a, sai Abba yace

"Hajiya kuyi hak'uri ai wannan ba abin kuka bane, kai Aryan ba wai na maka wannan kyauta bane domin ka fansar min da soyayyarka ba, nayi maka ne saboda Allah a matsayin d'an cikina, taso ka amshi wannan takardun, na gidan Hutun Basma ce da kuma takardun motanta guda uku, ni na baka su halak malak, ina so kafin lokacin Biki Ku tare a gidan" Yaya Ahmad ne ya matsa danya Amsa takardun, sai Abba yace
"shi nake so ya amsa da kansa, domin shima d'ana ne" jikin Aryan ne yayi sanyi, haka ya mik'e yaje ya amsa tare dayi masa godiya. Momy itama tayi masa Addu'a da Allah ya bashi mata tagari, har a zuciyarta taji tana son Aryan, taso ace ya zama sirikinta. Ammi kuwa ta gama k'ulewa kamar zata fashe dan haushi, Meena da Leema sun shaida Aryan kuma sun yaba da kyawunsa lallai sun dace da Basma, Yaya Naufal da yake yasan Aryan ya tayashi murna, amma har a azuciyansa baya son ya auri Basma domin tafi k'arfinsa.

Nan Umma tayita godiya, Abba yace
"Hajiya ya isa haka Allah ne ya baku, ina 'yata Khadija?" Kanta a sunkuye tace gani, Abba yace
"Masha Allah, Allah ya muku Albarka yasa Albarka a aurenku" ya kai dubansa ga Momy yace
"Hajiya Maryam gafa surukarku nan, matar Ahmad" ai sai Momy ta fad'ad'a murmushinta tace
"Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi, ai tunda tazo ma ba zasu tafi da ita ba, zata zauna anan domin ayi mata gyaran jini dasu Leema gaba d'aya" Abba yace
"To shikenan, Abu yayi kyau, bari na fita ana jira na" nan yayi musu sallama ya fice, Ammi ce ya mik'e da sauri tace

"Ahmad yanzu ka rasa matar aure sai wannan yarinyan, to ka sani ba da yawuna ba, dan bataimin ba" tana gama fad'an haka ta fice, da mamaki duk suka bita da kallon, Ahmad cike da tashin hankali yace ma Momy,
"Momy kinji abinda Ammi tace ko, dan Allah ki shawomin kanta" Momy tayi murmushi tace
"karkaji komai zata sakko ne" ta kai dubanta gasu Umma tace
"Hajiya kuyi hak'uri rashin fahimta ne" Murmushin yak'e Umma tayi domin abin ya bata haushi tace
"ba komai ai" nan Yaya Ahmad yace su tashi ya rakasu gidan da Abba ya basu, Basma ta mik'e tace
"Yaya Ahmad zani" hararan wasa yayi mata yace
"kinsan dai yanzu bakwa fita, kiyi hak'uri kiyi zamanki a gida" marairaice fuska tayi tace
"tom zanyi magana da Yaya Aryan" da sauri Aryan ya juyo yace
"a'a Basma magana a tsakani mu ya k'are" yana gama fad'an haka yayi waje da sauri, ai da gudu Basma ta bi bayansa tana kwala masa kira.

Ya kusa kaiwa gate, sai ya tsaya tsak amma bai juyo ba, ta cimmasa ta tsaya a gabansa tana haki, kallonta yayi ya kauda kai, hawaye ke sauka bisa kuncinta tace cikin sark'ewan murya
"Yaya Aryan guduna kakeyi na zama abin gudu ko, ko ka daina sona ne?" Runtse idonsa yayi ya bud'e su, sun rine sunyi ja yace
"Basma dole na gujeki domin ke yanzu ba tawa bace, Basma kin haramta a gareni, magana a tsakaninmu bai dace ba, domin zai tado min da mikin dake zuciyana wanda mai gama warkewa ba, ina Sonki Basma baya musaltuwa, amma ki sani soyayyan da mukayi dake kisa aranki tamkar mafarki ne, ki cireni a zuciyarki kiyiwa iyayenki biyayya" yana gama fad'an haka ya matsa ya cigaba da tafiyan, Basma durkushewa tayi a gurin ta saki wani kuka mai tsuma zuciya, Aryan shima da kuka ya fita gidan, yana fita ya tsaya gefen wani dakali ya durkusa agun ya shiga rera kuka tamkar k'aramin Yaro.

Leema, Meena da Deeja ne suka zo suka d'aga Basma, suka wuce da ita part d'in Momy. Umma suka fita itama tana kwalla, a haka suka cimma Yaya Aryan ita da Yaya Ahmad da kuma Yaya Naufal, dafashi Yaya Ahmad yayi, ya d'agoshi ya shiga share masa hawaye tare da gaya masa kalamai masu sanyaye rai. A haka ya sanyashi a mota ya wuce dasu gidan da Abba ya basu.

B'angaren Shureym kuwa Mami ta aika Sarkin Gida da wasu mutane garin Yola, an basu auren Safeena, sun kai musu akwati da komai da Shureym ya siya, anyi shagulgulan Biki lafiya an d'auko Amarya. sun sauka a gidanta dake garin Kano wanda Shureym ya gyara shi sosai, komai na jin dad'i akwai a gidan. Sun gama bikin auren sirri, wanda daga Mami sai Shureym sai wanda suka je nema masa aure sune kawai suka sani. An bar Amarya da Ango suna cin Amarci.

Momy ta samu Ammi akan batun Auren Yaya Ahmad da Deeja, tayi mata bayani mai gamsarwa, Ammi ta sauko, tace ta hak'uri amma tana son Ahmad ya zauna da matar anan cikin gidan President, ta da sanyawa Auren Albarka, Momy taji dad'in haka sosai, tace zata Sanar ma President domin a gyara part d'in da Ahmad zai zauna.

*Biki saura mako guda*
Anata shirin biki ta ko ina, mutanan Kano sun tattaro sun wuce Abuja, mutanan Kaduna ma haka, gidan president ya cika da dangi da abokan arziki, kowa kagan shi yana cikin farin ciki.

Amare kuwa sunsha gyara sai kyalli suke, a zuwa yanzu su Yaya Naufal da Yaya Jamal sun sauko da k'in da sukewa su Meena, yanzu burinsu bai wuce a d'aura aure ba susha amarci, sai dai a Kasan zuciyan Yaya Jamal yayi alkawarin sake aure da sabuwar budurwa domin shima ya mori aure, dan yasan Leema saura zai samu agunta.

Basma ta saduda sosai tayi sanyi, tana tsayawa tayi hira da Yaya Shureym amma a k'asar zuciyanta Aryan yana nan, kullun dare saita yi kuka na rashinsa, Shureym sai rawan jiki yake yi, yana nunawa Basma kuwala ta musamman, dan burinshi bai wuce yaga an d'aura Auren ba, domin yana cike da tsananin sha'awarta, yasan duk k'insa da take yi da an d'aura zata bada kai bori ya hau.

B'angaren Safeena, Yaya Shureym ya sanar mata da komai na aurensa da Basma, ta nuna rashin damuwa akan haka, sun tawo Abuja a tare, ya kama mata d'aki a hotel har a gama bikin su wuce America, Safeena burinta bai wuce ana gama shagalin biki ba su wuce America, ta juya Basma yanda ranta keso, domin Shureym ta gama dashi a tafin hannunta yake, sannan tayi alkhawarin Shureym bazai tab'a tarawa da Basma ba in dai tana raye.

Amarya Deeja tayi kyau tamkar ba ita ba, hatta Ammi da take k'inta ta yaba da yanda ta sauya, fatarta tayi kyau, kamannin ta da Meena ya fito sosai, a hankali taji ta kwanta mata arai saboda yanda Deeja take mata biyayya da kuma nuna kunya a gareta a matayinta na mahaifiyan mijinta, cikin k'ank'anin lokacin ta nima k'iyayyar da take mata ta rasa, har wautan kanta take gani akan meyasa ta nunawa Yarinya tsana haka. Deeja ta koma gida, ta samu su Ammi a sabon gidansu, domin a nan ne za'a d'aukota a kawota gidan president.

*Ana gobe biki*

Mutane sun gama hallara, ta wajen su Umma mutanan Gombe sunzo, sai dai mahaifinta Malam ba shida lafiya, dan haka Innarta basu samu zuwa ba sai danginsu, sunata shirye-shirye cikin kwanciyar hankali.

Yaya Aryan ya bar K'asan ana saura kwana uku biki, ya wuce K'asar Manaco domin yaji ba zai iya tsayawa bikin ba, koda ya isa k'asar ya kashe duk wayoyinsa ya soma Harkan karatunsa, Basma tana ransa, shi kad'ai yasan irin k'unan da zuciyansa yake ciki, kullun saiya kalla hotunanta da wanda take ita kad'ai da wanda suka d'auka tare a cikin system d'inshi, wani yayi murmushi wani yayi kuka, ya saba da haka, harya zame masa jiki.

*Ranar daurin aure*

Angwaye sun fito sunyi fas sai shek'i suke yi, ta b'angaren amare kuwa tsayawa fad'an kyawunsu b'ata lokaci ne, Basma koda tana cikin damuwa tayi kyau, tasha kwalliya amma bai haka zuban hawaye a fuskanta ba, duk wanda ya ganta saiya tausaya mata, ta k'ara tsukewa ta rame, ko tayi dariya yake tayi, sam bata farin ciki da wannan auren, Addu'a take Allah ya bata hak'uri da juriya akan auren.

Bayan sun idar da Sallah Juma'a limamin masallaci ya sanar da d'aurin Auren yaran President da Gomnan Kaduna, da kuma Sarkin Kano. Biki na 'yayan gata.

An d'aura auren
Yaya Ahmad da Khadija
Yaya Shureym da Basma
Yaya Jamal da Haleema
Yaya Naufal da Ameena
Yaya Adam da Munaya 'yar wazirin Sarkin Kano.

Anyi addu'o'i kana aka wuce taron walima a babban hol dake fadar Shugaban k'asa, anci ansha kowa ya shaida wannan aure, na 'yayan manya ne kuma masu gata.

Basma tana jin an d'aura ta shiga d'akinta ta kulle kanta, kwantawa tayi a gadonta ta fara kuka mara sauti, hoton Aryan a wayanta take kallo tace
"shikenan an rabamu, Yaya Aryan ina sonka Allah ya rabamu, Allah kasamin juriya da hak'uri azuciyata, Aryan na je soyayyarka a zuciyata, zan yi kok'arin yin biyayyar aure ga mijina, Allah ya had'a fuskokinmu yasa na zama matarka a aljanna" saita b'alle da sabon kuka. A haka barci mai nauyi ya d'auketa, ba ita ta farka ba sai bayan sallan La'asar. Wanka ta tayi, ta canza wasu kayan zuwa leshi marun mai fulawa fari, tayi makeup tamkar ba Basma ba, ta b'ata lokaci sosai wajen kwalliya, kana ta aza gwagwaro Fari, ta sanya takalmi mai tsini, turaruka kuwa

Please Login or Register in order to submit comment