Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hawaye tace
"amma Yaya Aryan a da baka jin irin haka, meyasa yanzu haka ke faruwa?" tana zubda hawaye.

Mik'ewa yayi da sauri ya kamota ta mik'e tsaye, rungumeta yayi tsam ajikinsa, take ya fara jin zafin jiki da ciwon kai, saketa yayi suna kallon juna yace

"Basma bansan me yake faruwa dani ba, tun bayan kwana biyu da suka wuce, duk lokacin da kika zo kusa dani ina shiga cikin mawiyacin hali, kaina ya rik'a min wani irin ciwo tamkar zan mutu, jikina kuma tamkar garwashi, a yanzu haka ina jin abinda nake gaya miki a jikinsa"

Zuba ma juna ido suka yi, tace
"Myn zan kira Yaya Ahmad in sanar masa domin anima maka magani"
Kama hannunta yayi yace
"karki gaya masa saboda kar mu tada musu hankali, yanzu dai ki cigaba damin Addu'a, zo muje mu karya tun d'azu aka aiko mana da breakfast daga gida"

Hannunta ya kama gam suka wuce dinning sunci sun koshi, suna yi suna hira kamar babu wata matsala a tare dasu.

Da midalin k'arfe biyu na rana Mutane suka fara zuwa, Yaya Aryan fita yayi ya basu guri. Basma tana tare dasu Deeja a d'aki sai tsiya suke mata, murmushi kawai take yi dan ita kad'ai tasan halin da suke ciki, kamar ta gaya musu amma saita fasa. haka suka yi mata yini sai dare su Yaya Ahmad suka zo suka kwashe su.

Basma na gefen Aryan yana nishi sama-sama, abinda ya faru jiya shine ya kuma faruwa yau, kuka Basma take yi mara sauti, Addu'a take yi tana tofa masa, a hankali ya samu natsuwa ya hau saman gadon ya gyara kwanciyansa, yau baijin zai iya tafiya ga shi bai wanke jiki ba, haka barci ya d'auke shi mai nauyi. Basma tashi tayi ta wanke jiki ta d'auro alwala Sallan Nafila ta gabatar tare da jero Addu'a, Allah ya kawo musu d'auki cikin matsalan su.
Nima dai na taya su da Ameen.

*Bayan mako biyu*

Su Basma suna cikin wannan halin babu wani sauyi, duk sun rame sunyi haske, d'an kyau da Amare su keyi su sam ba suyi ba. haka suka shirya suka nufi gida dan su gaishe su, sun isa ko wani part sun gaishe su, President yayi tafiya dan haka basu sameshi ba.

Part d'in Yaya Ahmad suka nufa, hira suke sosai Yaya Ahmad ya kalle su yace cikin kulawa

"Aryan, Basma anya babu wata matsala kuwa a tattare daku? kunga yanda kuka yi rama sai haske da kuka yi kamar wanda suka farfad'o daga ciwo"

Murmushi suka yi, Yaya Aryan yace
"Abokina mu da muka yi Auren soyayya ai babu wata Matsala da zai samu damuwa, kawai dai duk cikin Amarci ne muka koma haka, ko ya kika ce My Basma?"

Murmushi tayi tace
"sosai ma kuwa Mijina, hankalin mu kwance yake ba wata damuwa"

Yaya Ahmad yace
"to Alhamdulillah naga yanda kuka sauya ne lokaci guda, dole muyi zargin ko da Matsala"

Yaya Aryan yace
"aiko ba zamu sake zuwa ba sai munyi k'iba sosai, dan d'azu ma Ammi tirkemu tayi, wai me yake damun mu duk mun fita hayyacin mu"

Dariya duk suka saka yaya Ahmad yace
"Allah kuwa duk wanda ya sanku kafin aure in ya ganku yanzu sai anye kunyi rama"

Deeja tace
"raman ma sosai kam, kuma abin mamaki gaba d'aya suka yi raman, Allah yasa dai lafiya"

Harara Yaya Aryan ya watsa mata
"me kike nufi? kina nufin baki gamsu da abinda muka fad'a ba"

mik'ewa tayi da sauri tana dariya tace
"sosai kuwa, ai daga kai har Basma bakin ku d'aya, kuma shegen miskilanci ne daku" tana gama fad'an haka ta bar wurin da gudu dan kar Yaya Aryan ya mata hukunci.

Haka suka gama yinin su sai dare suka koma gida cike da farin ciki, suna isa gida, gabansu ya fara fad'uwa sun riga sun sadak'ar yau ma abinda suka saba fuskanta ne zai faru, sun kuma kasa hak'ura da juna, dan kullun sai Aryan yayi k'ok'arin kusantarta, amma abin yaci tura.

Yaya Ahmad yana kwance a d'aki ya juya ya kalli Deeja sai barci take yi, tunanin su Basma ya kasa b'ace masa a zuciya
"kuma ya kasa yarda da abinda suka gaya masa, yasan wannan karan Basma ba zata tab'a gaya mishi damuwarta ba tunda tana Son Aryan, sannan kuma yasan yanda Aryan ke Son Basma bazai cutar da ita ba, to me yake damunsu su biyun? meyasa su kayi rama haka?"

Tambayoyin da yakewa kansa kenan wanda ya zaga samun amsansu sai a bakin Aryan da Basma zai samu, gyara kwanciya yayi da niyyar gobe in Allah ya kaimu sai je gidan da safe yaga abinda ke faru ko ya matsa musu su gaya masa. Da wannan tunanin ne barci ya d'auke shi.

*Lallai Aryan akwai wata matsala a tare da kai, ko meye ne...?*

_*Hmmm yau dai dasan na tarwatsa farin cikin Makaranta wannan littafin, sai dai ince kuyi min hakuri haka na tsara labarin, kuma ina da dalili, insha Allah za kuyi farin ciki a nan gaba. Godiya gareku masoyana da irin Addu'an ku gare ni. Ina sonku sosai irin da yawa d'in nan Allah ya kara zumunci. Ameen*_

*Rahma Ce*
[8/15, 8:44 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*

_page_ *35.*

_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*

*Washe Gari*

Da k'arfe bakwai na safe Yaya Ahmad ya kama hanyar gidan Yaya Aryan. Yana isa yayi hon Mai Gadi ya bud'e masa Gate, yayi parking ya isa bakin k'ofar falon yayi nocking, Yaya Aryan dake kwance a kan doguwar kujera ya mik'e cikin nauyin jiki ya isa bakin k'ofan ya bud'e, sai yayi arba da Yaya Ahmad, sai da gaban Aryan ya fad'i, matsa masa yayi ya shigo cikin falon duk suka samu guri suka zauna, sai suka gaisa, Yaya Ahmad yace

"Ina Basma fa?"

Yaya Aryan yace
"tana d'aki, lafiya na ganka da sassafe haka?"

"Lafiya lau, nazo nayi magana daku ne, dan haka kira min Basma tazo"

Bai ce komai ba ya mik'e ya isa bakin k'ofar Basma, sai ya ki shiga ya tsaya bakin k'ofar yana bugawa tare da cewa
"Basma, Basma ki tashi ga Yaya Ahmad yazo"

Cikin magagin barci ta farka ta mik'e tare da bud'e murya yace "to".

Yaya Ahmad duk yana kallonshi, a ranshi yace
'ko me ya hanashi shiga d'akin oho' Yaya Aryan ya dawo ya zauna.

Basma ta fito sanye cikin doguwar riga ta yane gyale a kanta, zama tayi a one seater ta gaishe da Yaya Ahmad ya amsa cikin kulawa, shuru ne ya biyo baya na tsayin minti Uku, daga bisani Yaya Ahmad yace

"Aryan, Basma nazo domin muyi magana ne, a gaskiya ban yarda da bayanin da kuka min ba jiya, shiyasa na zo Yau dan jiya na kasa barci, Dan Allah karku b'oye min komai"

Basma da Aryan suka kalli juna suka had'a ido, Basma zata yi magana Aryan ya riga ta yace

"ka yarda da abinda muka ce maka mana domin ba komai"

Yaya Ahmad yayi murmushin k'arfin hali yace
"Basma in shi ba zai gaya min ba ke nasan ba zaki b'oye min ba, dan haka gaya min me yake faru?"

Hawaye ne ya soma zarya a idon Basma, ta d'ago ta kalli Yaya Aryan,  sai ya fara gir giza mata kai alamar karta gaya, Yaya Ahmad ya kira sunanta sai ta mai da kallonta gare shi yace

"Basma ina jinki"

Basma ta share hawayenta ta gaya wa Yaya Ahmad abinda ke damun Aryan, sai dai bata gaya mishi matsalan da suke fuskanta ba yayin saduwa sai ta boye wannan.

Yaya Ahmad ya kurawa Aryan ido sai ya sun kuyar da kai zuciyarsa na masa zafi, nan take idonsa suka yi ja. Yaya Ahmad yace

"Basma d'auko key d'in motanki ki shirya ki tafi gida"

Da sauri duk suka zuba masa ido, d'aure fuska yayi yace
"Nace ki tashi kiyi abinda na sanya ki" ya fad'a maganar cikin tsawa, jikinta na rawa ta mik'e tare da fashewa da kuka.

Aryan mik'ewa yayi cikin fushi yace
"Me kake nufi da ta tafi gida ba tare da izini na ba?"

Murmushi yayi yace
"Saboda ba kada lafiya, ba zata zauna ba domin tabbas matsalan ka zai iya shafanta" yaya Ahmad ya fad'i hakan ne domin ya tunzura Aryan dan ya tabbatar da ciwon nasa. Aiko Aryan ransa ya k'ara baci.

Basma sai gata ta fito tana ta kuka, Yaya Aryan ya tare mata hanya ya kama hannunta gam, kansa ne yayi mugun sarawa sai ya rik'e Kan da d'ayan hannunsa, Basma tace

"Yaya Aryan ka barni na tafi ko zaka ji sauk'in abinda ke damunka"

Yaya Ahmad ne ya matso wurin ya fintsike hannun Basma, ya kama Aryan ya zaunar dashi tare da kama kansa da k'arfi, Addu'a ya fara tofa masa nan take ya ture Yaya Ahmad suka fara dambe. Basma ihu ta soma security da suke gidan suka fad'o falon a sukwane suka kama Yaya Aryan yana cijewa.

Yaya Ahmad ya fad'a kitchen d'in Basma ya d'ibo ruwa a cup ya soma karanta Addu'o'i yana tofawa a ciki, bayan ya gama ya soma watsawa Aryan a jiki, wani k'ara ya saki yana gunji, haka yayi ta watsa masa har sai da yayi shuru yana gunji.

Da sauri Yaya Ahmad ya kira Naufal yace
"Naufal kana ina ne? ina so kaje gidan Malam Hashim ku tawo tare dashi gidan Aryan Akwai Matsala ne" bai jira mai zai ce ba ya kashe wayan.

Cikin tashin hankali Naufal ya mik'e ya fito, gidan Malam Hashim ya wuce ya d'auke shi suka nufi gidan Aryan.

Sun isa gidan cikin sauri suka fad'a falon, Aryan yana jin shigowar su ya saki k'ara, Malam Hashim ya kunna karwashin wuta ya sanya wasu Magani a ciki ya soma turara d'akin, Malam Hashim ya fara karanto wasu Addu'a yana tofa masa, Aryan yana gunji ya fara magana

"Zan fita, Zan fita, Zan fita, karku k'ona ni"

Malam yace
Bama buk'atar kiyi magana ki tafi kawai"

"Ni bazan tafi ba saboda ina son Basma"

Ai Basma sai cikinta ya d'uri ruwa.

Malam yace
"Meyasa kike son ta sannan baki shiga jikinta ba saiki shiga jikin mijinta?"

"Saboda tana burgeni, tun tana k'arama nake bibiyarta don na shiga jikinta amma ban samu hanya ba, saboda a jikinta banida mazauni dan Kakansu Bukar ya shayar da jikokinsa magun guna na tsarin jiki gaba d'aya babu wani jinnu da zai iya cutar dasu"

"To meyasa kika Shiga jikinsa bacin Basma kike so?"

"Soyayyan Basma yasa na shiga jikinsa, shima na jima ina son shiga jikinsa, ran nan ya kwanta ba tare da yayi Addu'a ba har barci ya d'auke shi. shine na samu hanyar shiga jikinsa, kuma bana so ya kusanci Basma saboda son da nake mata banson kowa ya rab'eta"

"Kina mace maye da son shiga jikinsa, wannan ai ba soyayya bace, tunda kina cutar da shi, dan haka zan konaki da Ayar Allah"

"Kar ku kona ni zan tafi har Abada bazan dawo ba"

Malam ya watsa masa wani ruwan Magani, k'ara ya saki yana birgima nan take yayi shuru kamar ruwa ya d'auke. Aka sanya karatun Al'Qur'ani Suratul Bak'ara, nan take barci ya kwashe shi.

*Hmmm duk abinda wasunku ke zargi akan Sihiri akaiwa Aryan kunata zaigin su Mami, to ba Sihiri ke damunsa ba, ba ruwan Mami, Yaya Shureym, balle kuma Jidda.* 🤪

Bayan komai ya lafa Yaya Ahmad ya kira su Ammi ya shaida musu abinda ya faru. Cikin tashin hankali suka zo gidan su Aryan. Sun zauna jugum-jugum suna jiran Aryan ya farka, cikin ikwan Allah kuwa sai gashi ya farka yana mai Ambaton Allah, zama yayi yana kallon Mutanen falon d'aya bayan d'aya, yana kai kallonsa ga Basma da take kuka sai ya yun k'ura da k'arfi yace

"My Basma me ya same ki kike min asaran hawayenka"

Haka ya isa wurin ta ya kama hannunta ya mik'ar ya zaunar da ita a bisa cinyarsa, sam ya manta da Mutanan dake falon, Momy cikin jin kunya ta mik'e ta fita daga falon, Ammi ma fita tayi tabi bayan Momy, Yaya Ahmad yace

"To Love Birds hala ka manta da mutanan dake d'akin ne?"

Dariya yayi yace
"ba dole na manta daku ba, Pretty na tana kuka"

Duk sai suka sanya dariya, nan Malam Hashim ya bashi wasu Magani da zai yi amfani dasu wanka da sha sai hayak'i, sannan kuma ya bashi shawarwari akan ya kula da ibadansa da kuma yawai ta karatun Al'Qur'ani da Azkar, Yaya Aryan yayi masa Godiya, nan suka yi musu sallama gaba d'aya suka tafi Gida.

Yaya Aryan ya zauna gefen Basma yace
"Babyna Allah yasa na samu lafiya kenan, kin ga yanzu bana jin komai in ina zauna gefenki"

Hawaye ta share ta d'aura kanta bisa ciyarsa tace
"Myn wallahi na firgita da lamarinka sosai, insha Allah ka warke hakan bazai sake faruwa ba".

Nan dai suka samu suka karya, suka sake wanka, Aryan yayi amfani da magun-gunansa, sai suka dawo falo suka zauna suna hira suna soyewa abin gwanin sha'awa.

*Bayan Kwana Biyu*
Aryan ya warware sosai babu sauran wani damuwa, da dare ya siyowa Basma kayan ciye-ciye, suka baje a falo suka ci abinsu, bayan sun kammala ko wanne ya wuce d'aki domin yin shirin barci.

Wani Rigan barci Basma ta d'auko, ta d'aga sama tana kallon rigan, jin-jina rigar take yi tana ayyana wa a ranta
'Anya zan iya sanyata kuwa?'

Aryan daya jima da shigowa yana kallonta, yace
"Dama kin mai data kin aje, dan kar ta bani wahala wajen cirewa, ki bari gobe in Allah ya kaimu sai ki sanya ki min kwanliya da ita da dare kafin mu kwanta"

Da sauri ta juyo dan harta tsora ta, kunya ce ta rufeta akan maganan daya fad'a, maida rigan tayi ta ajiye.
Arya yazo bayanta ya tsaya, d'aukarta yayi tsak ya ajeta bisa gado.

*Nima daga nan nayo waje, na basu guri tare da yi musu saida safe.*

*Washe Gari*
Da misalin k'arfe shida na safe, Basma ce kwance bisa jikin Yaya Aryan yana lallashinta akan tayi barci, sai shagwab'a take zuba masa. Da kyar ya samu tayi barcin, sai ya gyara mata kwanciya ya ja mata bargo, ya sauka ya zauna gefen gado, dafe kansa yayi cike da mamakin yanda ya samu Basma a cikakken Budurwa, tambayan kansa yake

"Dama Basma bata tara da Shureym ba kenan, lallai Allah kaine Mai cikakken iko, hak'ik'a babu wani Sarki sai Kai, kuma Kaine Majib'icin dukkan Al'amuranmu, Alhamdulillah da wannan babban kyauta daka bani, nasan ba wayauna bane ba kuma dubara na bane".

Hawayen farin ciki ne ya sauka kuncinsa, ya shiga jero Addu'a tare da yiwa Allah kirari, saida ya karanto sunayen Allah D'ari ba d'aya, ya cika da salatin Annabi s.a.w, sai ya shafa.

Basma ta bud'e ido tana kallonsa, ashe barcin nata bai yi nisa ba, ta taso a hankali ta rugumeshi ta baya tace

"uhum, uhum, Myn yunwa nake ji ka bani abinci inci"

Jawota yayi ya birkito ta akan jikinsa suna kallon juna, hura mata ido yayi yace

"kina kallo na kamar zaki had'iye ni, ko d'an kunyan nan ma" runtse ido tayi yana dariya tace
"kai Yaya Aryan ka daina cewa haka mana ba ina sonka bane, Ni dai ka bani abinci zanci"

"tom bud'e ido muyi magana, me kike so in miki wanda zai saki farin ciki sosai, Hasken Rayuwata kin bani kyauta mafi girman kyauta wanda yazo min a bazata, Basma nayi mamakin samunki a cikakkiyar..."

Bai k'arasa ba Basma ta had'e bakinsu guru d'aya saida suka yi tsayin minti biyar, kana ta zaro bakinta a nashi ta kalleshi ido cikin ido, tace

"Myn Kai ne kad'ai nake so, kuma kaine Allah ya zub'a da zaka mallakeni, Yaya Aryan so nake muje Asibitoci, Gidan Marayu, da Gidan Kurkuku mu basu taimako da abinda Allah ya bamu, in kamin wannan kad'ai, zanyi farin ciki sosai mara yankewa".

Rungumeta tayi tsam a jinshi tamkar zai maidata cikinsa, wani sabon So da K'aunarta ke k'ara ratsa zuciyarsa yana yad'uwa a duk sassan jikinsa.

_*To Readers nasan yau dai na saku farin ciki*_☺

*Rahma Ce*
[8/15, 8:45 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*

_page_ *36.*

_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*

*Bayan Mako D'aya*

Aryan da Basma sun murmure sunyi kyau sun fara kumari, kwance suke bisa gado Aryan yace

"My Queen nan da Mako guda Insha Allah zamu je Makkah muyi Umara tare da Honey Moon, amma fa na yin Ibada, sannan Gobe Insha Allah zamuje Asibitoci domin in cika miki alkwarinki"

Kallonsa take cike da So da K'auna tace
"Myn Godiya nake Allah ya k'ara maka Bud'i na Alkhairi yasa kafi haka"

"Ameen My Pretty" sai ya rungumeta tare tayi mata sumba a goshinta. Daga nan kuma suka yi Addu'an barci, cikin minti goma Basma barci ya d'auketa. Shima ba dad'ewa barci ya kwashe shi.

Saura kwana Uku su tafi Makkah, suka zagaye dangi tare da yi musu Sallama, har Kano sunje sun kwana d'aya, suka je Kaduna ma suka kwana washe gari suka dawo Abuja, a gidan Abba suka yini kowa na farin ciki da sauyawan su, sunyi kyau da k'iba gwanin sha'awa, sai dare suka koma Gida.

Ranar da zasu tafi, harda su Momy suka yi musu rakiya, Basma har kuka tayi saboda kewar 'Yan uwanta. A cikin Jirgi Aryan ya rungumeta a jikinsa yana lalla shinta har barci ya d'auketa.

*MAKKAH*
Sun samu masauki a hotel d'in kusa da Harami, suka yi wanka a tare sannan suka ci Abinci, Basma ta shirya cikin jallabiya Brown mai ratsin fari a jiki babu kwalliya fuskarta amma tayi kyau, sannan ta shirya Aryan cikin doguwar jallabiya fara da farar hula, ta sanya masa turare, tana murmushi tace

"My Aryan ina kishi ka fita domin gaskiya Mata karsu kallen min kai, dan ba k'aramin kyau kayi ba"

Murmushi ya sakar mata yace
"ai kema kinyi kyau sosai, ji yadda Jallabiyar ta amshi jikinki, nima gaskiya ina kishi dan haka Nik'af zaki sanya"

Dariya ta sanya tace
"Nik'af? bazan iya numfashi a ciki ba Allah kuwa, ban tab'a d'aurawa ba, Ni koda nayi Islamiyya bana sayawa sai dai ina sanya Hijab har k'asa da safa, amma bana iya sanya Nik'af, kuma ai fuskata ba kwalliya"

Dariya shima yayi yace
"Ai fuskarki ko ba kwalliya kyanki na nan, amma naji baza ki saka ba, sai dai zaki rik'a d'aure fuska kina bonewa"

Dariya ta kyalkyale da shi ta fad'a jikinsa, rungumeta yayi kamar bazai sake ta ba sai da suka yi minti biyu a haka kana suka saki ajiyar zuciya a tare yace

"kin ga tashi mu wuce masallaci" Ba musu ta mik'e suka wuce masallaci.

Sun duk'ufa wajen yin Ibada da yiwa Allah Godiya bisa Ni'imomin da ya basu, sannan kuma da Addu'an Allah ya k'ara musu zaman lafiya acikin zamansu ya barsu tare har a Aljanna, ya saka wa iyayensu da gidansu Aljanna. Sun rokawa dukka nin Al'umma Musulmi da kuma samuwar zaman lafiya a K'asar mu Nigeria da dukkan Duniya gaba d'aya. Nima dai na taya su da "Ameen Ya Rabbi"

*Bayan Mako Guda*

Suka wuce *MADINAH* dan ziyaran Masallaci Monzon Allah S.A.W. Basma ta kira Hajiya Kaltum ta sanar mata da zuwansu, cikin farin ciki tace su tawo gidan ta. Anan suka samu masauki da kyakkyawan tarba.

Bayan sun natsa, Basma ta kwashe labatinta tas ta bata Hajiya Kaltum, ba k'aramin mamaki tayi ba da labarinta, tace

"Ashe Basma ke *YAR SHUGABA* Ce, lallai rauyuwa kenan, da ace da farko na rik'e ki da wulakanci da baza ki Ni meni ba, Naji dad'i sosai kuma Nagode" Nan dai suka cigaba da hira.

A masallaci suke kwana danyin Ibada. Satin su biyu a Madinah suka shirya dawowa Makkah, Basma Check d'in kud'i ta rubutawa Hajiya Kaltum masu yawa wanda ni kaina ban san yawansu ba, ta bata ta ciresu a bank, dan cigaba da kasuwancin ta, Hajiya Kaltum tayi mata Godiya harda kuka, kaya ta had'a ma Basma na gyaran jiki, ta kuma had'a mata da guzirin wasu kayan. Cikin farin ciki da kewar juna suka baro Madinah, shima Aryan ya yaba sosai da Mutuncin Hajiya Kaltum.

*MAKKAH*
Sati guda suka k'ara a Makkah suka shirya dawowa k'asarmu Nigeria. Watan su guda kenan a K'asa Mai Tsarki, Basma sunyi Ibada sosai sunyi kuma Honey moon cikin Soyayya da K'aunar Juna. Haka suka tarkato zuwa K'asarmu Nigeria.

*Nace "Allah yasa Basma ta kwaso guziri mai Albarka a Makkah".* Lol☺

*NIGERIA*
Jirginsu k'arfe Biyar na yamma ya sauka, su Yaya Ahmad, Yaya Naufal, Meena, Deeja, Na'im da Anwar sune suka je tarbansu.

Gidan Abba suka wuce gaba d'aya da kayansu, gida ya hautsine da murnan dawowarsu, a falon Abba duk suka zaune, Abba ya sauko suka gaishe shi, yayi musu barka da dawowa. Nan hira ta b'arke a tsakaninnsu sai gab da Sallan Magrib kowa ya watse, su Basma suka shiga d'aya daga cikin d'akin dake Falon Abba suka yi wanka suka sauya kaya.

Bayan Sallan Isha'i  a part d'in Abba suka ci Abinci duka mutanan gidan, Yaya Ahmad yace

"In kun kimtsa zan mai daku gida"

Yaya Aryan yace
"Ai ni na kammala, dan na gaji ina buk'atar in kwanta da wuri"

Yaya Ahmad yace
"Basma ke fa?"

Itama tace
"Na gama" Yaya Aryan yace
"Kayan tsaraban nan a barsu anan washe bari zamu zo, kowa a bashi tsarabansa".

Sun shiga Mota sai suka fita gate, Yaya Ahmad ya wuce dasu k'ofar wani Gida dake kusa da gidan Abba, Aryan ya juyo da sauri yace

"ina zaka kaimu kuma? Don Allah ka kaimu gida mana, muna buk'atar mu huta, ka bari Gobe in Allah ya kaimu in munzo sai mu shiga nan d'in"

Dariya Yaya Ahmad yayi yace
"mai kake ci na baka na zub, Ni dai ku zuba min ido kurum"

Basma da Aryan suka had'a ido sai basu ce komai ba. Hon yayi Mai Gadi ya bud'e wangameman Gate, shiga yayi tare d'ayin kwana ya d'anyi tafiya kad'an, Manyan flat guda Uku ne a cikin Gidan, ko wanne da gab a tsakanin su, da kuma k'ofar shiga. Parking yayi a flat na tsakiya ya fito, key ya ciro a aljuhunsa ya bud'e k'ofar da zai sa dasu da cikin gidan yace

"Ku fito mu shiga mana"

Ba musu suka shiga, tafiya suka yi kad'an ya sadasu da k'ofar babban falon, ya bud'e k'ofar da key kamshin turaren wuta mai dad'i ya daki hancinsu, Yaya Ahmad ya shiga suma suka bishi a baya, kujerun Falon su na wancen gidan suka yi arba dashi, cikin mamaki Yaya Aryan yace

"Ya naga kayanmu a nan kuma?"

Yaya Ahmad ya zauna yana murmushi yace
"nan kuka dawo, gaba d'aya kayanku dake wancen gidan mun dawo muku dashi nan, muma nan mu ka dawo, flat na farko na Naufal ne, na biyu naku ne, na uku kuma nawa ne, munk'i tarewa munce sai kun dawo kun fara shiga kafin mu dawo, Abba ya gida mana shi"

Cikin farin ciki Basma ta mik'e ta shiga bin d'aku nan tana kallo, murna fal cikinta dan tsarin gidan yayi mata, katon falo ne sosai mai d'auke da d'akuna guda hud'u, ko wanne da toilet a ciki, an kuma sanya Furnitures a ciki, ga katon kitchen a falon da extra toilet. Daga cikin kitchen d'in akwai wani d'aki shine store d'insu, shak'e yake da kayan abinci da masarufi. A takaice gida ya tsaru yayi kyau sosai dan yaji kayan Alatu da more rayuwa.

Yaya Aryan ya soma Godiya, Yaya Ahmad yace
"Ka rik'e Godiyan ka, in ka bad'u da Abba kayi masa" ya mik'e yana Dariya, Yaya Aryan yayi masa rakiya, suna gabda barin falon Yaya Ahmad ya juyo yace

"Basma akwai swimming pool ta baya, akwai kuma Lanbu in kin za gaya ta bayan gidan, za kiga k'aramar k'ofa da zai sadaki da lanbun" Yana gama fad'a bai jira mai zata ce ba ya fita.

*Washe Gari*
Sun had'u gaba d'aya a gidan Abba, suka yi masa Godiya da gidan da ya sauya musu tare dayi masa Addu'a sosai, sun raba tsaraba gaba d'aya, harda na Mutanan Kano da Kaduna sun ware musu. A ranar su Yaya Ahmad da Yaya Naufal suma suka tare a Gida jensu.

*Da dare*
Basma da Yaya Aryan suna zaune a falo, Basma tayi pillow da cinyansa yace mata

"My Queen akwai wani shawara dana yanke, nasan kema zai miki dad'i in kika ji"

Basma ta tattaro natauwarta tace
"Ina jinka Myn"

"Yauwa Babyna, dama so nake ki had'u dasu Meena ku bud'e wata organization na taimakon Al'umma, Nak'asassu, Almajirai, masu k'ara min k'arfi, marasa lafiya da dai tallafawa Talakan K'asarmu baki d'aya, ta wannan hanyar ne za muyi amfani da dukiyar da Allah ya bamu domin mu nima Lahiranmu da shi, kinga Ni dasu Yaya Ahmad sai mu rik'a jagorantar ku akan abin, amma me kika gani?"

Wani farin ciki ne ya rufe ta, sai ta mik'e ta zauna tare da sumbatarshi a kumatu ta gyara zama tace

"Yaya Aryan ka sani farin ciki sosai Wallahi, na dad'e ina tunanin wani hanya zanbi dan taimakon Al'umma A matsayina na *'YAR SHUGABA* dan haka wannan shawaran naka yayi, Gobe Insha Allah zan tattauna dasu Meena".

" Masha Allah da kika

Please Login or Register in order to submit comment