Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi mai isanta kana ta shiga bayi dan tayi wanka, zuciyarta na nazarin abinda yasa Abba ya hanata ganawa da 'yan uwanta.

Da dare Momy ce zaune a falon Abba sai Basma, magana Momy ta shiga yi tace
"Basma anya kina jin dad'in zama da Shureym kuwa? In yana miki wani abu ki gaya min" murmushi Basma tayi tace
"Momy ba komai" kallonta tayi sosai tace
"Basma ada ba kya b'oyemin matsalanki, amma meyasa yanzu zaki b'oyemin?" murmushi ta kuma yi tace
"Momyna ba komai fa" murmushi kawai Momy tayi tace

"to shikenan, ki dai k'ara hak'uri, aure ba abin wasa bane ibada ce ta samun Aljanna, sannan ina mai gargad'inki Basma akan k'in amincewa da kika ki yi dashi a matsayin mijinki, ina ganin shine dalilin da yasa ya k'ulla miki sharri, dan haka a kul d'inki ki tabbbatar kin bashi hakk'insa, mijinki ne kuma halas d'inki ne, nasan baki sonsa amma ki sanya a ranki shine wanda Allah ya zab'a miki, dan haka ki amshi k'addarar ki sai Allah ya baki ladan akan haka, kuma duk inda kike ki rike mutuncinki dana aurenki"

Kuka Basma ta shiga yi, tana cewa a ranta
"duk yanda zan fahintar daku akan zamana da Shureym ba lallai wasu su gasgata ba, domin ya riga yamin mugun tabo wanda inna fad'a za'a ce na fad'a danna kare kaina ne, bana so kusan komai yanzu sai nan gaba kad'an a lokacin da kowa zai gasgata magana ta"

A fili tace
"insha Allah Momy zan ki yaye, nagode da kika aminta dani, kika bani yardanki a lokacin da kowa yaki yarda dani, Momy na Allah ya biyaki da gidan Aljanna" rungumeta Momy tayi tare da sanya mata albarka.

*Washe Gari*

Su Basma sun fito zasu koma America, iyayan nasu suka k'ara musu nasiha, kana gaba d'aya gidan suka tafi rakasu zuwa airport.

Basma ta tsaya gaban Yaya Ahmad tace
"Yayana zan tafi na barku zanyi missing d'inka sosai" murmushi yayi mata yace
"kin san ni kullun cikinsa nake, Allah ya kare ki daga duk kan abin k'i" saita rungumeshi tana fad'in "Ameen" a haka tayi ta bin kowa tana musu bankwana, tana zuwa wurin Abba sai ta rungumeshi ta soma kukan shagwab'a, Abba murmushi yayi yace
"Queen Basma ai bata kuka, dan haka ta daina b'ata hawayenta Abbanta kullun yana tare da ita" murmushi tayi na jin dad'i tace
"Abba ka daina fushi dani ko?"
"kwarai kuwa, ba kiga yau rakiya harda ni ba, ai na huce tun jiya, Abbanki bazai iya dogon fushi dake ba, dan haka ki kwantar da hankalinki, Abbanki na sonki" murmushi tayi tace
"nagode Abbana"

Bayan tayi sallama da duk family d'in ta, sai suka wuce suka shiga jirgi tanata waigensu, tana d'aga musu hannu. Suna shiga jirgi ta fashe da kuka mai tsanani.

Tsanar Shureym ya dad'u a ranta, ayyana irin abinda zata yi ta rama take a ranta, a haka har barci ya kwasheta, sai da jirkinsu ya sauka ta farka. Haka suka wuce gida a tsakaninsu babu um babu um-um.

Suna isa Safeena ta rungume Shureym, cike da farin ciki tace
"nayi kewarka Mijina, da fatan babu wani damuwa" murmushi yayi yace "babu" cikin tsokana Basma tace
"Acici baki ganni ba ne, tom na dawo sai kiyi hak'uri Addu'anki baici ba" d'aure fuska tayi tace
"nifa bana son rashin kunya waye acicin?" dariya Basma ta kwashe dashi, Shureym yayi mamakin ta yanda ta saki kamar ba ita bace mai kuka d'azu, tace

"haba Anty Safeena meye na d'aukan wuta, nifa ba ruwana da fad'a yanzu, in zaki sauko mushirya tom" murmushi Safeena tayi ta kalli Shureym tace
"halan an zane ta sosai shiyasa ta koyi ladabi" murmushi yayi bai ce komai ba, Basma tace
"ni dai bari naje nayi wanka nazo muyi hira, dan naga surutunki zai hana ni yin abinda ya kamata" tana gama fad'an haka tayi gaba abinta, tana dariya wanda ni mai rubutu ni kad'an nasan ma'anarsu.

Sake baki duk suka yi suna kallon Basma, zama Shureym yayi ya bama Safeena labarin komai, murmushi tayi tace
"lallai kace abun yaso ya jawo damuwa, to Allah ya kyauta, shiyasa naga Basma ta sako" Shureym yace
"tunda ta sako kema sai ki sako a zauna lafiya, ni fa a gaskiya dama ina son Basma, kawai dai bana son b'acin ranki ne" d'aure fuska Safeena tayi tace
"to kayi ta sonta mana sai me" murmushi yayi ya mik'e ya bata wuri, dan yasan ya tsokano fad'a.

Basma tana gama shiryawa ta fito falo, danbun nama ta dibo a plet da yawa tana ci, zama tayi a kan kushim tace
"Anty Safee ga danbun nama ko zaki ci" galla mata hara tayi tace
"kina zaune a gun saki ce min in ci, ki zuba min ki bani in kina son naci" dariya tayi taje kusa da ita ta aje plet d'in tace
"mai da wuk'ar, gashinan kici, ni bari na shiga kicin na d'aura mana abinci, dan yanzu ba zan yarda kuku na mana girki ba" Safeena sakin baki tayi tace
"ikwan Allah, Basma an girma anyi hankali" juyowa tayi tace
"haba Anty Safee, me kika mai dani ne, dama can da girma na" dawowa tayi gabda Safeena sai ta d'auketa photo a wayanta, tana cin dabmun nama, hasken wayar yasa ta d'ago tace
"kambu d'aukata kike ko?" dariya tayi ta k'ara d'aukanta, sai da tayi mata kala biyar kana ta dena, tace
"zan aje miki ne in kin haihu na nuna miki, a lokacin da kike kwad'ayin Danbun nama" tana gama fad'an haka ta shige kicin tabar Safeena cike da mamaki.

Tana shiga kicin ta tsaya ta zab'i hoton da Safeena ta fito sosai a ciki, saita goge sauran, kyakkyawan murmushi yayi, sai ta shiga d'aura abincin daren.

*Bayan Sallan Isha'i*
Su Shureym ne zaune a dinning Safeena na gefen damansa, Basma na dayan gefen hagunsa, suna cin abincin da Basma tayi musu, delof d'in kuskus da hanta wanda yaji kayan lanbu, sai farfesun kayan ciki da kuma juice d'in kwakwa wanda yasha madara.

Santi dukansu suke yi amma banda Basma da taketa musu dariya, tashi tayi ta shiga d'aukarsu photo tace
"gwara na d'auke ku in rik'a kallon lokacin da kuke santin abincina na farko da kuka fara ci" basu kawo komai aransu ba sai suka yi ta dariya, Basma murmushi tayi kawai, ita kad'ai tasan me take kitsawa a ranta.

Bayan sun kammala cin abinci, suka koma babban falonsu suka zauna, Yaya Shureym ya shiga yi musu bayani

"Safeena da ke da Basma Ku duk matana ne, ina so mu mance rayuwar da muka fara a baya, mu dawo mu soma rayuwa na aminci da juna, Basma ki yafemin muzguna miki da nayi, sannan nagode da kika rufamin asiri akan aurena da Safeena da kuma abinda nayi miki, ke Safeena ki d'auki Basma a k'anwarki, ke kuma Basma ki d'auki Safeena a matsayin Yayarki, dan Allah mu kiyayi b'atawa juna rai, dan haka yanzu zan raba muku kwana, ke Basma tunda na aureki ban tab'a kwana a d'akin ki ba, dan haka zanyi miki sati d'aya na amarcin da banyi ba, ke kuma Safeena sai kiyi hak'uri in na gama kwanakin, sai na rik'a kwana biyu-biyu a ko wani d'aki, in kuna da magana sai kuyi"

Safeena tace
"ba komai Shureym nima na yada makaman yak'i na, na d'auki Basma k'anwata, dan haka na yarda kayi mata kwankin Amarcinta" Basma kuma tace
"Nagode Yaya Shureym nagode Anty Safeena, sai dai zan nima afwanku akan cewa, yau na fara period kuma ina yin tsawon kwana shida kafin na gama, dan haka nace me zai hana ka rik'a kwana a wurin Anty Safeena, in period d'in ya d'auke sai kayi min kwana kin Amarci na" saita k'arasa maganar da sun kuyar da kai k'asa, alaman jin kunya, dariya duk suka yi Shureym ya kalle Safeena yace

"me kika ce game da bayanin Basma" murmushi tayi tace
"sai abinda kace tunda kaine Mai gida" dariya yayi na jin dad'i yace
"shikenan mun karb'i uzurinki, in ya so bayan kwana shida saiki amshi girki" farin ciki ne ya lullub'e Safeena, domin dama bata jin zata kwana ita kad'ai a d'aki dan tanada b'ukatar mijinta.

Nan dai suka shiga hira, Basma ta mik'e tace
"bari na mana salfee" sai duk suka mik'e suka shiga d'aukar hotuna, wani ta d'auki Shureym da Safeena suna dariya ga katon cikinta ya fito, wani yana rungume da Safeena, wani kuma su d'auka su uku selfee, wani kuma Safeena ta d'auki Basma da Shureym. Bayan sun gama Basma ta yi musu sallama ta wuce d'aki, suma d'aki suka wuce dan yin shirin barci.

Basma tana shiga d'aki ta rufe da key, tsalle tayi akan gado ta kwanta, tare da yin murmushi, can kuma sai ta fashe da kuka....

*Tofa wai me Basma take shiryawa ne*😳🤭

*Rahma Ce*
[8/9, 5:48 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *22.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Da misalin k'arfe uku na dare, Basma ta tashi ta gabatar da sallan Nafila, Addu'a tayi da niman yardan Allah akan abinda take shirin yi, haka ta zauna tayi ta tasbihi, har gabanin sallan Asubahi, kana ta k'ara yin alwala tayi raka'atanil fijri, sannan ta gabatar da sallan Asubahi, azkar ta karanta, sai ta tashi ta nad'e sallaya, idonta a rufe ta fad'a gado, murmushi ta saki, a ranta tace

"ashe ma Yaya Shureym mugun wawa ne, da nasan haka yake da saukin kai da tuni nasan abinyi, wai su sun d'auka da gaske period nake, hmm kana tunanin cin zarafin da kayi min da sharrin da kamin kasha ni masilla ne, wlh saina d'auki fansa mafi muni a gareka, azzalumi kawai" tsaki taja saita gyara kwanciya, cikin k'ank'anin lokaci barci mai nauyi yayi gaba da ita.

Sai k'arfe goma na safe ta farka, wanka tayi ta shirya cikin riga da sket English wears, ba wani makeup da tayi, fitowa tayi taga su Yaya Shureym suna Karin kumallo, murmushi ta sakar musu saita k'arasa wurin taja kujera ta zauna, gaishe su tayi suka amsa cikin kulawa, tace
"kuyi hak'uri na makara ban tashi da wuri na had'a mana breakfast ba" murmushi Safeena tayi tace
"Basma kenan, karki damu ai nice da girki, nasa kuku ya had'a mana tunda ni gaskiya bana girki" Basma harta kai hannunta zata jawo food wormer sai ta janye hannunta jin Safeena na fad'in kuku yayi musu breakfast, da sauri tace
"gwara da ban zuba ba, dan bazan iya cin girkinsu ba" mik'ewa tayi ta wuce d'aki, shi dai Shureym saurarensu yake yi yana kai loman abinci, a ransa yana yabawa Basma

"yanda take k'ok'arin yin abinci da kanta duk irin matsayinta da take dashi na 'YAR SHUGABAN K'asa, amma ita Safeena ba 'yar kowa ba sai iyayin tsiya, k'ilama bata iya bane, dan Ni ban tab'a cin girkinta ba"

Maganar Basma shine ya dawo dashi daga zancen zuci da yake, tace
"Yaya Shureym bari naje naci abinci" kallonta yayi sama da k'asa yace
"amma kinsan yanzu ba zan yarda da wannan fitan naki ba ko" marairaice fuska tayi tace
"yaya takeway kawai zanyi na dawo" d'aure fuska yayi yace
"ni bawai fitan bane damuwa na, kawai bana so ki had'u da d'an iskan saurayinki d'in nan ne" idon Basma ya ciko da kwalla bata ce komai ba, saita juya zata koma d'aki, dakatar da ita yayi yace
"kije amma na baki minti talatin, in kika bari ya wuce, to kinfi kowa sanin hukunci na, bawai na bari bane sanyi kawai nayi" bata tanka mishi ba, ta wuce abinta tana kissima abinda zata aikata mishi.

Tana fita studio ta wuce, wayarta ta basu ta nuna masu hotunan da take so a wanke mata, tana gama musu bayani ta wuce siyan abinci. Cikin sauri ta dawo ta basu kud'insu ta karb'i hotunan da wayarta, ta adana su a jaka, kana ta fita cikin sauri, taxi ta tara ya sauketa a gida ta shiga da sauri.

Ta taddasu a falo,
"sannunku da hutawa" tace, kana ta nufi d'akinta, Yaya Shureym ya dakatar da ita, damm taji gabanta ya fad'i, amma saita dake ta juyo, kallonta yayi yace
"amma kinsan kin d'auki kusan minti arba'in ko, daga siyan abinci shine zaki d'auki wannan lokacin" marairaice fuska tayi tace

"haba Yaya Shureym, kasan k'asar nan bafa Nigeria bane, duk yanda na tadda layi sai an sallami wanda suka rigani kafin a bani, su ba ruwansu da cuwa-cuwa, kuma bada motan gida na fita ba, da taxi ne"

Kallonta yayi a takaice kana ya d'auki telephone ya kira masu gadin gidan, tare da duk ma'aikatan gidan, bayan sunzo yace tare da nuna Basma
"karku sake ku bar wancen ta fita a gidan nan sai in na baku izini" duk wannan bayani a cikin harshen turenci yake musu, cikin girmama suka amsa masa kana ya sallamesu suka fita, mik'ewa yayi ya zo inda ta tsaya kana ya amshi ledan take away d'in, yace
"muje na taya ki ci" gabanta ne ya shigo dukan uku-uku, burin ta karya buk'aci ganin abinda ke cikin jakarta, haka suka jera suka shiga cikin d'akin, Safeena wani bak'in kishi ne ya tirnik'eta, tsaki taja tace

"ni sam bana burin wata mace ta rab'i Shureym, amma shegiyar yarinyar nan ta zame mini k'arfen k'afa, bari mu koma Nigeria saina raba wannan Auren, dan in ba haka ba, Shureym ya sameta kashina ya bushe, dan na shiga uku, dani da banza duk d'aya ne a gunsa" mik'ewa tayi ta wuce d'akinta cike da damuwa.

Suna shiga ya fincikota, a tsorace ta kalleshi, jakanta ya amsa, ai Basma Addu'a ta fara yi a cikin ranta domin ta gama tsorata, duk tunaninta bud'e jakar zai yi, da mamaki sai taga ya aje akan dressing mirror din ta, wani ajiyar zuciya ta saki a hankali, dawowa yayi wurinta, hannunta ya kama suka zauna kan kujera, jawota yayi kan jikinsa wanda har tana jin saukar numfashinsa a gefen kuncinta, juyo da fuskanta yayi, suka kalli juna ido cikin ido, sha'awar Basma ce kwance a kwayar idon Shureym, itama kuma tsana ce kwance a cikin kwayar idonta, bata ankara ba saita ji ya had'e bakinsu, ya soma sumbatar ta, duk yanda taso kwace kanta ta kasa, k'arshe hak'ura tayi sai da yayi iya ka yinsa kana ya saketa, kuka taso yi amma saboda karta nuna damuwa saita shanye su, mik'ewa yayi yace
"daga yanzu wannan ne irin hukuncin da zan rik'a miki, in dai kika sab'awa umarni na" sai ya fice.

Da gudu ta mik'e ta shiga bayi, brush ta soma yi tana dirjan harshenta, tana yi tana kuka, takai  kusan minti Sha biyar tana aikin abu d'aya, sai da taji bakinta ya soma yi mata zafi kana ta dena brush d'in, wanka tayi ta fito ta sanya kaya marasa nauyi, saita rufe k'ofarta, ji tayi bata jin yunwa, abincin da ta siyo saita sanya a fridge, d'auko wannan jakar tayi ta ciro diary d'inta, ta shiga rubuta labarin fitanta da Bilal, da harya kawo mata ice cream data manta a motansa, Yaya Shureym kuma daya ganshi ya kulla mata sharri, dama ta rubuta labarin tun farkon had'uwarta da Bilal a cikin diary d'in, saita d'aura da labarin bayan dawowarsu daga Nigeria, haka ta rubuta komai abinda ya faru, sai ta sak'ala hotunan data d'aukesu a cikin diary. Maida shi tayi majiyansa, saita mik'e ta dumama abincin da ta siya a microwave, bayan ta gama ta gabatar da Sallan Azahar sai ta bi lafiyan gado.

*Kasar Monaco*
Jidda ta matsawa Aryan wanda duk iya wulakanci yayi mata, amma tak'i rabuwa dashi, k'arshe dole ya sakko suka cigaba da mutunci kamar yanda ya buk'ata, don ya sanar mata shi sam ba zaiyi soyayya da ita ba, Aryan yayi waya da Umma ya sanar mata saura wata Uku ya dawo Nigeria, tayi masa Addu'a sosai kana tayi masa fad'a da nasiha akan jin tsoron Allah, yayi mata godiya yace  "Umma inna dawo zanje Gombe na dawo dasu Malam da Inna su dawo wurinmu mu zauna dasu" Umma tayi farin ciki sosai tace  "gaskiya ne, tunda Allah ya bud'a mana yanzu sai su dawo kusa damu, in ya so duk bayan lokaci sai mu rik'a zuwa Gombe muna gaisawa da sauran dangin mu". Nan suka yi sallama tana sanya masa Albarka.

*Nigeria*

Abba ya tattauna dasu Ammi da Momy akan zancen Basma, ya bama Momy hak'uri akan abinda ya faru, sun sasanta kansu kana ya gargad'i kowa akan kar abari su Meena suji komai, kamar yanda suka yanke da sauran iyayen kafin su tafi. Haka aka rufe maganar ba tare da sun fitar dashi ba.

Deeja ta damu Yaya Ahmad akan ya sanar mata abinda ke faruwa, hak'uri ya bata yak'i gaya mata, duk yanda su Meena suka so jin abinda ke faruwa amma ba suji komai ba a wajen mazajensu, k'arshe hak'ura suka yi da niyyar tambayar Basma, sun kira ta, itama tak'i gaya musu tace  "ku kwantar da hankalin ku, za kuji komai nan gaba kad'an" dole suka hak'ura badan sun so ba.

*America*
*Bayan kwana Hud'u*

Ya kama yau kwana biyar kenan da dawowar su Basma, cikin dare Basma ta tashi ta d'auki Jakar da diary d'inta ke ciki, ta gama sanya duk abinda ya kama, ta sanya wayar da take amfani wajen d'aukansu Yaya Shureym a ciki, ta barta a kunne, sai ta sanya dukkan gwala-gwalan zinarinta a ciki da hayan amfaninta, saita ta kulle jakar.   Tashi tayi ta shiga had'a kayanta gaba d'aya a cikin trolley guda uku, hatta takalmanta bata bari ba, bayan ta kammala tas, sai ta sanya duka trolley d'in a cikin kitchen dinta ta kulle, Sallan Nafila ta gabatar, ta shiga kwararo Addu'a akan abinda take shirin aikatawa, Allah ya bata sa'a ya taimaketa, Sallan Asubahi aka kira ta gabatar da raka'atanil fajri, sannan tayi Sallan Asubahi tayi azkar na safe, saita tashi ta sanya sallayan a cikin d'aya daga cikin trolley, gado ta fad'a ta kwanta ta soma sharb'an barci.  

*Da safe*

Misalin k'arfe tara na safe, Yaya Shureym yazo yana buga mata k'ofa, kamar bazata bud'e ba saboda barcin da take ji, zuwa tayi ta bud'e k'ofar tace  "Yaya Shureym lafiya kake buga min k'ofa? wlh barci ke damuna" cikin murmushi yace   "Lafiya lau, ina so ki d'an had'a mana breakfast kafin mu dawo daga asibiti, zan kai Safeena ne ba ta jin dad'in jikinta, daga nan za'ayi mata awon ciki" murmushi tayi tace "tom Yaya Allah ya bata lafiya" fitowa tayi ta tadda Safeena a falo sannu tayi mata saita amsa a yatsine, murmushi Basma tayi tace a ranta  "kisha kuruminki Malama, yau zan bar miki mijinki" a fili kuma tace  "d'an Baba yana baki wahala, Allah dai ya raba ku lafiya" ta amsa a takaice kana suka wuce.   Kitchen Basma ta shiga, ta gayawa kuku Breakfast d'in da take so su had'a musu, kana ta koma d'aki da sauri, ta shiga fito da duk trolleyn ta falon, ta aje a bayan kujera, saita rufe su da wani zani. Wanka ta tayi, ta sanya doguwar riga bak'a mai aiki purple, sai ta yi rolin da farin gyale tayi kyau sosai, d'akinta ta bud'e ta fita farfajiyan gidan da gudu a tsorace tana ihu, da sauri duk ma'aikatan gidan suka fito, cikin harshen turanci ta shiga gaya musu  "wani Abu ne a d'aki na Ku taimakeni Ku ciremin" suka tambayeta  "me ta gani" tace  "Ni bazan gane ko miye ne ba"  Da sauri duk suka shiga falon suka soma dubawa, d'akinta suka shiga su duka, da sauri tabi bayansu, k'ofar ta jawo da k'arfi ta sanya key ta rufe su, cikin sauri taja trolleyn kayanta har waje, ta bud'e gate ta fitar dashi, a haka harta fidda kayanta duka, su Ema sai ihu suke akan ta bud'e su, kyalkyacewa tayi da dariya ta d'auki hand bag dinta ta fice abinta, tana fita ta samu taxi ya kwashe mata kayanta sai airport. Suna isa ta ja kayanta, zuwa minti sha biyar an gama checking kayansu sun shiga jirgi, minti goma da shigansu jirgi ya daga zuwa k'asarmu Nigeria.✈  

*Su Basma an shuka tsiya😂😜, koya cakwakiyar zai kasance sai kun jini a next page...*  

*Rahma Ce*
[8/10, 5:30 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *23.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Jirgin su Basma ya sauka lafiya, drop ta d'auka taxi, ya kaita asibitin da Yaya Ahamd yake aiki, nan ta bufa, ta ciro trolley d'inta guda biyu da kuma wannan bak'ar jakar da diary ke ciki, ta jasu zuwa cikin asibitin, gefe ta tsaya ta samu d'aya daga cikin masu gadi yana ganinta ya washe baki dan ya ganeta suka gaisa tace
"aam Baba Dr Ahmad yana ciki kuwa? cikin ladabi yace
"yana ciki, motansa yana cikin wancen barandan yayi parking d'inta"

Murmushin jin dad'i tayi sai ta ciro wata farar takarda mai d'auke da wasik'a a ciki tace
"Baba Dan Allah ka taimaka ka kai masa wannan kayan, sauri nake jirgi na jirana, ka gane ni ai?" cikin dariya yace
"kwarai Hajiya na gane ki" murmushi tayi ta k'irga dubu Ashirin ta bashi tace
"Baba ga wannan saika ci goro ko" jiki na rawa ya amsa yayita shi mata da albarka, kiran wani matashin saurayi yayi d'aya ne daga cikin drivern asibiti, yayi masa umarni daya d'auki d'aya daga cikin trolley, shi kuma Baba yayi mata sallama ya sanya wasik'ar a aljiunsa, kana ya d'auki d'ayan trolley da kuma bak'ar jakar suka shiga cikin asibiti.

Basma binsu tayi a baya har saida taga sun isa k'ofar office d'in Yaya Ahmad, kana tadan tsaya, tana ganin sun Shiga sai ta juya cikin sauri ta isa bakin gate, taxi ta koma ta shiga, da gudu suka bar unguwar.

Mai gadi suna Shiga, Yaya Ahmad ya kalle su cike da mamaki yace
"Malam wannan kayan fa daga ina?" da dariya a fuskansa yace
"Uwar d'akinta tace na kawo maka" cikin mamaki yace
"wace uwar d'akin naka?" yace
"Basma mana, ita tace na kawo maka domin tace tana sauri ne ana jiranta, tace in baka wannan wasikar ma" saiya mik'a masa, cike da tsoro da mamaki Yaya Ahmad ya mik'e yace
"Basma kuma?" da sauri ya fita a office d'in, Baba mai gadi da d'ayan saurayin suka rufa masa baya, gate ya nufa yana hangen ko zai ga Motan da tazo a ciki, babu kowa bamu alaman wata mota, Baba mai gadi yace
"kaga ikwan Allah sun riga sun tafi, acan fa na hangi mota taxi wanda ya kawo ta, nima nayi mamaki dana ganta a cikin taxi" ajiyar zuciya Yaya Ahmad yayi ya shiga wasi-wasi da damuwa, komawa office yayi ya Shiga bud'e jakukunan, tabbas kayan Basma ne a ciki, bak'ar jakar ne ya nima bud'ewa amma arufe take babu key a jiki, zama yayi kamar wanda yayi aikin gajiya, dan jikinsa duk a mace yake, da kuma tsananin fargaba da zuciyansa yake ciki, bud'e wasik'ar ya yi, ya soma karantawa kamar haka...

*ASSALAMU ALAIKUM*

*Yaya Ahmad da fatan duk kuna lafiya, nasan zaka yi mamaki da ganin kayana ba tare da na bari mun had'u ba, Yaya Ahmad ina cikin damuwa na tsani rayuwar dana ke ciki, dan haka zanyi nesa da kowa ko zanji saukin abinda ke damuna, Yaya Ahmad kafi kowa sanin bana son auren da a kayi min, amma na hak'ura nayi biyayya gasu Abba, na d'auki alk'awarin yiwa Yaya Shureym biyayya in zauna dashi, amma kash sai dai shi a gunsa akwai mugun nufi a zuciyansa game dani, a ranar da muka shiga jirgi zuwa garin America lokacin aurenmu, anan cikin jirgi Yaya Shureym ya fara shayar dani ruwan bak'in ciki, wanda har yau ina cikin shansa, Yaya Ahmad na so gaya maka komai a wancen lokacin, saina ce bari nayi hak'uri bai kamata in fara kai k'ara ba, kuma ma duk abinda zan fad'a ba mai yarda dani akai, sai kai kawai nasan zaka yarda tunda kai kasan halinsa, d'aurewa nayi tun daga ranar dana tafi na bar gida har zuwa yanzu, Yaya Ahmad bari na tak'aice maka bayani, duk kan k'arin bayani da kuma labarin zamana a America yana cikin wannan diaryna na rubuta shi, da kuma wasu hotuna a ciki wanda zasu zame min shaida, duk a cikin wannan bak'ar jakan, akwai kuma wayata a ciki wanda akwai wasu hotuna a ciki, ga system d'ina ka aje min shi, key d'in dana baka rannan ka aje min shine mabud'in wannan jakar, ina so ka kai gida ka bayyana wa su Abba komai dake cikin jakar nan, tare da karanta musu wannan wasik'ar da kuma abinda ke cikin diary

Please Login or Register in order to submit comment