Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma na d'auki Aryan zai yi aiki a company Abbanmu, In ba damuwa"

Aryan cikin natsuwa yace
"Ayi haka kuwa? wannan dawai niya ai zata yi yawa, ga Deeja ga kuma ni" murmushi Yaya Ahmad yayi yace
"d'an uwa karma damu duk yiwa kaine" Aryan yace
mun gode Allah ya saka da Alkhairi" Umma ma godiya tayi harda yan kwallanta, Deeja ko murna ne kan murna, itama godiya tayi.

Nan fa hira ya b'arke sunata zan tawa, Amma fa banda Basma data takure, saboda irin nuna ko in kula da Yaya Aryan yayi mata, bayan minti talatin da zuwansu, Yaya Ahmad yace zai je wani wuri inya dawo zaizo ya d'auki Basma, nan yayi musu sallama Yaya Aryan ya rakashi waje, Basma ne ta juyo wurin Deeja tace
"saiki shirya ranar Monday da wuri zanzo domin mu tafi makarantan, ina so mu gama registration a ranar ne" cikin farin ciki tace
"insha Allah tun Asuba zan tashi na shirya da wuri" Umma tace
"da dai ya fi miki da wannan shegen barcin asaran da kike yi, to yanzu ga makaranta nan saiki cigaba da barcin mu gani" duk suka sanya dariya, Yaya Aryan ne ya shigo yace
"Umma wai ina furan ne? wallahi yunwa nakeji" da sauri tace
"af kaga na manta, da an dama Ahmad yasha kan ya tafi, ke Deeja d'auko min kwanan furan nan da kuma kindirmo had'e da sugar"  taje ta d'auko, nan Umma ta dama fura da nono da yawa, ta fara zubawa Basma a cup ta aje a gabanta, sannan sauran ta zuba musu.

Deeja ta mik'awa Yaya Aryan nashi yace
"mik'o min sugar na k'ara" ta mik'a masa ya k'ara, ya juya da kyau ya fara sha, duk suka fara sha banda Basma, Umma tace
"ya dai Basma yau na ganki wani iri ko lafiya?" dariya tayi tace
"Umma lafiya lau zan sha" Yaya Aryan ya mik'e ya shiga d'aki d'auko wani abu ya bar furan a wurin, yana shiga Basma tayi sauri ta d'auko furansa ta fara sha, Umma da Deeja suka sanya dariya ba tare da sunce komai ba, sun zuba ido suga drama ya Aryan zaiyi, yana fitowa yaga wurin wayam ba cup d'in furansa.

D'ago kan da zai yi, ya hango Basma tana sha hankalinta kwance, murmushi kawai yayi ya matsa kusa da ita yace,
"bani furana ai ba naki bane wannan" ko d'agowa bata yi ba, ta cigaba da sha, Khadija ce ta kwashe da dariya tace
"kai Yaya tunda ta d'auka naka sai kayi hak'uri ka d'auki nata kasha" d'aura fuska yayi ya harareta, sai ta gimtse dariyan da takeyi, Umma dai uffan ba tace ba, k'arshe ma tashi tayi ta shiga kicin dan ta duba tukunyarta, aiko tana shiga kicin ya saka hannu ya wafce kofin furansa, sai Basma ta sa kukan harda shagwab'a, ga hawaye na malala, mamaki ma ta bashi, Amma saiya dake ya koma ya zauna, murza gyad'a mai gishiri yayi, ya zuba a furan ya cigaba da sha, Umma ce ta fito daga abin mamaki, d'aure fuska tayi tace
"Aryan ba dai amsa kayi ba?" da murmushi fuskansa yace
"Umma ai ba nata bane nawa ne fa, shiyasa na amsa" d'aure fuska ta kuma yi tace
"banson shirme ita ma ba k'anwarka bace, shine baka barmata ba" aiko Basma ta samu goyon baya, sai ta kuma narkewa cike da shagwab'a tace
"Umma ni nashi zan sha ki ce masa ya bani" Umma taso tayi dariya Amma sai ta dake tace
"Aryan bata naka kayi hak'uri kasha nata" shima cikin yana yi na shagwab'a yace
"Umma nawa nake so na sha" Umma ganin zasu sa mata hauka sai ta shige d'aki ta basu guri, domin tasan da gan-gan Aryan yayi haka, zuciyarta ne ya fara mata zargin wani abu. Deeja ta dinga dariya a b'oye, haka Yaya Aryan ya shanye furan, harda lashe kofi, Basma na gefe sai kumbure-kumbure take yi.

*Nace ohhh su Basma ko ina akaje sai an raba hali lol.*😉😄

Deeja ta mik'e ta shige bayi, Yaya Aryan ya mik'e ya matsa kusa da ita ya d'auki furanta yace a hankali yanda Umma ba zata ji ba,
"Ga naki kisha kar kuda ya shanye miki, domin nima ban koshi ba, in baza ki shaba sai na shanye" hawaye cike a narkakkun idonta ta d'ago, sai suka had'a ido, ai gaba d'aya saita saukar masa da kasala, sun d'auki tsawon minti biyar suna kallon juna, ita tana masa kallon tuhuma "meyasa baka yafemin ba" shi kuma yana mata kallon "da sauranki ban hak'ura ba"

Shine ya katse kallon ya limshe idonsa, kana ya bud'e ya sakar mata wani shu'umin murmushi, da sauri ta sunkuyar da kai domin tabbas duk gangar jikinta ya amsa, bai kuma cewa komai ba, ya aje cup d'in a gabanta, ya sanya takalmi yace da k'arfi
"Umma na fita saina dawo" a cikin d'aki ta amsa masa
"adawo lafiya".

Yana fita Basma itama ta sanya takami ta bi bayan sa. Shi dai yaji ajikinsa Basma zata biyo shi, sai ya d'aure fuska ya cigaba da tafiya, sai da ya d'anyi nisa da gida kana ya juyo fuska d'aure, yace
"lafiya kike bina?" Cike da damuwa tace
"ba kaga sak'ona bane" yayi guntun murmushi yace
"inna gani me zan miki" marai raice fuska tayi tamkar zatayi kuka tace
"Yaya Aryan na baka hak'uri Amma kayi burus, kamar ma na k'ara zuga ka ne" ya kuma d'aure fuska yace

"da yake kin raina min hankali ba, zaki wani rubuta min a takarda, to ki sani bai min ba, kaya kuma suna nan na aje, duk lokacin da kika ga dama zaki zo ki d'auka"

Cikin rashin jin dad'in abin da ya ce mata tace cikin tsiwa,
"dan ma na baka hak'uri, wlh banda kaci darajan su Umma ba abinda zaisa na baka hak'uri, tunda wancen bada hak'urin bai maka ba, yanzu nace Yaya Aryan kayi hak'uri komai ya wuce" dariya ya kwashe dashi yace a ransa
"wannan Yarinya ba tad'a kunya zanyi maganinta" a fili kuma yace
"a haka zaki bani hak'uri kina min masifa? malama banda lokacin ki yanzu, sai anjima" ya juya zai tafi da sauri ta sha gabansa tace cikin marai raice fuska
"Yaya Aryan kaine kake hasalani, to naji zan baka hak'uri, Yaya Aryan kayi hak'uri bazan sake ba" sai tayi shuru,  murmushi yayi yace
"to naji na hak'ura Amma kad'an, ki wuce gida sai anjima" bai jira me zata ce ba ya wuce da sauri, ita kuma murmushi tayi, tace a fili
"Aiko zan maganinka".

Bayan sallan Magrib Yaya Ahmad ya dawo, kai tsaye ya shigo gidan, ya same su duka a tsakar gidan, ya kuma gaishe da Umma, ya kalli Basma yace
"kin shirya mu wuce ko?" tace
"na shirya" Umma tace
"ka tsaya kaci tuwo mana, itama yanzu ta gama ci" da sauri ya dubi Basma yace
"da gaske kinci?" dariya tayi tace
"eh mana na ci" yace
"tafd'i, aiko yau za ayi ruwa da k'ank'ara, keda bakya k'aunar tuwo" dariya duk suka yi tace
"eh yau dai naci na Umma na mai dad'i"

Yaya Ahmad ya mik'e yace
"Umma wallahi a k'oshe nake, sai dai wani lokacin inna zo" Umma tace
"Ba komai Allah ya kaimu" Basma ma mik'ewa tayi ta d'auki jakanta, suka yi wa Umma saida safe, Deeja tayi musu rakiya har mota.

Basma ta ciro waya Android mai kyau ta bawa Deeja tace
"ki rik'e a hannun ki, zan dinga kiranku da shi, ina jin lafiyanku" ta amsa tayi godiya sosai.
Yaya Ahmad ne ya kalli Deeja yace
"Hajiya ba magana ne" murmushi tayi tace
"akwai, ai d'azu mun gaisa" yace
"hakane Amma ai gaisuwa bata yawa"
"eh hakane, to ina wuni Yaya Ahmad" yace
"bazan amsa ba tunda saida na rok'a" d'ago kai tayi suka had'a ido sai ya kanne mata ido d'aya, da sauri ta sunkuyar da kai k'asa tana murmushi tace
"ayi hak'uri Yaya Ahmad bazan sake ba" dariya yayi yace
"karki damu, masu suna Deeja basa laifa dama, amma a wurina" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, a yanzu dai ta fara gane ina Yaya Ahmad ya dosa, domin duk had'uwansu saiya tsokaneta. Nan suka yi sallama ya ciro kud'i bandir d'in dubu d'ai-d'ai ya mik'a mata yace
"ga wannan ki sha sweet" sai tak'i karb'a, sai da Basma ta sa baki, kana ta amsa tayi godiya, sannan suka wuce.

Yaya Aryan sai bayan sallan isha'i ya dawo, bai samu Basma ba, sai hakan bai masa dad'i ba, domin yana son fad'ansu dan yana masa dad'i.

Bayan ya gama komai ya shiga d'aki da nufin kwanciya, sai ya ga d'akinsa a gyare, murmushi yayi domin yasan wacce ta gyasa masa, sauya kayan jikinsa yayi ya sanya na barci, ya kwanta akan katifansa, yayi d'ai-d'ai akan filo, ya d'aura kansa baifi minti goma ba yaji baburetin k'ark'ashin filo, da sauri ya mik'e cike da tsoro yana tunanin menene haka, Sam tunaninsa bai kawo masa waya bane, saboda shi baida ita, da sauri ya finciko filon yaga ko miye, waya ce android babba mai kyau a shinfid'e ya gani, mamaki ya cika shi, tace
"wannan yarinyar ko mayya ce sai haka, kullun sai ta barni da mamaki, nasan ba kowa ba ne sai Basma" 

Wayan ne yaga yana haske da alama kira ne ya shigo, da sauri ya matsa kusa ya d'auka ganin Basma a zanen kan wayan ne, yasa shi murmushi yace
"mayyar k'anwata" d'agawa yayi ya kara a kunne bai ce komai ba, itama bata ce komai ba har tsayin minti uku, ganin ba zaiyi magana ba yasa tace
"Yaya Aryaaan" tsigan jikinsa yaji ya tashi, irin yanda ta kira sunansa taja k'arshe, a kasale yayi murmushi wanda sai da taji sautinsa, itama murmushi tayi tace

"dama zance maka ne kayan d'akinka sunyi datti, zanin gadonka yana bukatar wanki da labule, kayi k'ok'ari ka bayar a wanke maka ko kai ka wanke, domin tsafta cikon addini ne, dan d'azun dakyar nake shak'ar numfashi, saboda yanda kayan ke tashi ya kuma had'e da k'amshin turare"

Tsananin fushi Yaya Aryan yayi, cike da b'acin  rai yace
"wai ke ni sa'anki ne? wallahi inda kina kusa sai na miki marin dayafi na rannan, mara kunya kawai"

kwashewa tayi da dariya tace
"haba Yayana Aryannny, daga gyara kayanka ai ba zai zama sauke mu raba ba, Allah dan ni ban iya wanki bane, dana wanke maka, shiyasa nace bari na gaya maka a wanke"

Murmushin takaici yayi yace
"ko kin wanke saina sake wankewa" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace
"kuma wannan wayar ta miye zaki aje min a d'aki?" tace
"dan na rik'a jin muryan Yayana, shiyasa na aje a gun" a wannan lokacin gyara kwanciyansa yayi gaba d'aya lamarin Basma ya daina bashi mamaki, tana da saurin hasala mutum, tanada saurin sakko da mutum in yayi fushi, Yarinya kamar mai Aljanu, a nushe yace

"to Yayan naki yace bai so, ki zo ki d'auki kayanki" cike da shgwab'a tace
"uhum ni ban yarda ba, ina son jin muryan Yayana ne, ba zan amsa ba" murmushi ne ya sub'uce masa yace
"shi kuma Yayan naki baya buk'atar jin muryanki, dan haka ba zai yi amfani da wayan ki ba, ni saida safe barci nake ji" sai ya gimtse kiran. Saiya rungume wayar a k'irjinsa, haka nan ya tsinci kanshi cikin nishad'i.

Basma sam bata ji dad'in gimtse kiran da yayi ba, hakanan ta tsinci kanta da k'ara son jin muryansa, sake kiransa tayi, baburetin d'in wayar ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya shiga, sai ya d'aga kiran, cikin kasalan murya yace
"Basmaaa, ki barni nayi barci mana" sai taji wani yarrrr, tsigan jikinta ya tashi, gaba d'aya sai ta ji wani irin nutsuwa ya shigeta, tace cikin irin yanayin muryan da yayi magana tace
"eh bazan bari ba sai munyi hira" cikin tsokana yace
"ke wai mayya ce" tace cikin tsiwa
"eh mayya ce Amma a gunka kai kad'ai" dariya yayi sosai yace
"to nama na d'aci gareshi yarinya dan yafi k'arfin ki" itama dariya tayi tace
"namanka dai zak'i zaiyi kanma a ce hancinka zai d'auki romo sosai" dariya duk suka kwashe dashi a tare, kana cikin dariya yace
"kwalelen ki Yarinya" itama cikin yana yin farin cikin tace
"ba wani kwalele Yaya Aryany" nan dai sukai ta hira cikin nishad'i- nishad'i da fad'a-fad'a.

Sai misalin sha biyun dare suka yi sallama, sun rabu cike da kewar juna, da rashin jin dadin rabuwansu.

Aryan da kyar barci ya d'auki shi, yanata tunani bar katai a kan Basma. itama ta b'angaranta da  tunaninsa ta kwanta, cike farin cikin duk suka kwana.

*Tofa anya kuwa? 🤔muje dai zuwaaa....*

*Rahma Ce*
[8/4, 5:17 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *9.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Washe gari*

Da misalin k'arfe hud'u na yamma, ya Aryan yayi wanka, sai ya d'auki d'aya daga cikin kanyan da Basma ta siya masa ya sanya, yayi kyau sosai da yake k'ananun kaya ne, sai ya d'auki hulan sanyi ya sanya a kansa saboda gashin kansa. Ya fito yace wa Umma sai ya dawo, Deeja tace
"Yaya Aryan kayan nan ya maka kyau, amma meyasa ka sanya hulan nan, ai daka cire zaka fi kyau" murmushi yayi yace
"Deeja banyi aski bane, kinga sumana ya taru shiyasa na sanya" murmushi tayi tace
"hakane, to sai ka dawo" kana yasa kai ya fita.

Tafiya yake bai san ina zashi ba, ya mik'e hanya sanb'al saida ya kai k'arshen layin su kana ya karya kwana, tafe yanke yana tunanin Basma da irin hiran da suka yi jiya, bai ankara ba wata mota ta taho a guje, gadan-dagan tawo kansa, ai ba shiri yayi tsalle ya koma jikin bangon wani gini saura kiris ya fad'a kwata, ya razana sosai, Basma dake cikin motan me zata yi inba dariya ba, da yake motan mai bak'in glass ne, Aryan ya kafa wa motan ido yana jiran wanda yake ciki ya fito, saida ta gama cin dariya sosai, kana ta bud'e ta fito, ido Hud'u suka yi sai ta kwashe da dariya, iya kuluwa yayi sai ya tamke fuska, cikin fushi yace
"dama kece kika son bigeni da gan-gan ko? anya Basma ba kida Matsala a kwakwalwa ba kuwa" yana fad'an haka saita tsaida dariyanta tace cikin tsiwa
"haba Yaya Aryan ya zaka kamanta ni da hauka, nifa da wasa nayi maka, tun daga nesa na hango ka nace bari na dan tsokane ka, ashe Yaya Aryan haka kake da tsoro" saita k'ara kwashewa da dariya, a yanzu shima dariyan yayi domin Basma ta kai mak'ura wurin shak'iyanci, tace
"Yaya Aryan dama fa wurinka zani, ka rakani wani wuri" kallonta yayi tare da tsare gira yace
"ni sa'anki ne, kije ki samu Deeja tana gida ita saita raka ki, amma ba dai ni ba" ai nan da nan Basma tayi fuskan tausayi tace
"Yaya Aryan ni kai nake so ka rakani" yayi murmushi yace
"to bazani ba" b'ata rai tayi kamar zatayi kuka tace
"haba Yaya Aryan kayi hak'uri muje ba zamu dad'e ba" ganin zata fara masa kuka yace
"to muje".

Nan suka shiga mota suka fara tafiya, ta sanya wak'ar larabawa yana yi a hankali, ta juyo tace
"Yaya Aryan kayi kyau amma abu d'aya ya b'ata wankanka" murmushi yayi bai tanka mata ba, ai bai aune ba sai yaje ta janye hulan kansa ta b'oye a dayan gefenta, da sauri ya juyo yace
"wai ina wasa dake ne?" tuni Basma ta shagaltu da kallon sumansa saura kad'an ta buga motan dake gabansu, da sauri ta gyara tuk'in ta mai da hankali kan hanya, Yaya Aryan ya kwashe da dariya yace
"Yarinya taga suma ba irin nata ba ta rikice" dariya kawai tayi bata ce komai ba har suka isa wurin shak'atawa.

Parking suka yi duk suka fito, suka jera ba tare da sunce ma juna komai ba, shi dai binta kawai yakeyi, sun isa wani wurin da aka zagayeshi da furanni masu k'amshi, wuri sanyi ga iska mai dad'i, kujerune a ciki da table a tsakiya duk suka zaune, weta ne ya zo da sauri ya tambayesu abinda za a kawo musu, Basma tace
"ice cream da shawarma da kuma drink" ta kalli Yaya Aryan tace
"Yaya me za'a kawo maka" yace
"duk abinda zaki ci shi zanci" murmushi tayi ta gaya ma weta ya tafi kawo musu.

Suna fuskantan juna Yaya Aryan yace
"dama nan wurin zaki kawoni" dariya tayi tace
"eh, saboda in dan saka ka waye, dan naga kamar baka waye ba" hararanta yayi yace
"kece dai baki waye ba da kike sanya k'ananun kaya ki fito ko ajikinki wai irin kin had'u" da sauri ta kalli jikinta tace
"Yaya kana nufin banyi kyau ba ne?"
"eh baki kyau ba saboda shigan bata dace dake ba" tace
"Yaya Aryan, na sanya ne saboda naga a mota nake" riga da wando ta sanya sun kamata sai dai rigan ya sakko har gwiwanta amma duk shape d'in jikinta ya fito sai ta yi rolling da gale a kanta ta rufe gashinta" yace
"eh, ai ba shiga bane na musulunci mace tayi ta fita" jikinta ne yayi sanyi tace
"To insha Allah bazan sake yin shigan na fito ba, amma zan rik'a sanyawa a gida" murmushi yayi yace
"da dai yafi miki" tace
"Yaya Aryan sumanka tayi maka kyau, meyasa kake rufewa?" ya kalleta suka had'a ido sai da suka kalli juna na tsayin minti uku, kana ya sauke ajiyan zuciya yace
"Basmaaa" sai duk jikinta ya mutu ta sunkuyar da kai k'asa, sai taji ta cigaba da magana,
"bana son barin suman, kuma yawan askewa yana k'ara yawansa, shiyasa nake yawo da hula, saboda in mutane suka gani suna yawan min magana akai" murmushi tayi tace
"Yaya Aryan dan Allah karka aske, zan siyo maka mayuka na maza, da zaka rik'a gyarawa, wlh har sheki zai rik'ayi, ba kaga yanda mazan India suke yi bane" murmushi yayi yace
"ni Basma bana son sumar dan a takure nake" marairaice fuska tayi tace
"to ko zaka aske, karka aske duka ni ina son ganinka dashi" hararenta yayi, kan yayi magana an kawo musu shawarman.

Sai wayar Basma ce ta d'auki k'ara, da sauri ta d'auka ta kara a kunne, tace
"My Shureym" saita shagwab'e fuska ta fara shagwab'a,
"bayan kasan ina missing d'inka, shine duk yau baka kirani ba ka manta dani" ta b'angaren Shureym kuwa ya shiga lallashinta.
Aryan zuciyansa ne ke dukan uku-uku hankalinsa ya tashi, amma saiya dake, ya cigaba da cin shawarman, amma abin mamaki kamar yana cin magani sam baya jin dad'in sa, sunkuyar da kai yayi k'asa, zuciyansa nayi masa zugi, numfashinsa yana fita da k'arfi, dakiya kawai yayi. Basma sun d'auki tsawon minti sha Biyar suna wayan, daga bisani suka yi bankwana ta kashe wayar.

Ta kalli Yaya Aryan tace
"Yaya kayi hak'uri na d'auki waya ban nima izini ba" d'agowa yayi idonsa ya kad'a ya d'anyi ja, sai yayi mata murmushin yak'e yace
"karki damu bakomai" murmushi ta mayar masa, ta mik'a hannu ta d'auko sauran shawarman da ya rage ta soma ci ko ajikinta. Sam bata lura da sauyawan yanayin sa ba, saida ta gama tace
"Yaya Aryan" ya d'ago ya kalle, tace
"bari muyi salfee mana?" murmushi gefen baki yayi yace
"ni bana hoto" shagwab'e fuska tayi tace
"ni dai dan Allah muyi" bata jira me zaice ba ta mik'e ta zo bayanta ta tsaya, shi kuma yana zaune, aiko ta kashe musu photo har uku, shi dai fuskansa ba yabo ba fallasa, gaba d'aya zuciyansa a takure yake, tace
"gaka kuwa yanda mukayi kyau?" ta nuna masa, ya kalla shima kanshi hoton ya ma kyau yace
"yayi kyau" tace
"Yaya muje gida yamma yayi sosai".

Bayan sun kama hanya, ta ciro hulansa ta bashi tace
"Yaya Aryan, gobe in Allah ya kaimu zanzo mu k'ara fita" murmushi yayi yace
"Allah ya kaimu" haka ta sanya wani wanka da music na soyayya, sai bin wakar take, shi ko kwantawa yayi a bayansa yana sauraren wak'ar da muryarta ,gaba d'aya ya shiga wani duniya wanda shi kanshi bai san wani irin duniya ya lula ba.

Ta sauke shi suka yi sallama, kana ya wuce cike da damuwa a zuciyansa, itama ta wuce cike da farin cikin a zuciyarta mara misaltuwa.

Da dare misalin k'arfe goma da rabi, Basma ta kira Yaya Aryan, yana kallon kiran yak'i d'auka, ta kira shi ya kai sau goma amma yak'i d'agawa, haka nan yaji ba zai d'auka ba, domin shak'uwar da zuciyansa yake da Basma, ya fara bashi tsoro kuma ga dukkan alamu ya soma shiga wani hurumi da ba nashi ba, dole ya d'auki matakan kaucewa damuwa.

Basma kuka ta shiga yi hawaye wannan na bin wannan, iyaka damuwa ta shiga, da kyar barci da d'auketa. Haka ma ta b'angaren Yaya Aryan, k'arshe ma tashi yayi ya gabatar da sallan nafila yayi Addu'a akan, Allah ya k'are masa zuciyansa da irin abinda ya soma raya masa game da Basma.

*Washe gari*
Basma da ciwon kai ta tashi, ta samu ta karya tasha magani sannan ta koma barci. Ta wurin Yaya Aryan kuwa ya samu sassauci game da abinda yake ji, ya shirya ya tafi kasuwa kamar yanda ya saba kullun, amma a k'asan zuciyansa yana tuna masa hiran Basma da Shureym sai damuwa ya ziyarce shi.

Da misalin k'arfe biyar ya dawo daga kasuwa, da sauri yayi wanka ya shirya ya fita, unguwar ya bari gaba d'aya saboda baya so su had'u da Basma. Ta b'angarenta kuwa ta zo tayi parking in da suka had'u jiya, tayi ta kiran wayan ba'a d'auka ba, kuma ta jira shi bai zo ba har kusan k'arfe shida na yamma, abinda bata sani ba Aryan yana hangen motanta ya b'oye a wani shagon aski, hakanan yaji tausayinta kamar ya fito sai kawai ya basar, haka ta hak'ura zuciyarta na mata zafi ta tuka motan a hankali, idonta na zubda hawaye, ta shiga damuwa na rashin zuwan Yaya Aryan, a haka ta isa gida kamar mara lafiya.

Shima Aryan cikin damuwa ya wuce gida bayan tafiyarta, koda Umma ta ganshi ta tambaye shi ko lafiya? yace mata kansa ke ciwo, sai tayi masa sannu.

Yau da wuri ya dawo gida ya kwanta, yau ma yak"i d'auka wayarta, a haka ko wanne ya kwana cikin damuwa.

*Washe gari Monday*

Basma da sassafe ta fito tazo gidansu Deeja, ta samu Deeja ta shirya suka gaisa da Umma, Aryan yana d'aki yana jinsu amma yak'i fitowa, dauriya Basma tayi tak'i tambayar ko yana nan, suka yiwa Umna sallama suka wuce University dake cikin Abuja, da yake ansan da zuwansu basu sha wani wahala ba wajen yin registration d'in, kuma dama president yasa hannu, Deeja an d'auke ta ba tare da zana wani exam ba, ta samu Medicine b'angaren mata (gynecology). Zuwa k'arfe biyu sun gama komai, sai suka kama hanyar gida.

B'angaren Yaya Aryan, ya tafi company su Basma, ya had'u da Yaya Naufal kamar yanda Yaya Ahmad ya gaya ma Naufal d'in, Yaya Naufal yayi masa interview, ga mamakinsa duka Yaya Aryan ya amsa masa, gashi dai ba digree gareshi ba amma ya amsa masa duk tambayoyinsa. Ya duba takardunsa sosai, cikin k'asaita da mulki yace

"sunana Naufal, a yanda na gwadaka kuma na duba takardunka gaskiya komai yayi yanda muke so, mun d'auke ka aiki, sannan bayan kamar watanni zamu turaka ka k'aro karatu kayi degree da masters, ga wannan kud'in kuma ka samu ka siya kaya na zuwa office, dole ne ka rik'a shiga mai kyau domin zaka rik'a ganawa da manyan mutane, office d'inka shine na b'angaren computer, kai ne mai shigar da komai in an fitar da kaya ko an shigo da su, da fatan ka fahimta"

Yaya Aryan cike da farin ciki yace
"na fahimta, nagode Allah ya saka da alkhairi" duk wannan bayanin cikin harshen turanci suke magana, kana Yaya Naufal ya rakashi katon office d'insa, mai d'auke da kujeru na alfarma da katon table, ga AC, ga fridge, kai har toilet akwai a ciki, komai dai normal, Yaya Naufal ya gama nuna masa komai ya fice, Yaya Aryan ya zauna kan kujeran table d'in ya juya yana kallon kud'in da aka zubama office d'in, sai hawaye ya soma zarya a kuncinsa, farin ciki da begen son ganin Basma ne ya bijiro masa, ba dan Allah yasa sanadin ta ba, da ba zai tsinci kansa a irin nan wurin ba.

Suna isa Basma ta fad'a d'akin Yaya Aryan ta kwanta bisa katifansa, cikin kankanin lokacin barci ya d'auke ta. Deeja ce ta

Please Login or Register in order to submit comment