Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baby love"  Hararenshi tayi ta mik'e tare ja jan tsaki ta bar wurin, cikin zafin nama yabi bayanta ya kama mata hannu, cikin b'acin rai ta juyo ta wanke shi da mari tace cikin fad'a "karka kuskura k'azamin hannunka ya kuma tab'a fatar jikina, na tsaneka Yaya Shureym bana son ganinka" tana gama fad'an haka tayi gaba abinta tana juya duk sassan jikinta.  Duk wannan abin ya faru akan idon Kaka Ma'u, yayi k'okarin bin bayanta, Kaka ta dakatar dashi tace   "kai Shureym bani son shirme, kasan dai Basma ba zata saurareka ba yanzu, dan haka ka bari ta huce in dai kana so ta koma gidanka"  

Zuwa yayi ya durk'usa gaban Kaka yace yana hawaye  "Hajiya dan Allah ki taimaka min kisa baki Basma ta koma d'akinta, nayi alkhawari zan gyara kuskurena" Kaka ta dafa kansa tace   "kaje zanyi k'ok'ari akai, sannan kayi Addu'a sosai akan in komawarta alkhairi ne Allah ya tabbatar, in kuma akasin hakane to ya zab'a muku mafi alkhairi" haka Shureym ya fita zuciyansa na masa zugi da radad'i akan Basma.  

Basma, Meena, Leema, Deeja suna zaune a d'akin Deeja gaba d'aya hira suke yi na yaushe rabo, Meena tace  "Basma baki bamu labarin ina kika je ba" Basma tayi dariya ta soma basu labarin zuwanta k'asar Etopia da kuma zuwanta Makka, harta k'are basu labarin, Leema tace  "lallai kinyi k'ok'ari, da fatan dai kinyi Addu'a Allah ya raba auren ki da Shureym a makka, dan wlh bana fatan ki cigaba da zaman aure dashi" Deeja tace  "in kuma shine alkhairin fa?" Meena ta harareta tace  "haba Deeja kamar baki taya Yayanki Aryan kishi, kinsan dai shine muradin Basma" Basma ta ya mutse fuska yace  "waye kuma Aryan?" a razane duk suka juyo suna kallonta, ta cigaba da cewa,  "aini ba Aryan a duniyata yanzu, dan ban sanshi bama" Leema ta kwashe da dariya tace  "wlh karya kike yi Malama, ga sonsa ina gani a cikin kwayar idonki kina wani zancen baki sanshi ba" Deeja murmushi tayi tace  "Antyna me Yayana ya mikine haka?" Hararansu tayi tace  "ban sani ba, kawai dai ban gane wanda kuke magana ba" murmushi suka yi Deeja tace a ranta  "yanzu haka akwai abinda ya mata, toma ina suka had'u da har za suyi fad'a? lallai dai akwai wani abu a k'asa" nan suka cigaba da hira Basma dai ita kad'ai tasan ya take ji a ranta game da Yaya Aryan, har yau sonsa bai ragu ba a zuciyarta, k'aruwa ma yake yi, tana azabtar da zuciyarta a kan dole sai ta daina tunanin shi, amma ta gaza yin haka.   

*Baya kwana Biyar* 

Yau kwana Biyar kenan da dawowar Basma, gida ya cika da 'Yan Uwa ana hidimar sunan Meena, yarinya taci sunan Fatima sunan Ammi, suna kiranta da Najwah.  Da yamma aka shirya waliman suna, family an hallara gaba d'aya a cikin gidan daga can baya, an sanya tempol da fararen kujeru ga kuma table a tsakiya, an yiwa wurin decoration, iyaye Mata da yaransu Maza da Mata sun hallara a wurin, iyayensu maza ne basa wurin, hatta Umma tazo da Yaya Aryan.  Sunsha kwalliya sai k'amshin turaren ke tashi,  

Basma tasha kwalliya riga da siket ta sanya na leshi pink color mai fulawa fari da bak'i, d'inkin ya amshi jikinta, bata sanya gyale ba, tasha d'auri tamkar gwagwaro, sai k'amshi ke tashi a jikinta, ta sanya takalmi mai tsini masu igiya, taku take d'as-d'as kamar wata hawainiya, haka ta isa gurin ta rik'a bin ko wani b'angare tana gaidasu, mai jawabi ya soma jawabi nan fa aka soma ciye-ciye ga sauti na tashi, Basma ce ta fara bud'e wurin da rawa cike da salo dan birge masu kallo, duk wannan abinda take yi bata san Aryan da gun ba. 

Shureym ya tashi ya fara mata mannin kud'i nan fa wuri ya kaure da ihu, ganin Shureym a bayanta yana rawa sai ta juyo ta galla masa harara tayi tsaki ta fice daga wurin rawan, can baya taje ta samu wuri ta zauna tana maida numfashi, wayarta ta ciro ta shiga bugawa kanta salfee, d'ago kan da zata yi ta waiga gefenta, sai karaf suka yi ido hud'u da Yaya Aryan...   

*Rahma Ce*
[8/11, 6:18 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *28.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Murtuke fuska tayi ta galla masa harara sai ta kauda kai, Yaya Aryan yayi murmushi ya kura mata ido, gaba d'aya ji tayi ta takura a gurin, mik'ewa tayi zata bar wurin, garin sauri takalminta ya turgud'e saura kiris ta fad'i, da sauri Yaya Aryan yace
"subhanallah" juyowa tayi idonta ya ciko da kwalla ta kalle shi tana ya mutse fuska alama taji zafi, murmushi ya sakar mata, murguda masa baki tayi ta wuce, wannan karan murmushin da yayi har fararan hak'oransa saida suka bayyana. Anyi taro an washe lafiya kowa yaje gida lafiya.

Basma tana zaune a d'akin Momy suna hira da Momy, sai ga Yaya Shureym ya shigo, ya risina ya gaida Momy kana ya zauna, Momy ta mik'e ta basu guri, shuru suka yi na mintuna, Yaya Shureym yace
"Basma dan Allah ya kamata ki tausaya min, ina son ki son da bana yiwa kai na, ki yafe min my Basma" fuskarta tamau tace
"ina Anty Safeena?" tambayan yazo mishi a bazata, har yakan manta da yana da Safeena, cikin sanyin jiki ya bata labarin barinta gidan da komai da ya faru, murmushi tayi ta mik'e ta isa gabansa tace
"ga wayata samin number ta" jiki na rawa ya amsa ya sanya mata sai ya mik'a mata wayan, komawa tayi ta zauna, ta shiga kiran number, bugu d'aya ta d'auka, suka gaisa, Basma tace

"nasan baki gane ni ba, Basma ce, na dawo kwana Biyar kenan daya wuce, ina so gobe in Allah ya kaimu ki biyo jirgi kizo Abuja"

Cikin farin cikin da borin kunya tace
"laaa Basma kin dawo, Alhamdulillahi, sai dai ba kud'i a wurina har yau Shureym bai zo yaga babynmu ba" ta k'arasa maganar cikin damuwa, Basma ta nisa tace
"ki turomin number account d'inki zan miki transfer, sai ki siya abin da kike buk'ata kishirya a nutse, ko zuwa jibi sai ki zo" cikin farin ciki Safeena tace
"nagode Basma Allah ya saka da alkhairi, dan Allah ki yafemin duk abinda na miki, ni kunyarki ma nake ji" Basma tayi murmushi tace
"karki damu komai ya wuce ai" nan suka yi sallama Safeena jikinta yayi sanyi.

Shureym duk yana sauraren maganar da suka yi, bayan ta aje wayar ya d'ago cikin fuskan tausayi yace
"Basma dan Allah ki saurare ni, ki tausaya min  plss" d'aura kafa tayi d'aya kan d'aya tace

"wai na ce kamin wani laifi ne? aure ne dai nace ba nayi, ka fita sabgata pls"

Tana gama fad'an haka ta mik'e, da sauri ya mik'e ya isa gabanta ya tsaya, kallonshi tashi sama da k'asa ta kauda kai, hawaye ne ya cika idonsa ya soma kwaranya a kuncinta, zuciyarta ne ya karaya cikin sanyin murya tace

"Yaya Shureym ni banga abin damuwa anan ba, tun farko kace baka sona Safeena kake so, shiyasa na sanya tazo ka d'auki matarka kutafi, Yaya Shureym jiki na fa kake so ba Ni ba, dan haka nayi Alwashin baza ka samu yanda kake so ba" tana kaiwa nan ta wuce ta bashi guri.

Zama yayi dirshen a kan tiles, kansa ya kama yana fidda hawaye sosai, Momy ce ta fito ta k'asaro wurinshi ta zauna tace
"Shureym kayi hak'uri in har komawar Basma d'akinka Alkhairi ne zata koma, ka barwa Allah komai" da sanyin jiki ya yiwa Momy godiya ya mik'e jiki ba kwari ya tafi.

*Bayan kwana biyu*

Safeena ta zo, ta sauka a gidan amma ta rasa wurin wa zata, saboda tasan babu wanda zai amsheta, kiran Basma ta yi a waya ta sanar mata da zuwanta, bayan minti biyar Basma ta fito cike da fara'a ta amsheta, part d'in Momy ta wuce da ita ta sauketa a d"akinta, masu aiki tasa suka kawo mata abinci da kayan motsa baki, zama tayi suka k'ara gaisawa, Basma ta d'auki babyn tayi kama da Yaya Shureym, Yarinyan ta kwantawa Basma a rai taji dama nata ne, hira suka yi sosai Safeena ta nima gafararta da ta yafe mata akan abinda ya faru, Basma ta yafe mata. Wanka Safeena tayi ta sauya kaya, Basma ta sanyata tayi kwalliya tayi kyau sosai, fitowa suka yi ta kaita d'akin Momy suka gaisa, suka je d'akin Ammi nan ma suka gaisa ba yabo ba fallasa, duk suka gaisa da mutanan gidan, daga k'arshe ta kaita d'akin da Shureym yake ta fito ta basu wuri.

Safeena tana ganin Shureym, sai farin cikin ya rufeta, duk haushin data d'auka dashi nan take ta huce, Shureym ya amshi babynsu yana kallonta cike da soyayya, anan suka zauna suka sha hira, shi kanshi Shureym yayi missing Safeena, nan suka sha soyayya kamar sabbin ma'aurata, Shureym yace
"Safeena ki taya ni rok'on Basma akan ta koma d'akinta" murmushi tayi tace
"ba ruwana kunfi kusa, yanda Basma ta sauko ta nuna min babu komai ta yafemin, karka zo ka had'ani da ita ba ruwana" jikinsa ne ya kuma yin sanyi.

*Washe gari* 

Abba ya dawo, gida ya cika da farin ciki, Basma na mak'ale da Abba shi kuma sai ririta ta yake yi, bayan komai ya lafa Abba yayi kiran Family Meeting a washe gari, sannan kuma da murnan taron dawowar Basma, cikin k'ank'anin lokaci aka shiga shirye-shirye.   Washe gari musamman aka kira mai kunshi ta zane duk matan gidan, Basma tasha kunshi tayi kyau, musamman suka kira masu makeup suka zo gida suka yiwa Matan gidan hatta iyayensu, tun k'arfe d'aya gida ya gama cika da Family, kowa nata hada-hada, masu abinci musamman aka kira su daga hotel suka kawo abinci kala-kala, duk cinka sai dai ka hak'ura ka barshi.   Da k'arfe biyu, Abba suna tare da Dady, Mai Martaba, da kuma iyayensu Mata da Kaka Ma'u, sai Yaya Ahmad da Yaya Adam, sai Yaya Naufal da Yaya Jamal, Yaya Shureym shima yana gun, Basma ce kad'ai sai Anty Husnah. Aka bud'e taro da Addu'a, Dady yayi Bisimillah yace  "Yau dai gamu dukanmu mun had'u, ga kuma Shureym da Basma, zamu tattauna akan zancen aurensu, yanzu mu iyaye me muka ga ya dace akan wannan lamarin, meye shawaranmu akai?"  Ummi ce ta fara magana Mahaifiyar Meena tace  "Ni ina ganin ayi sulhu Basma ta koma d'akinta" ai gaban Basma dam taji ya buga amma saita dake, Shureym wani murmushi ya saki a ransa wanda har sai da ya bayyana a fuskansa, Mami ma tace   "Gaskiya ne ayi hak'uri ayi sulhu Basma ta koma d'akinta" Ammi tayi tsaraf tace  "Ni ban amince ba" Momy saboda kawaici bata furta komai ba, Maman Leema Hajiya Murja tace  "ina bayanki Ammi nima ban amince ta koma ba, yanzu yayi mata haka nan gaba ya kenan?"   Dady ne yace  "bafa jayayya nace muyi ba, magana ta fahimta nace muyi" Mai Martaba yayi gyaran murya yace "kwarai kuwa, ni anawa ganin a tambayi Basma in ta amince ta koma d'akinta shikenan" Abba yace   "gaskiya wannan itace magana, Basma in ta amince zata koma shikenan, in kuma bata amince ba Shureym ya sauwak'e mata, daga yanzu ba zan kuma titasta mata ba"   Dady yace  "Hajiya Kaka baki ce komai ba?" murmushi tayi tace  "ina jinku 'ya'yan nan, in naji ba dai-dai ba zanyi magana, yanzu dai a tambayi Basma in ta amince zata koma" Dady ya kai dubansa ga Basma yace   "Basma kinji abin da muke magana akai shin zaki koma d'akin Mijinki Shureym ko kuwa ya sauwak'e miki?"  Ta d'auki kusan minti biyu kafin ta soma magana tace  "Dady Ni banda magana sai hukuncin da kuka yanke, nasan tabbas ba zaku cutar dani ba" saita k'arasa maganar tana kuka.  Shuru ne ya d'auki falon na tsayin minti biyu, Yaya Ahmad yace  "Basma karki cuci kanki fa, ki fad'i abin da ranki ke so" Yaya Naufal yace "kai ma kasan zab'inta ai, ba so take ta koma ba, kuma muma bama so ta koma wallahi" Anty Husnah itama tace "kwarai kuwa nima ban goyi baya ta koma ba, kawai ya maida mana Yarinya sai kace baiwarsa" Yaya Adam ne yace   "muyi hak'uri, Shureym dai yayi kuskure mu taru mu yafe masa" Yaya Jamal yace  "hakane kuskure kam an riga anyi shi, sai dai a koke gaba" Dady yace   "ya isa haka, ke Basma ki fad'i abin da ranki ke so kar gaba kizo ki kuka damu" Mai Martaba yace "ina ganin mu basu sati guda su sasanta kansu, in sunk'i sasantawa, sai mu mu d'auki mataki mu kuma zama akai"   Nan suka amince da wannan shawaran ta Mai Martaba, Shureym idonta ya ciko da kwalla bakinsa na rawa yace   "Abba tunda Basma ta baku zab'i, dan Allah ku bani Matata, wlh ina sonta kuma na gane kuskure na"  Dady yayi murmushin su na manya yace  "shureym kenan, kaje ka sasanta da Matarka kawai, in kun dai-daita shikenan, saika d'auketa Ku tafi".  Basma ce ta gyara zamanta cikin sanyin murya tace  "Dady ina son inyi magana" Dady yace  "an baki dama" tace  "Dama akan zancen Safeena ce matar Yaya Shureym, dan Allah kuyi hak'uri ku karb'eta a matsayin sirikarku, kuskure sun riga sunyi, ku yafe musu itama ta shigo cikin dangi, kunga yanzu sun fara tara zuri'a, bamu san iya adadin zuri'an dake tsakanin su ba, kuskure dai sunyi dan Allah Ku yafe musu, yanzu na kirata tazo dan ku gana da ita"  Shureym wani soyayyar Basma yaji yana fusganshi, farin cikin ya lullub'eshi, Dady ya nisa yace   "da kyau d'iyar albarka, kinyi tunani mai kyau, kai Shureym kira mana ita tazo nan" nan take Shureym ya kira Safeena, cikin minti goma sai gata ta shiga falon kanta a sun kuye, zama tayi gefen Basma, ta gaishe su, nan suka cigaba da tattaunawa, daga bisani Safeena da Yaya Shureym suka nima gafaransu, nan take suka yafe musu.  Suka  d'add'auki yarinyar data haifa suka sanya mata albarka, sai a sannan Mami ta nima gafarar Basma akan irin abinda tayi mata, Basma ta yafe mata, nan taro ya watse cike da farin ciki, Mazan suka tafi masallaci dan yin sallan La'asar, matan ma suka wuce b'angarensu dan gabatar da nasu Sallah. 
k'arfe Hud'u kuma su zauna wurin liyafan waliman dawowar Basma, wanda Abba ya shirya mata.  

*Rahma Ce*
[8/12, 7:11 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *29.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Wuri ya k'awatu sosai, b'angaren iyaye Maza daban tare da abokan Abba, sai iyaye Mata b'angare su daban tare da k'awayensu, yara Maza da Mata suma duk b'angarensu daban, sunata ciye-ciyen kayan kwalan da mak'ulashe, mota ce ta shigo gidan duk hankalinsu ya koma wurin ganin ko su waye a motan, Aryan ne ya fito ya doshi b'angare su Abba, risinawa yayi ya gaishesu, Dady dai yanata kallonsa, Aryan yace

"Amm Abba dama jiya naje Gombe na d'auko Kakanni na iyayen Umman mu, to shine suka ce na kawo su ku gaisa tare da tayaku murnan dawowar Basma"

Cike da farin ciki Mai Martaba yace
"Masha Allah, jeka tawo dasu, sannunsu da zuwa" Abba yace
"Umman ku fa?" yace
"tana tare dasu a cikin mota"
"madallah su k'araso ciki".

Aryan ya wuce wurin Motan ya bud'e musu, Malam Baffa ne ya soma fitowa sai Inna, dama suke mazaunin baya, sai kuma Umma ta fito daga mazaunin gaba,

Suka jero, Yaya Aryan yana gabansu, Dady ya zabura ya mik'e a rud'e, saboda ganin abinda baiyi tsammani ba a rayuwansa, barin kujeransa ne yayi ya fara tafiya ba tare da ya sani ba, su Abba suka bishi da kallo da kuma kalon inda yake kallo, Dady ya dafe kansa da hannu biyu yana ambaton Allah, wani k'ara ya saki sai ya yanke jiki ya fad'i, cike da tashin hankali su Abba da yaran suka rufa a kanshi.

Meena ce ta fara kuka tana fad'in Dady, Dady, Dady, su Umma sun kasa k'arasowa saboda abin ya tayar musu da hankali sam basu gane shi ba.

Cikin sauri suka d'auke shi sai a sibiti, zan iya cewa dukan mutanan wannan taro suka dunguwa zuwa asibiti, emergency aka shiga dashi, likitoci uku suka rufa a kansa, cikin wani na'ura suka sanya shi suna ta aikin bincike, Abba ya musu bayani yanda abin ya faru, sun fahimci matsalan daga kanshi ne, sai da suka d'auki awa guda a kansa suna aiki.

Daga wajen emergency d'in cike yake da Family d'insu, su Abba sai kaiwa da komawa suke yi, su Leema dasu Basma sai kuka suke, Ummi ma ta kasa dauriya kuka take kashirb'an, su Momy na lallashinta, Abba ne ya juyo yace

"yanzu fa Ibrahim Addu'a yake buk'ata ba kuka ba, dan Allah kuyi shuru muji da guda d'aya".

Likitoci sun fito daga d'akin, su Abba da Mai Martaba, sai Alhaji Gana Abokin Abba suka tare su, Doctor Jabir ne yace
"Yallab'ai muje office, nayi muku bayani" haka suka bi bayansu.

Duk suka samu guri suka zauna, Dr Jabir ya kalle su yace
"Yallab'ai bincikenmu ya nuna cewa Gomna Ibrahim ya tab'a samun loosing memory, to yanzu akwai abinda ya gani da yasa ya dawo dashi hankalinsa, munyi masa allurai da gwaje-gwaje wanda in ya farka zai dawo hayyacinsa gaba d'aya, kuma rayuwan da yake ciki yanzu ba zai manta ba, zai cigaba da rayuwansa kamar yanda ya saba, wancen tunanin daya rasa shine ya dawo kwakwalwansa"

Abba yace "Alhamdulillahi, yanzu zai kai k'arfe nawa kafin ya tashi?" Dr Jabir yayi murmushi yace
"zai d'auki lokaci kan ya farka, amma ba matsala bane"
"to Masha Allah, Allah ya bashi lafiya" duk suka amsa da
"Ameen" Dr Jabir yace

"yanzu nasa an canza masa d'aki na summan, kuma za'a iya shiga a duba shi amma dan Allah banda hayaniya, domin bama so a tashe shi, mun fi so ya tashi da kanshi"

Mai Martaba yace
"bakomai insha Allah za'a kiyaye" nan suka yiwa Doctor godiya suka fito.

Da sauri su Yaya Ahmad dasu Ammi suka tare su Abba, dan jin me yake damun Dady, cikin natsuwa Abba yace
"Alhamdulillahi ya farfad'o sai dai ya samu barci, da zaran ya farka komai zai yi dai-dai, sai dai likita yayi gargad'i banda hayaniya, Hajiya Fatima ku shiga a nutse ku duba shi, Yaranma duk ku shiga, sai ku fito su Ahmad su maidaku gida" Ammi tace
"to shikenan, Allah ya bashi lafiya" duk suka amsa da "Ameen".

Haka suka shiga d'akin a nutsu bayan sun gama duba shi suka fito, su Yaya Ahmad suka wuce da matan zuka gida, su Umma ma dasu Baffa Yaya Aryan ya maidasu gida ya dawo.

Nan aka k'ara security a asibitin, su Yaya Ahmad suna zaune a wajen d'akin, su Abba kuma suna zaune a ciki, sai Addu'a suke tofa masa.

A nan suka yi Sallan Magrib da isha'i, har zuwa lokacin Dady bai farka ba, damuwa ne ya soma ziyartan su kusan awa hud'u har lokacin bai farka ba, Abba ya kuma yiwa Doctor complaining, Dr Jabir ya k'ara basu hak'uri, ya tabbatar musu da zai farka karsu damu.

Har misalin sha biyun dare Dady bai farka ba, su Yaya Ahmad, Yaya Naufal, Yaya Shureym, Yaya Adam, Yaya Aryan, Abba, Mai Martaba duk a asibiti suka kwana, Alhaji Gana ya wuce gida shi da sauran Abokan Abba. A can gida kuma Matan hankalinsu a tashe suka kwana.

*Washe gari*

Da misalin k'arfe goma na safe Dr Jabir ya shigo duba Dady, duk su Abba suna gefe a zaune, Dr Jabir ya duba drip d'in dake mak'ale a hannun Dady, a hankali Dady ya sauke ajiyan zuciya, ya soma bud'e ido tamkar wanda ke tsoron haske harya bud'e duka, Addu'a  ya shiga karantawa, murmushi Dr Jabir yayi, Dady ya mayar masa da murmushi yace

"Baffana" dan fuskan Baffa ke masa gizo a idonsa, da sauri Abba ya mik'e ya isa baki gadon ya kama hannun Dady yace

"Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Mai Martaba Ibrahim ya farka"

Cikin muryan mara lafiya Dady yace
"Ina Baffana suke? ko basu na gani ba d'azun" cikin rashin fahimta Abba yace
"suwa kake magana akai?" murmushi Dady yayi ya kalle Mai Martaba yace

"ku kira min Aryan domin ya kawo min Innata da Baffana, da kuma k'anwata Aishatu, kuce masa su tawo tare da d'an Uwana Aliyu" cike da mamaki Mai Martaba ya kalli Abba yace

"inna fahimci Ibrahim yana magana akan bak'in da Aryan ya shigo dasu ne jiya, Allahu Akbar Allah Mai iko, kaji wani abin Al'ajabi, ban tab'a tunanin Ibrahim zai dawo hayyacinsa ba, kusan shekaru sama da talatin kenan"

Abba murna da farin ciki ya hanashi magana, hamdala da tasbihi yake wa Allah, wayansa ya ciro ya kira Ahmad yace

"Ahmad maza kaje gidansu Aryan, ka tawo dasu gaba d'ayansu ka kaisu gida, gamu nan likita zai bamu sallama zamu koma gida" Yaya Ahmad zaiyi magana yace
"Ahmad yanzu ba lokacin bayani bane, maza ka tafi ka aiwatar da abinda na saka"

Dr Jabir yayi dariya yace
"wato yallab'ai kasan sallama zan baku" cike da farin ciki Abba yace
"kwarai kuwa me zamu jira, bamu sallama da sauran magunguna su Naufal su tawo dasu, mu kaga tafiyar mu" sai ya tallabo Dady yace

"D'an Uwana sauko kaga mu wuce gida, ka samu kayi wanka kaci abinci ka rama Sallolin da ake binka, sai mu zauna Family Meeting yau ka gana da iyayenka" Cikin barin ciki Dady ya sauko yana murmushi, haka suka kai shi har mota suka tafi gida,.

Su Yaya Shureym suka amsa magungunan Dady, sannan suka wuce gida.

Gidan ya hargitse da Murnan dawowan su Dady, direct part d'in president suka wuce a can duk suka kimtsa suka ci abinci, Dady ya rama sallolinsa Magrib, Isha'i da kuma Sallan Asubahi.

Duk sun had'u a falon Abba suna zaune, sai ya jiki suke masa, Ummi sai murna miji ya farka, Meena kuwa baki har kunne dasu Basma, falo ya cika suda iyalensu suna ta hira da barkwanci cikin nishadi da farin cikin, sallaman su Yaya Aryan ne ya katse hiran nasu, Yaya Ahmad da su Umma suna biye a baya, wuri aka basu suka zauna

Dady ne ya mik'e ya isa in da su Malam suka zauna, ya durkusa ya had'a hannunsa biyu, Baffa ido ya zaro ya shiga murza idonsa, lallai wannan Ibrahima Khalil ne, an ya ko dai gizo nake gani?" kallon Inna yayi ya cigaba da cewa

"wai Ameena kina ganin abinda nake gani kuwa, wannan kamar Ibrahim d'in mu? kamannin fuskansu d'aya, sai dai shi mun masa sanin lokacin da yake k'arami ne"

Inna tace
"kwarai kuwa Malam nima abinda na gani kenan" falon yayi tsit suna kallon su, Dady yace cikin kuka

"Inna, Baffa, Ibrahim d'in ku ne ku daina tantama, ina Yaya Aliyu ina Aisha k'anwata?"
Ai gaba d'aya falon sai tsoro ya shigesu, Kaka Ma'u ta taso ta dafa kafad'an Dady ta kalli Abba tace
"Muktar ko dai fad'uwan da Ibrahim yayi ya samu matsala a kansa ne?" Murmushi Abba yace

"lafiyansa kalau, Allah ya dawo masa da hankalinsa ne, kuma wa'innan Kakannin su Aryan ne kuma sune iyayensa, ganin su da yayi jiya ne ya haifar masa da fad'uwa har yayi dogon suma, hakan ne yayi sanadin dawowan tunaninsa na tun lokacin da yana k'arami da Alhajinmu ya bigeshi ya rasa tunaninshi"

Gaba d'aya falon sun girgiza da zancen Abba, amma banda Abba da Mai Martaba sai Hajiya Kaka, sune kad'ai suka San wannan abin, saura duk sun d'auki Dady d'an uwansu ne na jini.

Falon ya cika da kabbara tare da yiwa Allah tasbihi, Malam da inna kuka suka sanya, Umma ma haka su Ammi ne suka taso suka shiga basu baki, Aryan mamaki ya cika shi ya shiga zancen zuci
"dama ashe Dady Babansu Meena shine Yayan Umma wanda ya b'ata tun yana k'arami, tasha gaya musu, wani lokacin har kuka take yi suna lallashinta" Khadija ce ta taso ta fad'a jikin Dady ta shiga kuka sosai cikin kuka tace

"Dady dama kai Abbanmu ne bamu sani ba, Abbanmu ya rasu shekaru kusan bakwai da suka wuce"

K'ank'ameta yayi a jikinsa yace
"Innalillahi wa inna ilaihur rajiun, Baffa wannan 'ya'yan Aliyu ne ashe? Yaya Aliyu ya rasu? ina Matarsa take?" Malam ya share hawayensa ya nuna masa Umma yace

"had'in zumunci muka yi musu da k'anwarka Aisha, wancen Yaro Aryan shine babban d'ansu sai Khadija ga tanan itace k'arama, Aliyu ya rasu da kewarka sosai, wani lokacin da girmansa ma kuka yake yi yana jimamin rashin ka, kullun zancenmu ko ka mutu ko kana raye, bamu tab'a tsammanin zamu sake

Please Login or Register in order to submit comment