Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ina ganin tayi barci ne" Cikin damuwa yace "ok" ya kashe wayar.

Basma ta cika 10cm haihuwa ta taso amai ta fara yi, haihuwarta mai fayar baki ne, amai take sosai tana yunk'uri, bayan ta gama aman sai nak'udar ta lafa a hankali barci ya fara fizgarta, hutun minti biyar tayi nak'udar ya dawo, cikin ikwan Allah bata k'ara minti goma ba ta haifo d'anta Namiji mai kama da Aryan sak. Yaron kato sai ihu yake Hamdala Basma ta shiga jerowa da yiwa Allah Tasbihi.

Yaya Aryan ya shiga kan layinsu kenan wayarsa ya d'auki k'ara, Likintansu ne ya kira shi ya d'auka suka gaisa sai Likita yace
"Madam tazo ita kad'ai Asibiti ba tare da kowa ba sai Driver, yanzu haka tana Labour Room, muna so a kawo kayan Baby"

Da k'arfi Aryan yace
"ta Haihuwa ne?"

Likita yace
"A'a tana gab, ku kawo kayan da sauri"

Godiya Yaya Aryan yayi masa, sai ya juya akalan Motansa ya nufi Asibiti, wayar Deeja ya kira yace mata
"Ki shiga part d'inmu ki had'o kayan Baby, da wanda Basma zata canza, da duk kayan da ake buk'ata a Asibiti sai ku tawo" bai jira amsar da zata bashi ba ya kashe.

Farin ciki ne ya rufe Deeja ta fito da sauri, Allah yasa ta idar da Sallah kenan tasa kaya. Had'a kayan tayi ta shiga wajen Meena tare suka tawo suka kira su Momy a waya suka sanar dasu.

Basma an ciro Mahaifa an gyara mata jiki, kaya ya rage a kawo ta sauya, Baby ma haka, Yaya Aryan a sittin ya shiga d'akin Haihuwar bai jira an bashi izini ba, Nurse Sa'a ta dakatar dashi

"Dan Allah Kaje waje mu gama tukuna saika shigo"

Ko saurarenta bai yi ba ya isa wurin Basma ya kama hannunta gam yace cikin muryan tausayawa

"Babyna Allah ya saukeki lafiya" tare da matsar kwalla. Murmushi Basma tayi sai ta kai hannunsa wajen cikinta tace

"Babynmu baya cikina yanzu dan ya fito" ware ido yayi ya shiga waige-waige, hango gadon Yaron yayi ya isa wurin, ya ganci a cikin towel an k'udun-dune shi, hannunsa na rawa ya kai ya d'auko shi, farin ciki ya sanya shi fitan kwalla, ya shiga jero masa Addu'a tare da godewa Allah, Basma na kallonsu tana murmushin farin ciki cike da so da k'aunar su.

Nurse Sa'a ce ta amshi Yaron don su sanya masa kayansa da su Deeja suka kawo, Basma ma sanya kayanta tayi Aryan ya d'auketa cak ya kaita d'akin hutawa na masu Haihuwa. Meena da Deeja suka rufa musu baya, dai-dai lokacin Ammi tazo tabi bayansu. Momy tak'i zuwa saboda kunyar 'Yar fari.

*Bayan Sallan La'asar* 
Aka basu Sallama suka wuce gidan Abba gaba d'aya. A side d'in Ammi Basma suka sauka tare da Babynsu. Nan fa kan ace miye gida ya soma cika da 'yan barka sunata zuwa, Anty Husnah ma da sauri tazo gidan dan ganin idon Basma an zama Mama, tasha tsiya wurin su Deeja, amma kuma sun yabama k'ok'arinta da juriya data iya kai kanta Asibiti. Abba yayi Murna da ganin jikinsa ya amsa Yaron yayi masa Addu'a tare da hud'uba.   Duk sun sanar da dangi wanda suke nesa, da yawansu sun d'aura d'amaran zuwa Abuja a washe gari, kuma in suka zo sai anyi suna zasu tafi. Leema kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Abuja don Murna, haka ma Safeena ta k'osa Gari ya waye su kamo hanya, Shureym sai da yaji wani iri aransa yace "Da yanzu wannan Yaron nawa ne, Allah Sarki, na amshi wannan k'addaran tawa, ka yafe min dukkan kuskuran dana aikata". Nima na tayaka da Ameen.   

*Ranar Suna* 
Yaro yaci sunan *Aliyu* Mahaifinsu Aryan, Suna kiransa da *Hydar*, ba k'aramin shagali suka shirya ba, wannan hidima ya tara Manyan Mutane Sarakuna da Manyan 'Yan Kasuwa.  An shirya k'ayataccen Walima bayan Sallan Isha'i a babban hol dake Abuja, hatta Abba dasu Mai Martaba, Dady duk sunje wurin, har Momy da take kunyar 'yar fari taje wurin, su Kaka Ma'u, Inna, Malam kawai suka bari a gidan, Wata Babbar Malama suka gayyata tazo ta bada Fatawa akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci*.   

Da farko Tarbiyyan Yara sun rataya akan Uba da Uwa wanda aka samu wannan D'a daga Jikinsu. Uba dole ne ya samarwa 'Ya'yansa Uwa Tagari haka itama Uwa dole ne ta samawa 'Ya'yanta Uba Nagari, Tarbiyya yana farawa ne tun daga ginshik'in Neman Aure.  Ma'aurata dole ne a yayin saduwa suyi Addu'a kamar yanda Monzon Allah s.a.w ya koyar damu kafin iyaye su kaiga saduwar Aure, kunga kenan an fara samar da D'an ta kyakkyawa hanya, daga nan lokacin da aka samu cikin wannan d'a, Uwa dole ne ta zama mai hak'uri tare ya yawaita Addu'a don samun d'a Nagari, Uba kaima yana da kyau ka sanya ido ka bata kulawa sosai tare da Addu'a har Allah ya sauketa Lafiya.  

Wasu Iyayen sukan fara da tsinewa ciki tun kan yazo Duniya, sai kuji Uwa na cewa 'Wannan shegen cikin ya isheni da muntsili' 'Na k'osa wannan jarababen cikin nan ya fito na huta' Wannan cikin kaza-kaza, tun d'a na ciki wata Uwar ke fara lalata shi kafin ya fito Duniya, dan haka jan kunne garemu Mata Ku kula sosai yayin irin wannan halin da kuka tsinci kanku, mugun furuci yana lalata Tarbiyyar Yaro, ki zama mai hak'uri da juriya domin a wannan lokacin kina cikin wani jarabawa ne mai dinbin lada, ki zama mai yin Addu'a da niman sauk'i a wurin Allah yayin da cikin ya dame ki.   

Sannan bayan an haifi Yaro, Uba zai masa kiran Sallah da hud'uba da sunansa, a wannan lokacin d'a zai hanasu barci wani Uban yaita tsaki yana zage-zage, wata Uwar kuma ma kaji tace  'wane kaza ka cika shegen kuka ai Allah wadaran wannan rikici naka', to wallahi dole sai mun kiyaye fidda mugayen kalami akan Yaranmu.  Duk abinda Uwa zata yi dole sai kin sanya ido da hak'uri da kuma Juriya, kuma dole sai kin fara gyara halayyarki kafin ki fara kafa tubalin Tarbiyyan Yaranki. Domin wasu Yaran yayin tasowarsu sukan fara koyan wasu halayya da Uwarsu keyi, koda ace mara kyaune a ganinsu mai kyaune tunda sun ga Uwarsu tayi.  Dan haka dole mu Iyaye Mata muna sanya ido a kan Yaranmu domin Mune Makarantar farko ga Yaranmu. Sannan da zarar yaro ya taso nuna masa yin Ibada akan lokaci, koyar dashi Addu'an safe da maraice, na shiga bayi, fita gida da sauran Azkar, kasance mai jansu a jiki kina tunatar dasu Tsoron Allah, ki sanyawa d'anki Tak'awa da kuma Tauhidi, nuna masa yanda Azabar Allah yake a ranar gobe k'iyama in suka sab'a masa, ki tsawatar musu in suna wasa da Sallah, ki jasu  a jikinki a nan ne zaki rik'a jin dukkan matsalolin su, rik'a duba takardunsu na makaranta kina ganin abinda yara ke ciki game da karatunsu.  

Kaima Uba ka ja 'ya'yanka a jikinka banda d'aure fuska, ko daka dawo daga aiki su rik'a gudu suna tsoron fad'anka, zauna dasu tamkar abokanka kayi wasa dasu ka tunatar dasu hakk'ok'in Allah wanda ya rayata akan su. Ka sanya su a makaranta masu kyau, karka zama me kyashin biya musu kud'in makaranta.  
Sannan mu sani yawan duka baya shirya yaro sai dai ya kangarar dashi, mu rik'a musu fad'a da Nasiha, karmu gaji.  Insha Allah duk abinda ya gani na sabon Allah zai guje shi, zai kasance mai gudun B'acin ranku, zai zama kamili nagari abin sha'awa gun kowa, Mutane za su rik'a kwatantaku cikin sawun Iyaye Nagari, haka yaron za'a rik'a kwatance dashi a cikin 'Ya'ya Nagari.  Allah ya bamu ikwan Tarbiyyan tar da Yaranmu bisa tafarkin Al-Qur'ni da Sunnah. Ameen ya Rabb   

Sai k'arfe Goma na dare aka gama wannan Walima, kowa ya koma Gida lafiya. Walimar ya burge Mutane sosai game da yanda Malamar ta bada bayani akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci*.  Anan Mami ta gane cewa tayi kuskure wajen Tarbiyyan Shureym, ta kuma d'auki Alkhawarin niman gafaransa, da gyara kuskurenta akan jikokinta.   

*Bayan Wata Guda* 
Deeja itama ta sullub'o 'Yarta Mace kyakkyawa mai kama da Basma, ranar suna taci sunan Umma 'Aisha'. Kamar yanda aka yi taron sunan Hydar haka akayi na Aisha, an shirya Walima  kyatacce akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci* 

Anyi taro lafiya aka watse lafiya. Inna itace ta zaunawa Deeja har zuwa tayi Arba'in.   

*Rahma Ce*
[8/20, 9:17 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑*

_page_ *40.*

*_Final page_*

_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*

*Bayan Kammala Wankan Jego*

Basma ta gama wanka, zaune take tasha kwaliya cikin d'inkin riga da sket na atamfa, Baby Hydar yana gefenta ta kwantar dashi, wayarta ce a hannunta tana latsawa da alama charting take yi, Sallaman Yaya Aryan shine ya katseta ta d'ago cikin murmushi tare da kallon so ta amsa masa, isa yayi kusa da ita ya zauna tare da rausayar da kai gefe yace

"Babyna kinga yanda ki kayi kyau kuwa, kamar Baby Hydar bai fita a jikinki ba, meye sirrin?"

Murmushi tayi wanda ya bayyana farin cikin ta tace

"Myn bafa komai, Ni ce dai yanda ka sanni sai dai fa na samu kyakkyawan kulawa wurin Ammi dan haka ita zaka tambaya sirrin"

Hararan wasa yayi mata yace
"Kinsan dai babu wannan tsakanina da Ammi, a bakinki ya kamata naji komai, yanzu dai mu bar wannan maganar yaushe zaki dawo gidanmu, ina missing d'inki Baby love, da kyar nake iya barci fa" ya k'arasa maganar cikin muryar tausayi.

Kanne masa ido d'aya tayi tace
"Uhum Myn nifa sai nayi wata biyu zan dawo"

Ido ya zaro waje yama kasa magana, da gudu ta mik'e ta bar wurin tana kwasan dariya, girgiza kai yayi ya d'auki Baby Hydar yabi bayanta, d'akinta ya sameta ya kwanar da Baby Hydar ya matsa wurin ta yace

"Babyna ko so kike in shiga wani hali?"

D'ago fuska tayi tana kallonshi cikin ido tace
"Baby nima na kosa na dawo gareka amma bansan ya zanyi ba, bazan iya sanar wa Ammi hakan ba, ka k'ara hak'uri suma sunsan ya kamata na koma karka damu"

Ajiyar zuciya ya saki tare da busa iska mai zafi yace
"ki shirya zanzo gobe Insha Allah zamu fita"

Ido ta zaro waje tace
"ina zamu kuma Myn? kunya nakeji"

Murmushi yayi yace
"Hotel zamu domin ina da buk'atar Babyna in ba so take in fara biye-biye ba"

Da sauri ta had'e bakinta da nashi domin bata son ya k'arasa maganar, sai da suka d'auki minti goma kana ta janye jikinta tare da sauke ajiyar zuciya, cikin kasalan murya tace

"Myn karka k'ara furta kalman da ya fito a bikinka domin kanada ni, Insha Allah zan kasance da kai a koda yau ba zan gaji da kai ba tunda nima inda buk'atarka, zan shirya mu fita amma gidanmu zamu ba Hotel ba, domin in samar maka farin ciki sweet babyna" saita manna masa kiss a goshinsa ta mik'e, tana mai cewa

"bari na kawo maka abinci dan nasan da wiya in kaci na rana".
Bud"e k'ofar da zata yi ne taci karo da Ammi, Ammi tace

"Ina zaki kike sauri haka?" Sosa k'eya tayi tace
"Abinci zan kawowa Yaya Aryan"
"Ok ga wannan ki shanye shi zuwa anjima da yamma" ta amsa goran tana godiya.

*Bayan Sallan La'asar*

Ammi ta sameta a d'aki tace
"Basma je kiyi wa Momynki Sallama yau zaki koma gida, da fatan kin gama shirya kayanki?"

"Eh Ammi na kammala bayan Yaya Aryan ya tafi"
"To madalla" saita fita.

Tana isa part d'in Momy ta sameta zaune saman kushim tana karanta wani Jarida, sallaman da tayi ne yasa ta aje Jaridar a gefe ta amsa mata, Basma ta isa gefenta ta zauna tare da kama hannunta tace

"Momyna sannu da hutawa"
"Yauwa My Basma"
"Nazo muyi sallama ne Ammi tace yau zan koma gida" ta k'arasa maganar cike da shagwab'a.

Hararan wasa ta mata tace
"Basma sai yaushe zaki girma da yin shagwab'a ne?"

Murmushi tayi ta langwab'ar da kai gefe tace
"Uhum Momy ina dake fa kinga kuwa bazan daina shagwab'a ba, ga Abba da Ammi, ga Dady da Ummin kd dasu Kaka Ma'u duk inada ku fa"

Momy tayi dariya tare da lakace hancinta tace
"Ki dai ragewa su Hydar"
Kunya ya rufeta ta sunkuyar da kai k'asa tana murmushi tare da wasa da yatsun hannunta.

Momy ta gyara zama tare da kiran sunan ta, Basma ta d'ago taga babu alamar wasa a tattare da Momy, natsuwarta ta tattaro tace
"Na'am Momy"

Momy tace
"Basma ina son in miki tuni akan hakk'in Mijinki dake kanki, Mata da dama wasu na kuskure akan da zarar Mace ta haihu saita jingine buk'atun Mijinta ta kama na Yaronta kuma wannan ba dai-dai bane, hakk'in Miji shine farko kafin hakk'in 'Ya'ya, A Ranar Gobe K'iyama Allah yana fara tambayan hakk'in Miji ne kafin hakk'in 'Ya'ya, sannan Aljannarki yana k'afar Mijinki inya d'aga ki shiga Aljanna, in kuma ya danne ki auka wuta. Allah yayi mana tsari da wuta Ameen.

Dan haka sai munyi karatun tanatsu sosai, Mata da dama suna jingine need d'in Mijinsu da zarar sun Haihu, wata ma ba tada lokacin wani hira da Miji ko girka masa abinci, kullun itace hidimar yaranta ba ruwanta da farin cikin Mijinta ko b'acin ransa, wata ma saboda d'anta saita hana miji hakk'insa, wai adole ita mai d'a, to wallahi mu hankalta Musani shi Miji yanada matuk'ar mahimmanci dole ne mu rik'a kula dasu muna basu lokutanmu domin samun da cewa.

Ki ware lokutanki kina tsarawa kanki ko wanne ki fita hakk'insa, Miji da kuma Yaranki, su Kansu mazan suna tausayawa Matan akan wasu hidimomin gidan har suke tayasu ma.

"Maza da dama suna fuskanta k'alubale a wurin wasu Matan nasu da zarar Mace ta haihu, ita kullun ba data lokacinsa, wata ma ta daina yin kwalliya, wata kuma tsafta ma ta rage, wata kuma yin abinci ma sai dole, babu wani kyale kyale da Miji zai gani a wurin Matarsa da sai sashi sha'awarta. Da ance wance kaza kin daina abubuwa kaza kin sauya, saita ce    hidimar Yara sune suke hanata. Hakan kesa Mazan suna sha'awar Matan dake waje masu kwalliya da kyale-kyale, da ya samu mai sonsa saiki fara damuwa Mijinki ya sauya miki, ke kaza-kaza, bacin kece kika bashi k'ofar yin hakan.

Shi dai haihuwa bazai sanya ki zama k'azama ba ko ki zama mara kwalliya da gyaran jiki ba, sai in dama kin sanyawa ranki sangarci, lalaci, son jiki da kuma rashin tunani, dan haka Mata mu kula sosai, dan da wayan matsalolin da wasummu suke fuskanta a gidan aure muke fara bada k'ofar aukuwarsa.

Namiji kamar Yaro yake jin kansa, yana buk'atar kulawa da tarairaya, 'yar soyayyan nan ko 'Ya'ya nawa ki kayi baki tsufa da yinshi ba, a kullun kina gyara kina tsafta Mijinki zai rik'a miki kallon yarinya ce".

Basma shuru tayi, gaba d'aya jikinta ya mutu tace
"Momy yanzu kina nufin da safe kafin in fara indimar Hydar na Babanshi zan fara?"

Momy 'yar dariyarsu ta Murmushi tace
"kwarai kuwa, ba da safe bama a ko wani lokaci ma, in har Mijinki mai fitan safiya ne dole ki tashi ki fara masa hidima kafin ya fita ki tabbatar ya fita da farin ciki a ransa wanda in ya tuna zai rik'a Murmushi da farin ciki, kinga kin samar masa farin ciki wanda ko ya fita hankalinsa da tunaninsa yana wurinki zai rika Allah-Allah ya dawo gida.

Ki zama mai kwalliya, canza shiga iri-iri, karki nacewa shiga guda d'aya, k'amshi karya rabu dake ki zama mai amfani da turaruka masu sanyin k'amshi, kuma kala-kala, karki yarda Mijinki ya fahimci k'amshin ki guda d'aya ne, ya zamana daban-daban, kuma ki tanada masu taushin k'amshi na wanciya barci ne wannan kawai. K'amshi yana d'aya daga cikin sirrin mace wanda zata mallaki zuciyar mijinta cikin sauki.

Sannan ki rik'a wa Mijinki Addu'a a fili da kuma a b'oye, in zai fita bishi da Addu'a tare da tarairaya wanda in ya tuna ki ya saki murmushi. Kuma karki kuskura ki sakarwa 'yar aiki hidimar mijinki dan wasu matsalolin daga nan yake farawa, sai jiki ance 'yar aiki ta aure mijin matar gida, wannan duk sakacin matane akan kula da hakk'in Miji. Nasan duk kin sannan wannan abubuwan tuni dai nake miki".

Ajiyar zuciya Basma ta saki mai k'arfi tace
"Momy nagode sosai, hak'ik'a duk Macen da tayi amfani da shawarwarinki zai mata amfani matuk'a sosai, Allah ya saka Miki da Aljanna yasa ki gama da duniya lafiya, ina alfahsri da samunki A matsayinki na Uwa a gareni, love u much Mom" ta k'arasa maganar tana matsar kwalla.

Momy tayi Murmushi tace
"Ai Basma lokacin ma yayi mana kad'an, domin na lura da *Anty Rahma* ta k'osa ta gudu ta barmu, ta koma labarin Jannat na cikin sabon littafinta *MAI HAK'URI (shi ke da riba)*.

Dariya Basma tayi ta mik'e tace
"Momy Anty Rahma tana k'ok'ari sosai ina jinjina mata matuk'a"

Momy ta wuce d'aki ta had'o mata wasu magunguna ta bata, Basma ta amsa tana murmushi cike da jin kunya tayi mata Godiya.

*Ni Rahma nace kunga Iyayen zamani*😉

Ammi itace ta mai da Basma gidanta, sai gabda Magrib ta barota ta dawo Gida.

Yaya Aryan sai bayan Sallan isha'i ya shigo gidan, mamaki ya cika shi yanda k'amshin Abinci ya cika masa hanci daga kitchen, tunani ya shiga yi, yasan tabbas ma'aikatan gidan sun gama aikinsu sun wuce part d'in su, tambayan kansa yake

'Waye a gidan nan?' Dan sam bai san da dawowar Basma ba. Zama yayi a falo yana jiran yaga wanda zai fito, baifi minti biyar da zamansa ba Basma ta fito cikin shiga na English Wears riga da sket, rigar iya cibiya ya tsaya mata, sket d'in kuma iya rabin cinya, gashin kanta ta d'aure shi da ribom ta saki jelan a bayanta, k'amshi take zubawa mai sanyin k'amshi, Baby Hydar ta sab'ashi a kafad'a, shima ta zuba masa nashi kwalliyar.

Yaya Aryan sakin baki yayi yana kallonta harta k'arasa wurinsa, kwantar da Hydar tayi ta koma kusa da shi ta zauna tare da kallonsa tana murmushi ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, hura masa iskan bakinta tayi a idonsa, ya lumshi ya kuma bud'ewa, magana zai yi ta had'e bakinta da nashi suka lula duniyar masoya, sun d'auki kusan rabin awa suna faranta ran juna, daga bisani Basma ta jaye jikinta tace cikin kasala

"Muje kaci abinci" Murmushi kawai yayi ya mik'e ya d'auki Baby Hydar tace
"Ki sameni a d'aki"

Bin bayansa tayi cike da farin ciki tace da k'arfi

"I love u Yaya Aryan"

Sai ya juwo cikin kulawa tare da d'age gira
"Love u too My Queen"

Ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta suka koma suka zauna yace

"Basma kin zamo min haske a rayuwata, sonki halitta ne daga tsatson jikina, zan kasance dake har abada taurauwata, zan cigaba sa shayar dake da ruwan farin ciki wanda yake kwaranya daga koramar masoya"
Ya sumbaci bayan hannunta.

Tace
"in sonka Mijina, Allah ya k'ara mana zaman lafiya da kwanciyar Hankali, ya kauda dukkan shairin Shaid'an, Mutum da Aljan, ya k'ara maka bud'i na Alkhairi ya kuma Albarkaci zuri'anmu"

"Ameen ya Habibty" ya amsa tare da manta mata kiss a baki, daga bisani sai suka mik'e suka wuce d'akinsu, dan cigaba da shayar da juna Zumar Masoya.

*Tammat Bi Hamdillah*

*_Alhamdulillah Ala Kullu Halin_*

Alhamdulillah, Yau Allah ya bani damar kammala wannan littafi mai suna *'YAR SHUGABA*, ina mai godiya ga Allah S.W.A daya bani ikon kammlashi cikin koshin lafiya.

*_MASOYANA_*
_*Bani da bakin gode muku masoyana masu bibiyar wannan labari, kunada yawa domin lissafaku wani sabon littafi zan cika, Allah ya saka muku da Alkhairi ya k'ara mana zumunci ya kuma had'a fuskokinmu a Gidan Aljanna. Ameen. Addu'o'inku yana isa gareni, Nagode sosai wallahi ina sonku sosai, so wanda baida algush😃, so irin da yawan d'in nan, irin totally d'in nan, ina yinku ba adadi Allah ya bar kauna. Ameen😍❤❤*_

*Wannan labari kamar yanda na fad'a a farko k'agaggen labarine, banyishi ko dan wata ko wani ba, hasalima idan muka fuskanci labarin yasha banban da yana yin mulkin k'asar mu da ma sarauta. Na yishi domin ilmantarwa da kuma fad'akarwa acikin siga na nishad'antarwa.*

_Allah ya bamu ikwan Amfani da abinda ke cikin wannan labari, kuskuren dake ciki Allah ya nisantamu dashi ya yafe mana gaba d'aya. Ameen._

_Taku a kullun_
*RAHMA KABIR* sai kun jini a sabon littafina wanda zaizo nan bada dad'ewa ba
*MAI HAK'URI (shi ke da riba)*

*Rahmar Ku Ce*💃😍 

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment