Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bisu ba, sun wuce tare da escot, ita kuma ta wuce wurin masoyinta, suka had'u a in da suka saba had'uwa, suka wuce wurin hutawa domin su samu yin hira mai dad'i. Sai misalin k'arfe shiga na yamma suka yi sallama da Yaya Aryan ta wuce gidan hutun da sauri, domin tana son yin wanka a swimming pool, dan ta kwana biyu bata yi ba.

Tana isa ta samu su Meena a wajen, haka itama ta shiga ta soma wankanta, Leema ce tace
"Besty wai yane naga duk kin sauya ne, ko akwai abinda ke damunki ne?" murumushi tayi a ranta tace
"soyayyan Aryan ya sauya ni" a zahiri kuma tace
"Me kika gani besty, ina nan a Queen Basma kamar yanda kuka sanni" Meena ce tayi caraf tace
"ba wani nan, da akwai abinda ke going wanda bakya so ki gaya mana, sam ban gane sauya wanki akan zancen aure ba, ko kuma soyayyar Yaya Shureym ke fizgarki" nan take Basma ta b'ata rai, bata ce komai ba, ta cigaba da wankanta, Leema da Meena suka had'a ido sai suka kwashe da dariya, hiransu suke bata tanka musu ba, harta gama ta bar su ta nufi d'akinta. Magrib ya gabato ba halin yin rawa, shiyasa ta wuce d'aki dan gabatar da Sallah akan lokaci.

Bayan k'arfe takwas na dare kamar yanda suka saba fita, yau ma cikin shirin doguwar riga masu fidda tsiraici su Leema suka sanya, Basma harta d'auko wata yalolon riga wanda duk rabin cinyarta a waje yake, sai zuciyarta ya karaya saboda da tunawa da tayi da Yaya Aryan, dole yasa ta maida ta d'auko wata doguwar riga mara tsagu, kuma mai kauri ta sanya, duk da haka tana jin wani iri, zuciyarta na gaya mata kamar taci amanar Yaya Aryan, haka dai ta shirya, ta taje sumanta ta sakeshi a bayanta, ta d'aura hular Queen, sai ta fito a Queen Basma tamkar yanda take a da, tayi kyau sosai, haka sukaita d'aukar photo kafin nan suka wuce.

Kamar yanda suka saba, Leema dama Jalal yana Abuja, cikin k'ank'anin lokaci ya bayyana, yazo suka tafi cikin hotel, Leema kuwa cikin group d'in su na mashaya ta nufa, nan suka soma ihu da kalamai masu dad'i, da irin missing d'inta da suka yi, Basma dai yau a d'arare take ta kasa sakin jikinta, duk hankalinta yaki kwanciya gani take kamar Yaya Aryan zai bayyana a gurin, dakewa tayi ta mik'e ta nufi saman step da abokan rawarta, suka fara cashewa cikin salo mai ban sha'awa.

A can gida kuma, Momy ta shiga part d'in Ammi domin ta kira su Meena, zata sanya su aiki a system d'inta, koda ta shiga wayam, da yake Ammi yau ita ke da girki tana part d'in president, mamaki ne ya cikata, sam bata san sun fita ba, kiran wayansu tayi amma duk a kwashe, girgiza kai tayi tace a fili
"wato Basma bata tashi rashin da'a sai su Meena sunzo, yau kenan a gidan Hutu zasu kwana, anya yaran nan suka aikata Alkhairi kuwa? amma zan d'auki mataki" sai ta ja tsaki ta fice rai b'ace.

Sai misalin k'arfe sha d'aya na dare Basma ta dawo hayyacinta, tunda ta soma rawa saita manta da duniyar da take ciki, Aryan ya fad'o mata a rai a zabure ta fita daga hol d'in ta shiga mota ta rufe, wayarta ta ciro ta kunna, sak'oninsa ne suka fara shigowa har kusan biyar, kan ta kaiga bud'ewa kiransa ya shigo, a tsora ce ta d'auka tamkar mara gaskiya tace
"My Aryan lol, afwan wayana ta mutu ba chrgy ne" murmushi yayi tare da ajiyar zuciya yace
"Alhamdulillah tunda lafiya kike, amma Basma baki tab'a min k'arya ba sai yau" damm gaban Basma ya buga, a tsorace tace
"k'aryan me nayi baby lol?" yace
"saboda tunda nake dake wayoyinki basu tab'a mutuwa babu chrgy ba sai yau, domin wayoyinki uku ne kuma layi daban-daban" jikinta ne ya d'auki rawa cikin rawar murya tace
"am am dama" tsawa ya saka mata
"yimin shuru karki b'atamin rai, ina kika je?" nan take fitsari ya kamata tace
"naje gidan Hutuna ne ni da su Meena" murmushi yayi yace
"good, to kinga abinda ya sa kika kashe waya, saboda yau su Meena sunzo har kin fara mantawa dani, haba Basma kinsan kuwa halin da kika sani dana ji wayarki a kashe"  marairaice murya tayi ta shiga bashi hak'uri, ajiyar zuciya yayi yace
"Basma babu komai banyi fushi ba, sai dai zan rubuta wannan ranar a cikin tarihin rayuwana, ranar da Basma ta fara min k'arya, amma ki kiyaye, kuma ki tabbatar kin ware min lokacina, domin na lura sai na dage miki akan su Meena, dan naga zasu rage soyayyar mu" murmushi tayi ta kuma bashi hak'uri da kalamai masu dad'i har ya sakko, sukayi hira mai dad'i, hakan ya d'auke su har kusan k'arfe d'aya, kana suka yiwa juna sallama.

Sai misalin k'arfe uku na dare suka koma gida, ko wacce d'akinta ta nufa ba ko tub'e kaya duk suka fad'a gado sai barci.

Yau kusan kwana biyar kenan su Basma basa kwana a gida, kullun sai sunje club, Basma tana k'ok'arin ki yayewa Yaya Aryan, domin time d'in wayansu na dare nayi take fita a hol, taje susha hira a waya.

Ta b'angaren Momy kuwa abin yana matuk'ar damunta, in suka fita da yamma sai da safe suke dawowa gida, sam bata nuna musu ta sani ba, kuma bata gayawa kowa ba, yau tayi shirin bin diddiginsu, Yaya Ahmad ta kira yazo sameta a d'aki, suka gaisa, bayani ta shiga yi masa akan su Basma, mamaki k'arara ya bayyana a idonsa, domin bai tab'a tunanin hakan zai faru ba, duk yawan security dake gidan, Momy ta gama gaya masa tsaf, tace
"ina so yau kaje gidan hutun Basma, ka gano min meke faruwa" ajiyar zuciya yayi yace
"insha Allah Momy zanje, domin ni abin nasu ma mamaki ya bani, a ce wai harda Basma, duk yanda akayi su Meena ne suka sauya ta" murmushin takaici Momy tayi tace
"ba ruwansu duk halinsu d'aya, ko da can ma haka suke yi"
"To Allah ya shiryesu, bari mu gani zuwa dare in basu dawo ba, sai na d'auki Naufal muje tare dashi".

*Rahma Ce*
[8/5, 6:46 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *12.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Da Dare*
Bayan sallan Isha'i, Yaya Ahmad ya nufi d'akin Momy ya tambaya ko su Basma sun dawo, Momy ta shaida masa masu dawo ba, da mamakin hakan yabar part d'in Momy, ya kira Yaya Naufal a waya yace masa ya fito ya raka shi wani guri, cikin sauri ya fito suka kama hanya.

Ta b'angaren Basma kuwa sun gama shiri tsaf sunyi hotunan da suka saba, sai suka fito haraban gidan suka shiga mota, mai gadi ya bud'e musu gate, d'aya bayan d'aya suka fice, wanda yayi dai-dai da shigowan Yaya Ahmad layin, ganin motocin su ne, sai Yaya Naufal yace
"to ai gasu nan sun fito ina ga gida zasu" Yaya Ahmad yace
"ai kuwa, amma bari mubi bayansu mu tabbatar da gidan zasu" da sauri ya juya akalan motansa yabi bayansu, tafiya suke da gudu kamar zasu bar gari, sun zo dai-dai kan kwanar da zai sadasu da gida, sai Yaya Ahmad yaga sun mik'e, da mamaki ya juya ya kalli Naufal yace
"ka gani ko, ba gida zasu ba, duk yanda akayi akwai inda suke zuwa yaran nan, Amma dai bari muje" sun cigaba da bin bayansu har su Meena suka isa hotel d'in.

Sun shiga ciki sunyi parking motocin, Yaya Ahmad yayi parking motonshi a waje, da sauri ya fito Naufal na biye dashi a baya, da shigansu sai suka hango su Basma cikin wani shegen shigan tamkar zasu gasar kyawawa, tafiya suke tamkar ba zasu taka ba, har suka shiga cikin club d'in, mamaki da tsoro ne ya lullub'e su Yaya Ahmad, binsu su kai a baya, escot na ganin su Naufal duk suka fara b'arin jiki, d'aya daga ciki bakinsa ya d'auki rawa yace,
"sir sannu da zuwa" Yaya Ahmad ya masa wani mugun kallo ya wuce su, har cikin hol d'in suka bi su Basma, suna hangen inda suke zauna, Yaya Ahmad yace
"Naufal ga key je gida da sauri ka d'auko Momy da Ammi, kace kawai suzo, dan bai kamata ace mu kad'ai muka gansu ba" cikin sauri Yaya Naufal ya amsa ya wuce, Yaya Ahmad ya samu wani kujera ya zauna daga baya duk yana hango su, bayan kamar minti ashirin saiga Jalal yazo ya kama hannun Leema suka bi ta wata k'araman k'ofa ta gefe suka fita, da sauri Yaya Ahmad ya bi bayansu, a hankali yake binsu tambayar b'arawo, har suka isa d'akin hotel d'in da Jalal ya kama, suna shiga ya dawo, jikinsa ne ya d'auki rawa saboda tsabar b'acin rai, yana dawowa hol d'in ya hangi Meena cikin wani group maza da mata suna d'aga kwalaben syrup, bai tsinke da lamarin ba saida ya hango Basma kan step tana kwasan rawa iya k'arfinta, da karairaya jiki, ai tuni wasu zafafan hawaye suka cika masa ido bai taba tsammanin haka ba, lamarin ya girgiza shi, wayansa ne ya soma ringing da sauri ya fita hol d'in, ya duba ashe Yaya Naufal ne sai ya d'aga, ya sanar masa sun zo, da sauri ya isa wurin motocin harda escot d'in su Momy, Ahmad ya kasa magana hannun Momy ya kama suka wuce cikin hotel d'in, haka su Ammi suketa binshi har suka isa d'akin da Leema ke ciki, kwankwa k'ofan yayi, daga ciki Jalal ya bud'e daga shi sai best da gajeran wando, Yaya Ahmad ya runtse ido ya bud'e, Jalal ya na musu kallon mamaki yace
"lafiya wa kuke nima?" daga ciki ne Leema ke cewa cikin d'aga murya
"baby waye ne? kazo mana wlh ina cike da buk'atarka fa" ai da k'arfin Yaya Ahmad ya bangaje Jalal ya kusa kai ciki, su Ammi ma suka rufa masa baya, a razane Leema ta mik'e tana ja da baya harta kai jikin bango, Allah yasa bata cire kayan jikinta ba, idonta ne kamar zasu yo waje saboda tsananin furgici, su Momy da Ammi sai suka hau salati, abin ya girgiza su, Yaya Naufal saboda fushi baisan sanda ya zaro bel d'insa ba ya shiga jibgar Leema, ai Jalal na ganin haka ya fice a sittin, Leema ta kasa ihu domin tashin hankalin da take ciki ya wuce na jin azabar dukan da Yaya Naufal ke mata, da kyar Ammi ta kwaceta tace su fita, haka suka fito cikin tashin hankali.

Momy tace
"ina su Basma suke" Yaya Ahmad yace
"muje in kaiku" ya musu jagora har cikin hol d'in, saboda dan dazon mutane da kyar suka samu hanyar shiga, Yaya Ahmad ne yace
"Momy ga Basma can" yayi mata nuni da inda take kwasan rawa, Ammi ne tace
"innalillahi wa inna ilai hir rajiun, mun shiga uku ni Faitima" idon Momy ne ya kawo kwalla, sai tayi saurin shanyewa tace
"ita kuma Meena tana ina?" cikin mutane Yaya Ahmad ya kusa dasu, ya kaisu hargun da take, suka tsaya ta bayanta, Momy ta dafata, Meena ta juya da niyyar kwararo ashar domin ta riga tayi tatil, ganin Momy a bayanta ne yasa ta mik'e zunbur tace cikin maye
"Ke ya kike min kama da Momy ce" wani wawan mari Yaya Naufal ya sakar mata saida taga taurari, a gigice ta kalle shi, ai tuni hanjin cikinta suka hautsine sai taji cikin ta ya murda, nan da nan jikinta ya d'auki b'ari, ta kasa magana sai rufe baki tayi, idonta tamkar zasu fad'o k'asa saboda tsoro, Momy ce ta kama hannunta suka fita waje, a cikin mota suka sanya ta kusa da Leema, sannan suka k'ara komawa cikin hol d'in.

Yaya Ahmad yabi ta baya ya hau kan step d'in, ya kutsa cikin masu rawan yaje ta bayan Basma ya ya jawota ta baya, ya rad'a mata magana a kunne
"In kin gama rawan ga su Ammi can suna jiranki" sai yayi mata nuni da in da suka tsaya" ai a razane Basma ta juyo, ganin Yaya Ahmad ne yasa tayi luuu zata fad'i k'asa, da sauri ya tallabota ya kamo hannunta suka sauka akan step d'in, mutane suna ta ihu yau Basma ta kula Namiji, a tunaninsu saurayi ne ta samu, suna sauka suka fita a hop d'in, su Momy suka rufa musu baya, ba wanda yayi magana duk suka shiga mota suka wuce gida.

Suna isa gida suka wuce part d'in su Yaya Ahmad, d'aki ya bud'e musu suka shiga, Yaya Naufal ya shiga dukansu saida ya musu lis sannan ya fito ya sanya key ya rufe su, Momy suka wuce part d'in president. Sun zauna dukansu a falon, sai gashi ya sauko ya zauna, Yaya Ahmad suka gaishe shi, sannan suka d'aura da bayanin abinda ya faru, mamaki ne ya ziyarci Abba mik'ewa yayi ya shiga safa da marwa a falon, sunan Basma yaketa ammabato yana girgiza kai, komawa yayi ya zauna, ya d'auki wayarsa ya kira number gomna Ibrahim mahaifin Meena, suka gaisa kana ya sanar masa da
"gobe in Allah ya kai mu suzo akwai family meeting na gaggawa" cikin ladabi ya amsa masa da
""to suna nan zuwa" sai suka yi sallama ya kashe wayar, gomna Ibrahim ya kalli mahaifiyar su Meena ya labarta mata abinda president yace masa, duk suka cika da mamaki suna Allah-Allah gari ya waye su wuce Abuja d'an jin ko lafiya.

Haka Abba ya kira sarkin kano yayi masa umarnin da suzo suma domin family meeting, cikin kulawa ya amsa da alkawarin suna tafe, Abba ya kalli su Ammi yace
"kuna gidan nan ace yaran nan suke fita suna wannan iskancin" cikin damuwa Momy tace
"yallabai kayi hak'uri, amma iyaka kulawa munayi, kuskuren da akayi shine yanda aka basu daman fita ko ina da mota ba mai kwab'a musu, an basu escot duk da haka ya zama aikin banza, Allah ya shirya mana su" duk suka amsa da "Ameen" Abba yace
"lallai laifi nane dana nuna musu gata, kanma ace Basma na sakar mata komai, a gani na Yarinya ce mai hankali kuma mun bata tarbiyya ga kuma ilimi na addini, ashe shirme mukayi, amma insha Allah daga yau zan d'auki tsastsauran mataki" yana gama fad'an haka ya haye sama cike da b'acin rai, su Momy suka bishi da kallo yau ran maza ya b'aci, haka zuka watse a falon cike da damuwa.

B'angaren Yaya Aryan yanata kiran wayan Basma, gata a kunne amma anki d'auka, ya kira ya kai sau ashirin amma ba a d'auka ba, hankalinsa yayi matuk'ar tashi, yana ji a jikinsa akwai abinda ya sameta, dak'ar barci ya d'aukeshi tare da yin mafarkai barkatai marasa tushe.

Basma kuka suke ba k'auk'autawa, kanma ace maka Meena da Leema tamkar zasu had'iye ransu, yau dai dubunsu ya cika, suna tsoron gamuwansu da iyayensu.

*Washe gari*
Da misalin k'arfe goma na safe, gida ya cika da dangi, an cika babban falon bak'i, abinci kala-kala aka jera, duk suna zazzaune, mai martaba da iyalensa Hajiya Sa'a da Hajiya Murja, sai gomna Ibrahim shima da matarsa Hajiya Sadiya, sai kakansu Ahmad Kaka Ma'u, sai su Momy da Ammi, President yana gefe shima, nan suka bud'e taro da addua, president ya soma bayani akan had'uwansu yace

"Mun had'u anan ne domin in sanar maku da cewa, na sanya aurensu Basma nan da wata d'aya, Basma da Shureym, Meena da Naufal, Leema da Jamal, bisa sadaki dubu D'ari, ina so duk sai ku fara shiri daga yau"

Cike da mamaki iyayen suke kallon juna, gomna Ibrahim ne yace
"Yallabai yaushe muka yi magana da kai akan batun aurensu, kace sai nan da shekara d'aya, amma me ya kawo sauyawan wannan lamarin" cike da fad'a Ammi tace
"wannan hukunci shine dai-dai, domin yaranmu suna gab da lalacewa ko ince summa lalace" falon ne ya hautsine da magana ko wanne yana tambayan meya faru, nan Ammi ta kira Yaya Ahmad yazo ya labarta musu komai, ai mai Martaba yafi kowa shiga tashin hankali, cike da b'acin rai yace
"a kira yaran dukansu" cikin k'ank'anin lokaci suka shigo sanye da kayan da suka fita jiya, salati iyayen nasu suka saki kowanne mamaki ya gama cika su, sai suka zauna, nan mai Martaba ya soma musu fad'a daga k'arshe ya shiga nasihi, ya kuma kafa musu doka.

"Daga yau na yanke fitanku waje" ya kai dubanshi ga Momy yace
"ke Maryam ina son yaran nan su zauna a part d'inki" ya cigaba da cewa
"sannan kuma na haramta muku amfani da waya, kuma koda lanbun gidan nan na hana kuje gun, daga part d'in Mominku sai part d'in Ammi da president, Ku tashi Ku bani guri mutanen kawai"

President ne ya dakatar dasu, suka koma suka zauna, yace ma Yaya Ahmad daya kira su Yaya Naufal, yaje ya kirasu.

Nan duk suka shigo da yake duk sun zo da iyayensu, Anty Husnah Autan Ammi wacce take aure d'an senator, Yaya Naufal, Yaya Ahmad, Yaya Jamal. Yaya Shureym, Yaya Adam duk suka samu guri suka zauna, Gomna Ibrahim shine ya fara magana yace

"Ku yaranmu ne, kuma ba zamu yanke muku hukuncin da zaisa muku damuwa ba, duk yanda kuka kai ga lalacewa baza mu k'iku ba, dan haka mun yanke aurenku nan da wata d'aya mai suwa za ayi insha Allah, kai Shureym an bada sadakin Basma, kai Jamal kai da Haleema, kai kuma Naufal kai da Ameena, dama tuntuni mun yanke haka domin mun fahimci kuna son junanku, sai dai yanzu saboda wasu dalilai mun dawo da zancen baya, za'a d'aura muku aure nan da wata d'aya mai zuwa, kai Ahmad da Adam kuyi k'ok'arin gabatar mana da wanda kuke so domin a had'a bikin gaba d'aya".

Yaya Naufal a ransa sam baiji dad'i ba saboda Meena ta gama fita a ransa, Yaya Jamal ma ransa ne ya b'aci dan Gaskiya baya son Leema ya tsani halinta, biyayya kawai zaiwa iyayensa.

Basma ita kuma kuka ta fashe dashi tace
"Wallahi Abba bana son Yaya Shureym, karku had'a auren nan" wani mari Yaya Naufal ya sakar mata wanda ya k'ara gigitata, kuka ta shiga yi sosai tace
"wlh zan mutu bana sonsa, dan Allah karku min haka, na tuba bazan sake ba"
Lamarin ba k'aramin mamaki ya bama iyayen masu ba, domin sun san Basma soyayya suke yi da Shureym, ta b'angaren Shureym baiyi mamaki ba, domin k'ila tana k'inshi ne saboda abinda yake ce mata, tsoronsa karta tona masa asiri.

Momy ce ta dakawa Basma tsawa, sai ta shiga natsuwanta, duk suka fito suka bar iyayen nasu, Basma tana fita tayi hanyar waje da gudu, ai da gudu su Naufal suka bita suna gargad'in masu gadi
"karku barta ta fita".

Kamata sukayi suka kaita d'akin Momy suka rufe, ihu take tana buga k'ofa
"kun daina sona kuna so na mutu, Yaya Aryan kazo ka ceceni zasu rabamu wayyo na shiga uku, wai ba mai Sona ne a gidan nan" surutai take ta yi kamar mahaukaciya, Ammi ce ta shigo falon zata bud'e k'ofar, president na shigowa yace
"karki kuskura ki bud'e ta, yau ina so ta nuna mana karshen hauka, kuma wlh na rantse aure tsakaninta da Shureym ba fashi" yana gama fad'a haka ya fice.

Kaka Ma'u ce ta sanya aka bud'e d'akin ta shiga, Basma ta rungumeta tanata sambatu, Addu'a taketa tofa mata, a tunaninta ko akwai jinnu a lamarin, lallashinta ta shiga yi har ta samu tayi shuru, tana ajiyan zuciya, da haka barci mai nauyi ya d'auketa.

Bayan komai ya lafa, su Meena da Leema an natsu, sun zama kamar kurame, farin cikin su ma za'a aura musu abinda suke so, sai dai zuciyansu na cike da damuwan waye Basma take so haka? sun tausaya mata sosai.

Yaya Ahmad ya wuce d'akinsa, damuwa ne ya shigeshi, yasan dole dama za'ayi haka, kira a wayan Basma ne ya shigo, yana dubawa yaga an rubuta my lol Aryan, kamar bazai d'aga ba saiya d'auka, Yaya Aryan ya fara magana
"Basma, Basma me ya sameki dan Allah kimin magana, ina cikin damuwa" hawaye ne ya kawo ma Yaya Ahmad na tausayinsu yace
"ba Basma bace Ahmad ne" cikin sauri ya tari numfashinsa
"me ya samu Basma dan Allah karka b'oye min" Yaya Ahmad yace
"ka kwantar da hankalinka Basma tana lafiya barci take yi" cikin damuwa yace
"Basma ba tada lafiya, karka b'oyemin akwai abinda ke damunta" kawai saita fashe masa da kuka....

*Rahma Ce*
[8/6, 9:02 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *13.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Hankalin Yaya Ahmad yayi matuk'ar tashi, cikin kulawa yace
"haba Aryan ya, kake abu kamar k'aramin yaro, nace maka Basma tana barci inna farka zansa ta kiraka" ajiyan zuciya Aryan yayi yace cikin damuwa,
"to shikenan nagode" nan suka yi sallama ya kashe wayar.

Basma ta farka da misalin k'arfe biyu na rana, Kaka Ma'u ta sanyata tayi wanka ta sauya kaya marasa nauyi, sallan Azahar ta gabatar kana aka kawo mata abinci, Kaka Ma'u ce ta matsa mata taci, loma uku tayi da kyar kana ta sha ruwa tace ta k'oshi, mik'ewa tayi kamar an tsikareta tace wa Kaka Ma'u tana zuwa sai ta fice, tayi sa'a falon ba kowa haka ta sanya takalmi ta fito haraban gidan, motocin gidan sun ragu da alama sun tafi raka su mai Martaba ne airport, hanyar k'ofar fita tayi tana waige-waige kamar mara gaskiya, masu gadi suka hanata fita, saita fara musu masifa akan su bata hanya ta wuce, ganin ta cije ne yasa suka bata hanya tawuce, tana fita, taga Yaya Ahmad zaune bisa wani dakali daga gefe ashe duk yana jin hayaniyansu, tsayawa tayi cak ta kasa tafiya, Yaya Ahmad ne ya mik'e yazo gabanta ya tsaya cike da tuhuma yace
"Basma bakya jin magana, ina zaki bayan an hanaku fita, ya kike so ki zama mara biyayya ne" fashe masa da kuka tayi, girgiza kai yayi ya kama hannuta suka koma cikin gidan, part d'in su ya wuce da ita ya zaunar da ita a gefen sa ya kira sunanta a nutse

"Basma kin ga abinda rashin ji ya haifar miki, naso ace haka bai faru ba, dana tsaya miki tsayin daka akan baki auri Shureym ba a baki wanda kike so, Basma meyasa kika aje tarbiyanki kika nima lalacewa haka, bayan kinyi saukar Al'Qur'ani har sau biyu, kina da sani akan littafai Addini sosai, a takaice in aka baki aji zaki iya rik'ewa a matsayin Malama, ya a kayi kika shagala da duniya haka Basma?"

Jikinta ne yayi sanyi sosai ta kuma b'arkewa da kuka tace
"Yaya wlh mun riga munyi kuskure, kuma wannan rayuwar a England muka koyoshi, insha Allah bazamu sake ba mun tuba, ni dai ka taimakeni karka bari a aura min Yaya Shureym wlh bana sonsa, kafi kowa sanin waye Shureym bai cancanta ya zama mijina ba" ajiyan zuciya yayi yace
"na sani Basma amma Abba ya riga ya yanke hukunci, ni shawara a gareki shine ki masa biyayya sai Allah ya sauk'ak'a miki lamarin"

"To Yaya kamin Addu'a, amma da son Aryan zan mutu"

Tsaki yayi baice komai ba wayarta ya d'auka yayi dailing number Aryan, bugu d'aya ya d'aga, sai ya mik'a mata ta kara a kunne, a cikin damuwa Aryan yace
"My Basma kina lafiya kuwa?" kuka ta saki wanda hakan yayi dai-dai da k'ara rikicewansa, cikin damuwa yace
"meya faru gayamin mana ko so kike nima nayi kukan". Tuni Yaya Ahmad ya bata wurin domin ya gaji da jin kukan nata, Basma ta shiga bashi labarin komai bata b'oye ba, ai zubbur ya mik'e a tsorace yace
"Basma shikenan kinyi sanadin rabuwanmu, shikanan kin jawo mana damuwa mara yankewa" ya k'arasa maganar cikin rawar murya, Basma sai tai k'ara tsinkewa da sabon kuka, Aryan kashe wayar yayi gaba d'aya, Basma taita dialing number akashe, a firgice ta mik'e ta fita da gudu, Yaya Ahmad yana waje, ganin ta a guje yasa ya bita a guje, wurin gate ta nufa, masu gadi suka tare ta, kuka take da magiya akan su barta ta fita, amma suka k'i har Yaya Ahmad ya cimmu su.

Kama hannunta yayi gam yana janta, ihu sa saka tana tirjiya, ihun ta ne ya dawo da duk hankulan mutanan gidan duk suka fito a guje, da yake sun dawo daga rakiyan, kafin su k'arasa cikin gidan sosai Basma tayi wani ihu saita langwab'e, a razane Yaya Ahmad ya juyo yaga idanunta sun kafe ta suma, jikinsa na b'ari ya d'auketa tsak ya shiga cikin gida da gudu, a hanya

Please Login or Register in order to submit comment