Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kumatunta ya kunbura da leb'enta, idonta yayi k'anana gaba d'aya ya sauya mata kamanni, hawaye ta share tace a fili
"Abba Ku kuka jamin" kaya ta sanya marasa nauyi ta cire zanin gadon ta ta sanya wani, taje ta kulle d'akinta ta koma gadon ta kwanta cikin k'ankanin lokaci barcin wahala ya d'auketa.

Shureym saida ya samu yayi wanka kafin ya samu nutsuwa, nadama ne ya lullub'eshi akan abinda yayi wa Basma, ga kuma kunyar Safeena da yakeji, wannan dalilin ne ya hanashi fitowa sai kawai ya kwanta har barci ya d'aukeshi.

Safeena kuwa ta kasa ta tsare a falo tana jiran fitowan Shureym, jin yayi shuru bai fito ba saita gyara zama ta kunna tv tana kallo, sai bayan k'arfe biyu Shureym ya fito daga d'akinsa, ya had'e giran sama dana k'asa yana hura hanci duk na borin kunya, Safeena tana ganin shi sai ta kwashe da dariya, dan gaba d'aya ya bata dariya sai wani basarwa yake yi, zama yayi gefenta yace cikin fishi
"meye kika gani na dariya a jikina?" ya mutse fuska tayi tace cikin tsiwa

"wlh Shureym kaji kunya, banda Allah yasa nazo na ritsaka, da ka kashe musu Yarinya, kanata cika min baki akanta, ashe duk burga ce na d'a Namiji, Allah ya kyauta maka, kuma ka sani Basma Yarinya ce imma zaka amshi hakk'inka, to ba da k'arfi zaka amsa ba saika bita a hankali"

Tana gama fad'a ta mik'e ta shige kicin, abinci ta zubo masa ta mik'a masa, murmushi yayi ya amsa tare da cewa
"Tnx my Baby, banyi tunanin zaki saurin saukowa haka ba" hararenshi tayi ta koma ta zauna tare da d'aura k'afa d'aya kan d'aya, ya soma cin abincin tace

"Shureym ina Sonka sosai, bazan iyi dogon fishi da kai ba, da ace d'azun baka rufe d'akinka ba, har na sameka a ciki, da saina sauke maka kwandon rashin mutunci, amma na sauko, sai dai yanzu na daina yarda da alk'awarinka domin nasan watara saika karya shi" zai yi magana ta d'aga masa hannu tace
"kai dai ci abinci kawai".

Bayan la'asar Basma tayi shigar doguwar riga abaya brown, tayi rolin da gyalen, jaka ta d'auka bak'i ta sanya takalmi bak'i, ta same su a falo bata kalli inda suke ba tayi hanyar fita, da sauri cikin tsawa Shureym yace
"ke ina zaki?" tsayawa tayi cak bata juyo ba kuma bata ba shi amsa ba, saida ya kuma maimaita tambayan, amma shuru ta masa, k'arshema tasa kai ta fice, a zuciye ya mik'e zaibi bayanta, Safeena na rik'e hannunsa tace
"haba Shureym wani irin abune wannan, ka duketa d'azun ka kumbura mata fuska, ka sani ko asibiti zata je, ka rabu da ita taji da kanta mana" cike da mamaki ya juyo ya kalleta yace
"Safeena yaushe kika zama haka? da har zaki tausayawa wannan shaid'aniyar yarinyan' murmushi tayi tace
"Shureym ni mace ce mai rauni, dole ne inyi saurin tausaya mata akan irin lahanin da kaso yi mata, tana gama fad'an haka ta d'aure fuska, kana ta wuce d'aki.

Basma tana fita ta tari taxi asibiti ta fara zuwa, likita ya dubata ya bata Magani da kuma alluran zazzabin da take ji, daga nan saita wuce wurin wani gidan abinci, zama tayi ta sanya aka kawota drink da snacks, nan taci tana nazarin wani mataki ya kamata da d'auka, a haka ta gama komai saita wuce wani studio na kusa da gidansu, ta shiga ta sanya aka d'auki hoton fuskanta kana aka wanke aka bata ta dawo gida.

Bata samu kowa a falon ba saita wuce d'akinta ta bud'e ta shiga tare da sanya key, wani jaka ta ciro ta bud'e da wani k'aramin key, ta ciro diary d'inta ta shiga rubuta abin da ya faru da ita na wannan ranar, sannan ta maida cikin jakan tare da sanya wannan hoton aciki, sai ta maida ta rufe ta ajeshi cikin wani dirowa, ta dawo kan gado ta zauna tare da rafka tagumi.
Wannan diary d'inta ne tun ranar da suka sauka a k'asar America, ta fara rubuta duk abinda Yaya Shureym yake mata na muzgunawa a ciki, dan ya zame mata tarihi da zata rik'a tunawa.

Wayarta ta ciro a jaka ta kunna, sak'onnin text suka fara shigowa, gaba d'aya text d'in yan uwanta ne, d'aya bayan d'aya ta rik'a karantawa, wani tayi kuka wani tayi dariya, nan take kewar family d'inta ya taso mata, WhatsApp d'inta ta bud'e, sakonni suka fara shigowa, ta mance rabonta da hawa online, group ta shiga na family d'insu, nan fa tayi sallama suka fara amsawa cike da murnan sake ganinta, duk suka gaisa na yaushe gamo, Meena ce tace
"ke Besty akwai labari muje group d'inmu" nan suka koma group d'in su mai sunan *Manyan Mata, One family* Leema ma ta shigo can sai ga Deeja ta shigo, yanzu su had'u ne a group d'in, sunata murnan ganin Basma, nan suka shiga hira, Meena tace
"kinsan kuwa Leema da Deeja ciki ne dasu" Basma cikin farin ciki tace
"Dagaske? kice mun kusa samun yara"
"Eh wallahi, two month yanzu"
"ikwan Allah, yanzu fa mun kai 3month da aure, lallai abin ba wuya, to Allah ya musu albarka ya rabasu lafiya, to Meena kefa?" Meena tace
"Ni nawa 1month ne yanzu"
"lallai kuce kun girma, Allah ya inganta" Deeja tace
"waya sani ko kema kina da naki a k'unshe bamu sani ba" dariya tayi sosai tace
"wace ni, ai in gaya muku banda komai, ina planning tukunna" Leema tace
"Malama ki fad'a mana gaskiya kawai"
"Hmmm Allah kuwa gaskiyar kenan" nan dai suka cigaba da hira, sun shafe lokaci sosai suna hira, sallama su kayi saboda dare yayi sosai a Nigeria, su kuma Basma yamma ne a nan. Cike da kewar family d'inta ta mik'e ta shiga kicin, abinshi ta shiga girkawa.

*Bayan Mako biyu*

Basma ta shirya da yamma k'arfe hud'u, tayi shigar riga da wando na Pakistan, tayi rolin da gyalen shi, jaka ta d'auka da takalmi ta ficewarta, yau tayi sa'a ba kowa a falon, taxi ta tare ta nufi wurin cin abinci, yau drink kawai ta sha, saita ciro wayarta ta hau online tana chart dasu Meena, wani saurayi ne mai tsayi kyakkyawa, ya tako a hankali har wurin da Basma ta zauna, ya tsaya tare da yi mata sallama, cike da kulawa ta amsa tare da d'ago kanta, cikin harshen labarabci yayi mata magana yace
"In zauna?" murmushi tayi tace "eh" sai ya zauna ya cigaba da magana
"Ni sunana Bilal dan k'asar Sudan, nazo nan karatun masters d'ina ne" murmushi tayi cikin larabcin tace
"sunana Basma Bulama ni 'yar Nigeria ce" cike da mamaki ya kalleta yace
"kina nufin ke 'yar Nigeria ce?" Tace
"kwarai kuwa" murmushi yayi yace
"nayi miki kallon ke 'yar k'asar labarawa ce, shiyasa ma nazo nayi miki magana, ashe 'yan Nigeria sunajin labarci sosai haka" dariya tayi tace
"sosai kuwa munaji, domin muna da makarantu acan na larabci" yace
"good, yanzu meya kawo ki America?" murmushi tayi tace
"Hutu muka zo tare da family na" yace
"masha Allah, in ba damuwa zan iya zama abokinki?" murmushi tayi tare da yin tunani kad'an tace
"eh ba damuwa" nan su kayi exchanging contact d'insu, tare da alkawarin zasu had'u washe gari in Allah ya kaimu, nan ya taka mata ta shiga taxi kana ya wuce shima yana farin cikin had'uwa da Basma, cikin k'ank'aninin lokaci ya kamu da Sonta, Basma irin tsarin matar da yake burin aura ce, dama ashe a Nigeria suna da kyawawan mata haka? Tambayan da yayiwa zuciyansa kenan, harya k'osa dare yayi gari ya waye su k'ara had'uwa.

Basma tana isa gida ta same su zaune a falon, kallon arziki bata yi musu ba ta wuce su, Yaya Shureym yace
"Basma wai ina kike zuwa ne?" cikin b'acin rai tace
"inda ka aikeni, kuma ka fita cikin rayuwata in ba haka ba zan maka abinda baka tsammani daga gareni" tana fad'an haka tayi gaba, bud'e murya yayi yace
"wlh in kika kaini mak'ura zaki sha wuya, mara kunyar banza" tsaki tayi ta bud'e d'aki ta rufa da k'arfi ya buga gam, kana ta sanya key, tayi wanka tare da d'auro alwalan Magrib.

*Washe gari*
Ya kama week end, yau Shureym yana gida yana hutawa tare da matarshi Safeena, da misalin k'arfe biyun rana Safeena ta fito, tazo d'akin Basma, bugawa tayi amma kusan minti biyu shuru Basma bata bud'e ba, saida ta kuma bugawa tare da bud'e murya tace
"Basma ki bud'e Safeena ce" murmushi Basma tayi ta sauko a kan gadon ta bud'e mata, da murmushi a fuskan Safeena tace
"Basma dan Allah kin iya wainar fulawa?" Basma tayi murmushi tace
"eh na iya"
"to dan Allah kiyi hak'uri ki d'an yi min mana, saboda Kuku basu iya ba, kuma wlh marmarinsa nake, in kuma ni nayi bazan iya ci ba" murmushi Basma tayi tace a ranta
"shegiya yanzu haka ciki ne dake, kuma in dai wainar fulawa ce za kici kuwa" tace a fili
"OK muje nayi miki"
"yauwa sis nagode bari na jiraki a falo" murmushi kawai Basma tayi bata ce komai ba, tace aranta
"wato yau kinzo da fuskan arziki kenan, saboda zaki more ni, dole a fake da cemin sis" kicin ta shiga, cikin minti talatin ta had'a mata wainar fulawa, taji kayan had'i kuwa, saita kawo mata harda ruwan sha, ta aje bisa table na falon, Safeena na gani ta Shiga lashe baki, jiki na b'ari ta jawo table ta shiga cin wainar, ai had'iyan farko ya tsaya mata a wuya, da sauri ta tashi da gudu ta fad'a bayin dake falo, ta shiga kwara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta, Basma zama tayi a falon tana zuba dariyan mugunta, Safeena a galabaice ta fito ta zauna tana maida numfashi, Shureym ne ya shigo falon yana fad'in
"Safeena lafiya har yanzu aman bai tsaya ba, ko zamuje asibiti ne?" cikin kasalan murya Safeena ta nuna Basma tace
"kaga wacce ta sani amai, nace ta min wainar fulawa saita zabga masa yaji da gishi, loma d'aya nayi na kasa had'iyiwa saida na amayar dashi" cikin b'acin rai ya kalli Basma yace
"dan Ubanki kashemin mata zaki ko, saboda kina bak'in ciki da abinda ke cikinta ko, to wlh maza tashi kije ki dafa mata wani wainar, kuma in kika yi kuskure jikinki zai gaya miki"

Jikin Basma a sanyaye ta koma kicin ta kuma b'ata lokaci ta had'o wani wainar ta kawo mata, Safeena ta saki ciki ta soma ci harda lumshe ido dan dad'insa saida ta cinye tas kana ta kora da ruwa.

Shureym ya kalli Basma yace
"D'auko wancen da kika b'ata ki cinye, dan wlh baza kimin asanar abinci ba" cikin k'unk'unai tace
"wlh ni na k'oshi" belt d'in wandonsa ya zaro ya rik'e, yaje ya d'auko plet d'in wainar fulawan ya dire a gabanta yace
"wlh sai kinci, in kuwa baki cinye ba jikinki zai gaya miki" ai da sauri ta sanya hannu ta d'ibo, tana kaiwa bakinta, zafin yaji da gishiri ya d'arsu a kan harshenta, ai da sauri ta furzar tare da goge harshen, Shureym ya zuba mata belt d'in a gadon bayanta, ai saita tsandara ihu ta shiga sosa bayan, bai hanashi sake zabga mata belt d'in jikinta ba, ya shiga jibgarta tare da cewa saita cinye shi, Safeena dariya ta shiga yi tare da d'aura k'afa kan table, saida yayi mata lilis kafin ya dena dukanta, kuka take tace
"Allah ya isa Shureym, haka kawai ka maidani baiwarka, wlh sai kayi nadaman abinda ka aikatamin, azzalumi fasiki, maci amana" wani wawan naushi ya kai mata a baki, nan take bakinta ya fashe ya shiga zubda jini, da sauri Basma ta dafe bakinta tana kuka, tashi tayi dakyar ta isa d'akinta...

*Rahma Ce*
[8/8, 5:41 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *18.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Bayi ta shiga ta gasa jikinta da ruwan zafi, domin duk jikin yayi mata tsami, bayan ta fito ta samu ta sanya kaya ta fice zuwa studio, photo ta d'auka aka wanke mata, fuskanta ta fito da kyau bakinta a kubbure, ta dawo gida. Rubutawa tayi a diary d'inta kamar yanda ta saba, kana ta koma ta ajiye shi a mazau ninsa, ta had'a tea tasha kana ta d'aura da pain relief tasha, saita bi lafiyan gado.

*Nigeria*

Gudu take tana ihu, Abba kawai take kira tana cewa
"wayyo Abba zai kasheni kazo ka taimake Ni, Momy na wai bakwa sona ne kuka bari zai kashe ni" a razane Abba ya farka daga barcin tare dayin Addu'a
*"A'uzu bi kalimatil lahit taammat min sharri ma kalak'a"* gumi ne ke tsatsowa a jikinsa, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, jingina yayi jikin gado, Momy ta farka a barci saita ganshi zaune, tashi ta yi ta zauna, cikin muryan barci tace
"yallab'ai lafiya ka zauna cikin wannan Daren?" agogan dake manne a d'akin ta kalla, k'arfe biyu da rabi na dare, sharce zufa yayi ya dafe kansa cikin damuwa yace
"Hajiya Maryam wlh mugun mafarki nayi da Basma, hakan ya nuna kamar tana cikin Matsala" Momy ta gyara zamanta tace cikin natsuwa
"Abba wannan aikin shaid'an ne kawai, amma Basma bata cikin matsala, saboda munsan wa muka bama 'yar mu fa, kawai dai kila ka sanya ta a ranka ne saboda rashinta na tsayin lokaci da bata tare damu" ajiyar zuciya yayi yace
"a gaskiya jiki na ya bani Basma tana cikin damuwa, insha Allah gobe in Allah ya kaimu da sassafe zanje America dan ganin lafiyar ta" ajiyar zuciya Momy tayi tace
"Allah ya kaimu goben nima saina maka rakiya" murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga bayi, alwala ya d'auro ya shiga jero sallan Nafila, itama Momy bata kwanta ba, tashi tayi itama tayi alwala tare da gabatar da nata Nafilan.

*Washe gari*

Da misalin k'arfe Bakwai na safe su Abba sun gama shirin tafiya, Abba ya hana Momy tafiya yace tayi zamansa ba zai kwana ba shima, Yaya Naufal tare da muk'arrbansa suka wuce airport ba tare da b'ata lokaci ba, dama jirgin President na jiran zuwansu, shiga suka yi suka kama hanya sai America.

*America*

Basma na kwance a d'aki sai nishi take fitarwa da k'arfi, numfashinta na fita da kyar, ta rufa da bargo amma duk da haka bai hanata jin sanyi ba, sai kerma jikinta yake yi, zufa ne ya lullb'eta hawaye na fita a idonta, a wannan lokacin tana buk'atar tai mako.

President suna isa, aka turo motoci daga gidan shugaban k'asar America ya kwashe su, sun gaisa dashi kana suka ci abincin, shi Abba ya kasa cin komai drink kawai yasha, burinsa bai wuce yaga Basma ba, wayarsa ya ciro ya kira Shureym, bugu biyu ya d'auka cikin ladabi yace
"Abba ina kwana?" Abba ya amsa fuska sake yace

"Shureym gani nazo k'asarku, ina gidan shugaban k'asa, kana ina kazo ka kaini gidanka, domin mu gaisa da Basma"

Ai bai k'arasa maganan ba jikinsa ya d'auki rawa, muryansa har tana sirk'ewa dan fargaba yace
"Abba naje wurin aiki gani bisa hanya zanzo"

"OK saika zo karka b'ata lokaci fa domin yau zan koma"
"to Abba, insha Allah gani bisa hanya". Sai suka kashe wayar.

Ai jikin Shureym na rawa ya tafi gidanshi, ya kira Safeena ya shaida mata zuwan President, itama hankalinta ya tashi, yana isa ya shiga gidan a sukwane, ya samu Safeena a falo tana kai kawo, da sauri ya kama hannunta yace
"kije gidan k'awarki, anjima in sun tafi zan kiraki ki dawo" jiki na rawa ta fice a gidan, d'akin Basma ya nufa ya bubbuga k'ofar amma shuru, hankalinsa a tashe yace

"Basma dan Allah ki bud'e, Abba ne ya zo zani na d'auko shi, dan Allah ki rufa min asiri zan gyara mistake d'in dana miki pls Basma, bari naje da sauri kinga ma kirana yakeyi" bai jira amsarta ba ya fice da sauri.

Hawaye Basma ta cigaba da fitarwa tace
"Bana son ganin kowa, gwara na mutu ma" tsaki taja ta mik'e da kyar ta shiga bayi wanka tayi ta sanya atamfa, riga da sket, bud'e k'ofar d'akin ta tayi, kana ta koma kan gado ta kwanta saboda zazzab'in bai saketa ba.

Sun iso gidan Shureym sai rawan jiki yake yi, yana fargaban Basma karta tona masa asiri, koda suka shiga falon sun zazzauna, sai Shureym yace
"Abba bari na kirata" murmushi yayi yace

"Basma fushi take dani, dan tasan da zuwana, ya kamata ace mun sameta a tsakar gida dan tarbanmu, barni da ita bari naje na lallasheta"

Gaban Shureym ne ya buga damm, amma sai yayi na maza yace
"OK Abba ga d'akinta chan" ya nuna masa d'akin da hannunsa, Abba mik'ewa yayi da sassarfa ya wuce d'akin, turawa yayi a hankali tare da sallama, Basma na kwance ta runtsa idonta hawaye me zafi ya fito a idonta, kanta ta santa cikin bargo ta share hawayenta, ta amsa sallaman a zuciyarta, Abba matsawa yayi gaban gadon cikin lallashi ya fara magana

"haba shalelen Abbanta fushi kike dani, kiyi hak'uri kinji Basma na, aiki ne ya hanani zuwa, wannan tafiyan musamman dan ke nayishi"

Kukanta ne ya fito fili, da sauri ya yaye bargon, sai yaga tana rawan sanyi, da sauri ya isa gareta ya dagota, jikinta ne yaji yayi zafi kamar wuta, yace
"ya salam Basma ba kida lafiya ne?" Langwab'ewa tayi a jikinsa, da sauri Abba ya d'auketa yayi falo da ita, ai Shureym yana ganinsu, gabansa yayi mummunar fad'uwa, rai bace Abba yace
"yanzu Shureym har zaka iya tafiya aiki ka barmin Basma kwance ba tada lafiya?" cikin in ina yace
"em em Abba ayi hak'uri, nima na fita nabarta tana barci, ban zata zazzabi take ba" Abba yayi tsaki yace
"shirman banza, Amanar dana baka kenan nace ka kula min da ita shine zanzo na ganta haka, Yarinya duk ta lalace ta fita hayyacinta" zama yayi da ita akan kujera ya kalli fuskanta, ai gabansa ne ya dad'i, da k'arfi ya furta
"Basma me ya sameki a fuska? ya bakinki ya kumbura haka, me yake faruwa ne wai?" Basma banda kuka babu abin da yake yi.

Jikin Shureym ya d'auki rawa cikin sark'ewan murya yace
"Abba fad'uwa tayi, santsin tyles ne ya kwashe ta ta fad'i, ina ga fad'uwan da tayi shine ya saukar mata da zazzab'i" Basma mamaki ne ya cikata da irin k'aryan da Shureym yake fad'a, Abba ya kalli Basma yace
"wai hakane Basma?" cikin kuka tace "eh" wani nannauyen ajiyar zuciya Shureym ya saki ba tare da kowa ya gane ba, Abba yace
"to Shureym zan tafi da ita Nigeria, inta samu sauk'i sosai sai na dawo da ita" da sauri Shureym yace

"haba Abba kayi hak'uri, ka barta anan, zan kaita asibiti a dubata da kyau, ko jiyan ma na bata pain relief tasha, bansan jikin nata yayi zafi haka da tun safe munje asibiti"

Ajiyar zuciya Abba yayi yace
"to shikenan bari mu tafi, sai ka d'auketa yanzu ka kaita asibiti mu zamu wuce kawai, Allah ya sauke" ya kalli Basma yace
"Basma su Amminki da Momy suna gaidaki, Yayanki Ahmad ya so zuwa, aiki ya rik'eshi" murmushi tayi tace a hankali
"ina amsawa" ta kalli Yaya Naufal ta gaisheshi, ya mata sannu da jiki, duk ta gaisa da wanda suka rako Abba, bandir d'in kud'i mai yawa Abba ya bama Basma yace
"ga wannan kud'in in kina buk'atar wani Abu" cikin murmushi tace
"Abba akwai kud'i a guna fa"
"eh na sani ki k'ara da wannan d'in" godiya tayi masa da kuma Addu'an Allah ya sauke su lafiya, ta bada sakon gaisuwa wurin su Ammi da duk family d'in ta.

Shureym ya kamata kamar gaske sai wani lallab'ata yake, haka suka yi musu rakiya har mota, Basma tana d'aga musu hannu tare da zubda hawaye, Abba tausayinta ya kamashi kwalla ne ya faru a idonsa, shanyewa yayi tare da d'auke kansa, har suka bar haraban gidan.

Shureym mota ya sanya Basma ya wuce da ita asibiti, likita ya bata Magani da kuma allurai nan akayi treatment d'inta, sannan ya biya da ita wurin siyayyan kayan ciye-ciye, ya siya mata su ice cream, kana suka dawo gida, d'aukanta yayi cak ya kaita d'akinta, bisa kan gadonta ya direta, ya zauna a bakin gadon, yace cikin sanyin murya

"Nagode Basma da kika rufa min asiri a yau, nayi nadaman duk abin da na ai kata miki, Basma wlh ina sonki sosai, ke kike ja nake dukanki, pls ki amince mu fara zaman aure kamar kowa"

Hararansa tayi tace
"Shureym ina so ka sani, a duniya kaine mutumin dana fi tsana, kuma kar kaga na rufa maka asiri, kawai na kyaleka ne saboda Iyayena su suka jamin duk wulak'ancin da kake min, ka mai dani baiwarka mara gata da galihu, wlh ka sani na baka talala ne kayi duk iskancin daka ga dama, wlh nasan akwai limit, wataran ko ance ka min wlh bazaka yi ba, dan haka ka tashi ka fita min a d'aki mayaudari kawai azzalumi"
Iyaka fushi ya zuciya, amma dakewa yayi bai furta komai ba, ya fice ad'akin tare da jawo mata k'ofa.

Kuka ta saki mai tsuma zuciya tace
"Abba kun cuceni, da gatana na zama baiwa, Ina *'YAR SHUGABA* na zama mara galihu" saida tayi kuka mai isarta, kana ta mik'e ta fita falo, kud'in da Abba ya bata ta d'auko su a inda ta bari, d'aki ta koma ta rufe, ta aje kud'in a inda take adana kud'inta, murmushi kawai tayi ita kad'ai tasan matakin da zata d'auka akan Shureym.

Safeena bata dawo ba sai cikin dare, ta shiga d'akinta, wanka tayi ta fito tana tsaki, zama yai tace

"gaskiya Shureym na gaji da wannan auren boyen, ya kamata a fito da zancen nan kowa ya sani, Ni da Mijina auren halal, amma ina guje-guje sai kace auren tsiya mukayi, to wlh da sake, ka kira Maminka ka sanar mata na gaji da wannan wasan kuran da nake da danginka"

Sassauta murya Shureym yayi cikin lallashi yace
"Haba my baby love, meye na damuwa? da zaran kin haihu magana zai bayyana a dangi, ran nan nayi magana da Mami ita tace haka, dan haka ki kwantar da hankalinki, yanzu cikinki ba wata hud'u ba, nan da 5month in kin haihu komai zaiyi dai-dai"
Ajiyar zuciya tayi tace
"to shikenan baby wlh d'azun naji haushi sosai, kawai an sani yini a gidan mutane" murmushi yayi ya kamota, nan ya shiga jefa mata zazzafar soyayyansa, tuni ya mantar da ita damuwa.

*Rahma Ce*
[8/8, 5:41 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *19.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Nigeria*

Abba sun sauka lafiya cikin dare, ya shaida ma su Momy Basma na gaishesu ba wata Matsala. Yaya Naufal ya labaratawa Yaya Ahmad duk abinda ya faru, damuwa ne ya ziyarceshi yace
"anya kuwa Shureym na kula da Basma?" Yaya Naufal yace
"yana kula da ita a yanda muka gani, kuma ai in da da matsala zata gayawa Abba" murmushi kawai Yaya Ahmad yayi a ransa yace
"ban yarda ba dole zanyi bincike akai, dan Basma tana da zurfin ciki, ni kad'ai take gayawa damuwanta ko Momy" a fili kuma yace
"hakane, to Allah ya bata lafiya ya k'ara musu zaman lafiya"
"Ameen" Yaya Naufal yace, kana ya wuce part d'inshi.

*Kasar Monaco*

Aryan yayi nisa cikin karatunsa, a yanzu hankalinsa ya kwanta, sai dai har yanzu bai maida jikinsa ba, yana waya dasu Umma da Khadija sai Yaya Ahmad, yanzu ya daina kashe wayansa kullun tana kunne, har yanzu bai dawo cikin walwala ba, baya dariya sai dai yak'e kuma shima saiya d'auro, murmushi ne kawai ya kanyi time to time.

Wata rana yana makaranta ya fito daga aji yana tafiya, karo yaci da wata ta tawo a guje bata lura dashi ba, d'agowa tayi cike da tsoro, cikin harshen turanci tace
"yi hak'uri wlh ban kula bane" gyad'a mata kai kawai yayi sai ya rab'eta ya wuce, binsa tayi da kallo cike da tunani barkatai,

"iya had'uwa wannan guy d'in ya had'u, ko dan wani kasa ne oho? Gaskiya bazan bari ya kub'ucemin ba, dan na kamu da sonsa, kuma shine dai-dai tsarina"

Abinda take fad'a a ranta kenan, da gudu ta bi bayanshi, bata san sunanshi ba gashi ya tsere mata, duk da haka bata hak'uri ba, ta cigaba da bin bayansa da gudu ta cimmasa, gabansa ta sha, sai ta tsaya cike da yin nishi tace

"Yi hak'uri na tsaidaka, sunana Jidda Bukar, ni 'yar Nigeria ce katsina state, muna zama a Abuja, nazo nan karatu ne, in ba zaka damu ba ko zan san daga ina kake? dan kayi min zubin d'an k'asar India"

Murmushi yayi a takaice yace cikin harshen

Please Login or Register in order to submit comment