Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na, Yayana nagode da kulawanka, nasan kaida Momy ne zaku fi kowa shiga damuwa, dan Allah ka bama Momyna hak'uri, kuma nayi muku alk'awari duk inda nake zan kula da kaina zan kare mana martaban gidanmu da mutunci na, insha Allah zan kiyaye duk kan hakk'ok'in Allah wanda ya rayata akaina, kuma zan kare igiyar Aure na.*

*Hawayena ba zasu daina zuba ba, har sai naji a raina kun yafe min laifin dana yi muku akan tafiya da nayi na barku, Ina sonku duka dangina. Abbana ku yafenin Ammi na kar kuyi fushi dani, zan dawo amma ba nan kusa ba, hasalima a yanzu bansan ina na nufa ba*😭.

*Bissalam*🙏
'Yarku Basma...

Kafin ya gama karantawa, hawaye ya gama wanke masa fuska, tashin hankali ya shiga mara misali, da sauri ya share hawayensa ya sanya wasik'ar cikin aljiunsa, kiran wani mai goge masa office yayi, ya taya shi fita da trolley, mota ya sanyasu, ya shiga mota zuwa gida cike da tashin hankali.

Basma suna isa airport ta biya mai taxi, ta ja trolley d'inta wanda ya rage guda d'aya, saita shiga ciki, ba wani b'ata lokaci suka shiga jirgi sai zuwa k'asar Etopia, jirgunsu na d'agawa taji gabanta ya fad'i, kewar family d'inta ya cika mata zuciya, ji tayi dama jirgin zai tsaya ta sauka, runtse idonta tayi tace a ranta

"Anya na yiwa iyayena adalci kuwa? anya na yiwa kaina adalci? shin ya za suji in suka ji labarin na tafi, Allah sarki Yaya Ahmad ban kyauta muku ba"

Ajiyar zuciya tayi tace
"Shureym kaine silan komai, dole in yi nesa da kai da kuma mugun nufinka a kaina, na tsaneka ba zaka tab'a cimma burinka a kaina ba, kuma so nake ka gane kuranka kasan cewa ni Basma 'yar halak ce" saita ja tsaki ta gyara zamanta.

Tsarbi counter ta ciro a hand bag d'inta, ta shiga salatin Annabi s.a.w, nan take taji natsuwa ya ziyar ceta, murmushi tayi saita lumshe idonta kamar mai barci.

Yaya Ahmad yana isa gida yayi parking, da sauri ya fito ya kwalawa wani driver kira, cikin sauri yazo, jakan ya ciro ya ce ya d'auki d'aya, shima ya d'auki d'aya ya rik'e da bak'ar jakar, falon Abba ya wuce dasu, suna shiga suka aje, ba kowa a falon sai ya sallami driver.   Zama yayi dirshen a k'asan kafet, ya rafka ta gumi tunani yake ta ina zai fara, wayansa ya ciro ya kira Amminsa cikin tashin hankali yace "Ammi kina ina? ki zo ina falon Abba" bai jira me zata ce ba ya kashe wayar, haka ya kira Momy itama, ya kira Naufal, ya kira Husna k'anwarsu, cike da damuwa duk suke fito, duk tunaninsu mutuwa akayi, kiran Deeja matarsa yayi ya kuma kira Meena itama, Ammi da Momy har rige-rigen shiga falon suke, tsayawa suka yi cirko-cirko ganin Yaya Ahmad shi kad'ai a falon, Meena ma cikin sauri ta isa falon haka ma Deeja, duk zama suka yi suna jero masa tambaya, Abba dake sama hayaniyar su yaji sai yayi sauri ya fito, ganin su gaba d'aya a falon ya tada masa hankali, saukowa yayi cike da fargaba yace  "lafiya kuka taru anan?" Ammi tace  "Yallab'ai, Ahmad ya kira mu yace mu taru anan, ni wlh duk hanlina a tashe yake, bamu san dalilin kiran ba" Ahmad mik'ewa yayi zai fita a falon, da sauri Abba ya tsaida shi "kai ina kuma zaka? bana son shirme, kazo duk ka tayar mana da hankali" hawaye ne suka ga ya sauka masa a kuncinsa, sai ya share bai ce komai ba ya fice, ai iya ka tashin hankali sun shiga ciki, domin basu tab'a ganin hawayen Yaya Ahmad ba da girmansa, danshi mutum ne mai d'auriya, da wuya kaga abinda zai tayar masa da hankali balle ya sashi kuka.  

Suna cikin zama na damuwa sai ga Yaya Naufal ya shigo, baifi minti biyar ba Anty Husna itama ta shigo, duk suka zauna suka gaishe da iyayan nasu tare da tambayan musabbabin had'uwarsu, kafin su basu amsa, Yaya Ahmad ya shigo ya nufi wurin trolley da suka shigo dashi, ya jawo su zuwa tsakiyar falon, Momy ce taji gabanta ya fad'i duk yanda akayi wani abu ne ya samu Basma dan tasan trolley ta ne.  Yaya Ahmad ya zauna ya soma musu bayanin yanda Baba mai gadi ya kawo masa kayan, sannan ya bud'e wasikar ya soma karanta musu, iyaka tashin hankali sun shiga, Abba mik'ewa yayi ya soma safa da marwa, Yaya Ahmad ya gama karantawa ai sai Momy ta fashe da kuka, su Meena ma haka, Ammi ce tayi jarumta tace "innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yanzu wannan kayan ta ne kenan, ta tafi da sauran?" Yaya Ahmad yace  "eh na bud'e na duba, ya tabbata kayan Basma ce"    Key ya ciro, dama fitan da yayi d'azun shine yaje ya d'auko a d'akin sa, ya sanya ya bud'e jakan, diary d'in ya ciro ya bud'e, shafin farko labarin shigansu jirgi a ranar da suka bar gida a matayinta na Amaryan Shureym, Yaya Ahmad ya shiga karantawa, ai sai duk suka d'auki salati, lokacin da yazo wurin da ya koma kusa da Safeena a cikin jirgi da kuma kissing d'in da safeena ta mishi, basu k'ara tsinkewa ba sai da ya bud'e d'ayan tsafin bayan saukarsu a America, da irin marin da Yaya Shureym yayi mata, kai komai saida ya karanta.   Yaya Ahmad ya shiga labarin irin dukan da Yaya Shureym ya fara yiwa Basma, hoton fuskanta data d'auka ya gani ya mik'e ya nunawa Abba, Abba runtse idonsa yayi saboda tsananin b'acin rai. 

Yaya Ahmad sai da ya karance musu tas abinda ke cikin diary, sun d'auki kusan awa biyu suna aikin sauraren Yaya Ahmad yana karanta musu, lamarin daya fi d'aga musu hankali shine labarin Safeena, da Basma ta bayar a matsayin wai Safeena matar Shureym ne, ga hotuna nan duk sun gani, a cikin jirgi ta k'arasa labarin yanda ta fito daga gidan Yaya Shureym, ta kulle ma'aikatan gidan a d'akinta.

Abba wani gumi yaji yana saukar masa, Ammi tayi tagumi tana yiwa Allah tasbihi, Momy ko hawaye ke fita a idonta, ta kasa furta komai sai Addu'a take a ranta, falon yayi shuru sai shasshek'an kukan su Meena ke tashi, hatta Anty Husna kuka take yi, Yaya Naufal hatta shi sai da ya zubda hawaye ganin irin yanda Shureym ya sauyawa Basma fuska saboda duka,  Abba ne ya nisa cike da damuwa yace  "duk wannan damuwar nine naja, da ban had'a wannan auren ba da duk hakan ba zai faruwa, lallai Shureym kaci mutunci na kuma kaci Amanar zumunci, Amma zanyi maganinka, in har na rasa Basma, wlh kaima saika rasa rayuwanka, kai Ahmad maza ka shirya da kai da Naufal, ku kira min mai Martaba yanzu da kuma Ibrahim su zo yanzu, mu tafi American domin muje muga Matar da Shureym ya aje a gidanshi a ma tsayin Matarsa, na tabbatar Mai martaba bai san da wannan Auren nashi ba"  Nan take su Yaya Ahmad suka kira su, suka kuma shaida musu gasunan zasu biyo jirgi, basu sanar musu komai ba, sun dai ce kirane ta tagaggawa daga president.   

*Bayan awa biyu*
Su Mai Martaba sun iso fadar Shugaban k'asa, ba b'ata lokaci ya sanar musu America zasu domin tabbatar da wani lamari, Dady ne yace  "to an sanar da Shureym da zuwanmu" Abba yace "bai sani ba kuma ba za'a sanar musu ba, sai dai kawai su ganmu, in munje mun dawo zan sanar muku da komai"  Damuwa ne ya ziyarci su Mai Martaba, haka suka kama hanya suka wuce airport, cikin minti sha biyar jirginsu ya d'aga sai K'asar America.

Sun bar su Momy a falon sunyi jugum-jugum ko wanne da abinda yake sak'awa a rai, babban damuwar su da tashin hankalinsu shine

*ina Basma ta nufa...*

*Rahma Ce*
[8/10, 5:31 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *24.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Etopia*

Basma ta sauka a jirgi, sai rarraba ido take ko za ta ga wanda zata iya tambaya, jikinta yayi sanyi ganin tazo garin da bata tab'a zuwa ba, tsoro da fargaba ne ya cika ta, runtse ido tayi ta bud'e tace a fili
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, laa ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazza zalumin, astagfirullah wa'a tubu ilai" abinda tayi ta maimaitawa kenan a zuciyarta, a hankali ta soma jin k'arfin gwiwa da natsuwa, fitowa tayi bakin hanya ta tari taxi, cikin harshen turanci tace
"Hotel mai kyau nake so ka kai ni" cikin harshen turanci ya mai da mata da
"to shigo mu tafi". Ya kai ta babban hotel mai kyau, ta biyashi kana ta wuce ciki, kud'in d'aki ta biya, saita ja trolley d'inta, wata daga cikin ma'aikatan Hotel d'in suka yi mata jagora har d'akin data kama.

Wanka tayi ta gabatar da duk Sallolin da ake binta, bata jin zata iya cin abu mai nauyi, telephone ta d'auka ta kira cikin holel d'in da a kawo mata coffee da kuma Burger, haka suka kawo mata, ta soma cin Burger taji sam teste d'insa ba dad'i, ajiyewa tayi tasha coffee d'in kawai. Tunanin ya za tayi rayuwa anan take yi, can ta tuno da rayuwarta da Yaya Aryan ta tabbatar da shi ta aura duk haka bazai faru ba, kuma ba zata sha wannan wahalar ba, hawaye ya sauka a kuncinta, tace

"ya Yaya Aryan zaiji in yaji labarin na gudu" tunani barkatai tayi kamar zata kunna d'ayan wayarta saita fasa, dan tasan za'a iya nimanta ta layin, cire sim d'in tayi a wayan sai ta adana a cikin wallet d'in ta. Lafiyan gado tabi ta kwanta tana tunanin rayuwa, da haka barci ya d'auke ta.

*America*

Yaya Shureym sun dawo daga Asibiti, baifi minti 20 da wucewar Basma ba suka dawo, hon yayi amma yaji shuru ba'a bud'e masa ba, ba gate man a wurin, saukowa yayi ya bud'e da kansa ya koma mota ya shigo da ita, bai damu daya rufe gate d'in ba, waige-waige yayi amma bai ga ma'aikatan gidan ba, tsaki yaja sai suka shiga falo.

Suna shiga suka fara jin ihu da hayaniya daga cikin falon, bin inda ihun ke fita suka dinga bi har suka isa k'ofar d'akin Basma, kallon-kallo Shureym da Safeena suka yi suna tunanin su waye a ciki, Shureym ne yayi k'arfin hali ya bud'e k'ofar, arba yayi da mai gadi da sauran ma'aikatan gidan sunyi gwimi sai zaro ido suke yi, cike da mamaki ya shiga tambaya su, nan suka bashi amsa, murmushi mugunta Yaya Shureym yayi ya kalli Safeena yace

"kinga aikin shaid'aniyar yarinyar nan ko, wato kwana biyu tayi lamb'o ta natsu kamar ba ita ba, amma yau tasa kai ta fita duk dokar dana sa mata, baisa ta fasa k'etare wa ba, ta musu dubara ta fice, wlh yau inta dawo Ni da ita ne, sai nayi mata dukan da tunda aka haifeta ba ayi mata shi ba, kuma yau saina amshi hakk'ina da k'arfin tsiya"

Yana gama fad'an haka ya wuce ya bama Safeena wuri, Safeena jikinta yayi sanyi, domin ta fara tsorata da lamarin Shureym akan yanda ya damu da budurcin Basma, kishi ne ya rufeta saita bi bayansa a fusace.

Masu gadi haka suka fita sum-sum, dan ba suji duk abin da suke cewaba, a cikin Hausa su kayi magana, sun koma bakin aikinsu.
Safeena ta cimmasa a cikin falon, ya zauna sai gumi yake yana kwafa yace
"Yarinyar nan ni zata rainama wayo, ni bata bani hakk'ina ba taje bama wancan d'an iskan, wai ta yaya zan yarda ba bin maza Basma take yi ba" Safeena ce tace

"Wai kai Shureym meyasa ka damu da Basma ne haka? yarinyar da bata sonka batasan kana yi ba, plss karabu da ita mana ka huta" cikin tsawa yace

"ya isa, ya isa Safeena, wlh kika kuma furta kalman in saki Basma sai na miki abin da baki tunani, banda albarka cin cikin dake jikinki da saina huce haushi na akan ki, kuma in baki sani ba ki sani ina matuk'ar son Basma, son da ban tab'a yiwa wata Mace ba, ban yiwa kaina ba, na gaji da danne zuciyana akan Son da nake mata dan kawai in saki farin ciki, tom daga yau na daina b'oyewa ina son Matata sosai"

Safeena fatsewa tayi da kuka wi-wi, ta kasa ce masa komai, cikin fushi yace
"Malama in zaki min shuru kiyi shuru karki k'ara min damuwa tom" dole ta sassauta kukan, dan tasan halinsa sarai, zai iya mata abin da bata tsammani.

Su Abba sun shigo k'asar America gari ya soma duhu, basu b'ata lokaci ba motoci suka zo d'aukansu daga gidan shugaban k'asan America. Suna d'aukansu Abba yayi umarnin da su fara zuwa gidan Shureym, in yaso saisu wuce can gidan president su kwana washe gari su wuce Nigeria. Sun isa k'ofar gate d'in gidan, Abba yace suyi parking a waje su shiga.

Ta b'angaren Shureym kuwa suna zaune a falo ransa a b'ace yake, sai duba agogon Hannunsa yake yi har zuwa lokacin Basma bata dawo ba, ya cika yayi mak'il kamar zai fashe dan haushi, ita dai Safeena tayi turus da ciki, tayi tagumi dan yau gaba d'aya Shureym ya saurya mata ba wanda ta sani bane,

Suna cikin wannan zaman ne ko wanne da abinda yake sak'awa a rai, sallaman Yaya Ahmad ne ya katse musu dukkan tunanin su, a zabure Shureym ya mik'e idonsa tamkar zasu yo k'asa dan tsoro, Yaya Ahmad fuskansa ba yabo ba fallasa ya shigo, su Mai martaba suna biye dashi a baya, ai nan take Shureym yaji tamkar k'asa ya bud'e ya shige ciki, cikinsa ne yayi wani k'ara alaman ya kulle masa, idonsa tamkar zasu yo k'asa ya kalli Safeena wanda itama ta gama tsurewa tana tsaye, dukansu sun gama shugowa falon, sun kafe su Shureym da kallo kowan ne yana nazarin su, atamke fuskokin su yake tamkar anyi musu mutuwa.

Mai Martaba ne ya kalli Safeena yace
"Yarinya ke wacece a gidan nan kuma ina Basma take?" Cikin rawar baki Shureym ya amshe maganar
"Em em baf baf Baffa Ku zauna mana a kawo muku ruwa" Mai Martaba ya dakatar da shi yace
"Banyi magana da kai ba, ke bani amsan tambayata" cikin sanyin jiki da tsoro tace

"Ni ma Matar Shureym ce watanmu 8 da aure kenan, anyi bikinmu da wata d'aya akayi aurensa da Basma, kuma Basma tun safe da ta fita har yanzu bata shigo ba, muma zaman jiran shugowarta muke"

Cike da tashin hankali Mai Martaba ya kalli su President yace
"kunji abinda wannan Yarinya tace kuwa? kai Shureym abinda ta fad'a gaskiya ne?" sun kuyar da kai yayi k'asa ya kasa cewa komai, gumi ne yake karyo masa, tashin hankali ya shiga, hawaye ne ya fara zarya a kuncinsa ya kasa d'aga idonsa. Mai Martaba yace
"yanzu Shureym abinda ka aikata mana kenan?" Dady ne ya nisa yace
"da kyau Shureym yanzu sai ka fita ka nimo mana Basma mu tafi da ita, shine ran nan harkana iya kawo mana k'aranta, ashe Kaine azzalumi maci amana daka ci Amanarmu" yana gama fad'a president yayi murmushin takaici yace
"am Ibrahim Basma bata k'asar nan, a yanzu haka mu kanmu bamu san inda take ba" cikin tashin hankali Dady da Mai Martaba suka ce
"what" dama kunsan da haka, wai mai yake faruwa ne?" anan ne Shureym ya soma kuka wiwi yace
"Na shiga uku Basma ina kika je, karki min haka, wlh ina son ki dan Allah ki dawo gareni, bazan iya rayuwa babu ke ba" wani wawan mari Yaya Naufal ya sakar masa a kumatu yace cikin zafin rai

"mugu azzalumi maci amana, wlh kayi asaran rayuwa Shureym, ka b'atawa k'anwata rayuwa, ka kwashe dukkan farin cikinta, bak'in cikinka yasa ta tafi tabarmu, yanzu bamu san wani hali take ciki ba, kaci amanar zumunci" hawayen bak'in ciki ne ya zubo a idon Naufal, hakane yasa shi dole yayi shuru, kuka Shureym yake sosai yace

"Abba Ku yafe min, na yarda nayi kuskure, amma dan Allah karku raba aurena da Basma, ina sonta sosai dan zan iya mutuwa in aka rabamu, dan Allah Ku nimo min Basma"

Yaya Ahmad murmushi yak'e yayi dan takaici yace
"Baka yi kuka ba tukunna Shureym, wa san yara kake yi" Abba yace
"tunda idonmu ya gane mana komai mu wuce makwancinmu" Dady yace
"kwarai kuwa, amma Ni fa banga ta barci ba, Basma nake so in san ina ta tafi" Abba yace
"karmu damu insha Allah zata dawo cikin k'oshin lafiya, tun d'azu na sanya Commissioner 'yan sanda Mukhtar ayi binciken airport, dan sanin wata k'asa ta tafi, sai mubi bayanta" Yana gama fad'an haka suka fita, sun bar Shureym  durk'ushe yana kuka cike da tashin hankali kamar k'ara min yaro, nadama ya rufe shi yana dana sani.

Koda ya d'ago ko kallon inda Safeena take baiyi ba, d'akinsa ya wuce ya shiga had'a kayan shi, Allah-Allah yake gari ya waye, yaje office d'insa ya musu sallama ya wuce mahaifansa Nigeria. Safeena ma bata yi k'asa a gwiwa ba wajen had'a kayanta, dan ta tabbata barin su k'asar America yayi, kuma k'afar Shureym k'afarta, koda zai yankata gunduwa-gunduwa ne, sai ta bishi.

Abba sun isa masaukinsu, suka ci abincin suka huta, su Dady duk suka kira matayensu akan Gobe in Allah ya kaimu su hallara zuwa abuja dukansu, ki wanne ya wuce makwancinsu. Haka suka kwana ko wanne cike da damuwa, yanzu tashin hankalinsu ina Basma ta tafi.

*Washe gari*

Basma tana farkawa ta shirya cikin doguwar rigan atamfa, ta sanya farin hijabi ya kawo mata iya gwiwa, ba dan kwali a kanta da yake hijab d'in mai hula ne, kayanta ta gama had'a su, fitowa tayi daga hotel d'in tana Jan trolley d'in ta, airport ta wuce tayi duk abinda ya kamata, saita shige jirgi sai k'asar Saudia, zuciyarta cike da farin ciki domin zata ziyarci d'akin Allah da kuma Masallacin Annabi s.a.w, tasan cewa zata samu farin ciki acan da samuwar dukka nin natsuwa.

*Rahma Ce*
[8/10, 5:32 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *25.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*K'asar Monaco*

Yaya Aryan tunda gari ya waye yaji gaba d'aya hankalinsa ya koma Nigeria, tunani barkatai ya shiga yi, cikin sauri ya mik'e ya shiga had'a kayansa, yana kammalawa yayi wanka ya shirya cikin Manyan kaya, Shadda ganila ash color ya sanya hula bak'i da takalmi, tare da sanya bak'in tabarau, yayi matuk'ar kyau, hakanan ya tsinci kansa cikin nishad'i, burinsa bai wuce ya ga Ummansa, ya wuce airport sai Nigeria.

*America*

Su Abba sun kamo hanyan Nigeria, Shureym ya tafi office d'insa ya aje musu komai nasu, ya sallame su, sunyi-sunyi ya k'arasa aikinsa amma yak'i dole suka hak'ura, gida ya koma ya kwashi kayansa, Safeena na biye dashi ba um ba um-um a tsakaninsu, sun shiga mota da duk kayansu, shureym ya sallami duk ma'aikatan gidan ya bama wani abokin aikinsa Key d'in gidan, dama gidan na ma'aikatansu ne, airport suka wuce baifi minti talatin da zuwansu ba jirginsu ya d'aga sai Nigeria.

*Nigeria*

Yaya Aryan ya sauka lafiya, taxi ya shiga ya sauke shi a gida, yana shiga suka gaisa da mai gadi, ciki ya shiga ya wuce d'akinsa, wanka yayi ya sanya k'ananun kaya, kana ya nufi sashin Umma, bata san da dawowansa ba, domin yana so yayi surprising d'inta, yana shiga falo yaga Iya mai aikinta suka gaisa Iya tace
"aiko Hajiya bata nan" zama yayi ya kira number Umma ringing biyu ta d'auka yace
"Umma kina ina na dawo ina son in baki mamaki kuma bakya gida, da safen nan ina kika je haka?" murmushi tayi tace
"Aryan wani irin ka dawo, ba munyi da kai sai nan da wata uku zaka dawo ba, meya dawo da kai yanzu?" dariya yayi yace
"Umma hankalina ya dawo gida ne wlh, kewarku ya cikani sosai, shiyasa na dawo, yanzu kina ina ne?" tace
"ina gidan shugaban k'asa wurin Khadija" yace
"Da fatan dai lafiya ko?"

"lafiya lau, ka k'ara so ka gaishesu mana"
"To Umma gani nan zuwa" haka ya mik'e ransa bai masa dad'i, yana ji kamar karya je.

Khadija ta kira Umma ta sanar mata da abinda ke faruwa, dalilin zuwan Umma kenan da safen domin tayi musu Allah ya kyauta.

Yaya Aryan ya isa gidan president, ya same su Umma a part d'in Momy, zama yayi a k'asan kafet, Kansa a sunkuye ya gaishe dasu Ammi, ganin falon cike da mutane ya sashi jin wani iri, sai ya fito Deeja ta biyo shi a baya.

Sun zauna a barandan shan iska dake cikin farfajiyan gidan, nan suka k'ara gaisawa suka shiga hiran zumunci, Deeja bata yi gigin gaya masa abinda ke faruwa ba, Umma ce ta fito ta samesu suna zaune cikin barandan, murmushi Umma tayi, farin ciki ne ya mamayeta Aryan ya dawo da walwalansa, Addu'a tayi Allah ya bashi mata ta gari. K'arasawa tayi wurin tace
"Deeja ni zan tafi in Ahmad ya dawo ki gaishe shi" Deeja ta kwab'e fuska kamar za tayi kuka tace
"kai Umma baki dad'e ba fa, kuma da kin jira sun kusa k'ara sowa ma" murmushi tayi tace
"haba Deeja baki ganin Yayanki ya dawo ne, so nake inje in had'a masa abinci dan nasan da wuya inya karya ma" Murmushin jin dad'i Yaya Aryan yayi yace
"kinsan kuwa Umma nayi missing d'in Abinci ki, kuma akwai yunwa a tare dani, ki tafi kawai nima ina bisa hanya" dariya tayi tace
"yauwa Aryan saika tawo" nan tayi sallama da Deeja ta wuce ta shiga mota driver ya jata sai gida.

Aryan suna zaune a wurin Yace
"Deeja lafiya naga gidan naku da taron mutane?" murmushi yak'e tayi tace
"lafiya lau, president ne yayi umarni da duk a taru anan, mutanen kano da Kaduna duk sunzo, yanzu jiran isowarsu muke daga America" yace
"to Allah yasa lafiya, Nima ina ganin bari na gudu ba zan iya jiran su dawo ba, zuwa gobe in Allah ya kaimu zanzo na gaishesu" bai rufe baki ba, motoci suka fara shigowa cikin haraban gidan, Deeja tace

"laaa gaka sun dawo ma muna zancen su" murmushi kawai yayi baice komai ba, yana kallon mototcin da suke shigowa, da sauri ya mik'e lokacin yaga su Yaya Ahmad sun fito ya isa wurin yana dariya, suka kama hannun juna cike da farin ciki a fuskokinsu Yaya Ahmad yace
"Aryan saukan yaushe?" cike da dariya yace
"yau na sauka"
"to kai da mu kayi waya kace sai nan da wata uku zaka dawo" murmushi yayi yace
"wlh naji hankali na yayo gida burina in ganin a Nigeria" gaban yaya Ahmad ne ya fad'i amma saiya dake, ya mayar masa da murmushi yace
'lallai fa kace kana kewarmu"
"kwarai kuwa nayi"

Nan ya wuce wurin President ya risina zai gaisheshi, Abba shafa kansa, ya kama hannun Aryan suka wuce babban falonsa.

Falon ya cika da dangi, Dady, Abba, Mai Martaba, da duk iyalensu, Ammi, Mami, Momy, Umma, Hajiya Murja, Duk suka gaisa, suna cikin wannan zaman ne sai ga sallaman Yaya Shureym a birkice ya shigo, Safeena na biye dashi a bayansa, Mami na ganinsu gabanta ya fad'i damm, a razane ta mik'e tace
"Shureym lafiya na ganka haka wurjanjan" zuwa yayi ya rungumeta ya soma kuka wiwi, duk mamaki ya cika mutanan falon banda su Abba dasu suka san komai.

Yaya Aryan yana gefen Yaya Ahmad suna hira k'asa-k'asa, Dady ne yayi gyaran murya yace
"Kai Shureym samu wuri ka zauna, da fatan duk kun san musabbabin taruwan mu anan, akan Shureym da Basma" ai yana furta Basma Yaya Aryan ya d'ago fuskansa gabansa ne ya shiga dukan uku-uku, mutanan falon yabi da kallo amma baiga Basma ba, dama tun d'azu yake raba ido ko zai ganta, amma shuru ba alamunta, kamar zai tambayi Deeja amma saiya fasa.

Abba yasa Yaya Ahmad ya karanta lettern da Basma ta rubuta da kuma diary d'inta, nan ya shiga karantawa iyayen sai salati suke yi dama su Mai Martaba basu san komai ba sun dai je America sunga Shureym da mata, Mai Martaba jikinsa yayi sanyi, yace a ransa
"lallai shureym yaci amanansa" k'arin tashin hankalinsa yanda Shureym ya maida Basma tamkar baiwansa.

Yaya Ahmad ya gama karantawa, Aryan gumi ya gama jik'ashi, kamar shine yayi karatun, falon ne yayi shuru, Ummi tace
"ai biri yayi kama da Mutum, kazo ka kawo k'aranta harda yiwa Yarinya k'azafi, ni dama ban yarda ba, ashe kai ne ke cutar da ita"

Mai Martaba yace
"ka kyauta Shureym, yanzu amanar da muka baka kenan, kaci amanata da zumuncinmu ban tab'a tsammanin haka daga gareka

Please Login or Register in order to submit comment