Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

turanci
"sunana Aryan Aliyu, Dan k'asar Nigeria" ido ta zaro tace
"wow ashe k'asarmu d'aya, wlh gani nayi ba kayi kama da 'yan Nigeria ba, amma nayi murna sosai, cewa nayi bari na biyo ka saboda naga Kana da sauk'in kai, in ba damuwa ko zamu kulla abota" ransa ne ya b'aci, amma saiya dake cikin rashin sakin fuska yace
"nagode, amma ba zai yuwu ba kawai, in dai mun had'u sai mu rik'a gaisawa" yana gama fad'an haka ya wuce, binsa ta cigaba da yi tare da yi masa magayi akan suyi exchangen number, tsayawa yayi zuciyansa na tafasa cikin masifa yace
"ya isa dan Allah, kiyi hak'uri ina da mata, pls ki fita a harkata, sai wani bina kike kamar naci miki bashi" jikinta ne yayi sanyi bata k'ara furta komai ba sai ta juya ta fara tafiya, tausayi ta bashi sai ya dakatar da ita yace
"Jidda kiyi hak'uri ban cika son ana takura min ba" juyowa tayi idonta ya cika da kwalla tace
"ba komai na fahimceka" Numbern shi ya karanta mata, kana suka yi sallama.

Ta wuce cike da murna shi kuma ya tafi cike da tunanin Basma, ji yake kamar yaci amananta, wani b'angare na zuciyansa yace
"bakaci amana ba, itama ai tanacan tare da mijinta" runtse idonsa yayi hawaye mai zafi ya fito masa, ji yayi komai ya dawo mishi sabo, zazzab'i ne ya rufeshi, sai ya tafi gida cike da matsananciyar damuwa.

Tun daga wannan ranar Jidda ta mak'alewa Aryan, Sam baya son abinda take masa, yana k'ok'arin janye mata amma sai k'ara shige masa take, ita burinta bai wuce ta samu zuciyar Aryan, ko bazai aureta ba tunda yace yana da mata, zata amince masa su tab'a rayuwa ko kad'an ne, domin tana fama da sha'awansa.

Aryan yana gida a kwance da yamma, sai yaji anyi masa knocking, tashi yayi ya tafi ya bud'e, mamaki me ya rufe shi ganin Jidda ce, murmushi tayi masa sai tabi gefensa ta shige d'akin, binta yayi da kallon yana mamakin yanda akayi tasan gidansa, cikin nuna ko rashin damuwa Jidda ta cire mayafinta ta zauna a kan kujera mai mazaunin mutum d'aya, komawa yayi ya zauna kujeran dayake fuskantarta tace

"Nasan kayi mamakin yanda akayi na gano gidanka, kasan ance mai son d'an tsuntsun shike binsa da jifa, Aryan wlh ina sonka amma kak'i bani gurbi a zuciyanta"

Aryan d'aure fuska yayi yace
"Jidda nafiso ki bar alak'anmu da abota kawai, domin bana tunanin zaki samu gurbi a raina, dan na riga na bada soyayyata ga wata"

Hawaye ne ya cika mata ido tace
"pls Aryan, ni wlh ko kaina kace in baka a shirye nake" mik'ewa tayi ta juya a gabansa ta cigaba da cewa
"Kalli surata da kyau, ina da duk abinda mace take dashi a jikinta wanda namiji zai mora, dan Allah ka yarda dani in zama mai d'ebe maka kewa, koda baka sona in har ka yarda min da haka zanyi murna"

Aryan cikin b'acin rai ya mik'e nuna mata hanyar waje yace
"Jidda natsaki na tsani mata masu irin halinki, ki sani har ki mutu ba zaka samu yanda kike so ba domin nafi k'arfin iskancinki, kuma ki sani Ni ba kalar ki bane, ki gaugauta cireni a cikin jinsin mutanan da kikasani" jiki na rawa ta mik'e zata bashi hak'uri, cikin tsawa ya dakatar da ita
"Na ce ki fita" da sauri ta kwashi kayanta ta fita tana mai jin haushin kanta, rufe k'ofarsa yayi tare da sauke ajiyan zuciya, Addua yayi da k'ara niman tsari ga irin wannan matan.

Tunanin Basma ya shiga yi,
"Yarinya ce mai natsuwa, duk wayewarta a kame take, ga kud'i da jin dad'i na rayuwa amma akwai tarbiyya mai kyau, har abada yanajin ba zai samu mace kamarta ba" hawaye ne ya zubo mashi yace a fili

"Basma har abada ina sonki, babun macen da zan aura ta kai matsayinki, nasan haduwata dake wani jarabawa ne a rayuwana, Allah ya rabamu ina tsananin sonki, Allah ka bani wacce zata share min hawaye na".

*_Aryan nima na tayaka da cewa "Ameen". Masu karatun bari mu koma k'asar America mu ga wainar da Suke toyawa._*

*Bayan wata guda*

Basma ta warware, zamansu kuma yana nan zaman doya da manja, da dad'i ba dad'i, kadaran kadahan, Basma yau tasha Riga da wando English wears, saita d'auko gyale tayi rolin iya kyau tayi, jaka ta d'auka ta fito falo, Safeena ta tarar tana shan fruit, Safeena tace cikin tsokanar fad'a

"Ayawo yau kuma shigan yan iska kike ji?" Basma bata tanka mata ba, illa tsaki taja ta fice, Safeena ta ce
" 'yar rainin wayo, zaki had'u da Shureym shine dai dai da iskamcin ki".

Basma na fita taxi ta shiga ta wuce inda suke had'uwa da Bilal, ta sameshi yana jiranta, kallonta yake cike da soyayya yace
"Basma kinyi kyau sosai" murmushi tayi tace
"nagode muje ko" wurin shak'atawa suka wuce, suna tafe suna hira, Bilal yace

"Basma yaushe zaki kaini gidan ku na gaida da Iyayenki, nifa da gaske sonki nake kuma aurenki zanyi, dan har na fara magana da Ammi na" Murmushi tayi tace

"ni iyaye na suna Nigeria, yanzu da Yaya na muke a nan k'asar, kuma ina so ka sani gaskiya ina da aure" ai bata k'arasa maganar ba ya juyo a zabure yace
"pls my Basma ki daina fad'an wannan maganar imma wasa kike" murmushi tayi tace
"Bilal da gaske nake, Mijina dai baya tare dani yana k'asarmu" tab'oye masa hakan saboda bata son yasan komai nata, cike da damuwa ya samu guri yayi parking yace

"meyasa kike wasa da aure, Basma na tabbata ke mace ce mai ilimin addini, meyasa bakya amfani dashi, yanzu kusan 1month da had'uwarmu, sauk'in abin ma tun farko kink'i Amincewa dani muyi soyayya, kin ce ke kin d'ukeni brother d'inki ne, dama nike kid'ana da rawa, da tun farko kin gaya min kina da aure da alak'anmu batayi nisa ba, ko kuma dana nasan yanda zan fuskance ki, amma ba damuwa naji dad'i da kika gayamin gaskiya, zan koyawa kaina hak'uri da soyayanki, sai mu cigaba da zumunci"

Murmushi tayi tace
"nagode da tunatarwa, insha Allah zan gyara muje ko"

"yanzu ina muka nifa?" murmushi tayi tace
"muje wurin wasa da mota ko?" dariya yayi yace
"OK my Friend" dariya tayi tace
"abotan harya fara aiki kenan" murmushi kawai yayi ya tada mota suka cigaba da tafiya.

Sai k'arfe bakwai na dare Basma ta dawo daga wurin kallonta wasan mota, Bilal ya sauketa a k'ofar gida, hakan yayi dai-dai da cillowar motan Yaya Shureym, ita kuma tana d'aga ma Bilal hannu harya wuce, sannan ta shiga gida.

Ta samu Safeena zaune sai d'irkan abinci take, tsaki Basma taja tace
"Mutum baida aikin yi sai ya zauna yaita d'irkan abinci kamar jaka, wai dole ita mai ciki" Murmushi Safeena tayi bata ce komai ba domin ta riga ta had'a mata bomb mai kwacenta yau a gun shureym sai Allah.

Safeena ta gayawa Shureym daya dawo, k'arya da gaskiya akan fitan da Basma take yawan yi da kuma mummunar shiga, ransa yayi matuk'ar b'aci, fita yayi nimanta wuraren shak'atawa ko zai ganta a can, amma haka ya karad'e yawan nimanta bai ganta ba, dawowansa kenan yanzu daya hangota tana d'agawa wani hannu, ransa ya k'ara b'aci sosai kishi ya rufe masa ido, da sauri ya shiga gidan yayi parking.

Falo ya shiga da sauri ya soma kwalawa Basma kira, da sauri ta fito tana fad'in
"dan Allah karka fasa min kunne, sai wani kwala min kira kake, sai kace tsohon makawo" a zuciye ya bud'e baki zaiyi magana, sai ga Bilal ya kwad'a sallama ya shigo falon, Basma saida gabanta ya tad'i, amma saita dake tace cikin Fara'a
"Friend hala nayi mantuwa ko?" murmushi yayi yace
"kin manta da ice cream d'inki kina sauri"
"ayya wlh ban kula ba, nagode kuwa sosai"

Shureym ai sakin bakin yayi yana kallon ikwan Allah, cikin harshen turanci Bilal yace masa
"ina yini big brother" Shureym ya amsa a tak'aice, sai ya fice da sauri.

Yaya Shureym zama yayi akan kushim yana cizon leb'ensa, gaba d'aya kishi ya rufe masa ido. Har wani d'aci bakinsa yake masa saboda b'acin rai, Basma tana ganin ya zauna bai ce mata komai ba, sai kawai ta shige d'aki.

Shureym ya d'aga wayarsa ya kira Dadyn Kaduna, Gobna Ibrahim, suka gaisa Dady yace
"Shureym ya Basma da fatan kuna lafiya?" cikin k'unan rai yace
"Dady Basma tana cin Amanta, fita take yi tana hurd'a da wasu maza a waje, yau tun rana ta fita sai yanzu ta dawo, kuma Dady wani saurayinta ne ya kawota gida, yanzu yabar falon mu" a razane Dady ya mik'e yana fad'in

"Inalillahi wa inna ilai hir raji'un, Basman ce ta zama haka, to maza ku shirya gobe-goben nan ku tawo Nigeria, zan kira family meeting gaba d'aya zamu had'u a Abuja duka, kayi hak'uri kaji Shureym karka ce mata komai" sai suka yi sallama.

Dady ya fara kai koma a falo sai salati yake,  Ummin Meena dake zaune itama ta mik'e a tsorace tana tambayarsa
"Alhaji lafiya?" kallonta yayi bai ce komai ba, ya shiga niman number Mai Martarba Sarkin Kano, suka gaisa, sai ya shaida masa akwai family meeting a Abuja gobe in Allah ya kaimu, nan suka yi sallama. ya d'aga waya ya kira President, shima haka ya shaida masa kamar yanda suka yi da Mai Martaba, President cikin mamaki yace
"Ibrahim lafiya dai ko?" cikin murmushi yak'e yace
"Lafiya Kalau sai in munzo zaka ji komai insha Allah" da haka suka yi sallama.

Dady ya koma ya zauna, itama Ummi ta zauna, ya shiga gaya mata Abinda Shureym yace masa, cikin salati Ummi tace

"wlh k'arya yake yi, ba dai Basman mu ba, sai dai in sharri zai mata, dan ba haka muka tarbiyyantar da ita ba"

Cikin b'acin rai Dady yace
"karki shaideta domin d'an yau ba a iya masa, kuma ai ba tare dasu muke zama ba, hasali ma ba gari d'aya muke ba, Basma zata iya komai tunda dama bason Shureym take ba" sai jikin Ummi yayi sanyi ta shiga nazarin maganar Dady...

*Rahma Ce*
[8/9, 5:47 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *20.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Safeena cike da damuwa tace
"amma Shureym anya baka jawo tonuwar asirinmu ba, domin in dai Basma taji cewa ka kai karanta ne, tofa zata gaya duk abinda ya faruwa, da kuma dukanta da kake yi"

Runtse idonsa yayi ya bud'e, cike da damuwa yace
"wlh Safeena raina ne ya b'aci, idona ya rufe sam ban kawo haka ba, sai yanzu da kika tunatar da ni, yanzu ya kike ganin za'ayi" cikin damuwa ta rafka tagumi tace
"ina ganin karka gaya mata, kace kawai ana nimanku ne, inya so inta je can taji komai, kuma na fison dama kowa yasan dani a family d'inku dan nagaji da b'oye-b'oye" cike da damuwa Shureym yace
"haba safeena bai kamata ace abinnan ya fasu yanzu ba, kawai ki tayani da Addu'a kar asirinmu ya tonu" yana gama fad'an haka sai ya mik'e ya shige d'aki, Safeena ta bi bayansa da kallo, ta yatsine baki tace
"ba Addu'an da zanyi, in maganar ta fito karshe dai ace an raba aurenka da Basma, kuma abinda nake so kenan".

Shureym yana shiga d'aki ya kira Maminsa ya sanar mata duk abinda ke faruwa, hankalinta ya tsahi ta shiga yi masa fad'a, tace
"yanzu kazo kaja asirina zai tonu, a gaskiya ba yanzu naso ace maganar nan ya fito ba, domin hakan zai iyi barazana ga aure na, kuma kaima za ka fuskanci fushin Mahaifinka, gaskiya zan San abinyi" tana gama fad'a ta kashe wayar.

Kai komo ta shiga yi a d'akinta tana tunanin hanyar da zata bullowa lamarin, zama tayi tayi dogon nazari, murmushi naga tayi sai ta ce
"Allah ya kaimu goben, na samo mafita".

Da dare Shureym ya kira Basma a waya, yasan in yaje d'akinta ba zata bud'e ba, yace
"ki shirya gobe in Allah ya kaimu zamu tafi Nigeria, Dady ya kirani yace muje akwai Family miteeng, dan haka ki shirya da wuri da sassafe mamu tafi" cike da murna tace
"Allah ya kaimu" saita kashe wayar.

Mikewa tayi, tayi rawa da tsalle, tana murnan zata ga family d'inta, kaya ta shiga had'awa kamar wacce zata bar garin duka ba dawowa. Zan iyace cewa barci b'arawo shine ya saceta, amma sam ta kasa sukuni, kosawa tayi gari ya waye.

*Washe gari*
Yau Basma harda yiwa Safeena sallama sai fara'a take mata, Safeena tace
"hoo su Basma za'a tafi min da miji sai dariya kike, to Allah yasa in kin tafi karki dawo" harara Yaya Shureym ya galla mata, saita gimtse sauran maganarta tana dariya k'asa-k'asa, Basma kuwa cike da dariya tace
"Ameen ya rabb, nima bana fata na dawo, kuma mijinki gaki ga shi, babu abinda zan miki dashi, ni dai na barki lafiya" saita fice tare da jan trolley kayanta.

Safeena ta bisu har mota tare da musu Addu'a, haka suka wuce airport, Shureym yana cike da damuwa, Basma kuma cike take da murmushi.

*Nigeria*

Gidan President ya cika da dangi, sunzo sunata zumunci, da yake ya kama yau rana ce ta Juma'a, mazan gidan duka suka taru suka tafi babban masallacin Juma'a na Abuja.

Bayan sun dawo gida, iyayen maza da mata suka had'u a babban falon bak'i na shugaban k'asa, anan aka shirya musu abinci a tsakiyar falon kan babban dadduma daya mamaye falon, yara kuma suka baje nasu liyafar a part d'in Ammi, can suke hidimarsu.

Bayan sun gama cin abinci suka shiga hiran zumunci, Abba (President) ya kalli Dady (Gobno Ibrahim) yace
"Ibrahim yanzu gamu duk mun had'u gaba d'ayanmu, ina so ka sanar mana musabbabin had'uwarmu anan daka buk'aci muyi"

Dady ya nisa ya d'ago ya kalli Abba yace
"naso ace Shureym da Basma sun zo tukunna sai kuji bayani a bakinsu, dan dama mun had'u anan ne domin su, na tabbatar suna gab da shigowa" Mai martaba yace
"A'a Ibrahim ka fara sanar mana da komai kafin zuwansu" Mami (Hajiya sa'a) tace
"kwarai kuwa, ya kamata mu ji komai, domin ni hankali na ya ya shi" Hajiya Fatima (Ammi) tace
"gwara ka fad'a kawai domin mu fara tattaunawa akai" ita dai Momyn Basma bata iya furta komai ba saboda nuna kawaici, Hajiya Murja Mahaifiyar Leema ita ma bata furta komai ba, Ummin Meena kuwa shuru tayi cike da damuwa a fuskanta.

Dady yayi gyaran murya ya gaya musu duk abinda Shureym ya fad'a masa jiya, ai duka falon sai suka d'auki salati, Momy kuwa wani irin fad'uwa gabanta yayi, idonta ne ya kawo kwalla zuciyarta na mata suya, Abba sun kuyar da kai yayi ya kasa yin magana, duk falon ya d'auki shuru sai k'aran fanka da kukan AC ke tashi, Mami ce tace

"hmmm nasan za'a rina saboda Shureym ya sanar min cewa tsawan watannin bikinsu da suka yi, Basma tak'i bashi had'in kai suyi rayuwar aure, akwai ranar da har fad'a suka yi nice na sasanta lamarin, har nayi masa fad'a, akan cewa yarinya ce ya bita a hankali, Shureym tunda yaji su Meena duk suna d'auke da ciki abin ya dameshi, nice nake lallashinsa"

Mai Martaba ya katseta da cewa
"meyasa kinsan da wannan matsalan yanzu tsawon wata 7 da aurensu, sai yanzu za ki fad'a da kika ji matsala ta kunno kai?"

"Mai martaba gani nayi Basma ba son aure tayi ba tun farko, shiyasa nace bari mu lalkab'ata harta hak'ura ta yarda da shi".

Ba wanda ya tanka mata sai duk suka yi shuru.

Sallaman shigiwar su Basma falon, shine ya k'atse shurun domin kusan yaran nasu duka shun shigo falon suna murnan ganinsu Basma, Yaya Ahmad na rik'e da hannun Basma sai suka samu guri suka zauna a gefe, duk yaran suka zauna, Yaya Naufal, Yaya Shureym, Yaya Adam, Yaya Jamal, Anty Husnah, Meena, Leema, Deeja, twins din Momy k'annan Basma.

Falo yayi Albarka, kowa ya zauna duk suka gaishe da iyayensu, sai dai fuskokinsu babu walwala, Basma ta tashi ta isa gaban Abba ta zauna tare da sanya kanta akan cinyansa, cike da b'acin rai ya tureta tare da cewa
"tashi ki bani wuri" da sauri ta d'ago ta kalleshi, cikin shagwab'a tace
"Abba me nayi kake fushi dani" shuru yayi mata, sai duk jikinta yayi sanyi, takai kallonta ga Momy, saita kauda kai a ranta tana tausayawa d'iyarta, duk tabi fuskokin iyayan nasu babu wanda yayi mata dariya ko murmushi, duk ransu na b'ace, cikin tashin hankali tace
"Wai me yake faruwa ne?"

Dady ne yace
"Ku su Meena Ku tashi Ku fita Ku bamu wuri, Anwar da Na'im kuma kuje d'akinku kiyi karatu, ku kuma mazan ku zauna ayi maganar daku" jikinsu duk a sanyaye su Leema suka fita, Basma ta mik'e zata bi bayanzu Dady ya daka mata tsawa yace
"zauna karki sake ki fita, dama zaman danke a kayi shi" kuka ta fara yi ta koma kusa da Yaya Ahmad ta zauna, hannunta ya kama ya shiga lallashinta.

Falon yayi shuru na tsawon minti biyar, Dady ya kalli Shureym yace
"Shureym ina so ka sanar mana da abinda ka gayamin jiya a waya"

"Shureym cike da fargaba da damuwa ya shiga zayyana magana k'arya da gaskiya, bayan ya gama gaya musu abinda ya gayawa Dady sai ya d'ora da cewa
"Basma bata jin maganata, ban isa in sata ba ko in hanata ba, zagi iri-iri na cin mutunci babu wanda bata yi min, zata fita da banzan shiga na fidda tsiraici, ban isa inyi magana ba" ai bai k'arasa ba Basma tayi magana cikin d'aga murya da tashin hankali tace
"karya kake Yaya Shureym, wlh sharri kake min" takalli iyayenta ta cigaba da cewa
"wlh Aba sharri yake min, Ammi yanzu ku kun yarda da bayaninsa, Mai martaba wlh Yaya Shureym sharri yake min, karku yarda da maganar shi" ta rarrafa ta isa gaban Mominta tace
"Momy in kowa bai yarda dani ba nasan ke zaki yarda dani" Momy sun kuyar da kai tayi k'asa hawaye mai zafi ya sauka a kuncinta, Abba ne ya mik'e da sauri ya wanke Basma da mari guda biyu, tare da hamb'arinta da k'afansa yace

"tir da halinki Basma, acikin zuri'ata kin fita zakka sam baki halinmu ba, kuma in kika kuma yin magana anan wlh jikinki zai gaya miki, mituniyar banza kawai"

Dady ne ya mik'e ya kama Abba yace
"haba Yallab'ai, bai kamata ka duketa ba" komawa duk suka yi suka zauna. Momy cikin fushi tace

"Tunda nake ban tab'a sanya baki a cikin lamarin Basma ba saboda ina nuna kawaici, amma yau zanyi magana, a irin tarbiyyan dana bawa 'yata bana tunanin zata aikata abinda Shureym ya gaya, in kuma ku kun yarda toni wlh Ni bazan tab'a yarda da magan ganunsa ba, dan haka Basma 'yata ce, nice nayi nak'udarta babu wanda zai d'aura mata k'azafin zina in d'auka"

Saita mik'e taje ta kama hannun Basma suka yi hanyar fita daga Falon, yaya Ahmad shima mik'ewa yayi cikin b'acin rai ya kalli Shureym yace

"D'an iska banza baka isa ka yiwa 'yar Uwata sharri ba, domin nafi kowa sanin mugun halinka, dama mazinaci kamar ka ai dole kaga kowa ma haka yake, Basma nasan abinda zata aika nasan wanda ba zata yi ba, mak'arya cin banza dana hofi" shima sai ya bi bayan su Momy. suna gabda zasu fita Abba ya bud'e murya yace

"Maryam wlh muddun kika sanya k'afa kika fita a falon nan to a bakin aurenki, Kai kuma Ahmad wlh in ka fita saina sassab'a maka mutumin b'anza kawai, har zaka zo ka goyi bayan shaid'ayar yarinya nan, tun farko dama ta nuna bata Son shi, dan haka kome aka ce tayi to zata iya aika shi"

A gigice Momy ta tsaya ta juyo tana mamakin furucin Abba, mai martaba yace
"Subhanallah Yallab'ai wani irin furuci ne haka?" Ammi da Ummi da sauri suka mik'e suka isa wurinta, Momy tana kukan bak'in ciki amma sam bata karaya ba dan tana bayan Basma, gabanta su Ammi suka sha, tare da rik'o mata hannu suka jata har zuwa mazauninta, Yaya Ahmad ya kama Basma ya had'ata da jikinsa yana lallashinta, haka suka isa cikin falon suka zauna.

Mai Martaba yayi gyaran murya yace
"Dan Allah kuyi hak'uri kar b'acin rai yasa a yanke hukunci cikin fushi, ba tare da bincike ba, ke Basma gaya mana gaskiyar abinda ke faruwa" kuka ne yaci k'arfin Basma tace

"Wlh ban tab'a zina ba ban tab'a ba, kune iyayena ku zaku shaideni akan haka, wlh ban tab'a ai'kata abinda yace muku ba ko d'aya daga ciki" kuka ne yaci k'arfinta saita d'aura kanta a cinyar Yaya Ahmad, jikinta ne ya soma kad'uwar jin sanyi nan take zazzab'i ya rufeta...

*Rahma Ce*

[8/9, 5:47 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *21.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Shuru suka yi suna sauraren kukan Basma, tausayinta ne ya kamasu, Ammi ce tace
"to shikenan, ni ina ganin gaba d'aya wannan abun rashin fahimta ne, dan haka sai a sulhunta su komai ya wuce, sai su tafi, Dady yace
"kwarai kuwa abinda ya kamata ayi kenan"

Mai Martaba ya shiga yi musu nasiha mai ratsa zuciya, daga bisani ya d'aura da cewa
"President banji dad'in yanda ka d'auki wannan lamari da zafi ba, da har ka furta mummunan kalma ga Hajiya Maryam, in hankali ya gushe ai hankali ne ke nemoshi, dan Allah mu rik'a kai zuciya nesa, duk sai mu taru muyi hak'uri komai ya wuce, kai kuma Shureym kaji tsoron Allah, in har kana cutar da ita Allah ba zai barka ba"

Abba yayi wa mai Martaba godiya, ya soma yiwa su Basma nasiha, bayan ya gama yace
"Basma kije part d'ina ki jirani, kai kuma Shureym ka shirya zuwa gobe in Allah ya kaimu da safe zaku koma, shikenan zaku iya tafiya"

Haka suka watse kowa da damuwa a ransa, Amma banda Shureym da Maminsa wanda zuciyarsu yayi haske tunda an kashe magana ba tare da Basma ta tona komai ba, duka Matan suka wuce part d'in Momy, anan suka bar Mazan suna tattaunawa.

Yaya Ahmad yabi bayan Basma suka zauna a falon Abba, ya kalleta cikin nutsuwa yaga duk ta rame haske kawai ta k'ara, yace
"Basma me Shureym yake miki, ki gaya min gaskiya fa, dan bana son k'arya" guntun Murmushi tayi tace cikin sanyin murya
"Yaya Ahmad babu komai, kawai dai kasan halinsa na saurin fushi, anan ne muke dan samu sab'ani, amma bayan haka ba komai" kallonta yake cike da zargin abubuwa kala-kala domin sam bai gamsu da amsar da ta bashi ba, sai yace
"shikenan tunda ba zaki fad'a ba, in ya kusa kashe ki saiki fad'a" murmushi tayi tace
"Ni ba zai ma kashe ni ba" mik'ewa yayi yace
"bari na kawo miki abinci da maganin zazzab'i kisha, dan d'azu naga har kad'uwan sanyi kike yi" murmushi tayi race
"wlh Yaya tsabar shiga shock ne ya sani zazzab'i, amma ka kawo min zansha ko kaina zai rage min ciwo" harya fara tafiya sai tace
"Yaya d'an tsaya in baka ajiya" zage Jakarta tayi ta ciro wani k'arakin key guda d'aya, sai ta mik'e ta isa wurinsa tace
"Yaya dan Allah ka ajemin wannan key d'in inna tashi amsa zan maka magana sai ka bani" d'aga key d'in yayi yace key d'in miye ne wannan?" murmushi tayi tace na sirrina ne, ni dai ka ajemin wataran zan maka bayani akansa" gyad'a kai kawai yayi sai ya fita, tare da juya key d'in a hannunsa, yana tunanin ko na miye.

Abba ya samu Basma a sashinsa, zama yayi ya kirata, sai tazo ta zauna gefensa a k'asa, kanta ya d'ora bisa cinyansa, sai ya shiga yi mata fad'a daga k'arshe yayi mata nasiha, kuka Basma take yi mara sauti, a haka Yaya Ahmad ya samesu shima ya zauna ya zubawa Basma abincin ya mik'a mata yace taci, Abba ne ya kalle shi fuska a d'aure ya shiga yi masa fad'a akan abinda ya aikata d'azun, hak'uri Yaya Ahmad ya bashi da alkhawarin hakan ba zai sake faruwa ba, nan suka zauna suka cigaba da hira, har Basma ta kammala cin abincin kana ta mik'e zata fita da kulolin abincin, dakatar da ita Abba yayi yace
"Basma barshi Ahmad ya tafi dasu, ki hau sama kiyi wanka jakar kayanki yana d'akin kusa da nawa, anan zaki kwana" rau-rau tayi da idonta tace
"Abba ina son inga su Meena da su Ammi ne fa" murmushi yayi yace
"anjima in zamuci abincin dare zaki gansu, dan haka kiyi abinda na saki" hawaye ne ya ciko idonta, kawai saita haura sama zuwa d'aki, ta shiga rusa kuka sai da

Please Login or Register in order to submit comment