Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakinsa dai-dai da fuskansa, Namiji ne mai cike da kwarjini ga faffad'an k'irji, suman kansa luf-luf yake tamkar d'an India, in ya d'auki lokaci baiyi aski ba gashinta yana taruwa wanda zai iya kamawa da ribom, gashi da santsi sosai. Hakane kesa kullun Kansa da Hula baya son sumansa na fitowa, ba kowa yasan sumarsa haka yake ba saboda baya fita ba hula, sai dai in yaje masallaci wurin yin Alwala sai mutane su gani.

'yan Matan unguwansu Aryan sun rud'e sosai akansa, suna haukan sonsa, shi kuma bai san ma suna yi ba. Shekarunsa Talatin (30yrs) a duniya har yanzu baida budurwa, baima kallon mata balle ma su birgeshi, shiyasa ranar da sukayi ido hud'u da Basma gabansa ya fad'i domin shi Sam baya kallon mata, amma fuskan Basma ya kasa b'ace masa a ido saboda wulak'ancin da tayi masa. A yanzu kullun burinsa bai wuce ya samu kud'i ya farantawa Ummansa rai da k'anwarsa abin sonsa.

*Cigaban Labari...*

Malam lawal ne ya kwad'a ma Aryan sallama, firgigit ya farka daga dogon tunanin da ya shiga, cikin sark'ewan murya yace
"Naam Malam Lawal ashe harka iso" cikin dariya Malam Lawal yace
"tun d'azu nazo, nayi maka magana naga gaba d'aya hankalinka ya yi nisa ince dai lafiya?" murmushi yayi yace
"lafiya lau Malam Lawal, ya kwanan iyalin?"
"Lafiya lau, d'azun nan naga Deeja zata aiken Ummanku, sai na tambayeta ko ka wuce? sai tace aika fita da wuri"
"eh wallahi na fito da wuri, da yake na biya wajen saro kayan miya"
"Ok, Allah ya bamu sa'a da kasuwa mai Albarka"
"Ameen Malam Lawal". Nan suka cigaba da tattaunawa akan maganar kasuwan.

B'angaren su Queen Basma sai goma na safe suka farka, ko wacce ta fito cikin shigan mu ta Hausawa, Leema ta sanya leshi riga da zani rafa, Meena ta sanya shadda doguwar Riga, Basma kuma ta sanya atamfa super, d'inkin Riga da siket, ba k'aramin kyau sukayi ba, ko wacce da gyale a kanta, hakan da suka yi sai suka bani mamaki, gaba d'aya kamar ba sune jiya suka yi shigan dogayen riga sai kace ba 'ya'yan Musulmai ba, suka tafi zuwa club.

Queen ce tace
"Ni zan tafi gida domin a yanzu haka ana jirana domin yin breakfast, in kuma za kuje tom sai mu tafi tare" Leema ta yatsine fuska tace
"Ni bazani ba saboda Momynki akwai takura gwara-gwara Ammi, dan haka hotel d'in da muka sauka ni da Meena zan wuce" Meena tace
"kai Leema kiyi hak'uri muje kawai kinga fa sunsan muna garin nan bai kamata muje wani guri ba tunda duk Family ne mu ba bare ba" Queen ta yi hanyar fita tace
"ban takurawa kowa ba, in kun so ku fito mu tafi in kuma kun k'i ko wacce ta kama hanyar inda zata, yau dai ba mai kwana min a wannan gidan, nima gidan Ubana zani na kwana" tana gama fad'an haka tasa kai ta fice, tsaki Meena tayi tace
"In kina tak'ama da mulki muma fa gidanta muka fito, kinga Leema mu wuce gidan President d'in inya so in munyi two days sai ki koma Kano ni kuma na wuce Kaduna, domin wallahi ina missing Family na" Murmushi Leema tayi tace
"hmmm wallahi nima hankalina ya koma gida fa, yanzu fa iyayenmu sun d'auka yau ne zamu dawo daga Dubai da muka tafi, bacin yau satinmu d'aya da dawowa, muna biyewa Queen bayan ita iyayenta sun ga dawowarta a ranar, muko munyi k'arya sai yawo muke bamu nan bamu can" Dariya Meena ta kwashe dashi tace
"kefa saboda Jalal kika tsaya anan" hararan wasa Leema tayi mata tace
"Ke kuma saboda mashayarku kika tsaya, saboda kinsan in kika koma gida Yaya Jamal zai takura miki ba shiga ba fita" duka Meena ta kaiwa Leema saita goce ta fice da sauri tana dariya. Haka su dukansu suka d'unguma zuwa babban gidan Shugaban k'asa.

*WACECE QUEEN BASMA?...*

_*Rahma Ce*_
[8/3, 12:59 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *3.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*WACECE QUEEN BASMA?*

'Yace a wurin Alhaji Mukhtar Bukar Bulama, wanda yake shugabancin k'asarmu Nigeria a yanzu. Asalin Mahaifinsa d'an Maiduguri ne Kanuri, mahaifiyarsa kuma mai suna Asma'u 'yar Gombe ce Fulani, Alhaji Bukar Bulama babban d'an kasuwa ne, yana fita k'asashen waje sosai, ya jima baiyi aure ba saboda yanayin kasuwancinsa, Mahaifin Asma'u Alhaji Salis, abokinsa ne k'ud da k'ud wanda a sanadin kasuwanci abotansu ya had'u, ganin Ahaji Bukar Bulam baiyi aure ba yasa Alhaji Salis ya bama Alhaji Bukar auren 'yar tilo d'aya Asma'u.

Suna zama a cikin garin Kaduna a Unguwar Rimi, Alhaji Bukar an sanshi sosai, Mutum ne mai tausayi da taimakon talakawa, yaransa biyu a duniya Mukhtar da Halimatus Sadiya, sun taso cikin gata da kulawa kuma Asma'u tayi k'ok'ari sosai wajen basu tarbiyya mai kyau.

Mukhtar yana gama primary mahaifinsa ya turashi karatu k'asar Germany a can ya fara secondary school d'insa. Tafiya ya kama su Alhaji Bukar zuwa Gombe sanafin rasuwan  mahaifiyar Asma'u, bayan sunje basu dawo ba har akayi Addu'an bakwai kana suka kamo hanyar Kaduna, basu fita daga Gombe ba akan hanyarsu suka bige wani yaro, cike da tashin hankali suka nufi Asibiti dashi, aka karb'esu emergency, an samu yaron ya farfad'o, amma baya iya magana sai zaro idonsa yake waje, Likita ya basu tabbacin yaron ya samu Matsala a kwakwalwansa, hankalin Alhaji Bukar yayi masifar tashi, sunyi iya bincike ganin an gano iyayan yaron amma shuru ba a gano ba, da haka ya d'auki yaron ya wuce dashi Kaduna da nufin in ya samawa yaron lafiya ya maidashi wurin Iyayensa.

Alhaji Bukar suna dawowa da kwana biyu ya shirya zuwa kasar Germany da iyalensa domin duba lafiyan Yaron daya bige, wanda baya iya magana. Da isarsu da kwana biyu cikin ikon Allah Yaron ya soma magana, sunan shi kad'ai ya iya tunawa Ibrahim, amma banda haka bai tuna komai ba, Likitoci suka tabbatar musu da Yaron ya samu mancewar kwakwalwa (loosing Memory). Abin ya damu Hajiya Asma'u sosai hakan yasa Alhaji Bukar ya bar Ibrahim a wajen Mukhtar ya fara karatu shima, sai suka tarkato suka dawo Nigeria.

*Bayan shekaru mai tsawo*

Su Muktar sun dawo Nigeria wanda dukkansu sun gama karatunsu sun samu aiki, har zuwa lokacin Ibrahim bai dawo cikin kwakwalwansa ba. Sadiya kuma tana karatu a KASU, tun dawowar su Mukhtar Allah ya daurawa Sadiya son Ibrahim, Abu kamar wasa har mahaifiyarsu ta ganeta saita kwab'eta, abinda basu Sani ba shima ta wurin Ibrahim d'in ya kamu da son Sadiya, daga bisani ya bayyana mata zuciyanshi suka fara soyayya.

An sanya bikin su Ibrahim da Sadiya ba b'ata lokaci, wanda Alhaji Bukar yace ta cigaba da karatunta a d'akin mijinta, Mukhtar shima yana soyayya da k'anwar Sarkin kano mai suna Fatima, soyayya tayi k'arfi wanda hakan yasa aka had'a bikin su duka a kayi. Anyi biki sosai na manyan Attajirai, ko wacce ta tare a sabon gidanta da Alhaji Bukar ya siya musu a unguwar sunusi.

Wata rana Alhaji Bukar ya shirya tafiya k'asar Dubai shida Mahaifin Asma'u, domin kula da kasuwancinsu dake can, a hanyar dawowarsu jirginsu yayi hatsari suka rasu. tashin hankali ba'a sanya masa rana, wannan Family sun shiga cikin damuwa da k'unci na rashin jigonsu, Hajiya Asma'u ta zama ba Uwa ba Uba ba Miji sai sauran danginta da yaranta. Hakan ya girgizata wanda haka yasa ta samu ciwon hawan jini. Su kuma su Mukhtar sun rasa Bango abin jingina watarsu. Ibrahim yayi kuka matuk'a domin da bazar Alhaji Bukar yake taka rawa, har yau baisan shi waye ba ko danginsa, yasan dai su Hajiya Asma'u basune iyayensa ba, ya kasa tuna komai na danginsa.

Bayan Addu'an Arba'in duk dangi suka watse, an rab'e musu gadonsu, Muktar ya had'a duka dana k'anwarsa Sadiya dana Ummansu ya cigaba da kasuwanci dasu sannan yana aikinsa. Shi kuma Ibrahim sun bashi wani kaso mai tsoka daga dukiyar nasu kamar yanda mahaifinsu ya rubuta a cikin dairy d'insa, Ibrahim ya amsa yana godiya harda kukansa, daga nan shima ya cigaba da business.

Hajiya Fatima matar Muktar ta haifi d'a Namiji mai suna Ahmad, bayan shekara guda ta kuma samun ciki, bata so ba amma dole ta hak'ura saboda Alhaji Mukhtar yana son abinsa, haka ya d'auki Ahamd ya bama Ummansu ta cigaba da rik'onsa.

Bayan wata tara ta kuma haifo d'anta Namiji mai suna Abubakar suna kiransa da Naufal. Sati biyu da haihuwarta Allah ya azurta Alhaji Ibrahim samun k'aruwa da d'a Namiji wanda suke sanya masa suna Jamal. Sun raini 'ya'yansu cikin Kauna da soyayya, sun basu tarbiya sosai domin kud'insu bai hanasu tsayawa bisa tarbiyyan yaransu ba.

*Bayan shekara biyu*
Hajiya Fatima ta kuma haifo 'ya mace suka sanya mata Asma'u suna kiranta da Husnah. Ta b'angaren Hajiya Sadiya ita bata k'ara haihuwa ba tana rik'e da d'anta Jamal.

Alhaji Mukhtar ya rik'e mukamin Commissioner har kujera uku, soyayyar da ya samu wurin Mutane yasa ya fito takaran gomna, cikin ikwan Allah ya samu. Ta b'angaren Ibrahim shima yana ta samun mukamai a wurin aikinsa dukiyarsu sai hab'aka take ta ko ina.

Alhaji Mukhtar ya k'ara aure da 'yar wani hamshak'in mai kud'i a garin Kano 'yar Alhaji Buba mai Naira itace 'yarsa tilo guda d'aya mai suna Maryam, anyi Biki sosai na manyan Mutane, Alhaji Mukhtar ya tare da ita a gidansa na Gomnati, gida d'aya ya had'asu da Hajiya Fatima, suna zaune zaman lafiya ba tashin hankali.

*Bayan shekara Hudu* yana kujeran Gomna, Hajiya Maryam ta Haifi 'yarta mace k'atuwa ga kyau, suka sanya mata suna Basma, Basma ta taso cikin gata da soyayyan iyayenta, Yaya Ahmad yana sonta sosai tun tana k'arama suka shak'u sosai, bata shiri da Yaya Naufal, Anty Husnah kuwa duk inda zata suna tare, tun tana k'arama ta koma hannun Hajiya Fatima, Nono kawai ke kaita gun Momynta.

Itama Hajiya Sadiya ta k'ara haihuwar 'ya mace aka sanya mata Ameena suna kiranta da Meena, tserayen wata biyu ne tsakanin haihuwar Basma da Meena.

Yaya Ahmad da Yaya Naufal kusan tare suka wuce k'asar Malesia karatu, Yaya Ahmad yana karanta Medicine Yaya Naufal yana karana Biochemistry. A lokacin Anty Husnah tana secondary school.

Basma kuma tana primary. Hajiya Fatima wanda suke kira da Ammi ta gama sangartata duk wani rashin ji ta sani, ga tsokanar fad'a a makaranta, duk wani kiriniya tare suke yi da Meena da yake makarantar su d'aya. A daffafe suka kare primary saboda irin kai k'aransu da iyayen yara keyi, kasantuwar iyayensu manya ne shiyasa ba'a koresu ba.

Hajiya Maryam ta k'ara haihuwar yara Maza 'yan biyu Anwar da Na'im, anyi shagali sosai da haihuwarsu, su Basma kuwa murna har kunne. So tari Hajiyar Maryam wanda suke kira da Momy bata ragawa Basma tayita mata fad'a hakan yasa Basma bata son kwana a b'angarenta sai wurin Ammi saboda Ammi na kula da ita bata son b'acin ranta.

An d'aurawa Anty Husnah aure da Jabir d'an senator, sun had'u a makarantar Abu Zaria inda ta fara karatu, an d'aura auren tana cigaba da zuwa makaranta. A wannan shagalin bikin ne akayi taron da ba'a tab'a yiba, mutanan Gombe, Maiduguri, kano duk sun hallara, matar Sarkin Kano yayan Ammi, Hajiya Murja tazo bikin wanda ta taho da 'yarta mace sa'ar su Husnah mai suna Haleema suna ce mata Leema, tun daga nan su Basma aka samu kawa, da zasu tafi Leema ta kafe saita zauna  wurin Ammi, haka mahaifiyarta ta barta mai martaba Sarki Abdallah ya amince Leema ta zauna wurin Ammi domin yasan gidan Gomna Muktar Bukar Bulama akwai tarbiyya.

Abdullahi shine ya gaji sarautar gidansu bayan rasuwan Babansu, Yayane ga Hajiya Fatima, uwa d'aya uba d'aya suke, yana da mata biyu Hajiya Sa'a itace Uwar gida tana da yara biyu duk Maza Adam shine babba sai Shureym shine k'arami, sai Amaryansa Murja yarta guda d'aya ce itace Leema, sun d'aura son duniya sun azawa Leema kowa na dangi yana sonta, tun tana k'arama ta taso cikin sarauta, gimbiya Leema 'ya ga Sarki Abdallah.

Hajiya Sa'a Mace ce yar k'arya da son duniya ta shigewa Hajiya Maryam Momyn Basma, amma Momy tak'i sake mata saboda halayyarsu bai zo d'aya ba, Hajiya Sa'a basa shiri Sam da Ammi wato k'anuwar mijinta, hakan yasa Momy tak'i sake jiki da ita.

Hajiya Sa'a ta sangarta Shureym da gata, ta d'aura son duniya ta bashi saboda tana ganin shine zai gaji kujaran Babansu, shiyasa tun yana k'arami take kiranshi da Prince Shureym, hakan yana masa dad'i sosai. Adam shi kuma Mutum ne salihi ba yida hayaniya hakan yasa nasu yazo d'aya da Hajiya Murja, a wurinta yake komai. Shureym yana America yana karatun Engineering, shiko Adam Madina ya tafi karatunsa bangaren Islamic studies.

Basma, Meena, Leema duk makarantar d'aya suke secondary, a part d'in Ammi suka tare domin Ammi ita bata kwab'a musu, Meena ta kwaso kayanta ta dawo gidansu Basma gaba d'aya.

Alhaji Ibrahim Baban Meena ya samu cigaba sosai, wanda yaita samun K'arin girma a wurin aikinsa, ya tura Yaya Jamal karatu inda su Yaya Ahmad suke k'asar Malesia yana karanta Business admin.

Gomna Muktar Bukar Bulama ya sauka a kan kujeran Gomna bayan shekara takwas daya shafe akai, ya k'ara samun kurajeran Sanator wanda ya wuce Abuja, sai weekend yake dawowa gida Kaduna. Dukiyarsu na gado sai hab'aka yake yi.

Su Yaya Ahmad sun gama karatunsu gaba d'aya duk sun dawo, Yaya Ahmad ya fara aiki a babban Asibiti dake garin Abuja, Yaya Naufal kuma ya karb'i kasuwancin Abbansu ya cigaba da juyawa. Yaya Jamal ma dukiyar Dadynsa ya cigaba da rik'ewa.

Ta b'angaren Mutanan Kano kuwa Yarima Adam ya dawo ya fara lecturing a BUK, shi kuma Shureym bai riga ya kammala masters d'inshi ba.

Su Basma an zama 'yan Mata sun gama Secondary School yanzu suna England suna karatu. Basma na karanta Micro Biological, Leema tana karanta Pharmacy, Meena kuma tana karanta Low.

Tunda suka koma England rayuwarsu ta k'ara sauyawa, sun had'u da 'ya'yan turawa da kuma 'yan k'asashe daban-daban, Basma tunda ta soma karatu saita natsu ta zama mara son magana, amma fa akwai tsiwa in aka tab'ota, Meena kuma akwai shegen surutu, Leema kuma akwai ji dakai da kuma k'asaita na Sarauta.

Sunyi farin jini sosai saboda suna da k'ok'ari sosai. Meena ta had'u da wata yar ajinsu ta koya mata zuwa club, abu kamar wasa Meena in bata je club ba bata jin dad'i, tun su Leema na mata k'orafin ta daina zuwa har taja ra'ayin Leema ta fara zuwa.

Abu na farko da suka koya shine Meena ta shiga group d'in 'yan shaye-shaye, tun bata iya ba harta kware sosai wajen zukar sigari da shan kwayoyi.

Leema kuma Mace ce mai yawan sha'awa, in Meena ta jata cikin group d'insu saita kasa sakewa a haka harta had'u da Jalal suka fara soyayya tun bata sakewa harta sake dashi, Jalal ya fara fita da ita yawo kullun sai sun fita. A hankali yayi ta jan ra'ayinta gareshi, tun tanak'in amince masa harta bashi kai bori ya hau. Tun daga nan suka d'inke da Jalal, ya mai da ta tamkar Matarsa shine mutum na farko da yasa fara sanin ta a 'ya mace. A hankali Leema ta raba shi da duk 'yan matanshi, Basma kullun cikin musu nasiha take akan sun gurb'ata tarbiyyan da iyayensu suka yi musu dasu gyara halinsu.

Meena tayi murmushi tace
"ke bazaki gane ba, meye amfanin zuwanmu k'asar waje bamu waye ba, ai wannan itace wayewar, kinga ni shaye-shaye kawai nakeyi ita kuwa Leema da Jalal take harka, kinga ta samu abinda zuciyarta take so".

Basma tayi tsaki tace
"Allah ya kyauta" Murmushi Leema tayi tace
"ki shirya yau muje club dake Allah za kiji dad'in wurin sosai" Basma tace
"Kun dameni da zancen club d'in nan, yau dai zani inga abinda akeyi a gun shikenan kunyi farin ciki ko?" cikin farin ciki suka ce
"wow munyi Murna kema zaki shigo sabon rayuwa ki huta da rayuwan duhun kai"

Sunje club gaba d'ayansu, yanda Basma taga wurin sai ya sanyata farin ciki musamman data ga 'yan rawa sai hakan ya kwanta mata arai, dan a duniya Basma tana son rawa, kawai sai ta mik'e ta nufi wurin rawan ta hau, cike da mamakin mutane suka bita da kallo, ji tayi k'afarta ya k'asa d'aukarta, dan gani tayi ido ya mata yawa bazata iya ba, su Meena ne suka fara kiranta
"common Besty ki fara" nan kowa ya fara ihu suna mata kirari dan ta fara, nan kanta yayi chargy taji wani k'arfi da dakewa saita fara rawa cikin salo naban namaki, sai wurin ya kaure da ihu, dan tayi matuk'ar burgesu, ba wanda yayi tsammanin ta iya rawa haka, hatta su Leema sunsha mamaki. Nan aka fara mata yayyafin kud'i kan basma ya k'ara kato saida tayi sosai kana ta sauko, koda ta samu guri ta zauna sai mai wurin ya kawo mata kud'in data samu bud'en bakinta tace ya barshi. Murna sosai yayi ya mata godiya.

Tun daga wannan rana Basma ta fara zuwa club burinta bai wuce taje tayi rawa a yi mata kuwwa a fasa mata kai. Musamman ta shiga makarantar koyan rawa babu irin wanda ba a koya mata ba hatta na larabawa.

*_Rahma Ce_*
[8/3, 12:59 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *4.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

An shirya gagarumin gasa na rawa a k'asar England, Basma na d'aya daga cikin masu fafatawa. In ta dawo daga school babu abinda take yi sai gwajin rawa, su Leema suke k'ara mata k'arfin gwiwa.

Ranar taro, k'aton hol cike yake mak'il da mutane maza da mata, ko wanne yana mazauninsa, ga kuma masu tantance rawar daga gefe, zaune suke akan kujeru na alfarma, ga dogon table a gabansu an d'aura kayan motsa baki da kuma abin sha, masu fafata gasar su Hamsin ne, a ciki ake son a finda zakara guda d'aya wanda aka tanada mak'udan kud'i da key na mota sai kuma hular Queen na rawa ga wanda taci, sai na biyu dana uku kyautar kud'i. Gasar maza da mata ne, Ganin yawansu da Basma tayi sai zuciyarta ya tsinke ta karaya, gani take ba zata ci ba, jere suke akan layi wannan na bin wannan, sun sanya riga top mai dogon hannu sai kuma wando dogo pencil ya matse jikinsu, rigan ta kama su daga sama zuwa ciki, k'asan kuma ya bud'e, tsayinta ya kawo rabin cinya. Wasu sun sanya hula a kai wasu kuma sun baje gashin su a baya, shigar Basma tayi mata kyau, ta dunk'ule gashinta ta sanya hula, ba wani makeup a fuskanta amma tayi kyau sosai. Basma itace ta goma sha shida a cikin jerin layin.

D'aya bayan d'aya suke fitowa suna gwada rawan su, alkalai suna dubawa tare da rubuta makin, 'yan kallo kuma suna ihu in rawar tayi musu kyau ga masu gwajin.

A haka layi yazo kan Basma, cikin salo da kwarewa ta fara rawa mai ban sha'awa, a hankali take komai cikin nutsuwa, lauye duk sassan jikinta take yi tamkar roba, ta d'auki tsayin minti ashirin tana rawa, nan fa hol ya kaure da ihu da alama rawarta ya birge su. Alkalai suka dakatar da ita suka ce ta tafi, na gaba yazo ya nuna nashi.

Da haka har aka gama tantance rawar su Hamsin. Daga cikin alkalai wani ya mik'e yace cikin harshen turanci, zasu cire mutane goma daga cikin su, domin fafatawa na k'arshe, washe gari zasu yi rawa a cikinsu za'a tantance Mutum na farko dana biyu har zuwa na uku da sauran numbers. Nan fa hol yayi tsit ana son aji su waye zasu shiga gasa ta k'arshe.

An fara kiran Mutum na farko da haka har aka je kan Mutum na tara, Basma bata ji sunanta ba sai ta sadak'ar da ta rasa gasar, wanda basuji sunan su ba sai kuka wasu kuma damuwa ya bayyana a fuskokinsu, Basma bata an k'araba taji an kira sunanta Basima MB a ta goma, da yake da haka tayi regista da sunan ta basima MB, saboda basaja, kuma ita ba 'yar k'asan ba ce. Ai hol saiya kaure da ihun su Leema da Meena sauran Mutane ma suka tayasu ihun. Da haka aka tashi taro Maza hud'u mata shida sune zasu fafata a washe gari.

*Washe gari*
Hol ya cika mak'il da Mutane fiye dana jiya ma, nan kowa ya samu guri ya zauna, yau shigan dasu Basma sukayi kusan irin na jiya ne sai dai an sauya launin kalan kayan da suka sanya jiya. Alk'alai suka baza ido, na farko ya fito ya fara fafatawa, har aka kai na biyar, daga nan sai aka tafi hutun tak'aitaccen lokaci.

Bayan an dawo aka d'aura har zuwa na k"arshe ta fito wato Basma, nan ta soma kafa tarihi domin rawar ta na yau yasha ban-ban dana jiya, Basma ta dage iya iyawanta, sai baza rawa take tamkar ba ita ba, inba ka mata kallon caf ba bazaka shaida Basma ce ba, domin tayi shiga na b'adda kama. Saida tayi rawa sosai sannan aka dakatar da ita, alk'alai sun fita a hol sunje had'a marking, sai da suka b'ata kimanin rabin awa kana suka dawo kan high table suka zauna, sun fara fad'an sakamako daga na goma ne, har suka zo kan na shida ya rage saura mutum Hud'u, Basma na ciki, a haka har suka fad'i na Hud'u dana uku, saura Basma dawata 'yar k'asar England d'in, sai aka tafi hutun rabin sa'a, nan fa kawayen su Basma suka rufe ta da Murna Addu'a suke Allah yasa itace mai nasara. Burin Basma ko na biyu tazo zatayi farin ciki tunda ta kafa Tarihi a fagen rawa.

Koda aka dawo daga hutun takaitaccen lokaci, hol d'in yayi shuru ana jiran aji wacce tayi winning, mai fad'an sakamako saida yayi shurun minti biyar kafin ya furta first position Basima MB kece ki kai nasara, d'ayan kuma ta zama na biyu, hol d'in ya kaure da kuwwa, nan take aka d'aurawa Basma Hular Queen, wannan dalilin ne yasa Basma take amsa sunan Queen Basma. Sunyi hotuna kala-kala hatta gidan TV na k'asar sun nuna gasar a TV.

Taro ya watse, su Meena cike da farin ciki suke, kana ganinsu kasan yau suna cikin murna, har gidan da suke zama aka kaiwa Basma motarta da kuma kud'in data samu. Tun daga wannan lokacin su Leema fankama da d'aga kai ya k'aru, Basma kuwa sunan ta sai da ya shiga cikin k'asar England sosai, kowa na sonta har wani respect d'inta ake.

Ana saura shekara d'aya su gama karatunsu su dawo k'asarmu, Mahaifin Basma ya fito takaran shugaban k'asan Nigeria, Mahaifin Meena ma ya fito takaran Gomnan jahar Kaduna. Abu kamar wasa da lokacin zab'e yazo duk suka ci zab'en. Mahaifin Basma President Mukhtar Bukar Bulama sai kuma Gomna Ibrahim Abubakar, yana amsa sunan Alhaji Bukar wanda ya rik'eshi.

Farin ciki wurinsu Basma ba a magana musamman suka dawo Nigeria akayi bikin rantsar da iyayensu, tun daga wannan lokacin sai suka chanza salo suka k'ara sauya rayuwansu ga mutane, suka keb'e kansu, musammam aka samu ascot suka bi su Basma England suna basu kariya, feeling da d'agawa ya k'aru a wajensu Leema.

Su Basma sun kammala karatunsu sun dawo gida, ta matsawa president saiya gina mata gidan huta a Abuja, haka ya sanya aka mata k'erarren gini aka zuba kayan da ta buk'ata, koda suka dawo Abuja suka sauka, domin yanzu Alhaji Mukhtar yadawo Abuja da iyalensa suna gidan shugaban k'asa, su Meena da Leema suma nan suka sauka, sun k'i komawa gidansu saida suka shafe wata guda kan suka wuce gidajen iyayensu.

Akwai wani lokaci da Basma ta tafi kano hutu, tunda Hajiya Sa'a ta ganta saita k'udurta wa ranta Prince Shureym ya samu mata, tayi alkhawari yana dawowa zata turashi yaje gun Basma su dai-daita koda baya sonta, burinta Shureym sai 'yar babban mutum zai aura. Saboda wannan k'udirin nata ne yasa ta k'ara shigewa Momy mahaifyar Basma, dole yasa ta shirya da Ammi, domin tasan tabbas sai tabi ta wajenta tunda Basma a hannunta take, Hajiya Sa'a bini-bini tana Abuja, kasan tuwar su Ammi basu san nufinta ba sai suka sake mata suka saba sosai, zumunci ya k'ara kulluwa mai k'arfi.

Duk wannan abinda Hajiya Sa'a takeyi Shureym bai sani ba yana can America, shi a can ya had'u da wata 'yar Yola mai suna Safeena, soyayya sukeyi sosai, sunyi wa juna, Alkwari aure in sun dawo k'asarmu.

Hajiya Sa'a tayi k'ok'arin had'a Basma da Shureym a waya suna gaisawa, da kyar ta shawo kan shureym bayan tayi masa bayani akan Basma, ya amince amma da sharad'in

Please Login or Register in order to submit comment