Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu labarin duk
abinda ya faru dashi asaman wannan tsaunin
Harda ceton
rayuwarsa da aljani ramzas yayi
Awannan lokaci anyi shagali sosai. Na murnar dawowar yarima saiman
Saboda haka sai jarumi zamnal ya zo gaban saiman
yace ya shugabana yaushe kake ganin zamuci gaba da tafiya zuwa birnin aljanu na hamshak .?
Dajin haka sai yarima saiman yace
Ai sai gobe zamuci gaba da tafiya Saboda yanzu akwai gajiyar gudu wacce mutanenmu suka sha
Dajin haka sai jarumi zamnal yace to ya shugabana inba zaka damuba inaso ka bamu izinin fita gasar farauta ta karshe
Kamar yadda muka saba gudanarwa a can birnin mu
aduk shekara arana irin wannan domin nasan idan muka Isa kogon tsafin boka awaisul masawi
Ba Zamu sake fitowaba sai bayan shekaru masu yawa
Dajin wannan batu sai nantake yarima saiman ya tuno da mahaifinsa sarki abu saiman
Kuma tabbas yasan cewa ayanzu haka 'yan lokuta
kadan ne suka rage masa arayuwarsa
Kuma gashi bashi da ikon zuwa ceton rayuwarsa
Don haka saiya kasa yin magana kuma nantake idanunsa suka kada sukayi jawur kamar zai fashe da kuka
Koda ganin haka sai gimbiya suhaila ta matso gabansa ta tsugunna tace
Saboda me bazaka amsa masa bukatarsa ba kwaya daya tak awajenka
Kada ka zama mai manta alheri mana
Badan Shiba ko don soyayyar da kakeyi mini ya kamata ka amsa masa bukatarsa
Kuma Awannan gasa da za'ayi nice nakeson na zama alkalin wannan gasa
Tana gama fadin haka saita Mike tsaye
Yayinda shi kuma ya bita da kallo
Tareda cewa shin kinsan hatsarin dake cikin wannan gasa kuwa da har kikeso kisa kanki acikinta.?
To indai haka ne to nima zan shiga cikin wannan gasar ayi dani
Dajin haka saitace ai idan har ka shiga cikin wannan gasar to zaka zama maison zuciya domin kuwa tabbas kaine zaka lashe wannan gasa
Don haka dolene kabarni na yi alkalancin wannan gasa
Kuma Ina mai tabbatar maka da cewa babu abinda zai sameni kamar yadda ka tabbatar mini da cewa
Sirrin karfinka yana jikina to haka nima Sirrin karfina ajikinka yake
Don haka kuwa babu abinda zai same ni na tabbatar maka da hakan
Kafin yarima saiman yake wani wani abu tuni gimbiya suhaila ta taka da kafafunta taje wajenda dakaru suke tareda jarumi zamnal
Da zuwa sai ta dubesu gaba daya tace
Yaku ababan alfaharin birnin ramlatul Saif shin Acikinku mutum nawa ne suke da ra'ayin binmu zuwa gasar farauta..?
Kafin ta gama rufe bakinta tuni wasu zaratan dakaru guda goma sha biyu
Matasa majiya karfi sun fito
Gimbiya suhaila ta kare musu kallo gaba daya sannan ta fara yi musu bayani akan wannan gasa kamar haka
Tsarin wannan gasa shine zamu bazama acikin daji neman dabbar da tafi kowacce dabba girma acikinsa
A yaketa gaba da gaba ba tareda an harbeta da kibiyaba ko an Dana mata tarko ba
Za'a yaketa ne da karfin damtse duk Wanda ya sami nasarar wannan gasa to nayi masa alkawarin kujerar waziri acan birnin mu ramlatul Saif bayan mun dawo daga fadar boka awaisul masawi
Idan kuma Kafin lokacin ajali ya riskeka
To zamu baiwa danka wannan matsayi kuma zamu ajiye gawarka a inda bazata Lalace ba har mu koma birnin ramlatul Saif mu binne gawarka a inda ake binne sarakunan birnin mu
Kodajin hakan sai dakarun suka fara tsallen murna ba shiri suka kama dawakansu suka hau
Sannan gimbiya suhaila ta shige gaba suka bita Abaya yarima saiman kuwa ya bisu da kallo
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEM BAKAR GABA
PART 17
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
lokacin da su jarumi zamnal suka shiga
cikin daji domin gasar farauta sai suka
dinga yin azababben gudu atsakaninsu
har suka shiga cikin daji saboda tsananin
jin dadin gasar da zasuyi saida suka yi nisa
da barin sansaninsu sai suka karawa dawakansu
karfin gudu domin suga wanda zai fara gajiya da wuri
koda suka karawa dawakansu karfin gudun
sai suka cika da mamaki
bakomai bane ya basu mamaki ba face
ganin cewa itama gimbiya suhaila ta iya jure
karfin gudun da suke iya yi har tana sarrafa dokinta
, duk yadda taga dama fiye da yadda suma suke iya sarrafa nasu dawakan domin kutsawa takeyi cikin sarkakiyar
bishiyoyi, ciyayi, aka za, idan kuma tazo bakin rami
sai kaga Tayiwa dokinta kaimi yayi tsalle ya tsallake ramin
wani lokacin ma sai kaga har mikewa takeyi tsaye akan dokinta ta rike linzaminsa
ba tareda ta fado kasa ba nanfa suka cika
da tsananin mamakin irin wannan bajinta
da takeyi domin duk cikinsu babu wanda zai iya sarrafa doki irin yadda takeyi
nanfa suka fara tunani acikin zuciyarsu suna cewa
shin gimbiya suhaila a ina ta koyi sarrafa doki irin wannan?
anya kuwa yarima saiman ma kansa yasan ta iya sarrafa doki kamar haka?
to idan kuwa hakane menene dalilin dayasa ta boye masa?
tambayar da kowannensu ya dinga yiwa kansa
kenan ba tareda sun san amsartaba
haka dai
suka yita yin gasar tseren gudu har suka bar dajin da suke cikinsa
suka shiga wani daji wanda akewa lakabi da harjazul maksi
dajin harjazul maksi dajine wanda ya yi kaurin
suna wajen manyan dabbobin daji masu matukar hatsari
domin agaba daya dajin baka samun kananan dabbobin daji irinsu
barewa,gada, kunkuru dadai sauransu
dabbobin da kawai suke rayuwa acikin
wannan daji sune manyan dawa kamarsu
zaki, damisa, kura, maciji, da kuma manyan
tsuntsaye masu iya daukar mutum alokaci
guda da dai sauran dabbobi masu hatsarin gaske
suma kansu manyan dabbobin idan suka rasa abinci
saidai kaga suna kama 'yan uwansu da karfin tsiya sun cinyesu
wannan daliline yasa kananan dabbobi
sukayi hijira daga wannan dajin suka gudu izuwa wasu dajijjikan don su tsira da rayuwarsu
koda suka iso wannan daji sai dukkaninsu
suka rage karfin gudun nasu tareda dora hannuwansu
akan kuffinan takubbansu suna kallon kowacce
kusurwa ta dajin domin suga dabbar da zasu farauta
jarumi zamnal ya dubi gimbiya suhaila wacce ta basu tazara sosai
jarumi zamnal ne yake biye mata baya yace
ya shugabata zaifi kyau ki koma bayanmu kici gaba
da alkalancinki mu ki kyale mu muyi wannan farauta
koda jin haka sai gimbiya suhaila ta juyo tayi
masa wani murmushi mai kama dana mugunta
wanda ya kasa gane me nene manufar wannan murmushi nata
nantake
ta juyo ta koma baya su kuma suka shiga gaba tana biye dasu
lokacin da suka isa tsakiyar dajin alokacin yamma tayi
dokunansu sun gaji saboda tsananin kishirwa da yunwa
har sun fara yin sassarfa
kwatsam sai suka hango wasu manya manyan
dabbobi suna fitowa daga cikin kowacce kusurwa ta
dajin sunyi musu kawanya babu hanyar
da zakabi ka wuce kowannensu yana dalalen harshe saboda tsananin yunwa
koda suka yi arba da wadannan dabbobin daji
sai dukkaninsu suka figice suka fara nadamar
kawo kansu cikin wannan daji
saboda sun tabbatar da cewa
yau sun kawo kansu dajin HALLAKA
shi kuwa jarumi zamnal hawayene ya zubo masa
sakamakon tunawa da yayi cewa yanzu bashi da damar da zai iya ceton kansa
balle ya ceci rayuwar gimbiya suhaila kwatsam sai suka jiyo wani irin gurnani mara dadin ji
yana tahowa daga can nesa koda ragowar namun
dajin suka jiyo gurnanin wannan zaki sai dukkaninsu suka
tarwatse suka bar wannan wajen da alama suna matukar tsoronsa
nanfa dakarun suka tattare jikinsu waje daya jikinsu yana kakkarwa saboda ganin mutuwa muraran
koda ganin haka sai gimbiya suhaila ta ce dasu
haba ababan dogaron birnin ramlatul saif
kada ku baiwa birnin mu kunya mana a idon duniya
inaso kusa ajikinku cewa kune masu nasara akan wannan zaki
ku cire tsoronsa daga zuciyarku zaku sami nasara akansa
na tabbatar muku da haka
koda jin haka sai dukkaninsu suka ji duk wani tsoro ya gudu daga zuciyarsu take suka zare makamansu aka fara kallon kallo atsakaninsu
alokacin da zakin ya fara karta kafafunsa akan kasa yana kokarin afka musu
suna cikin hakane kwatsam sai suka jiyo kukan wata rikakkiyar mikiya daga can samansu
koda ganin haka sai suka ga gimbiya suhaila ta daga doguwar rigarta
ta zaro wata sharbebiyar takobi mai matukar kaifi da tsini
kawai saita kalli dakarun tace
ku kuji da wannan zakin ni kuma zan tunkari wannan mikiyar
koda jin haka
sai zamnal yace ya shugabata karki aikata haka tunda ke baki iya yin yaki ba
dajin haka sai tayi murmushi tace shin kasan lokacin dana fara koyar tseren doki?
zamnal ya girgiza kansa alamar bai sani ba
suhaila tace to kamar yadda na iya tseren doki to haka
na iya yaki da takobi don haka saika zuba ido ka ganiā€¦..
suna cikin yin wannan magana ne wannan katuwar mikiya ta sunkuyo da kanta kasa da nufin ta suri gimbiya suhaila
nantake kuwa gimbiya suhaila tayi tsalle ta tsallake harin nata
sannan ta sake yin wani tsallen ta haye kan mikiyar suka ruguntsume da masifaffen yaki
da ita da wannan katuwar mikiyar
take mikiyar ta tashi sama dauke da gimbiya suhaila
ta luluka da ita cikin gajimare tana kokarin
wulluta daga gadon bayanta ita kuwa gimbiya suhaila sai ta rukunkume jikin mikiyar tana kokarin danno kanta kasa
nanfa suka fara kokawa ita dai mikiyar
burin da take yi shine ta sami damar wullota kasa
daga gadon bayanta yadda zata hallaka nan take
wannan daliline yasa gimbiya suhaila taki yarda ta fado kasa
koda ganin haka sai wannan mikiyar ta kwallara kara
wacce tasa dajin gaba daya ya amsa amon karar tata
faruwar hakan keda wuya sai ga dangin wannan mikiya
suna bulbulowa daga sassan dajin kafin cikar dakiku sun
kachame da yaki asararin samaniya
mikiyoyin suka dinga yunkurin daukar ta da kafafunsu
ita kuma tasa takobinta tana mai da musu da martani da ita
wohoho sai gashi gimbiya suhaila tana ragargazar wadannan mikiyoyin tamkar ana sassabe agona
duk inda ta ratsa sai dai kaga sassan jikinsu yana zubowa kasa daga sama
kamar ganyaye suna zubowa kasa daga kan bishiya
sai gashi ta zame musu kamar annobar mutuwa
duk inda takai sara sai ta zubar da akalla guda goma
jini kuwa ya dinga fallatsi daga sama tamkar ana ruwan jini
wohoho saboda wannan gumurzu da sukeyi
sai wannan murgujejen zakin ya tsaya ya fasa afkawa su jarumi zamnal shima ya zama dan kallo
daga can kuma sai zakin ya afkawa su jarumi zamnal din suka kachame da sabon fada
koda ganin haka sai gimbiya suhaila ta kara zage damtse wajen yakar wadannan mikiyoyin
kafin cikar dakika sittin ta kashe su gaba daya
saura wanda take kansa shi dinma sai ta kama wuyansa ta danno shi kasa da karfin gaske
koda suka dira akasa saita gabza masa naushi
atsakiyar gadon bayansa
take gadon bayan nasa ya karye ya fadi kasa matacce
kuma awannan lokacin wannan zakin ya
tarwatsa dakarun saura zamnal shi dinma dashi da dokinsa
zakin ya turo su kusa da wani katon rami mai zurfi wanda duk wanda ya fada cikinsa sai ya hallaka
koda ganin haka sai gimbiya suhaila ta falfala da azababben gudu ta tsinko wata murtukekiyar jijiyar bishiya
ta wullawa jarumi zamnal ya cafe adaidai lokacin da kafafun dokin nasa suka zame ya fada cikin wannan ramin BAKAR GABA
PART 18
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Lokacin da jarumi zamnal tareda dokinsa
Cikin wannan ramin sai gimbiya suhaila ta rike wannan murtukekiyar igiyar da hannun ta na hagu
dokin ya fada cikin ramin shi kadai
Nanfa suka fara kallon kallo atsakanita
Da wannan zakin kai da gani kasan kallo ne na shakkar juna
Daga can sai
Zakin ya daka tsalle ya taho kanta da nufin
ya bangajeta da kirjinsa
Nantake ta murgina kasa zakin bangaji iska yq
fadi kasa shi kadai
Kafin ya dago gimbiya suhaila tayi sauri ta daure
Wannan murtukekiyar jijiyar bishiyar ajikin kugunta
Sannan ta gyara tsayuwarta tana mai shirin tunkarar zakin
Take zakin ya juyo zuwa gareta cikin gudun gaske da nufin ya cafi makoshinta
Koda yazo inda take sai ta sa hannunta na dama ta gabzawa wannan zakin naushi
Amma sai zakin ya shanye dukan nata suka ruguntsume da fada mai muni
Wohoho hakika gimbiya suhaila ta kasance jarumar gaske
Domin dukda kasancewarta mace
Kuma
akwai ciki ajikinta sannan akwai mutum adaure akugunta
Sai gashi tana yakin da cikakken kuzari
Tamkar babu wani kayan nauyi atattare da ita
domin wannan cikin baya hanata tsalle tsalle da zulle zulle
takeyi taki bari zakin ya sami nasarar taba jikinta
duk lokacin da ta sami nasarar yankar jikinsa ko saransa da takobi sai dai taji kara ta tashi kamar haduwar karfe karfe
amma shikuwa yakasa samin nasarar tabata saboda tsananin zafin namanta
ana cikin wannan fafatawa ne kawai sai ta hangi wata bishiya akusa da inda take
koda ganin wannan sai ta daka tsalle daga inda take ta haye kan wannan bishiyar kamar ta kasance biranya ba mutum ba
nantake ta daure wannan jijiyar bishiyar da jarumi zamnal yake rike da ita yake kokarin fitowa daga cikin ramin
su kuwa ragowar dakarun mikewa suka yi zaune daga inda suke
dukda cewa zakin yaji musu mugayen raunika saboda tsananin mamakin irin jarumtakar da takeyi
domin sun tabbatar da cewa tabbas itama ta kasance jarumar gaske wacce samun kamar ta acikin mata awannan nahiyar zaiyi wahala
domin ko yarima saiman suna ganin kamar da kadan zai fita karfin damtse
koda ta gama daure wannan jijiyar bishiyar
sai ta sauko daga kanta sannan suka sake kachamewa da sabon fada
awannan lokaci sai fadan nasu sai ya kara muni fiye da farko
domin ragargazar junansu suka dingayi
tun afarkon haduwarsu zakin ya yakusheta akafadarta ta dama take wajen ya dare jini yayi tsartuwa harsaida ta kwarara uban ihu saboda tsananin zafi da zugin da taji
cikin zafin nama itama ta suri zakin ta daga sama
dukda irin girmansa da karfin damtensa ta gwara shi da jikin wata bishiya
take bishiyar ta karye ta fadi kasa cikin sauri zakin ya sake tasowa kanta zumbur da nufin ya turmusheta ya kachalchala mata fuska
koda ta lura da nufinsa sai itama ta daka tsalle
sama ta tari zakin
dukkansu suka mirgino kasa atare suka fara kwarmatsuwa da juna
nantake zakin ya fara kokarin kama fuskarta da hakoransa da faratansa da nufin ya gatsa
sai itakuma taki ta bashi damaryin hakan dukda cewa
kaifi da tsini yaki yayi tasiri ajikin zakin saita
dinga gabza masa wawan naushi afuska sannan tayi kukan kura
ta daga wannan zakin sama tayi hajijya dashi sannan ta cillashi acikin wannan katon ramin
wanda duk wanda ya fada cikinsa sai ya mutu komai hatsabibansa
alokacin da suke wannan fafatawar da wannan zakin
ashe bata saniba jarumi zamnal ya
fito daga cikin wannan ramin koda yaga
irin tsananin jarumtakar gimbiya suhaila saiya kame kyam
ya fara tunani acikin zuciyarsa abinda ya fara tunani shine
anya kuwa wannan gimbiya suhaila ce wacce na sani
ba wani aljanin ne ya sace taba yazo yake shirin yaudararmu?
yana cikin wannan tunanin ne ta karaso inda yake cike da murmushi
tace
kada kuyi mamakin abinda ya faru yanzu
domin dole ce tasa na bayyana jarumtakata agareku
na tabbatar idan har banyi haka ba da yawanmu sai mun hallaka awannan fafatawa
maganar sakamakon nasarar wannan gasa kuwa duk cikinku babu wanda yayi nasara
amma kuma na jinjina muku gaskiya domin na tabbatarda cewa kuma ba kananun jarumai bane
saboda duk dabbobin da suke cikin wannan dajin
ba irin dabbobin da suke nahiyarmu bane
ma'ana dukkansu akwai bakaken aljanu ajikinsu
wannan dalilin ne yasa suke da matukar kwarjini agurin duk wani bakon halitta daya shigo cikin wannan dajin
shikuma wannan zakin aljanin da yake jikinsa
yafi na ragowar karfi da kuma kwarjini
wannan dalilin ne yasa yafi ragowar kwarjini har suma suke jin shakkar sa
saboda haka yanzu zamu koma izuwa
can sansaninmu Kuma abinda zancewa yarima shine
gaba dayanmu babu wanda ya sami nasara acikin wannan gasa
kodajin haka sai gaba daya dakarun suka dubi junansu gaba daya
sannan wani daga cikinsu yace
ya shugabata mu mun yarda bamu sami nasara ba awannan gasa amma kuma ai kece kika cinye ta don haka mun yarda kece kika cinye ta
dajin haka sai tayi murmushi tace
aini bana daga cikin dakarun gasa amma
ni alkalancine aikina saboda haka saimu juya yanzu mu tafi
tana gama fadin haka saita tsuke bakinta tayi fito
take dawakansu wadanda suka tarwatse acikin daji suka dinga dawowa
sannan taje ta kama dokinta haye ta kama hanyar komawa sansaninsu
suma kuma suka biyota abaya
suka zabureshi
sukayita tafiya ba kakkautawa har suka iso sansaninsu
da isowarsu suka ga jama'ar sansaninsu sun tsaya
sunyi cirko cirko suna jiran karasowarsu don ganin wanene jarumin wannan gasar
nantake suka taho suka taresu cikin murna
kowanne daga cikin tawagar burinsa shine
ace dan uwansa ne ya cinye wannan gasa
itakuwa gimbiya suhaila kai tsaye ta wuce gaban yarima saiman
tayi masa wani tattausan murmushi sannan tace
naje wannan aiki daka sakani kamar yadda ka bukata naje nayi shi
amma agaba daya dakarun mu babu wanda yayi nasara
dajin haka sai yarima saiman ya juya da sauri ya shige cikin tantinsa sannan gimbiya suhaila tabishi abaya
suna isa cikin tantin ya juyo ya kalleta kallo mai nuna alamun rashin yarda yace inada tambayoyi ne kawai gareki nakeso ki amsa mini su cikin gaskiya
tun daga lokacin dana aureki shin na taba boye miki wani abin acikin raina?
dajin wadannan tambayoyi sai zuciyar gimbiya suhaila ta buga da karfi har taji kwalla ta zubo mata
sannan tasa hannu ta goge hawayen tace
gaskiya ne tunda nake dakai baka taba kokarin boye mini wani abuba acikin zuciyar ka kuma baka taba neman wata alfarma ba gurina
koda jin haka sai yace
kiyi hakuri da tambayoyi na bawai ina zarginki bisa cewa zakici amanata bane ba ko kuma zaki yaudareni bane
to menene dalilin dayasa kika boye mini jarumtakar ki
tsawon lokaci mai tsawo baki taba nuna mini itaba?
kuma menene dalilin dayasa kika yi yaki da
wannan murgujejen zakin alhalin kina dauke
da juna biyu ko kuwa bakya tsoron wani abu ya same kine?
dajin wadannan tambayoyi sai gimbiya suhaila
tayi shiru nadan tsawon lokaci sannan tace
*** *** ***
kamar yadda ka sani azahiri ka nemi aurena ne
agurin attajiri manhas amatsayin mahaifina
to ina bakin cikin sanar dakai cewa bashi bane mahaifina ba
sai dai kuma shine ya rukeni amana tamkar shine ya haifeni
sakamakon rashin samun haihuwa dashi da matarsa
sun kula dani kamar sune suka haifeni
tun daga kuruciyata har z uwa girmana
basu taba yi mini wani abuba wanda zai cutar dani ba
har zuwa sanda suka aurar dani agareka
hakan ne ya haddasa soyayya mai tsanani ta shiga tsakanina dasu
mahaifina na asali shine mafarauci mabwas
mabwas yakasance adalin mutum ne mai tsananin jarumtaka ta ban al'ajabi wanda ya karar da rayuwarsa gaba daya acikin daji kuma namijin gaske wanda baisan tsoro ba
mahaifiyata ma ta kasance mafarauciya kamar mahaifina ana kiranta da suna mubnaika
itama jarumace ta gaske kuma kyakkyawar gaske ta gaban kwatance
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME BAKAR GABA
PART 19
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Farkon haduwar mafarauci mabwas da mahaifiyata shine
wata rana ma haifiyata mubnaika ta fita
yawon farauta acikin wani daji dake can
nahiyar bakaken fata domin ta sami
labari abakin abokan sana'ar farautarta
cewa akwai nau'o'in dabbobin daji acikinsa
wadanda suka banbanta dana wannan nahiyar tamu
don haka idan har ta sami nasarar samun dabbobi
masu yawa idan ta koma can nahiyar su
zata sami kudade masu yawa saboda
haka kane ta sayar da rayuwarta ta shigo
cikin wannan daji saboda ta yarda da kanta sosai
lokacin data shigo cikin wannan dajin
sai ta kama hanya tana tafiya cikin sanda
yadda babu dabbar da zata ji motsin tafiyarta
awannan lokaci tana sanye da kayan farauta
wadanda suka nuna tsantsar kwarjininta
wannan daji data shiga kuma cike yake
da dogayen bishiyoyi masu manyan ganyaye wadanda suka sa dajin yayi duhu
saboda ko hasken rana ba sosai yake
haska cikin dajin ba ita kanta jaruma mubnaika tasan cewa ruwa baya tsami banza
ma'ana dole ne asami munanan dabbobi
acikin dajin kamar yadda dajin ma ya kasance mai ban tsoro
koda tayi nisa acikin dajin sai ta fara
hango wani katon kogon dutse agabanta
tana ganin wannan katon kogon dutse
saita kara sauri harta iso gaban dutsen
sannan ta tsaya cak tana kallonsa da nazarinsa
domin sanin menene acikinsa kawai
saita sunkuya ta debi kasar bakin kogon
ta shanshana ta da hancinta don tasan
irin halittar da take cikinsa
bisa mamaki sai taji bataji kamshin ko wacce halitta ba
koda ganin haka sai taji bata yarda da abin
da kasa ta nuna mata ba don haka sai ta
nemi itace ta kunna wutar kyastu
ta
sannan ta shiga cikin kogon don ganewa
idonta gaskiyar lamari tana fara shiga
cikin kogon saita cika da mamaki
domin kashushuwan mutane dana manyan dabbobin daji ta dinga gani acikinsa
da alamu sun shafe shekaru da zama matattu
tana taka kashushuwan jikinsu nan take yake karyewa
koda ganin wannan al'amari sai ta cika da tsananin mamaki sai tace azuciyarta
shin wacce irin hatsabibiyar dabbace acikin wannan kogo da har ta dade tana hallakar da mutane da dabbobi?
gaskiya ko wacce irin dabbace wannan ta cika shu'umar gaske abar tsoro
shin kuwa ya kamata in shiga cikin wannan kogon? ta tambayi zuciyarta
sai wata zuciyar ta daka mata tsawa tace kada ki mayar da zuciyar ki raguwa mana keda kika fito domin. neman suna mai zai sa kiji tsoron abinda kika hadu dashi yanzu
bayan kinsan shine abinda zaisa kiyi suna aduniya
idan har kika kuskura kika ja da baya tabbas kin barwa kanki abin kunya
kuma duk wahalar da kika sha abaya ta tashi abanza
da ki mutu a acikin gida gwanda ki mutu afagen daga ko ba komai za'a dinga tunawa dake
tana gama wannan tunanin sai taji shakkar komai
ta gushe daga cikin zuciyarta don haka
sai ta ci gaba da tafiya tana haska ko ina da wannan wutar itacen
abinda ya dada bata mamaki da wannan kogon dutsen shine ganin tsananin girmansa kamar unguwa guda
ahankali ta iso karshen dutsen tana zuwa karshensa
sai taji an daka mata tsawa sannan wani irin ruri ya ratsa dodon kunnenta wanda ta kasa gane ko na menene
sannan taji an sake kwallara kara wacce
ta sa kogon ya amsa kuwwa tamkar
kunnuwanta zasu dode kafin ajima sai taji
wata gagarumar iska ta taso ta ta kowacce kusurwa ta kogon sannan sannu ahankali iskar ta dinga kadawa aguri guda sannan tace dunkule ta zama wata irin murtukekiyar macijiya wacce tsawonta yakai girman bishiyar dabino
kaurinta kuwa yakai na rikakkiyar bishiyar kuka
wani irin hucin turirin hayaki yana fita daga cikin kofofin gashin jikinta
nan take ta tsaya ta karewa mubnaika kallo sosai sannan ta bushe da dariya tace
barkanki da zuwa kogon hallaka kuma kushewa ga duk wani mai yawon neman suna aduniya
yake wannan matashiyar budurwa ki sani cewa nice uwar hatsabiban aljanu na duniya
kuma abar tsoro ga duk wani mahaluki da yayi arba dani
ke bama mutane jinsinki ba hatta aljanu suna shakkar haduwa dani balle dabbobi
tunda na wanzu acikin wannan kogon dutsen nake shayar da kaina jinin bil'adama da kuma aljan
sannan ina da karfin sihirin d zan iya janyo ruhin
duk wani mai burin neman suna a ko ina yake a duniya
wannan daliline yasa kema kika kawo kanki nan
da yawan mutane ire irenki sun kawo kansu izuwa wannan kogon amma babu wanda ya taba fita araye
dajin haka sai jaruma mubnaika ta kyalkyale d dariya
itama sai ta dakawa macijiyar tsawa tace
karya kikeyi tsohuwar azzaluma ina rantsuwa
da karfin tsafi karshenki yazo baki isa ki iya wuce wannan ranarba
domin koda zan mutu sai dai muyi mutuwar kasko tare dake
kafin ta gama fadar abinda take fada sai macijiyar ta bushe da dariya akaro na biyu sannan ta shammaci mubnaika ta kawo mata duka da jelarta
cikin bakin zafin nama ta sunkuya jelar ta harbi iska
itama sai tayi sauri ta zaro takobinta daga cikin kufe ta fadawa macijiyar
suka kachame da azababben yaki mai tsananin firgitarwa da tayar da hankali
kai inda ace akwai wani mutumin akusa dasu lokacin da suke wannan fafatawar idan bai kasance gawurtaceccen jarumiba zai iya haukacewa
ko kuma idan bai iya zulliya da kauce kauceba
cikin 'yan dakiku zai hallaka saboda tsananin tashin hankalin da sukeyi atsakaninsu
domin duk sanda macijiyar ta kawowa
mubnaika duka ko kuma harbi da bakinta da zarar ta kauce saidai kaga duk abinda ta samu nan take yake dagargajewa koda kuwa dutsene ya zama kamar nukakken gari
idan kuwa ta kawowa mubnaika harbi da bakinta
idan ta goce saidai kaga wani bakin dafi ya zubo kasa
nan fa fadan nasu ya karayin tsanani duk sa'adda mubnaika ta sami
nasarar sarar jikin macijiyar da kaifin
takobinta saidai kaji wata kara ta tashi kamar karar haduwar karfe da karfe
kogon dutsen saiya fara girgiza kamar
zai ruguje saboda tsananin bala'in da fadan nasu yake haifarwa
inbadon mubnaika tana da tsananin zafin nama ba da tuni ta hallaka farat daya a gurin macijiyar domin wannan macijiyar tana da tsananin karfin damtse nesa ba kusa ba
ita kanta macijiyar tayi mamakin yadda suka dade suna fafatawar da mubnaika
domin tunda take bata taba shafe dakiku sittin ba suna fafatawa da wata halittaba face ta hallaka ta
amma sai gash yau ta hadu da bil'adama guda daya wacce suka shafe dakiku masu yawa suna fafatawa
a wannan lokaci sai da jaruma mubnaika ta raina kanta taji tana nadamar shigowa cikin wannan kogon domin ta fuskanci cewa indai suka jima suna fafatawa ahaka nan da "yan dakiku kadan zata iya gajiya
da zarar ta gajin kuwa shikenan wannan hatsabibiyar macijiya ta sami nasara akanta
babu abinma da yake kara firgita ta face
ganin cewa ko kadan karfin sihirinta
yaki yayi takanta akanta
domin ta jarraba yin hakan sau da dama amma babu alamar nasara
don haka saita kara zage damtse wajen yaki da ita
ana cikin wannan fafatawar ne maciyar ta shammaci mubnaika ta gabza mata wawan duka da jelarta
saboda karfin dukan saida tayi sama taje ta gwaru d jikin wani dutse take gudan jini yayi fitar burgu daga hancinta da kuma bakinta
saida taji kamar kashushuwan bayanta sun karye saboda karfin naushin
tayi kokarin mikewa tsaye awannan lokaci
amma sai taji ta kasa koda mikewa zaune
saboda tsananin jigatar da tayi
ita kuwa wannan maciyar da taga haka sai ta sake kyalkyalewa da dariya sannan tace
dama na fada miki baki isa ki iya kwacewa ba daga hannuna don haka yanzu kinaji kina gani zanzo na tsotse jinin jikinki sannan kuma na hallaka ki gaba daya
macijiyar na gama fadin haka saita taho zuwa kanta gadan gadan
ta sunkuyu da katuwar fuskanta mai kama da ta mutane kasa
nan take wasu kananan allurai suka fito daga cikin

Please Login or Register in order to submit comment