Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan aljanin
Sannan ta zauna bisa turba ta kwantar dashi akan cinyarta
Sai a sannan ne ya kula da karayar da take jikin kafarsa
Cikin daka tsawa tace da lamakus yaje ya samo kiraren da za'a gyara masa kayar tasa
Nantake aljani lamakus ya bace cikin abinda bai wuce dakika biyu ba ya dawo dauke da kirare sirara tare da danyun bawon bishiya
Sannan tace da aljani lamakus shin ka iya gyaran karaya ?
Cikin biyayya aljanin yace eh ranki ya dade
Mubnaika tace to ai saika fara aikinka ko
Take kuwa lamakus ya fara gyara karayar amma abin mamaki
sai yaga babu alamar jin zafin gyara atattare da marwan
Ba komai ya jawo hakanba face kallon fuskar jaruma mubnaika da yakeyi a wannan lokaci ita kuma sam bata fahimci hakaba
Ana cikin gyaran ne sai tayi tunanin ya kamata taje ta yi masa shinfida
Kafin a gama yi masa gyaran
Take kuwa ta sauke kansa daga kan cinyarta ta juya ta shige cikin tantin
Shigarta keda wuya sai taji jarumi marwan ya kwarara uban ihu
Cikin firgita ta fito daga cikin tantin
Koda ta fito sai tayi arba da aljani lamakus hancinsa yana zubar da jini
Cikin razana aljanin yace
Ya shugabata hakika gyaran nan ba zai taba yiwuwa ba muddin bakya nan wajen domin ganinki ne yake
hanashi jin radadin gyaran karayar nan dake jikinsa
Don wanna jinin da kika gani akan hanci na ba komai ya jawo hakanba face naushinsa saboda barin gaban fuskarsa da kikayi
Dajin wannan magana sai kuwa ta dawo daidai inda fuskarsa marwan take
Ta sunkuya tanayi masa murmushi
Shikuma lamakus yaci gaba da yin aikinsa ba tareda
sun sami wata matsalaba haka suka gyara karayar suka gama
Ana gama gyaran ne kuwa barci mai nauyi ya sace jarumi marwan
Bayan ya farkane ya bata labarin irin gwagwarmayar da yasha da wannan sihirtacciyar dorinar ruwa
Koda gama bata wannan labari sai kawai ta rungume shi tare da fadin cewa
Tabbas na yarda dakai ne zanyi rayuwa
Kuma ba'a halicceni ba saidon na zama matarka don haka
Tashi yanzu take zamuyi aure ni dakai
Shikuma aljani lamakus saiya zama shaida atsakanin mu
Tana gama fadin haka sai ta kama kafadunsa ta tasheshi tsaye suka fita daga cikin tantin
Sannan ta zaunar dashi suna masu fuskantar juna
Shi kuma
aljani lamakus saiya dauko wannan kan dorinar ruwan ya ajiye shi acan gefensu kadan
Take mubnaika ta tashi taje ta dora hannunta akan mushen kan
dorinar ruwan tare da rufe idanunta Tsawon dakiku kamar mai sauraron wani labarin
Bayan nan kuma sai ta dauki kyastu ta kunna wuta ta cilla jikin kan dorinar ruwan
Take wuta ta kama kamar ansa karmami sannan ta dawo inda jarumi marwan yake
Ta mika masa hannunta cike da murmushi yasa wata 'yar karamar zabira ya yanka
Sannan shima ya yanki nasa tafin hannun ya kara akan nata hannun jininsu yana haduwa da juna
Atare cikin hadin baki duk su biyun suka ce
Munyi alkawarin zama daya tare har abada kuma ba zamu taba rabuwa ba Suna gama fadin haka
Sai dukkansu suka fara murmushi farinciki
Haka suka kasance suna rayuwar aurensu a cikin wannan daji har aka sami cikina aka haifeni
A ranar da suka haifeni sun yi farinciki sosai na samun haihuwar jaririya kyakykyawa
Kuma suka rada mini suna SUHAILA a lokacinda na fara girma da kansu suka dinga koyar dani horon yaki da iya yin farautar manyan namun daji
A wannan lokaci banida abokin yawo face aljani lamakus tare dashi mukeyin duk wani wasa da nake sha'awa
Har na kai shekara bakwai
Ashe Ita kuma wannan dorinar ruwan da mahaifina ya kashe
Ba komai baceba face baiwar wani babban sarkin birnin aljanu
Ana kiransa da suna sarki mafazil shine wanda ya sana'anta wannan sihirtacciyar dorinar ruwan domin aiwatar da wani sihirinsa na tsafi
wanda bincike ya tabbatar masa da cewa bazai taba samun
cikar burinsa ba face ya hallaka duk halittun da suke rayuwa akarkashin ruwa
Wannan daliline yasaka shi sana'anta wannan sihirtacciyar dorinar ruwa
Kuma duk abinda ya faru ya riga ya gani kuma yasan cewa tabbas ya aikata masa kuskure
Koda gama ganin wannan al'amari saiya rusa uban ihu sannan yace
Dolene na dauki fansa akan abinda yayi mini kuma fansar
nan ba akan iya shi kadai zata tsaya ba saita shafi duk wani makusancinsa
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN BAKAR GABA
PART 23
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Inda muka tsaya
Ashe Ita kuma wannan dorinar ruwan da mahaifina ya kashe
Ba komai baceba face baiwar wani babban sarkin birnin aljanu
Ana kiransa da suna sarki mafazil shine wanda ya sana'anta wannan sihirtacciyar dorinar ruwan domin aiwatar da wani sihirinsa na tsafi
wanda bincike ya tabbatar masa da cewa bazai taba samun
cikar burinsa ba face ya hallaka duk halittun da suke rayuwa akarkashin ruwa
Wannan daliline yasaka shi sana'anta wannan sihirtacciyar dorinar ruwa
Kuma duk abinda ya faru ya riga ya gani kuma yasan cewa tabbas ya aikata masa kuskure
Koda gama ganin wannan al'amari saiya rusa uban ihu sannan yace
Dolene na dauki fansa akan abinda yayi mini kuma fansar
nan ba akan iya shi kadai zata tsaya ba saita shafi duk wani makusancinsa
Cigaba
Wannan shine alkawarin da sarkin aljanu mafazil ya daukarwa kansa
Ni kuma mafarauci marwan tareda mahaifiyata suka cigaba da horar dani dabarun yaki dana farauta
Har y zamana cewa tun ina da shekara bakwai ina iya fita farauta ni kadai
Kuma na sami nasara akan duk abinda nayi karo dashi
HAKIKA MASU IYA MAGANA SUNYI GASKIYA DA SUKACE BAREWA BATA YI GUDU BA DANTA YAYI RARRAFE BA
DOMIN DUK IRIN JARUMTAKAR SADAUKI MARWAN DA KUMA MAHAIFIYARTA
SAIDA TA GADOSU KAI HATTA A BANGAREN KYAU SAITA ZAMA KAMAR AN TSAGA KARA
DOMIN DUK WANDA KA KALLA TSAKANIN MARWAN DA MUBNAIKA SAIDAI KAGA SUNA TSANANIN KAMA
Ana cikin wannan haline wata rana aljani lamakus tareda suhaila
sun fita yawon shakatawa domin babu abinda suhaila
takeso sama da taga suna yawo a cikin samaniya tana giftawa
Ta saman dajijjika da kuma birane tana ganinsu kanana
shi kuma jarumi marwan tareda mubnaika suna cikin daki
suna gudanar da zaman takewar su ta aure
sai suka wata irin iska mai karfi tana kadawa kafin su ankara
sai suka ji duk jikinsu yayi sanyi kamar an zare musu lakar jikinsu
Take barci mai nauyi ya sacesu sai farkawa sukayi suka gansu
a cikin wata tangamemiyar fada mai girman gaske
Cike da
dakarun yaki masu matukar kwarjini da ban tsoro hannuwansu
rike makaman yaki masu matukar hatsari
Bisa kan wata katuwar karagar mulki kuwa wani katon mummunan aljani ne
Mai girman gaske cike da kwarjini da ka ganshi kasan dole ne kura taci nama
Ma'ana dole ne ya kasance jarumin gaske gaske kuma mashahurin matsafi
kowa afadar yayi tsit kamar mutuwa ce ta gifta babu maiyin koda tari
atsakiyar fadar kuwa wata katuwar katangace mai tsawon gaske
Kasanta kuma wutace takeci kamar an zuba mata makamashin mai
Aljan
Sarki mafazil ya mike tsaye ya dubi jama'arsa cikin wata irin kakkausar murya yace
Yaku mutanen birnin hamshak
Dukkanku kun sani cewa babu wanda ya isa ya shiga cikin hurumi na ya fita lafiya
Shi wannan bakon saurayi da kuke gani ba karamin hatsabibi bane
Domin shine bil'adama na farko daya taba rusa mini shirina sai shi
Dukkanku kun sani cewa banida burin da yafi naga naga bayan
babban abokin gaba ta wanda aka shayar damu tare wato sarkin yaki ramzas mahaifin aljani harisul mar'uf
Hakika yanzu daf nake da cika burina amma sai gashi wannan
saurayin ya rusa mini komai saboda haka yanzu agaban idonku zan dauki fansa akansu
Yana gama fadar haka saiya juyo ya kalli su jarumi marwan yace
Ku kuma yanzu zan baku zabi guda biyu saboda nasan yadda
kuke matukar kaunar junanku
Zabi na farko shine ku sasanta atsakaninku daya ya mutu ya
bar daya domin ku karya alkawarin da kuka daukarwa
junanku tun a farkon haduwar ku ko kuma ku mutu gaba daya shikenan an manta da tarihin jarumtakarku.....
Kafin ya gama fadin abinda yake bakinsa sai yaji jaruma mubnaika
ta daka masa tsawa tace
Karyarka tasha karya tsohon azzalumi baka isa ka kasa mu karya
alkawarin da yake tsakanin muba
Koda jin haka sai shima yayi murmushi sannan yace
Ai dolece zatasa ku karya alkawarin don haka mu zuba mu gani
Yana gama fada haka saiya karanta wasu dalasiman tsafi
Faruwar hakan keda wuya saiga wasu irin sihirtattun kunamai
suna shigowa ta saman fadar
Adadin su yakai guda dubu kuma kowacce daga cikinsu tana
Da fuka fuki ajikinta wanda zasu dinga tashi sama dasu
Take kunaman suka yo kansu marwan
Nanfa marwan da mubnaika suka juya baya suka hade jikinsu
Suka ruguntsume da kokawa da wadannan kunaman
Duk kunamar da suka daka nan take take faduwa kasa
Amma saboda taurin rai irin nasu sai kaga sun sake tashi anci gaba da fadan dasu
Ashe alokacin da aljani mafazil ya dauko su marwan acikin
gidansu saidaya zuba musu wata irin guba acikin jikinsu wacce
zata rage musu kuzari da karfin jiki
Koda aka shafe sa'a daya ana fafata wannan kazamin yaki
Sai wadannan kunaman suka fara samun damar harbin su jarumi marwan da wani irin mummunan dafi mai karfin gaske
Nantake sukaji duniyar ta canja musu wani irin mummunan
radadi ya dinga ratsa sassan jikinsu
Take jiri ya dinga dibarsu dukkansu suka tabbatar da cewa tabbas
lokacin mutuwarsu yayi
Don haka sai marwan ya ture mubnaika ta fadi kasa
Sannan shima ya fada kanta ya lullubeta yadda babu wata
kunamar da zata iya harbinta suka ci gaba da harbin gadon bayansa sannan yace
Ya masoyiyata saboda alkawarin da muka dauka ni dake kada mu zama masu son kanmu
Kada ki manta yanzu fa bamu kadai bane muke rayuwa ba
Harda 'yarmu wacce muka haifa wato suhaila
Don haka ni na yarda na hallaka ke kije kici gaba da rainonta...
Kan ya gama fadar abinda yake bakinsa sai itama ta tureshi
Ya koma kasa ita ma ta danne shi irin yadda yayi mata tace
Ai ba kaine ka fara yin alkawari ba a tsakanin mu
Nice wadda
ta farayi don haka kuwa ni ya kamata in fara mutuwa bakaiba fatana kawai ka ruke soyayyata acikin zuciyarka
Haka dai sukayi ta murgin murgin atsakaninsu
Kunaman
nan kuwa sukayita harbinsu a jiki har yazamana jinin jikinsu ya gurbace da dafi
Daganan basu san sanda suka mirgina cikin wannan katon ramin ba wanda wuta take ci acikinsa ba
Suka mutu duk su biyun
Al'amarin 'yarsu kuwa suhaila da aljani lamakus bayan sun gana yawon shakatawarsu
Sai dawowa sukayi gida suka tarar da gidan babu kowa saidaima hargitsewa da yayi
Alamar babu lafiya nantake suhaila tashiga cikin daki ta dauko madubin tsafin mahaifinta ta shafeshi taga hoton duk abinda ya faru
Dukda kasancewarta yarinya karama saida tayi kuka sosai na rashin iyayenta
Da kyar aljani lamakus ya rarrasheta sannan yayi mata alkawarin zai sadata da wasu iyayen daban masu kirki
Wadanda zasu riketa amana tayi rayuwar farinciki tareda su
Daga wannan rana lamakus ya dauketa suka bar wannan dajin da suke da zama
++++++++++++++++++++++++++++++
+++++++++++
Acan birnin ramlatul saif kuwa akwai wani hamshakin attajirin dan kasuwa wanda ake kira da suna manhas
Manhas attajirin gaske ne yana da matar aure guda daya mai suna sadwisa
Tunda sukayi aure basu taba samun haihuwa ba sai bayan shekara hudu dayin auren nasu
Sannan suka haifi 'ya mace kykykyawa wacce suka kwallafa soyayyarsu gaba daya suka dora akanta
Aranar da suka haifeta ne suka sanar da mutane haihuwar da sukayi sannan sukayi alkawarin ba zasu bari kowa yaga wannan yarinya ba hatta ma'aikatan gidansu
sai alokacin da balaga alamun girma suka fara bayyana ajkinta
A wannan lokacin ne zasu nunawa duniya 'yar da suka samu domin nema mata mijin aure
Wannan yarinya da suka haifa kuwa sai lokacin haihuwarsu yazo daidai dana suhaila ma'ana dai sa'annin juna ne
Bayan shekara bakwai da haihuwar wannan jaririya sai wani irin gigitaccen ciwon zuciya ya kamata ba irin maganin da basu nema mataba amma yaki yayi aiki har gurin bokaye sunje sunyi musu bayanin irin ciwon
Amma kowanne boka sai yace shi baisan maganin wannan ciwoba
Amma saboda tsananin soyayya ta da da mahaifa sai suka ki hakura da neman magani
Wata rana acikin yawonsu ne suka hadu da wani b oka
Bokan yace masa yakai wannan attajiri
Ka sani cewa
Saidai kayi hakuri domin 'yarka ba zata taba samun lafiyaba
Domin mutuwa zatayi amma kayi hakuri abin bauta yayi alkawarin bazai baka kunyaba akan alkawarin daka dauka ba
Daga ranar da 'yarka ta mutu aranar zaku sami wata yarinyar wacce zata maye maka gurbin 'yar taka
Kuma zaku so juna fiye da yadda kuke soyayya da 'yarku
Kuma zata kasance jarumar gaske wacce zata auri dan sarkin garinku wato yarima saiman
Sai dai ina mai umartarku daku kira wannan yarinya da sunan da tazo muku dashi
Kuma ku tilasta mata akan ta boye jarumtakarta karta bayyana ta ga kowa sai bayan shekaru ashirin masu zuwa alokacin da zasuyi wata tafiya tareda mijinta yarima saiman
da wannan bayani sukayi bankwana da wannan bokan suka tafi suka barshi
Suka zuba ido suga ranar da maganar wannan bokan zata tabbata
Bayan dawowarsu daga wajen wannan bokan da kwana talatin kuwa sai wannan 'ya tasu ciwonta ys kara tsanani sosai
Fiye da farko har rai yayi halisa ta mutu suka zubar da hawayen shakuwar da sukayi
Amma basuyi kukan da zaisa mutane susan me ake cikiba
Attajiri manhas ya fito wajen dakarunsa yace da guda uku ya umarsu suje kasuwa su sayo masa katuwar akatin katako
Domin yanaso ya zuba kayansa aciki
Take kuwa hadiman suka je kasuwa suka sayo cikin abinda bai wuce sa'a daya ba suka dawo
Sannan attajiri manhas ya tashi shi kadai yayi bad da kama ya ha kan doki ya fice ta bayan gidan ya tafi makabarta ya binne 'yar tasa
Yakamo hanya zai taho gida kenan sai yaji an kira sunansa ta baya
Cikin firgita manhas ya juyo
Take yayi arba da aljani lamakus har manhas ya figita zai ruga da gudu kenan
Sai lamakus yace saboda me zaka gudu bayan abinda kake nema yana hannuna
Cikin rawar murya manhas yace me kake nufi nifa ban gane maganar ka ba
Lamakus ya kwantar da jikinsa akasa
Take saiga suhaila tayi tsalle ta diro daga gadon bayan nasa
Nanfa ya kura mata idanu cike da tsananin mamakin yadda yaga suna matukar kama da 'yarsa kamar an tsaga kara
Saidai ita tafi 'yarsa marigayiya kyau sosai saboda tafita haske da shekin fata da kuma gashi
Amma hatta tsawon jikinsu dayane babu wani banbanci
Take yaji ya kamu da tsananin soyayyar wannan yarinya
Tamkar dama can sun dade da sanin juna
Itama kuma suhaila tabi attajiri manhas da kallo ya zamana suna ta kallon juna ko kiftawa basayi
Aljani lamakus ya katse shirun da yake tsakaninsu da fadin cewa
Ya kai wannan attajiri kaine kadai ya kamata ka rike wannan yarinya a duk fadin duniya
Don haka ne muka kawo maka ita sannan kuma samun wannan yarinya zai debe maka kewar 'yarka marigayiya
Kuma ina tabbatar maka da cewa zatayi biyayya agareka sosai
Sannan ya kalli suhaila itama yace
Yake 'yata wannan shine lokacin da zamuyi bankwana dake
Domin ba zaki sake ganina ba har abada amma ina mai farincikin cikawa iyayenki burin da yake cikin zuciyarsu
Sannan ina mai gargadinki cewa kiyi biyayya sosai ga wannan sabon mahaifi naki
Da wannan furuci nakeyi miki bankwana sai wani lokacin idan da rabon zamu sake haduwa
Yana gama fadin haka saiya bude fukafukansa. Ya tashi sama ya bace bat
Yayinda ita kuma suhaila tabi shi da kallo idanunta suna ta zubar da kwalla
TABBAS MASU KARIN MAGANA SUNYI GASKIYA DA SUKA CE
IDAN AKA SABA DUK RANAR RABUWA SAI JUKATA SUNYI ZAFI
ba komai ne ya haddasa wannan hawaye a idanunta ba face
Tunawa da tayi da mahaifanta wadanda ta rabu dasu a rana tsaka
Sannan kuma gashi yanzu ta rabu da abokinta wanda ta saba dashi sosai
Daga can sai attajiri manhas ya rarrasheta yace kiyi hakuri yake 'yata
Komai na duniya bashida tabbaci amma yanzu mu zamu yaye miki duk bakin cikin da yake cikin zuciyarki bayan nan saiya umarceta data shiga cikin wannan akwatin
Baya ta shiga sai ya ciccibeta ya dorata akan dokinsa
Ya kama hanyarsa ta komawa gida
Tafiyar rabin sa'a kacal yayi ya isa gida ya kaita turakar da 'yarsa marigayiya take
Daga wannan rana suka ci gaba da rainonta kamar sune suka haifeta
Soyayya da shakuwa mai tsanani ta shiga tsakaninsu
Fiye da wacce take tsakaninsu da marigayya kuma tun daga wannan lokaci
Ya dinga samun daukaka acikin arzukinsa
Har zuwa sanda ta girma ya bayyana ga jama'ar garin a matsayin 'yarsa ta cikinsa
a wannan rana anyi shagali sosai domin saida 'ya'yan manyan attajirai da sarakuna da jarumai saida suka shiga neman aurenta a wannan rana
Saboda hakane attajiri manhas yace ta zabi wanda zata aura atsakaninsu
Amma saitace ita bata da zabi kawai dai tanaso ta auri wanda yafi kowa jarumtaka akasar
Da manhas yaji abinda ta fada saiya je ya fada musu
Saboda haka suka shirya gasar fada acan wani daji inda manyan jarumai na nahiyar suka halarta
Amma aka rasa wanda yaci gasar face YARIMA SAIMAN
Koda tazo nan a labarinta sai idanun yarima saiman suka ciko da kwalla
Ya kamu da tsananin tausayinta domin sai yanzu ne yasan asalin tarihin rayuwarta
Kuyi hakuri kan dogon lokacin dana dauka banyi muku post ba
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN BAKAR GABA
PART 24
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Koda tazo nan a labarinta sai idanun yarima saiman suka ciko da kwalla
Ya kamu da tsananin tausayinta domin sai yanzu ne yasan asalin tarihin rayuwarta harsaida hawaye ya zuba daga idanunsa saboda tausayi
Suhaila tace
Wannan shine tarihina amma ina mai baka hakurin boye maka wannan sirri
Dajin haka sai yarima saiman yace
Ashe dai bamu kadai bane muke shirya BAKAR GABA acikin zuciyarmu ba
Harda ke saboda haka ina mai yi miki alkawarin cewa dole saina daukar miki fansar abinda aljani mafazil yayi miki
Adaidai wannan lokaci da suke wannan hirane suka lura ashe har gari
Ya waye ba tareda sun ankara ba koda ganin haka sai ya fito
Daga cikin tantinsa
Yace da jama'arsa gaba daya su shirya yau zasu tafi aiki na karshe
Wato birnin hamshak
Domin dauko kubar muftahul sihir ko ta halin kaka sannan su dauki fansar abinda yayiwa iyayen gimbiya suhaila
Yana gama fada musu haka sai ya shiga cikin tantinsa ya dauko wani garin magani ya watsa acikin bakinsa
Sannan yace to daga yanzu bazan kara jin barciba har tsawon wata guda
Inda zai daukeni kammala wannan aiki da yake gabana
Cikin rabin sa'a jama'ar tasa suka gama shirye shiryensu tsaf
Sannan yarima saiman ya shige gaba su kuma suna biye dashi a baya suka nufi hanyar zuwa birnin hamshak
+++++++++++++++++++++±++++++++
+++++++++++
Acan filin yaki kuwa inda ake fafatawa da dakarun sarki abu saiman
Da dakarun boka ulumanu kuwa abin yayi muni
Domin babu bangaren da basajin jiki acikin wannan duk inda sarki abu saiman yasa gabansa saidai kaga dakarun boka ulumanu
Suna zubewa kasa matattu kamar ana sassabe a gona
Haka shima bangaren boka ulumanu bai tsaya saurarawa dakarun abu saiman ba
Hakika tashin hankali ba abin so bane domin komai rashin imanin mutum idan yaga yadda dakarun suke mutuwa kamar annobar mutuwa ce ta fada kansu
Jini kuwa ya dinga fallatsi akan kasa kamar an bude idaniyar ruwa
Sassan jikin bil'adama ya dinga shawagi asararin samaniya
A bangaren manyan gwarazan kuwa sai neman junansu sukeyi amma har asannan sunki haduwa
Saida aka kwana kuma aka yini ana wannan yakin amma an rasa bangaren da yake yin nasara
Wannan al'amari ba karamin dugunzuma hankalin boka ulumanu yayi ba
Domin shi azatonsa baifi cikin sa'a biyuba zasu gama da dakarun birnin ramlatul saif ba
Bisa dole duk bangare biyun suka buga kugen tsayar da yaki
Kowa ya koma sansaninsu
Sannan suka debe gawarwakin jama'ar da suka rasa rayukansu
Acikin dakarun sarki abu saiman kaso biyune suka mutu awannan rana
Acan bangaren boka ulumanu kuwa kaso uku da rabi ne suka rasa rayukansu a wannan fafatawa
Ba komai ne ya baiwa dakarun sarki abu saiman nasaraba face
Cewa suna yakin ne da dukkan karfinsu kuma su basu da burin ci gaba da rayuwa a duniya
Tunda sun tabbatar da cewa basu da nasara awannan yaki
Sannan kuma sunaso su kare martabar kasarsu da kimarta yadda har duniya ta nade baza'a mantada ita ba
Awannan rana sunyi farinciki sosai saboda ganin wannan nasara da suka samu
Kashe gari kuwa da sassafe dukkan dakarun bangarorin biyu suka sake fitowa filin daga domin ayita ta kare
Sannan aka buga kugen ci gaba da yaki
Nanfa suka ruga kan junansu suka sake kachamewa da azababben yaki fiye da wanda suka yi ajiya
Awannan safiya saida kasar gurin ta dinga jijjiga kamar zata dare biyu
Ihun mutane dana karafkiyar karafa ya cika dodon kunne
Kowanne bangare ka duba babu abinda zaka gani sai sassan jikin bil'adama
Babu abinda zai baka tausayi sama da kaga mutum an sare masa kafafu an barshi da gangar jiki
Yana neman taimako amma saikaga memakon a taimakeshi saidai atakeshi abarshi awajen har ransa ya bar jikinsa
Ana cikin wannan yakin ne boka ulumanu yaga tabbas neman ayi ragas tsakanin dakarunsa dana sarki abu saiman
Da ganin haka saiya umarci dakarunsa da cewa su dasawa dakarun abu saiman tsawa
Take kuwa aljanun sukayi tsalle suka tashi sama da nufin su dingayi musu dauki daidai
Koda ganin abinda yake shirin faruwa sai shima abu saiman ya karanta wasu dalasiman tsafi
faruwar hakan keda wuya saiga wata irin wuta ta fito daga cikin bakinsa
Ta tashi sama ta dinga bin aljanun daya bayan daya tana konawa
Kafin kace meye ta gama kona aljanun kurmus
Kuma adaidai lokacin ne dakarun bangarorin biyu sukayi ragas dayansu bai tsira da rayuwarsa ba
Ya zamana daga sarki abu saiman sai kuma boka ulumanu
Suka dubi junansu kallo wanda ake cewa kar ta san kar
Alokacin fuskar boka ulumanu tana wani gyatsine da nuna tsantsar kiyayya
Shi kuwa abu saiman saiya bushe da dariya yana mai nuna ulumanu da yatsa yace
Kana mamakin ganin yadda akayi ragas tsakanin jama'ata da kuma taka ko?
To kadaina mamaki domin shirina ya zarce tunaninka
Ni farinciki na kawai shine kada ka sami nasara akan mu cikin sauki
Burina kawai shine naga na hanaka cika burinka cikin sauki sannan kuma naga na fitar maka da jini daga jikinka kafin ajalina ya riskeni
Don haka saika shirya tarata
Yana gama fadar haka saiya falfala da azababben gudu zuwa kan ulumanu takobinsa
Na ruke a hannunsa suka ruguntsume da azababben yaki
Hakika fadan manyan zakuna daban yake dana kananan karnuka
Domin kuwa wannan fadan nasu sai ya zama abin sha'awa ga duk wanda yake da damar tsayawa kallo
Duk sanda takubbansu suka hadu da juna saidai kaga tartsatsin wuta yana tashi
Tamkar ana hura wuta a makera sai gashi karfinsu yana kokarin zuwa daya
Kura kuwa ta tashi kamar ana tada kura
Tamkar jikinsu bana jini da tsoka bane ba
Saboda har wani tashi sama sukeyi idan suna fadan tamkar tsuntsaye masu fuka fukai saida suka yini suna wannan gumurzu dare ya raba
Amma basu daina gumurzun ba tamkar wadanda dama can basa gajiya
Har zuwa safiya alokacin ne takubbansu suka dakushe gabaki dayansu
Saboda haka sai duk suka watsar dasu sannan suka afkawa junansu da naushi hannu da kafa
Nantake kuwa suka hadawa junansu jini da majina
Domin wani irin naushi suka dinga yiwa junansu tamkar kayan tsummo kara
Nanfa duk suffofin fuskar su ta fara canjawa gaba dayanta duk ta kukkumbura saboda karfin naushi
Da alama idan aka ci gaba da wannan fadan a haka to babu wanda zai yi nasa a cikinsu saidai duk suyi kare jini biri jini daga baya kuma suyi ragas
Koda yin wannan tunani sai boka ulumanu ya shammaci sarki abu saiman ya debo kasa ya watsa masa ita a cikin idanunsa
Take idanun suka rufe ya daina ganin komai kafin yayi wani yunkuri boka ulumanu ya shuri takobin wani mataccen badakare ya jefo masa ita
Nantake takobin tazo ta cake ajikin wuyansa
Take jini yayi feshi daga jikin wuyan
Amma saboda taurin rai kafin ya fadi kasa sai shima ya shuri takobin wani badakaren sannan ya daka tsalle daga inda yake ya a saman ya sarewa boka ulumanu hannunsa guda daya na hagu
Nantake ya diro kasa tareda hannun ulumanun
Amma duk da haka bai fadi kasa ba sai ya dire akan gwiwarsa ta dama
Ta hagu kuma sai ya tsayar da ita ya dora hannunsa na hagu akai
Hannun damansa kuwa takobin daya sare hannun ulumanu ce ya caketa akasa tana digar da jini
Fuskarsa cike da fara'a yanayin murmushin farinciki har ransa ya fita daga jikinsa
Koda boka ulumanu yaga ya rasa hannunsa guda daya saiya kwarara uban ihu
Nantake ya karanta wasu dalasiman tsafi ya tofa akan dungulmin hannun nasa don tsayarda jini
Nan da nan kuwa jinin ya tsaya a daina jin radadin da yakeji
Sannan ya kwarara uban ihu wanda yasa dajin gaba daya ya amsa kuwwa
Sai ya waiwaya yaga duk yawan dakarun daya taho dasu sun mutu babu ko guda daya face aljani harisul mar'uf
Don haka saiya kwallawa harisul mar'uf kira kafin ya rufe bakinsa ya bayyana
Yace to ai mu mungama aikinmu sai kai kuma kazo mu shiga cikin garin domin ka hallaka mana abin bautar tasu
Da jin haka sai yace an gama ya shugabana
Amma ina fatan kaima ka zama mai cika alkawari
Yana gama fadar haka sai ya kunna kai cikin birnin ramlatul saif
Ulumanu yana biye dashi abaya tunda suka shiga cikin garin boka ulumanu yaga baiga kowacce irin halittaba mai rai acikin birnin koda kuwa kaza babu har suka karade birnin gaba dayansa nantake ulumanu yace
Acikin zuciyarsa to ina mutanen wannan gari suka gudune na nemesu na rasa?
Gaskiya ya zama wajibi na bincika madubin tsafina domin na gani da idanuna
Yana gama fadar haka saiya zaro madubin tsafinsa
Ya shafeshi da hannunsa lafiyayyen take yaga lokacin da mutanen birnin sukayi gudun hijira zuwa wasu kasashen dake nahiyar wasuma barin nahiyar sukayi gaba daya yadda bazai iya binsu

Please Login or Register in order to submit comment