Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kamosu ba
Yana cikin binciken ne ya tuna cewa sarki abu saiman yana da da guda daya mai suna saiman kuma tunda aka fara wannan yakin ya nemeshi ya rasa
Domin kuwa da ace ya halarci wannan yaki dolene ya ganshi saboda shima matashi ne kuma jarumi uban sadaukai har an tabbatar da cewa yafi mahaifinsa jarumtaka
Koda yin wannan tunani sai ya juyar da akalar bincikensa kan yarima saiman
Amma saiyaga tsafin nasa yaki yayi tasiri domin koda ya matsa wajen yin binciken saiyaga madubin tsafin nasa yayi baki sidik harya fara kokarin yin bindiga ya fashe
Bisa dole ya tsayar da binciken nasa yace acikin zuciyarsa
Tabbas akwai boyayyen al'amari akan wannan yaro kuma tabbas idan ban gaggauta bincike akansa ba
Zai iya zamowa silar hana cikar burina
Haka dai ya cigaba da zancen zuciya har suka iso kofar gidan sarauta
Adaidai nan ne boka ulumanu ya dakata da tafiyar da yake yi sannan yace da harisul mar'uf
Yakai gwarzon jarumi
Anan ne zan dakata na jira ka kaje ka hallaka wannan maciyar wacce suke bauta mata
Ka bincika sosai kofar da zata sadaka da wannan macijiya tana cikin wannan gidan sarauta ni zan jiraka a awannan gurin
Koda jin haka sai harisul mar'uf yashige cikin wannan katon gidan sarautar
Hakika gidan sarautar birnin ramlatul saif ya cika kato
Domin idan ka ganshi kamar ba mutanene sukayi gininsa ba saboda tsananin girmansa shi kansa aljani harisul mar'uf saida ya zama dan karami yayinda ya shiga cikinsa
Haka dai ya dinga bincike sosai har saida ya isa wannan dakin bautar
Hakika dukda girman wannan gidan sarautar saiya zama kankani akan wannan dakin bautar
Daga can karshensa kuwa wata tsohuwar macijiya ce wacce masana suka tabbatar da cewa tafi shekaru dubu aduniya Domin tun kafin agina wannan birnin take
Sai bayan an ginashi ne mutanen zamanin suka maida ita abar bauta saboda ganin irin abubuwan al'ajabin da take yi
Koda ganin wannan macijiya sai harisul mar'uf ya bude fukafukansa ya tashi sama ya afka mata domin yayi mata kwaf daya
Koda ya rage baifi saura kamu ukuba atsakaninsa da ita
Sai kawai ta hura masa wata iska daga bakinta
Nantake kuwa yaji kamar an daure masa jikinsa da manyan sarkoki
Sannan tayi wulli dashi zuwa saman rufin dakin take yaje ya gwaru da ginin
Ya fado kasa sannan ya sake dawowa suka kachama da masifaffen yaki a wannan rana harisul mar'uf yaga tashin hankalin da bai taba ganiba arayuwarsa
Domin saida ya raina jarumkarsa
Yayi nadamar tunkarar wannan macijiya
Harsaida ta kai sun rushe wannan gidan sarautar gabaki dayansa
Da sauran gidajen da suke cikin birnin
Hatta kasashen da suke makwabtaka da birnin ramlatul saif saida suka shiga tashin hankali domin gaba daya nahiyar babu inda wannan tashin hankali bai shafaba
Aljani harisul mar'uf saida yayi nadamar karbar wannan kwangila ta kashe wannan maciyar a hannun ulumanu
Saida ya suma sau uku yana farfadowa
Karaya kuwa yayita sau goma ajikisa
Da kyar da sidin goshi ya iya hallaka wannan maciyar
Yana kasheta kuwa jini ya balle daga cikinta kamar an bude magudanar ruwa
Awannan lokacin ulumanu yana saman wani katon tsauni yana kallon fafatawar da sukeyi ta cikin madubin tsafinsa
Koda yaga harisul mar'uf ya hallaka wannan macijiya sai ya rusa ihun farinciki sannan ya tashi sama kamar tsuntsu ya diro a inda aka harisul mar'uf yake
Take ya nunashi da yatsansa wata iska ta shureshi tayi sama dashi
Sannan shima ya cika wata battarsa da jinin wannan macijiya
Ya tashi sama
Wannan iskar kuwa wacce ta dauki harisul mar'uf tana biye dashi abaya
Basu zarce ko ina ba sai kogon da mahaifiyar aljani harisul mar'uf take wato aljana zamira
Nantake boka ulumanu ya sauke harisul mar'uf akasa sannan ya gyara masa duk karayar da take jikinsa
Ita kuma nantake ya karya sihirin da akayi mata ya dawo da ita ainihin siffarta daga siffar da aka mayarda ita ta gunki
Bayan ta dawo ainihin siffarta sai shi kuma ya bace bat ya barsu su biyu kacal
A wannan lokaci harisul mar'uf da zamira sunyi matukar farincikin ganin junansu
Shi kuma ulumanu ya koma zuwa kogon tsafinsa ya ci gaba da shirin tsafinsa da wannan jinin
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A FILIN YAKI BAYAN SARKI ABU SAIMAN YA MUTU
SHI KUWA BOKA ULUMANU YA SAMI ABINDA YAKE NEMA A BIRNIN
++++++++++++++++++++++++++++++
+++++++++++
AL'amarin yarima saiman kuwa lokacin da suka kama hanyar tafiya birnin hamshak
Sai da suka shafe sa'a hudu suna tafi saida tsakar rana suka iso wani daji mai yalwar 'ya'yan itatuwa
Suna isowa daidai wannan daji sai yarima saiman ya dakata da tafiya ya juyo
Yace da mutanensa
Dukkan ku anan zamuyi bankwana daku kuci gaba da zaman jirana har naje na dawo domin daganan inda muke zuwa birnin hamshak tafiyar rabin sa'a ce
Sannan ya karasa bakin keken dokin suhaila sukayi bankwana akan cewa zata tsaya jiran dawowarsa
Amma sai yaga a wannan lokaci itace take karfafa masa guiwa akan zai sami nasara akan abinda zaiyi a cikin birnin
Daga baya kuma sai yaga hawaye ya zuba daga cikin idanunta
Ganin wannan hawayene ya tabbatar masa da cewa tabbas aikin gama ya riga ya gama
Ma'ana tayi bincike ta gano cewa anci birninsu da yaki
Mahaifinsa ya zama matacce
Take kwalla shima ta zubo masa
Nantake yaji ya kagu da yaje birnin hamshak ya dauko wannan kubar ta muftahul sihir
Sannan ya kawo karshen wannan bakar gabar da take tsakaninsa da boka ulumanu
Ana cikin hakane saiga aljani markazulu shima ya iso wannan sansanin
Nantake duk su biyun suka tashi sama cikin gajimare
Tabbas tsafi gaskiya ne agurin ma'abotansa
Sai gashi yarima saiman yana gudu a sararin samaniya bisa kafafunsa
Harma yana kokarin gifta aljani markazulu
Ba komai ne ya jawo hakaba face kaguwa da burin cika aikin da yake gabansa
Allah ya hadamu da alkairinsa ameen
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT TO ENTERTAIN YOU

DOMIN SAMUN CIGABAN WANNAN LITTAFI SAI KU KASANCE DA
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
BAKAR GABA
Kashi na shida 6
Littafin Habibullah muhammad kabara
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at hausaebooks.com.ng










BAKAR GABA
PART 25
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
yarima saiman kuwa lokacin da suka kama hanyar tafiya birnin hamshak
Sai da suka shafe sa'a hudu suna tafi saida tsakar rana suka iso wani daji mai yalwar 'ya'yan itatuwa
Suna isowa daidai wannan daji sai yarima saiman ya dakata da tafiya ya juyo
Yace da mutanensa
Dukkan ku anan zamuyi bankwana daku kuci gaba da zaman jirana har naje na dawo domin daganan inda muke zuwa birnin hamshak tafiyar rabin sa'a ce
Sannan ya karasa bakin keken dokin suhaila sukayi bankwana akan cewa zata tsaya jiran dawowarsa
Amma sai yaga a wannan lokaci itace take karfafa masa guiwa akan zai sami nasara akan abinda zaiyi a cikin birnin
Daga baya kuma sai yaga hawaye ya zuba daga cikin idanunta
Ganin wannan hawayene ya tabbatar masa da cewa tabbas aikin gama ya riga ya gama
Ma'ana tayi bincike ta gano cewa anci birninsu da yaki
Mahaifinsa ya zama matacce
Take kwalla shima ta zubo masa
Nantake yaji ya kagu da yaje birnin hamshak ya dauko wannan kubar ta muftahul sihir
Sannan ya kawo karshen wannan bakar gabar da take tsakaninsa da boka ulumanu
Ana cikin hakane saiga aljani markazulu shima ya iso wannan sansanin
Nantake duk su biyun suka tashi sama cikin gajimare
Tabbas tsafi gaskiya ne agurin ma'abotansa
Sai gashi yarima saiman yana gudu a sararin samaniya bisa kafafunsa
Harma yana kokarin gifta aljani markazulu
Ba komai ne ya jawo hakaba face kaguwa da burin cika aikin da yake gabansa
Domin birnin hamshak ba a doron kasa yake ba
Asararin samaniya akayi gininsa kuma a tsaye yake cak akan iska baya wani girgidi saboda karfin sihirin masarautar
Agaba daya duniya awannan zamanin babu masarauta mai karfin mulkin wannan birnjn da kuma karfin sihirinsa
Komai karfin sihirin mutum ko aljan idan ya shiga cikin wannan birni
Saiya hadu da wadanda suka fishi ko mai da yake takama dashi
Sannan ga yawan dakarun yaki da suke dashi wadanda su kadai zasu iya yakar duk kasashen duniya
Mata kuwa da kayan alatu babu kalar wadanda babu acikin birnjn
Domin su kansu gidajen da suke cikin birnin mafi yawansu anyi musu adone da zinare
Hakan ns zai tabbatar maka da cewa wannan birnin ya cika aljannar duniya
Domin komai sarautar mutum idan ya shigo birnin hamshak saiya zama kamar dan kauye
Saboda zaiga abubuwan da bai taba ganinsu ba arayuwarsa
Duk da tsananin kyau da kawar da wannan birni yake dashi duk sai ya zama abanza
Domin jama'ar kasar gaba daya
Basa kaunar garin saboda tsananin zaluncin sarkin garin wato sarki mafazil
Wanda ya kasance azzalumin gaske
Wanda baya tausayawa jama'ar kasar
Ko kadan wajen karbar haraji
Sannan komai kankantar kuskuren da aka aikata masa hukuncin kisa yake yankewa
Baya sassauci ko kadan tsakanin talaka dame kudi
Kuma duk irin wannan kyale kyale da yake cikin birnin ya zuba shine saboda ya tara dukiya mai yawan gaske
Saboda dole yayiwa jama'ar kasar cewa duk wanda yake da burin ci gaba da rayuwa dolene ya sayi wadannan kayan kawa ya saka a gidansa
Ko kanaso ko bakaso
Idan kuwa kaki hukuncin kisa ne akanka
Lokacinda su yarima saimsn tare da markazulu suka tashi sama suka nufi birnin hamshak
Sai suka yita tsala azababben gudu
Tamkar gudun tauraruwa mai wutsiya
Ahanksli suka dinga kusantar birnin tun suns hangoshi daga nesa har suka fara ganinsa akusa dasu
Nantake duk su biyun suka cika da tsananin mamaki
Domin ganin kofar birnin sukayi a bude babu mai gadi ko guda daya
Koda suka karaso bakin kofar birnin sai suka tsaya cak
Sannan yarima saiman ya dubi markazulu yace
Yakaj abokina hakika tunda kaga haka to sarki mafazil yasan da zuwanmu
Domin tabbas ruwa baya tsami banza
Akwai wani tuggun da suka shirya mana
Don haka dolene mu canja siffarmu yadda dakarun wannan birnin ba zasu gane mu ba
Yana gama fadin haka sai aljani markazulu ya rikide zuwa wata siffar daban
Sannan shima yarima saiman ya rikide ya koma zuws siffar da aljani markazulu sak
Idan ka gansu sai kayi zaton cewa hasan da usaini ne
Domin hatta girman jikinsu da fuka fukansu
Take suka shiga cikin birnin tamkar dama sun kasance haifaffun garin
Haka dai sukayita kutsawa cikin birnin su shiga nan sufita can
Kuma duk inda suka gifta sai suga kamar babu wanda yake kallonsu
Domin duk inda suka kutsa saidai suga kowa yana gudanar da harkokinsa na yau da kullum
Saida suka yini cur suna tafiya kuma babu inda suka nufa face gidan sarautar birnin
Domin dauko gatarin sihiri na miftahul sihir
Adaidai wannan lokacine suka iso wani gindin wata rijiya
Wacce abakinta wani yaro ya tsaya yana kokarin tura murfin rijiyar don ya debi ruwan da yake cikinta
Koda suka iso bakin wannan rijiya sai sukaji wannan yaro ya kallesu yace
Yaku wadannan baki ku taimaka mini na janye wannan murfi saboda girman iyayenku
Kodajin wannan magana sai duk su biyun suka cika da tsananin mamaki
Cikin matukar kaduwa suka kalleshi sukace
Yakai wannan saurayi shin tayaya akayi ka iya ganemu? Alhalin duk mu biyun mun rikida daga ainihin siffarmu?
Dajin wannan tambaya sai saurayin yayi murmushi sannan yace
Shin a tunaninku babu wanda yake kallonku acikin siffar ku ta ainihi
tundaga lokacin da kuka shigo wannan birnin?
To indai hakane to kusani kun yaudari kanku domin babu wanda baya kallonku
Kawai dai an zuba muku ido ne don aga iyakar gudun ruwanku
Da zarar kun shiga cikin gidan sarauta to shikenan kun shiga inda ba'a fitowa
Domin ko gawarku ba'a isa agani ba
Dajin wannan batu sai duk su biyun sukayi cirko cirko suna kallon juna
Daga can sai yarima saiman yace da markazulu
To indai hakane to wannan canja siffarmu da mukayi to bata da wani amfani don haka sai mu kara sauri har mu isa cikin gidan sarautar ayi abinda za'ayi
Yana gama fadin haka sai ya kara gaba markazulu na binsa a baya
Cikin 'yan dakiku suka iso gidan sarautar tun daga nesa suka sha jinin jikinsu
Domin sun tabbatar da cewa a wannan rana sun kawo kansu gidan mutuwa inda karfin damtsensu dana sihirinsu ba zaiyi tasiri ba
Domin dakaru suka gani na jinsin bakaken aljanu girda girda masu kirar halittun farko
Wadanda adadinsu yafi kwatancen mai kwatance
Sun kasu kashi uku
Kashi na farko suna tsatstsaye abakin kofar gidan sarautar ruke da miyagun makamai
Kashi na biyu kuma suna zaune ne akan katangar gidan sarautar
Kaso na uku kuma suna yawo ne akan iska sunyiwa katangar gidan sarautar kawanya ta yadda babu halittar data isa ta wuce face ta ratsa ta cikinsu
Koda ganin wadannan dakaru sai markazulu ya kalli yarima saiman yace
Yakai maigidana tabbas yau mun kawo kanmu zuwa ga hallaka domin bamu isa mu iya ketara wadannan dakrunba har mu shiga cikin gidan sarautar nan mu dauko kubar miftahul sihir ba
Koda jin haka sai yarima saiman ya daka masa tsawa yace
Saboda me zaka karyawa kanka gwuiwa akan abinda muka dade muna shiri akansa
Ina mai tabbatar maka da cewa koda zaka tafi ka barni ni ni kadai saina shiga cikin wannan masarauta na dauko abinda nazo nema don haka idan ba zaka iya ba sai kayi ta kanka domin nasan ko ka gudu ba zasu kyalekaba
Yana gama fadin haka sai ya sake rikidewa ya koma zuwa ainihin siffarsa
Sannan ya falfala da gudu ya tunkari wadannan dakaru
Take suma suka falfalo da gudu zuwa kansa nantake suka lullubeshi kamar wasu kudaje sunga kazanta
Suna masu kai masa sara da suka koda suka gama lullubeshi
Sai yayi kukan kura yana daga inda yake ya tarwatsasu da kaifin takobinsa
Markazulu da yake can gefe daya koda yaga abinda ya faru ga yarima saiman
Sai shima ya falfalo da gudu zuwa inda suke wannan fafatawa
Suka kachame da azababben yaki mai matukar munin gaske
Duk sanda makaman yakinsu suka hadu sai kaji wata irin kara ta tashi tareda tartsatsin wuta
Haka kuma duk inda su jarumi saiman suka durfafa saidai kaga dakaru suna zubewa kasa matattu kamar ana sassabe agona
Jini kuwa ya dinga fantsama a sararin sama kamar an bude idaniyar ruwa
Sassan jikin wadannan dakaru kuwa saita cika filin da ake wannan yaki
Duk sanda wadannan dakaru suka sari jikin jarumi saiman ko kuma aljani markazulu
Sai suji kamar sun sari karfe domin ko kwarzanewa jikinsu bayayi
saboda wannan tsumin na dodo garjaju wanda suka sha
Amma fa suna jin zafi da radadin bugun da aljanun sukeyi musu
Kuma duk da cewa suna samun nasara akan aljanun sai abin ya zama abanza
domin duk da cewa gashi dai suna kashe dakarun amma sai kara ciccidowa suke kamar daga sama ake zubo su
Koda aka jima ana wannan gumurzu sai su kayi tunanin tabbas idan aka jima ana wannan fafatawa zasu iya gajiya kuma da zarar sun gaji shikenan abokan gaba zasuyi nasara akansu
Koda yin wannan tunanin sai duk su biyun suka daka tsalle sama da nufin su haura katangar
Koda dirarsu akanta sai sukaji an dakesu da kafafu take duk su biyun suka rikito kasa
Sakamakon wannan wawan naushi da suka sha daga wajen dakarun da suke zaune akan katangar
Kafin aljanun su yi musu rubdugu sai suka mike tsaye zumbur kamar babu abinda ya samesu suka sake kachamewa da yakin kuma sunayine suna budawa kansu hanya ta karfi da yaji har suka isa bakin katangar
Take suka karayin wani tsallen akaro na biyu suka dira kan katangar
Cikin zafin nama suka saka takubbansu suka tsarge dakarun da suke gabansu
Suka budawa kansu hanya
Nanfa aka kasa azababben tseren gudu tsakanin su yarima saiman da wadannan dakaru
Alokacin dakarun suka dinga jefo musu masu da kuma kibiyoyi
Amma sai kaga suna kadesu da takubban dake hannunsu suna dada kutsawa gaba
Su kuma dakarun basu fasa binsu kamar dada karosu akeyi
Suna cikin wannan azababben gudu ne kwatsam sai suka yi arba da wani murgujejen aljani wanda ya ninka ragowar aljanun da suka baro abaya girma da kuma siffar karfi
Ku ina ajikinsa a murde yake kamar jikin tsohuwar bishiyar kuka
Kafin su ankara ya cafkesu duk su biyun ya daga su sama ya wulwulasu kamar yara sun sami 'yar tsana sannan ya wullasu sama take duk su biyun je sukayi sama kamar an wulla tsakuwoyi
Sannan suka rikito
Bisa sa'a sai rigar jarumi saiman ta makale ajikin wata azarar gini
Shi kuwa markazulu saiya fado kasa tim kafin yayi wani yunkuri
Wannan shirgegen aljanin yazo ya cafkeshi ya kama fuka fukansa guda biyu ya karya su
Take aljani markazulu ya kwarara uban ihu sannan ya fadi kasa sumamme
Koda ganin haka sai yarima saiman ya cire wannan rigar data makale ajikin ginin
Sannan ya kwarara ihu yana mai kusantar wannan aljanin
Da ganin haka sai aljanin ya bushe da dariya sannan yace
Lallai wannan yaro ka cika mai tsaurin ido yanzu kai da bakafi in talitseka ba
Kaine kake tunanin zaka iya tarata da yaki to gaskiya ka yaudari zuciyarka
Don haka ba'a sanin maci tuwo sai miya ta kare
Yana gama fadar haka sai ya kawowa yarima saiman mummunan sara
Wanda inbadon yayi gaggawar kaucewa ba da sunansa shekakke
Gurin kuwa da wannan takobi ta sauka saiya samar da wani wawakeken rami
A wannan lokacin da abun yake faruwa ne sarki mafazil ya iso daidai wannan guri don yaga abinda yake wakana
Koda yaga yarima saiman dan kankani kuma shi kadai saiya bushe da dariya
Sannan ya tsaya yana kallon wannan fafatawa domin yasan babu ta yarda za'ayi ya sami nasara akan sarkin yakinsa damasuru ba
Balle har ya zo su fafata dashi gaba da gaba
Nanfa aka sake ruguntsumewa da fada fiye da na farko
Sai a sannan ne ya gane cewa damasuru ba karamin sadauki bane
Wanda shi kadai ma daidai yakeda wata babbar rundunar
Ko mai da yarima saiman yake dashi saiyaga wannan aljanin ya ninkashi sau dari
Domin bama ya isa kare hare haren da yake kawo masa
Kuma har ya hadamasa jini da majina babu kyan gani
Idanunsa sun fara gani dashi dishi
Ba zato babu tsammani sai akaji wata irin guguwa mai karfin gaske tana kadawa a saman fadar tamkar zata yaye rufin fadar
Nantake kowa ya daga kansa sama don ganin abinda yake faruwa
Koda suka ga abinda yake saukowa sai kowa ya kame kyam
Ba komai suka gani ba face tsohon sarkin yakin birnin kuma babban masoyin sarkin garin wato mahaifin sarki mafazil
Shine sadauki ramzas mahaifin aljani harisul mar'uf kuma yaba dauke da gimbiya suhaila agadon bayansa
Shi kansa sarki mafazil saidaya razana sakamakon yin arba da sadauki ramzas
Yadora hannunsa akan kufen takobinsa kamar ya zareta ya afka masa amma saiya dake
A hankali aljani ramzas ya sauka kasa sannan ya ajiye gimbiya suhaila agefe daya
Ya juyo ya fuskanci sarkin yaki damasuru yana mai yi masa nuni da ya afko masa
Nantake kuwa damasuru ya kawo masa mahaukacin sara da nufin ya tsargeshi biyu
Cikin zafin nama ya kaucewa saran sannan yasa takobi ya yanka wuyan aljani damasuru
Koda ganin abinda ya faru ga damasuru sai hankalin kowa ya tashi sannan suka shiga taitayinsu
Cikin takama aljani ramzas ya kalli aljani mafazil yace
Yakai abokin gabata kuma daga babban masoyina marugayi sarki darkusma
Ka sani cewa yau itace ranar da zaka girbi sakamakon bakin zaluncin da kake aikatawa tsawon shekaru
Kuma kamar yadda mahaifinka ya fada maka cewa dana harisul mar'uf ne zai ci gaba da mulkin wannan birni to tabbas haka za'ayi
Domin yau nazo ne da shirin tsira ki halaka bana tsoron mutuwa
Idan kaima ka shirya saika taho yana gama fadar haka sai ya falfalo zuwa kan sarki mafazil
Suka kachame da masifaffen yaki wanda yafi wanda sukayi abaya muni
Wohoho
Hakika fadan manyan dawa bashida dadin kallo domin ana fara wannan yaki hankalin duk wanda yake cikin fadar ya tashi
Saboda wani irin tartsatsin wuta daya dinga tashi asanadiyar fadansu
duk wanda yakaiwa wani hari bai sameshiba to duk abinda ya samu take suke raba shi biyu komai girmansa da kwarinsa
Hakika tashin hankali ba abin so bane domin a wannan lokaci saisu yarima saiman da kuma ragowar dakarun birnin suka zama 'yan kallo suka kame kyam kamar gumaka
Shikuwa aljani markazulu da yake cikin halin suma karar haduwar makamansu ce ta sa ya farka
Amma saiya manta da karayar da take jikinsa shima yabisu da kallo
Tabbas wadannan aljanu guda biyu sun cika sadaukan gaske kuma fasa taro
Cikin lokaci kankani suka hargitsa fadar ragowar dakarun da suke ciki suka fara hallaka
Sakamakon dirkar ginin data fara fado musu
Ba shiri suma suka fara gudun ceton ransu
Koda aka jima ana wannan fafatawa sai duk suka hadawa junansu jini
Domin sarki mafazil ya sami nasarar saran aljan mafazil a damtsensa na hannun hagu
Amma kafin ya ankara shima ya rama yasare shi atsakiyar gadon bayansa
Kuma ciwon yayi zurfi sosai har saida ya kwallara ihu saboda zafi da radadin da yaji
Adaidai wannan lokacine suka fara jiyo ihun wasu dakarun daga wajen fadar
Cikin sauri aljani ramzas da sarki mafazil suka juya domin suga abinda yake Faruwa
Take sukaga aljani harisul mar'uf yana ragargazar dakarun da suke tsaron kofar gidan sarautar yana shigowa da karfin tsiya
Mahaifiyarsa tana binsa abaya Kafin wasu 'yan dakiku ya gama tarwatsasu ya iso inda ake wannan fafatawar
Take ya bude bakinsa yace
Yakai abbana ka yau nine danka harisul mar'uf kuma ina tareda mahaifiyata zumaira
Kodajin haka saiyaji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinsa
Take ya fara kaiwa sarki mafazil mahaukatan hare hare tun yana iya kare kansa har ya kasa
Nan danan yayi masa jina jina yadda ko dan ya tsansa bazai iya dagawa ba
Sannan ya juyo ya kalli gimbiya suhaila yace
Ke kuma sai kizo ki dauki fansar ran iyayenki akan wannan azzalumin
Koda jin haka sai ta taho fuskarta cike kwalla a lokacin data tuna da mahaifanta na asali
Take ta karbi takobin hannun yarima saiman ta falfala da gudu
Sannan ta daka tsalle sama ta caka masa takobin a tsakiyar kahon zuciyarsa
Take ya kwallara mahaukatan ihu take ya kama da wuta ya kone kurmus saboda karfin sihirin jikinta
Nantake suka garzaya inda aljani markazulu yake tsaye suka kama karayarsa aka gyara masa ita
Sannan suka shiga cikin gidan sarautar aka dauko kubar miftahul sihir
A wannan rana aljani ramzas dasu harisul mar'uf sunyi kukan farin cikin sake haduwa da junansu
Bayan an kwana biyu kuma aka dora aljani harisul mar'uf amatsayin sabon sarki a birnin hamshak
Shi kuma mahaifinsa ya koma kan mukaminsa na baya wato sarkin yakin birnin
Sannan su yarima saiman suka kama hanya dauke da miftahul sihir
Suka bar cikin birnin suka koma can sansaninsu
Daga nan suka tafi can kogon tsafin boka awaisul masawi wato kogon darul sihir
Saida suka shafe kwanki goma suna tafiya kuma basu hadu da wani abu mai cutarwa ba sannan suka iso bakin wannan kogo
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT TO ENTERTAIN YOU BAKAR GABA
PART 26
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Sannan su yarima saiman suka kama hanya dauke da miftahul sihir
Suka bar cikin birnin suka koma can sansaninsu
Daga nan
suka tafi can kogon tsafin boka awaisul masawi wato kogon darul sihir
Saida suka shafe kwanki goma suna tafiya kuma basu hadu
da wani abu mai cutarwa ba sannan suka iso bakin wannan kogo
Shidai wannan kogon yakasance babbane kuma yakai girman gari guda
Domin tsaunine guda aljanu suka fafake cikinsa ya zama tamkar
gari bisa umarnin shugabansu boka ulumanu
Kuma ajikin wannan kogo babu wata kofa da zaka gani ka iya bude shi
Amma koda suka iso wannan wuri sai jikin dutsen ya fara
tsagewa take sukaga wata irin katuwar kofa ta bayyana
wacce take da girma sosai kuma an sana'antatane da zallan bakin karfe
Take yarima saiman ya umarci wasu dakaru guda hudu wadanda
suke dauke da kubar miftahul sihir da suzo su zirata a mazauninta
Cikin sauri dakarun suka taho dama ba akan dawakai sukeba
Sannan suka zira kubar ajikin kofar take suka koma baya suka tsaya
Sai gani sukayi kubar ta fara juya kanta wata irin kara ta
dinga tashi tana cika dodon kunne Bayan 'yan dakiku sai kofar ta bude kanta
Nanfa suka cika da tsananin mamaki domin ganin yadda
wannan kogo aka kawata cikinsa tamkar wata babbar masarauta
Kuma acikinsa sai sukaga gida gida acikinsa kamar yadda tsarin cikin gari yake
Nanfa dukkansu suka kame kyam kamar gumaka ana jiran aji mai yarima saiman zai fada
Daga can sai suka ga ya bushe da dariya cikin farin ciki
Sannan yace
Yaku 'yan uwana tabbas yau na sami kwanciyar hankali sakamakon ganin na cikawa mahaifina burinsa
Na kawo ku kogon tsira wato darul sihir inda zaku ci gaba da rayuwa
Sannan mu koma daga baya zuwa can birnin mu don mu sake rayashi
Yana gama fadin haka sai ya kutsa kansa cikin kogon dutsen
Sauran mutane suna biye dashi
Hakika a wannan ranar sunyi matukar farin ciki mara misaltuwa
Kuma ana cikin wannan halin farin cikin ne sukaga gimbiya
suhaila ta fadi kasa alokacin da cikinta yake murdawa yanayi mata ciwo
Nantake hankalin kowa ya tashi kuma murna ta koma ciki
Shi kuwa yarima saiman hankalinsa yafi tashi akan na kowa
domin ganin irin halin da matarsa ta shiga
Cikin gaggawa wasu kuyangi suka zo suka dauketa suka shige da ita cikin wani gida
Dake cikin kogon suka fara kokarin karbar nakudarta
Ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai akaga kogon dutsen
ya fara amsa kuwwa tamkar zai tsage
Komai na cikinsa ya fara girgiza kamar zai fado kasa
Wani irin haske ya mamaye kogon tare da wata irin kara wacce ta cika kogon
Sannu a hankali komai ya fara lafawa kuma adaidai lokacin ne gimbiya suhaila ta haifi wani kyakykyawan jariri
Kuma mai kirar mazaje domin har a sanda aka haifeshi
Hannuwansa a rufe suke kuma yana da matukar kwarjini da siffar jaruman gaske
Kuma ana haifar tasa sukaga wani irin haske ya fito daga
can wani sako na kogon dutsen ya shiga cikin kirjin jaririn
Koda kuyangi sukayi arba da wannan jariri sai duk suka ruga
da gudu suka bar cikin

Please Login or Register in order to submit comment