Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga musu kafane zuwa ranar sakamako alokacin da kowa zai mutu sannan ya kara tashin kowa zuwa gareshi yayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata ba sabonsa
Sunana kuma shine bahjaht bintu usman na fito ne daga can wata nahiyar daban
Dukda cewa ban kasance jaruma ba kuma bana tsafi
Kuma nazo wannan nahiyar taku domin yada wannan addini nawa na musulunci
Tunda na baro gida ubangiji na ne yadinga bani kariya akan duk abubuwan sharrin da suke kan hanyata har nazo na birninku
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT TO ENTERTAIN YOU BAKAR GABA
PART 28
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Kodajin wannan tambaya sai wannan budurwa tace da farko dai kamar yadda ka tambayeni game da addini na
Shidai addini na shine addinin musulunci wanda ake bautar ubangiji guda daya
Wanda bai haifaba kuma ba'a haifeshi ba
Shine wanda ya halicci sammai da kassai da kuma abubuwan da suke cikinsu
Kuma ya haliccesu ne domin su bauta masa amma sai wasu daga cikin mutane da aljanu suka bijire masa suke bautar wasu abubuwa sabaninsa
Kuma yana sane da hakan kawai yana daga musu kafane zuwa ranar sakamako alokacin da kowa zai mutu sannan ya kara tashin kowa zuwa gareshi yayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata ba sabonsa
Sunana kuma shine bahjaht bintu usman na fito ne daga can wata nahiyar daban
Dukda cewa ban kasance jaruma ba kuma bana tsafi
Kuma nazo wannan nahiyar taku domin yada wannan addini nawa na musulunci
Tunda na baro gida ubangiji na ne yadinga bani kariya akan duk abubuwan sharrin da suke kan hanyata har nazo na nahiyarku
Koda suka gama jin abinda ta fara sai duk sukaji jikinsu yayi sanyi sakamakon wannan jawabi
Nata
Har saida yarima saiman yaji wannan yarinyar ta burgeshi
Yadda ta iya fitowa ta saida rayuwarta domin yada wannan addini nata
Shikuwa jarumi basdar kasa yin hakuri yayi don haka saiya sake tambayarta yace
Shin yanzu kina nufin cewa ubangijinki yanayin duk abinda aka rokeshi?
Dajin wannan tambayar sai bahjaht tayi murmushi sannan tace
Ko shakka babu inda ace dukkannin halittu na farko dana karshe zasu hadu a guri guda su rokeshi wata bukata kuma ya biyawa kowanne abinda ya rokeshi
Babu abinda zai ragu acikin daukakarsa saidai misalin abinda allura take tawayarwa idan aka sakata acikin teku
Ku kuwa da hankalinku kunsan cewa allura bata isa ta ragi yawan ruwan teku da komai ba
Dajin wannan bayani sai sadauki basdar yaji zuciyarsa ya buga da karfi
Sakamakon jin yadda take da fasahar zance kuma wannan zancen da takeyi maganace wacce tafi karfin tunanin bil'adama
Kai koda ababen bautarsu bai taba jin sunayin irin wannan furuci ba
Gimbiya suhaila kuwa saita girgiza kanta acikin zuciyarta tace lalle wannan addini abin bincikawa ne
Don haka sai ta yafito su yarima saiman da hannu suka kebance a gefe daya
Sannan ta dubesu tace dukkanku idan kukayi la'akari da wannan budurwa
Zaku fahimci cewa addininta addini ne wanda yake da barazan akan addinin tsafi
Ina mai tabbatar muku da cewa idan muka karbi wannan addini to babu shakka sai mun denayin addinin da muka gada agurin iyayen mu
Sannan kuma zai hanamu aiwatar da tsafin da mukeyi kuma muke rayuwa acikinsa
Kodajin haka sai jarumi basdar ya dubi mahaifiyarsa yace
Yake ummina tabbas akwai abin dubawa dan gane da wannan addini
Yakamata mu jarraba ta idan mukaga gaskiyar addininta sai mu karba
Domin kodaga bayanin da muka saurara yanzu daga gareta ya kamata musan cewa
Addini guda dayane tak
Ragowar addinan kuwa duk na karyane
To abin tambaya anan shine wanne addini ne na gaskiya acikin addinan da muke dasu?
Kuma idan har macijiyar da kuke bautawa acan birninku itace ubangijin gaskiya
To meyasa aljani harisul mar'uf ya sami nasara akanta?
Koda ya gama fadin haka sai yarima saiman ya kalleshi sannan yace
Tabbas kaima kazo da magana mai girma kuma na fuskanci kai yarone mai kaifin kwakwalwa amma ina mai gargadinka da kada ka nunawa wannan budurwa cewa mun gamsu da addininta sai tayi abin al'ajabin da zai nuna girman ubangijin ta
Yana gama fadar haka sai ya umarcesu dasu tashi su ci gaba da tafiya
Nantake kuwa suka hada kayayyakinsu suka kama hanya da nufin subar budurwar a wannan gurin
Kawai sai sukaji budurwar tace
Idan har baku gamsu da bayanin da nayi mukuba to inaso
Ku tafi dani zuwa can fadar boka ulumanu anan ne zaku gasgata maganata
Koda sukaji abindata fada sai duk jikinsu yayi sanyi suka juyo suka ce taya akai kikasan inda muka dosa?
kodajin haka saitace
Ai wannan ba wani abu bane agurin ubangiji na. Alokacin da kuke wannan tattaunawane ya sanar dani duk wani abu daya faru daku
Kai hardama abinda zai faru acan fadar tasa saboda haka nake rokonku daku yarda mu tafi tare
Ba tareda gardamar komai ba suka amince
Sannan suka dunguma gaba daya aka nufi fadar boka ulumanu
Saida suka kwana biyu suna tafiya akan dawakansu
Kuma awannan lokaci koda yaushe idan ta juyo sai taga jarumi basdar yana satar kallon ta
Don haka sai ta dauko wani farin kyalle ta rufe fuskarta dashi
Akwana na ukun ne suka iso fadar boka ulumanu tun daga nesa suka fara hango dakaru na bakaken aljanu masu matukar
Kwarjini ruke da makaman yaki
Koda ganin haka sai jarumi ya umarci mutanensu dasu zauna anan su jirashi
Nantake kuwa suka cika umarni ya zamana dagashi sai yarima saiman da kuma mahaifiyarsa ne suka doshi wadannan aljanu
Take suka ruga da gudu sukayi cikin aljanun suka ruguntsume da azababben yaki
Duk inda suka sa gabansu saidai kaga dakarun aljanun suna zubewa kasa matattu
Kafin cikar dakika goma sun gama hallaka dakarun aljanun
Sannan kuma suka ratsa ginin fadar suka shiga cikinta
Suna shiga sukayi arba da boka ulumanu cikin gagarumar shigar yaki fiye da ta farko
Jikinsa cike yakeda gurayen tsafi
Koda yaga sun shigo cikin fadar tasa saiya kyalkyale da dariya
Sannan yace
Lallai kun yaudari kanku tunda har kuma shigo cikin fadata
Kadafa ku manta kowa acikin gidansa sarki ne gaba dayanku babu wanda zai tsira da rayuwarsa
Koda jin haka sai yarima saiman yace
Ai inda babu kasa anan ake gardamar kokawa yanzu saika fara takan dana sannan ka dawo kanmu
Suna gama fadin haka sai suka ja da baya suka tsaya suna kallon abinda zai faru
Nantake boka ulumanu da jarumi basdar suka ruguntsume da azababben yaki fiye da wanda sukayi a farko
Hakika idan tsohon jini ya hadu da sabon jini dolene abin ya baka sha'awa domin kowa yana fadanne da dukkan karfinsa
Duk da cewa makamansu sihirtattune saida ya zamana sun dakushe gaba daya babu sauran kaifi ko kuma tsini
Fadar kuwa ta dinga girgiza gininta ya dinga zabtarowa kasa
Amma saboda tsananin naci irin nasu sunki su hakura da yakar junadin da sukeyi
Saboda haka sai suka zubar da makaman nasu suka fara amfani da karfin sihirin su
Wajen yakar juna koda suka fara amfani dashi din
Sai komai ya kara tsamari domin fadarce gaba daya ya fara girgiza
Cikin 'yan dakiku kadan ta fashe sannan ya kama da wuta
Amma wani abin mamaki shine ko kadan wutar taki ta kama jikin boka ulumanu da jarumi basdar
Su kuwa yarima saiman da gimbiya suhaila saida suka fice daga cikin fadar domin ceton rayukansu
Kai saida takai cewa ma karfin sihirin nasu ma ya daina tasiri
Saidai da karfin damtsen su suka koma amfani
Nanfa fada yasha banban domin sai asannan ne boka ulumanu ya fara gane kurensa
Saboda yadda jarumi basdar ya dinga dagashi yana bugawa da kasa
Kamar kayan wanki nan da nan kuwa ya hada masa jini da majina tun yana iya mai da martani harya zamana baya iyawa saidai kokarin kare kansa
Ana cikin wannan yanayi jarumi basdar ya shaki boka ulumanu da hannu daya
Ya dagashi sama kafafunsa na yawo asaman iska
Alokacin da idanunsa suka kumburo sukayi jajur saboda tsananin wahala
Yace masa 'yanzu ina sihirin da kake takama dashi kuma ina karfin damtsen naka
A yanzu ba zasu iya cetonka ba daga mutuwa ba
Yana cikin wannan maganar ba zato ba tsammani sai boka ulumanu ya
Shammaceshi ya zaro wata wukar kashi mai matukar dadin haske ya chaka masa ita acikin wuyansa
Take wukar ta fasa wuyan nasa jini yayi feshi
Saboda zafi da zugin da yaji baisan sanda ya saki wuyan boka ulumanu ba
Ahankali boka ulumanu ya mike tsaye sannan ya kyalkyale da dariya sannan yace
Ai dama na fada maka nine zansami nasara akanku
Matsalar zuriyarku itace kurari da cika baki
Amma ni kuma nasara ce abar da nake takama da ita
Ina mai tabbatar maka da cewa
Koda ace ka sami nasara akaina babu abinda zai hanaka mutuwa
Sakamakon dafin da yake jikin wannan sihirtacciyar wukar tawa.………
Kafin ya gama maganar da yakeyi tuni jarumi basdar ya dako tsalle daga inda yake
Ya cafi wuyan boka ulumanu da hannuwansa bayu ya murde
Ji kake wata kara tana tashi kararas
Kawai sai ya saki gawar boka ulumanu ta fadi kasa
Sannan shima ya fadi kasa sumamme
Acan wajen fadar kuwa koda suka ga an shafe sa'a guda jarumi basdar bai fito ba
Sai hankalin kowa ya tashi musamman ma iyayensa
Suka fara tunanin wannan abu da yake faruwa da alama babu lafiya
Kuma gashi fadar tana faman ci da wuta aka rasa wanda zai iya shiga
Domin hatta su yarima saiman sihirin tsafinsu yaki yayi tasiri
Kawai sai gani sukayi bahjaht ta falfalo da gudu daga cikin ayarinsu
Ta danna kanta cikin wannan wutar kuma ba tareda wutar ta cutar da ita ba
Cikin kankanin lokaci sai gata ta fito da jarumi basdar
Akan kafadunta cikin wani mummunan hali mai kama da suma ko mutuwa
Take tazo ta jiye musu shi a gabansu
Ba shiri likitoci suka fara kokarin yi masa magani domin a shawo kansa
Saida suka yini sunayi masa magani amma babu alamun nasara
Daga can sai suka dago suka dubi yarima saiman suka ce
Ya shugabanmu saidai kayi hakuri domin dafin da yake jikin wannan sihirtacciyar wukar kashi
Babu wani magani da zai iya karyashi duk duniya kuma duk wanda aka samasa wannan dafin baya wuce kwana daya araye
Kodajin haka sai hankalin kowa agurin ya tashi suka fara zubar da hawaye domin sun saddakar da cewa mutuwa zaiyi
Koda bahjaht ta kula da yanayinda suke ciki saita dubesu gaba daya tace
Nayi rantsuwa da ubangijin musulunci duk duniya babu wanda ya isa ya warkar da jarumi basdar daga wannan ciwo face ubangijin musulunci
Idan har zaku bada gaskiya dashi to yanzu take zanyi addu'a akan ya bashi lafiya
Kodajin abindata fada sai hankalin kowa ya dawo kanta suka kura mata ido
Sannan yarima saiman yace daita kin tabbata ubangijinki zai bashi lafiya?
To tabbas idan dai har hakan ta faru nayi alkawarin zamu karbi wannan addini naki
Kodajin haka sai bahjaht tayi murmushi sannan ya karasa gaban basdar ta karanta wata addu'a ta tofa masa akan raunin nasa
Faruwar hakan keda wuya sai suka ga wani bakin jini ya fito daga cikin raunin nasa sannan ahankali wajen ya hade kamar babu abindaya sameshi
Nantake kowa ya cika da mamakin gaske
Kuma asannan ne basdar ya farfado daga suman da yayi
Koda ya farka yaga bahjaht agabansa sai kawai yakai hannunsa ya taba kurmin wuyansa ko zaiji wannan raunin
Kawai sai yaji gurin ya hade babu alamun ciwo a gurin
Nantake ya daga muryar sa da dukkan karfinsa yace
Yaku 'yan uwana daga yau inaso ku shaida cewa nima na bada gaskiya da ubangijin musulunci
Kafin ya gama rufe bakinsa sai gaba daya jama'ar suma sukace
Muma mun bada gaskiya da ubangijin musulunci
Take farinciki ya tunuke bahjaht
Ba shiri ta biya musu kalmar shahada suka maimaita suma
Sannan ta ce dasu yaku wadannan mutane hakika yanzu kun zama 'yan uwana
Kuma ku sani wannan addini yanada ka'idoji kuma shine addinin dayake damar da zaman lafiya ga kowanne mutum
Acikin addinin musulunci babu banbanci tsakanin talaka da mai kudi da kuma masu mulki
Sannan kuma tsafi ma haramun ne a addinin musulunci
Nandai suka dunguma gaba daya suka tafi can birnin ramlatul saif alokacin da gaba daya ya gama rushewa akasa
Babu sauran wani gini wanda bai fadi ba
Da suka iso wannan birni sunyi kukan bakin ciki sosai
Kuma asannan ne suka fara aikin gina wani sabon birnin sannan kuma bahjaht tana koya musu yadda ake bautar ubangiji
Awannan lokaci soyayya mai karfi ta shiga tsakanin bahjaht da basdar amma kuma babu wanda ya taba fadawa wani da baki saidai su dinga nuna alama
Bayan sun gama gina birnin ne yarima saiman ya hau kan kujerar mulkin mahaifinsa
Ana cikin shagalin bikin sarautar ne atsakiyar fada kawai sai akaji
Jarumi basdar ya mike tsaye yace
Ni bazan taba bari wannan damar ta wuce ni ba
Domin ayanzu ne ya kamata na bayyana soyayya ta ga budurwar data sace mini zuciyata
Yake bahjaht ina mai neman alfarmarki daki taimaka ki karbi soyayya ta
Yana cikin wannan maganar ne sarki saiman ya taso daga kan karagarsa ta mulki
A fusace yazo ya kwada masa mari yace
Bai kamata ka bayyana wannan soyayya acikin bainar jama'a ba
Alhalin baka da tabbas akan cewa tanasonka
ko kanasone kunyar jama'a tasa ta karbi soyayyarka
Kodajin abinda sarki saiman ya fada sai bahjaht ta sauko daga kan kujerar da take zaune
Ta taho inda suke fuskarta cike da murmushi tace
Tabbas nima tun daga sanda na fara ganjnka zuciyata ta kamu da soyayyarka
Saboda haka zanfiso adaura aurenmu a awannan rana domin ta zama abar tunawa
Awannan ranaaka daura auren bahjaht da basdar kuma birnin ramlatul saif yaci gaba da wanzuwa har zuwa yau
ALHAMDULILLAH ANAN AKA KAWO KARSHEN WANNAN LABARI MAI SUNA BAKAR GABA
JINJINA AGAREKU
SAYYADI LAWAL SOJA
ABUBAKAR ABUN HAJIYA
PRINCE RAYYAN
GWASKA
Abdullah yakub faru
MARYAM IBRAHIM
HAFSAT MUHAMMAD UMAR
STAR BOY UMAR
IBRAHIM MIJIN YAWA
SULAIMAN ZIDANE KD
Jamilu abdurrazak ma'abocin hikima dandume
DADAI SAURANSU
SAI MUN HADU A WANI SABON LITTAFIN MAI SUNA MAMAYAR BAZATO

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment