Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dudduba wannan daji ko zamu sami inda zamu sameshi
koda suka ji jawabin markazulu sai hankalin gaba daya mutanen ya kara tashi fiye da ko yaushe
wasu ma har kuka suka dinga yi domin su aganinsu yarima saiman ya zama gawa
koda jarumi zamnal yaga halinda suka shiga sai ya daka musu tsawa yace
wai waya fada muku cewa shugaba ya mutu?
ku sani koda ma ace zai mutu dolene saidai ahannunmu
don haka kowannenmu tare dashi za'ayi wannan tafiya
don haka zamu kasu ne zuwa kaso biyu
kaso daya zasu tsaya ne akarkashin kulawar aljani markazulu
kaso na biyu kuwa suna karkashin kulawata ne
inaso mu dudduba gefen wannan tsauni ko'ina da ina hatta cikin ciyayi sai mun duba
dukda nasan markazulu ya bincika daya bangaren na wannan tsauni to mu sai mu duba wannan bangare
domin mu ya kamata mu zage damtse wajen nemansa
tunda duk irin halin da ya shiga ya shiga ne domin kubutar da rayuwarmu
zamnal yana gama wannan jawabi sai ya raba dakarunsa biyu, mutanen gari ma haka wasu sukayi bangaren hannun hagu na tsaunin
wasu kuma sukayi bangaren hannun damansa
haka sukayi ta tafiya suna duba cikin ciyayin dake cikin dajin
idan sukazo wajen koramu kuwa sai su tsaya su shiga ciki
suyi nutso akarkashin ta har sai sun tabbata baya ciki sannan zasu fito
hakama idan sukazo kwazazzaban duwatsu ko cikin koguna sai sun bincika cikinsa
saida suka shafe yini guda suna yawon neman yarima saiman amma sama da kasa suka kasa ganinsa
bisa dole suka dawo izuwa inda suka rabu jikinsu asanyaye aka rasa me cewa uffan, wasu ma kuka suka kamayi domin sun tabbata yarima saiman ya zama gawa
da ganin haka sai zamnal ya daka musu tsawa yace
yarima yana raye ina da tabbacin cewa bai mutuba
domin aljani markazulu ya duba mana kan wannan tsauni yace baiga gawarsa ba
sannan muma da kanmu mun duba wannan bangaren na tsaunin nan bamu sami gawarsa ba
don haka dolene ya kasance rayayye domin inda ya mutu da mun sami gawarsa
sai dai ina da tabbacin cewa yana cikin mawuyacin hali yanzu haka
babban bakin ciki na shine rashin sanin tsayayyen gurin da yake
balle muje mu kai masa dauki, amma ina da tabbacin cewa indai
ahalin yanzu yana raye to dolene ya tsira da rayuwarsa ya dawo garemu
don haka ya zama dole agaremu mu tsaya adaidai wannan wuri mu jirayi dawowarsa koda kuwa zai kai shekara guda bai dawoba don nasan idai yana raye dolene ya dawo garemu domin rayuwarsa da kuma burinsa suna nan
babbar matsalarmu ayanzu itace gimbiya suhaila
idan ta farka daga barcin da takeyi me zamuce mata dangane da lafitar mujinta?
dajin wannan tambaya sai markazulu yace ai ba zata taba farkawa ba daga wannan barcin da takeyi ba
harsai dai idan nine na tasheta domin yanzu kula da rayuwarta data abinda ke cikin cikinta duk suna hannuna
ni na gama nawa kai kuma mai karatu mai kake
ganin zai sami yarima saiman?
sai na jiku
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME ART 13
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
To yau rahoton dana samo akansu yarima saiman shine
al'amarin yarima saiman kuwa lokacin da santsi
ya kwasheshi ya fadi kasa sumamme akan wannan tsauni
sai ya dinga gangarawa izuwa kasansa yana
buguwa da jikin duwatsu hakan ya haddasa
masa manyan ciwuka ajikinsa har sai da takai
hannunsa na hagu ya karye yana cikin wannan
haline kawai ya gangaro izuwa kan wani katon
dutse wanda da zarar ya fado kan dutsen take kansa zai dagargaje
adaidai wannan lokacine kwatsam sai wani
katon tsuntsun ya taho daga sama ya sure shi yayi sama dashi
nantake ya luluka izuwa cikin sararin samaniya
cikin azababben gudu tamkar kiftawar tauraruwa mai wutsiya
cikin kankanin lokaci tsuntsun ya bace bat
tamkar bai taba wanzuwa ba sai da tsuntsun
ya shafe 'yan dakiku yana tafiya sannan ya iso kan wani katon tsuburi
yana zuwa bakin sai tsuburin ya dare gida biyu
ya samar da wata katuwar hanya nantake tsuntsun
ya shige cikin tsaunin sannan kofar ta mai da kanta ta rufe
sannan tsuntsun ya rikide ya koma siffar wani katon aljani tsoho tukuf
cikin sauri wannan aljanin ya fara gyarawa yarima saiman karayar dake jikin hannunsa
tareda kuma saka masa magunguna akan raunikan da yaji ajikinsa
bayan ya gama gyara masa jikin nasa sai ya samo
ruwa ya yayyafa masa faruwar hakan keda
wuya sai yarima saiman ya farfado daga doguwar sumar da yayi
yana farkawa sai ya tashi zaune firgigit da nufin ya mike tsaye
cikin sauri wannan aljani yasa hannuwansa guda biyu ya dafa yarima saiman yace
haba yakai wannan sadaukin zamani kuma
gwarzon karnin da muke ciki kayi hakuri ka zauna
mana domin mu tattauna wadansu muhimman
maganganu tsakanin ni da kai
koda jin haka sai saiman ya dubi aljanin afusace yace
mai zan zauna nayi anan kana ganin halin da mutanena suke ciki akasan
wannan tsaunin
koda jin haka sai wannan aljanin yayi murmushi
saboda ya fuskanci cewa yarima saiman baisan
inda yakeba ahalin yanzu kuma baisan cewa
ya sami raunika ba tareda karaya ajikinsa sai ya sake cewa
yakai wannan jarumin dan sarki ai yanzu haka komai ya riga ya wuce
dajin haka sai ya kalli aljanin afusace yace
mekake nufi da wannan maganar taka?
ba tareda aljanin yace uffan ba sai ya nuna
jikin bangon dutsen da hannunsa nan take
sai hoton duk abinda ya faru ga gareshi ya bayyana
tun daga lokacin da santsi ya kwasheshi har
zuwa sanda aljanin yaje asiffar tsuntsu ya daukoshi
da kuma abinda ya faru tsakanin dakarun yarima saiman
da wadannan manyan zakuna ya bayyana har
zuwa sanda aljani markazulu yaje ya taimaka
musu ya kashe wadannan sihirtattun zakunan
da kuma wahalar da suka sha ta yawon nemansa
koda gama ganin wannan al'amari sai nantake
yarima saiman yaji duk jikinsa ya hau ciwo
sai sannan ya lura da cewa akwai ciwuka ajikinsa
koda ya kalli hannunsa na hagu sai yaga ashe
ya sami karayane harma an gyara masa ita sannan
an saka masa magunguna ajikin dukkan ciwukan nasa
da ganin wannan abu yarima saiman baisan
lokacin da hawaye ya zubo masa ba cikin sauri
wannan aljani yasa hannuwansa ya share masa hawayen nasa
sannan yace haba yakai jarumin jarumai hawaye
bai dace da irin ku ba kadafa ka manta ayanzu
kaine shugaban dukkan wani sadauki na wannan zamani
ina mai tabbatar maka da cewa ayanzu duk
hatsabibanci jarumi, sarki, ko kuma matsafi
dolene yayi shakkar tunkarar ka domin ana cewa
mai laya ya kiyayi mai zamani to yanzu zamanin
nakane kai kadai sai yadda kaso zakayi
inaso
ka sani ba don naje na taimakekaba a lokacin
da kake gamgarowa ba daga kan wannan tsaunin ba
da tuni ka dade da shekawa barzahu kuma
dolene ka zauna anan kayi jinyar jikinka koda ta sati biyuce
domin ka sami kwarin jikin da zaka iya tunkarar
fadar sarkin aljani na birnin hamshak
dajin
haka sai saiman ya kwallara uban ihu saboda
tsananin bakin ciki sannan ya kalli wannan aljani yace
yakai wannan aljani ina godiya bisa taimakon da kayi mini
sannan inaso insan wanene kai da kuma dalilin
da yasa ka ceci rayuwata? dajin haka sai aljanin yace
da farko ni sunana ramzas asalina nine sarkin yaki abirnin hamshak
ina da mata guda daya sunanta zumaira sannan
ina da wani da maisuna harisul mar'uf
tun
harisul mar'uf yana yaro nake koyar dashi dabarun
yaki iri iri har saida ya zama sadaukin gaske
kuma gagara badau domin tun awannan lokacin
yana fafata kazamin da dakaru masu yawan
gaske kuma matasa masu jini ajika ya bazar dasu gaba daya
ya sami nasara akansu ba tareda an sami wanda
zai iya lakutar koda jikinsa ba wannan jarumtaka
dasa da yake yi tasa ya shahara aciki da wajen
birnin mu har ake masa kirari da jarumi dan jarumi jikan jarumai
aduniya babu abinda nakeso sama da wannan
da nawa guda daya da matata don haka banason
abinda zai bata musu rai komai kankantarsa
sarkin dake mulkin birnin hamshak a wannan lokaci
ana kiransa da suna darkusma
sarki darkusma ya kansance adalin sarki mai
matukar kaunar jama'ar kasarsa fiye da yadda yake kaunar kansa
tun lokacin da ina yaro karami mahaifina yake
zuwa dani gidan sarautar birnin mu ina wasa
agaban sarki darkusma hakanne yasa sarki
yake matukar kaunata kuma yake riritani wani
lokacin ma idan akayi baki wadanda basu
san alakar dake tsakanina da sarki sai su zata cewa
shine mahaifina saboda tsananin shakuwar dake tsakanin mu
sarki darkusma yana da da guda daya wanda
ake kira da suna mafazil dukda cewa sarki darkusma
ta kasance adali sai halinsa ya banbanta dana dansa mafazil
wato mafazil ya kasance azzalumin gaske
mara tausayin talakawa ga kuma tsananin
girman kai da rashin imani, domin shi bai dauki zalunci abakin komai ba
wannan daliline ya haddasa 'yar tsama tsakaninsa da mahaifinsa sarki darkusma
har sai da takai jama'ar birnin mu sun kasa hakuri
da irin zaluncin da yarima mafazil yake musu
da suka ga mahifinsa adaline saiya zamana
duk lokacin da yayi musu ba daidai ba
sai
su zo su kawowa mahaifinsa kara shi kuma
nantake agaban wadanda suka kawo karar zaisa a hukunta shi
wasu lokutan da wannan abu yake faruwa duk
ina tareda sarki suke faruwa har zuwa nake
gaban sarki na fada inyita rusa kuka ina rokonsa
akan yayi hakuri ya kyale yarima mafazil
amma
sai yace shi bazai hakura ba domin ba adalci bane
ya hukunta talakawansa agaban idon kowa
amma yace bazai hukunta dansa ba saboda
shi daban ne wannan daliline ya haddasa kiyayya
mai karfi tsakanina da yarima mafazil
domin
shi a tunaninsa nine na haddasa kiyayya tsakaninsa da mahaifinsa
saboda kaunar da yake yi min tasa hatta makarantar
yaki da muke zuwa wacce mahaifina yake koyar wa acikin ta
waje daya muke tsayawa da yarima mafazil
akullum yarima mafazil bashida burin da yafi yaga bayana
ya sha dana mini mugayen tarkunan mutuwa
amma ina tsallakewa da tsananin wahala wadanda
ni kaina bana taba tunanin tsallakesu
a haka
muka girma ni dashi har zuwa lokacin da mahaifina ya mutu
aka nadani sarkin yaki na birnin hamshak
koda
na sami wannan mukami sai ya kara saka mini kusanci da sarki darkusma
ya zamana ko zaman fada sarki baya zama sai ina nan
kuma ba kowacce shawara yake karbaba sai wacce na bayar
a lokutan da ake irin wadannan abubuwa kuwa
yarima mafazil yana gefen karagar mahaifinsa
yana zaune yana kallon abubuwan da suke faruwa
don haka sai ya fara tunanin anya kuwa sarki
ba so yake ya munafurce shi ya hana shi sarautar
da ya gada tun iyaye da kakanni ba?
tun sarki darkusma baya fuskantar abinda yake
cikin zuciyar yarima mafazil har ta kai ta kawo
yana iya fuskantar komai don haka wata rana
sai ya kirashi izuwa cikin turakarsa bayan ya karaso
sai sarki ya dubeshi yace yakai dana hakika
na fuskanci dukkan abubuwan dake cikin zuciyarka
a kullum idan na kalli cikin kwayar idanunka
babu abinda nake face tsananin gabar da kake
yiwa abokinka sarkin yaki ramzas da kuma
zargin da kakeyi akaina na tunanin anya kuwa
ina kaunar ka kuma ina da burin barmaka gadon karagar mulkina?
abinda nakeso ka fuskanta shine hannunka
baya taba rubewa ka yanke ka wullar ba koda
kuwa zakayi hakan to dolene kaji radadi ajikinka
kuma dolene kayi kuka harka zubar da hawaye ta dalilin hakan
to aduk lokacin da kayi laifi kai kana jin bakin ciki ne guda daya
shine na matsayinka na dan sarki ana hukunta
ka agaban talakawa ni kuma bakin cikina guda biyu ne sune
yau ace na saka dakaru suna dukan dana guda daya tilo
wanda bani da wani magajin inba shi ba
bakin cikina na biyu shine
yaya zaka kasance anan gaba bayan babu raina
yayin da ka zama sarkin wannan birnin na tabbata
idan har ba sauya rayuwarka kayi ba
to talakawa zasuyi maka biyayyar dolene ba zasu taba kaunar ka ba
kuma akullum zasuyi ta addu'ane akan ubangiji
yakawo karshen mulkinka domin mulki da zaluncin baya taba dorewa
kaga da zarar hakan ta faru shikenan sarautar birnin hamshak ta bar birnin mu har abada
wannan daliline yasa nake kokarin hukunta ka domin ka gyara rayuwarka ta nan gaba
amma ba wai don bana kaunar ka ba
lokacin da sarki yake wannan bayani babu
abinda yake yawo acikin zuciyar yarima mafazil
face yana rayawa ne aransa kawai karyar banza
mahaifinsa yake fada masa don haka bai tsaya
sauraren karashen maganarba ya fice daga
cikin turakar mahafin nasa gaba daya
lokacin
da yarima mafazil fice daga cikin turakar
sai
mahaifinsa ya fashe kuka ya tabbatar da cewa
lallai karshen mulkin gidan su ya kusa kwacewa
daga hannun zuriyarsu don haka sai yayi amfani da karfin sihirinsa
ya bace daga cikin turakarsa ba tareda kowanne
badakare ya ganshi ba hatta dansa mafazil
kuwa ya bar gidan sarautar kai tsaye ya wuce
izuwa gidan sarkin yaki ramzas da zuwa kofar
gidan sarkin yaki sai ya bayyana tsulum sannan ya aika wani badakare yaje
yayi masa sallama dani
nantake kuwa badakaren ya cika umarni
lokacin
da badakaren ya sameni ya sanar dani sakon
sarki sai abin yayi matukar dauremini kai kenan
domin dukda kusancin dake tsakanin mu dashi
duk da cewa ya dauke ni kamar dansa na cikinsa
bai taba zuwa gidana ba don haka saina biyo
badakaren da sauri azatona wani gagarumin
yakin ne ya taso koda na fito nayi arba da sarki darkusma
saina kamu da mamaki domin banga alamun
tashin hankali ba atattare dashi
don haka sai ya ruke hannuna yace yakai dana
kuma garkuwar birnin hamshak yau maganar
danake son yi dakai ta sirri ce don haka sai mu
shiga daga ciki mu tattauna akan wannan magana
dajin haka sai na wuce gaba nayiwa sarki darkusma jagora
muna isa cikin gidan sai mukatarar da harisul mar'uf
yana baiwa kansa horon yaki awannan lokaci yana yaro karami
yana ganin sarki darkusma sai ya rugo da gudu
yazo ya tsugunna ya gaisheshi cikin fara'a
sarki darkusma ya dauke shi ya dagashi ya shafa kansa
sannan yayi masa addu'a irin ta addininmu ya tofa masa a tafin hannuwansa ya ajiyeshi ya tafi ya ci gaba da baiwa kansa horon yakin
sannan muka wuce izuwa cikin wata turaka muka zauna
zaman mu keda wuya sai sarki darkusma ya dubeni yace
yakai dana lokaci yazo wanda zamu rabu dakai
kuma mulkin kasar nan zai koma hannun dana mafazil
ni nasan mutanen kasar nan zasu shiga tsananin tashin hankali
hatta kai kanka da matarka da danka sai kunfi
kowa shiga cikin tashin hankali abinda nakeso
da kai shine ka sallami matarka da danka
su tafi can wata nahiyar daban su cigaba da rayuwa
domin tsira da rayuwasu, domin nasan yadda
dana yarima mafazil ya tsaneka to dolene ya shafi 'ya 'yanka
kuma kaima dole sai yayi farautar ranka aduk inda zaka shiga aduniya
aguri dayane zaka iya rayuwa ba tareda an ganoka ba
wannan guri shine
nantake ya nuna mini wannan kogon dutse da muke ciki ayanzu
bincike ya tabbatar da cewa nan da shekaru
masu yawa a cikin wata masarauta ta bil'adama
za'a haifi wani gawurtaccen jarumi mai tarwatsa maza
wanda bincike ya nuna cewa zaizo wannan birnin namu domin daukar kubar miftahul sihir
akan hanyar zaizo wucewa takan tsuburin hijrul maut
har ya fadi ya kusa hallaka to awannan lokacin
zakaje ka dakoshi ka taimaka masa
harya
sami lafiya sannan ka taimaka masa ya mallaki kubar miftahul sihir
nasan cewa dolene sai yarima mafazil ya mutu awannan yaki
don haka awannan lokaci sai ka je ka nemo danka harisul mar'uf
ka dora shi akan karagar mulkina idan kayi
mini haka to shikenan raina zai kwanta lafiya acikin kushewa ta
dajin wannan bayani sai kwalla ta zubo mini
na dubi sarki darkusma nace akan wanne dalili
kake maganar na taimakawa makiyanmu wadanda zasu zo
domin su raba mu da abin bautarmu?
sarki yayi murmushin yake yace
ai kaddara ta riga fata ba komai ne ya janyo
wannan kaddarar ba face halin dana
inda
ace dana zai koma adali to da duk wadannan abubuwa ba zasu taba faruwaba
maganar kubar miftahul sihir da kake kuwa
inaso ka sani ai ita wannan kubar ba guda
daya bace ba acikin gidan sarautar birnin nan
muna da irinta kwaya biyu kuma duk amfaninsu daya
don haka daga yau inaso ka rabu da iyalinka
ba zaku sake saduwaba sai nan da shekaru masu yawa
kuma nima ayaune zanyi bankwana dakai domin rayuwata tazo karshe
lokacin da yazo nan azancensa sai duk mu biyun muka fashe da kuka
da kyar muka rabu dashi sannan ya koma cikin gidan sarautarsa
ni kuma naje na kebanta da matata zumaira
nasanar da ita abin da yake faruwa kuma na fada mata cewa subar cikin wannan garin a wannan daren
sannan na mika mata takobin da nake fita
yake yake da ita nace idan dana ya girma ta damka masa ita
domin nima na gajetane tun iyaye da kakanni
da kyar muka itama muka rabu da ita ta dauki
harisul mar'uf alokacin yana barci ta gudu dashi suka bar birnin hamshak
kashe gari da sassafe sai naji ana yada jita jitar
sarki darkusma ya mutu kuma wai yarima mafazil yace
nine na kasheshi sannan aka taho da dakaru masu yawa
karkashin jagorancin yarima mafazil sun nufo gidana don su kasheni
koda ganin haka sai nayi sauri nayi shigar yakina
sannan na sallami dakarun da suke gadin gidana na karbi takobin daya daga cikinsu
na kama hanyar fita daga birnin hamshak
akan
hanyata ne nayi kicibus da dakarun birnin mu da kuma yarima mafazil
nantake muka ruguntsume da masifaffen yaki
hakika badon na kasance jarumin gaske ba da
tuni na dade da shekawa barzahu
saboda saida muka shafe kwanaki ina yaki dasu nini kadai
dakyar na samu na tsira da rayuwata harna iso zuwa wannan kogon dutse
sai bayan na iso ne na gane cewa yarima mafazil ne
ya kashe mahaifinsa,don ya gaje karagar mulkinsa
kuma duk bala'in da matata zumaira take shiga
ahalin yanzu shine yake turo mata dasu
domin
yasan indai bata da lafiya danta harisul mar'uf
zaije ya samo mata magani burinsa shine harisul mar'uf ya mutu awajen neman magani
kaga idan ya mutu itama kamar ta mutune
yanzu haka ma harisul mar'uf yana tareda boka ulumanu
domin yayi masa alkawarin zai samarwa da mahaifiyarsa
lafiya idan har ya taimaka masa ya kashe masa
macijiyar da birnin ku suke bautawa kai kanka
kasan fada da wannan macijiyar ba karamin tashin hankali bane
sai tsananin sa'a da rabone zasu ceceka daga hannun wannan macijiyar
wannan shine labarin da na samo dangane dasu
to mai karatu mai kake tunanin zai faru nan gaba ?
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCORAGEMEN BAKAR GABA
PART 14
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Nidai labarin dana samo dangane dasu yarima saiman shine
saiku saurara kuji
koda aljani ramzas yazo daidai nan alabarinsa
sai yarima saiman ya nutsu yana nazari dangane da labarin
daga can saiya dago da kansa ya ramzas yace
yakai wannan adalin aljani tabbas rayukar tana da ban tausayi kuma tana kama da irin rayuwata
gaskiya na tausaya maka yadda ka iya jure rashin matarka da danka
kuma kanaji kana gani babu yadda zakayi ka taimaka musu
lallai yarima mafazil ya cika azzalumi kuma mara imani
tabbas karshensa yana nan zuwa nan bada jimawa ba
haka dai su yarima saiman suka dinga hira har dare yayi
sannan yarima saiman ya sami guri ya kwanta barci abinsa
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA YARIMA SAIMAN
Acan sansaninsu sarki abu saiman kuwa lokacin
da ya sana'anta mutum mutumi yaturasu izuwa
hanyar da su boka ulumanu zai biyo yazo birnin ramlatul saif
tare da dakarunsa sai nantake dakarun mutum mutumin
suka bace bat basu bayyana ako'ina ba sai dajin
farkon na iyakar birnin ramlatul saif ,koda bayyanarsu
sai suka sami wasu manyan bishiyoyi masu
duhuwoyi suka hau kansu suka zazzauna
suka dana tarkunan kibiyoyin allurai a saman
bishiyoyin dake cikin dajin gaba daya sannan
suka hau kan wasu bishiyoyi mafiya tsawo
da duhuwa suka buya yadda ko alamun su bazaka iya gani ba
haka suka zauna jiran abokan gaba tsawon
'yan sa'o'i basu ji ko alamar tahowarsu ba
sai bayan sa'o'i biyar sun shude sannan suka
fara jiwo sautin tahowar rundunar boka ulumanu
tun daga nesa suka dinga jiyo sautin bugun
manyan ganguna masu karar gaske
koda
rundunar suka iso kurkusa sai dakarun mutum mutumin suka
fara harba musu wadannan kananun sihirtattun alluran nan
nantake kuwa alluran suka dinga huda jikin
dakarun ba tareda sun sani ba akalla kibiyoyin
sun shiga jikin dakaru akalla guda dubu daya
da dari biyu da doriya amma duk wannan abu
dake faruwa dakarun da boka ulumanu basu ankara ba
sai da sukayi tafiyar rabin sa'a sannan dakarun
suka dinga yanke jiki suna fadowa daga kan
dawakansu suna kakarin mutuwa kafin cikar
dakiku goma sai duk gaba dayansu suka zama gawarwaki
koda ganin abinda yake faruwa sai ragowar
dakarun da kuma boka ulumanu suka ja linzaman dawakansu
cikin firgici domin basu san menene ya jawo hallakarsu ba
nantake boka ulumanu ya sauko daga kan tsuntsun tsafinsa
ya dubi gawarwakin yaga wata farar kumfa
tana fitowa daga cikin bakunansu sai ya mika
hannunsa ya dangwalo kumfar bakin daya
daga cikinsu ya shanshana ta sannan ya juyo
ya kalli dakarunsa yace tabbas an kawo mana
harin bazato akan hanyarmu don haka bara na duba
naga silar faruwar hakan nantake ya dauko
madubin tsafinsa ya shafeshi domin ganin gaskiyar al'amarin
mai makon madubin tsafin yayi haske yaga
abinda yake faruwa amma sai madubin tsafin yayi baki sidik
ya fara kumbura yana shirin yin bindiga ya fashe
koda ganin abinda ya faru sai boka ulumanu
ya takarkare ya kwarara uban ihu
sannan yace
ko shakka banayi tabbas abokan gabar mune
suka fara kawo mana farmakin sumame
don
haka dole ne muyi taka tsantsan yanzu akan
hanyar mu don gujewa sake shiga cikin wani tarkon mutuwar
yana gama fadin haka sai ya koma kan tsuntsun tsafinsa
ya zauna sannan ya shige gaba aka fara tafiya
domin zuwa birnin ramlatul saif da yaki
duk abinda ya faru gasu boka ulumanu sarki abu saiman
ya gani acikin madubin tsafinsa kuma shine
ya hana boka ulumanu ganin abinda yayi silar
mutuwar mutuwar dakarunsa ta hanyar karfin sihirinsa
don haka sai ya kara tashin wasu mutum mutumin
ya tura su izuwa da jijjikan da suke kan hanyar birnin guda biyu
kaso na farko ya raba musu turarrukan da zasu kunna a daji na biyu
kaso na biyu kuma ya ya basu basu tarkunan
da zasu binne akarkashin kasa tareda tsumin tsafi
wanda yake tsotse jinin jikin duk abinda ya taba jikinsa
nantake kuwa wadannan dakarun mutum mutumin
suka je sukayi abinda aka umarce su
kaso
na farko sukaje daji na biyu suka kunna wuta sannan
suka watsa wannan turaren sihirin faruwar
hakan keda wuya sai kasa ta dinga tsagewa
wasu irin manya manyan kunami suka dinga
fitowa daga karkashin kasa su dai wadannan
kunamai adadinsu ya kai dubu biyu kuma kowanne
daya daga cikinsu yana da fuka fukai guda biyu
wadanda dasu ne suke amfani wajen tashi sama
koda bayyanar wadannan sihirtattun kunamai
sai daya daga cikin dakarun mutum mutumin ya kallesu yace
mai girma sarki abu saiman ya umarceni da in sanar daku cewa
duk gaba dayanku yana so ku bace da gani
da zarar dakarun boka ulumanu sun iso sai ku afka musu da yaki
dajin haka sai dukkan kunaman suka durkusa alamar mubaya'a
nantake kuwa kunaman suka bace da gani bat gaba dayansu
shi kuwa boka ulumanu lokacin da yabar dajin
da alluran sihiri suka farmakesu sai ya tafi cikin tsananin bacin rai
babu abinda yafi tayar masa da hankali face
ganin yadda madubin tsafinsa yaki yayi aiki yayin
da yayi nufin bincike akan dalilin faruwar hakan
tabbas yana da tabbacin cewa sarki abu saiman
ya kawo masa wannan hari amma kuma baisan
tarkon da sarki abu saiman ya kafa masa nan gaba
sai a sannan yayi nadamar rashin yin cikakken
bincike akan sarki abu saiman domin tabbas
yanzu shima yasan cewa sarki abu saiman
ya cika gwarzon jarumi kuma matsafi
duk da
cewa yana da tabbacin samun nasara akansa
amma yana shakkar haduwarsu domin kar ta san kar ce a tsakansu
amma wannan tunani bai saka shi tunanin
komawa da baya ba haka suka dinga kusantar
birnin ramlatul saif cikin mugun nufi
tafiyar sa'a guda
suka shafe sannan suka iso bakin iyakar daji na biyu
koda isowarsu daidai wannan daji sai boka ulumanu
ya daga kansa sama ya karewa dajin kallo tsaf
yana nazarinsa ta hanyar karfin sihirinsa amma
sai awannan karon ma baiga alamar wani abin cutarwa ba
don haka sai ya juyo ya kalli dakarunsa yace
to nidai abinciken na tabbatar da cewa babu
wani abin cutarwa acikin wannan daji
amma
duk da haka ina mai shawartarku da kada mu kuskura
mu saki jiki da wannan daji domin ako da yaushe
al'amura suna iya sauyawa koda gama fadin
haka sai ya zare takobinsa ya juya ya shiga
cikin dajin cikin jin izza da yarda dakai
ragowar
dakarunsa nasa ma sai suka biyo bayansa
tareda zare nasu makaman amma fa duk wanda
ka kalla acikin su take zaka fuskanci cewa lallai amatukar tsorace suke
amma
ban da aljani guda daya wannan aljani kuwa
ba kowa bane ba face aljani harisul mar'uf daga sarkin yaki ramzas na birnin hamshak
domin shima tafiya yake yi cikin yarda da kansa
ba tareda ya zare makami ba koda suka iso
tsakiyar dajin ba zato ba tsammani sai suka
ga wasu manyan manyan kunamai sun bayyana sukayi musu kawanya
nantake kunaman suka afka musu aka muse
aka ruguntsume da azababben yaki kunaman
suka dinga harbin dakarun boka ulumanu
nanfa suka ruguntsume da masifaffen yaki
kunaman suka dinga harbin dakarun boka ulumanu
suna faduwa kasa matattu babu abinda zai
baka mamaki face ganin yadda kunaman
ko
aljani suka harba sai dai kaga ya fadi kasa matacce
nan take cikin kankanin lokaci nanfa kunaman
suka firgita dakarun boka ulumanu suka zare
takubbansu gaba daya suka afkawa kunaman da masifaffen yaki
lokaci guda suka kasuwar rayuka ta dinga ci acikin dajin
domin in banda sautin kukan dakaru da kuma
ihun wadannan kunamai babu abinda kunne yakeji
boka ulumanu kuwa da aljani harisul mar'uf
duk inda suka shiga sai dai kaga kunaman
suna zubowa kasa matattu domin harisul mar'uf
wata irin jarumtaka ya dinga yi ta ban al'ajabi
duk inda yakai sara ko suka sai dai kaga kunaman
suna zubowa kasa matattu kamar ana sassabe a gona
shi kuwa boka ulumanu yana amfani ne da karfin sihirinsa
koda boka ulumanu yaga idan idan suka sake
daukar lokaci mai tsawo kunaman zasu iya
yiwa dakarunsa mummunan barna
domin
kunaman suna da matukar karfin sihiri
koda
gama yin wannan tunani sai boka ulumanu
ya runtse idanunsa tareda karanta wadansu dalasiman tsafi
faruwar hakan keda wuya sai wata irin zazzafar wuta ta bayyana
take wutar ta dinga bin kunaman tana konasu kurmus
koda kunaman suka ga haka sai suka fara kokarin tserewa daga filin yakin
amma sai wutar ta dinga binsu duk inda sukayi tana konasu
abinda zai baka mamaki dangane da wannan
wutar shine ko kadan bata kona dakarun boka ulumanu
domin zakaga har ratsawa suke ta cikin wutar ba tareda tana konasu ba
kafin cikar dakiku goma gaba daya kunaman sun

Please Login or Register in order to submit comment