Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutuwa.
sannan yace
yakai gwarzon shekara mahaifiyarka bazata
taba samun lafiya ba hsar sai kaje kowanne
bakgare na duniya ka samo mata wasu
tsumummuka ka hada su waje daya ka bata
tasha sannan zata sami lafiya kamar babu
abindaya sameta.
sai kaje ka samo wadannan abubuwa sannan
zakayi shirin tunkarar boka salban
kodajin haka sai harisul mar'uf ya ta karkare
ya kwarara uban ihu
yace narantse da darajar hawayen
mahaifiyata saina samo mata wadannan
tsumummuka koda zan rasa rayuwata
sannan na yanko kan boka salban na tsireshi
atsakiyar birnin da yafi kowanne birni yawan
matsafa don hakan ya zamo gargadi
agaresu.
dajin haka sai boka garman yace
ina da wani taikako da nakeson baka na
wani sihiri mai karfin gaske wanda zai
kareka dga dukkan wani hatsari da tsautsayi.
sai harisul mar'uf yayi murmushi ga boka
garmana
sannan yace
ina da takobin da indai ina tare da ita zata
dinga bani kariya.don haka daga yau abzamu
sake haduwa ba ni dakai sai ranar da naje
na samo wannan magani.
kuka daga yau mun kulla bakar gaba da
boka salban.
koda gama fadin haka saiya bude fuka
fukansa ya tashisama ya luka acikin
gajimare cikin azababben gudu na gaban
kwatamce.
duk inda ya gifta ya tarar da wani ayari na
aljanu da sun ganshi saidai kaga sun chanja
hanya saboda tsananin kwarjiinsa.
idan kuwa tarom yan fashine cikin kankanin
lokaci yake tarwatsasu.
sai daya shafe kwanaki bakwai yana tafiya
sannan ya iso bakin wani birni na aljanu don
haka ya yanke shawarar ya shiga wannan
gari ya kwana idan gari ya waye sai ya kama
hanya ya cigaba da tafiyarsa.
nan take kuwa ya sauka abakin kofar wannan
kasa sannan ya matsa gaban kofar ya
kwankwasa.
bisa mamaki sai wani aljani ya leko yan
cewa wannan wanne me karar kwanane yake
bugu mana kofa alokacin da muke morewa
da kyawawan matanmu?kowanene ya
gaggauta juyawa da baya tun kafin fishina ya
sauka akansa.
koda wanna me tsaron kofa yazo nan a
zancensa sai ran aljani harisul mar'uf ya
baci.amma saiya basar yace nine harisul
maruf wanda yake neman mutuwa da
kudinsa kuma akoda yaushe.
dajin haka sai ran mai tsaron kofa ya baci.
nan takekuwa ya bude kofar wannan kasa.
sai dakaru sukayita fitowa da makamai iri iri
tamkar duniyar zasu yaka.
bayan wadannan dakaru sun gama zagaye
harisul maruf sai sukayi kukan kur suka afka
masa da sara da suka.cikin tsananin zafin
nama d ajuriya da bajinta nan take aljani
harisul mar'uf ya shiga kai sara da suka
cikin salo irin an manyanyan jarumai.
cikin kankanin lokaci ya karar dasu ya
zamana saura shugabansu.
nan take kuwa shugaban masu tsaron kofar
ya ruga aguje domin ya fadawa sarki
abindaya faru.
tafiyar keda wuya sai sai harisul maruf ya
matsa gaban kofar wannan birni wacce
takeda girma sosai.idan ta fadi sai an sami
manyan giwaye guda dari biyar sannan zasu
iya dagata.yasa kafarsa ya doki kofar.
nan take kuwa wannan kofar ta rufta ciki.
kuma adai dai wannan lokacin ne sarkin
wanna garin ya iso.
koda yaga abindaya faru sai ya kwarara uban
ihu. Koda yaga irin muguwr barnar da yayi masa
sai ransa yayi matukar baci tare d kwalla
ihu.
domin bincike ya tabbatar da cewa aduk
lokacin d wani sadauki ya balla wannan
kofar to daga ranar to daga bashi ba mulki
acikin kasar harsai ya nemi hadin kan
wannan sadauki sun tari masifar d zata afko
musu.
nan take kuwa ragazalu yasa hannu ya
finciko sarkin kofa sannan ya dubeshi yace
ka jawo mana bala'in da bamu taba
shigaba,tundaga sanda aka kafa wannan
kasa,tunda ka janyo mana sadaukin aljanun
duniya harisul mar'uf,don haka hukuncinka
shine kisa.
nan take yasa takobi ya datse masa
kai,sannan yayi wurgi da gawar,tare da bawa
dakarubsa umarnin suyi mubaya'a ga harisul
maruf
nan take dakarun suka cika umarni
sannan sarkin ragazalu ya tao da kafafunsa
yazo gaban harisul maruf yayi mubaya'a tare
da fadin
kagafarceni ya sadukin duniya bisa irin
tozartar da akayi maka acikin kasata.
bakomai ya jawo hakaba face tsaurin ido rin
na sarkin kofa,
yakai wannan babban jarumi dagani har
jama'ata mun mika wuya agareka,kuma
muna neman taimakonka sakamakon karya
alakadarin kasarmu dakayi na balla mana
kofa,
kuma bincike ya nuna cewa daga lokacin da
aka balla wannan kofa zaman lafiya zai kare
a wannan nahiya,sakamakon kawo mana
farmaki da kasashen ahokan gaba zasu
dingayi badon komaiba sai don su mallaki
dukiyarmu ta dangin zinare da lu'u lu'u
yanzu haka.maganar da nake maka wasu
kasashen sun fara shirin kawo mana
mamayar bazato yau ko gobe.
lokacin da sarki ragazalu yazo nan azancnsa
sai ya fashe da kuka,
al'amarin da yasa zuciyar harisul mar'uf tayi
sanyi kenan don haka sai yadubi sarki
ragazalu yace
yakai wannan adalin sarki zan
taimakeku,saboda banason ganin anzubarda
jinin wanda baijiba bai ganiba.
don haka nayi alkawarin taimakon
mayakanku,don haka yanzu sai kuyi shirin
gyara kofar wannan gari tun kafin abokan
gaba su cimmaku.
koda sarki ragazalu yaji haka saiya kamu da
tsananin farinciki sannan ya umarci wani
badakare da yaje yayi shelar ana neman duk
wani magini da yake cikin kasar da ya
hallara abakin kofar wannan birni
nan take kuwa wannan badakare angama ya
shugabana sannan ya bace.
kafin cikar.sa'a biyu duk wani magini ya
hallara
sannan sarki ya basu umarnin fara gini
kafin cikarsa'a bakwai sungama gini wannan
kofa
sannan aka aka dada kara dakarun tsaro ako
ina acikin garin aka cigaba da jiran ta inda
dakarun zasu bullo
a.haka.suka.kasance cikin shigar yaki taban
tsoro.
saida suka shafe yini guda sannan abokan
gaba suka iso.
awannan rana anyi gagarumin yakin da
ba'ataba kamrsaba awannan nahiya.sannan
anyi asarar dukiya mai tarin yawa.
bisa dole kowanne bangare yajanye
dakarunsa gaba daya.
tundaga wannan rana kasashen dake duniya
suke matukar tsoron wannan birni saboda
arin sa'ar da suka samu awannan yaki.
a zatonsu har yanzu harisul mar'uf yana
cikin kasar.
wash gari kuwa da sassafe harisul mar'uf
yatashi yabar kasar bayan sunyi sallama da
sarkin garin da yan majalisarsa.
sannan yanausa cikin gabashin duniya don
nemowa mahaifiyarsa magani,
sai da yayi tafiyar shekara guda sannan ya
iso dajin da yake dagashi sai bangon
duniya.na gabas
saboda haka sai harisul mar'uf ya zaro
sihirtacciyar takobinsa dake daure a
kugunsa.
sannan ya zaro wata yar taswira wacce ya
samu agurin sarki ragazalu
yabudeta ya duba.
nantake yayi arba da wani kogo acikin
taswirar,wanda yake nuni da shine hanyar da
zata kaika bangon duniya nagabas.
nantake kuwayasake bude fukafukansa yana
mai kusantar kogon kai tsaye.
yana shiga cikin kogon sai yayi arba da wata
yar siririyar hanya wacce take da tsananin
nisa.
nantake kuwa ya nufi wannan hanyar kai
tsaye yana mai gyara rukon takobinsa.
kwatsam sai yayi arba d wata bakar kunama
wacce ta tokare hanyar kogon gaba
daya.sannan wannan kunamar tasa kafa ta
daki wani dutse da kafarta guda daya
nantake kuwa wannan dutse ya gangara yaje
ya toshe hanyar da harisul maruf ya shigo.
mai makon ma harisul mar'uf ya firgita
sai abin ya bashi mamaki don ganin irin
wannan azababben karfi irin na wannan
kumama.
bakomai yabashi mamakiba face gani yadda
ta iya ture wannan dutse da kafarta daya.
alhalin inza'a tara manyan aljnu guda ashirin
bazasu iya mirgina wannan dutseba.
yana cikin wannan tunanine yaji kunamar
takawo masa harin bazato.
cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle ya
koma gefe daya don ya soma tunanin ta
hanyar dazai bullu mata.
nanfa aka soma kallon kallo tsakanin sa da
wannan kunamar na tsawon yan dakiku.daga
chan sai harisul mar'uf ya nufi kunamar cikin
mugun nufi,
suna haduwa aka ruguntsume da masifaffen
yaki nagaban kwatance suka wanzu suna
masu kaiwa junansu sara da suka.
shidai yana amfanine da takobin sihirinsa ita
kuma tana amfanine karinta da kuma
hannayenta wajen kai masa hari.
duk sa adda harisul maruf ya sari jikin
kunamar sai sai yaji kamr dutse ya sara.
ita kuma kunamar duk sanda ta kawo masa
hari ya kauce duk abindata samu nan take
yake ruburbushewa ko kuma ta haddasa
wawakeken rami.
sai da suka shafe sa'a guda suna
fafatawa,sannan kunamar ta sami nasarar
yankan harisul mar'uf agadon bayansa.
nantake harisul mar'uf ya kwalla ihu.saboda
zafi da zugin da yaji.cikin tsananin dauriya
ya daka tsalle tsalle kamar daga cikim baka
aka wullashi ya fada kan gadon bayan
kunamar sannan ya caka mata takobi a ido.
nan take kuwa idon kunamar ya fashe jini
yayi tsar tuwa.nantake kunamar ta haukace
ta dinga kawo masa mugayen hare hare
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
LITTAFIN BAKAR GABA PART 3
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING HABIBULLAH KBR
nan fa wannan fada ya dawo sabo kogon ya
soma girgiza tamkar zai ruguje.
cikin dan kankanin lokaci aljani harisul a fita
daga hayyacinsa saboda tsananin wahalar da
yakesha awajen kunamar.
saidaya zamana yakasa maidawa kunamar
da martani saidai yunuri kare kansa kawai
yakeyi.
koda aka shafe wata sa gudar sannan harisul
mar'uf yasami nasarar cakawa kunamar
takobi atsakiyar wuyanta.
nantake kunamar tafadi kasa ko shurawa
batayi ba.
sannan shima ya fadi kasa sumamme.
sai bayan sa'a uku sannan ya farfado daga
suman da yayi.
yana farfadowa ya tuna da ciwon dake gadon
bayansa
nantake yadauko magani daga cikin jakar
guzurinsa.yazuba aciwon dayake
bayansa.sannan ya tashi yagyara damararsa
ya nufi hanyar da zata fitar dashi daga
wannan kogo,sai bayan yan dakiku sannan
yafita daga cikin kogon.
yana fita yayi arba da wani tafkeken daji mai
matukar kwarjini daban tsoro,
shidai wannan daji yakasance babban daji
mai dauke da ababan tsoro,
don hatta bishiyoyin dajin siffofin dodanni ne
dasu,
kuma awannan lokaci rana ta bude.hakanne
ya haddasa wata iriyar zazzafar iska acikin
wannan daji.
duk haka baisa harisul mar'uf tsoroba ya
dada kutsa kansa cikin dajin cikin azabbaben
gudu acikin sararin samaniya da nufin ya
wuce ta saman dajin.
kwatsam sai yaji tamkar an ruke fuka
fukansa yadda bazai iya motsa suba.
bisa dole yaci burki asama don yaga abin da
zai faru.
yanacikin wannan haline yaji wata kakkarfar
iska ta zukoshi kasan wannan dajin.
alokacinda wannan iska ta sauke harisul
mar'uf akasan wannan dajin.
kwatsam sai yayi arba da wasu manya
manyan macizai masu matukar ban tsoro.
sudai wadannan macizai adadinsu yakai
dubu daya.haka girman kowannensu yakai
giman bishiyar dabino haka kaurinsu yakai
bishiyar kuka.
idanunsu kuwa tamkar angasa dan buda a
wuta.
alokacin da wadannan macizai sukaga
harisul mar'uf asararin samaniya sai suka
bace tamkar basu taba wanzuwa ba,sannan
itama wannan iskar ta dauke tamkar bata
taba samuwaba.
kuma alokacin ne harisul mar'uf ya daina
ganin macizan.
al'amarin daya matukar bashi mamaki kenan
sannan ya fara tunanin irin masifar da take
cikin wannan dajin,domin yasan ta hanyar
dazai bullu musu.
gashi kuma azahiri yaga halittu agun amma
yanzu kuma yaga basa wajen yanzu.
nan take azuciyarsa kawai ya shiga dajin kai
tsaye,amma ya dinga kula da motsin
kowacce irin halitta ya gani.
sannan ya zaro takobinsa ya kutsa kansa
batare da fargaba ba.
awannan lokaci rana ta bude tamkar zata
gasa masa kansa.
sai dayaje tsakiyar dajin sannan kasa ta fara
tsagewa tamkar zai rufta cikinta,bishiyoyi
suka soka karyewa,duwatsu suka dinga
mirginawa.
kwatsam sai harisul mar'uf yayi arba da
wadannan macizai suna saka shi atsakiya
yadda babu wanyar da zai iya wucewa.
daya daga cikin macizan ya sari wani dutse
dake kusa dashi,nantake dutsen ya rbe gid
biyu wata bakar kumfa tayi tsartuwa daga
bakin macijin.
alokacin da wannan abu ya faru harisul
mar'uf yana tsaye yana kallon ikon allah.
kwatsam sai wadannan macizai suka taso
masa da harbi suna wani irin kuka mara
dadinji.
nantake aka ruguntsume da azababben yaki
nagaban kwatance yana zamana suna masu
kaiwa juna sara da amakamansu.
shidai harisul mar'uf yana amfni da
takobinsa.
su kuma suna kai masa harin da bakinsu
dakuma jelarsu,wajen kai masa sara,
nanfa guri ya rincabe da hucin macizai
saboda tsananin bala'i,
cikin kankanin loakci suka hargitsa dajin da
buge buge.
duk sa'ar da suka kawo masa duka ya kauce
duk abinda suka samu nan take yake
ruburbushewa,
idan sara suka kawo masa da bakinsu idan
ya kauce suka sami kasa,nan take suke
haddasa wawakeken rami mai zurfin gaba
biyar.
shikuwa harisul' maruf saran macizan yake
baji ba gani.wani lokacin idan ya daki daya
daga cikinsu sai kaga kamar an janshi da
majaujawa,duk da irin wannan girma nasu,
hakika jarumataka baiwace duka wanda allah
ya bawa ita ya dace kaduba girma irin na
wadannan halitttu amma sai gashi aljani
guda daya yana neman rinjayarsu.
lokacin da gumurzu yakai gumurzu sai
macizan suka fuskanci nasarar da yake
samu akansu sai duk gaba dayansu suka ja
da baya suka tsaya ana kallon kallo
atsakaninsu.
shidai harisul mar'uf game da wadannan
macizai shine.
dukda yana samun damar saransu da
sukarsu amma daya daga cikinsu yaki ya
mutu saboda tsananin taurin eansu.
sukuma macizan shine
suna tunanin hamyar da zasubi su hallakashi
cikin sauki batare daya sami nasarar hallaka
daha daga cikinsu ba.
nantake kamar hadin baki suka sake afkawa
kan juna da azabben yaki wanda yafi na
farko.
awannan lokacin suaknsu macizan sai suka
chanza salon fada suna masu kai da kansu
da jelarsu lokaci guda.
duk sa'adda ya kauce duk abinda suka samu
nan take yake ruburbushewa ya zama kamar
gari.
ana cikin hakane wani maciji mai matukar
sa'a ya shammaci harisul mar'uf ya gabza
masa jelarsa agadon baya,
saboda tsananin karfin dukan sai da harisul
mar'uf yayi sama ya gwaru da jikin wani
katon tsauni.
nan take wani gudan jini yayi fitar burgu
daga bakinsa,sannan yaji gaba daya jikinsa
yadau zafi. ya mike tsaye tare da gyara tsayuwaarsa.
nan take ya sake rugawa izuwa kan
wadannan macizai,cikin mugun nufi yana mai
karaji da kuwwa yana mai kai sara da suka
cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta
fiye da farko.
a wannan lokaci sai ya canja salon yaki ya
koma kai sara a tsakiyar makwallaton wuyan
macizan,cikin sa'a kuwa wadannan macizai
suka fara halaka,ihun su da rurinsu ha cika
dajin baki daya.
babu abinda zai baka mamaki face ganin
yadda harisul mar'uf yake hallaka wadannan
macizai farat daya.
wani lokacin ma har tsalle zakaga yanayi
akan kawunansu yana wasa da hankalinsu.
cikin kankanin lokaci yagama hallakar dasu
baki dayansu.
sannan ya tashi ya bude fukafukansa ya
luluka acikin sararin samaniya,yanufi
hanyarda zata kaishi karshen dajin.
sai da yayi tafiyar sa'a biyu,
sannan yayi arba da wata siririyar gada
wacce farkonta wasu gumakan dodanni ne
akame.
kasan gadar kuma wutace takeci wani
lokacin ma.idanta lashi gadar sai wani turirin
hayaki ya tashi sama.
adaidai inda harisul mar,uf yake ga wani dan
karamin allon sanarwa an rubuta.
yakai bakon wannan daji ka sani .
wannan itace gadar da zata sadaka da abin
da kazo nema.dolene kabi ga kanta kaje
karshenta sannan zaka sami abinda kake
nema.
wadannan gumakan daka gani ba gumaka
bane dodannine bazasu taba mutuwaba face
kaje karshen wannan gada kadau abinda
kake nema.
yana gama karanta wannan allo sai ya
sakejin wannan iska ta sake zuko shi kasan
dajin baga ajiyeshi ako inaba sai bakin
wannan gada.tazarar dake tsakaninsa da iga
bata wuce taku dayaba.
kuma har awannan lokaci wadannan dodanni
suna cikin siffar gumaka.
kawai sai harisul mar'uf ya daga kafarsa ta
dama ya dorrta akan gadar kawai sai yaga
idanun wadannan dodanni ya bude,alamar
cewa ruhinsu ya soma dawowa.
batareda tsoroba ya sake dora kafarsa ta
hagu kan gadar.
nantake wata irin walkiya ta baiyana ta
haskake dajin baki daya dukda cewa ranace
ba dareba.
walkiyarna daukewa ruhin wadannan dodanni
ya dawo.
nan taki suka biyo harisul mar'uf
abaya,nanfa suka kasa tseren gudu dashi
domin su kamashi su hallakashi.
wohoho dan kaji ance ga k gudu to sa
gudune baizo ba.
ana fara wannan tseren gudune gadar da su
ke kai ta soma girgiza kamar zata karye.
bakomai ya janyo hakaba face tsananin
karfin takunsu.
saida suka wuce sa'a uku sannan suka iso
tsakiyar gadar,inda nanne wutar tafi gasawa,
nanfa tsananin zafi ya soma ruda harisul
mar'uf inda matukar galabaitar dashi kenan
hartakai cewa,baya iya gudu sosai.
cikin kankanin lokaci wadannan suka iso
inda harisul ma'uf yake.
cikin shammace daya daga cikinsu yasa kafa
yayi bal dashi.
sabo da karfin dukan sai dayayi sama kamar
anjanyeshi da majajjawa ya tafi kamar zai
fada cikin wutar amma sai ya wulkila jikinsa
ya rike karfen da akayi gadar dashi. da
hannunsa na dama sannan yadawo kan
gadar akaci gaba da tseren gudun
atsakaninsu.
a lokacinda wannan abu ke faruwa sai gadar
ta fara girgiza tana neman tsinkewa.
koda dodannin suka lura da haka sai gaba
dayansu sukayi tsalle suka sha gaban harisul
mar'uf suna masu kaimasa duka da
kafafunsu nantake kuwa suka rikirkita saboda
tsananin zafin namansu,da kuma karfin
damtsensu.
koda aka dau tsawon lokaci ana wannan
artabu sai ya fuskanci.
tabbas idan aka dau tsawon lokaci ana
wannan artabu tabbas zai iya hallaka.
koda yagama wannan tunani sai yayi yataka
kan daya daga cikin dodannin cikin
azababben gudu yadinga tafiya akan
kawunansu harya isa kan na karshens.sanna
ya sauka izuwa kan gadar yana tsala gudu
fiye da farko saigashi awannan lokaci yayiwa
dodannin mugun nisa.
sai bayan sa'a daya sannan ya fara hango
wata yar karamar bishiya.adaidai kuma
wannan lokaci gadar da suke kai ta tsinke..
cikin zafin nama harisul mar'uf wani itace da
akayi gadar dashi ya dinga kamawa yana
hawa sannan ya iso karshen gadar.
yannzuwa karshen gadar ne ya hango
dodannin sunyi wani irin tsalle suna kama
gadar.
koda ganin hakan sai harisul mar'uf yayi
tsalle ya haye kan wannan wannan bishiya
sannan ya tsinko wata ciyawa dake kana
bishiyar.
yan tsinkar ciyawar yaga duk gaba daya
dodannin sun kama da wuta sun kone
kurmus koda boka ulumanu yazo nan a labarinsa
saiyaga gaba daya hadiman sun nutsu suna
sauraronsa.
da ganin haka sai yayi dariya sannan yace
wannan shine takaitaccen tarihin harisul
mar'uf bayan bukata ta biya zan karasa
muku tarihin nasa.
yana gama wannan magana sai duk gaba
dayan hadiman sukai sujjada agareshi suna
masu cewa.
nasara ta tabbata agareka ya sarkin
matsafan duniya....
kafin sukarasa maganar tasu boka ulumanu
ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba.
+++ ++++ ++++ ++++
wannan shine abinda ya faru afadar boka
ulumanu mai shirin mulkar duniya.
al'amarin yarima saiman kuwa alokacin da
suka kutsa kai izuwa cikin wannan daji sai
suka kasance cikin suna masu tsala
azababben gudu nagaban kwatance tamkar
zasu fita daga duniyar gaba daya.
basu tsaya da tafiyaba saida suka fuskanci
dare yayi sannan suka yada zango awani daji
mai matukar duhuwa.
a sannan ne yarima saiman ya umarci
dakarunsa dasu tsaya da tafiyar d suke.
nantake kuwa suka cika umarni.
wani badakare mai suna zamnal ya matsa
kusa da yarima saiman yace yashugabana ni
aganina bai kamata mu yada zango awannan
dajiba domin baza'a rasa mugayen namun
daji acikinsa ba.
dajin haka sai yarima saiman ya juyo ya dubi
zamnal yace
shin baka ganin muna tafiyane tare da
mata,yara da tsofaffiba?
kasani tafiyarmu dasu awannan yanayi yafi
hatsari akan zaman mu a wannan daji.
saboda haka ina umartarku dakuje ku kafa
mana tanti inyaso gobe da safe sai muci
gaba da tafiya.
dajin haka sai badakaren yace angama ya
shugabana.
sanna ya tafi ya umarci yan uwansa dasu
kafa tantunan da za'a kwana aciki.
sannan wasu kuyangi sukaje suka shirya
musu abincin da zasu ci.aka mikashi ga
kowanne tanti.
bayan angama shirya komai sai yarima
saiman yafito ya dubi dakarunsa yace
yaku yanuwana duka gaba dayanku kunsan
abindaya baro mu daga gida.
adalilin hakane na yanke hukuncin da nake
ganin shine zai amfanemu.wannan shawara
itace
ni banaso ko mutum daya daga cikinmu ya
mutu,domin yin hakan babbar asarace
agaremu.
shawara ta farko dazan baku itace kada daya
daga cikinku yace zai tayani fada da duk irin
abinda kukaga na hadu dashi.
shawara ta biyu itace
aduk inda kuke ku kasance kuna tare da juna
koda kuwa wani abin tsoron kuka
gani,muddin bagani kukayi zaku hallaka gaba
daya ba.
shawara ta uku itace
aduk inda muke kada mudinga yin barci gaba
dayan mu idan dare yayi,saidai midinga raba
dare.
aduk sanda wani ya nemi taimako to mu
taimaka masa koda bai kasance dan kabilar
mu ba.
idan mukayi riko da wannan shawara to
tabbas bukatarmu zata biya.
da wannan kalami nake muku bankwna sai
bayan wayewar gari zamuci gaba da tafiya.
da gama fadin haka sai ya wuce izuwa cikin
tantinsa.
sannan suma ragowar tawagar suka tarwatse
kowa ya koma abakin aikinsa.
bayan ya isa cikin tantinsa saiya tarar da
gimbiya suhaila taci ado.ga wasu kuyangi
guda biyu suna bata abinci abaki,biyu kuma
suna yi mata tausa.
daganin sigowar yarima saiman sai
wadannan kuyangisuka tashi suka fice daga
turakar suka bar yarima da gimbiya suhaila
kadai a zaune acikin tantin.
cikin farinciki gimbiya suhaila tace lale
marhaban dababban masoyina na duniya.
nantake ta rugo da gudu ta rungume yarima
saiman sannan
zo muje mu zauna yakaimijina domin tsawon
wannan lokaci da muka dauka banganka ba
ji nake tamkar shekara guda ce bamu
haduba.
dajin haka sai yakama hannunta sukaje suka
zauna akan wata shimfida mai taushi.
sannan yadubeta yace.
kamar yadda kika kasance haka nima
nakasance domin dalilin halin dana shigane
yasa nina umarci dakarunmu dasu dakata da
tafiya.
haka kuma acikin tafiyata bana tunanin
wahalar dake gabanmu muddin kina kusa
dani.
yanzu haka muna cikin daji hayatul arzum
akwai muggan dabbobin daji acikinsa kuma
acikinsa zamu nemi hnayar zuwa dajin
kurusul saudam.
dajin haka sai tace dashi hakane amma
akwai wata matsala.
LIKE AND COMMENTS IS OUR (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
LITTAFIN
BAKAR GABA PART 4
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
koda boka ulumanu yazo nan a labarinsa
saiyaga gaba daya hadiman sun nutsu suna
sauraronsa.
da ganin haka sai yayi dariya sannan yace
wannan shine takaitaccen tarihin harisul
mar'uf bayan bukata ta biya zan karasa
muku tarihin nasa.
yana gama wannan magana sai duk gaba
dayan hadiman sukai sujjada agareshi suna
masu cewa.
nasara ta tabbata agareka ya sarkin
matsafan duniya....
kafin sukarasa maganar tasu boka ulumanu
ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba.
+++ ++++ ++++ ++++
wannan shine abinda ya faru afadar boka
ulumanu mai shirin mulkar duniya.
al'amarin yarima saiman kuwa alokacin da
suka kutsa kai izuwa cikin wannan daji sai
suka kasance cikin suna masu tsala
azababben gudu nagaban kwatance tamkar
zasu fita daga duniyar gaba daya.
basu tsaya da tafiyaba saida suka fuskanci
dare yayi sannan suka yada zango awani daji
mai matukar duhuwa.
a sannan ne yarima saiman ya umarci
dakarunsa dasu tsaya da tafiyar d suke.
nantake kuwa suka cika umarni.
wani badakare mai suna zamnal ya matsa
kusa da yarima saiman yace yashugabana ni
aganina bai kamata mu yada zango awannan
dajiba domin baza'a rasa mugayen namun
daji acikinsa ba.
dajin haka sai yarima saiman ya juyo ya dubi
zamnal yace
shin baka ganin muna tafiyane tare da
mata,yara da tsofaffiba?
kasani tafiyarmu dasu awannan yanayi yafi
hatsari akan zaman mu a wannan daji.
saboda haka ina umartarku dakuje ku kafa
mana tanti inyaso gobe da safe sai muci
gaba da tafiya.
dajin haka sai badakaren yace angama ya
shugabana.
sanna ya tafi ya umarci yan uwansa dasu
kafa tantunan da za'a kwana aciki.
sannan wasu kuyangi sukaje suka shirya
musu abincin da zasu ci.aka mikashi ga
kowanne tanti.
bayan angama shirya komai sai yarima
saiman yafito ya dubi dakarunsa yace
yaku yanuwana duka gaba dayanku kunsan
abindaya baro mu daga gida.
adalilin hakane na yanke hukuncin da nake
ganin shine zai amfanemu.wannan shawara
itace
ni banaso ko mutum daya daga cikinmu ya
mutu,domin yin hakan babbar asarace
agaremu.
shawara ta farko dazan baku itace kada daya
daga cikinku yace zai tayani fada da duk irin
abinda kukaga na hadu dashi.
shawara ta biyu itace
aduk inda kuke ku kasance kuna tare da juna
koda kuwa wani abin tsoron kuka
gani,muddin bagani kukayi zaku hallaka gaba
daya ba.
shawara ta uku itace
aduk inda muke kada mudinga yin barci gaba
dayan mu idan dare yayi,saidai midinga raba
dare.
aduk sanda wani ya nemi taimako to mu
taimaka masa koda bai kasance dan kabilar
mu ba.
idan mukayi riko da wannan shawara to
tabbas bukatarmu zata biya.
da wannan kalami nake muku bankwna sai
bayan wayewar gari zamuci gaba da tafiya.
da gama fadin haka sai ya wuce izuwa cikin
tantinsa.
sannan suma ragowar tawagar suka tarwatse
kowa ya koma abakin aikinsa.
bayan ya isa cikin tantinsa saiya tarar da
gimbiya suhaila taci ado.ga wasu kuyangi
guda biyu suna bata abinci abaki,biyu kuma
suna yi mata tausa.
daganin sigowar yarima saiman sai
wadannan kuyangisuka tashi suka fice daga
turakar suka bar yarima da gimbiya suhaila
kadai a zaune acikin tantin.
cikin farinciki gimbiya suhaila tace lale
marhaban dababban masoyina na duniya.
nantake ta rugo da gudu ta rungume yarima
saiman sannan
zo muje mu zauna yakaimijina domin tsawon
wannan lokaci da muka dauka banganka ba
ji nake tamkar shekara guda ce bamu
haduba.
dajin haka sai yakama hannunta sukaje suka
zauna akan wata shimfida mai taushi.
sannan yadubeta yace.
kamar yadda kika kasance haka nima
nakasance domin dalilin halin dana shigane
yasa nina umarci dakarunmu dasu dakata da
tafiya.
haka kuma acikin tafiyata bana tunanin
wahalar dake gabanmu muddin kina kusa
dani.
yanzu haka muna cikin daji hayatul arzum
akwai muggan dabbobin daji acikinsa kuma
acikinsa zamu nemi hnayar zuwa dajin
kurusul saudam.
dajin haka sai tace dashi hakane amma
akwai wata matsala. cikin tsananin mamaki yadubeta yace
me kike nufi ?
gimbiya suhaila tace idan muka fiya yada
zango to hakan zai baiwa magauta dama
akan mu
shin baka tunanin cewa akwai wata sabuwar
masifar da take shirin fadomana bayan ta
boka ulumanu ?
kodajin haka sai hankalin yarima saiman ya
tashi yaji gaba daya zuciyarsa ta dugunzuma
nantake ya nuna bangon tantin nasu da
yatsansa na hannu
faruwar hakan keda wuya saiga hoton fadar
boka ulumanu ta baiyana tundaga lokacin da
sukayi walimar farko afada ,har izuwa
lokacinda ya aiki aljani markazulu ya kashe
dodo sharmanu da yarsa .
koda sukazo daidainan sai hoton komai ya
dauke tamkar baitaba wanzuwaba.
da ganin haka sai gimbiya suhaila ta dubeshi
tace to wannan abu daya faru bakaramin
tashin hankali bane anahiyar nan baki
dayaba ,domin dodo garjaju bazai taba
hakuriba akan wannan abu daya faruba .
kodajin haka sai yarima saiman yabushe da
dariya sannan yace .
nafiki sanin kowaye garjaju don haka kafin
muje inda yake zansan hanyar da zamubi mu
hallakashi farat daya
nantake ya tashi yaja hannun gimbiya
suhaila izuwa kan wanish luntsumemen gado
suka kwanta .
kwanciyarsu keda wuya sai bacci ya daukesu
acikin tantin.
acan sansanin dakarun su yarima saiman
Kuwa sai raba kwanciya kamar yadda ya
tsara musu suka raba kansu gida biyu kaso
nafarko suka fara kwanciya sannan kaso
nabiyu suka kwanta
kash hakika rashin sani yafi dare duhu ashe
awannan wuri da suka yada sansani akwai
wasu mugga muggan yanfashi amma su
akaidarsu basayin fashi acikin dare sai da
asuba ta doso kai sannan suke farawa zuwa
faduwar rana .
wannan daliline yasa basu kawowa su yarima
hariba tun sanda shigo dajin.
amma kuma tundaga shigowar su yarima sai
suka fara haka tarkuna yadda zasu kashesu
farat daya .
acikin tantin yarima Kuwa lokacin da suka
nutsa cikin barci .gimbiya tayi wani mafarki
inda ta hangi wasu kananan karnuka akan
hanyarsu suna kokarin yi musu kisan farat
daya .
koda daidainan amafarkin nata saita farka
afirgice,tasa hannu tatashi yarima .
cikin firgice tadubi yarima tace yakai
masoyina kayi hakuri bisa tashinka daga
barci da nayi .
hakan ta farune sakamakon wani mummunan
mafarki da nayi .tun ina yarinya idan nayi
mafarki yana zama gaskiya ba'a taba samun
akasiba
to a darennan nayi mafarki inda aka
nunamini wasu muggan yanfashi akewaye
damu suna dana mana tarkunan
mugunta.idan har bamu dauki matakiba to
tabbas zamuyi asarar rayuka da yawa .
kodajin sai ya dubeta yace madallah da mata
tagari hakika ina matukarjin dadi da irin
taimakon dakike bani
nantake ya tashi yafita daga cikin tantin nasa
ya nufi inda dakarunsa suke,koda sukaga
yarima sai suka durkusa cikin
girmamawa.yarima ya dubesu yace
akwai wani abu dake shirin faruwa idan har
bamu dauki matakin gaggawa ba
shawarar dazan baku itace dakunga alfijir
yafara fitowa kusami kibiyoyinku,kusaita
hanya guda daya daidai inda tarkon yake
saiku harbata,to dazarar kunyi haka tarkunan
abokan gaba zasu lalace.gurin da aka birnine
tarkunan Kuwa yana nan gaba damu daga
barin gabas tafiyar rabin sa'a idan har muka
sami nasarar lalata tarkunan to zamu sami
nasarar fita daga san saninmu lafiya
nine kadadai wanda zai taresu da yaki da
zarar munyi gaba da gaba dasu.kukuma
saiku zama yan kallo .
ku aikinku shine bawa jama'armu tsaro.idan
mukayi haka to zamu sami nasara akansu .
haka suka kasance cikin wannan halin hr
izuwa lokacin da alfijir yafara ketowa nan
take Kuwa dakarun suka Debo kibiyoyi suka
dana ajinkin baka sannan suka sukayi tafiyar
rabin sa'a.sannan suka saita gabansu kadan
suka harba kibiyoyin,kwatsam saiga wasu
muggan tarkuna suna fitowa daga karkashin
kasa masu matukar hatsari ga rayuwar dan
adam.
faruwar hakan keda wuya saiga wasu
muggan yanfashi suna fitowa daga cikin
maboyarsu suna masu karji gami da kuwwa
nufo su yarima saiman .
koda ya rage baifi saura taku gomaba
tsakaninsu da sansanin sai yarima saiman
yafito cikin muguwar shigar yaki .
nantake yasa kafa yadoki wasu dakaru dake
gabansa .saboda karfin dukan saida sukai
tsalle

Please Login or Register in order to submit comment