Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya ganin abinda yake faruwa
ihun da karajin dodannin ya cika dajin gaba daya
karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne
bala'i yayi bala'i duk inda su yarima saiman suka
danna shida markazulu sai dai kaga dodannin suna zubewa
kasa duk da tsananin karfin damtsensu
ba komai ya jawo
hakaba face tsananin karfin damtsen su yarima saiman
da kuma zafin naman su
cikin kankanin lokaci suka hargitsa dajin gaba daya
cikin sa'o'i kadan suka kashe da yawa daga cikin dodannin
koda ganin haka sai dodo garjaju ya kwarara uban ihu
sannan ya dakawa dakarun nasa tsawa nan take duk suka fadi
suka zama gawarwaki ko daya daga cikinsu bai tsira ba
nantake dodo garjaju ya falfalo da gudu izuwa kan su yarima saiman
yana zuwa saiya kawo musu mummunan sara
da wata siririyar addarsa nantake sukayi tsalle
suka tsallake harin nasa
koda addar ta karci kasa saita haifar da wani wawakeken rami
wanda za'a iya binne mutum goma acikinsa
nantake ya fara kawo musu mugayen here hare
domin ganin ya hallakasu amma sai abu ya gagara
saigashi 'yan kananun halittun daya raina suna kokarin bata masa
lokaci koda ganin haka sai dodo garjaju ya shammaci aljani markazulu ya
gabza masa wani wawan sara agadon bayansa
nantake markazulu ya ya sulale kasa sumamme
koda ganin abinda ya faru sai zuciyar saiman
ta fusata yaji wani irin gagarumin karfi ya shige shi
nantake ya juya suka sake kachamewa da sabon yaki fiye da ko yaushe
saigashi yarima saiman yana wata irin jarumtaka taban al'ajabi
domin har tashi sama yakeyi kamar tsuntsu
yana kaiwa garjaju sara da nufin ya hallakaahi
koda dodo garjaju ya gano manufar saiman
kuma ya tabbatar da cewa idan har ya bari wannan takobin ta sauka ajikinsa to shikenan anci galaba akansa
sai ya kara zage damtse ya hada da kaiwa saiman
naushi da bugu da nufin yi masa rotse
koda ganin haka sai yarima saiman ya
dinga goce goce
yana kaucewa harin garjaju duk sa'adda garjaju ya kawo masa idan ya sami gini ko wani abu nantake ya ke ragargaza shi
kamar an nika gari
shima abinda ya sa ya kasa hallaka yarima saiman
shine yarima saiman yana da tsananin zafin nama
fiye da tunanin mai tunani duk sanda yakai masa hari kafin harin ya sauka. akansa sai kaga ya goce
koda dodo garjaju yaga ya kasa hallaka yarima saiman
da karfin damtse sai ya wangame bakinsa nantake wata irin iska mai karfin gaske ta
fito daga cikin bakinsa
ta suri yarima saiman tayi sama dashi ta dinga
wulwulashi asama yana hajijiya acikinta
cikin kankanin lokaci yarima ya soma fita daga hayyacinsa
koda yaga zai hallaka saiya fara karanta wadansu dalasiman tsafi acikin zuciyar sa
faruwa hakan keda wuya sai wannan iskar ta bace
sannan ya sauko kasa ahankali bisa turba rike da takobinsa ahannu
sai awannan lokacin dodo garjaju ya gane cewa bakomai ne yabaiwa yarima saiman wannan gagarumin karfi ba face wannan takobin sihiri da take hannunsa
koda gano hakan sai ya bushe da mahaukaciyar dariya
sannan ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi
koda ya gama karantawa sai aka fara ruwan wasu manya manyan duwatsu masu girman gaske
koda ganin hakan sai yarima saiman ya falfala da azababben gudu
don gujewa wadannan duwatsu sannan ya fara karanta wadansu dalasiman tsafin domin tsayar da
wadannan duwatsu, amma bisa mamaki saiyaga duwatsun
sunki su tsaya kamar kara zubosu ake dada yi koda
kafinya ankara wani dutse yazo yayi bal dashi
yafadi can gefe daya sannan itama takobin ta fadi can gefe daya
koda ganin haka sai dodo garjaju ya bushe da dariya
sannan yaje ya nuna saiman da dan yatsansa
nantake wasu murtuka murtukan sarkoki suka daureshi
sannan yaje ya dauki takobin yana mai kyalkyala dariyar samun nasara
nantake ya kulle su yarima saiman da aljani markazulu da wata murtukekiyar sarkar tsafi
sannan ya sakasu acikin wani katon keji ya tafi dasu cikin gidan sarautarsa
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GASU YARIMA SAIMAN BAYAN SUN ISA DAJIN AJALI
liҠɛ ąŋɖ ĆơmmɛŋŧŞ iŞ ơųř ɛŋĆơųřąɠɛmɛŋ
BAKAR GABA
PART 9
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
Al'amarin su jarumi zamnal kuwa lokacinda suka
nufi hanyarda zata kaisu birnin askandariya
sai suka wanzu suna masu sauri da gaggawa
domin su isa birnin cikin kankanin lokaci sannan su koma izuwa sansaninsu
tafiyar sa'a takwas sukayi sannan suka fara
hango kofar shiga birnin askandariya don haka
sai suka tsaya sannan suka hada hannuwansu waje guda
tareda karanta dalasiman tsafi
faruwar hakan keda wuya sai dukkan su suka rikide suka koma
siffar fatake sannan kuma jikinsu duk raunika
da kagansu zaka zaci cewa sun sha gwagwarmaya akan hanyar tafiyarsu
sannan suka nufi kofar birnin tareda hajarsu 'yar kadan
koda suka isa bakin kofar shiga cikin birnin
koda suka iso dafda kofar sai dakaru masu tsaron kofar birnin
suka suka zagayesu tareda zare makamansu ta yadda babu wanda zai iya fita daga cikin su
koda ganin haka sai su jarumi zamnal sukaja linzaman dawakansu suna jiran suga abinda zai faru
daga can saiga wani badakare kakkarfa wanda
shine shugaban masu tsaron kofar ya fito daga cikin kofar birnin
yana tafiya cikin jin izza da takama ya fito gaban wadannan dakarun mya tsaya ya karewa su jarumi zamnal ido tsawon 'yan dakiku yana nazari akansu akansu
daga can sai yace
yaku wadannan baki inayi muku marhaban da zuwa birnin askandariya
kuma birnin
sarki marhus birnin da babu kamarsa a fannin kere kere awannan nahiya
yaku wadannan matafiya shin zan iya sanin daga inda kuke
da kuma dalilin zuwanku wannan birni?
kodajin wannan tambaya sai
jarumi zamnal yace
mu fatakene daga can wata nahiyar daban
hanyace ta biyo damu ta wani daji dake can bayan birninku
ayarinmu yakai mutum dubu hudu to ahanya ne muka gamu
da wasu guggun 'yan fashi muka fafata kazamin
yaki tsakanin mu dasu suka kashe dukkan abokan tafiyar mu
muma da kyar da sidin goshi muka tsira da rayuwarmu
muka gudu akan hanyar mune muka zo giftawa ta hanyar
wannan birnin saboda haka ne muka bukaci
ataimaka mana a barmu mu shiga wannan birni
mu dan huta tsawon 'yan kwanaki dan sayi abubuwan da
zamu saya mu kama hanya mu tafi izuwa kasarmu
koda jin wannan bayani sai shugaban dakarun ya nutsu ya sake kurawa zamnal idanu
yana karayin nazarinsa tsawon 'yan dakiku daga can
saiya matso gaban zamnal yace ba zamu baku damar shiga wannan birnin ba
sai munfara caje kayanku don muga abubuwan da suke ciki
koda jin haka sai zamnal yayi murmurshi sannan yace babu
matsala jeka dubasu
nantake shugaba masu tsaron kofar ya umarci wasu dakarunsa
dasuje su duba kayan
kafin ya gama rufe bakin nasa tuni dakarun
sun fara caje kayan ko zasuga wani abu wanda ba'aso ashiga dashi birnin amma aka rasa
〇 sai gaba dayansu suka dubi shugaban nasu suka fada masa cewa babu komai aciki
dajin haka sai ya girgiza kansa yace shikenan abude musu kofa
nantake kuwa aka bude kofa suka shiga gaba dayansu
sannan aka maida kofar aka rufe
lokacinda su jarumi zamnal suka shiga cikin birnin askandariya sai suka sake rikidewa
izuwa siffar dakarun birnin hindu sannan suka kama hanya suka shiga cikin gari
duk inda suka shiga acikin garin saidai kaga ana kallonsu ana mamakin yadda suka baro can nahiyarsu
suka iya zuwa wannan birni alhalin tafiyace ta shekara talatin
kuma duk wanda ka kalla acikinsu zamnal zakaga shekarunsa
basu wuce ashirin da biyar ba
haka dai su zamnal suka dinga kutsawa cikin birnin
suna kallon irin gine ginen da akayi awannan birni
masu ban sha'awa wadanda suka fita daban da irin gine ginen birninsu
nanfa suka kamu da tsananin mamaki suna ayyanawa aransu ce
lallai tafiya mabudin ilimi ce wanda bai yi yawon duniyaba bai more kallo ba
lokacinda suka iso tsakiyar birnin sai jarumi zamnal
yaga wasu matasa guda biyu suna tafiya suna hira abinsu sun fito daga wani dan karamin gida
koda ganinsu sai jarumi zamnal ya dakatar da dakarunsa
sannan yaje gaban wadannan matasa ya mika musu hannu
suka gaisa cikin fara'a
sannan jarumi zamnal ya dubesu cikin yarensu yace
yaku wadannan matasa mu bakine daga birnin hindu
hanyace ta biyo damu izuwa wannan birni naku shine muka hadu daku akan hanya
don haka nake neman taimako wajen ku
kodajin wannan batu sai daya daga cikin matasan yace
kai kuwa wacce irin bukata kake da itaa?
jarumi zamnal yace
munaso ne ku nuna mana hanyar da zamubi muje kasuwar garin nan?
kodajin wannan tambaya sai wannan saurayi yayi murmurshi sannan yace
lallai na yarda ku bakine
domin na fuskanci baku san tsarin wannan birnin ba
aka'idar wannan birni kasuwarsa tanaci ne sau daya acikin kowanne sati
tun farkon kafuwarsa domin burin sarakunan wannan birni shine
sunason wannan ranar cin kasuwa ta dinga zama ranar tunawa da ranar da aka kafa wannan birni
don haka koda kun shiga cikin kasuwar wannan gari
ba zaku sami koda kwayar hatsiba
koda jin wannan batu sai jarumi zamnal ya girgiza
saboda ya fahimci cewa dolene su kwana a garin har zuwa ranar cin kasuwa
sannan su sayi abinda zasu siya su kama hanya su tafi izuwa sansaninsu…..
yana cikin yin tunani ne daya daga daga cikin matasan ya katse shi da cewa
kasuwar wannan birni tanaci ne a kowacce ranar laraba
don haka saura kwana biyu kacal sati ya zagayo
kodajin haka sai jarumi zamnal ya ce to ko zaku iya nuna mana unguwar da zamu samo gidan kwana domin yada zango kafin ranar cin kasuwar tayi?
dajin wannan tambaya sai matashin yace babu damuwa kuzo mu rakaku
jarumi zamnal yace to bara naje nayiwa 'yan uwana bayanin abinda ake ci
nantake ya juya yaje garesu yayi musu bayanin yadda ake ciki
sannan gaba dayansu suka bi bayan wadannan matasa
akan hanyar tafiyarsu ne jarumi zamnal ya dubi matasan yace
ni sunana zamnal inba zaku damu ba zanso
ku fada mini sunanku domin daga yanzu mun zama abokai nida ku
daya daga cikin matasan yace ni sunana hasuf sannan ya nuna abokin tafiyarsa yace
wannan kuma sunansa zasif ni dashi hassan da usaini
kuma wancan gidan da kukaga munfito shine mahaifar mu
iyayen mu sun mutu ne sakamakon wani sihiri da wani boka wanda ake kira ulumanu ya jarraba shine sihirin ya fada kan iyayen mu duk suka mutu tundaga wannan rana duk wani
mutum idan ya shiga cikin gidan take anan yake daskarewa
ya zama kamar kankara daga baya kuma saiya ruburbushe ya mutu
alokacinda wannan abu ya faru mu bama cikin gidan mun tafi kasuwa domin sayowa iyayen mu abinci
shine muka dawo muka tarar da wannan danyen aiki da yayi mana
mu kanmu munyi mamaki da mukaga kowa
yana mutuwa ta sanadiyar shiga cikin gidan mu
amma mu babu abinda yake samun mu
kodajin haka sai jarumi zamnal ya jijjiga kansa
sannan yace lallai boka ulumanu babban azzalumi ne
kuma nima na samu labarinsa awajen wasu fatake akan hanyar mu ta zuwa nan
kuma sunce dani tabbas nan da
'yan watanni za'a haifi jarimin da zai hallaka shi
kodajin wannan batu sai su hasuf suka tsaida dakata da tafiya suka sake duban zamnal suka ce
yakai wannan bako mai cikar kama dagas ke ne abinda kake fada kuwa?
kodajin wannan tambaya sai zamnal yace tabbas maganata gaskiya ce
amma ba zaku tabbatar da maganata ba sai idan lokaci yayi kun gani da idon ku
suna cikin wannan hirane suka iso kofar wani babban gida
zasif ya ce dasu zamnal wannan shine saukar baki
kuma mai gidan ya kasance mutumin kirkine shi
gidan yana da tsaro sosai ta yadda ba sai anbukaci dakaru
masu tsaron lafiyar kuba domin da zarar wani abu ya shiga wannan gida wata mummunaar manufa
nantake zai kama da wuta ya kone kurmus
wannan dalili ne yasa duk wani mai laifi baya yarda ya kusanci gidan nan
kodajin haka sai jarumi zamnal ya yayi murmurshi sannan yace
yaku abokai na nida dukka abokan tafiyata muna godiya agareku
kuma duk sanda kuke da sha'ar sake ganin kuna da ikon shiga wannan gida
nantake suka juyawa su hasuf baya suna masu daga musu hannu
suka nufi kofar shiga wannan gida
koda sukazo bakin kofar sai nantake kofar ta bude kanta
suka kutsa kansu ciki
suna shiga cikin gidan sai kofar ta sake kulle kanta
suna shiga cikin gidan sai suka yi arba da wani dattijo fuskarsa cike da furfura
nantake ya karaso gaban su jarumi zamnal yace
inayi muku lale marhaban da zuwa gidan amana
yaku wadannan baki ku sani cewa mugu baya taba
samun damar shigowa wannan gidan ba tunda ga lokacinda na ginashi
kawo iyanzu
kodajin haka sai su jarumi zamnal suka rissina suka gaishda wannan dattijo
sannan suka ce sunaso ya basu aron dakunan da zasu kwana biyu kacal sannan su kama hanya su tafi subar wannan birnin
dajin haka sai dattijon yayi murmurshi yace
yaku wadannan baki ku sani cewa bana gina wannan gida bane don neman tara dukiya mai yawa ba
na ginashi don saukar mutanen kirki wadanda suka san mutuncin manya
tabbas ku mutanen kirki ne domin tun daga sanda kuka shigo cikin gidan nan
don nayi muku ragi ku bada dirhami hamsin kacal
don haka koda kun karamin ko drhami dayane
akan kudin dana bukata to bazan karba ba
lokacinda wannan dattijo yazo nan azancensa sai mamaki ya kama su jarumi zamnal sukace aransu
tabbas mutanen wannan gari suna da matukar mutumci da karrama bako
don haka sai dukkansu yi masa sannan suka kirga darhami hamsin cif cif suka bashi
sannan shi kuma yayi musu jagora izuwa cikin gidan
ya kai kowa izuwa masaukinsa
tareda basu abinci da abin sha suka cika cikin su
kasancewar awannan lokaci dare yayi sai duk gaba dayansu suka sami waje suka kama barci abinsu
domin huce gajiyar tafiyar da suka sha
acikin wannan gida suka kwana biyu kuma kullum sai su hasuf sunzo sun tayasu hira
akwana na biyun ne wanda yake shine ranar cin kasuwa
sai su jarumi zamnal suka hada kayansu suka fito
sukayiwa mai wannan gida godiya daya basu masauki
sannan suka fito wajen gidan koda fitowarsu
sai sukaga su hasuf sun nufo wannan gida
koda suka hadu sai suka gaisa sannan suka dunguma gaba daya suka tafi kasuwar garin
tafiyar rabin sa'a kacal sukayi sannan suka isa kasuwar
itadai wannan kasuwa ta kasance babbar kasuwace
wacce 'yan kasuwa suke zuwa daga sassa daban na duniya
suna kawo hajarsu asaya sannan su sayi wata su tafi
babu abinda yafi yawa a wannan kasuwar sama da kayan kira, irinsu, takobi, garkuwa, sulke, mashi
dadai sauransu mutane suna zuwa suna ta neman abinda suke bukata
koda isowarsu wannan kasuwa sai suka wuce kai tsaye izuwa gidan sarkin makera
koda zuwansu sai sarkin makera ya taryesu hannu biyu
sannan ya tambayesu abinda suke bukata
nantake jarumi zamnal ya fada masa suna bukatar keken doki mai inganci
kodajin haka sai sarkin makera yace yakai wannan barde
akwai wani keken doki guda daya tak agurina wanda jiya jiyan nan muka gama hadashi don haka zo muje na nuna maka
nantake ya bishi abaya sukaje yaga keken dokin
sannan akayi cinikinsa akan dirhami dubu hudu
suka suka bashi kudinsa sannan suka samu kosassun dawakai suka daurawa keken dokin
suka fara jansa domin tafiya inda sansaninsu yake
kwatsam sai sukaji hayaniya abayansu gami da ihun mutane yara da tsofaffi
nantake suka juyo bayansu don ganin abinda yake faruwa
ashe wasu guggun 'yan fashi ne suka shigo
cikin kasuwar suketa yiwa mutane kwace duk wanda kuwa yayi yunkurin hanawa nantake suke sare masa kansa
nanfa mutane suka fara gudun ceton ransu
koda 'yan fashin suka kyallara idonsu sukaga keken dokin da su jarumi zamnal suka saya
sai suka yo kansu da nufin su kwace keken dokin
koda ganin haka sai jarumi zamnal ya zare takobinsa
tareda sauran dakarun da suke tareda shi
zamnal ya dubisu hasuf
yace ku ku koma gefe kada wani abu ya shafeku
nantake su jarumi zamnal suka sakarwa dawakansu linzami suka shiga cikin dakarun sumamen
nanfa aka ruguntsume da azababben yaki na gaban kwatance
karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne
duk inda su jarumi zamnal suka shiga saidai kaga dakarun sumamen suna zubewa kasa
duk da tsananin yawansu sai gashi ya zama na banza
domin sun kasa tsinana komai akan su jarumi zamnal
wani irin yaki suka dinga yi suna suna hadawa
da tsalle tsalle kamar tsuntsaye suna yawo
a saman 'yan fashin suna sare musu kawuna
cikin rabin sa'a kacal suka gama kashe gaba dayan 'yan fashin
adai dai wannan lokacin ne sarki ya iso tareda dakarunsa
koda sukaga su jarumi zamnal sun gama kashe 'yan fashin
sai ya kamu da tsananin mamaki ya tsaya yana kallonsu
daga can sai ya karaso garesu koda ganin haka sai su jarumi zamnal suka durkusa suka gaisheshi
sarki marhus ya dubesu yace
yaku wadannan baki masu jarumtakar al'ajabi muna godiya
da taimakon da kukayi mana sannan kuma ina gayyatarku zuwa gidan sarautata domin karrama ku
dajin haka sai jarumi zamnal yayi charaf
yakai wannan sarki
muna godiya da wannan karramawa taka da kuma wacce mutanen ka sukayi mana
amma yanzu bamu da lokacinda zamu tsaya walima
saboda shugaban mu yana can yana jiranmu
kodajin haka sai sarki marhus yace waye shugaban naku?
jarumi zamnal saiya sake rissinawa yace
kayi hakuri ba zamu iya fada maka ba
amma nan da 'yan wasu shekaru masu zuwa kaida kanka zakasan shi
jarumi zamnal suka sukayi ban kwana dasu hasuf
sannan suka juya suka tafi suka bar birnin askandariya
tafiyar sa'a takwas sukayi kamar farko sannan suka isa sansanin su
da zuwa sai suka kwankwasa kofa
lokacinda suka kwankwasa kofa sai wani badakare yazo ya bude musu kofa suka shige
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA SU JARUMI ZAMNAL BAYAN SUN JE SUN SAYOWA GIMBIYA SUHAILA KEKEN DOKIN DA ZATA HA
BAKAR GABA
PART 10
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING
HABIBULLAH KBR
al'amarin su yarima saiman kuwa lokacinda
dodo garjaju ya kamasu ya kulle acikin keji ya
shiga dasu cikin gidan sarautarsa
bai zame
ko inaba sai cikin wani katon dakinsa wanda yake kulle masu manyan laifuka aciki
shidai wannan daki an ginashine da zallan duwatsun wuta
babu wata halitta data taba shiga cikinsa ta fito araye tun daga sanda aka gina wannan daki
yana zuwa sai ya ajiye su agefe daya amma bai fito dasu daga cikin wannan daki ba
sannan ya tsaya ya kura musu ido sosai yana kallonsu
koda ya kalli fuskar aljani markazulu sai fuskarsa ta fara gyatsine
kamar an aiko masa da sakon mutuwa saboda sanin cewa shine ya kashe masa dansa
nantake yaji kamar ya zura hannu acikin kejin ya zaro shi ya wulla abaki ya cinye
amma saiya fasa
saboda yasan babu abinda zaiyi ya huce bakin cikin daya darsa masa azuciya harsai yayi masa hukuncin da yayi alkawarin yi tun farko
sannan ya kalli yarima saiman yace
lallai wannan yaro anyi hatsabibin gaske tunda nake aduniya
ban taba haduwa da halittar da muka shafe dakiku biyar muna yaki da itaba face na hallaka ta
amma sai gashi na dau lokaci mai tsawo ina yaki da wannan karamin halittar inda badan nayi da gaskeba da zai iya samun nasara akaina
yana zuwa daidai nan azancen zucinsa saiya fice daga cikin dakin ya janyo kofa ya rufe
bayan fitarsa da kamar rabin sa'a sai su yarima saiman suka farfado
suna farfadowa sai suka tsinci kansu acikin kejin karfe
aljani markazulu ne ya fara farfadowa sannan saiman shima ya farfado
koda ya farfado kuma ya kalli gefensa yaga yarima saiman
kuma ga sarkoki an saka masa hannu da kafa sai
kuma ya tabbatar da cewa bazasu taba tsira ba daga sharrin dodo garjaju ba
sai nantake nadama tazo masa don ya fuskanci yarima saiman bazai iya cetonsa ba
koda yarima saiman yaga markazulu ya zurfafa cikin tunani
sai yayi murmurshi sannan ya dube shi yace
yakai abokina kaga yadda rayuwa ta juya damu ko?
to haka duniya take yau nasara tana gareka gobe kuma tana hannun waninka
abinda nake nufi dakai shine
duk sanda zakayi wani aiki kasa gaskiya acikin zuciyar ka
duk lokacin da ka sami wani aboki na zaman gida ko akan hanya ka zama mai gaskiya
'yan uwanka zasu zama masu kaunarka da girmamaka
afadin duniya munafuki baya zama mai nasara
mai gaskiya kuwa duk irin tsananin wahalar daya shiga baya taba faduwa kasa
don haka inaso ka sani tun afarkon tafiyar na san cewa
kazone da nufin ka tayani yakar dodo garjaju mu debo tsuminsa tare dakai
idan muka gama kai kuma sai kaci amanata ka kasheni
duk da yanzu nasan cewa kai da kanka kasan nafika duk irin abinda kake takama dashi
walau karfin damtse, iya yaki da sanin tuggunsa ko sihiri babu wanda ban fika ba domin ka gani da idanunka
duk wani motsi da kakeyi tamkar atafin hannuna kakeyinsa
to yanzu na fuskanci tunanin da kakeyi na nadama ne bisa ganin ni cewa ni dakai gaba daya zamu hallaka
ba tareda mun sami ribar komai ba acikin wannan tafiya
shin wannan hali daka shiga bazaisa kayi madaba
akan abinda kake shirinyi?
dajin haka sai hawaye ya zubowa markazulu yace
tabbas maganarka gaskiyace na yarda da duk abinda ka fada
kuma nayi nadama akan duk abubuwan danayi arayuwata
abu daya ne kawai banyi nadamarsa ba
wannan abu kuwa shine bijirewa boka ulumanu da nayi
tabbas boka ulumanu ya sakani zalunci wadanda bansan adadinsu ba
bansan adadin mutanen daya sakani na hallakabA
duk irin bakin halin dana kowa to awajensa na samo iliminsa
tabbas ko yanzu idan na mutu bazan taba yafe masa ba
yarima saiman ya tashi ya matso kusa da markazulu yadda suna iya kallon juna sannan yace
naji dadi da wannan magana taka amma ina mai tabbatar maka da cewa ni ba zan mutuba awannan gida
kuma kaima ba zan bari ka mutuba tare dakai zamu fita
dajin haka sai markazulu ya dubeshi cikin rashin yarda yace
tayaya kake maganar zamu fita daga nan alhalin nida kai duk mun zama fursunoni?
dajin wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan yace
ai tun daga lokacin dana bar gida na fara tanadin zuwan wannan rana don haka sai ka zuba idanu zaka gasgata zancena
suna cikin yin wannan saiga babban dan dodo garjaju nan ya shigo
wato jurishan tareda kannensa sunzo don suga halittun da suka wahalar da mahaifinsu akaron farko na rayuwarsa
koda suka gansu 'yan kananu sai suka bushe da dariya
suna nunasu da dan yatsa suna cewa wadannan sune suke ganin zasu iya ja da mahaifin mu
lallai sun yaudari kansu abubuwan da basufi mu sa kafa mu talitsesu ba
dajin haka sai ran markazulu ya baci yana daga cikin kejin ya tofawa wani dodo yawu afuska
da ganin haka sai ragowar dadannin suka fusata suka kafa zasu fasa kejin
sai suka jiyo mahaifinsu yana daka musu tsawa nan take kuwa suka dakata da abinda suke shirin yi
garjaju ya karaso gabansu ya kwadawa jurishan mari
sannan yace daga yau kada ka sake janyo 'yan uwanka
ka kawo su gurin wadannan fursunoni domin suna da matukar hatsari
koda kannen jurishan sukaga yadda mahaifinsu
ya zabgawa jurishan mari duk sai suka kyalkyale da dariya
alokacinda shikuma hawaye ya zubo masa kenan
sannan ya juya ya fice daga cikin dakin
mahaifinsu yana biye dasu abaya sannan ya janyo kofa ya rufe
fitarsu keda wuya sai saiman ya dubi markazulu yace
kaga wannan abu daya faru?
markazulu yace wannan wacce irin tambaya ce ni da ba makaho bane taya zan kasa ganin abinda akayi
saiman yace to duk wannan da kake gani yana daga cikin irin tsare tsaren da nayi akan wannan tafiya
nan gaba shi da kansa zai dawo nan domin mu hada kai dashi
kuma ka zuba ido ka ga abinda zai faru
haka dai sukayita fadi in fada har dare yayi barci ya sacesu basu saniba
al'amarin dodo jurishan kuwa lokacin da suka
fito daga cikin dakin tsaron fursunoni saiya wuce
izuwa bayan gidan sarautar tasu cikin bacin ran
abinda mahaifinsu yayi masa agaban kannensa da kuma yadda suka dinga kyalkyala masa dariya
sai hawaye ya zubo masa yace amatsayina na babba a wannan masarauta ni mahaifina zaiyi wa haka alhalin
ko a yau ya mutu nine zan haye kan karagar mulkin kasar nan
lallai sai mahaifina ya gane kuskurensa sai dai inyaso ayi biyu babu
ko dai ni na hallaka ko shi mahaifin namu ya mutu
ni ban damu da wata karagarsa abinda na damu
dashi kawai kimata da mutuncina dolene mahaifina
yayi nadamar abinda yayi mini
yana zuwa daidai nan azancen zucinsa sai
ya mike tsaye ya koma cikin gidan sarautar kai tsaye ya wuce izuwa cikin dakin da aka kulle su yarima saiman ya bude ya shiga ciki
yana zuwa sai ya tarar dasu duk sunyi barci ya zura hannunsa
ya tabasu suka farka daga barcin da sukeyi
firgigit cikin tsoro aljani markazulu ya mike domin azatonsa kashe su dodo jurishan yayi
koda ganin haka sai yarima saiman yayi murmushi sannan ya ruko hannunsa yace
ka nutsu mana tsoron me kake ji ka nutsu kaga abinda yazo dashi mana
dodo jurishan ya kallesu cikin nutsuwa yace
yaku wadannan jarumai ku kwantar da hankalinku
nasan duk irin bukatarda kuke da ita kuma ni zan taimaka muku don na huce bakin cikin abinda mahaifina yayi mini
ammafa ku sani koda na same ku sani koda na samo muku shi dale sai kunyi da gaske wajen kasheshi domin ba karamin hatsabibi bane
koda jin wannan batu sai yarima saiman yace
yakai jurishan nasan cewa kai kana da sabanin ra'ayi da mahaifinka
don haka nayi maka alkawarin idan har ka samo mana tsumin tsafinsa
ba zamu bari ka hallakaba kuma kaine zaka gajeshi
dajin haka sai jurishan yayi murmushi yace
ni koda ban sami gadon mahaifina ba abinda nake da bukata kawai shine ku hallakashi
domin mu huta da bakin mulkin da ya dade yana yi mana
yana zuwa nan azancensa saiya juya ya fice daga cikin dakin
fitarsa keda wuya sai yarima saiman ya kalli markazulu yace
na dade da cusa kiyayyar dodo garjaju azuciyar dansa jurishan
domin tun sanda muka baro gida nake tura masa da mugayen labarai akan mahaifinsa
sannan na sanar dashi cewa mahaifinsu ne ya kashe mahaifiyarsu
amma duk wannan abu da nakeyi ban taba zuwa masa acikin siffata ba
ina zuwa ne awata siffar daban bana zuwar masa a siffata
don haka jurishan shine zai zama makamin mu awannan lokaci
al'amarin dodo jurishan kuwa lokacin da ya fita daga dakin tsaron da aka kulle su yarima saiman
sai ya wuce izuwa dakin da mahaifinsu ya ajiye tsumin tsafinsa
shidai wannan daki yana wani bangare ne na cikin gidan
babu mai iya shiga cikinsa sai 'ya 'yan dodo garjaju domin ya lamuncewa kowa ya shiga ciki yayi duk abinda

Please Login or Register in order to submit comment